Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

qarfi ne tun kafin a haife mu
akeyinshi, sai nake ganin kamar wuta za a qara
ma lamarin, tunda duk basu jituwa bane,
maganin kar a fara kar ayi, Baba Hassan ya
girgiza kai yace aa ina ga hakan ne maslaha a
cikin wannan gaban, dole muke kawo qarshen
wannan Gaban kuma inaga wannan ce hanyar da
zai sa a samu sulhu, So ina ga Baba hakan daidai
ne, Baba Gambo yace Hakan daidai ne kuwa
baba, sai dai a roqa Allah ya daidaita tsakanin
mu duka, M.Zailani yace Hussaini ka fahimci
abun da Yayanka yace? Baba Hussaini ya gyada
kai, yace wannan gaskia ne, daman bawai naqa
bane ina gani kamar ba za a daidaita ba, baba
hassan yace always pray for d best broda. Yace
toh Allah ya sa mu ga da kyau. M.Zailani yace
toh shkn tunda har kun amince da Raayina.
Hakan zaayi (ni nace me zaayi tsoho? Harara ya
wurgo ni da ita)

********
Maysah da Tsoho suna zagaya gida, ya na bata
labarin Soyayyar shi da Aishalle, tana ta daria
yace muje mu kaima Yayanki Ziyara, Tace
wanne daga ciki? Yace muje dai, rabon da Tsoho
yazo bangaren samari Har mantuwa ta manta,
kai tsaye dakin farko ya qwanqwasa ya shiga,
Zayd ne kwance da fara singileti ba bacci yakeyi
ba amma daga ganinshi buge yake, ga kwalbar
giya ta Gulder da Star ya shanye, Gefenshi
Diyya ce kwance tana bacci, Tsoho firgici
Maysah firgici, tsaf tagane wanda tayi fada da
amira ce shekaran jiya, lallai Abun Yazayd ya
girmama, har gadon baccinshi yake kawaota,
Allah ya shirya! A hankali Tsoho yace Giyah? Ga
mace Kwance a cikin Gidana? Inalillahi wa ina
ilaihir rajiun, Zayd ya miqe duk da ya dan
tsorata amma da yake dan dunia yace me ran
qarfe lafia ka shigo Sassan mu? Ko nema na
kakeyi? Tsoho ya share yace ziyara kawai na
kawo ma, Amma bari muje kafin ya ce komai
Maysah ta riga tsoho fita, jikinta rawa yakeyi,
har suka koma Sassan tsoho basu tanka wa Juna
ba, Duk Zuri'ata Zaidu kaine Daban Allah ya
shiryaka Dole na muku Aure, dole nake aurar
daku duka, Ya Allah kai mana da kyau.
******
Fadila da Suraj a dakin hajia Ama suna Soyewa,
tana zuba mai shagwaba Wai gaskia ba zai tafi
kano week din nan ba, yace baby kiyi hqr so
kike a koreni a wajen aiki? Tace ba sai a maka
transfer ba? Yace ina kike so mu zauna idan
munyi aure? Ta daga kai sama tana tunani tace
Kaduna, yace daman tunanin mu daya, kar ki
damu da hannuna na zana gida a kaduna har an
fara gini fadila tayi ihun murna tace thank u
mysuraj, Sarkin Gida ne ya shigo da Sallama
yace Tsoho na kiran ku, suraj yace mu suwa?
Yace dukkan ku na cikin dakin nan, har da Hajia
Ama, taro ne na gaggawa, suraj yace toufa Allah
ya sa lapya, fadila gaya ma su hajia a ciki da su
Islah, aka sanar dasu duka. Kowa ya Hallara
abun mamaki harda yayyinsu da matansu da
sukayi aure na nesa ne kawai babu to lapya inji
Islah?duk suka zazzauna, One by One tsoho ke
kallonsu, daga matayensa zuwa yaransa zuwa
jikoki harda masu musu Abincin GANDU, Tsoho
ya gyara Murya Ina Zaidu?? Jawad yayi qarfin
halin cewa yana Dakih, be ji aikena bane? Jawad
ya miqe bari na kirashi, yace kai Jawad Zauna,
Ya kalli inda mata suke yace RUMAH jeki kira
yayanki Zaid, gabanta ya fadi haka ta miqe tayi

Sassan Samari, ta kusa minti 5 tana tunannin
yanda zata shiga dakin, sai tayi jihadin Sallama
da qarfih, fitowanshi wanka kenan, daga shi sai
towel, yace waye? Shigo, ta shiga saurin rintse
ido tayi, ya daure fuska ke Lapya? Uban me ya
kawo ki dakinah? Tace kayi haquri, Tsoho ke
kiranka, kowa na chan kai kadai ake jirah, tana
kai wa nan tayi saurin fita yayi dan jimm tabbas
ya san meeting din nan nashi ne, ya dan firgita
amma dayake namijin dunia ne ya dake ya zira
jallabiyansa yayi cikin gida da takunsa. Ya shiga
wakeken parlorn da Sallama, Gabanshi ya fai
ganin idanuwa akansa, duk ya tsargu ya sha jinin
jikinsa, kusa da Jawad Ya zauna.
Tsoho yayi Bismillah tare da guntun
muqqadima da sallama duk aka amsa mai, Ya
fara cikin maganarsa ta manya : Ahh, batare da
bata lokaci ba, kamar yadda kuka sani a wannan
Zuriah tawa, idan Namiji ya fara aiki, Mace ta
gama sakandire ana masu aure, kuma ni ke
zaban musu mataye da mazaje, kuma DOLE abi
umarni nah, kasancewar ina da Zuriah da yawa
nake hada aure uku uku, ko hudu hudu wata
sain har biyar biyar, wannan abu ne da kuka
sani ba sai na dinga nanata shi ba a duk lokacin
da zanyi hadi, Bana Zaa aurar da Mutane 12,
maza 6 mata 6, gaban Masoyan nan 12 yabada
HINGIM, fargaba ya shiga zuciyoyinsu, kunsan
dai duk maganar da na yanke ta zauna, ko da
yake ban yi tsammanin musu daga daya daga
cikinku ba don na san kunsan Qaidojin Gidan
nan, ba a soyayyah ko auren bare, wacce ko
wanda M.Zailani ya zaba shine magana.
Gabansu ya sake yankewa ya fadi Tsoho ya
cigaba da jawabi, Toh na riga nayi tsarina kamar
haka ; ZAYYAD na baka HANIFA, SAMIR na baka
AMIRAH SURAJ na baka BILKISU MU'AMMAR na
baka ISLAHULKHAIR, JAWAD na baka FADILA,
ZAYD na baka RUMAYSAH. Tashin hankali,
Firgici, Rudani, Kurumta, Makanta, Bebanci ya
dirar ma Masoyan nan 12lokaci Guda ba sa gane
komai ba sa jin komai ba sa fahimtar komai ba
kuma sa ganin komai...
Shin wannan Hadin Zaiyiwu?
Shin Wannan Gaba zata tsaya kuwa?
Shin Akwai Sulhu tsakanin yan Dakin Hajia
babba, da Dakin Ama da na kuma Umma Hajja?
👻This is just the Beginning👻
A Cigaba??
1⃣7🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕
⃣ GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee 💕Biebee Isa💕Parlorn yayi
tsit kamar ba kowa cikinta sai qarar fanka,
Tsoho ya cigaba da magana, kuma zaa daura

auren nan ranar jumaah me zuwa ma'ana nan
da kwana 7, firgigit suka dawo hayyacinsu kallo
daya zaka masu duka zaka ga tashin hankali a
fuskokinsu, Jawad ke maimaita sunan fadila a
bayyane tare da kallon inda yammatan ke
zaune kuka yaga rabin ransa bilkisu keyi,
zuciyarsa ya hau zafi da ya hango fadila rakube
tana cizgar kuka, lokaci daya ya tuna rashin
kunya ta da shirga mishi, nan da nan haushin ta
da tsanarta suka darsu a ransa da sauri ya
girgiza kai wlh ba zaiyuwu ba da sake.
A bangaren Mua'amar kuwa Tunani yake yama
za ayi ya auri watan da ba Hanifa ba, ai ba zai
mayuwu ba da sauri ya rarafa gaban tsoho tare
da ririqe mai kafa, yace tsoho, kar kayi mun
haka, ka taimakeni ka bani Haneefa, haneefa ce
rayuwata. Baba Mudassir yace kai Mua'amar
meye haka?Tsoho ya daga ma baba mudassir
hannu yace, barshi ya gama, ina jinka Amar, ko
kunya be jiba ya cigaba da cewa tsoho ka
taimakeni, kaji tausayina ya qarashe fadi tare
da kuka me zafih da ya kubce masa, Tsoho ya
shafi kanshi a hankali yace kayi haquri, na san
menakeyi, Wata rana zakayi Alfahari da wannan
hadin nawa, Girgixa kansa yayi da qarfi tare da
runtse idanuwa, Samir ma ya matso yace tsoho
danAllah kar ka rabani da Islahulkhair ya xa ayi
ka hadani da Amira? Damm gaban Amira ya
yanke ya fadi, bata qin samir hasalima ita bata
yi baqincikin wannan hadin ba, fargabanta daya
Samir Islah yakeso, to idan samir ya qita to wa
zai sota? Suraj zaiyi magana Baba Hassan ya
wurga musu harara shi da Zayyad ba shiri
sukayi gum, Shi ko Namijin duniya wato Zaid,
ko a jikinsa don ya san wannan abu ba zai yuwu
ba, ya ma xaayi ya auri wannan qaramar
yarinya? In short ba me mun auren dole, ni
banda mata da ta wuce badiyya so tsoho ma zai
tashi daga wannan mafarki coz it will never
happen.****
Tsoho ya bi su duka da Ido, Kuka sukeyi ba
mazan ba ba matan ba, Idonshi ya tsaya kan
Ruma ganin hawaye kwance kan fuskar Maysah
yasa zuciyarsa sosuwa, ya furta a hankali Rumah
zo nan, a hankali ta miqe ta nufa gunsa, yace
Rumah me ya saki kuka? Rumah bakya son
wanda na baki? Kuka me tsuma rai ta fashe da
shi. A hankali daidai yanda zaijita taceTsoho kar
ka mun haka, ya zaayi ka hadani da Yazayd?
Tsoho ko ka manta rannan da-- da sauri ya
katseta ta hanyar sa hannu a bakinshi, ta girgiza
kai, ta dan daga murya ba zan yarda ba tsoho,

ba zan yarda ba, Mashayi? Mazi--- tasss kakeji,
Baba Abbakar ya kasheta da mari, abunda be
taba yi mata ba kenan, Maysah ta dago
idanuwanta da suka rine sukayi jazir ta kalli
babanta, a hankali tace Appa ya nuna ta da
yatsa, yace ke kin isa Tsoho yayi miki zabi kice
ba kyaso? Toh idan ni na haifeki baki da mijin
da ya wuce Zaid, sai anyi auren nan, sai dai ki
mutu Rumaysa, cikin isa da gadara Zaid yace
wai wani zaid din? Ni fa ba zan auri wata yarinya
a dangi ba, ina da wacce nakeso, Uncle Abbakar
ya wurga mai wani mugun kallo, duk
tsagerancin Zaid sai da ya ji shakkun Babban
Maysah. Hajia Babba dake zaune ta gama cika
pal, tace ai ba qarya yayi ba, duk cikin wannan
hadi ba wanda xaiyuwu, babu yanda xaayi ni ko
jikokina su hada iri da dangi Aljanu da Mayu, to
Alhaji tun wuri ka chanza wannan maganar don
wallahi ba zaiyuwu ba, wannan maganar
maganar nosense ce, maganar banza, jikana ya
auri jikar Hajjo ko Aishalle? Sai dai a mafarki
wollai, Parlorn yayi shiru, ta inda Hajia babba
ke shiga ba ta nan ta ke fita ba, sai bambami
take tayi. Kowa ya xuba mata ido, sai zagezage
take tayi, Miqewa yayi Qyam sakamakkon jin
kanshi da ya sara Qirjin shi ya shiga yi mai zafih
ya sa hannu ya dafe, ba wanda ya lura dashi don
hankaliksu na chan gun Hajia Babba da ke ta
faman masifa ita ba zata hada iri da dangin
mayu da Aljanu ba , Hanyar Qofa ya nufa
hannunsa dafe da qirjinsa, ji yayi qaffafuwansa
sun gaxa daukar sa jiri ya fara dibarsa, sai ji
suke Timmm Tsoho ya Xube qasa, nan aka shiga
rigerigen nufan inda tsoho yake, Baba Hassan
ne ya sa hannu wurin hancinsa be ji tiririn
nishinsa ba, cikin kaduwa ya ce A dauko mota,
Jawad Zaid Muammar Suraj da Samir ne suka
fita da gudu don dauko mota hankalin su Ya
tashi ganin ba alamun Numfashi tattare da
tsoho, Suko matan kuka suka sa barin ma
Maysah, ita ko Hajia Babba kuwa kururwa take
tana cewa waiyo Mallam Kar ka mutu ka barni,
kayi haquri kar baqin cikinmu ya kasheka, ka
tashi Mallam. Baba Usman ne yace haba Hajia
ce miki akayi ya mutu? Tayi saurin cewa Auuu
be mutu ba? Be tanka ta ba anan ne Suraj Ya
shigo ya ce baba ga motan nan gaban parlor,
nan su jawad suka shigo ko wannensu ya dauko
motarsa, nan Zaid ya cicibe tsoho shi kadai yayi
wajeh dashi, bayan motan da ke parke gab da
parlon ya shimfideshi a baya, kowa ya samu
mota ya shiga Suraj kuwa da Tsoho ke bayna

motarsa ya zagaya ya ja Motar sai Asibitin Dr
Munnir na Alheri Hospital. Convoy akayi,
saboda kidima Hajia babba da Hajia Ama, da
Umma Hajja mota daya suka shiga, motar Zaid,
Iya rudewa sun rude, hajia Ama da Umma hajja
dai hawaye suke don tun rasuwar Baba Rabi'u
basu qara ganin tashin hankali ba irin na yau,
ita kuwa Hajia Babba bata fasa ihu ba tana Allah
kar ka kashe Alhaji, Allah ka raya shi, Waiyo ni
karime, Zaidu ba a iso bane? Zaid da ya qulu
sosai, yana son Tsoho sosai yana fargaban rasa
shi amma wannan matar ta cika mai kunne,
tsawa ya daka mata yace idan ba ki min shiru ba
zan zubar dake a nan, da sauri ta kama bakinta.
*****
Islah a bayan mota riqe da hannun Maysah riqe
da hannun Fadila a bayan motan Samir, Amira
na gaba kowannen su Hawaye ke bin kuncinsu,
tunda suke a rayuwansu ko ciwon kai basu taba
ganin yayi ba. Amma yau shine harda yanke jiki
ya fadi, Suna cikin matsanancin tashin hankali
wanda roqonsu Allah ya tashi kafadar
Tsohonsu..
***
Ko da suka isa Asibitin Already Dr's and Nurses
na jiran su a entrance don tun a hanya Baba
Gambo ya kira Dr Munnir ya Sanar dashi komi.
A haka aka daura tsoho a kan gado aka jashi
zuwa A&E wato Accident and Emergency. Tsoho
Allah sa a Dace
1⃣8⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu by🏠by 💕Biebee Isa💕 💕Biebee Isa💕Biebee💕Biebee Isa💕 Da sauri Liktoci
suka du'kufa gurin ceto ran tsoho, Zuriarsa na
wajeh hankalin su tashe yake, kowa da kallan
tunanin da yake, Hajia Babba sai kai kawo take
binibini ta lewa dakihn, Hajia Ama kuwa ta
kame guri guda da tsura ma dakin ido, bayan
kamar rabin awa, Dr Munnir ya fito yana shar'ce
gumi, da sauri suka xagaye shi, ya kallesu ya
girgiza kai, yace ku muje office. Har wasu dai
suka riga Dr shiga ofishin shi, nan da aka
zazzauna, wasu kuma na tsaiytssye don duk
Girman Opishin Dr ya gaza dauke Iyalan
Zailani.. Dr ya kalli Manyan Yarsn Tsoho, Yace ya
akayi haka? Su Baba Hassan duk suka zaro ido?
Yace ya kuka bar Ciwon Zuciya ya ma Tsoho
mummunan kamu farat daya? Duk suka dau
sallalami, Ya kuka yi wannan sake? Hajia Babba
tace wlh baqin cikin mu ne, Waiyo ni kaina. Zaid
ya watsa mata mugun harara, ya cigaba da
cewa, munsamu mun shawo kan matsalan da
qyar. toh gaskia Dole ku kiyaye bacin ran sa,
dole kuke mai abubuwan da yakeso, nd ku

nisantar da shi daga abubuwan da baya so, Nd
dolenku kumai abun da yakeso kafin ya farfado,
don gudun hakan na iya sa wa zuciyarsa ta buga
farat daya. Gaban kowan nensu ya fadi,
Mu'ammar ya girgiza kai ya fita daga dakin,
Jawad ya bishi hakan nan Zaid. Duk aka bisu da
ido, Dr yace idan kuma kun gaji da hidimar sa
tunda ya tsufa ku barshi kawai ya mutu, Hajia
babba ta zunduma uwar ashar, Dr kaci Kwal
Ubanka, mu barshi ya mutu fa kace? Yace
ahtoh, ai don ina ganin abunda ya ke so me
girma ne, ba zaiyuwu ba, tace Dole kuwa zai
yuwu, dole a aurar dasu ga maqiyansu,. Ke kima
waanan jikokin naki magana, dole suke aurensu
ba don na so ba, sai don ceto ran Mallam. Ta
miqe tare da fadin tashi dan Usmanu, muje mu
ga yaran nan. Balki ku biyo mu duk suka bi
bayanta jiki a sanyaye, ya rage daga Zuriar
Umma hajja sai na hajia Ama cikin ofisihn Dr.
Dr ya miqe yace toh bari na barku ku zanta.
*****
Ai wallahi ba zan yarda na auri wata Islahulkhair
ba, Ya zaayi ma hakan? Da sauri Aunty Sadiya ta
riqi danta tace Amar baka fini Tsanar wannan
hadin ba ban qi ayi tashin hankali ba don a fasa
auren nan, but bamu da choice, i love my
Father, i cant watch him die, please sonn, u nd
bilkis will listen to me and marry dem for a
short period of time, da Yaji sauqi xaka saketa
ka auri Hanifar ka kaji? Kema dole muke matsa
ma Suraj ya sakeki kinji? Bilkisu ta na kuka tace
indai wannan zaisa Tsoho ya tashi ya ji sauqi toh
wlh ko waye xan aure shi. Aunty Sadiya ta
rungumeta yau diyata. Its just for a short
period of time. Aunty Abida ta kalli nata yaran
tace dat goes same for d u three, Zaid, Jawad,
Hanifa bama son wannan hadin but we love our
Father. Shine Gatanmu da duk wanda muke
taqama dashi. We cant let him die. I knw y'll
love Tsoho nd Ya'll sacrifice for him ryt suka
gyada kai, then do dis for him okay? Nd
remember its just for a short period of time...
Aunty Zainab rungume take da dants Samir
daga chan gefe Baba Gambo na kallonsu cike da
takaici, kuka ko Samir kamar mace? Amirar
Annoba ce? Aunty Zainab ta kalleshi ta mai
Alaman ya fita, Baba Gambo yayi gaba. Ta shafa
summar kansa tace *Samir* yace Mami kiyi
shiru, dole zan Auri Amira don ceto ran tsoho
Amma dole zanyi kukan rabuwa da Islah.
Mamin tace haba Samir, abunda yayi Islah shi
yayi Meerah, ka duba ka gani, da sauri yace wlh

shes nothing like dat-- yi shiru mana. There are
times da zaka so abu sai Allah ya hanaka don ba
Alheri bane a gareka, sai ya Musanya maka da
abun da yafi Xama Alheri, Maybe Islah ba
Alheri bace a gareka, Maybe Amirar ce Alheri,
kuma ita Allah Ya tsagaa rabonka da ita. Think
wise son, u are d bravest i've ever seen, ya
qirqiro murmushi yace i will marry Amira. Tayi
murmushi tasan ba ya amince da Amira ba ne
Aa sai dai don kawai ya faranta ran maminsa.
****
Toh ni ba sai nace muku komai ba, duk nan kun
mallake hankulanku, nd kunsan whats right, so i
trust u to do the right thing, Baba Hassan ne ke
wannan maganar.Umma Hajja tace ai na san
Yan jikoki na da ladabi da biyayya, masu son
Farincikin Uwayensu, nasan ba zasu bar son
zuciyarsu ya shiga cikin wannan Lamarin ba,
Baba Hussaini yace toh ya kuka ce? Hajia Ama
tace ai nasan jikokinmu sun Amince, don suna
son wannan tsohonsu sosai koh? Rumaisah tace
idan akwai wanda yafi makaho makanta, kurma
kurumta gurgu gurgunta, zan aureshi don ceto
ran tsoho, wanda ya soni ya qaunace ni, Fadila
ta kalli Suraj, tace nima na amince zan auri
YaJawad duk da na san aurensa baraza na ne a
kaina, Amma ina son Tsoho sosai, dole nake
haqura na ba Tsoho abunda zaisa sa farinciki.
Islah na matsar kwallah tace Zan auri Ya Jawad.
Zayyad yayi karaf yace muma mun Amince
zamu auri Hanifa da Bilkis Allah ya sa hakan yafi
zama Alheri Aka Amsa da Amin. Hajia Ama ta
kalli Baba hussain tace na gaya muku yan
jikokina Akwai ladabi Biyyaya. Yace ai nagani
Allah muku Albarka Ameen...
Hajia Babba ta shigo da zurianta a bayanta
fuskokinsu murtuk, suka zazzauna. Dr Yashigo
yace toh duk kun shirya ba Tsohonku abun da
yakeso? Sukace Ehhh. Yace toh MashaAllah.
Allah ya tashi kafadun shi. Yace kuma a barshi
ya huta, yana so kowannensu yaje gida don be
son hayaniya. Haka Baba Hassan ya sa aka
tattarasu akwa maida Gida. Da qyar Hajia Babba
ta amince zata tafih. Daga shi Sai Baba Ussaini
suka tsaya...
GASKIAN LAMARIN.
Kwana 2 kafin (2days Back)
TSOHO zaune da Family Doctor dinshi Dr
Munnir, kuma amininsa wanda ya san duka
Sirrin Tsoho da yanayin GIDAN GANDUnsu, ,
amma Tsoho ya girme mishi nesa ba kusa ba,
don ko tsaran su Baba hassan ne, Tsoho yace Dr

bansan yanda za'ayi yi na hada auren nan ba,
don kasan dan yanzu ka haifeshi ba ka haifi
halinsa ba, suna iya bijire mun suce tunds basu
na haifa ba zasu mun rashin ta ido balle
dukkansu soyyaya suke, toh ina tsoron su ki
Amincewa. Dr ya nisa yace Akwai Shawara idan
zaka iya, Tsoho yace me ke nan? Dr ya sausauta
murya ya ma tsoho qusqus a hankali me kama
da rada, Tsoho yayi daria yace hakan ma zaayi,
ta wannan hanyan zan magance duk wata
matsalata. Zanga idan Zasuyi man Hallacin na,
Zangani idan ina da mahimmanci a rayuwansu,
naji dadin shawarar nan amma taya zanyi na
zube qasa har na dauke numfashi na? Yace kar
ka damu, akwai maganin da zan baka ka sha, be
da illa. Zai taimaka maka gun aiwatar da
qudurinka, kuma idan aka kawo ka asibiti, da
drip din da Allurorin da zaka sha duk masu
Amfani ne ga me lafiyayyen jiki kamar su
Bcomplex d.s. so kar ka damu, ba abun da zai
shafi Lafiarka. Tsoho yayi murmushi yace
nagode likita Allah ya sa mu dace yace
Amin...Toufa jamaaa kuna jin wannan plan din
na Tsoho? Duk yabi ya tada ma Zuriarsa hankali🤔🤔
nidai nace kaiii Tsohon nan Namijin Duniya ne👻.
_Bibilicious Biebee_
1⃣9⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 Gandu Gandu 🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Sai da Tsoho
yayi Baccin Awa12 kafin Maganin bacci ya sake
shi, A lokacin Daga Dr sai Baba Yan 3, Dr
munnir yazo yana duba shi, DrMunnir ya kashe
ma tsoho ido alamun komai daidai. Sai yace
MashaAllah jiki ta warware, ina ma iys
sallamanka. Amma zan barka ka dan huta,
Tsoho yace me zai zaunar danih tunda naji
sauqi kunsan da ina cikin hayyacina ai da ba a
kawo ni nan ba. Dr yayi daria yace haka ne. Nan
ya rubuta musu takadar Sallamah, Baba Hassan
ya kira Suraj yace kazo kai maida mu Gida.
*****
Kowa yayi murnan ganin tsoho ya tako da
Kafarsa. Barin ma maysah da take kukan
murna, don ta ba Tsoho mutuwa. Sashensa yayi
Hajia Babba sai rawan Jikin Alhaji me kake so?
Alhaji me za a maka? Yace wanka zaiyi, nan
BabaAbbakar ya umurce kowa da a bar Tsoho ya
huta...
WASHEGARI
Tun daga nesa ta hangoshi bataso ya cimmata
sai ta qara sauri, tun jiya take avoiding dinshi,
da gudu ya tankarota, yana kiran Fadila, haba
Fadila ki tsaya mana, Ya qaraso, Fadila y are u
avoiding me? Tace Ya Suraj yace shhh, fadila

Tsoho ya ji sauki, ba abunda ke damunshi ynz,
lets run, lets leave dis place, muje wani wuri a
daura mana Aure, i cant do without u, kukan da
take boye ya kubuce, sai da tayi me isarta ba
tare da ya hanata ba ta girgiza mai kai, tace
Yasuraj wallahi tallahi ina sonka, zan auri Ya
Jawad and zaka auri Bilkis, idan muka gudu,
mukaje aka daura mana aure me mu kayi
kenan? Mu bijire ma iyayen mu? Bakin cikin mu
ya kashe tsoho? Gaban ya cigaba da wanzuwa
frm generation to generation? If we leave, they
will be seperated forever, maybe this f only
way to End our Family's Malice, Ka roki Allah ya
sa hakan yafi Alheri, And Allah ya ba mu ikon
rungumar wannan Kaddarar, tana kaiwa nan ta
ruga da gudu. Tayi sashensu, A hanya ta ci karo
da Bilkisu da ta fito daga Sashen Tsoho, taja ta
tsaya, Bilkisu na watsa mata harara, tace listen
to me Fadila kar ki ga kamar Gobe Zaki zama
Mallakin Yajawad kice zaki zake, ki kira kanki
matarshi, to bari kiji Yajawad nawa ne, Aurenku
suna ne kingane? na dan wani lokaci ne, idan
komai ya daidaita zai sakeki ya aureni, so i want
u to keep ur distance, ban yarda ayi seducing
masoyina ba. Fadila tayi murmushi ta shar
hawayenta. Tace Bilkisu bana son Jawad bana
kaunarsa toh mesa xanyi tunanin Jan hankalinsa
ko ra'ayinsa? Kuma da kike cewa nan ba da
jimawa ba zai sakeni, kin ga na miki kama da
wadda zata zama bazawara in future? in kinso ki
ka she aurenki ki zama bazawara, ki sami wani
miji amma badai Jawad ba, i dont love him but
i will make sure dat he never ever gets back to
u get dis into your thick skull Jawad ya miki
nisa. tayi gaba ta barta bakih bude tana
mamakin karfin Halin fadila ita da ba sonsa take
ba.
*****
Islahulkhiar kwance a green carpet din field din
Gidan idonta lumshe, tana tuna moments dinta
da Samir, time din da suke kwallo, ko kwallon
kwando ko skipping rope, Maganar Hajja Ama
ta tuna inda take cewa _kuyi haquri da wa'enda
aka zaba muku, ku roki Allah ya sa sune Alheri,
ku Maida Soyayyar masoyan ku a kansu, ku
maida Soyayyar Masoyanku Soyayyar
yanuwantaka don ku Yanuwan juna ne Allah
muku Albarka_ islah ta matse hawaye tace Allah
kasa Ya Mu'ammar shine Alheri a gareni. Tsaki
taji an buga tsuuu Ta na dagowa taga Amira da
Hanifa. Amira tace lallai kam kin ma kanki
Kiyamul laili, gwanda da kika haqura da

Yasamir, don nice matar da aka zaba mai.
Gwara da kika dangana Allah hada kanku da Ya
Mu'ammar din Islah ta girgiza kanta ta miqe ta
kakkabe jikinta tayi gaba don bata son hayaniya.
Hanifa da qarfi tace aikin banza, ko me zakiyi Ya
Mu'ammar ba zai taba sonki ba, ni yake so ni
kadai, jini na ke gudana a zuciyan shi, da komi
ya daidaita zai sakeki ya aureni, dan ba zai taba
hada iri da dangin mayu da aljanu ba. Chak
Islah ta tsaya, kamar ba zata yi magana ba kuma
sai ta dawo da baya, ta tsaya Daf da Hanifa tace,
Wai tada jijiyoyin wuya na meye ne? Naga dai
tsoho ya san dake ya zaba mishi ni? Duk da jinin
naki na gudana a jikinshi, ki bari ya sakeni mana
yazo ya aureki kafin ki gaya min magana, but as
far as m concerned ni zai aura Gobe, nd m d
choosed person its not my fault dat m more
beautiful and talented dan u, its not my fault
dat i'm chosen for him, so Maybe tsoho ya ga
rashin dacewar ku ne ya zaba mishi ni, if u have
a problem go meet Tsoho, amma idan zaki bi
shawara ta, ki koya ma kanki Son YaZayyad don
Ya Muammar will never ever come back to u,
tana kaiwa nan tayi gaba ta barsu baki sake,
chan kuma Amira ta pashe da daria, kaii ashe
Islah na da baki haka? Wai its not her fault😂 wato wato
shes more talented nd more beautiful dan u,
ooo Islah got attitude, Hanifa takaici goma da
ashirin, ashe wannan haka take? Ai bata taba
zatan zata tanka mata ba, Ga haushin darian
mugunta da Amira ke mata. Ji tayi kamar ta sa
Ihu don takaici.
********
A yau Jummaa Wurin Huduba Liman yayi
sanarwa za a Daura auren Jikokin me Masallacin
nan, ana buqatar kowa ya tsaya bayan an Idar
da Sallan Jummah. Haka kuwa akayi, ana Idarwa
aka daura Auren ZAYYAD da HANIFA, ZAID da
RUMAISAH, JAWAD da FADILA SURAJ da
BILKIS, SAMIR da AMIRA da kuma MU'AMMAR
da ISLAHULKHAIR bisa Sadaki dubu Hamsin
lakadan ba Ajalan ba, aka shafa kuma aka
wadata su da Rengem na shinkafa(lol) Tsoho
baki har kunne, Angwayen kuwa kadaran
kadahan duk da Mu'ammar da Jawad ba su
tsaya daurin auren ba. Nidai nace oho dai an
riga da an daura. Ko da ku ko baku sai da Tsoho
ya Daura muku aure👻
_Bibilicious Biebee_
2⃣0⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Daren da
Aka daura Auren abu dunia ya ishe Sabin
maauratan, da Angwaye musamman Amaren,

daga Zaid sai Amira kadai ne basu da wata
damuwa sosai ko wannensu na sashensu jikinsu
duk yayi sanyi.
Kuka wiwi Rumaysa keyi, Shikenan me afkuwa
ta afku, YaZayyad ya mata nisa, yanxu YaZayd
ne mijin ta. Allah ka ba ni ikon Cin wannan
Jarabawar. Amma ce ta dafata da sauri ta share
hawayenta don bata so Amma taga kukanta
hankalinta na iya tashi, Amma ta mata
murmushi cikin hausarta da har yau be fita tace
Maysah kuka kike yi koh?
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment