Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

fadila ce za a harba, so stop
blaming ursef kajih dana? Yace thank u
Mummy. Duk suka fice, Zayd ya bi bayansu don
nema musu masauki duka...
*****
Maysah nakan sallaya ta idar da sallar maghrib,
jawad kuma na kan gadon da fadila ke kwance
har zuwa yanzu bata farfado ba, rashin
farfadowanta ya fara bashi tsoro, ya riqo
hannunta yana murzawa a hankali, ya na
magana me kama da sambatu, inda yake cewa
ke me tsiwa, kika sake kika mutu sai na biki, toh
meye amfanin rayuwata idan kin mutu?ai ban
gama jan bakinki ba idan kika murguda min
bakih, so its early for u to die, sai kuma ya fara
hawaye, kamar an tsunguleshi ga goge hawayen
idanunsa ya dan daga murya yace ke dallah ki
tashi. Kamar tajishi, cikin ikonAllah fadila ta
bude idanuwanta a hankali, ta sauke su fes kan
Jawad da sauri ta hade rai tare da murguda
mishi bakih. Da sauri jawad ya hada bakinshi da
nata.
5⃣4⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Fadila ta
daddage ta gantsara ma jawad cizo a bakih, ya
dan saki karah ya saketa, ta sake murguda mai
bakih, shi kuma ya ja bakin a hankali, yace you
are Okay, Dont make me worry too much about
u like dis, sai a sannan komai ya dawo ma
Fadila, ta tuno cewa harbinta akayi, ta sa
hannunta ta shafih kafardarta taji bandage, da
sauri tace Ya Jawad someone was trying to
shoot u, yace shhh, save ur strength i know wat
happened, a halin yanzu an kama su, amma
sunqi magana, sunqi fadan wanda ya turo su,
but it wont be long before they expose who
sent dem. Tayi ajiyar zuciya, Fadila,e kikeso?ina
ke miki ciwo? Ta murgudi bakih, tace ni ka kaini
gida, ni ka kaini maiduguri, ina son ganin tsoho
da Mummy, yace karki damu, su tsoho na nan

kd, basu dade da tafia ba, Gobe zasu dawo
kinji? Ta gyada kai a shagwabe, yace look who's
here, ta kallo inda yake kallo, tayi yunqurin
tashi tace Maysaaah, yayi saurin maida ta, yace
ke mallama koma ki kwanta, Maysah da ta tsaya
kallonsu don kalar Soyayyar su ta birgeta, ta
qaraso kan gadon ta riqo hannun fadila Tace
sannu sis, ya jiki? Fadila tace yaushe kikaxo?
Kwana nawa anan? Kwananki 2, ta zaro ido, tace
m happy to see u sis, Maysah tace same here,
get well soon kinji? Fadila ta turo bakih tace ni
fa ba abunda ke min ciwo m okay. Jawad yace
yauwa baby haka nakeso, ta harareshi tace
mallam ni ba baby bace sunana fadila, yace
yarinya bari a sallame mu mu koma gida, sai na
yi maganin ki, ai kinsan halina. Fadila ta koma
ta kwanta kan cinyarshi inda taga kanta da farko
ba tare da tankashi ba. Shi kuma ya shiga shafar
kanta fuskarshi dauke da farinciki.
*****
Washegari su Tsoho da iyalanshi suka dawo,
sunji dadin ganin fadila ta ji sauki don ynz ma
Zaune take Jawad na bata abinci a yangance
take amsa. Tsoho yace tunda ta farfado da
alamun ta warke, yau xasu koma, Baba hassan
yace Jawad ya maganan Gunmen din? Har ynz
ba su fadi wanda ya turo su ba? Yace Eh baba
basu fada ba, ni ban masan me ake ciki a yanzu
ba, Zaid yace yanzu idan na rakaku zanje Police
Station din naji abinda ake ciki, Hajia babba dai
ta sha jinin jikinta ganin Jawad ko kallonta beyi
ba balle ya gaisheta, ga Zaid nan ma fushi yake
da ita, ta na son jikokinta, Sai da Tsoho yace ayi
addua don nemar lafiyar fadila da karfi tace
Ameeen, amma hakan be sa Jawad kallonta ba.
Haka dai yan Maiduguri auka tafi, Zaid ya shaida
ma Maysah suma yau din zasu koma da laasar.
Fadila ta sa Maysah ta kira mata Amal, baa yi
15mins ba sai ga Amal da mijinta Rufa'i, mijin
Amal yace da Jawad wlh baka kyauta mana ba, a
matsayin mu na Makwafta mu ya kamata mu
riga kowa sani, abu har an kwana biyu ba muji
ba? Jawad yace kuyi hqri, tunda akayi abun so
daya na koma gida, kuma ban dade va, suna
cikin fira sai ga Zaid ya dawo, suka gaisa da
Rufa'e, zayd yace da Jawad ya tashi suje police
Station, Jawad yace aa bros, kai dai kaje, ni ina
nan da matata, fadila ta murguda bakih tare da
hararashi, hakan da tayi ya basu daria dukah,
Maysah tace Ya Jawad kuje kawai, trust me
zamu kula maka da matarka, kaga ma maman
Irfan, tana nan ko? Amal ta gyafa kai, tace uo

wife us safe, ya danyi shiru kafin ya kalli fadila
yace baby naje? Ta murguda baki tace sai ka
dawo, ya xo ya bata peck suka juya zasu fita, har
waigen ta ya ke juyowa yanayi.
*POLICE STATION*
Har ynz sunqi magana sir, Zayd ya ce suna ina?
Wani kofur yace suna nan cikin interogation
room, Zayd yace i want to see dem, be sha
wahala ba aka barsu su ka shiga, suna nan an
daure su gam su 3, Wurin dan karamin Zayd ya
nufa, ya ce kai, wa ya turo ku ku kashe Kani
nah? Mutumin ya dago zai yi ma Zaid rashin
kunya, yana dagowa suka hada ido da shi, eye in
eye, sai ya dauke fuska dob Zaid din ya mai
wani irin kwarjini, Allah ya ma Zaid wani baiwa,
duk iskancin da tsagerancin mutum ya hada ido
da zayd sai ya raina kanshi, hakan ta faru a
yanzu don zaid ya juye ya koma terror dinsa,
barin ma da ya amshi bindiga ya saito kan
mutumin, Zaid yace ka ganni nan, i care less abt
u, is either u tell me who ur boss is, or i will
shoot u, tuni mutum ya rude kallo daya ya ma
zaid ya san zai aika, murya na rawa yace pls
dont shoot, i will tell u what happened, Gambo
Kashe Arna da aka daddaure aka yi selotaping
bakinshi ya fara jijjiga yana zaro ido, alamun be
so a tona ubangidanshi. Mutumin da ya ce
sunanshi killerman yace Ranar wednessday, Oga
ya kira mu, yace zamu mishi aiki Officer yace
waye oga? Killer man ya nuna Gambo
kashseArna da hannu, yace na boss dinshi ne,
shi time din yana lagos, so kuma aikin
Emergency ne, shi ne ya tura mu gurin shi Boss
din, ni da frnd dina muka je Guest house dinshi
don mu ganshi ya bamu bayannin yanda yake so
aikin ya kasance, so boss be ji dadi da ya ganmu
ba, don yace shi yafi yarda da aikin Oga Gambo,
i assured him dat he has nothing bto worry
about, don Oga trained me well, ni ne nayi
Gadonshi a wannan Sana'ar, so nan boss ta
bamu Full Address na Gidan Jawad, nd his
picture, we asked if he's married or living with
his parents yace no he is living alone, nan muka
tabbatar mishi by d end of d day Jawad zai
mutu. So sai nace mishi me yake so a mishi? Sai
ku Amsar min Documents din da yayi signing na
Contracts, sai ku kasheshi, bance kuyi robbing
dinshi for money, i will give u Enough, i dont
want any mistakes. Nace kar ka damu Boss,
zakaji sanarwar mutuwar jawad kafin jibi. Muka
tafi mukaje ni da abokina, bansan yadda akayi
polisawa suka shigo ba, mu kaji tsoro sosai, so

we ran for ourlives tho we were captured.
Officer yace toh kuna nufin ba ku ku ka harbi
ba? Then who did?Killer man yace Oga ne, Ashe
tym din da muka tafi gidan Jawad tym din ya
dawo daga lagos, akan hanyar ne na sanar dashi
gamu nan zamuje chan, so sai ya biyo bayanmu.
Shi kuma yayi harbi. Zaid cikin daga murya yace
wai who are we talking? Who is dis
motherfu**er dat wants my bro dead? Da sauri
killerman yace sunanshi Alhaji Haladu Maidala
NNPC, Iya rudewa da kaduwa Jawad ya shiga,
yana mamakin Alhaji Haladu, mutumin da ya ke
girmamawa kamar mahaifinshi, mutumin da
yaje bi sau da kafa, baba ma yake ce mishi,
shine yake so ya ga bayanshi? Me ya mishi
haka? Zaid ya juyo ya kalli jawad yace u knw
someone by d name Haladu? Kai kawai ya
girgiza mai Alamar, Eh, Zaid ya kalli Officer
yace you guys shud go get Dis Haladu of a guy,
or i will, nd if i do i will be d one to kill him,
DPO yace no sir, lets do dis d right way, ka bar
hukuma tayi maganinshi, Zaid yace hukuma ai
bata hukunta babban mutum kamar Haladu,
nasan zaayi cukucuku a barshi ya fita, DPO yace
na tabbatar maka wannan case dib bazaayi
cukucuku ba, don daga sama aka kira mu, daga
chan Lagos aka kiramu, kaga kuwa magana na
hannun manya, dole a saka Haladu behind bars,
Good inji Zaid, Nan take aka bada order din aje
a zo da Haladu, motoci 3cike da yansanda suka
tafi chapko shegen. Ba kuma su sha wahala ba
gurin gane inda yake, suka nema ya bisu a
hankali yaso kawo musu gardama, nan wani
police mara mutunci ya chafko wuyarshi, aka
saka mai Ankwa aka tasa qeyarshi sai police
Station, Haladu ya kalli sergeant yace waya baku
damar ci mun mutuci gaba mutane haka? Do u
know who i am? Jawad ya fito ya kalleshi yace
Baba me na maka kakeso kaga bayana? Me na
taba ka? Where did i ever go wrong? Alh Haladu
yayi mamakin ganin Jawad, duk a zatonshi an
kashe shi, yace forgive me Jawad, wallahi ban
taba sonka ba, duk abun da nake maka
munufurci ne, zuwan ka NNPC ka min illa
babba, ka kwace min matsayina a gun
gwamnati, da maaikata, komai sai dai a ce
Jawad, ka fara dakusar min da tauraruwata da
ta haska diniyan nan, duk inda ya kamata aga
Haladu Maidala ba a ganinshi saidai aga Jawad
Zalani, Alhalin nafi Shekaru 20 ina aiki a
wannan Maaikatar, shisa nace kawai bari na ga
bayanka, Jawad ya kalleshi cikin tsana yace its

not my fault dat m more hardworking dan u,
Hassada ce matsalarka, da ace ka gaya min haka
da na bar maka aikin kwatakwata, don mu ba
matsiyata bane, Jawad ya juya ya fita daga
Office din, Zayd ya kalli DPO yace sunyi filing
case akanshi, so sun makashi kotu, nd kuma kar
a bada belinshi har lokacin, Alhaji Haladu yace
Noo, pls dont do dis to me, Zaid ya kalleshi
galala yace; this is wat u get wen u mess with a
Zailani.
Cambridge England
A hankali ya bude idonshi, ya sa hannu ya shafa
kanshi, qaton bandage ya ji, nan Dr ya shigo
tare da mutumin da ya buge shi,You are finally
up inji Dr, murmushi kadai Amar yayi, What
happened? Last i check i checked i was brot
here, dr ya mai bayanin duk abun da ya faru,
tare da gaya mishi yanda aka sha wahalan
neman jini, da kuma yarda yaruwarshi tazo aka
bada jini, da sauri yace who? Dr yace she said
she's yo relative, she was here earlier but she
left after being sure that she's all okay, da sauri
yace did she leave a message or something?Yes
she left her number incase something came
up, may i have d number, Dr ya bude file
dinshi ya ba Amae number, ganin sunan Islah
ya fito kan wayar yasashi cixge drip din
hannunshi,yace i gotta go, Dr yana kiranshi
amma be tsaya ba, sai da ya bar Asibitin.
Straight Cambridge University ya nufa.
********
What? Kika ba wannan mugun jinin ki? Inji
zaineema da ta tsani Mu'ammar don Islah ta
gaya mata waye Mu'ammar a gareta, Islah tace
Eh zaineema, he was running outof Blood, nd
kuma ba inda ba a nema O- ba, ba a samu ba,
so i helped, Zaineema xatayi magana sukaji ana
kwankwasa kofar, islah ta tashi ta bude,
ganinshi tsaye ya sa ta mamaki, a ranta tace
wato ya warke kenan? Islah nagode, Allah ya
saka miki da Alheri, naji dadi sosai, haka ake so
ka zama mai yafiya idan aka maka abu, dis
shows dat u'v forgiven me, dakatar dashi tayi ta
hanyar daga mai hannu, tace haka mukayi da
kai? Kar ka ga na maka donating blood ya sa ka
fara jin dadi, ko ka yi tunanin na mance abun da
ka mun, to ka sani har yanzu ina jin haushinka,
har yanzu ban son ganinka, har yanzu na
tsaneka, it doesnt change anything. taimakon ka
kawai nayi, ko ba kai ba naga wani na neman
taimakona na zan bashi, don na gaji taimako
wurin Kakata, Islah me zanyi ki yafe min?

Wallahi na kamu da sonki, ta tabe bakih tace
shisa ake so idan mutum zaiyi abu ya dinga
tunanin abunda zai faru Gaba, dubeka yanzu u
look miserable, u left me Ya Amar, yace M
here now, tace too late, ka koma gurin hanifar
ka, yace haba Islah ya kike magana Haka? Kar ki
manta hanifa matar wani ce, ba kyau, islah ta
tabe bakih, tace ka manta soyayyarku? Har shan
jinin juna kukayi saboda shaukin so, Amar yace
kar ki maida hannun agogo baya, ni da hanifa
mun zama history, Hanifa mace ce, ta dade da
zubar da wannan digon jinin months ago gurin
period dinta, nd u knw wat matters d most
now? I hav ur blood running through my veins,
shine abunda yafi muhimmanci gareni a yanzu.
_Bibilicious B
5⃣5⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕DonAllah
Islah ki bani wani chance, wallahi ba zakiyi
nadama ba, We'll start afresh, we'll build our
home, a new life here, saboda karatunki m
willing na xauna a nan har sai kin kammala, i
wont cut u off, jus gimme ds one chance, Islah
ta kalleshi galala, tace ba ka da abun da zaka ce
min, ta shige ciki tare da banko kofah. Ran
Mu'ammar in yayi dubu ya baci, ya zaayi ya
tsaya yarinya kamar Islah ta dinga wulakanta
shi? Amma kuma be kamata ya ji haushi ba don
laifi ya mata take hukuntashi, but Dole zai
koma Naija cikin week dinnan, don ya san
Tsoho kadai ne zai daidaita tsakaninsu, amma ta
ya zaije ya samu tsoho da wannan zancen? Da
wani ido zai kalli Tsoho? Ai ido da kunya, but
InshaAllah zai kokarta ya je dai cikin satin nan.
******
Islah ina tunanin abunda kike ma Ya'amar is too
much, wlh naga yayi nadama, har ya fara ban
tausayi, kinsan wani bazai taking nonesense
dinki ba, amma shi tunda ya san shine me laifi
nd he wants to make it up for u, beyi fushi ba,
amma shawara zan baki, ki haqura haka nan, ki
zauna da mijinki ki manta da komai, Islah ta
kalli qawarta zaineema, tacd Zainee what he did
cant be forgiven dis soon, Zainee ta tabe bakih
tace A dai bi a hankali kar garin jan Aji ajin ta
tsinke, Islah tace haba dai ai wuce naaan...
Kaduna
Zaid da Maysah sukayi shirin dawowa Abuja, har
bakin mota jawad ya rakosu, ya rungume Zaid
ya na mai godia sosai, Zaid yace dont be silly
bro, kar ka mun godian komai, Maysah tace Ya
Jawad a kula min da kanwata, lalala matata ce
kanwarki? Tace eh mana, na bata 11days, yace

bawa ni tace ka tambayeta, ya maqe kafada
kamar wani yaro ba wani, wayon yayi yawa, ya
zaayi ku girmi miji kuma ku girmi mata?Zaid
yayi daria, yace Kyaleshi kinji Ruma, shiga mota
mu tafi kar muyi dare, ta shiga mota zaid ya ja
motar suka bar haraban Asibitin, jawad na ta
daga musu hannu har suka fice, shi kuma yayi
hanyar Dakin da aka kwantar da Fadila.
_Bayan kwana 10_
Amal ce ta shigo dakin da basket a hannu,
Jawad yace su Mummy Bonbon sai a juya a
koma gida don An sallame mu, tace barka, wato
kaima sunan nan ya shiga bakinka koh? Yace
ehmana tunda baby haka take ce miki nima
haka zan dinga ce miki, fadila na jinsu bata
tanka musu ba, Amal tayi daria tace, Toh zaman
me kukeyi? Eh discharge letter zaa kawo mana
sai muyi ta tafia. Tace ok, suna zaune sai ga
nurse tazo, Jawad yace tasa wasu attendants
suzo tayasu kai kaya mota. Wata nurse ta nurse
ta shigo da wheelchair, Jawad yace wannan fah?
Nurse din tace na patient ne, za ta hau a kaita
mota, jawad ya zabga mata harara yace matata
ba gurguwa bace, we dont need it, jawad ya
nade hannun rigarsa ya sabi fadila sama kamar
wata baby ko kunyan Amal be ji ba yayi waje da
ita, ya na tafia yana cewa baby gida zamuje
kinji? Ta murguda bakih tace ai naji komai ko
mallam? Yace wai idan bakiji bane sai na qara
fada miki. Ta turo bakih, ya duqa yayi kissing
dinta, tace ya jawad wats dis? Nan ya dan
karkata ya bude back seat, yace kar ki daina
murguda min bakih ki gani. Ya kalli Amal dake
ta musu daria yace Hajia muje koh?tace ina zan
bi wadannan fightlovers din? Kar ka damu da
mota nake zan bi bayanku? Yayi daria ya bude
driver seat, yace kinsan kawar taki yar rigima
ce, ya dan kalli Fadila ta ko galla mai harara,
yayi daria ya shiga motar.
******
Tun bayan dawowansu gida, jawad Ke kula da
matarsa, har Amal tace zata samo musu mai
aiki Jawad yace kar ta damh, its his duty to take
care of his wife, musamman aka bashi break a
gurin aiki, sun ma kori Alhaji Haladu a aiki don
ana Zarginsa da Murder Case, Jawad ya na kula
da fadila, ita kuwa sai Shagwaba take zuba mai
san ranta, shi kuma yayi ta lallabata yana biye
mata, don jin ta yake kamar jinin cikin
hantarsa, A zaman da sukayi a asibiti ne ta
fahimci cewa Jawad na da saukin kai, da kuma
barkwanci, uwa uba ga iya Soyayayh.Wani

azababben sonsa ke shigarta, har tana jin Jawad
cikin ranta.
Maiduguri
Tsoho ya kura ma kofar parlornsa ido yana so
ya tabbatar da idonsa ba gizau yake mishi ba,
Mu'ammad da ya kasa karasowa ciki saboda
kunya ya zube guiwa bibbiyu yana hawaye, Shi
din ne inji Tsoho, Amar ne, tsoho ya kauda
kansa gefe, da rarrafe Mu'ammar ya qaraso
cikin parlorn ya kama kafaffun tsoho duka yana
neman gafararsa, Tsoho ka Yafe min, na tuba, lh
na tuba, ba zan sake ba, kayi min rai, Tsoho na
da saurin karaya, ga shi kuma yana son jikan sa
sosai, nan da nan ya ji tausayin Mu'ammar, ya
dagoshi ya rungume, Amar, ba ka kyauta min
ba, Amar yayi saurin daga kai, na sani tsoho,
shisa nake neman gafarar ka, Tsoho yace na
yafe maka. Amma ka gaya min dalilinka na
barin gida, Abunda Mu'ammar ya gaya ma Islah
shi ya kara gaya ma Tsoho, tsoho ya jinjina kai,
yace ba kyauta ba, in banda wauta irin taka nisa
da gida zne zai sa ka manta soyayyar wata kuma
ka kuma fara soyayyar wata?yanzu kana sonta
ita islahr?da sauri Amar yace fiye da komai
tsoho, kuma gashi kafin dawowarka na tura ta
karatu, Mu'ammar yace karatu har ina? Tsoho
yace kusa daku chan Ingila, muammar ya
jinjina kai, sam be nuna ma tsoho ya ga Islah ba
ko ya san inda take ba. Tsoho yace ka tashi kaje,
zanyi shawara.
Mu'ammar ya mike ya rungume tsoho yace
Nagode. Ya fita, sai da yaje dakin Hajia Ama da
duk sassan dakinta ya gaidasu duk suna
mamakin dawowarsa da kuma sauyi da yayi na
zuwa gaishe su, kafin ya shiga Sassan Umma
hajja da Sassan dakinta duka ya gaishesu, suma
dai mamakin Shi sukeyi. Sassan su ya nufa wato
sassan hajia Babba, ba ta nan taje sunan jikar
wata kawarta, A kofar parlor yayi Sallama tare
da kutsawa ciki, Hanifa ce zaune kan carpet da
alamun ta ji sauki kafar ta warke, da sauri ta
kalli wanda ya shigo tace Yaya Mu'ammar?
Murmushi ya mata a yanxu banda so na
yanuwantaka, ba wani son da yake mata, ita ma
din haka don ta maye gurbinsa da Zayyad, tace
sannun da zuwa, yauwa Hanifa, ina mutan
gidan? Wallahi sunje suna, me ya sameki a
kafa? Tayi murmushi tace wlh turgudewa nayi
na dan goce anma naji sauqi sosai, Allah sarki
ina maigidan naki? Tace yanzu ya fita, Bilkisu ce
da Suraj sukayi Sallama, Ganin Mu'ammar tsaye
yasata qarasawa da gudu, oyoyo ya'amar,

mu'ammar ya dagata sama yana juyawa, oyoyo
lil sis i missed u, me more bro, Mu'ammar ya
ajiye Bilkisu ya miqa ma Suraj hannu don suyi
musabaha, suraj yayi kicinkicin da fuska, bilkisu
ta mishi Alama da ido, haka dai ya daure ya
bashi hannu, suja gaisa, be yarda Mu'ammar
yaja shi da fira ba ya fita waje don har yanzu
yana jin haushin abunda ya ma qanwarsa. Kafin
kace kwabo magana ta zagaya Gidan Gandu
Mu'ammar ya dawo. Da labari ya iske hajia
babba a gidan suna dole ta musu sallama ta
dauko hanya don ganin Jikanta..
Abuja
Sir, Senior Consultant na neman wa yanda suka
gama housemanship, sakon da ya iske Zayd
kenan a office dinshi Yace okay, gashi nan xuwa,
ya miqe Ya nufi Conference room na meeting
din Doctors, Senior Consultant na nan tsaye ya
na Congratulating dinsu akan gama programme
dinsu da sukayi for almost a year, zai gaisa
dakai sai ka fada mishi sunanka, da aka zo kan
Zaid, ya bashi hannu suka gaisa, yace i am Dr
Zailani, Mutumin ya kura ma zaid ido, yana son
tunano sunan, yace Dr Zailani as in Dr Zaid
Zailani? Xaid ya yi murmushi yana mamakin
yanda akayi ya san sunanshi Zaid, don duk
asivitin dr Zailani ake kiranshi dashi, yace yes
sir, Dr james yace are u married? Zaid yace yes
sir, Dr yace after dis, meet me in my office,
Zaid tace ok sir.
******
Zaid zaune gaban Desk din Dr James, Dr James
yace Dr Zailani, ina so muyi wata magana dakai,
but m not sure dai, but before dat whats d
name of ur wife? Ba tarw da Zaid ya kawo
komai a ransa ba yace Rumaisah Abubakr
Zailani, dr james yace ohh, daman nace m not
sure, sorey for d diaturbance u can go, Zaid
yace no problem sir, but why dd u ask? Dr
James yace 2weeks back akwai wata da tazo
private hospital dina da daddare bearing d
name Badiyya Zaid Zailani, Gaban zaid ya yanke
ya fadi, i am familiar wth hausa names but
bantaba jin irin sunayenta ba, dy are unique,
shisa da kamin introducing kanka as Dr Zailani i
tot she's uo wife or ur sister. Zaid da zufa ya
shiga tsatsafo mai yace Dr, Me ya sameta? Was
she sick? Dr ya tabe bakih, yace d girl is too
arrogant she dint listen to me wen i was
advicing her about HIV and AIDS, Zaid ya xaro
idanuwanshi baki na rawa yace is she?? Dr
James yace Yes She's HIV positive. Luuuu Zaid

ya fadi sumamme.
Gidan Gandu
5⃣6⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Da sauri Dr
James ya tari gaban Zaid, ganin idanuwansa
bude ya sashi zaton ko mutuwa yayi, ya dagoshi
yaga jikinsa da nauyi, ajiyar zuciya ya dake da
ya lura akwai rai jikin Xaid, sai a sannan ya lura
ashe ba suma xaid yayi ba daskarewa yayi lol,
fiffita ya shiga yi ma Zaid, hawaye kawai ke
sunturi a idon Xayd, nan Dr ya fara zargin wani
abu, ko dai badiyyar matarshi ko yaruwarsa? Ya
dan kalleshi a sanyayye yace Zailani let me get
u help, Dr na fita, Zaid ya sulale ya bar office
din Dr James, yana hada hanya yana
tangartangar kamar xai fadi ya nufi motarsa, ya
ma rasa tunannin da xaiyi, ya fincika motarsa
sai gida, a hanya Zaid ya sha kwalbar giya ta kai
hudu, irin gudun da zaid ke shararawa ya wuce
misali, fuskar shi bacin raine zallah, Allah kadai
ya kawo Zaid gida lafia, be ma iya jiran megadi
ya bude mai gate ba ya fito ya shige, tun daga
Gate Zaid yake kwalla ma Diyya kira har ya
shigo parlo, Badiyyan da yanzu tayi baqih ta
rame ta ji kiran xaid agogonta ta kalla ko 1 beyi
ba, lafia toh ya dawo gida yanzu? Ta miqe tazo
parlo, da karfin hali tace swthrt ka dawo, tayi
Yunqurin Rungumeshi, Fayau ya taske ta mari,
ya qara marinta, cikin ihu tace Zaid me na maka
ka tsaneni haka? Cike da takaici yace me kika
man? Har kina da bakin tambayan me kika min?
Ya shiga kwallo da ita ta na kuka, duka ko ta ina
yake mata, da hannunsa da kafar sa, harda su
nushi.
Tunda tayi parking tasan cewa gidan nan babu
lafiya, da sauri ta ftp tayi cikin gida, da gudu ta
qarasa ta riqo Zaid, Haba Yazayd, kayi haquri,
xaid ya daddage ya ture Maysah iya kar
karfinshi ta fadi kasa rajagab, ya cigaba da cin
uban badiyya ta kwala ihu. Maysah bata daddara
ba ta miqe ta qara nufoshi tana jan hannunshi,
yana juyowa ya kamtse ta da marih, ya ja
hannunta ya wurgata dakinshi, yace stay outta
dis, ya dawo yana cire belt din jikinsa ko a haka
ya bar badiyya ta ci duka, Zaid ya shiga laftar
badiyya, a yanxu kasa kukan tayi, cikin tsawa
yace ni kika cuta badiyya?ni kika shafa ma
HIVand AIDS? Da sauri Badiyya ta dagi ta
kalleshi, yanzu ta gane dalilin dukar nan, tana
mamaki ya akayi Xaid ya gane, tayi karfin halin
cewa Myzayd, kayi haquri pls, we can spend d
rest of our lives together, Dr yace if we can
abide by d rules we are safe, Zaid pls forgive

me, we can live long, Akwai hanyar da zamu
morewa rayuwa nd even have kids of our own,
Ya zabga mata belt a gadon baya, ta saki ihu,
Allah ya sawwaqe na, ke ki haifa man yara?
Allah ya kiyaye Mazinaciya ta haifa min yaro, ni
ba dan iska ba, ban taba Zina ba, Diyya tayi wani
murmushi tace yes kai ba mazinaci bane,
Amma kai mashayi ne a wurin Allah daya muke,
so gwara ka sakko mu rufa wa juna asiri aikin
gama ya gama, yau ko sai kin san kin auri
mashayi dan giya wani nushin da Zayd ya ma
Badiyya a baki sai da bakin ya fashe hancin ya
fara habo, ya yarda belt din ya hau ruwan
cikinta na SAKEKI, BADIYYA SAKI 3 sai dai
kanjamau ya kashe ni da na cigaba da zama
dake, ya dinga jibgarta yana nusarta ba sassauta
wa,. Rumaisah ta fito da gudu fuskarta yayi jaaa,
idonta cike da hawaye, ta gama jin komai, kuma
idan ta bar Yazayd zai iya Badiyya, Iya karfinta
ta tattaro Zaid jikinta, da qyar ta iya turashi
daki ta kulle, ke zabin tsoho zo ki budeni kafin
na hada dake, kizo ki budeni, Maysah ta ki
kulashi, tazo gurin da Badiyya ke kwance ta na
nishi sama sama, tace Aunty Badiyya Kiyi
kokarin tashi na kaiki Asibiti, Badiyya ta girgiza
kai na, tace pls Maysah ki yafe min,
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment