Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

lallai manzon Allah s.a.w yayi gaskiya, ya kalli me napep din yace malam da gaske kake fada min wannan maganar,
mutumin yace alkur'an ba karya nakeyi maka ba, to ribar me zanci in nayi maka karya, farouk ya sauka sauri2 yace ina zuwa dan Allah,
karasawa yayi ya danka wa kanikawan motar yace gobe zaizo sai ya fadi kudin aikinshi,
da sauri ya shiga napep din suka wuce ji yakeyi kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a gida,
suna isa ya kira anty laila yace tana ina ne, tace ya shigo ciki suna ciki da su malam saleem,
da sauri yace malam kashe machine dinka kazo muje, gaban me keke napep ya fadi yace bawan Allah babu abin da za'ayi min dai ko,
farouk yayi dariya yace ay malam ka zama dan gida dan Allah shigo muje,
ya kashe napep din ya shiga addua har suka karasa cikin parlon, basu tarar da kowa a parlon ba farouk yace mishi ya zauna yana zuwa, dakin anty laila ya shiga bata ciki, ya kirata a waya tace ya zagayo suna garden..

Bayan sun gama sauraron mati drivern taxi cikin farin ciki anty laila tace karya fure take bata ya'ya,
gaskiya duk wanda ya rike Allah da manzonsa to wallhy bazai tabe ko ya dawwama ciki bakin ciki ba,
kun ga ikon Allah cikin kankanin lokaci shaidu sun kewaye mu har sunyi mana yawa, isma'il yayi dariya yace irin wannan dabaibayin da sukayi ma zulfah ay wadannan shaidun basuyi yawa ba anty, saboda in an ki wani dole a yarda da wani, farouk yace hakane Allah ya kara taimakon mu....

Abba ya kamata kaje ka duba yarinyar nan ko dan cikin da ke jikinta,
ka daina barin zuciya tana rinjaye akan ka daga baya kazo kana dana sani,
ya dago kanshi ya kalli mummy yace wallhy mummy zuciyata ta kasa barina inje gurinta,
kullum ganin ta nakeyi wacce ta rabani da farin cikina, mummy shaidun nan sun isa mutum ya gasgata wannan alamarin, wallhy ko kadan bana son adinga min maganarta,
farouk dake zaune yana latsa waya ya maida earpiece kunnenshi ya fara bin wakar da karfi ya mike yana jan kumatun afrah dake homework, mummy ta harareshi tace umara wai kai meke damunka ne duk ka canza,
yaro sai kace wanda yake kora wani abu,
sadeeq yayi tsaki yace wallhy kuwa mummy tunda suka hada kai da anty lailah suna shirme wai suna bincike shikenan suke ji kamar ana kada su da ruwan hanji,
farouk yayi dariya yace a gurinka ne shirme mudai muna gayyatarka kotu gobe saboda muyi maka tambayoyin mu na shirme,
Sadeeq yayi tsaki ya harareshi yace to ba sai kaxo ka daukeni ka kaini ba,
farouk yace oho dai kuma wallhy idan mukayi nasara ba karam--- muryar nurain ta katseshi,
ya dan duka yace ina wuni yaya, nurain yace lafiya lau farouk, ya kalli mummy yace keyn dakin daddy zaki bani akwai wasu takardu da zan dauka,
tace to ta mike tana hararar farouk,

Binciken takaddun yakeyi mummy na tayashi,
cikin drawrr kayanshi mummy ta bude taga diary da wata takadda a saman shi,
idonta ya ciko da kwalla ta kalli tsohn diaryn ta dauko shi hade da takardar, zama tayi tana duba rayuwar da sukayi tare ta kunci da ta dadi har zuwa auren hadiza mummy duk inda ta bude sai ta zubda hawaye,
rubutun da yayi a karshen diaryn shi ya daga mata hankali, ta dinga binshi tana maimaitawa,
*** ga abin da ke cikin diaryn,,

Innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
Yau alhamis 29 aug ta zame min ranar bakin ciki a rayuwata,
ranar da mantata a gurina abu ne mai matukar wahala sakamakon kama matata Hadiza da cin amanata,
zuciyata bazata iya daukar wannan bakin cikin ba dan bansan shekarun da ta dauka tana cin amanata ba, Allah na gode da baka sa muna rabo tare da ita ba,kuma a kullum ina rokonka ka fitar da gurbatattun iri a cikin zuri'ata..
Mummy jikinta na rawa ta dauki takaddar ta fara karantawa,
Ni Hasheem na saki matata Hadiza saki uku abisa cin amanata da tayi,
can kasa signing dinshi ne da date din da yayi, mummy ta dukunkune takardar tana tunani cikin tashin hankali a zuciyarta tace on 29 ciwonshi ya tashi washe gari ya tafi england, kenan wannan shine dalilin tashin ciwonshi,
nurain ya dafata ta dago a firgice yace mummy tunanin me kikeyi tun dazu nake ce miki na gansu, tace hmmm sannan ta mika mishi takardar, cikin tashin hankali nurain ya gama karanta takaddar, ya kalli mummy yace mummy yanzu ya Za'ayi, tace kaidai bari duk na rikice nurain Allah ya kaimu gobe.....

Mrs tijjani shattima....
[22:00, 06/02/2016] Aysha Ya'u Kurah: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 6⃣5⃣
By Aysha Ya'u Kurah

****10th October ***

Tun asuba anty amarya da sanah ke zaune suna sake sakensu suka kira bamba da maimzy akan kar su yarda su tsorata,
su dake sosai kar wata tambaya ta basu tsoro saboda har yanzu a ganinsu laila bata da wata kwakwarar shaida,
sai gurin takwas suka rabu cikin farin cikin sanah ta wuce dakinta ta tarar da sadeeq na bacci ta shiga wanka ta shirya tana zaman jiranshi ya tashi ya shirya su tafi kotu,,

karfe 10 kotun ta cika makil, kowa na zaune wasu sunyi jugum wasu kuma suna hirar ko yaya wannan rikitacciyar shari'ar zata kaya oho,
Barr saleem, laila, da taheer suna zaune guri daya,
laila ta kalli agogo karfe 10:05 yace saleem isma'il har yanzu bai karaso ba gashi yanzu alkali zai shigo,
saleem ya kalli kofar shigowa kafin yayi magana ya hango ismo tafe rike da hula a hannunshi, karasowa yayi ya mika ma taheer hannu suka gaisa ya zagayo gurin da su saleem suke a hankali yace an gama tana can na bada gadin ta gurin yan sanda,
anty laila tayi dariya tace shegiya lashe money tana tunanin zuwa bank sai ta ganta a court,
ismo yayi dariya yana waige2 ya daga ma farouk hannu ya zauna,

shigowar alkali ne yasa aka samu nutsuwa a kotun,

Da bismillah ya fara kamar yadda ya saba, sannan ya bukaci a gabatar da jadawalinsu ba tare da bata lokaci ba,
bayan introduction na lawyers "saleem da Tahir" sai mai gabatarwa ya mike ya gabatar da shari'ar da za'a cigaba na zulfa'u Adam,
alkali yace batare da bata lokaci ba zamu fara wannan shariar da ta zama karashe, a shigo da mai laifi, aka shigo da zulfa'u da kamanninta suka canza saboda damuwa da rashin cin abinci,
alkali yace barr tahir bismillah, tahir kurah ya mike yace ya mai shari'a ni bani da wata shaida da ta rage in gabatar saboda tun zaman farko na gabatar da shaiduna masu karfi wanda ya kamata ayi musu duba sosai sannan a bi wa wadannan bayin Allahn hakkinsu,
saidai idan daya bangaren sun gabatar da nasu shaidun ina iya yi musu tambaya, nagode ranka ya dade,
sai da aka dau mintina biyu sannan alkali ya dago kanshi yace barr saleem shin kun tanadi shaidun da zaku gabatar a kotu, barr saleem ya mike bayan ya shafa adduar da ya dade yana yi, sannan ya fara da bismillah yace ya mai shari'a kamar yadda kotu tasani ba dani aka gabatar da shariar farko ba,
amma in shaa Allahu daga yau za'a kareta dani bi iznillahi ta'ala, zanso a bani dama in gayyaci sadeeq mijin zulfa'u saboda akwai wasu tambayoyi da zan mishi,
alkali yace an baka dama, sadeeq ya mike ya isa gurin yana kallon zulfa'u da kanta ke kasa,
bayan gabatar da suna da rantsuwa,
saleem yace malam sadeeq ka fadi da bakin ka cewa mahaifinka ya kiraka a ranar da zai dawo, ko zamu iya sanin abinda ya fada maka,
sadeeq ya kara hade rai dan duk ganinshi shirme sukeyi yace ya tambayeni ina matata,?
saleem yace muna ji kai kuma wace amsa ka bashi,
ya saci kallon zulfa yace lokacin muna tare da ita nace gata nan,
sai yace min dayar fa,?
saleem yace dakata sadeeq,
ya juya yana kallon alkali yace ya mai shar'ia marigayi ya kira sadeeq ya tambayeshi ina matarka, be ce ina matan ka ba matarka kadai yace, da sadeeq yace mishi gata nan in da ita yake nufi bazai tambayi dayar ba, sai yace ina dayar dat means akwai wani abu da yake son fadi game da ita dayar matar tashi tunda har ya tmbayi ina take,
ya maida kallonshi gurin sadeeq yace uhum a lokacin sai kace mishi ne,
sadeeq cikin kosawa yace lokacin bata kasar nan tana india jinyar mahaifiyarta, saleem yace yauwaa mun gode malam sadeeq, ya juya yace ya mai shar'ia a rike wannan gurin dayar matarshi tana india jinyar mahaifiyarta,
yace na gama tambayoyina akan sadeeq ya mai shari'a ban sani ba ko abokin aikina yana da ta cewa,
alkali ya tambayi tahir yace a'a babu, sannan aka bukaci yaje ya zauna,
saleem yace ya mai shari'a wacce zanyi ma tambaya ta biyu mahaifiyar sadeeq ce itama a wannan daren da mijinta ya dawo cikin damuwa ya fadi mata damuwace akan matar abba, har a lokacin bai ce matan abba ba, kuma gida daya yake da zulfa'u a ranar da ya dawo sun gaisa dashi sosai cikin farin cikin ganin surukarshi, in da ita yake nufi ya mai shari'a ay bazai ki fadi ba tunda gata a gabanshi,
sannan yanzu zan kira wacce zanyi wa tambaya ta uku itace amaryar marigayi,
anty amarya da bata dade da shigowa gurin ba ta karaso ta tsaya, saleem ya kalleta yace sannu anty,
tace yauwa, yace anty ko zaki iya fada mana ranar da marigayi zai dawo kema ya kiraki kan maganar matarshi, ta girgiza kanta tace bai kirani ba, yace okk may be bai sameki bane ko kuma kema a ranar kina india gurin jinya,
cikin rashin fahimta tace jinyar wa?,
sanah cikinta ya saki sosai kiris ya rage fitsari ya fito,
saleem yace jinyar yayarki mana, ko bakisan bata da lafiya ba, anty amarya tace gaskiya ban sani ba, saleem yace wow abun mamaki har yar uwarki ciki daya tayi ciwo baki sani ba, to duk ba wannan ba, ranar da abun zai faru ko zaki iya gaya mana inda matar sadeeq take? bafa zulfah ba, diyarki nake nufi,
anty amarya tace ita bata kasar ma ta tafi dubai sarin kaya, sanah fitsarin dake rike a mararta ya fito da karfinshi gumi kota ina keto mata yakeyi,
saleem yace iyye ashe business woman ce,
to ya mai shari'a kaji dayar matar tashi dubai taje sarin kaya sai a hada shi da amsar mijinta a basu mazauni sosai a takadda saboda zata amsa su da kanta bayan nayi tambayar da zanyi ma wani yanzu,
ya juya yace barr ko kanada tambaya ko jaa,
tahir ya girgiza kanshi cikin rudu,
saleem yace to anty mun gode zamu bukace ki anjima,
ya mai shar'ia ina son a bani dama in shigo da wata shaidar
, alkali yace an baka, aka fita aka shigo da mukhtar wanda ganinshi kadai yasa duk gabobin jikin sanah suka rike guri daya,
Bayan tambayar suna da rantsuwa, saleem yace malam mukhtar ko kasan waccan ya nuna sanah dake zaune ta kura ma mukhtar ido,
mukhtar yace farin sani ma,
saleem yace a ranar 3 ga watan sept ko zaka iya fada min kana ina, mukhtar yace ina england tare da waccan yarinyar,
sanah tasa ihu tace wallhy sharri yake min na rantse da Allah so sukeyi a kama ni, ni ban sanshi ba,
alkali ya buga tebur yace baiwar Allah nan kotu ce ba gurin rashin da'a ba, ya kamata kisan irin maganganun da zakiyi,
barr saleem ya kalli mukhtar yace ko xaka ita takaita mana labarin abinda ya kaiku england,
nan da nan ya warware mishi komai har hoton da sukayi sai da ya taho mishi dashi sannan ya fada musu abinda ya hadasu fada har daddy ya shigo ya ji su,
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun abun da sadeeq da rabin mutanen gurin ke fadi kenan,
da kyar aka samu nutsuwa sannan saleem yace ya mai shar'ia wadannan tambayoyin da nayi sune mafarin tafiya a cikin wannan shari'ar yanzu muna cikin binciken kasa uku kenan bamu san wacce kasa bace gaskiyar inda matar sadeeq taje INDIA, DUBAI ko ENGLAND, wannan amsar daga bakinta kadai zamu ji, sannan mu shiga cikin shariar ka'in da na'in nagode ya mai shari'a,

Hutun rabi awa aka bayar ni kuma na kashe wayata nayi hanyar waje in nemo abin da zanci dan naji dan cikina na neman galabaita saboda yunwa,
sai na dawo karasa dauko rahoto

Mrs tijjani shattima..
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: [18:05, 07/02/2016] Aysha Ya'u Kurah: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 6⃣6⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Bayan dawowa daga hutun rabin awa can na hango sadeeq ya dafe kanshi cikin tsananin rudu da tashin hankali,
to ba sadeeq ba ma mijin sanah daukacin mutanen gurin suna zaune sun zuba mata ido cike da mamaki, sanah kuwa duk jikinta a jike yake tabbas da ta samu koda karamar kofa ce agurin to da babu abinda xai hanata gudu...

Alkali ya fara magana cikin nutsuwa yace bayan hutun rabin awa yanzu zamu cigaba da gabatar da shari'a,
barr taheer ko kanada jaa akan tambayoyin barr saleem,
barr tahir ya mike yace bani da jaa ya mai shari'a amma wadannan tambayoyin da saleem yakeyi ko kadan basu cikin shariar da mukeyi, tambayoyi ne yake yinsu a bisa son zuciyarshi saboda rashin kwakwarar hujjar da zai fitar da wacce ake zargi,
ko ma wace kasa sanah taje tunda har an tabbatar da bata kasar samm bai kamata ma a sako ta acikin wannan zancen ba,
ya mai shari'a bisa la'akari da rashin shaidar da zata gamsar damu da kai nake rokon wannan kotu da tayi saurin yankewa mai laifi hukuncin da ya dace,
tambayoyin da saleem yayi kuma wannan shari'a ce da zasu yi ta a gida ba anan ba,

Alkali ya kalli taheer yace munji korafinka barr tahir,
barr saleem bismillah, barr saleem ya mike yace ya mai shari'a zanso a bani dama inyi wa zulfau wasu yan tambayoyi,
alkali yace an baka, ya fito ya karasa gurin zulfa yace malama zulfa'u ina son ki bude bakinki ki amsa min tambayoyin da zanyi miki ,
amsar tambayoyin sune zasu bamu saukin gabatar da shaida, zulfa ta gyada kanta,
saleem yace ko zaki iya fada mana yanayin tsaftar ruwan da kikayi amfani dashi gurin dama kunun,
zulfa a hankali tace tsafatatacce ne dan ko da na gama damawa sai da nasha,
yace to bayan kin ajiyeshi a gurin ajiyar abinci babu kowa cikin gidan,
tace eh babu kowa a ciki ni kadai ce,
yace kuma har lokacin dawowar mutan gidan baki ga kowa ya shigo gidan ba saboda masu gadi sunce wasu mata sunzo gurinki, zulfa tace ina daki bayan na fito daga wanka sai naji ana buruntu a gurin dinning sai na fito dan nayi tunanin ko su mummy sun dawo ne,
ko da na fito sai banga kowa ba na leka ta window sai na hango beebah kawar sanah kuma itama ta ganni, sai na koma na dauki wayata dake kan dinning na wuce daki dan a tunanina ko gurin anty amarya tazo,
saleem ya juya ya kalli alkali yace ya mai shari'a zulfa'u taga kawar sanah a gidan, kuma masu gadin gidan sunce mutum biyu ne suka shigo neman zulfa'u kenan beeba ce ta zama biyu ko kuma dai tare suke da wata wacce ita zulfa'un bata ganta ba, wannan amsar inason jinta a bakin masu gadin ya mai shari'a amma ba yanzu ba sai lokaci yayi,
yanzu dai in an bani dama inason inyi wa sanah wasu yan tambayoyi,
sanah da idonta yayi ja rike da waya tana neman beeba ta mike ta karaso a hankali kamar wacce kwai ya fashe ma aciki, a zuciyarta tana fadin ya akayi shari'ar nan ta juye haka,
kwarin gwiwa ta samu da ta tuna zata iya karyatawa tunda babu beeba a gurin,
malam saleem ya kalleta bayan fadin suna da rantsuwa yace malama sanah a ranar da abun nan ya faru ko zaki iya fada mana kina ina,
sanah ta share gumin fuskarta tana kallon sadeeq da anty amarya sannan ta dake tace ina india jinyar mahaifiyata, malam saleem yace wayyo Allah ya bata lafiya amma yanzu ta ji sauki ko,
sanah ta gyada mishi kai, yace to da taji sauki ne sai kika wuce sarin kaya dubai, ko kuwa ya akayi, sanah ta daburce tace ehh dama inada shirin tafiya dubai sai kuma ciwonta ya tashi shine na tafi da niyyar in taji sauki sai in wuce, saleem yace amma ciwon na sirri tayi saboda kar wani ya sani ko,
sanah tace ban ganeba, saleem yace abunda nake nufi ciwon nata babu wanda ya sani sai ke ko, sanah tace eh bata son a daga hankalin mutane ne shiyasa, saleem yace Allah sarki,, ko zaki iya kira mana ita a waya mu gaisheta,
sanah jikinta ya fara rawa ta fara kame kame,
tahir yace objection ya mai shari'a ya kamata mai tambaya ya daina ruda wacce yake tambaya ta hanyar tursasawa,
saleem ya kalleshi yace laifi ne dan musulmi ya gaida mara lafiya,
ya mai shari'a in akayi la'akari da zunzurutun ladan da ake samu in aka gaida mara lafiya inaga ya cancanta a kirata mu gaisheta dukkanmu har da kai ma dan mu samu ladan gaba daya ko ba haka ba ya mai shari'a ya karasa fadi yana ma tahir murmushi,
anty laila dake zaune kanta yayi girma ta kasa magana saboda kwarewar aiki irin na saleem tayi murmushi tace aiki ga mai kareka,
alkali yace korafi bai karbu ba barr tahir,
barr saleem cigaba, saleem yace nagode ranka ya dade,
ya kalli sanah yace kin kirata,
sanah tace wayata babu charge,
saleem yace to ay kin haddace numbr akanki ko, ko dayake ma barshi ga sadeeq bari mu kira da wayarshi, saleem yace malam sadeeq ko zaka iya kira mana surikarka mu gaisheta,
sadeeq baiyi magana ba ya zaro wayarshi yayi dialing ya mika ma saleem,
saleem ya karba wayar ya dawo gaban alkali yasa ta a speaker, ringing uku wayar tayi ta dauka cikin muryar isa tace sadeeq ina gajiya,
sanah ta fashe da kuka hade da toshe baki,
saleem yace lafiya lau mama kin dawo lafiya ya jikin,
cikin rashin fahimta maman sanah tace sadeeq dani fa kake magana jikin wa kuma ina naje,
saleem yace ance min baki da lafiya ne kun tafi india tare da sanah,
tace a'a ni lafiyata kalau ba kuna tare da sanah a England ba ko kun dawo ne,
saleem yayi saurin datse wayar yace ya mai shari'a da fatan kaji abinda mara lafiyar ta fadi ko,
ya kalli sanah yace malama sanah nidai na shiga rudu gaskiya, na kasa gane wacce kasa kikaje tsakanin india, dubai , ko England,
dan Allah ki fitar damu cikin duhu,
sanah kukanta ya tsananta tace sharri zakuyi min wallhy wannan ba muryar mahaifiyata bace,
to ma ina ruwanka da inda naje kayi bincikenka akan wacce kake tuhuma mana ni meye nawa a ciki tunda kowa ya tabbatr bana kasar,
saleem yace oooo hakane fa, dan Allah kiyi hakuri na wuce gona da iri to bari inyi miki tambayar da ya kamata inyi miki,
shin ko ke kika aiki kawarki beeba gidan a ranar tunda dai babu wanda take mu'amala dashi a gidan sai ke,
sanah tace karya zulfa'u take ma beeba dan ta daura mata sharri itama bata kasar sanda abun ya faru kuma har yanzu ma bata dawo ba,
saleem yayi murmushi yace to Allah ya dawo da ita lafiya,
har yanzu dai ban gama dake ba,
ya kalli mai sharia yace ya mai shari'a inason in gabatar da wata shaidar in an bani dama,
alkali yace an baka, saleem yace ina son a kira min mati drivrn taxi,
cikin minti biyu mati dan kauye ya hallara gaban kotu,
bayan yayi rantsuwa saleem yace malam mati ko kasan wannan, ya kalli sanah yace kwarai na taba daukota daga airport din abuja zuwa kaduna,
saleem yace to da kuka zo a tasha ka sauketa,
yace a'a hayin banki mukaje muka dauki kawarta, nan ya kwashe duk labarin ya fada musu, sanah cikin kuka tace ya mai sharia wallahy karya yakemin wallhy ban taba ganinshi ba hadawa sukayi dan a kulla min sharri, wallahy karya suke min,
dakyar mai shari'a ya iya sa sanah tayi shuru sannan ya tambayi tahir ko akwai tambayar da zaiyi ma mati,
tahir yace babu amma ya mai shari'a daga jin wannan ansan shiryayyen plan ne, barr saleem raina ma kotu hankali kawai yakeyi dan har yanzu bai kawo mana shaidar da zamu gamsu ba, saboda haka ina rokon kotu tayi watsi da wannan shaidar....

Mrs tijjani shattima....
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: [18:23, 07/02/2016] Aysha Ya'u Kurah: ◆◆ZULFAH ◆◆ 6⃣7⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Alkali ya kalli tahir yace munji korafinka barr tahir,
barr saleem cigaba,
saleem yace ya mai shari'a ta yiwu wannan shaidar ba tayi karfin da za'a kori wannan shari'ar ba saboda yanda zamanin nan ya canza mutane zasu iya rantsuwa da alkurani akan karya kamar yadda mati yayi yanzu a gaban kotu,
zanso kotu tabani dama in gabatar da shaida ta gaba isma'il Musa,
alkali yace an baka, yace nagode ya mai shari'a,
ismo ya mike ya dauko laptp dinshi ya fito ya tsaya bayan ya fadi sunanshi da rantsuwa,
sannan ya fara bayanin haduwarshi da beeba sannan ya bukaci a jona flash din da ya ciro a jikin lptp dinshi a katon plasman dake court room din,
cikin minti 5 aka hada komai kowa ya nutsu yana son sauraro da ganin abinda ke ciki, mamaki ya bayyana a fuskokin mutanen dake gurin musamman anty amarya da ko ina na jikinta ya dau rawa babu kakkautawa,
tabbas su laila a shirye suke yau babu mai fitar dasu a gurin nan,
bayan an gama sauraron bayanan beeba,
sanah ta kara sa ihu murya na rawa tace wallhy wannan hadin computer ce in gaskiya ne ina beeban take,
ta kalli saleem tace wai me na tsare maka ne da kake ta hada min wannan sharrin, ya mai shari'a wallhy wannan aikin computer ce,,
saleem yayi murmushi yana kallon yadda jikinta ya jike da hawaye,
yace ya mai shari'a babu mamaki wannan computer ce in akayi la'akari da yadda ilmin yanar gizo ya yawaita a wannan zamanin da muke ciki yanzu, amma xanso a kara bani dama ta kusa da karshe domin in gabatar da wata shaidar,
mai shari'a cikin mamakin kwarewa da confidence irin na saleem yace an baka dama barr saleem,
barrister saleem ya kalli ismo ya mishi alama da ido ismo ya fita yaje gurinsu beeba dake kuka tun shigowarsu,
ta kalli ismo tace nurah ni zaka ma haka,
ni zaka yaudara,
yayi dariya sosai yace ke wai baki da fahimta ne,
isma'il nake ba nurah ba,
yace ma yan sandan su wuce da ita,
sukayi gaba ismo ya bisu a baya,,
sanah na ganin beebah ta lankwashe kanta gefe daya tace shikenan na mutu, ta toshe bakinta ya'yan cikinta suka fara karo da juna,
kusa da sanah aka tsayar da ita,
cikin muryar kuka beeba tayi rantsuwa sannan saleem ya fara mata tambayoyi,
ta fara kame kame tana kuka,
ta sadakar a ranta kawai gara ta fadi gaskiya may be ta samu sassauci tunda ba ita ta zuba ba,
Wani wawan naushi sanah ta kaima beebah a baki bayan ta gama bayani,
tace karya kikeyi wallhy yaushe kika ganni,
beebah ranta ya baci sosai suka cakume juna suna masifa suna tonawa junansu asiri, da kyar aka samu aka rabasu dukkansu suna kuka sosai,
saleem yayi murmushi ya kalli sanah yace anty wannan ma ki dubata da kyau babu mamaki fuska muka sa mata dan mu muki sharri,
ya rage murya yace har yanzu kin kasa fada mana gaskiya da bakinki ba, duk ko da irin kwararan shaidun da muka gabatar,
meyasa kika kashe shi,?
meyasa baki tsaya kinyi tunanin duk wanda ya kashe mui'mini jininshi baya barinshi yayi kwanciyar hankali ba,
meyasa baki tsaya kin roki
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment