Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

dukkan tsiya be yi
ba, ya daga hannu zai mareta, tayi saurin cewa
babban balaeen chan, wlh tlh ka tabani sai na
rama, sai munyi duke duke koni ko kai cikin
gidan nan(jimun ikon Allah sai kace wata me
qarfi), Jawad ya fara zare belt din jikinshi zai
ma fadila duka, da sauri Maysah ta fito, bata
zaci abun yayi zafi haka ba, Ta janyeta daga
gaban Jawad Haba Fadila wats ur prblm?
Yajawad din kike ma tsawa haka, da qarfi fadila
tace ma Maysah Quite just shuttup md watch
him flog me, Kai kuma idan har baka dakeni ba
baka cika Jawad Mudassir Zailani ba, Aikam
Jawad ya daga belt zai shauda mata Mu'ammar
ya qaraso gun da gudunshi tare da riqe belt din,
Ya ja Jawad baya, yace cool down man, ba
girmanka bane, huci jawad kawai yakeyi Fadila
tace ai da ka bar shi ya daken niko na shayar
dashi mamakin rayuwa wlh, Jawad ya zabura
Mu'ammar ya riqo shi, wai kai meke damunka
ne? Sai kace baka san halin jikokin hajia Ama da
umma hajja ba? Ai ba da'a ne dasu ba, basu da
kunya, Fadila ta ma Mu'ammar kallon tara saura
kwata, tace aiko muke da da'a da kunya, ga
babban marasa kunya nan, masoyan ku da
Bilkisu da Haneefa, idan kuwa babban mara
da'a kuke nema toh ga Amira, jikokin waye?
Last i checked jikokin Hajia-- maysah tayi sauri
rufe mata baki, Ta kalli su, Tace Yajawad,
Ya'ammar don Allah kuyi haquri, ba don halin
mu ba, Jawad ya yarda belt dinshi, yana ma
fadila kallon tsana yace Amar lets go, i dont like
dis Girl at all, fadila ta gantsara ma maysah cizo
a hannu, maysah ta saketa da sauri tana yarfa
hannu, Fadila ta riqe qugu, hey, i dont need-inshort i dont want to be liked by someone like
u, as a matter of Fact, i dont like u either, tana
kaiwa nan ta ja hannun Maysah ta wurgata cikin
mota, ta zagaya ta shiga ta fincike motar ta yi
reverse yare da barin unguwar gabaki daya.

(Eeelerh u get lever oooo)👻
1⃣3⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕By 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Maysah
tace ina zaki kaimu? Ki tsaya, Fadila tayi parking
tare da sauke ajiyar zuciya, first of all kar da ki
qara yi man haka, Shikuma Jawad din ya qara
gigin tabani yagani, zan bashi mamaki wlh,
Maysah tace kiyi haquri sis let it pass, fadila
tace ya wucei, Maysah tace let me drive, ba
musu fadila ta fito ta koma sit din Maysah ita
kuma ta koma ta shige tare da jansu suka nufa
Gida.
*****
Jawad ke hada kayanshi, shi zqi koma Gombe,
tunda uwashi ta haifeshi ba a taba Embarassing
dinshi haka ba, kamar ace yarinya kamar
wannan fadilar ta gaya mai magana be ma ta
komai ba? Dole yake barim garin, haka ya bar
Gidan be ma kowa Sallama ba har bilkisu. Ba
wanda ya san anyi, Mu'ammar be fada ma kowa
ba, Maysah ma haka.
Bilkis tayi tayi ya fada mata abin da yasa shi
tafiya ya qi fada, sai kuma ta sa kuka wai satin
shi 3 bezo weekend ba, gashi yau friday bazaizo
ba? Bayason kukanta yace kar k damu zan biyo
Jirgi InshaAllah Yau din nan, just to see u, don
ni zaman Maid ya Isheni, dadi kamar xai kashe
Bilkisu ta shiga kichin don hada ma Yajawad
Abinci. Kafin ta shiga ta tsara kwalliya.
******
Badiyya ce ta fito daga Airport din Garin
London, kasancewar ba yau ne ta fara zuwa
qasar ba, ta sha zuwa da Alhazawarta, Taxi ta
tsaida tare da fadawa ciki, tace ya kaita cikin
gari, sai da sukayi tafia me nisa kafin ta sauka ta
biyashi, sannan ta tsaida wani Taxi din, tace Ya
kaita Illford shopping center, ya kaita ta
sallameshi, ta shiga ciki, wurin Babban wuri ne,
ba shagon da babu, wurin bangaren yara ta
nufa, ta siya Toys da kaya, kafin ta matsa ta
shiga lodo chocholates, tayi siyayya sosai kuma
ta kashe kudi, Fitowa tayi ta tsaida Cab, tace
akai ta Rand Street, Ba ajima ba suka iso
Unguwar, ta lumshe ido tana tunano kwatancen
gidan Zaid Ali a qwaryar boka. Ta na tunowa ta
na ma me mota kwatance sai ga su har gaban
Gidan, a lokacin har dare ya farayi, ta biyashi
tare da kinkimar leda ta yi qofar gidan, hannu
ta sa ta danne Bell din.
*****
Wata hadadden yarinya nagani da ba ta wuce
20years ba tsaye kan stool, gaban ta wani ne da
alamun dai mijinta ne hadadde ne me cikar

kamala, tie ta ke ciremai, shi ko sai kissing
kumatunta yakeyi yana mata waqan My short
wifey, tana mutsu mutsu tace Yazayd kaga dai
ka Bari, sauri nake da wanne zanji da rigiman
babies dinka ko da rigiman Ka? A lokacin ta
gama kwance tie din, ya sunkuceta cike da so
da qauna yace Yarinyata,bazan gaji da fada miki
ina sonki ba, i love u so much. Hanyar daki yayi
da ita sukaji an dann Bell, Zarah tayi sauko wa
daga jikin mijinta, tace I will get dis, i think
mummyn becky ce, kaje ka fara shower din
kafin nazo, idan kagama ka fara masu Miemee
da Biebie, tana fadan hakan ta na tafia don
bude qofa, unlocing qofar tayi tare da bude
qofar, Gabanta ya yanke ya fadi, mamaki ya cika
Zarah, hasken da ta qara besa ta qi ganeta ba
Baki na rawa tace Ba--diyyah, Badiyya a ranta
tace shegia guntuwa sai kyau take qarawa, a fili
kuwa murmushi tayi tace Hello Baby Zarah, its
good to see u too, ta raba ta shige gidan tare da
barin matar gidan a waje, zarah ta shigo tana
qoqarin qaqaro murmushi sannu da zuwa, ta
shiga kicin ta kawo mata juice da cookies, Zayd
ne ya sauko yana Yarinyata ke da waye? Maman
becky-- maganar ta maqale a fatar bakinshi
sakamakon ganin wata yayi kamar Badiyya,
Badiyya ta miqe ta tako kusa dashi, murya qasa
qasa tace Hello Luv, Zarah tayi saurin shan
gabanta, me ya kawoki Gidan na? Diyya tayi
murmushi tace mutum yana tare da wanda
yakeso, nazo qasar ne, shisa nace sai nazo na
gaidaku, ban kyauta ba? Zarah tace kin kyauta
mungode, now leave, Diyyah ta kalli Zaid Ali
tace how rude of ur wife, is dis how she treats
ur visitors? Zaid ya jefeta da wani irin mugun
kallo, yace badiyya ki bar gidan nan, tace not
until i have wats rytfully mine back, Zarah da
qarfih tace kina hauka, wasu yara yan duguiw
guduiw kyawawwa suka fito da gudu daga wani
dakih, Badiyyah ta nufesu tare da rungumesu,
Hello sweethearts, look wat i bought for u, ta
miqa musu ledojin tsarabar da ta musu,
Miemee ta kalli uwarta tace Mummy who is
she?? Zarah tace miemee do u remember dat
monster dat was chasing u in ur dreams?? Da
sauri ta gyada kai Tace is she d monster
mummy? Zarah ta daga mata kai alamun Eh, da
gudu miemee ta ja er uwarta biebee sukayi
daki. Badiyya ta dago cikin duniyanchi tace dats
very brave, kina brainwashing yaranki, mesa
baki fada musu m dia daddy's first love ba? Zaid
ya daka mata tsawa Enough, get out now before

i call d cops, nd u knw here u dont bribe cops,
so ki fita tun muna shaida juna Badiyya, Zarah
tace u are asking her nicely, ta finciko badiyya
ta wurgar a waje kamar wasu kayan waki, ta
koma da sauri ta dauko ledojijinta ta watsa
mata su a fuska ta nuna ta da yatsa stay away
frm my husband. Kika sake dawowa gidan nan
zakiga abunda zai faru dake.Ta kullo qofar sa
qarfih. Zaid ya sunkuceta yace karki damu, she
isnt going to ever come back, nd if ta qara
dawowa, she is going to face me not u. Ta
rungume shi tace i love u yazayd lets go nd
calm ur babies down yayi murmushi tare da
nufar dakin yaran da ita👻(wanda basu karanta
Akwai Lokaci na biebee isa ba, ku nema ku
karanta).
****
Kuka Badiyya keyi sosai, wai itace nan? Mqewa
tayi tana bin hanya tana kuka, Zarah nd Zayd
must pay for dis, wayarta ta ciro ta latso
Bokanta, tana kuka tace Boka sun wulaqantani
boka ina so kayi musu--- shiru tayi ta bi wani gu
da kallo, Numfashinta qiris ya rage ya dauke
sakamakon wanda ta gani tsaye daga gefe
sanye da 3qtr da top sai Hula Qube ta mazan
hausawa, waya yakeyi kuma da harshen hausa,
Boka yace hello hello diyyan shagali kina jina?
Da sauri Badiyya tace zan sake kiranka, ta share
hawayenta ta nufa gurinsa tun da ya dago kai ya
kalleta be dauke idonsa ba, ya cigaba da
wayarsa Jawad kasan dai banda manyan kaya?
Ka dinko min kuma kace ma tsoho ba sai ya
biyoni ba, cikin satin nan zan dawo, Bye i gotta
go. Daidai nan Badiyya ta fashe da kuka da sauri
ya qarisa gunta Hey Miss, are u okay? Ta girgixa
mai kai, wat happened to u? Cikin kissa tace yau
na xo banda ma sauki, kallonta yayi yace kina
jin hausa ne dama? Ba gashi nayi kaji ba? Muje
na sama maki masauki, tace bansan kowa ba,
pls take me wit u, bansan hannun da zan fada
ba, kaga kai musulmi ne danuwana pls ka
taimakeni ya danyi guntun tsaki yace da uban
wa ya kawo ki nan din? Tace wlh Grads naxo, ya
tsaida musu Cab, ya shiga gaba ta fada baya da
sauri, Wooow take fada a ranta, wannan gayen
ya hadu,ban taba ganin hadadden gaye
kamarshi ba, yo wannan ai ya fi wanda tazo
qasar danshi kyau, Ai dole zatayi aiki kan
wannan, dole take samun wannan a matsayin
Miji, tana tunane tunanenta suka iso wani dan
qaramin gida, Ya fito ta bi bayanshi ya bude
suka shiga, har dakin shi ya kaita, yace ki kwana

a nan kafin gobe na sama miki gurin zama, ta yi
mai far da ido, tace Nagode sosai Allah ya saka
da Alheri. Ya miqe zai fita, tace Bawan Allah kai
dan Nigeria ne? Ya daga kai eh, wani gari yace
Maiduguri, tayi farr da ido, laaa ashe dan garin
mu ne, pls ya sunanka? Cikin qosawa yace
Sunana ZAID MUDASSIR ZAILANI👻👻
1⃣4⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕by💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Badiyya ta
maimaita sunan Zaid sunanka? Ya ce eh sunan
kenan, ya bar mata dakin, badiyya ta fada gado
tana murna, Zaid ya tafi Zaid ya dawo, wannan
zaid din yafi Zaid Ali kyau da wayewa, to su
zarah a jiqa zaid a sha na sami wanda ya fi shi
komai, daman wanin halin ga Allah baiwa ne
wannan zaid din bazan yarda ya kubuce mun ba,
haka ta kwanta tana me farincikin wannan sauyi
da Allah ya mata.
*****
Zaid M.Zailani jikan Alhaji M.Zailani, da Hajiya
karime da ga Mudassir da Abida Fari dogo me
cikar halitta, Shekarunsa 28, a yanzu ya gama
karatun likitancinsa a nan Oxford University,
Zaid ya cika komai saidai matsalarsa Daya
shaye shayen da yakeyi da taurin zuciya, be bin
mata, a ganinsa mata matsala ne, yanmatan
turawa sun sha chusa kansu gunsa amma ya na
basarwa, Tina kadai yake saurara itama Iyakarsa
da ita romance be zarcewa da yaga ta na neman
wuce gona da iri zai tsallaketa, Zayd be shakkar
kowa abunda ya sa agaba shi yakeyi, ba me
chanza mai raayinsa tun yana qarami, ko Jawad
sai dai ya shafa mai lafiya gurin Kaffiya, sun Sha
fada da Zayyad, Lokacin da suke makaeanta
Zayyad na mai nasiha kan shayeshaye, amma
sai ya fara mai masifa yana fadin its a free
world, so kowa yayi harkan gabanshi, duk
Zuri'ar M Zailani daga iyayen zuwa jikokin ba
me shan ko da sigari ne, sai Zaid, be fiye shan
taba ba sai Giya, shan giyansa ma na masu aji
yakeyi, sai dare yake sha. Hakan ya kasance a
yanzu, fridge ya bude ya dauko kwalbar
Giyyanshi ya fara kwankwada, yana lumshe
idanuwa. Badiyya ce ta fito daga dakih ta na
neman kicin Ganinshi tayi kwance kan 1sitter,
daga shi sai singlet, nan da nan diyya ta
kwadaitu da shi, haka ta haye Zaid, cikin bacci
yaji ana shafanshi, ya miqe da sauri idanuwansu
suka qanqance, Zaid ya hankadeta, cikin tangadi
yace keee, are u trying to rape me?? Diyya ta
mai far da ido, ta sa hannunta kan bakinta tace
mai shhhh, ya koyi shirun, ta fada kanshi ta
shiga kissing dinshi, ya biye mata, tana qoqari

zuge mai belt yayi saurin watsar da ita a qasa,
ya nuna ta da yatsa dont even think abt dis. Yayi
cikin daki ya barta yashe a qasa, side smile
Badiyya tayi tace muje zuwa. Daki ta bishi ta
ganshi yashe kan gado, gyara mai kwanciya tayi
ta zo ta baya ta runguneshi, suka yi bacci,
assalatu ya tada Zaid, ganin Badiyya yayi
rungume dashi tana sharar bacci, komi da ya
faru jiya ya dawo mai, ya qare ma Badiyya
kallo, kyakyauwa ce, daman akwai masu kyan
nan a Naija, well haka yake son mace wayayya,
ya miqe ya shiga toilet yayi wanka tare da
dauro alwala, be tada ta ba ko da yayi sallah, ya
shiga kicin dan hado musu brk fst, 8am ta fito
Tana wannan yauqi tana kwarkwasa ta zube
jikinshi,ta bashi peck G'mrn My Zaid, be hanta
abunda take mai ba, m so hungry, yace i cooked
u brkfast, tayi farrr rwly? Show me, Yace i will if
u let me, ta gane me yake nufi ta daga shi da
sauri, ya riqo hannunta ya kaita har kichin, suka
zauna suka ci tare, harda feeding juna, cikin
kwana 3 badiyya ta siye zuciyar zaid, haka yake
son Matan Naija su kasance a waye, kullum
suna maqale da juna. Badiyya ta fahimci Zaid,
iyakanshi Romance. Sai ta daina zaqewa tana
biye mai yanda yakeso.
*******
Ta kalleshi cike da qauna tace My jawad, wats
troubling u dis days? Yayi faking smile yace
bakomai baby, tace me ya sa ka tafi ba tare da
kamin bankwana ba lst 3weeks? Kuma da kazo
last week ba mu samu munyi magana ba, me ya
faru? Yace bakomi kissu na, tace har ka fara
boye mun abu ko ya jawad? Noo baby ba haka
bne toh menene? Nan ya kwashe komai ya gaya
mata game da abunda ya hadasu da fadila,
bilkisu ta tashi tana huci kam balaee, Shine ka
qyaleta? Yace hey babe chill mana, ya wuce,
tace wlh be wuce ba, ya kamo hannunta duka
biyu yace nace ya wuce ko? Ta ce naji, ta miqe
ta barshi zaune.Dakin Aj ta shiga ta na huci ke
lpya? Tace kinji kinji, ta kwashe komai ta gaya
mata ita ma tace balaee, harda Ya'amar dina
aka ma rashin kunya, tashi muje sassan su.suka
fita gabaki daya.
*****
Hajia Ama zaune tana bare gyada, su Bilkisu
suka shigo, sai da gaban hajia ama ya fadi don
ba zata iya tuna ranar qarshen da suka shigo
sassanta ba, Ba su da niyar gaisheta, tace mai
gado lapya? Bilkisu ta watsa mata harara hanifa
tace ina maras kunyan jikarki? Fadila nake nufi

Hajia Ama tace ba sa nan suna chan gidan
Yayanku hafiz dukkansu 3, yayansu dai ba
yayanmu bq, don mu ba hada jini da mayu da
aljanu ba, hajia Ama tace kuyi hqri, Bilkis tace
idan bamuyi hqr ba hauka zamuyi? Suraj da
Zayyad da suna cikin dakin Ama, tun shigowar
su sukejin su, Suraj yace yaran nan basu da
kunya, ya fita Zayyad ya bi bayanshi, ke uban wa
kuke ma magana haka? Hanifa ta kalleshi galala
ta watsar, dan ubanki nikike ma wannan kallon?
Tace an kalla din, bilkis tace ke kika tsaya
kulashi, ni ai idan na raina bola ko shara ba
zubawa cikinta, tass kakeji ya kamtseta da
marih, ya juya ya ba hanifa nata Allah ya isa
mugu azzalumi shege daniska, charr ran maxa
ya baci, belt ya ciro ya fara shauda musu,
Zayyad ya qwace su yace ku gudu, yaja shi yana
haba, meyasa ka biye musu, hajia Ama ma
fadan biye musu da yayi takeyi. Da gudu suka yi
sassan Hajia Babba suna kuka, hankalinga ya
tashi, da qarfi ta fito, wai waye, uban me kuke
ma kuka? Nan suka shirga mata qarya da gaskia,
wai Zayyad da Suraj ne suka kullesu suka musu
dan banzan duka, ko dankwali bata sa ba tayi
sassan Hajia Ama da sauri masifa na cinta,
Aishalle yau sai kin ci buhun ubanki, kika sa
jikokin ki suka ma bayin Allah duka ko? Nima
yau sai munyi na mu, Ama ta fito, suraj da
Zayyad na bayanta, tana kar ku sake kuce
komai, kuna jina? Ama ta kalleta tace kiyi hqr
yaya karime, ba haqurin da zanyi, shegu mayyu
wanda suka gaji maita, sai na daka ki yau cikin
gidan nan, tayo kanta gadan gadan ta maqure
nata wuya, Suraj ya finciko hajia babba ya
watsar a qasa, wani irin Ihuuu hajia babba ta
sake kamar an sa Lasfika, daidai nan Jawad ya
iso, yana zuwa ya sakar ma Suraj nushi a hanci,
suraj beyi watawata ba, ya rama nan dambe ya
kaure, Zayyad yazo da niyyar rabasu, Jawad ya
kaimai nashi nushi a baki, nan zayyad ya zuciya
ya rama, sai abun ya koma 2in1, Ihu su hanifa
keyi hajia babba nayi, Hajia Ama tayi saurin
shiga sassan Umma hajja don ta ga ko su baba
Abbakar na nan, fadan qarfi akeyi anan fadila,
Maysah da Islah suka shigo gidan, ganin fadan
maza yasasu sakin kuka duka, Maysah tayi
sassan Tsoho da gudu, bawanda ya iya shiga
fadan sbd duk mata ne, Islah tayi boys qrts don
neman Yasamir. Har jawad ya far habo ga jini ta
baki.
*****
Shigowan shi gidan kenan, daga nesa ya hango

su suna dambe, hango jawad yayi yana firda
jini, danuwanshi uwa daya uba daya aka ma
wannan taron dangi? Balaeee, yarda trollynsa
yayi ya cire er whyt top dinsa yayi wurgi da ita,
ya ruga da gudu, wani tsalle yayi ya chafko
zayyad ya hadashi da bango, ya finciko Suraj ya
dinga kaimai nushi, abunka da wanda ke gym'n
Jawad ya dago kai ya kalleshi ya sakar da
murmushi suka tarar ma Suraj, suna duka,
daidai nan Tsoho ya iso gurin Ba kasafai yake
fitowa daga parlornsa ba, amma yau shine har
sassa, Su hanifa sai kuka akeyi, hajia babba na
ganin tsoho ta qara fashewa da kuka, Samir ya
rugo da gudu tare da Mu'ammar zasu shiga filin
dagan Tsoho ya musu alamu su tsaya, tsoho
yace ku bar fadan nan, Ku bari nace, Jawad ya
bar dukan Suraj, shi ko wannan cigabawa yayi
da kilar suraj kamar Allah ya aikoshi, tsoho ya
qara cewa nace ka bari ko? Ai da alamu be jin
tsoho, da qarfi Tsoho Yace ZAIDU👻👻1⃣5⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 by💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Ture Suraj
yayi tare da zuwa ya dauko rigarsa ya nufi
sassan su, duk suka bishi da kallo, Tsoho ya kalli
Samir tare da miqa mai wayarsa ya ce kiramin
Dr Munnir, hannu na rawaSamir yayi dialling no
din, ringing daya ya dauka ya miqa ma tsoho,
Allah ya qara ma tsoho tsawon rai, Dr muna
lpy? Ya amsa, yauwa danAllah kazo ka duba min
yara na nan, yace toh gani nan zuwa, Tsoho yace
kowa ya tafi sashensa. Zayyad ya kama suraj ya
kaishi dakin Ama, aka watse. Ba a jima ba Dr
yazo, a duba Suraj, ya bashi pain reliver Tsoho
yace aje a duba Jawad, ko da Dr yaje sashen
hajia Babba korarsa tayi tace ba sa buqatar
likita munufukan banza..
******
Har kwana 2 shiru kakeji, kowa yayi zaton Tsoho
zaiyi magana akan fadan shekaran jiya qala be
ce ma kowa ba, kamar baayi ba, Be qullaci kowa
ba, ko da Zaid yazo gaisheshi be nuna mai
komai ba faramfaram, yana mai wasan kaka da
jika, har suna sa ran Tsoho zai masu magana
amma be ce komai ba.
Hajia Babba ji take da Zaid, duk cikin jikoki ta fi
yi dashi, amma gurza mata RM yakeyi,
mamanshi Abida ma tafi sonsa.
*****
Lamarin Gidan ya qara tuburewa sabon Gaba ya
qara qulluwa, Samarin Gidan kuwa zumuncin su
ya baci, dama suke zumunci a gidan amma tin
bayan fadan nan ba me cewa dan uwansa qala,
Gaba me qarfih suka dauka da junansu. Duk
wa'annan abubuwan da suke Tsoho na sane da

su.
Ya samu su Ido, yana tunanin shikuma haka
Qaddararsa take? Gaban da Iyalansa keyi na
matuqar damunsa. Amma InshaAllah komi yazo
qarshe, yasan abinyi..
****
Haka ne bigbrosamir abubuwan gidan nan ya
rinchabe, kowa gaba yakeyi, ni ba abunda ya
damen da gaba kowa nawa ne, yace shiya sa
kike burgeni ba ruwan ki da 'yan ubanci,tace
kaima ai haka bigbrosamir shisa nake sonka,
yayi daria, yanzu ka fa da mun wannan shigar
zai burge Yazayd? Samir yace sis na fiso ki bar
mgnr Zaid, tayi rau rau da fuska zatayi kuka, ba
zan mishi ba ko yasamir? Ba zaiso ni ba? Duk ta
bashi tausayi don yasan ta na son zaid, yace kar
ki damu zai soki, bana so kikai kanki ne, na fiso
ya zo gunki tace toh shkn bigbrosamir, zan
kama kaina.
*****
Ta shigo Gidan da motarta, Taci gayu sosai, ta
fito ta na taku daidai, fitowar Amira daga
sassan Umma hajja kenan taga baquwar fuska,
Amirah ta nufeta da murmushi sannu da zuwa,
Badiyya tace yauwa, Amirah tace gun Hajja
Ama kika zo ko umma Hajja? Badiyya tayi far
da ido, ko daya, gun Zaid nazo da fatan yana
nan, Nan da nan fuskar Amira tayi dif, tace
bashi kike binshi ko tara? Diyya tayi dan
murmushi yan dunia tace ko daya naxo ansar
zuciyata ne da ya sace min, da fatan kinsan inda
ya ajiye shi, in ran amira yayi dubu ya baci, tace
ke shegia eriska me bin maza har gidansu, ki
bar gurin nan ko wlh na miki tunbur kuma na
lalada miki dan banzan duka Badiyya tayi daria,
ke yarinya, kinsan dai ni ba tsarar ki bace ko? A
banza zan baki shekaru 5 ko 6, zan miki uzuri
daya dan naga kina kama da myzayd, nd kamar
kina hauka da sai kinyi nadamar furucin nan,
Amirah tace na rantse da Allah ina iyawa, idan
kin san mutuncin kanki ki bar gidan nan ynz, in
ko ba haka ba, zaki ga Haukana don mugun
bugu zan miki, na kareraya ki, na kaiki asibiti na
kuma yi jinyarki, Daria sosai badiyya keyi,
Amira ta kwnace dankwali au daria ma na baki
ko? Tayi dammara, daidai nan Maysah ya qaraso
gun da gudu ta sha gaban Amira, Haba Amira
me ya hadaki da baquwa? Wannan er iskar zata
shigo mana gida tai mana karuwanci, wai her
Zaid, ko uban wa yabata yazaid din, haba Amira
kiyi hqr mana, ke dalla matsa matsoraciya,
tsayuwar rin wannan cikin gidan nan balaee ne,

Ji gashin doki, ji man kanti ji matsatsun kaya,
wlh kamar jikar bokan tudun qarfe, ai wlh sai ta
bar gidan nan ynz ba anjima ba, kafin Allah ya
jarrabe mu da Kwarantsa cikin Gida, Maysah
tace haba Amira, ita ko diyya daria kawai take,
Maysah ta juya ta kalli diyyah haka kurum taji
gabanta ya fadi, ko me ya sata faduwar Gaba
oho? Ta dai daure tace baiwarAllah kiyi haquri
danAllah, Yazayd kike nema? Bari a dubo maki
shi, ta ja hannun Amira, daga nesa suka hango
Yazayd din na jogging, ita ko badiyya ta qarasa
gun shi, shikuma ya daga ta sama suka rungume
juna, Haka kurum Maysah taji gabanta ya
tsananta bugawa, Amira kuwa baki ta bude
galala, kaiii Rumguma? Tsanar Yazayd da karuwa
(sunan da ta samata)ya shigeta, meye haka,
gabansu suke iskanci? Bata ga komai ba sai da
taji badiyya nacewa haba Zayd kai da kace zaka
nemeni har kwana 5 shiru? Nayi missing dinka,
ina tunanin ko ka mance ni? Cikin sigar lallashi
yace so sorry my diyyah, wlh i was busy ne, har
yau ban siya sim ba shisa ban nemeki ba, but its
a good thing u came over, i'm glad to see u, ya
akayi kika gane gidan? Ta mai far da ido, kasan
familyn Zailani ba boyayye bane, yace haka ne,
Sai sannan Zaid ya lura da Meerah da ke tsaye
wata a gefenta ba tare da ya kalli Maysah ba, ya
kalli Amira yace ke ya ma sunanki?? Amirah ta
watsa mai wani mugun harara, Badiyya tace kai
honeybunch ur sis is hilarious, ya danyi gyatsine
yace haka take bata da hankali, ya qara kallon
Amira yace Zo ki kai Badiyya gurin Hajia Babba
kice mata baquwa tace, Badiyya tace Oh no
dear, ba yau ba, i jus came to check on u, but
next time musamman zanzo gaida Inlaw's na,
yayi dariar jin dadi yace yauwa sweety, ya ja
hannunta ya rakata har mota, Amirah da Maysa
suka bisu da ido, Maysah na tir da wannan hali
nasu, Ameerah kuwa takaici da baqin ciki kamar
tayi kuka, Maysah ta ja hannunta ta fizge tayi
dakin Yasamir,Yana ganinta ya miqe tsaye yace
lilsismeerah menene waya tabaki? Ta na huci,
bigbrosamir daman Yazayd dan iska ne? Ynz
wata tazo gidan nan nemanshi kaga yanda ya
rungumeta? Ta kwashe komai ta gaya mai,
Samir yace toufa, shima Zaid da rigima yake,
yasandai ba wanda zai aura mishi bare, kar ki
damu kece matarshi, na auri wannan? Allah
shi kyauta na aureshi, kai kaga abunda sukeyi?
Ai wlh bazan aureshi ba, shi gashi wayayye. Yayi
karatu turai ya zama chris tucker, toh wayewa
ma ya ci ubanshi, Samir daria ya fara, isit funny

bigbrosamir? Ni ynz wa zai aureni? Kowannen
ku is in lov? Kuma ni ba zan auri daniska ba wlh,
kar kuma Tsoho yace zai zaban mun daga cikin
yayyinmu wanda sukayi aure. Shidai Samir har
yagaji da surutan Amira, ya daiyi shiru yana
jinta, wani Lokaci tabashi daria wani Lokaci ta
bashi takaici, shidai yace Allah ya shirya Amira
nikuma biebee nace Amin👻
n
by biebee
GIDAN GANDU
1⃣6🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕
⃣ GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Hajia
Babba, Hajia Ama da Umma Hajja zaune a
parlor, Tsoho ya kalli Ama yace Aishalle me ya
faru sati 2 da suka wuce? Aishalle tayi
murmushi don ta san ko ba dade ko ba jima sai
yayi maganar, nan ta kwashe komai ta fadi mai
tun daga shigowan su Hanifa har fadan, Tsoho
ya jinjina kai, Charaf hajia babba ta chafe, baka
da labarin rashin ta idon da Fadila ta ma Jawad,
rashin kunya da zage zage, amma be ko kalleta
ba balle ya duketa, toh shi suraj ya hade bilkin
da hanifan ya zane, shi ko zaid ya zo ya lakada
mai na jaki ai dan'uwa befi danuwa ba. Tsoho
yace shikenan, Allah shi kyauta, ku tashi ku tafi,
ya kalli Umma hajja, yace ki turo mun Hassan
Hussaini da Gambo tace to Mallam hajia babba
ta buga tsoki, M.Zailani ya gyada kai Allah ka
shirya.
*******
Baba Hassan, B.Hussaini da B.Gambo zaune a
kasa kan carpet, Tsoho yace toh kunji hukuncin
da na yanke ya kuka gani? Baba hussaini ya nisa
yace anya Baba wannan abu xai yiwu, kasan
gaban nan me
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment