Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

su sake haihuwa ba. Maryam
din Ama na da shekara 7 Hajjo ta qara haifan
Yan biyu mata, Hassana da Hussaina, Aishalle
kam kamar ita aka ma haihuwan nan murna
kamar mene, tace wlh Yaya Hajjo ke er baiwa
ce, daga yan uku sai yan biyu dama ni, tace
kema Allah xai baki....
*****
Hannun hajjo saqale da nashi, kuka take tayi jin
abun da ke fita daga bakin mijinta, Hajjo na so
na zame miki Gata har qarshen rayuwarki,
amma da alamu kwanana yana gab da qarewa,
tace wai rabiu me kake cewa haka? Cuta ba
mutuwa ba fa? Hajjo kenan sati biyu kenan ina
fama da ciwon cikin nan, nidai dan Allah kayi
shiru, Hassan ne da qanenshi suka shigo dakin
ganin mahaifansu na kuka yasa suma suka fara
kuka, Da qyar rabiu yace hassan Allah muku
Albarka, jeka kira mun babanka, da gudu ya
fita sai gashi ya dawo da Musbahu da Aishalle a
rude, Asha Rabiu ciwon ne haka? Sannu yace
yaya ka yafe man idan na taba bata maka, Yaya
ga Amanar iyalai na, na san zaka kula mun dasu,
Kafin Musbahu yace wani abu rabiu ya cika yace
ga garin ku nan, Tashin hankali.
4⃣🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Inalillahi wa
ina ilaihir rajiun, shi ne abunda Musbahu ke
maimaitawa, Hajjo kuwa don rudu kasa kuka
tayi, Musbahu yayi qrfin halin fita kiran maqota
don a suturceshi cikin awa da be wuce daya aka
kai Rabiu gidanshi na gaskia, kafin aka zo
zaman makoki, Karime ta dan rude da farko
amma daga baya sai ta gyagije wai Allah ke
kama maqiyanta ta hanyar kashesu.
******
Bayan Arbain; Musbahu ya rungumi iyalan
marigayi qaninshi, dukkansu ba wanda be zuwa
makaranta banda Hassana da Hussaina.
********
Bayan wata 5
Aishalle kince kina son muyi wata magana? Tace
eh Mallam, daman wani abu na hango, yace me

ke nan? Tace Me zai hana tunda Yaya Hajjo
tagama Takaba me zai hana ka aureta? Ina ganin
ta hakan ne zaka fi kula da ita kuma ka riqe
amanar da qaninka ya bar ma, ya tsura mata
ido, dama chan yayi wannan tunanin amma
yana tsoron abun da zaije ya dawo shisa ve gaya
ma kowa ba, kaii amma Allah yayi ma Aishalle
albarka Akwai da kaifin tunani, yace Aishalle kin
tabbata wannan shawarar taki har ranki? Don ni
bana so nayi abunda zai bata ranki, tayi
murmushi Maigidana kenan, kamanta hallacin
Hajjo a gareni? Ko kirkinta da kular da ta bani
ka mance wlh wannan abu har raina, don a
qasar nan banda kamarku. Yace toh shkn, na
amince, tace ka taso muje mu kai qoqon barar
mu, yayi daria yace Aishalle baki da dama.
Karime dake labe bakin kofa ta na jinsu idonta
ya rufe tsabagen tashin hankali, kishi da Hajjo?
Aiko zaayi yaqin basasa na biyu a gidan nan, keji
wannan hegiyar mayyar, dan taga na barta ta
zauna shine har da gayyato hajjo, ganin sun
kusa fitowa ne yasa ta shige dakinta da gudu.
******
Hajjo jin maganar tayi bambamraqwai, ya zaayi
ta auri yayan mijinta? Kuma Mijin Yaya karime?
Aishalle tayi sauri tace donAllah yaya hajjo kar
ki baza mun qasa a ido, kinsan duk wnda zaki
aura a bayan mijina yake, kuma so kike kiyi
aure wani gurin ya rabaki da yaranki? Auren
mijina ne mafita gareki, hajjo ta harareta,
hussain da ya shigo yace Umma danAllah ki auri
babanmu, shiru tayi sai chan tace Allah ya hada
kawunnan mu. Suka amsa da Amin. Ji sukayi
ance idan ka isa Allah ya tsinen, ni zaka ci wa
mutumci? Hajjon zaka aura? Qanwata? Yayi
murmushin takaici, yace ynzun kika san cewa
qanwarki ce? Ai aure be haramta tsakaninmu
ba, kuma kamar anyi angama, ta chakumo
wuyanshi, tace kuran sai ka saken, ya ce so kike
na sakeki? Wani dan guntun tunani tayi tace da
sauri aa kar ka saken danAllah, amma yasin da
sake ba zata sabu ba. Daria yayi ya ja hannu
Aishalle sukayi qofa ta juyo ta fara zagin Hajjo,
Musbahu ya leqo yace qara ce mata uffan a
bakin Aurenki wlh kuna kika tafi kin tafi kenan.
Dif kakeji kamar an dauke wuta, sai murgude
murgude da harare hararen da takeyi, ba halin
magana. Oh su karime ashe ana san auren😜......
Ana idar da Sallahn jummaa aka daure Auren
Hajjo da Musbahu.....
******
Bayan Shekara 15.

A halin yanzu
Hajia Babba(karime) Haihuwan ta 10 Shida sun
rasu saura Abida, Sadiya, Zainab, sai Usman
haushinta daya yaranta maza duk sun rasu daya
kawai ya rage mata. Hajiya Ama(Aishalle)
yaranta Aliyu, Umar Abubakar, Maryam, Rabi'u
sai Auta Nuratu. Tun Da aka yi Auren Hajjo da
Musbahu ko batan wata bata taba yi ba, Yaranta
da Rabiu basu da bambanci da yaran Musbahu a
cikin Gidan.
******
Dalilin da ya sa na tara ku anan shine; Na yanke
hukuncin hada aurenku duka, kasancewar ku
Maza duk kun gama makaranta ga Sanaar ku
kunayi, ya kalle Mudassiru da Labaran yace
matsayin qannai na kuke, amma aure be
haramta tsakanin ku da 'yayana ba, saboda haka
kai Mudassir kaine babba, na baka Abida, kai
Labaran Sadiya ce matarka, karime sai faraa
take tayi, don tasan sai yanda tayi dasu
mudassir din Musbahu Zailani ya cigaba da
cewa, Hassan Maryam ce taka Hussaini kuma
Nuratu, Gambo kuma na baka Zainab. Aliyu
kuma zaka auri Hassana, Umar kuma Hussaina,
Abubakar kuma akwai diyar Alhaji Mai dala'ilu
Hafsat, yace ya baka ita charaf Karime tace
Wa?? Ai kuran baku isa ba, Hafsatun da ke son
Usman? Kuma mun gama magana da
mahaifiyar yarinya tace ta ba usman Hafsatu,
Wlh ba wani Habuvakar, karime sanin dukian
Alhj me dalailu ne yasa ta ke son hada danta da
diyarshi, Shi dama Abubakar ya fita daban cikin
gidan, yace Baba a bar ma Usman din, duk daya
ne, don be son Auren yanzu musamman na
zumunci, ya cigaba da cewa ni dama ina son na
qaro ilimi, , yace toh shkn da kai da Usman din
duk daya ne, Allah ya ba da xaman lahya. Suka
amsa da Amin gabaki daya, Karime tace yauwa
Alhaji maganan Zainab da Gambo, ya xaayi ka
hadata da gambo? Bayan kasan hajjo bata
qawnar jinina? Wani kallo da ya watsa mata ya
sata nustuwa lokaci guda..
*****
Sunyi qoqarin fahimtar junansu, kowa yayi
naam da hadin da aka mai, Zainab kuwa tana
son Gambo qwarai da gaske amma Karime tana
laantar wannan hadin, Gambo ma yana danne
zuciyar sa, don duk dakin Hajia babba ita kadai
ce ta fita daban, Hajia Hajjo(mama hajja)da
Goggo Ama suka lallasheshi kan yayi haquri
yama babansu biyayya, Haka dai yayi haquri ya
chusa ma kanshi son Zainab don ya lura tana

sonshi.
A haka akayi aurensu, nan cikin gidan aka fidda
ma kowa gidansa ciki da parlo, aka aje amare
anan. Abubakar har ya tafi qasar Rasha(Russia)
don karatu.
A qasar Russia ya hadu da Yarinya me suna
Raijana, course mate dinshi ce, yau da gobe
suka shaqu, har suka qullah soyayyah
tsakankinsu, har Abakar ya yanke hukuncin
aurenta, Raijana ta gabatar da Abbakar ga
mahaifinta, dayake mamanta ta dade da
rasuwa, fir babanta yaqi wai bazai aura ma dan
Africa diya ba, ta dage ta nace tace wlh sai ta
aureshi, yace shiko idan ta nace sai ta aureshi,
to ba ruwanshi da ita, ya yafeta, da yake sun
yan chan sun dauki soyayyah da mahimmanci ta
tsallake mahaifinta ta ja hannun Abbakar, Haka
sukaje wani massalaci aka daura aurensu.Haka
suka gama karatunsu, sukayi shirin dawowa
NIGERIA, yace su zo suyi ma babanta sallama,
suka nufa gidanshi amma yana ganin su ya
musu korar kare, yace beson qara ganin
Raijana, haka suka wuto Nigeria guiwa a sage.
*******
Zaune suke a parlorn M.Zailani gabaki daya ana
cin Abincin Gandu, yayi sallama hannunshi riqe
dana Raijana, duka suka zubo musu idanu,
Umma Hajja ta fara ganeshi da sauri ta miqe
tana tafa hannu ga Abbakar ga Abbakar, gunta
ya nufa don tun kafin ya girma ita yafi sani don
tana sonshi kamar ita ta haifeshi, ya rungumeta
ta shafa sumar kanshi, ya nufa M.Zailani ya
zube ya na kwasar gaisuwa, kafin ya nufi Hajia
Ama yana gaidata farinciki ya mamayeta amma
kawaici ya hana ta nuna, ta amsa, sannnn ya
Gaida Hajia Babba ta amsa cikin yatsina. Ya
gaida yanuwanshi, Idon M.Zailani kan Raijana da
take tsaye bakin qofa, yace Abbakar wacece
wanchan, yayi murmushi ya kamo hannunta ya
kawo ta gab da baban nashi, cikin turancinta
tace Good Afternoon Papa, cikin turancin yan
da yace hawwayu? Tace fine papa, Yace
Abubakar wacece wannan? Abbakar ya
murmusa yace Matata ce, Duka dakin suka hada
bikin wurin cewa MATARKA?5⃣🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 by 👂💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Hjia babba ta
fara tafe hannayenta biyu tana salati, Abbakar
kafira ka auro ka kawo ta cikin gidan nan?wani
mugun harara ya jefeta dashi, Hajia Ama tace
yanzu daman baka da wayau, Abbakar ya dafe
kanshi, Umma hajja tayi saurin miqewa ta ja
hannun Raijana tayi waje da ita, sassan ta ta
kaita ta shigar da ita dakih, ta debo mata abinci

ta mata alamun ta ci sbd ba ta iya turanci ba,
Raijana tayi murmushi tace thank u, Umma
hajja ta komo cikin babban parlo, Abbakar xube
gaban babanshi, yace Baba ka yafe mun, bana
son aikata sabo ne yasa na aureta, kuma
musulma ce, ta rabu da mahaufanta saboda ni,
baba idan na rabu da ita ban mata hallaci ba, na
kuma ci amana, shiru ya gifta na wasu yan
lokkuta M. Zailani yace shikenan Allah ya maka
Albarka, na yafe maka, amma daga yau ba
wanda zai qara auren bare, kuma ni zan zaba
ma kowannenku mataye da mazaje, yace
nagode baba, Abbakar ya matsa gun
mahaifiyansa Hajia Ama, yace Ama danAllah ki
yafe mun, tace bakomi Abbakar Allah ya bada
saman lfy. Yace Umma hajja ina raijana? Tace
tana chan daka, ya nufe dakin tana ganinshi ta
fashe da kuka, Abbakar ur family is against our
marriage ryt? Ya rungumeta yace dont cry, dy
are not like dat, i explained evrything to dem,
and dy understood me, u have nothin to worry
abt.
*****
30 years later..
Baba Mudassir da Aunty Abida(first daughtern
karime) na da yara 7, Tahir, Fatima, Noorayne,
Zayd, Farida, Haneefa sai auta Ahmad, Baba
Labaran da Aunty Sadiya na da yara 5, Yusuf,
Khamis, Mu'ammar, Yusra , Bilkisu. Yaran Aunty
zainab(diyar karime) da baba Gambo(dan Hajjo)
2, Samir, Samar. Baba Usman kuwa da Aunty
hafsat diyarsu daya Ni'ima sai da suka shekara
15 da aure suka haifeta. Baba Hassan (dan
Hajjo)da Aunty Maryam(diyar Aishalle) na da
yara 4, Imran, Faisal, Munira, sai auta Nasir,
Baba Hussaini da Aunty Nur yaransu 3,Irfaan,
Zayyad da Raffiyah, Baba Aliyu(dan Aishalle) da
Aunty Hassana (diyar hajjo) nada Yara 3, Aisha,
Nabila sai fadila, Baba Umar da Aunty Hussaina
na da yara 2 daga Suraj sai Islahulkhair. Uncle
Abbakar da Aunty Raijana(er mutanen Russia)
diyarsu daya tilo Rumaysa'u....*********
Yawancin jikokin M.Zailani sunyi aure, shike
hada auren jikokinsa, Be hada auren jikan dakin
Hajjo da jikan karime ko jikan karime da na
Aishalle, hada yan daki yakeyi (misali dan baba
hassan da diyar baba Hussaini) ko kuma diyar
(Baba labaran da dan baba mudassir) shi a
ganinshi hada auren jikokin Karime da jikokin
hajjo ko na Aishalle matsala zai haifar don yana
sane da gaban dake qulle tun kafin a haifi
yaransu, amma ya kan hada jikokin Aishalle da

Jikokin hajjo aure don su yasan Akwai yarda da
amincin junansu. A qaidar gidan M.Zailani
namiji daya gama karatun degree dinshi zaa
mai aure, sai ya dauki matarshi ya tafi da ita
duk inda zai kaita, mace kuwa da ta gama
sakandire ake mata aure ta qarasa gidan
mijinta. Jikokin gidan kama sukeyi don da wuya
ka tsame wannan kace yana da kyau wannan be
dashi, duk kakansu su ka dauko wurin kyau da
haske, Sai dai kowa da halinsa, suna gaban da
suka ga kakkaninsu sunayi, yan dakin Umma
hajja da hajia Ama kadai ke zaman lafiya,
Amma baka ra'ban yan dakin hajia babba, don
da kun wuce sai ta zagi kakarku.
Maza 7 zasu kammala degree dinsu ko wa da
fannin karatunshi, gabaki dayansu suna Oxford
University, Mata 6 kuma ke jarabawar qarshe,
kuma da sun gama za a hadasu Aure, matsalar
gidan baka soyayyah don baka san da wa zaa
hadaka ba, amma ba zaa rasa wanda kake burin
a hadaku dashi ba.. Wannan kenan.
Kowa da halinsa, Islahulkhair ba ruwanta da
kowa, maganaa be dameta ba, Yan dakin Hajia
babba ke mata laqabi da er jiji da kai, Fadila
kuwa ba ta da haquri ko kadan, idan ka mata
laifi nan zata wanke ka tas, shisa Haneefa da
bilkis ke shakkunta, Ni'ima kuma gata nan dai
lafiyarta lao amma idan ta maka abu sai ka zata
me ciwon hauka ce, abunta dai kamar sakarya,
kuma Qalaw take, Rumaysah kuwa haqurinta
yayi yawa, matsalarta daya Nawa, bata abu cikin
hanzari, ko abinci su keci kowa sai ya tashi ya
barta, yan dakin Hajia babba ba irin zagin da ba
sa ma mahaifiyarta kasancewar mahaifiyar ta er
wata qasace, kyanta dai ya fi tada musu hankali,
suce mata mayya Aljanna, ko su zage kakarta
Ama, tafi duka jikokn gidan kusanci da Tsoho
(M.Zailani) saboda yanda take kuka dashi, tayi
mis tausa, da fita, har yaqi cin abincin GANDU
yace Na ta zaici..
A halin yanzu suna ta fama da Jarabawa ta
NECO...
*******
Gida ya kachame, yau baqin turai zasuzo, shiri
ake tayi ba babba ba yaro, shekara 5 kenan
rabon su da gida, Har masu aure 'yan nesa da
kusa sunzo, misalin Qarfe 2 daidai suka shigo
gidan, Waiyo Allah, Akwai maza Hurul Ayn
dama? Ko wannensu najin kanshi, sai dai su
basa yar tsama da junansu, ba ruwansu da beef
din iyayensu ko kakaninsu, son junan su suke
kasancewar sunyi shekara kusan 6 guri daya

inda ba su da uwa ba uba... Sallama sukayi a
parlorn Tsoho, Murna ya lullube iyaye da
kakaninsu, zube wa sukayi gaban tsoho suna
kwasar gaisuwa, kafin kowa ya nufi iyayensu, a
ka gaigaisa.. Tsoho yace Sarkin Gida ka kaisu
cikin Sashensu kowa ya zabi daki, yace ku biyoni
suka ja Akwatinnansu suka nufa sashensu, ko
wannensu ya dauki daki suka shige don huta
gajia..Wurin 5 yanmatan Gidan suka shigo don
yau evening paper sukayi, Babban parlo suka
shige suka ga yayyinsu suna fira da tsoho,
kowacce ta nufi yayanta ta rungume, Tsoho yace
oh Allah, ko Sallama babu? Ku tashi kuje kuyi
wanka kuci abinci kafin ku zo a gaisa ko? Suka ce
toh, suka fice, har ta kusa bakin qofa yace
Rumah, ta juyo tace naam tsoho, idan ba ki gaji
zuwa anjima ki min wannan hadin shayi tace
angama tsoho bari nayi laasar, yace yauwa er
albarka. Zayyad ya bita da ido, wacece wannan
tsoho? tsoho yace duk ba ku san juna ba,
zumuncin ku ya tabarbare, kowa nashi kawai ya
sani, dan wannan daki be san dan wannan dakin
ba, Zayyad yace ayi haquri tsoho, ayi mana
uzuri shekara 5 rabon mu da gida, mun san
juna matsalar baza mu sheda juna ba, Tsoho
yace Allah shi kyauta. A ranshi kuwa ya ce dole
zan chanza wannan rashin zumunci, na san abun
da zanyi, ko kun qi ko kunso sai kun zama
TSINTSIYA MADAURINKI DAYA, Ya kalli
Mu'ammar yace yaushe Zaidu din zai dawo?
Muammar Ya tabe bakih chan yace nan da wata
3, tsoho yace wai saboda mene baku dawo tare
ba? Inace duk tare kuka fara karatun? Samir
yace kwantar da hankalinka nan ba da jimawa
ba zai dawo cikin yanuwanshi. Tsoho yace akwai
abunda ba kwa so na sani, Suraj yace kasan ko
sun boye ma ni me fada ma ne, yace toh Allah
sa dagaske ne, suka ce hakan ne ma. Yauwa da
kunyi bautan qasa sai Aure ko? Muamaar yace
Aifa maganar kenan Aure Aure mundawo
GIDAN GANDU kenan, duk suka sa daria....6⃣🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebie Isa💕Biebee Isa💕 Yau basu
da
paper, suna gida, Fadila ta shigo Sashen Uncle
Abbakar, Aunty Raijana na zaune na kallon wani
Fim, Aunty Maisah fa? Cikin hausarta da har yau
be fita tace ki dubata dakih, ta shiga, tsakih ta
buga da qarfi, Oh Allah haka zaki qare dai, don
fa kiyi sauri ki shirya ya sa na kiraku tun dazu,
amma ji beki shafa ki keyi, Maysah tace sorry
riga kawai zansa tace wlh ki same mu sassan
Baba Hussaini, bari naga Islah ta shirya, ta iske
Islah ta shirya suka dai ta ke jira, Islah tace

lemmie guess maysah bata shirya ba, Fadila ta
yi dan guntun tsaki tace ke da kika san komi,
yaya Suraj ya shigo dakin yana Sisi bani
earpiece dina, islah tace bro donAllah bari mu
dawo zan baka, yace kinga dai ki-- shiru yayi da
idonsa ya kalli fadila, murmushi ta mai tace
Yasuraj ina wuni, ya mayar mata da murmushin
yace wacece wannan? Tace fadila ce, lalala haka
kika qara girma, kai murmushi ta mai, Yace ina
zaku ne? Islah tace walimar Quranin qawarmu,
ya kalli fadila yace tohm muje na kaiku koh? Ta
dago kai suka hada ido da sauri ta sunkuyar da
kanta, Islah tace wai sarkin Nawa muke jira,
wacece sarkin nawa kuma? Maysah ta shigo
dakin tace iyayen mita gani nan, Yasuraj ina
wuni? Ya sakar mata murmushi ya ganeta don
fuskar aunty Raijana gareta, yace Rumaysah wai
duk kun zanqale banda su o'eh Islah ta turo
bakih tace kai koh yaya? Ban ma yi missing
dinka ba, yace liar, ku tashi muje, suka nufa
parking lot motar da Tsoho ya ba kowannensu
bayan dawowarsu, ya bude ya shiga Islah ta
bude gaba zata shiga yace ke zaki shigo ki isheni
da surutu koh? Ko ma baya jareh, Eeelerh dawo
gaba kinji suka tsaya kallon kallo waye kuma
eelerh anan? Ganin Fadila yake kallo yasa ta
gane da ita yake, ba musu ta shiga gaba, Maysah
da Islah suka shige baya, Ya kalleta eeelerh ina
zamu ma? Jikin ta yayi sanyih ta gaya mai, bini
bini yake jan ta da fira, Islah cikin rada tace
maysah kin ga abunda na gani? Ita ma cikin
murya qasa qasa, ngani, Yasuraj ya fole, suraj
ya kallo su ta mirror yace gulmanmu, me kuke
cewa? Sukayi daria, suka iso gidansu Fatima
Bobboi wace ake ma sauka din, fita su Islah
sukayi, fadila zata fita taji Yasuraj ya riqe mata
hannu juyowa tayi cikin tsiwa taga yana kallonta
ba shiri ta kai kanta qasa, a hankali yace I love
you fadila, Kallonshi tayi da sauri yace Fadila
will u marry me? Murya na rawa tace, Yasuraj
kasan dai we are not allowed to fall in love koh?
Kayi sauri ka cire wannan tunanin don baka san
wacce tsoho zai baka ba, yace fadila, yanzu ba a
auren dole, all m asking is for u to let me love
u, nd i promise u, u wont regret it, ya qare
matse hannunta, yace pleaseee, a hankali tace i
love u yasuraj, ya sake ajiyar zuciya. Islah ce ta
durquso ta window, hey are u coming on not?
Suraj yace shes not byebye, Fadila tayi mata
gwalo, Rumaysah tace ke ma dai ina ruwanki ki
zo mu shiga ciki, in yaso sai muce ma bobboi
tana love cikin mota. Sai da Suraj ya tabbatar ya

gina sonsa a ziciyar fadila kafin yace ta shiga ta
mata Allah sanya Alheri ta kira su Islah su zo su
wuce.
******
Nikam Mu'ammar ka gaya ma hanifan? Ya dan
tabe fuska yace kasan bana son raini, but zan
aika Bilkis, Jawad yace kana bani mamaki wlh,
kana son abu amma girman kai dinka ba zai
barka ka furta ba, kuma idan gudu kake kar
tsoho ya hadaka da wata, dama ka bar tunanin
nan, dan a kanmu Culture dinnan na auren hadi
zai tsaya, fine ba xa mu aura bare ba, but a bar
mu mu xabi na cikin gidan da kanmu, amma
idan kaga zaka tauye ma kanka haqqi ka auri
wacce baka so den goodluck wit dat, Guy, ya ka
dauki zafi ne haka, yace Allah bana son bacin
rai, wai hadin Aure kawai sai a hadani da wacce
banaso, yace wlh akwai matsala don ba yarda
zanyi ba, yanzu ma Bilkis zanje nayi
approaching, Muamar ya kaimai duka, kaii
carefull dats my lil sis, Jawad yace na ga nima
hanifan sista tace, hurt my sis nd i will hurt urs,
sukayi daria daga nesa suka hango haneefa ta
fito daga sassan su tana yauqi, Jawad ya miqe
tare da cewa man up and tell her wat u feel,
yaqwala mata kira Hanee, ta qariso tana
wannan yauqi, Yajawad yadai? Yace Yayan ki ke
kira, wane yayan? Ya nuna mata mu'ammar tace
ok, ina Bilkisu ne? Tana sassan hajia babba, yace
ok yayi gaba ita kuma ta nufa Yamu'ammar how
far, yace hanee m in love, jin maganar tayi
wani bambaraqwai, tace with who? With you ta
zaro kyakyawan idonta tace what? Shima ya zaro
mata nashi yace Yes i love haneefan Baba
Mudassir tayi rau rau da fuska, Yamu'ammar
namiji ne da ko wacce mace zata so, haneefa
tace amma Yamua'ammar kasan tsoho--shh ya
dakatar da ita, i dont care abt tsoho's decision
ol i know Is dat i lob u, unless ban miki bane
ba, tace Aa fa ba haka bane, yace nasan me kike
tsoro, but its high time su bar wannan Culture
din, munji ba zamu aure bare ba, amma a bar
mu mu xabi na gidan da kanmu. Bazan tava iya
auren yarinyar da bana so ba gaskia, Tace toh
shkn, Allah ya bamu saa, ya dan kallota is dat a
yes? Ta kashe mai ido daya nan suka zauna suna
firar soyayyah..
*****
Hajia Babba tace Ahh yau Jawad a sashe na?
Tunda kuka dawo so daya ka shigo dakin nan da
ba ni na haifi uwarka ba kuma na riqi ubanka ba
da na ce kai ba jikana bane ban san ko Aishalle

ta shiga tsakani da kai ba, yayi daria, kin cika
mita wlh, wai ni meye matsalarki da Hajia Ama
ne? Ko don ta aure miki miji?Tsohon ma ya
tsufa amma kina kishinsa har yau, ko don ta fiki
kyau ne? Da yarinta? ai fa ya zunguro ma
kanshi, nan ta fara zagezage da tsinuwa, yo
indai kyau irin na mayu ne wlh na yarda na fi
duwawu muni, Allah ya tsareni da kyaun Mayyu
da Aljannu, nan ya shige dakih yana daria zaune
ya ga bilkis tana ninke kayan Hajia Babba, yace
Sis ya dai? Ta fadada murmushin ta, duk cikin
causins dinta Yajawad ya fi burgeta, ta na
mugun sonsa Yajawad ina wuni, yace me kikeyi?
Hajia ta sani ninkin kaya, Ya ce duk cikin yaran
gidan nan Hajia ta rasa wanda zata sa aiki sai
matata? Dadi kamar ya kashe bilkisu amma ta
wayance tace matarka kuma? Wace matarka?
Yace ke mana, ko ba zaki aureni ba? Tayi mai
far da ido, tace Dan tsoho zai baka mata,
Yajawad yace ke ni rabani da wannan hadin
zumuncin, ni ke nagani nakeso inaso sai dai in
kece ba kyasona, da sauri tace ina sonka fa
Yajawad, yace lets stick togeda, ba me rabani
dake kinji? Ta gyada Kai tana murmushi.
********
Sanye yake da 3quarter hannunshi riqe da
basketball ball, leqawa dakin Jawad yayi ya ga
bayanan, ya leqa dakin mu'amar beyanan, tsaki
yayi ya ga suraj kwance yace guy muje muyi
basketball, Suraj yace uhm uhm not in d mood,
Zayyad muje muyi, zayyad yace No thanks tsaki
yayi yace Kar Allah ya sa kuyi, haka ya isa field
din da ke bayan Sashen Hajia Ama yana
bouncing ball din. Da ya hango basketball court
dn ya wurga ball din, daga chan nesa
Islahulkhair ce ke skipping, ji tayi saukan
Qwallo a kanta, qara ta sake na shagwaba ta
dafe kanta tana kallon wanda ya jefeta da ball
cikin tsiwa tace ba ka gani ne? Ya kalleta yace da
kika ga ball me sa baki matsa ba, Miskilancin
Islah ya tashi, ta ga idan har ta tsaya tanka
mishi tana iya sake kuka ta duqa ta dauki rope
dinta ta wuce warta, har ta kusa barin field din
ya daga murya yace Islahulkhair tsaya wa tayi
bata juyo ba, yace kin iya B.Ball? Juyowa tayi
tace wat if na iya? Yace i want u to play wit me
pls, kamar ba zata tanka ba sai kawai ta qaraso
tace lets do dis, ya fara bata ball din suka hau
bugawa, sai da yayi mata 12-0 wai ita ojoro yayi
haka zatace ba ta yarda ba sai a sake, haka suka
dinga yi ko daya bata ci ba, tace a qara one last
time, yace Nooo nan ta yi wayon kwace ball din

taje ta sa a ragar sa, yabita ya qawace ball din ta
yi tangar tangar zata fadi ya tallabota suka zube
a qasa suna daria sosai, yace Islahulkhair I need
smeone da zan dinga games da ita bayan nayi
aure, i love games, nd u fit wat i like, so u want
to be my game partner nd my life partner? Ta
tsureshi da ido, yace zan fahimceki idan kika ce
aa coz nasan beef din da ke tsakanin Grandma
dina and ur grandma, but kar fa ki manta mun
hada kaka da ke da babana da mamanki Uwasu
daya ubansu daya nima ina da jinin Umma
hajja tatare dani so ban ga dalilin da zaisa ki qi
ni ba, oh maybe ban miki ba, ya miqe ya barta
kwance har ya juya, Islah tayi saurin cewa
Yasamir ya juyo ta miqa mai hannu da ga
kwance, ya sa hannu ya dago ta, cikin sanyin
muryarta tace Yasamir m scared, yace i knw wat
u are afraid of, dis Culture has to stop now, ba
Zamanin daaa mu ke ba, trust me pls, ta daga
mai kai tace ok. Yace I love u Islahulkhair, cikin
kunya tace i love u Yasamir..👻
7⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Sun gama
exams qarfe 12 suka dawo gida, Maysah ta
shiga wanka, ta ci abinci, ta fito da sauri tana
yana gyalenta na afta dress, ta kalli mamarta
tace Amma na je gurin tsoho, cikin hausarta,
akwai dambun nama a kitchen ki kai mishi, da
sauri ta shiga kichin ta dauko, ta nufa Sassan
tsoho.Ta shiga dakin da Sallama, aka amsa ta, ba
shi kadai ke dakin ba su biyu ne, ta ce tsohona
ina wuni ya ce cikin sake fuska, Ruma kina lfy?
Ya exams? Lahya Alhamdulilahi, ta kalli wanda
suke tsaye tare dace Yazayyad ina wuni yace lfy
lau Ruma tayi murmushi, Tsoho yace ki diba
bedside na nan tun da safe babanki ya kawo
man newspaper nace sai kin dawo zaki karanta
man, ta miqe cikin yanayinta ta nufi dakin
Tsoho, Zayyad ya bita da ido, ta dauko jaridar ta
matso da sofa ta zauna ta shiga karanta mai
newspapern nan cikin qwarewa da muryar ta
mai dadi. Lumshe ido zayyad keyi sakamakkon
jin muryar ta dake ratsa jinin jikinshi cikin
kwanyar kansa.Nan take zuciyarsa ta kamu da
son Rumaysah, duniyar tunani ya fada, ba tare
da sanin ta gama har ta shiga dakin Tsoho don
dauko mashi magungunanshi, Tsoho sai magana
yake mai amma inaa hankalinshi baya gareshi,
Tsoho
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment