Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

yace sorry friend, wallhy na manta ma kana waje,
ay dole ka manta, bani mukulli hilal ya fadi yana hararar shi, sadeeq yace calm dwn abokina baku gaisa da gimbiya ba,
yayi tsaki ya waiga ya kalli sanah da ke kallonshi itama,
zaro ido hilal yayi sosai ya maida kallonshi gurin sadeeq, yace marafa wannan ce sanah,
sadeeq yace yess itace rabin raina, ita nake burin ta zama uwar ya'yana, hilal yayi ajiyar zuciya yace to Allah ya taimaka sannu amarya,
murya can kasa tace yauwa ina wuni, lafiya lau kawai yace,
ya kalli sadeeq yace bani key in wuce sai kazo,
sadeeq ya mika mishi key yace okk sai na taho,
hilal bai kulashi ba ya sa kai ya fita yana tausaya ma abokinshi....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 2⃣7⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Hilal tsaye jikin window a hotel din da suka sauka, ya kalli agogo a karo na uku 11:43 ya maimaita da bakinshi,
yace lallai marafa ya fada tarkon yarinyar nan,
dole in taimaki abokina bazan yarda tayi destroying rayuwarshi ba,
bazan yarda ya aureta har ta haifa mishi gurbatattun ya'ya ba, yana ta "safah da MARWAH" a cikin dakin,
ko abinci kasa ci yayi,
sai after 12 sadeeq ya shigo,
hilal ya dago kai ya kalleshi, sadeeq yace bakayi bacci ba,
hilal yace umm banyi ba,
sadeeq ya daga kafadunshi ya shiga toilet saida yayi wanka sannan ya fito,
spray kadai ya fesa ya kunna tv,
Hilal yace marafah inada magana da kai, sadeeq ya hade rai sosai yace ina jinka,
ya dawo kusa dashi yace akan yarinyar nan da kakeso ne marafah,
sadeeq yace uhumm ina ji,
yace yarinyar nan bata dace da kai ba abokina,
nasan yarinyar nan wallhy bata da kamun kai ko kadan, bai dace ka dauko ma familynka wannan yarinyar ba, wace irin amsa ka tanadan ma ya'yanka in suka taso suka ga mace kamar wannan a matsayin mahaifiyarsu,
kayi tuna'--- enough sadeeq yace da karfi, I hv hrd enough hilal, nasan kasanta ta fada min komai,
hilal baki bude yace ta fada maka komai kuma kake sonta a haka,
sadeeq yace yess me zai hana,
ka bani kunya hilal, dama ashe yadda kake nuna kai ustaz ne ba haka bane ashe green snake ne kai,
ashe ma gara ni duk iskanci na bazan taba neman yin sex da mace ba,
wallhy ka bani kunya hilal,

Hilal cikin rashin fahimta yace ban gane ba fa,
me kake nufi, sadeeq yace sanah ta fada min komai, ta fada min ka nemeta har ka dauketa ka kaita wani guri kana neman raping dinta Allah ya kwaceta a hannunka,
ta fada min komai kuma nasan bazata min karya ba kuma bazata taba zubar da mutuncinta a waje ba,
dama ta fada min kace zakayi komai dan ka bata mata suna tunda taki yarda da kai,
shine zaka zo ka tsara min karya da gaskiya dan in yarda da kai, mtsww yaja tsaki ya juya cikin bacin rai, hilal ya dafe kanshi dan baida mafita a cikin maganar nan, lallai yarinyar nan ta kware sosai a iya sharri,
ya kalli sadeeq cikin damuwa yace ka yarda da abin da tace maka kenan ni baka yarda da abinda nace ba,
tun muna yara muke tare da kai marafa, kasan komai nawa nasan naka,
kasan abinda zanyi nima haka,
kasan bana maka karya bama taba boye sirrikan junanmu, amma a yau ka yarda da maganar macen da baku wuce wata biyu tare ba,
ka bani mamaki marafa,
ba wani mamaki dalla malam sadeeq ya fadi da karfi yace mutum na iya canzawa lokaci daya,
kai da bakinka kace min kasanta kafin ma in fada maka komai,
saboda haka babu abinda zaka fada min in yarda,
hilal idonshi yayi ja sosai yace lallai marafa ka hadu da makirar mace,
wallhy wannan zata rabaka da kowa naka ciki harda mummy da daddy,
nagode sosai da maganganun da ka fada min,
Sadeeq yaja tsaki ya cigaba da kallonshi yana fadin maganganu marasa dadi,

hilal ya koma gefen gado ya dafe kanshi, yayi alkawarin gobe da wuri zai tafi, zai rabu da sadeeq duk ko da irin shakuwar da sukayi zai cigaba da mishi addua har Allah dawo dashi kan hanya, kalmar "fasiki" da sadeeq ya ambatawa hilal ita tafi bata mishi rai, a ranar hilal bai runtsa ba saboda bacin rai, ana idar da sallar asuba ya wuce tashar mota ya hau ya taho kaduna....

Sadeeq na tashi yaga baiga hilal ba, yayi tsaki yace wannan kuma shi ta dama,
son sanah ya rufe ma sadeeq ido ya dauki yarda ya bata,
ta fada mishi karya da gaskiya akan hilal da dan uwanshi Nurain, tasan dole in nurain yaji zai aureta ya fada mishi abinda ya faru ita kuwa zata iya komai dan taga bata rabu da sadeeq ba, zuciyar sadeeq cike take da tsanar hilal da Nurain, ya tsani namijin da bazai iya kama kanshi har ya auri mace kafin ya nemi biyan bukata a gurinta,
godiya ya dinga wa Allah da ya hada shi da sanah, mace kyakykyawa ga aji, gashi bata zubar da mutuncinta gurin wani ďa namiji ba, (tabdijam),

Jalila je ki kiramin farouk,
Kuma kice ma zulfah ta shirya kafin ya fito, jalila ta rufe laptop dinta tace mummy ni wallhy kinsan nafi son a kaita boarding, kinga gara a kaita ko Dambo ne zata fi maida hankali akan karatu kuma hankalinta zaifi kwanciya,
amma anan ga anty amarya ga yaya abba in ya dawo damuwa zata hanata karatu, acan kuwa zata hadu friends ta mance damuwa ta yi karatunta ko ya kikace, mummy tace umm kuma maganarki haka take,
ni matsalata da dambo wannan ďangalallen uniform din,
kinga ita matar aure ce, jalila tace zata iya sa tyt har kasa mummy, dan Allah a kaita can zan hadata da juniors dina wallhy zataji dadin makarantar sosai,,
mummy tace to shikenan bari nurain ya shigo inji ta bakinshi, je ki kirata suje capital school anso result, tace to mummy, ta tashi ta fita cikin jindadi....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 2⃣9⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Ranar monday da safe suka yi shirin kai zulfah makaranta,
tayi kyau sosai cikin uniform dinta white long sleeve top da blue burberry skirt dan karami, ta daura blue suit akan rigar da necktie irin skirt dinta,,
mummy tayi mata nasiha sosai wanda tace tuni ne dan nasan zaki kama mutuncinki, ki kula sosai da karatu, ba ruwanki da kawayen banza,
jalila tace mummy karki damu akwai yaran da zan hadata dasu kuma basu da matsala,
mummy tace to Allah ya bada sa'a sai munzo visitn,
suka fito parlour mummy na daga musu hannu,
anty amarya na zaune a parlon tayi tsaki da taga sun fito, suka gaisheta ta amsa da kyar,
suka wuce dakin daddy, nan ma nasihar yayi mata sannan ya kara bawa jalila kudi in taje skull ta canza mata,
jalila tace lallai kudi sun miki yawa, ga na yaya nurain inga ticket din kudin,,
ta bude jakarta tana dariya ta fito mata dashi, jalila tace wuu kudin sun miki yawa bari in ajiye maki wannan a account saboda wasu bukatu, zulfah tace to amma wadannan takardun sune kudi a makarantar,
jalila tace eh ki ajiyesu da kyau duk abinda zaki siya ki tafi dashi zasu baki,
zulfah ta kara boye shi a jakarta suka wuce,

Admin block sukaje nan aka bawa zulfah class da hostel,
ss1 science suka bata da kyar dan nurain ya roka da art zasu bata saboda performance dinta a interview is poor,
class din suka nufah da wani teacher wanda naji jalila na kiranshi da mr Samuel,
sun tarar da physics teacher a class din mr samuel ya shigo dalibai suka gaisheshi,
Ya amsa, ya gaisa da mr badore sannan yayi introducing new student a gurin sauran daliban,
sit din kusa da wata kyawawar yarinya a ka zaunar da ita,
Yarinyar ta yafito hannun jalila tace anty jally ya kike,
ta shafa fuskarta tace am fyn Rolex,, ga kawa nan na kawo muku, ina frisky,
Rolex tace tana commerce,
jalila tace zan bi ta class dinsu ku riketa amana kinji,
rolex tayi murmushi tace karki damu anty jally hostel dinmu daya,
jalila tace eh, rolex tace to babu komai Allah ya zaunar damu lafiya, ameen jalila tace sannan ta fita tana daga ma zulfah da idonta ya ciko da kwallah hannu,
Physics teacher ya gama koyar dasu sannan geography ya shigo,
daga shi sai break, ana fita break rolex ta koma kusa da zulfah tace hii, am Habiba Usman by name nd uu, zulfa tace Zulfa'u Adam,
rolex tamika mata hannu tace wow nyc name, nyc to meet u, da fatan zamu zama kawaye,
zulfah tayi dariya ta mika mata hannu itama tace in shaa Allah,
da gudu frisky ta shigo class din ta zauna kusa da rolex, ta kalli zulfa tace rolex wannan itace new comer din da anty jally ta kawo,
rolex tace eh mana, frisky ta mika mata hannu tana murmushi tace am Farida yakubu da fatan mun zama kawaye, zulfa tayi murmushi tace eh, rolex ta amshi skul bag dinta ta ajiye a locker suka fita yin break..

Ana tashi suka tayata kwasan kaya suka wuce hostel, cornersu suka shiga duk suka zazzauna suna maida numfashi,
tare suka shirya kayan, kawayensu duk in zasu wuce sai sun shigo sun gaisa da newcomer, saida suka shirya komai sannan suka kwanta dan su huta kafin la'asar tayi, zulfah dai na kallonsu itama ta kwanta tana tunanin irin rayuwar kuma da zatayi a skull, gashi sam bata gane yadda malaman suke koyarwa,
tunanin su jalila ta dinga yi tasan yanzu yan biyu sun dawo gida ta share hawayenta ta runtse idonta ko zatayi bacci...

Mrs tijjani shattima....
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 2⃣8⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Satin sadeeq biyu, duk inda zulfah tasan zasu hadu bata binshi,
shi kuma gareshi hankalinshi kwance yake saboda sun shirya da abin sonshi, soyayyarsu sukeyi baya tuna kowa sai ita, damuwarshi daya yadda mummy ko kallon inda yake batayi a gurin daddy, anty amarya da anty laila kadai yake samun sauki,
yadda mummy da nurain ke mishi abin na matukar damunshi amma wani bangare na zuciyarshi ya kitsa mishi gara hakan saboda yana free lyf dinshi ba'a mashi maganar wannan kucakar yarinyar,,

duk bayan two days yake zuwa abuja gurin sanah har ya koma da matukar kewarta,
dan shi da ta yarda ma da anyi aurensu tun yanzu ya tafi da ita amma sam taki yarda, tace sai nan da 1yr in ta gama makaranta haka ya yarda badan ranshi yaso ba...

Cikin kwanaki Nurain ya gama ciku cikun nema mata makarantr dambo international school dake barnawah kaduna,
ya gama mata komai har uniform da sport wears sun bata, ranar saturday suka tafi shopping ita da jalila, provision jalila tayo mata kamar hauka, babu abinda bata siyan mata ba wanda tasan zata bukata na amfani, haka suka je ta siya mata tyt milk, ash nd white saboda uniform dinta,
sai gurin yamma suka dawo gida,
anty laila ta tayasu shirya kayan suna hira dukansu,
mummy ta shigo tace ma zulfah gobe ki shirya kije ki gaida mahaifinki kinji,
zulfah cikin farin ciki tace to mummy,,
murna zulfah ta dinga yi zata je taga babanta, ta rasa abinda zata rike ta kai mishi yaji dadi..

Karfe biyu driver ya dauko su ya kawosu babbar saura,
zulfah kamar zata balla kofar ta fito saboda murna,
dai2 gidansu motar tayi parking, suna fitowa suka fara jin hayaniya a zaure,
marka ce ta fito ita kadai take masifarta tana ganin zulfah tayi turuss tana kallonta,
zulfah ta tsuguna har kasa tace ina wuni goggo,
marka tabi zulfah da hararar bakin ciki, tace da ban wuni ba zaki ganni,
uban me ya kawoki gidana, ko matsiyacin ubanki bai fada miki karki kara zuwa gidan nan ba,
idon zulfah ya ciko da kwalla,
jalila tayi ma goggo kallon rashin kunya tace ke kuma baiwar Allah me yayi zafi haka, daga magana sai zagi sai kace wacce take jira,
marka ta harari jalila tace na zaga din dan uwarki,
kema na zageki ko kina da abinyi,
jalila cikin bacin rai tace banda abinyi amma zaki gane ba'a zagan min uwa a kwana lafiya,
"Isah" ta kirah drivern da ya kawo su, ya fito da kakin sojoji ya sara mata, tace maza ka kama min matar nan mu tafi da I--- ay goggo bata jira jin karashen ba ta ari na kare da gudu tana ihun neman dauki,
jalila ta dago zulfah tace sorry sis kar dan wannan abun yayi spoiln mood dinki,
kin fita har abada shiyasa take bakin ciki, yanzu ina ne kike ganin zamuga baba, zulfah ta share hawayenta tace mu shiga gidan goggo ameena in tambayeta, jalila tace ma isa suna zuwa,
suka shiga gidansu fa'ee da sallama, fa'ee na daga baya tana wanki ta amsa tana goge hannu, tace waye,
zulfah ta karasa bayan ta dafa bayanta tace fa'ee ni ce,
da sauri fa'ee ta waigo suka hada ido ta kurma ihu ta rungume zulfah, tana fadin goggo ki fito ga zulfa'u,
goggo amina da ta gama suyar gyada marau, ta kashin gida dan ta huta ta mike da sauri tace wace zulfar, fa'ee tace zulfar inna saude ta gidan su marka,
da sauri ta fito itama ta rungumeta harda yar kwallar farin ciki, suka ce zulfah ke ce kika zama haka a cikin wannan dan lokacin,
kai Allah na gode maka da ka nuna min wannan ranar da zulfah ta fita daga kangi,
Allah ya jikan saude da rahama goggo ameena ta fadi tana share hawayen da daga gani na farin ciki ne,
zulfah tace ameen, tare muke da bakuwa, goggo ameena tayi sauri ta kalli jalila,
tace yi hakuri yar nan, zo muje ciki ku huta,
suka shiga daki dukkansu,
goggo ameena ta basu mafici ta fito ta kira fa'ee ta kwance bakin zaninta ta bata dari biyu tace ta siyo musu lemon kwalba a shagon tanimu,, sannan ki dauki kular babanku ki amso min bashin alalen gwangwani na naira 100 a gidan atine kice gobe zan kawo kudin kuma tasa miki manja da yaji da yawa,
kiyi sauri fa,,
fa'ee ta fita da sauri tana murna, cikin minti biyar ta dawo da fanta mai sanyi da alalen gwangwani mai kyan gaske (ni kaina ya bani sha'awa)
cokula goggo ta debo musu da kyar jalila ta fara ci,
tana fara ci taji da dadi suka cinye duka dan atine alalenta baya kwantai saboda yadda take gyarashi,
suna gamawa suka kora da fanta,
goggo ameena taji dadi da sukaci abincin saida sukayi sallah sannan suka fara hira, ta tambayi goggo ina babanta, goggo ameena ta gyara zama ta bata labarin duk abinda ya faru ranar aurenta da auren salaha da kuma tafiyar babanta da kabiru kano,
tace ki kwantar da hankalinki babanki na cikin koshin lafiya, dan suna haduwa da malam kuma yana kewarki kema, ita kuma marka tana ganin sakamakonta amma har yanzu bata san annabi ya faku ba, dan babangida ya auri hanne bayan ya auri salaha,
kullum cikin fada suke basu da wani kwanciyar hankali, yanzu haka delu ta tafi rabon fada itama marka nasan can ta nufa yanzu da kuka ganta, in kikaga salaha da hanne bazaki ganesu ba saboda masifa da bala'i ke abin dai babu dadi,
zulfah tayi ajiyar zuciyar jin lafiyar babanta kalau tace to alhamdulillah goggo dan Allah kice ma baban garbati in yaje yace ina gaisheshi sosai,
goggo tace in shaa Allah zan fada mishi, an sa ranar kawarki fa'ee nan da wata uku, zulfah tace iyye, fa'ee wa zaki aura,
fa'ee ta ruga waje da gudu cikin kunya, goggo ameena tace malam labaran,,
zulfah tace Allah sarki yayan malam saleem aiko na mata murna wallhy,
waiko goggo kinajin labarin malam saleem, fa'ee ta shigo tace eh mana ai tun tafiyarki da sati daya ya koma makaranta yanzu naji ance yana Singapore,
jalila tayi murmushi dan tasan mummy ce tayi sponsoring dinshi da ya samu school a can,
sun dade suna hira sai 5 suka tashi tafiya, jalila ta bawa goggo dubu goma da alkawarin in biki ya zo zasu zo in shaa Allahu, zulfah ta ja hannun fa'ee ta bata dubu biyar cikin kudin da farouk ya bata kafin ya tafi school,
tace koda bana nan zakiyi aure ki siya wani abun dashi, fa'ee tace ina zaki je,
zulfah tace makaranta zan je, ta zaro ido tace a ina,
Zulfa tayi dariya tace anan garin mana,
fa'ee tace kinji dadinki nima malam yace zan cigaba da makaranta, Allah ya bada sa'a zulfah nayi matukar kewarki wallhy,
zulfah tace nima haka fa'ee Allah ya sanya alkhairi,
suka fita ta shiga mota kamar kar su rabu, a cornerr shiga layinsu ta hango delu da marka suna tafe suna masifa kamar karnuka,
wasu mata na binsu a baya suna kallonsu,
ta runtse idonta tayi hamdala ga Allah da ya cireta a cikin wannan rayuwar, Allah ya bata sa'a a karatunta ya daurata akan malamai da ďaliban makarantar....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆3⃣0⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Satin ta uku a makaranta ta fara sabawa da komai na makarantar da taimakon Allah da taimakon kawayenta da basu barinta ta taba komai a provision dinta,
komai da nasu ake amfani a corner,
haka a class duk abinda da bata fahimta ba rolex na koya mata,
wanda itama rolex bata gane ba sai suyi gruo discussion da su charity Ameh da wani ibrahim Adam, yaron nada kokari sosai,
a haka har Allah ya taimaketa ta gane duka subjects din musamman chemistry tafi jin dadin shi..

Rayuwarsu sukeyi gwanin sha'awa su uku gasu dukkansu kyawawa,
kuma suna girmama malamai da seniors dinsu,
wannan dalilin yasa ake kaunarsu duk inda suka shiga, zaman zulfa'u dasu rolex yasa ta kara wayewa, tazama yar gayu sosai duk ranar saturday da daddare suke yin social nyt,
ranar sunday kuma su zauna suyi hirar gidajensu cikin nishadi da kawaye,
rayuwar danbo tanada bambanci da sauran boarding skull saboda babu takura in dai ba a bangaren karatu ba, kasancewar ta mixed school baisa yaran cikinta lalacewa,
kuma duk yaran masu hannu da shuni ne a ciki,
zan iya cewa zulfah nada sa'a a rayuwarta domin wani dan mai kudin ma bai samun damar shigowa makaranta irin danbo, shiyasa takema mummy da duk zuriarta adduar samun aljanna,
ta cire tunanin sadeeq a ranta duk da sonshi na nan makale cikin zuciyarta,
kullum tana adduar Allah ya fitar mata dashi ta huta, tasan Allah maji rokon bawa ne wata rana son zai fita in shaa Allah...

Kwanaki, watanni, sun shura an tasan ma shekara,
daga anyi hutu ake zuwa daukarta a makaranta, haka suna ziyartar junansu da rolex da suke zaune a malali,
sai frisky dake zaune a kinkinau,

Bangaren sadeeq kuwa saura kiriss ya kare karatun shi, duk hutun da yake dawowa baya ganin zulfah hakan yafi mishi dadi, kuma bai taba tambayar ina take ba, haka babu wanda yace mishi ga inda take, yasan dai anty amarya tace makaranta aka kaita,
duk tunanin anty amarya sadeeq ya saki zulfah shiyasa aka kaita makarantar kwana,
shiyasa suke kulle kullensu ita da kanwarta Aneesah da kuma maman sanah,
zaunar da sanah sukayi suka sata a gaba akan ta yarda suyi aure da sadeeq tunda ya matsa, kar hakurinshi ya kare ya hakura ya nemi wata, nan dai suka ingizata ta kirashi tayi mishi kissarta da ta saba, sannan ta mishi maganar aure,
kamar jira yakeyi ya mike tsaye yanata murna yace zaizo gida nan da 2wk in sun gama final training, ranar sadeeq saboda murna har party ya hada a makaranta, farin cikin da yake ciki ba mai misaltuwa bane, sai gurin 2 yayi bacci saboda farin ciki..

Ranar da suka gama bai jira komai ba yayi airport dan baiso ko kadan ya bata lokaci, suna isowa ya dauki drop ya taho kaduna,
sai bayan isha'i ya shigo gida,
da murnarshi ya karaso cikin parlon inda daddy ke zaune, ya durkusa ya gaida mummy,
ta amsa mishi ba yabo ba fallasa, ya juya gurin daddy ya gaisheshi, daddy yace shine ko ka kira kace kana tafe, yayi murmushi yana sosa keya,
nurain ya shigo parlon sadeeq ya gaisheshi ya amsa ya cigaba da magana da mummy, daddy yace aje ayi wanka a huta ko babana,
sadeeq ya sunkuyar da kanshi dan baijin zai iya barin gurin bai fadi abinda ke ranshi ba,
anty amaryace ta shigo, tana mishi sannu da zuwa fuskar nan tata kamar gonar auduga, ta nemi guri kusa da daddy ta zauna,
sadeeq yaji dadin zuwanta kuma ya samu kwarin gwiwa,
amm ummm dama--- daddy yayi dariya yace fadi mana babana, menene,
yace umm daddy dama inaso ka nema min auren sanah ne iyayenta sun ce a turo,

SANAHHH nurain ya fadi da karfi hade da mikewa tsaye....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆3⃣1⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Anty amarya ta saci kallon mummy da daddy dan taga rction dinsu,
basu ce komai ba amma farar fuskar nan ta mummy ta canja tayi jawur saboda bacin rai,
Nurain ya kalli sadeeq cikin daga murya yace wace sanar,
sadeeq wit his fl confdnc yace sanah dai da ka sani,
Nurain zufa ta keto mishi yace kana cikin hankalinka kuwa abba, to in ma hankalinka baya jikinka kayi maza ka nemoshi dan wallahy bazaka auri wannan yarinyar da ita kanta bata san adadin mazan da tayi mu'amala dasu ba,
anty amarya ta rushe da kuka tace sharrin da zakayi ma sanah kenan,
wato dan ta rufa maka asiri shine ita zaka bita da sharri ta mike tayi daki tana kukan munafurci,
daddy hankalinshi ya tashi dan baya son hayaniya ko kadan, yace zunnurain me kake fadi haka,
yace wallhy daddy yarinyar nan bata da maraba da karuwa,
cikin bacin rai sadeeq ya tashi yace sai dai in kaine bakasan yawan matan da kayi mu'amala dasu ba,
amma wallhy sanah kamamiyya ce,
haba yaya nurain dan ka nemeta da fasikanci taki yarda shine zaka bita da sharr--- cikin bacin ran maganarshi nurain yayi kanshi ya dinga marinshi yana dukanshi ta ko ina,
da kyar daddy ya iya janye sadeeq,
fuskar nurain ta canza gaba daya jikinshi sai rawa yakeyi yace ni kake fada ma wannan maganar,
wace mace ce ta isa in nemeta da faskinci, babu ita har duniya ta nade,
sadeeq murya a dashe yace karya kakeyi wallhy ka nemeta bazata maka karya ba,
kuma sanah ta isa ka nemeta saboda har ka mutu bazaka samu mace kamarta ba,

Nurain cikin fushi ya kara yin kanshi, mummy dake kuka ta rikeshi tace barshi nurain,
ranka ya daina baci nasan abinda zakayi nasan kuma wanda bazaka yi ba,
yaje na yarje mishi aurenta yaje ya aureta ta zame mishi uwa wuce muje,
ta kama nurain suka wuce daki tana kuka, daddy ya zaunar da sadeeq ranshi a bace yayi mishi fada sosai akan abinda yayi ma nurain,
sadeeq da zuciyarshi ta kangare yace wallhy daddy da gaske ne abinda na fada bakaji anty amarya ma ta fada ba,
daddy yace ya isheni nace,
gobe zanje nema maka auren kowa ya huta,
tashi kaje kaci abinci ka huta,
sadeeq hankalinshi ya kwanta ya mike yayi dakinshi yana jin dadi, daddy ya runtse idonshi zuciyarshi na tafarfasa, baya kaunar wannan auren amma haka zai yarda ayi kuma yasa a dagema danshi da addua saboda yana cikin halaka,

A dakin mummy kuwa nurain na zaune yana rarrashinta shima idonshi jajur,
da kyar ya lallabata ya tashi ya tafi daki yana tunanin yadda sanah ta maida mishi sadeeq wawa,
babu abinda ke mishi yawo a kwakwalwa kamar sharrin da sanah ta mishi, wato shi bai fadi abinda tayi mishi ba, shine tayi saurin yin rigakafin sharri,
abubuwan da ta mishi ya shiga dawo mishi,

Tunani***
a ranar da abun ya faru ya dawo gida lokacin duka yan gidan basu
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment