Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

hawaye, Cikin damuwa
Zayyad yace pls Hanifa, lemmie help you, ko
karfin magana bata da, amma da yake jinin
hajia babba na cikin bargonta, tayi qoqarin
bude bakih tace I dont need your help...
_Bibilicious Biebee_
3⃣1⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕tsura mata ido
yyi yana kallonta, chan ta cije bakih tare da
fadin Waiyo Hajiarmu, da sauri Zayyad ya kira
wata nurse a waya ta shaida mai gata nan tafe,
Hanifa ta jigata amma taqi yarda Zayyad ya
taimaka mata, Har isowan nurse din tana nan
kwance da sauri nurse din ta shiga agaza mata,
bayan ta gano bakin zaren neh, ta mata Allura,
ta rubuts magunguna tare da ce mai kar ya tada
hankalinshi, period ne wands ke xuwa ma mata
everymonth. Ita nata da hakan yazo, Zayyad ya
tausaya mata sosai, har ya na tunanin dama zai
iya dauke ciwon ya maida ma kansa da yayi, don
shi Allah yayi shi da tausayin mace, Yanzu duk
month haka zata kasance? Allah sarki Allah ya
baki lpy.
Zaria
Ko da ya iso Zaria, Staright gidan Ammar yayi,
yana sakawa da warwarewa, har ya danna horn
a gaban gidan, cikin rawar jiki me gadi ya
budeh, Islah ta leqo ta window, ganin Yayanta
ne ya sa ta fita da gudu, yana parker motan ya
fito, Islah ta rungumeshi tare da fashewa da
wani irin kuka me tsuma rai Suraj ya rungumi
k'anwarsa, yana bubbuga mata baya alamun
rarrashi, tayi shiru tana ajiyar zuciya, ya ja
hannunta har parlo, Ya kalleta yace Isi meya
fadu dake? Nan ta kwashe komai ta gaya mai,
Ran Maza ya qara baci, ohh baki san cewa baya
ma kasar ba? Ta dago rinannu idanuwanta ta
kalleshi, baya kasar? Ina yaje? Suraj ya mike,
yace i dont know, nd i dont care, all i knw is dat
u wont sleep a day here again, je ki kwaso
kayan ki, da gudu ta shuge dakih A gurguje ta
hada kayanta cikin Katoton Akwati, ta dauki duk
wani abun da zaats amfana, ta qwala mai kirah,
yaya i need help here, zuwa yayi ya ja akwatin
tare da fadin ragguwa, tayi daria tare da kulle
ko ina, suka fita ta ba ma mai gadi key, Mai gadi
na son tmby amms ganin ba fuska ya sa shi yin
shiru, haka suka dauki hanyar Kano. Ba su rufe
Awa 3 suka shigo kano, Bilkisu na nan zaune,
Islah ta shigo da Sallama, kallo daya ta musu ta
watsar, sai dsi ta amsa sallamar chan ciki, Islah
tayi murmushi kisuwa matar yaya, ta kalleta ta

harara, Islah dai ta zauna tana jiran suraj ya
shigo, Sai ko gashi da Akwati, Bilkisu ta miqe
tayi hanyar daki, ya kalleta yace madam a nuna
ma Isi dakinki inda zata kwana koh? Harara ta
banka mai tace ba shegiar da zata kwana min
dakih, Yayi azaman damk'o wuyanta, da sauri
Islah tace haba Yaya ka barta mana, ni ko a
parlor sai na kwana, Suraj ya ja kayanta Ya tura
dakin Bilkisu yace idan har bazaki iya kwana
daki daya da ita ba, to u have to choice ko
dakina ko parlor, Allah ya sawwaqe na kwana
dakin ka, kuma ba zaa zo gidana a sani kwanan
parlor ba Wlh ta buga tsoki ta shige dakin, Suraj
yayi murmushin takaici yace yau zaki gane baki
da wayau, yayi niyyar bin ta daki ya lallasata
Islah ta tsaida shi, haba yaya, ai ba a biyewa,
Bilkisu qanwarka ce fa, zakaji dadi Yayanta ya
duke nih? Ka kwantar da Hankalinka, zan kwanta
parlo, wlh bazaki kwanta a parlo ba, saidai ki
kwana chan dakina nisai na kwanta a parlo, tace
ok none of us will sleep here, i will talk to
bilkisu. Suraj yace dnt waste ur tym sis, she's
never going to change, dnt forget she's got
hajia babba's blood running thru her veins,
Islah daria tayi tace i will try my best.
******
Kan Gado ta iske ta, zama tayih kusa da ita tare
da riqo hannunta, bilkisu ta harareta tare da
janye hannunta, Islah ba ta daddara ba ta sake
riqe hannunta tare da murmushi, ta cire baki ta
kira ta, Bilkisu, ba ta damu da rashin tankata ta
fara magana, Bilkisu, u are my lil sister and i
love u so much despite d fact dat u hate me
much as u hate my brother, tun muna yara mu
ka tashi da tsabar junan mu ba tare da sannin
tak'amaiman abun da ya sa mu ke kin jinin
junan mu, yes zamuce babu shiri tsakanin
iyayenmu da kakaninmu, Shekara da Shekaru
maganar arziki bata taba shiga tsakanin mu ba,
fadan yau daban na Gobe ma daban. Gashi har
munyi aure, I got married to u brother, nd u
got married to mine, ji dai saboda kiyayya,
Yayanki ya tsallake ni ya bar Kasar ba tare da
sanina ba, saboda tsanar daya mun bema son
ya bude ido ya ganni cikin gidansa, tunda aka
kaini betaba kwana gidan ba, ji dai zamanki da
yaya suraj, babu wata magana me dadi, ki kalli
girman YaSuraj ki maida mishi magana,kiyi mai
rashin kunya, kuma kina sane da wannan auren
anyi shi ne har abada, idan kina tunanin
Yajawad xai dawo miki, to ki cire wnnan
tunsnin, theres NO chance dat we'll all get back

to our lovers, Mesa ba zamu cika ma Tsoho
burinsa ba? For how long zamu cigaba da
wannan rayuwa? For how long xamuyi tayin
gabar nan? Think Bilkisu, think, i knw u have a
good heart, itsjust dat u let Anger controls u.
Kiyi tunani Bilkisu. Tana kaiwa nan ta haye gado
ta kwanta, Jikin Bilkisu yayi Sanyih, ta san duk
abin da takeyi ba daidai bane, duk abinda Islah
tace hakan ne, zama tayi tana tunanin Rayuwa,
Abun da ta kasa ganewa shine Suraj ne mijin ta
na har abada, ta bar tunanin Jawad, lokaci daya
hawaye ya fara sintiri a idonta, dama tun Asali
Bilkisu bata da nayi sai abunda Hanifa tace tayi,
bar ta dai da riqo idan ka mata laifi, Hanifa ke
controlling dinta, daga karshe Kwanciya tayi
gefen Islah.
******
WasheGari Bilkisu na tashi ta shiga kicin ta hada
musu breakfast, abun da bata taba yi ba, wato
hada abinci da Suraj, sai da ta kammala ta shiga
dakih, har ynz Isi na bacci da yake tana fashin
Sallah, Bilkisu ta shuga wanka, ta fito tana
shiryawa ne Islah ta tashi, tare da fadib matar
yaya good morning, harara ta sakar mata amma
irin hararan nan na wasa me murmushi, Islah a
ranta tace Alhamdulilah, ta fara sakowa, toilet
ta shiga ta shirya. Misalin Qarfe 8 ya fito parlo,
Ganin Coolers akan dinning ya sa shi mamaki,
ko da yake kila lil sis dinshi ce ta hada musu
break don yasab strongheaded Bilkisu ba zatayi
ba, da Karfih yace Isiiiii, Islah tace Yaya ka fito?
Yace yup. Ta ja hannun Bilkisu bayan ta gama
shiri, tace zo muje parlo, Bilki ta bata rai tace
kije kawai, haba mana matar yaya, ki ajiye
wannan pride din gefe, ur husband is awake,
Bilkisu ta tunzura, kinga dai bana so koh? Ya
haquri, zo muje parlorn, da qyar ta bita
parlorn, ya bisu da ido, sunyi matuqar kyau da
kama da suka jero, Islah ta lura da mayatacen
kallon da suraj ya bishi da su. Suraj ya mazeh
yace Islah naji girkin ki na qamshi zo kiyi
serving dina i cant wait to eat lil sis cooking,
islah tace Yaya, i dint cook dis food, cikin
mamaki yace who did? Ta daga kafadu tace ur
wife did. Bilkisu ta dauke fuska kamar bata san
da zamansu a parlorn ba, Suraj ya kalli bilkisu,
wato yau yaci darajar Islah har break aka yi
mishi, yaji dadi amma ya share yace
Islahulkhair yi sauri ki karya, don yau nake son
na dawo ba kwana zanyi ba, Bilkisu na san cewa
ta bishi amma girman kanta ya hanata, haka
suka gama breakfast suraj ya sa kayan Islah

mota, Islah ta rungumeta tana jin hawayen
bilkisu a kafadun ta, amma batace mata komai
ba, har bakin mota ta raka Islah batare da ta
kalli Suraj ba, ta koma ciki da gudu sakamakon
hawayen da ke niyyar fito mata, bro donAllah
muje da ita, tunda ba kwana xakayi ba, ya
girgiza kansa, ta bashi tausayi, yace gwara tayi
zamanta lil sis, sai nan gaba ita da maiduguri,
idan ba haka ba Hajia Babba da Aunty Sadiya za
su kara chusa mata wasu abubuwan banza a rai,
na samu ta fara sakkowa. Islah ta jinjina kai.
Haka Suraj ya bar gate din gidan suka kama
Hanyar Maiduguri.
3⃣2⃣&3⃣3⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕
Abuja
Da Kyar ya samu ya zame jikinsa daga jikinta,
ya fara gajia da jarabbar Badiyya, shikenan ita
ba ta da wani aiki sai wannan, gashi sai kiransa
akeyi a asibiti, yau shine Dr on Call, ya kalli
Agogo Karfe 10 da rabi, tsaki yayi ya shiga
wanka, ko da ya fito tana nan kwance kamar
ruwa, tsaki ya sake bugawa, a gurguje ya shirya
cikin suit dinshi, ya bar gidan.
Maiduguri
Fitowar ta kenan daga Sassan Umma Hajja ta ga
wani mota kamar motar YaSuraj ya danno kai,
shi din ne k'ila da bilkisu donsu biyu ne, ta fada
a ranta, ta tsaya tana kallo har sukayi parking,
Islah ta fito suka hada ido, ai da gudu suka rugo
suka rungume Juna Maysah tace Hey Sis, me
kikeyi a Maiduguri? Noo i shud be asking u d
same, Suraj yace Maysah ba ta ganni bane, da
sauri Rumaysah ta sake Islah ta qarasa gunshi
tana daria, sorry Yasuraj, wlh i was carried
away, ina wuni! Suka gaisa tace ina mutan
gidan? Suna Sassa, Amma Aunty Hussaina
(maman su Islah) ds Aunty Hassana sunje biki,
islah tace toww, bari na kai gaisuwa gun Tsoho, i
missed him alot, taja hannun Maysah sukayi
gaba, Suraj ya daga murya Isiii wa zai daukar
miki wannan k'aton Akwatin? Tayi daria haba
bigbro, ka qarashe ladarka mana, yace zaki sani,
suna tafia Maysah tace Islah wat ar u duin here
har da qaton Akwati? Islah tace kar ki damu sis
sai dai mun zauna. Haka suka qarasa parlorn
Tsoho, Hajia Babba ce zaune kusa da Tsoho
suna cin Tuffah, Sallama sukayi tsoho ya dago ya
amsa, sai kuma ya fadada murmushin shi,
Rumah wacece na ke gani kamar Islahulkhair.
Itace tsoho, Islah ta qarasa gunsa tare da daura
Kanta kan cinyarsa, tsoho ya shafa kanta yana
daria, Islah kin yi kewa na da yawa, nima

haka.tayi murmushi ta durqusa ta gaida kakar
mijinta hajia babba, sai da Hajia Babba ta gama
hura hancinta kafin ta amsa, ko uban wa ya
kawo ta? Bata gama tunani ba sai ga Suraj yayo
sallama, Tsoho yace kai Surajo yanzu kaima
kake tafeh? Suraj ya shigo ya duqah yana
kwasar gaisuwa. Tsoho ya amsa cike da jin dadi,
irin jin dadin da yakeji a duk lokacin da
jikokinsa suka zo gaidasu, yana sonsu sosai,
Rumah yau baki be rufuwa an ga Yar uwa,
maysah tayi murmushi, Islahulkhairi ina Mijin
naki? Ko sai ya gama gaida iyayensa kafin zaizo
gaisheni, Damm gaban hajia babba ya buga.
Islah tayi shiru, yace ina Mu'ammar din ne wai?
Da qyar Islah tace ba tare muke ba da Yaya
Suraj nake, A'aha chan kika bark mijin naki?
Suraj yayi saurin cewa ai yayi tafia ba ya ma
qasar, hajia karime tayi saurin tashi don barin
wurin, sai dai tsoho ya katse mata hanzari.
Karime ina Mu'ammar yaje? Yands tsoho yayi
maganan zaka san cewa ransa a bace yake, ta
fara inda inda, Ai ya danyi wata tafiya ne, amma
ya kusa dawowa, tsoho cikin bacin rai yace
Mu'ammar ya ya bar kasar nan ba tare da
sanina ba? Tayi karaf tace Ai ba dadewa zaiyi ba,
ke karime, ki fita idonaba dadewa zaiyi ba? Toh
mesa ba a gaya min ba? Ke kinsani me sa baki
sanar dani ba? Tace yi haquri na Shafa'ah ne, ya
juya ya kalli Islah ke Islahulkhair me yasa me
tafi dake ba?kyarma ta fara yi don bata taba
ganin bacin ran tsoho kamar na yau ba, Suraj
yace ki bude baki kiyi magana, ta lura shi suraj
ko a jikinsa, ta kasa magana karshe sai ta fashe
da kuka. Suraj yace Tsoho bari dai kaji maganar
gaskia, tun da aka daura auren nan aka kai Islah
Zaria bata saka Mu'ammar a ido ba, be taba
zuwa yaji ya take ba, ya ta kwana ko me take
buqata, haka ya barta ta dinga kwana a gidan ita
kadai cike da tsoro da fargaba, bata taba sanar
da kowa ba, Hajia babba ta fara borin kunya yo
dama ya zaiyi ya kwana gida daya da ita, ya
rantse ya maya ba zai iya kwana rumfa daya da
ita ba don ko ba sonta yake ba, ina dalili? Sursj
ya harzuqa, wato mu da muke kwana da wanda
ba ma so miye kashe mu? Ko ce miki akayi
muna sonsu? Maysah ta ce Yasuraj kayi shiru
DanAllah, kayi haquri kabar maganan, Hajia
Babba tace bar tsinannen, bar shi ya cigaba,
karshe ma ya bugeni, da wannan gaya min
magana da yakeyi, Islah dai kanta a kasa tana
kuka.. Sallamar baba hassan da Baba Umar yayi
daidai da sake Sallatinsu, Baba hassan ya qaraso

da sauri yana fadin hawaye? A idon baba? Waya
sa baba kuka? Gabaki daya suka juya kallonsu ga
tsoho, abun mamaki hawaye kwance a kumatun
tsoho, hajia babba tace hawaye? Lallai abun ya
girmama, baba Umar ya zube gaban tsoho yace
Allah ya huci ranka babanmu, ka fada mun
wanne daga cikin yaranmu suka sa ka kuka mu
tsine musu su bi dunia. Ya kalli yaransa islah da
suraj yace wallahi sai na tsine ma ku in dai a
dalilin ku baba ya zubda hawaye. Tun Yarintata
har girmana ban taba ganin hawayen baba ba
sai yau, ba abun da zai hana nayi muku bakih,
da qyar tsoho yace Umaru, baban suraj ya kalli
tsoho, yace kullll na qara jin kace xaka ma dan
cikin ka baki, ka bari, ba ka san hadarin bakin
mahaifa ba? Shi dai be ce komai ba, ya kalli
Baba Hassan, yace Hassan jeka kiramin Labaran
koma dai kira min kowa a gidan. Baba hassan ya
fita jiki na rawa, hajia babba kuwa jikinta yayi
sanyih matuqa, tunani takeyi wabi hukunci
tsoho zai yanke don taga ya dauki abun da
Zafih...
Lagos
Hanifa ya jikin naki? Wata uwar Harara ta zabga
mai, yace Allah ya bki haquri, zan fita ne idan
da akwai abun da zan siyo miki sai ki fada, ko
tanka shi batayi ba ta tashi ta bar mai dakin ta
shigewarta toilet,zama yayi bakin bedside
drawer tare da dafe kanshi, oh Allah yanzu shi
kuma haka zai cigaba da rayuwars? Hanifa fa
qanwar qanwarsa ce, don ko ya girmi Zaid, ya
kuma girmi Jawad amma yana tolerating din
hallayarta. Wayarsa ya jawo ya kira besty dinsa,
ringining daya ta dauka, hello Atutu, yes Ango,
kina ina ne? Ina gida, kasan ina shirin tafia, ina
zaki? Tace gobe zan tafi Umrah ya dnyi jim, tace
anything? yace yes lets meet up pls, tace now?
Yes like now where? Yace ur eatery, tace ok i
will jus dress up, see you there, ya miqe ya fita
ya shige mota sai TANQUIEEZ Eatery, Befi
15mins da zuwa ba itama ta iso cikin shigarta ta
alfarma. Ta zauna Ango lafiya? Haka ka koma?
Yace Fatiti ya znyi da Hanifa? Bata sona, ba ta
qaunata, ba ta mun magana, shekaranjiya she
fell sick kamar zata mutu, tana ta murqususu
kamar zata shideh, nazo cikin tashin hankali ina
tambayarta wats wrong wlh fati in kin tanka
itama ta tanka, na zo zan taimaka mata ta tashi,
yanda kika san wuta ya tabata tayi saurin janye
jikinta, nace let me help u hanifa, qiriri qiriri
naga tsanata a kwayar idonta, yarinyan nan ta
kalle ni taxe she doesnt need my help, zayyad

ya qarashe maganarsa kamar zaiyi kuka. Atutu
tayi shiru tana nazari tare da tausayin abokin
nata, tace Zayyad ka cigaba da haquri da Addua,
InshaAllah she will come to her senses, nd
nasan tana sonka, ya girgiza kansa no, bata sona
i can see hatred in her eyes, tace we will find
out if she loves u or not. Yace how?? Tace we
will make her jealous...
*********
Duk sunyi zaune sunyi tsuru tsuru kowa na son
ji me ya faru, barin ma aunty hussaina da ta
shigo ynz, ganin Islah da suraj gaban Tsoho ya
sa hankalinta tashi, Allah kasa taron nan ban
dan su bane, Allah yasa ba laifi sukayi ba. Tsoho
ya kalli Baba Labaran(Baban Mu'ammar) Da
Aunty Sadiya yace Labaran kunsan da tafiar
Mu'ammar kasashen waje? Baba labaran ya rasa
ta cewa ya fara inda inda, Ke Saadiya da izinin ki
Mu'ammar ya bar matarsa ya bar kasar? Tayi
shiru, ya juya ya kalli yan parlorn ya zayyane
musu komai abun da ke faruwa tsakanin Islah
da Amar, wuri ya dauki salati, Aunty Hussaina
sai da tayi hawaye sbd tausayin diyarta. Baba
labaran ya ce ayi haquri Alhaji, mun tuba, a
yafe mu. Tsoho ya kalli baba labaran yace
Labaran idan ban isa da kai ba, ban haifeka ba ai
na isa da matarka kuma nine na haifeta. Kuma
ina tunanin ya ci ace an sanar dani tafiar
Mu'ammar, da sauri baba labaran yace donAllah
kar kace haka wlh tallahi bamu da uba sai kai, ni
da danuwa na Mudassir ba mu da wanda ya fika,
kaine uban mu, kar ka juya mana baya. Ni kaina
bansan da tafiar Mu'ammar ba sai rannan da zai
tafi, ka yafe min. Tsoho ya tabe bakih yace kira
min Mu'ammar a wayah, nan fa daya duk gidan
ba me numban Mu'ammar, tun tafiarsa be kira
kowa ba, Baba labaran ya rantse be da numban
Mu'ammar don be kira sa ba, Aunty Sadiya ma
tace ba ta da numbern shi. Tsoho yayi shiru ya
kalli Islah yace kiyi haquri Islahulkhair,
Mu'ammar ya bar qasar nan saboda be son
bude ido ya ganki koh? Yana so har sai na gaji
da ganinki na raba aurenku koh? Toh ga sako
zuwa ga Mu'ammar, ni Musbahu Zailani ba zan
raba auren Islahulkhair da Mu'ammar ba, Idan
ya dawo nan kusa falillahil Hamd, idan ko be
dawo ba, ko shekaru dubu zai yi qasar waje to
ya san da saninsa cewa Islahulkhair na nan da
aure, ko da xai sake wani auren ba tare da
saninmu ba, Auren Islah na kansa, Akwai
Aurenshi akanta, kuma Auren nan har abada sai
dai in daya ya riga daya mutuwa, ku isar da

saqona gunsa in ma hanani numbarsa kukayi to
a Banza, ku tashi ku tafi na sallami Kowa.
_Bibilicious Biebee
3⃣4⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Islahulkhair
zatayi magana Babanta Ya girgiza kansa ta ja
bakinta tayi shiru, haka suka fara fita daga
parlon tsoho, Hajia Ama ta ja Islah sashenta, ta
dinga bata magana ta hanyar Waazi da kalamai
masu sanyaya rai, ta rungumeta tace kar ki sa
komai a ranki, ki tafi sassan ku ki huta kinji?
Maysah ku je, Maysah ta ja hannun ta sukayi
Sassan Baba Umar, Islah tace ke Maysah baki
gaya min ynda zamanki da yazayd ya kasance
ba, ina fatan zaman naku da sauki, Maysha tace
hmmm kinji kinji, ta kwashe komai ta gaya
mata tun daga barinta gidan tsoho da yanda
suka biya suks dauki diyya har zaman bautan da
ta ma diyya da uwarta xuwa dawowanta nan,
Islah ta jinjina kai, lallai kinyi qoqari, ynz sai da
yaxayd ya auri karuwarsa? Ke gwara muyi
zaman mu nan da mu koma gidajen mu muna
kwasar bakin ciki. Kinsan qazantar da baki gani
ba toh maidata tsafta. Maysah ta jinjina kai
Allah ya mana da kyau tace amin. Mu danno
Fadila. Ringing daya biyu ta dauka, Amaryar Ya
Amar Islah tace banza ki hau IMO muyi
VideoCall tace ok, Nan suka fara video call, Islah
tace Guess what? Fadila tace ke banason
guessing games tell me, Islah ta hasko mata
Maysah Ihu fadila ta saka tace noway, wlh ba
zan yarda ba, ke kikaje Abuja? Ko ita ta zo
Zaria? Wait kamar dakinmu na Sassa, suka
kyalkyale da daria, wai wat are u two doing in
Maiduguri? Its a long story my sis, dallah ku
gaya min, nan Maysag ta kwashe labarinta ta
fada ma Fadila, Islah ma ta fada mata nata,
Fadila ta hau masifa, ke Maysah haka kike
dama? Duk da bani san jawad wlh be isa ya
kawo min karuwa da uwarta nayi hidima da su
ba, kambu, kin hadiye da yawa, sanyin zuciyarki
tayi yawa haqurin ki yayi yawa, gashi yaso ya
ajiyeki, lallai, kaii dangin hajia Babba ba suyi
ba, Shine Ya'ammar ya tsallake qasar ko? To yafi
ruwa gudu, kar ya tsaya kasar sin ya qara gaba,
Amma wlh banso hukuncin da tsoho ya yanke
ba, tsoho na shiga haqqinmu, da sauri Islah tace
keee yi shiru, kar ki sa su baba su tsine mana,
duk suka yi daria. Maysah tace Eeelerh ya
zamanki da Yajawad, fadila ta kyaba bakih, tace
ni ina ruwana dashi ba abunda ya dameni dashi.
Kowa harkar sa yakeyi. Suka ce laaa Allah shi
kyauta.

*****
Ya Suraj ne ya leqo yace kuna ina?ni zan juya,
Islah da Maysah suka fito, Yaya ka kwana mana,
noo Isi, i need to go now, toh Allah ya tsare,
wai Maysah me kikeyi ne anan ko kema Zaid
din ya bar qasar ne? Duk suka sa daria tace Aaa
yaya aure ya qarah, Suraj ya zaro ido yace
Aure? Waya aura? Tace wata Badiyya ce, suraj
da mamaki yace Bareh? Tsoho ya yarda? Tace
ehh amma Appa ya daura auren, suraj ya
girgixa kai ya na mamakin uncle Abbakar da ya
daura auren kishiyar diyarsa. Suka rakashi ya
ma Umma hajja bankwana, suka shiga sashen
Hajia Ama, sannan sukayi sashen Tsoho inda
tsoho yace Suraj ka ji tsoron Allah, kar ka
Wulaqanta Bilkisu don kaga Mu'ammar ya
wulaqanta Islah, kowa yayi da kyau zai gani,
Suraj yace InshaAllah Tsoho ya mai sallama...
Bayan wata 3(3months later)
Ba abunda ya sauya nadaga Rayuwar Xuriar
Zailani, ko wanne na chan na fama, Duk lokacin
da hanifa zatayi period dai ta sha wahala, yanzu
ya abun ya shahara har suma takeyi, ta
gwammace ta mutu da Zayyad ya taimaka mata
a cewarta. A bangaren Samir da Amira kuwa
kullum Amira sau ta bibiyeshi tana mai
magana, wani zubin ya amsata wani zubin kuma
ya watsar da ita, abun ya dameta, amma ba
taba gaya wa kowa ba, kusan da cewa Amira tayi
sanyih ba Amirar da bace, Suraj da Bilkisu kuwa
fada ya ragu tsakaninsu, Bilkisu za tayi abinci
dashi, amma ba ya ganinta, rayuwar dakih ta
komayi, zata gama abinci kafin ya da wo aiki da
ta gama zata shigewarta daki, shi ma da ya
dawo xai ci abinci yayi dakinsa, be nemanta don
yana jin buruntunta a cikin dakih. Jawad da
Fadila kuwa ba Uhm ba Uhm Uhm, kowannensu
jiran dan uwansa yakeyi ya tanka su hau sama
da masifa, amma kowannensu na kame kai, ba
ruwan kowa da kowa, in ma ya fita be dawowa
sai chan dare, ita kuwa da ta gaji da xaman
kadaici sai tayi shigewarta gidan Amal maman
Irfaan, Amal ta zaunar da ita tana mata nasihohi
da waazin haqqin miji, amma fadila kunnen
uwar shegu takeyi da ita, maganan ya shiga
tanan ya fita tanan. A fannin yan Abuja, Ango da
Amaryarsa, cin karensu sukeyi ba babbaka,
Badiyya ba ta da wani aikinyi sai neman zaid,
shi ko Zaid ya qi jin abubuwan da take mai, ba
dare ba rana, har beson dawowa daga aiki, in
ma ya dawo ya ga zata matsa mai sai dai ya
tsallake ta ya wuce ys shige dakinsa ya kulle, in

ko ya mata haka har kuka take mar. Islah ko da
Maysah sunyi qibarsu ba su da wata matsala,
kullum suna tare da tsoho, Mu'ammar na chan
wata uwa dunia ba wanda ke ds labarinsa. Tsoho
ya sama Zaid ido be kirashi ba be nemeshi ba,
jira yake ya gudun ruwansa ko xaizo daukar
matarsa ko ba zai zo ba. A gun Zaid kuwa
tsakanin sa da Allah ya manta da wata Maysah,
tunda ya bar maiduguri ve qara waiwayenta ba
sai Yau Asabar.
Daga shi Sai Diyyarsa cikin mota, Kadan ya rage
su iso Maiduguri, Gun Maman diyyar sukaxo,
wai bata jin dadi ita diyyar zata rakata India, so
shi zaid din gobe zai koma Abuja, ko da suka iso
Gidansu Zaid suka wuce duk da diyyar bataso
hakan ba, straight dakin Hajia Babba tayi
shikuma yayi Sassan Tsoho, Ganin mutum
sukayi qiqam a kansu, Aunty Abida tace ina
muka samo wannan kuma? Hajia babba ta duba
tace Laaaah Er gayu ce, diyya ta qaraso hajiar
mu ina wuni, lafya lao er gayu, ta kallo Aunty
Abida tace Sannu, Aunty Abida tace yauwa,
Hajia wacece wannan? Hajia babba tace ban son
tsiyar banza, Badiyyar ce baki gane ba? Mtsw Er
gayu ke da zaidu kuke tafe? Ina zaidun yake? Ta
tabe bakih, yaje gun wanchan tsohon, Aunty
Abida tace keee iya bakinki, baban namu ne
wanchan? Baki da tarbiya koh? Badiyya ta mata
wani mugun kallo, har ga Allah bata gane itace
mamar zaid dinta ba, Hajia Babba tayi karaf
tace ke Abida ban son wulaqanci, baqonka
annabinka, Hajia wani irin iskanci ne wannan?
Baban namu ne wanchan? Ke Abida tafi
sasshenki, Anty Abida ta fita ranta a bace, duk
rashin kirkinta ta na son Tsoho, wai wannan ce
matar Zaid? Lallai ta mata kallon tsoro da farko.
Mata kamar karuwa, ji uban gashin doki a kai,
wai ita zata kalla tace mata sannu, ta tuna
yarinyar arxiki Maysah kullum sai ta shigo
gaisheta, idan ko zata gaidata sai ta zube qasa ta
ce Ina kwana Mummy, amma ko kallo bata
isheta ba, kuma babanta zata ce ma wanchan,
wato shi ba komai bane, Tayi qwafa tace
bakomi, koma menene Zaid kai ka ja mun da ka
auri fitsararriya.
****
Tsoho me ran karfe, Yace Wani kamar Zaid,
yace ba kama bane, nine, yaxo ya kwashi
gaisuwa, tsoho yace daman ana ganinka?
Rabonka da nan wata kusan hudu kenan, Zaid ya
shafa kansa, kayi haquri Tsoho wlh aikine, yace
toh oo ni dai na zata amaryarka ta sa ka mance

da mu kamanta da matarka da ka bari anan.
Dam Gaban Zaid ya fadi, ya maimaita kalmar
mata a ransa, be dinke ba sai da yaji sallamar
Maysah ta shigo da sauri tana tsoho zskaci
Kwadon Rama? Gabanta ya fadi da suka hada
ido baga lurs dashi ba, shi ko sai a sannan ya
tuno da cewa Yarinyar nan na nan. Da sauri ta
saita nutsuwarta tace YaZaid ina wuni? Kazo
lafiya? Be kai ga Amsawa ba sai jin badiyya yayi
tana cewa Myzayd kazo mu tafi pls, kasan mama
na chan itakadai ba ta jin-- maganan ya maqale
a fatar bakinta Idonta ya kaiga Maysah, ta qara
hakse ta ciko sosai. Kallon da take mata ne yayi
yawa hakan yasa Maysah shan jinin jikinta
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment