Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

nayi kuskure dan Allah ki yafemin,
tace na yafemaka abba, dama ban rikeka a raina ba kullum addua nake maka kuma gashi Allah ya amsa min adduata,
ya dago yace nagode mummy dan Allah kicigaba da yi min addua,
mummy tace ay wannan dolene abba addua babu fashi in shaa Allah,
cikin dabara tayi mishi nasiha akan sakaci da addua da kuma son zuciya, dan duk su suka jawo mishi wannan matsalar,
ta dade sosai tana mishi nasiha cikin hikima inda ya fahimci kurakurenshi sosai kuma yayi nadama akansu ba tun yau ba,, jalila taji dadi sosai yadda mummy tayi mishi taje ta hado mishi abinci ta zauna gabanshi yanaci suna hira amma sam hankalinshi baya gurin, zuciyarshi ta tafi can wani tunanin na daban, daga an taba kofa ko yaji takun tafiya zai dago da sauri ko zai kara ganin zulfah,
saida ya gama cin abinci sannan suka fita chemist tare da jalila dake jin dadin dawowar yayanta cikin hayyacinshi .....

Sanah ce durkushe gaban anty amarya da ta zuba tagumi sai kuka takeyi,
anty amarya taga bata da niyyar dakatawa ta daka mata tsawa cikin fushi tace wannan kukan ya isheni ki rufemin baki, duk laifinki ne sanah, nasan bai wuce shegen halinki na yawo da rashin tsaftace muhalli bane ya hada ku, ko kuma akwai wani babban laifin da kikayi mishi dan haka kawai sadeeq bazai miki irin wannan dukan ba,, sanah cikin kuka tace walhy babu abinda na mishi lafiya lau muka shigo gidan nan dashi wai dan kawai nace ke zai fara zuwa gaisarwa shine wannan shegiyar yarinyar taja hannunshi suka wuce dakin mummy ni kuma zuciya ta dibeni na zo buga mata glass ya kareta na sameshi shine yayi min irin wannan dukan wallhy anty sai sadeeq ya raina kanshi yanzun nan zan tafi gurin alpha, amarya cikin firgici tace wani alphan? Sanah tace alpha demola wata kawata ce ta hadani dashi ay badan taimakon da alpha yake min ba da tuni sadeeq ya sakeni ko kuma in zama kashi a gidanshi, duk abubuwan da kika ga yanayi duk aikin demola ne, (subhanallah, astagfirullh).
Anty amarya ta zube a kasa tace ashe ke kika kashe kanki, yanzu ke baki iya kissa ba sanah,
ashe wayewarki ta banza ce baki san yadda zaki magance alamuranki ba sai kin je gurin boka, wa ya fada miki aikin boka naci ya dade yanzu da kowa ya waye addua ta yawaita,
lallai kin tafka babban kuskure, sanah ta riko hannunta tace anty to yanzu ya kike ganin zamuyi dan ni wallhy bazan iya rabuwa da sadeeq ba, anty amarya ta yi jugumm tana tunanin yadda zasuyi, can ta dago tace na gano mafita, zaki zauna a nan gidan kisan duk yadda zakiyi da kissa da dabara har mummy ta saki jiki dake sai ki roki gafararta,
ni kuma zan dinga bi ta gurin daddy har sadeeq ya kara dawowa hannunki daga nan sai ki maidashi naki na dindindin,
sanah tayi dariyar jindadi tace haka ne anty gaskiya naji dadi Allah barmin ke, nan suka gama kullenkullensu har dare yayi suna abu daya...

Hmmmm. ...

Mrs tijjani shattima..
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 4⃣1⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Kwanaki kadan da wucewar wannan alamarin,
su mummy suna cikin farin ciki sosai dan yanzu ya'yanta sun hada kansu,
Nurain da sadeeq in suna gari suna tare ko da yaushe a dakin mummy suna hirah cikin jindadi,

babu abinda yanzu yake damun sadeeq da ya wuce tunanin zulfah da ko kadan ta daina hada hanya dashi, kullum zai zauna saitin dakinsu ko kitchen ko zai ga fitowarta amma inaa dan sam taki yarda su kara haduwa tun ranar da abin ya faru,
wani lokacin yakanji kamar ya tambayi jalila amma sai ya fasa dan karta dauka wani abun ne a ranshi game da zulfah,
shi kuwa bawai sonta yakeyi ba a ganinshi kawai dai zuciyarshi na muradin ganinta ne, duk irin kokawar da gangar jikinshi keyi da zuciyarshi akan fitar da kara son ganinta abin yaci tura dan kamar daďa ingizata yakeyi,
haka shi kadai zaita kewaye gidan ko zaiga inuwarta amma babu hali,
wani lokaci ma in abin ya taso mishi sai yayita magana da zuciyarshi akan ni fa ba son yarinyar nan nakeyi ba to meyasa nakeson ganinta, in ya kasa samo ma kanshi amsa sai yayi tsaki ya runtse idonshi cikin jin zafin abinda zuciyarshi ke mishi. ...

Suna zaune a kitchen suna aiki sai hira sukeyi suna dariya, sanah ta shigo da hijab a jikinta tana murmushi ta karasa ta gaida anty laila,
ta kalleta ta amsa ba yabo ba fallasa, tace kawo in tayaki anty, laila tace no barshi kawai,
ta cigaba da aikinta, jalila ta kama yan wake2 tana girgiza jiki sanah bataga fuska a gurinsu ba bare tace zata tayasu aiki, fita daga kitchen din tayi da sauri tazauna a parlor tana kuka, Nurain suka shigo tare da sadeeq, ganinsu yasa ta kara sauti a kukanta,
sadeeq yayi tsaki ya wuce, nurain ya girgiza kanshi ya karasa kusa da ita yace lafiya me yafaru
ta sauko ta durkusa a kasa tana kuka tace yaya nurain ku yafemin nasan zaiyi wuya ku yafe min, amma dan Allah ku sami koda karamin guri ne a zuciyarku ku yafe min,
ka tayani ba su mummy da sadeeq hakuri wallhy nayi nadama bazan kara yin abinda nayi ba dan Allah,
Nurain ya tausaya mata dan harga Allah ya dauka da gaske ta saduda tunda wata daya kenan tana zarya gurin mummy da sadeeq dasu jalila akan su yafe mata amma babu wanda yake kulata, ya kalleta a hankali yace ya isa haka biyoni , ta mike tana murmushin jindadi tamishi gwalo a baya suka wuce sama,
gefe ta samu ta zauna tana kuka a hankali sadeeq ya mike zai fita nurain ya dakatar dashi yace dawo ka zauna abba, sadeeq ya koma ya zauna yana hararar gurin da sanah take,
nurain ya kalli mummy yace mummy dan son annabi kiyi hakuri ki yafe ma sanah, ko Allah muna mishi laifi ya yafemana ya kamata muma mu xama masu yafiya, dukkan alamu sun nuna cewar sanah har cikin zuciyarta tayi nadama, irinsu lada mutum yake samu in har suka shiryu a sanadiyyarshi kayi hakuri abba ka yafe ma matarka ku koma ku gina rayuwa akan addinin islama, mummy tayi ajiyar zuciya zatayi magana wayarta tayi kara, dauka tayi da sallama daddy yace ku sameni a parlor Aisha, mummy tace to ta mike tace ku tashi muje anjima ma karasa maganar, suka fita dukansu,,,

Daddy yace dafatan kin fahimceni ko Aisha, mummy ta gyada kanta tace hakane Allah ya yafe mana muma,
anty amarya dake kukan munafurci tace nagode yaya da kika yafemana nasan kinada kyakykyawar zuciya nagode sosai yaya,
mummy tace babu komai Allah ya zaunar damu lafiya,
daddy ya kalli sadeeq dake cika yana batsewa yace abbana kayi hakuri ka dauki matarka ka bata dama ta karshe kaji, nasan abbana yana da hakuri kacigaba da hakuri Allah ya maka albarka, acan ciki yace ameen daddy,
ya mike ba tare da ya kara cewa komai ba, daddy yayi dariya a zuciyarshi yace kamar ba shi ake fada dashi akanta ba, dama duk son da ba na Allah ba to tabbas sai an samu matsala,
nan ya cigaba da yi musu nasiha har gurin goma na dare, ya kalli anty amarya yace kije kicema sanah ta fito su tafi,
ta mike taje daki saida ta gama kitsa mata duk yadda zatayi ta kwantar da kanta har ta dawo da martabarta a gurin sadeeq sannan suka fito tana mata fada da karfi kamar da gaske,
a waje suka ga sadeeq shida nurain shima fadan yake mishi sannan suka rankaya mota suka wuce...

Mrs tijjani shattima....
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 4⃣2⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Kwance yake guraren 12am a dakinshi, rungume da pillow idonshi a lumshe yana sauraron wakar ''"manwa laage'' ta film din HNY,
juyi kawai yakeyi yana hango surar zulfa a cikin kwayar idonshi, in ya bude idonshi kuma tunaninta ya addabeshi,
yayi wurgi da pillon yayi tsaki a xuciyarshi yana masifar wannan balain dake neman zame mishi cuta,
ji yakeyi kamar ya rufe ido ya ganshi a cikin gidansu ko zaiga ko da inuwarta ne,
ya mike zaune ya dafe kanshi dan Allah ne kadai yasan yadda yakeji a zuciyarshi, can ya fara kokawa da zuciyarshi akan meyasa zai dinga tunaninta yarinyar da ko sec skull ma bata gama ba, yar kauye kwaila wacce bata waye ba,
sai yaji kamar ya samu saukin abun sai kuma wani sashi na zuciyarshi ya sake bijiro mishi da tunani fiye da na baya,
bude kofar dakin da akayi shi yasa shi dagowa ya kalleta,
ďan karamin tsaki yayi ya kauda kanshi, ta karaso cikin dakin fuskarta dauke da mayaudarin murmushi ta zaune kusa dashi kamshin turarenta ya daki hancinshi,
hannu tasa a kafadunshi tana daddanawa a hankali tace am sorry once again dear in shaa Allahu yanzu ne zamu fara rayuwar aure mai inganci Wanda musulunci ya tanadar mana,
ka yafe min sweety in shaa Allahu bazaka kara samuna da laifi ko wane iri ba, jikin sadeeq ya mutu saboda yadda take mishi waiwaiyi a gaba da bayan wuyanshi, ya kalleta yace komai ya wuce sanah Allah ya yafe mana,
ta shige jikinshi tana mishi godiya cikin salonta da tasan yana rikitashi,
a wannan daren sanah ta nuna mishi tayi missing dinshi matuka,
gareshi kuwa duk wani abu da take mishi sai ya dinga ganin kamar zulface, mikewa yayi babu kwari a jikinshi ya shiga wanka,,
bayan yayi wanka yayi alwala ya fito yayi salloli da adduoin da mummy tace ya dinga yinsu,
rokon Allah ya dingayi akan ya cire mishi tunanin da ya manne a zuciyarshi kamar mayen karfe, ji yakeyi da da yadda zaiyi ya cire xuciyarshi da ya cireta ya huta ko kuma yayi deleting duk wani tunanin da yakeyi akan zulfah,
bai samu bacci ba a wannan daren har saida yayi sallar asuba sannan bacci mai cike da mafarkai ya daukeshi...

Yaya abban daddy kazo ka fitar da mu yawo,
anty jalila ta fita yawo tace bazata je damu ba kuma muma bazamu zauna a gida ba,
ya kalli afrah dake ta mishi surutu yace to maza kuje ku shirya mu tafi bambinos,
ihu suka sa dukkansu su ukun suka wuce ya kwalawa amrah kirah dan yasan itace bata da surutu, ya kalleta cikin dabara yace zaki iya kawo min abinci in ci kafin mu wuce, tace kaii bazan iyaba mummy zata min duka in na bata mata abinci,
yace kuma gashi jalila bata nan ko, tace eh fatsin ma bata nan saidai ince ma mummy tazo ta zuba maka,
yace a'a mummy na hutawa ina ma wannan antyn taku ummm yama sunanta, da sauri tace anty zulfa, yace yauwa ehh ita,
je kice ta kawo min, tace ay ta koma skull yaya baka sani ba,
yayi dariya yace na manta ne amma ay ni na kaita,
tace laaa yaya mu muka kaita da abban ayda banda kai a cikin motar,
yace baki dai ganni ba amma motata na bayan taku maza ki shirya mu tafi,
ta ruga ciki da gudu, ya mike ya fita da sauri dan karsu sashi yawon da bai shirya ba,,

Zama yayi a mota yana tunanin yadda zaiyi ya ganta dan baijin zai iya bacci in har bai ganta ba, ya jingina jikinshi a jikin kujera a fili yace wai meyasa zuciyarshi ta gaza hakuri akan yarinyar nan ne,
meyasa takeson janyo mishi raini gurin kucakar yarinyar nan, why??
Tada motarshi yayi zuciyarshi na ingixashi bai tsinci kanshi a ko ina ba sai a kofar "danbo" tsaki yayi sosai yace to me zance mata,
wai meke faruwa dani ne?, abunda ya dinga tambayar kanshi kenan, in ya tada mota zaiyi gaba sai ya taka burki,
wata zuciyar tace to ka siyan mata wani abu mana kace mummy ce ta aiko ka, murmushi yayi ya tsaya akan wannan shawarar,
siyayya sosai yayi mata a wani store ya tsaya ya siyan mata kaza da fresh milk mai sanyin gaske, sannan ya siya fruits kamar hauka a railway, yana zuwa kofar makarantar suka tambayeshi inda zashi,
yace yazo ganin kanwarshi ne, mai gadi yace gaskiya ba'a ganin yan extnsion a wannan lkcn,
sadeeq yace sako na kawo mata plss ka taimaka in ganta,
yayi jumm sannan yace ya sunanta, sadeeq yace zulfa'u, mai gadi yace zulfa'u wa?, sadeeq ya fara kame2 dan ko za'a yankashi bai san sunan babanta ba,
mai gadin cikin bacin rai yace I tot as mch nasan kai saurayinta ne kawai,, in da kai yayanta ne na gaske ay zaka san sunan mahaifinta,
gaskiya bazaka samu ganinta ba,
sadeeq ranshi ya baci sosai yayi tsaki sosai yana ma zuciyarshi nuni da abunda yake gudu kenan gashi tun a gate an fara yasan ita ko kallonshi ma bazatayi ba,
zaiyi magana uncle majeed ya fito daga cikin motarshi yace hii sannu,
sadeeq ya mika mishi hannu yace yauwa ya kk,
uncle majeed yace am fyn kamar naso inganeka ,
sadeeq yace wrlly,
majeed yace yeah brodan smiling beauty ko,
sadeeq yace noo zulfa'u dai,
uncle majeed yayi murmushi yace ay ita nake nufi, sadeeq yace oo ay bansan nicknm dinta ba kenan, majeed yayi dariya yace muje daga ciki sai in sa a kiramaka ita,
motarshi ya shiga maigadin ya bude musu gate sadeeq ya bishi da harara suka wuce, kofar office dinshi sukayi parking ya bude ma sadeeq yace ya shiga ciki bari ya kirata,
sadeeq ya shiga kayataccen office dinshi wanda ke cikin cafe, office din da ko student da teachers basa shigarshi,
yanzu ma ya shigar da sadeeq ciki ne saboda wata manufa tashi,
ya fita yana murna dan yana ganin yau zai mika kokon bararshi gurin yayan smiley,
sadeeq zaune a office din yanata kalle2, idonshi ya tsaya chakk kan makeken hoton zulfa wanda akayi mata ranar inter house, sai kuma wani a gefenshi rike da speaker a hannunta duk tayi kyau a hotunan sosai,,
kallonsu sadeeq ya tsaya yi haka kawai ya samu kanshi cikin nishadi,
yasa hannu jikin hoton kirjinshi na bugawa da sauri2,
Salamu alaikum ta fadi hade da shigowa dan duk tunaninta farouk ne,
muryarta ta daki dodon kunnenshi ya mayar da bakin glass dinshi da sauri ya waigo, damm!! kirjinta ya buga da karfi ta tsaya tana kallonshi, shima ya kasa dauke idonshi dake cikin glass a kanta.....

Mrs tijjani shattima....
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 4⃣3⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Shuru ne ya ratsa gurin na tsawon mintina 3,
zuciyoyinsu kamar zasu fado dan tsananin bugawa,
zulfah tayi saurin sunkuyar da kanta kasa muryarta na rawa ta katse shurun tace ina yini,
bai bata amsa ba ya tako yazo har inda take,
ya kalleta sama da kasa ya lumshe idonshi murya can ciki yace lafy lau,
shurun ne dai ya kara ziyartar gurin,
kallonta yakeyi sosai tana wasa da yatsun hannunta,
ya kauda kanshi da sauri saboda yadda zuciyarshi ke ingizashi
yace ummm dama mummy ce ta aikoni muje in ki amshi sakon dan sauri nakeyi,
ta gyada kanta ta juya ta fara tafiya kamar wacce kwai ya fashe ma a ciki,
ya bude motar ya shiga sakko da kayan motar tanata kallonshi cikin mamaki dan dai babu abinda bata dashi,
duka2 ma yaushe ta dawo makarantar da mummy xata kara aiko mata da wasu, muryar uncle majeed taji a bayanta yace badai har zai wuce ba,
tayi murmushi kawai ba tare da tace komai ba,
ya kalli sadeeq yace tun yanzu zaka tafi har kun gama hirar,
sadeeq yace unmmm inada gurin da zanje ne,
majeed yace okk to je ki kira su farida suzo su tayaki ko, ko kuma ni in tayaki ya fadi yana mata wani irin kallo mai cike da fassarori, ta zaro ido tayi dariya tace a'a wace ni, bari dai na kirasu ta dauki leda daya tayi gaba ba tare da ta kalli sadeeq dake tsaye jikin motarshi yana kallon irin kallon da majeed ke mata, sai da ta kule sannan ya dauke kanshi hade da ajiyar zuciya ya dawo kusa da sadeeq yana murmushi,
sadeeq yace bari na wuce nagode sosai, uncle majeed yace naga kamar kana sauri da akwai maganar da nake so muyi da kai, sadeeq yace okk ba matsala ina jinka, uncle majeed yace maganar mai muhimmaci ce, ko zaka bani numbrka sai inzo gida in sameka, sadeeq yace babu matsala xan iya baka ko 30mnts ne,
uncle majeed yaji dadi sosai yace to nagode mu shiga ciki,
sadeeq ya rufe motarshi suka wuce ciki,
Abdulmajeed ya kalli sadeeq yace magana zanyi maka akan kanwarka, ko kuma ince inason mika kokon bara na gurinku, tun ranar farko da na daura idona akan kanwarka Allah ya jarabceni da sonta, na kasa fada mata ne saboda ina son ta maida hankalinta tayi karatu,
kuma inason in fara neman izini a gurin iyayenta shiyasa ban sanar mata ba,
yau da na ganka nayi decidn in fada maka so dat kayi min iso gidanku a bani izini, in shaa Allahu zan riketa da amana in har zaka shige min gaba,
zufa ce ke ketowa sadeeq tunda majeed ya fara magana, sai da ya kai aya sannan sadeeq ya cire glass din idonshi ya goge zufa a fuskarshi,
ya kalli majeed, yace naji abinda ka fada, sai dai kuma am sorry to tll u tanada aure,
majeed ya zaro ido yace aure, sadeeq bldly yace yess aure,
innalillahi kawai majeed ke fadi a ranshi dan ya gaza yarda da
abinda sadeeq ya fada mishi,
ya kalli sadeeq idonshi ya soma kadawa saboda tashin hankali yace amma bata taba fada min ba,
kuma a skull ma babu wanda ya sani,
sadeeq da ranshi ya fara baci ya mike yace to yau na fada maka, abinda yasa take karatu mijinta ba anan yake ba,
ya duba agogon hannunshi yace zan wuce Allah ya bamu alkhairi, bai tsaya jin abinda majeed zaice ba ya fita zuciyarshi na suya,,,,

A waje yayi parking motarshi saboda bacin rai, ya shiga cikin gidan bai ko kalli masu gadin dake gaishe shi ba,
a daki ya samu mummy zaune ita da anty laila suna hira,
ya gaishesu ya nemi guri ya zauna, mummy ta kalleshi tace abba lafiya kuwa,
anty laila ta mike tace mummy ay kema kinsan bazai wuce yunwa ba, bari in je in kawo maka gas ta fadi tana mishi dariyar tsokana,
yayi tsaki a zuciyarshi yace dama yunwa ce ke damunshi da yaji dadi,
Dan damuwar dake dankare a zuciyarshi bazata barshi ya iya kai koda rabin loma bakinshi ba,
mummy ta juyo sosai ta maida hankalinta a kanshi,
tace fada min damuwarka abba, ya sunkuyar da kanshi kasa yana tunanin ta inda zai bullo mata da maganar, saida ta tambayeshi kusan sau hudu,
sannan ya daure da kyar yace mummy dan Allah maganar da zan miki karki yi mata wata fassara ta daban,
tace uhumm inajinka, yace ammm-- umm dama wa'azi naji akan haramcin abinda kukayi,
a firgice tace me mukayi,
ya kalleta yace mummy wallhy haramun ne matar aure taje makarantar da maza sukayi mata kawanya, makarantar kwana kuma mummy, ba lallai bane kowa yasan tanada aure, ni kawai fa bawai dan wani abu nake miki maganar ba sai saboda gudun kwasar zunubin da mukeyi dukkan mu,
mummy ta harbo jirgin sadeeq, ta hade rai sosai tace a wane hadisin aka haramta makarantar mace, a kirkirarren hadisin kwakwalwarka ko kuwa,
yau ne kasan cewa zulfah matarka ce, wato dan kana gudun zunubi ne ma yasa kayi magana a lokacin da karatunta yazo karshe,
to ka kwantar da hankalinka dan ni tuni na yanke shawarar rabuwarku saboda bazan cutar da kai da abun da baka so ba, itama gara a saukake mata ta samu wani ta aura kowa ya huta, saboda haka kaje ka kawo min takardarta ni da kai da zulfah duk mu huta da kwasan zunubi,
jikin sadeeq babu inda bai bari saboda tashin hankali, ko kadan ya kasa saita kanshi, mummy dake kallonshi ta wutsiyar ido ta rike dariyar da ke son kufce mata ta kara hade rai tace abba magana nake maka,
cikin rawar murya yace mummy ay kince baki yafemin ba ko bayan ranki in na saketa,
tace ay yanzu ni nace da bakina, wallhy na yafe maka abba duniya da lahira, bazan matsa maka ba tunda kanada wacce kakeso, sadeeq ya mike da kyar kamar xai fadi yace to mummy zan je gida in kawo miki, tace a'a zo akwai takarda anan bari in kira jali--- ya fita da sauri bai jira ta karasa maganar ba,,,
dariya mummy tayi sosai tace lokacin ramuwar mu yayi abba,
sannan ta mike ta rage a.c dake dakin tana mai jin dadin ganin sadeeq yanzu ya fara son zulfa'u, godiya ta dinga yi ma Allah da ya nuna mata wannan ranar da sauran numfashinta....

Mrs tijjani shattima..
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: [16:33, 31/01/2016] Aysha Ya'u Kurah: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 4⃣4⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Allah ne kadai ya tsare sadeeq a hanyar shi ta komawa gida dan sam bai iya kallon gabanshi saboda yadda idonshi ya mishi nauyi sosai, jijiyoyin kanshi sun rike tam kanshi na sarawa kamar zai rabe biyu,
motarshi ma a bude ya barta saboda tsabar rudu, bai ko bi takan sanah ba ya wuce daki ya zube a kan gado,
kalaman mummy da na uncle majeed suka dinga kai kawo a cikin kwakwalwarshi,
ya zaiyi ya fahimtar da mummy halin da yake ciki,
ta ina zai bi ya fara fada mata bazai iya sakin zulfa'u ba, duk da yasan ba sonta yakeyi ba amma bazai taba gigin rabuwa da ita ba,
ya runtse idonshi kanshi kamar zai fado kasa,
mafita ya shiga nema ya kamo can ya kamo nan har dare ya raba bai samo ma kanshi mafita ba,
yana idar da sallar asuba ya shirya kayanshi cikin yar jaka karama hade da abubuwa masu amfani,
dakin sanah ya shiga ya tarda ta tana wawan baccinta da ta saba,
tsaki yaja ya ajiye kudi masu yawa kan mirrow dinta yasa kai ya fita ba tare da ya san inda zashi ba,
airport ya nufa zai hau jirgi ya tafi lagos daga nan ya bar kasar ma baki daya, babu mamaki in har baya kasar da take dole zuciyarshi ta hakura da azabtar dashi da takeyi akan yarinyar dashi ba sonta yakeyi,
text ya tura ma mummy akan tafiya ta sameshi ta gaggawa dan kar taji shi shuru, tana gama karantawa tayi dariya kawai ta ajiye wayar ta cigaba da adduointa..

A lagos ya kama hotel dan ya dan runtsa kadan kafin yamma ya shirya tafiya inda ya yanke shawarar zuwa wato dubai,
karar wayarshi ce ta katse mishi baccin da yakeyi, ya juya yana mika ya dauki wayar, mummy tace an tashi lafiya abba,
gabanshi ya fadi sosai ya mike zaune yace laafiya lau mummy, tace naga text dinka kai kuma maimakon ka sauke nauyin dake kanka kafin ka tafi, to yanzu dai ina jiran--- katse wayar yayi da sauri hade da wurgi da ita ta fadi ta tarwatse, idonshi yayi jawur dan ba karamin chaza mishi kwakwalwa mummy takeyi ba, in dai har zata cigaba da mishi wannan maganar to gaskiya bazai kara kiranta ba,
wata zuciya tace to kai ka rubuta sakin mana tunda dama ba sonta kakeyi ba,
nan da nan wata ta kwabe shi ta mishi nuni da bashi ba kwanciyar hankali in har ya aikata wannan aikin,
kwanciya yayi ya kifa kanshi a pillow ko zai samu sauki abinda yake ji, abubuwan sun mishi yawa, shi ya zaiyi da rayuwarshi, haka ya kwanta yanata juyi har la'asar bai kai komai bakinshi ba, rabon da yaci wani abincin kirki har ya manta,,

Hello anty dee ina kwana,
daga daya bangaren anty amarya tace lfy lau sanah ya gidan da fatan dai kuna nan lafiya, lafiya ba lau ba anty, yanzu na tashi na tarar da kudi akan mirrow na duba ko
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment