Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

sadeeq yayi yace uhumm,
mummy tace to abincin fa kar dai har ka koshi,
maganarshi a makoshi yake yinta yace banda apatite mummy,
ya wuce side dinshi ba tare da ya saurari me xata ce ba....

Mrs tijjani shattima.....
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: [8:47PM, 08/02/2016] Aysha Ya'u Kurah: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 7⃣0⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Yana shiga daki ya zauna ya dafe kanshi yanajin zugi a can cikin zuciyarshi,
ko wanka ya kasa tashi yayi saboda tsabar bakin cikin dake dankare cikin zuciyarshi,
To shi saleem din mahaukaci ne da za'a bashi matar wani tun bai saketa ba kuma da cikinshi ya yarda,
lallai suna so ayi yakin da bazai taba karewa ba duk ranar da suka bijiro mishi da wannan maganar,
haka sadeeq ya dinga tunani ya mike ya zauna kamar zararre sai can yamma ya samu yayi wanka ya fito ya shiga parlon mummy dan ya fara jin yunwa,
tun kafin ya karasa yaji suna hira su uku kuma duk akan kwarewar aikin saleem ne,
hango tahowarshi farouk yayi ta makeken show glass din dake parlon,
ya maza ya canza maganar yace wallhy anty nakosa auren nan yazo wayaga ango da amarya,
ya kalli zulfah yace ji nakeyi kamar in janyo watannin haihuwarki ki haihu musha biki, zulfah da bata fahimci auren wa yake nufi ba tayi dariya tace ay na fi ka kosawa in haihu in huta da wannan cikin duk da ba wani wahala yake bani ba amma na dan samu sauyin wasu abubuwa, anty laila tayi murmushi tace ay dama ciki ko baka laulayi dole ka samu sauyi har sai ka haihu zaka huta, Allah dai ya raba lafiya ameen sukace dukkansu dai2 lokacin sadeeq da ya dade tsaye yana jinsu ya karaso ciki a tunaninshi ba wanda ya ganshi bai san farouk tuni ya ganshi ba,
farouk ya dauki wayar zulfah yayi flashing saleem yana kallon sadeeq yace sannu yaya abba,
ko kallon inda yake sadeeq baiyi ba,
anty laila tayi murmushi tace irin wannan cika da batsewar fa abba,
ya kara hada rai ya zauna a dining yace lfy ba tare da ya kalleta ba,
wayar zulfah ce ta fara ringing da sauri farouk yace saleem ne ya kiraki tashi maza kije daki ki amsa kar waleed ya hanaki ji kawoshi,
zulfah ta mika mishi waleed ta karbi wayar tasa a kunnenta tana tafiya a hankali murya can kasa tace assalamu alaikum,
sadeeq ya runtse idonshi da yayi jawur wani abu yakeji yana nukurkusarshi a ko ina na cikin jikinshi,
kauda abincin da ya zuba yayi ya tashi ya fita daga parlon gaba daya numfashin shi yana sama yana kasa, garden ya nufa ya zauna cikin kunan rai dakyar da addua ya samu zuciyarshi ta dan lafa,
yanata mamaki da takaicin yadda zulfa'u ta shareshi, ay ko sannu da jiki tayi mishi ko dan ďan da suke shirin raba uwarshi da ubanshi tun kafin yazo duniya,,
bai bar gurin ba har saida gari ya fara duhu sannan ya fita ya tafi masallaci..

Wata hudu bayan wucewar wannan, alamura da dama sun faru ciki harda fitar takabar mummy, sadeeq kuwa tun washe garin faruwar wannan yayi kaura da gidan gaba daya dadin da yaji ma aikinshi sai weekend yake samun hutu,
wani lokacin ya dawo gida wani lokacin yayi zamanshi duk ko da irin azabtar dashi da zuciyarshi takeyi akan zuwa ganin abinda takeso haka ya danne yafi karfinta saboda tsananin kishin zulfah na neman buga mishi zuciya,

Zaune suke da mummy a parlor suna hira mummy na duba kayan jariran da suka siyo ita da anty laila, mummy ta kalleta a hankali tace zulfa'u kuna waya da abba kuwa,
zulfah ta gyada mata kai tace eh mummy, mummy ta dago wata sweater tace da wace wayar kukeyi dan dai naga rabon da ki kunna waya an dade, tace umm dama da ta yaya farouk ne kafin ya tafi training kuma tunda ya tafi bamu kara waya ba,
mummy ta fito da ido waje tace watan farouk biyu kenan da tafiya kina nufin tun lokacin bakuyi waya ba,
zulfah ta sunkuyar da kanta kasa,
mummy ta rage murya cikin rarrashi tace kiyi hakuri zulfa'u nasan kina fushi da abba, kiyi hakuri ki yafe mishi, abba mutum ne mai raunin zuciya duk sauran sun fishi karfin zuciyar jurar abu, dan Allah karki ga laifinshi akan abunda ya aikata nasan kinason shi kuma duk tunaninki bai wuce shi baya sonki ba ko, to wallhy kinji na rantse zan iya ce miki babu macen da abba yakeso a yanzu da ta wuce ke, dai2 lokacin anty laila ta karaso tace hakane mummy,
saboda tsananin kishinki yanzu sam abba baya min waya ko yazo gidannan wkend baya nemana ko shiga inda nake haka ko kiran farouk baya yi ko farouk ya kirashi baya dagawa dan yana ganin kamar so mukeyi mu raba aurenku mu bawa saleem,
mummy tayi murmushi tace ay shima umara ya cika tsokana ina jinshi rannan yana hango abba ya fara wayar karya da sadeeq ashe abun da yake nufi kenan ja'irin,
anty laila tayi dariya tace kema mummy dan Allah karki bata mana plan mu hadu mu ganar dashi ta inda zai gane kurensa ya daina biye ma zuciya, mummy tayi murmushi tace to amma fa na kankanin lokaci dan bazan biye muku zuciyar abbana ta buga ba,,
anty laila tayi dariya tace mun yarda mummy, nan suka cigaba da hirarsu hankali kwance zulfa ta kwashe kayan ta kaisu dakin mummy gurin da sauran kayan suke...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: .....
[1:09AM, 09/02/2016] Aysha Ya'u Kurah: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 7⃣1⃣
By Aysha Ya'u kurah

Zulfa'u na zaune a dakinta tana shan wani maganin sassaken mangaro da mummy ke amso mata tun cikinta na wata 7,
tana sha tana yatsina fuska saboda yadda take jin mutsu2 a cikinta,
kwanciya tayi bayan ta gama sha tana tunano rayuwar da tayi tun zamanta da Marka har zamansu da su sanah da irin sharrin da akayi mata,
ta shafa cikinta a zuciyarta tana gode ma Allah dan badan ya taimaketa ya wanketa daga wannan zargin ba da tuni an shafe babinta a doran kasa,
wayarta ta dauka ta kira mahaifinta da nasarori ke binsu shi da kabiru dan yanzu har karamin gida ya siya a Na'ibawa inda yasa kabiru yayi aure ya bashi daki,
ko bi takan marka bayayi dan baya kaunar ko sunanta yaji, tana fara ringing ya dauka suka gaisa ya tambayeta tana nan lafiya ko,
ta amsa mishi cikin jin dadin jinshi cikin farin ciki,
yace ya su hajiya ki kara yi musu godiya fa, mijinki ma kiyi mishi godiya satin da ya wuce yazo ya bani mota wallhy,
dan Allah ki kara mishi godiya itama hajiya duk da na kirata na mata ki kara yi mata dan godiya bata kadan Allah ya sa aljanna ce makomarsu ya dawwamar daku cikin farin ciki,
zulfah murya a dashe tace ameen baba ka gaida yaya kabiru da anty Badiyya,
yace zasu ji in shaa Allah ya kashe wayar itama ta kashe tana mamakin yadda akayi sadeeq yasan inda mahaifinta yake,
Allah ya saka mishi da akhairi abinda taji zuciyarta ta fadi kenan,
kafin ta ajiye wayar taji tayi kara ta duba taga zabba'u da sauri ta dauka tace my z square,
zabba'u tayi murmushi tace maman biyu ya kike,
tace lafiya lau,
zabba'u tace ya babynmu har yanzu shiru fa muke ji na kosa muzo mu sha suna,
zulfah ta yatsina fuska cikin tsokan tace bashi da zuciya babyn nan naku har yanzu yaki fitowa may be babanshi yake son gani,
zabba'u tayi dariya sosai tace wato shi babyn baya fushi da babanshi kenan,
zulfah tayi tsaki tace yaki tayani in gaya miki ay yana fitowa sai na mishi dundu guda biyu nima in rama, zabba'u tace me zai hana ki tsoma shi cikin ruwan sanyi daga kin haifeshi,
zulfah tace gud advise hakan za'ayi amaryar ismo,
ke ni ban ma fa tambayeki ba, wato dan munafurci badan malam saleem ya fada min ba ke bazaki fada ba ko,
wato ku lokacin ina cikin wani hali ku soyayyarku kuka kulla da ido ko,
to bani labari tun daga day 1 or else,,
zabba'u da takasa daina dariya tace else watt,,
zulfah tace kema kin san sauran,
zabba'u tace to ayi mana afuwa zanzo gobe sai kiji komai kinji,
alamar tsayuwar mutum taji a gabanta takasa bawa zabba'u amsa ta maza ta dago kanta sukayi ido hudu yana tsaye ya harde hannu cikin kananan kaya,
kauda kanta tayi da sauri tace sai kinzo dear ta kashe wayarta tana kokarin gyara maternity wear din dake jikinta saboda rigar is sleeveless, hularta ta dauka ta tura gashinta ciki ta fara kokarin mikewa dakyar ta mike tabi ta gefenshi zata wuce ya riko hannunta da sauri,
ka sakeni ta fadi ba tare da ta juyo ta kalleshi ba,
gabanta ya dawa ya dago fuskarta yana kallonta ba tare da yayi mata magana ba, kauda kanta tayi da sauri saboda wani irin rikitaccen kallon da yake mata ta fara kokarin kwace hannunta ya matseshi da karfi ya janyota jikinshi,
cikin masifa tace dan Allah ka sakeni ji yadda ka wani jawoni kamar idonka baya ganin ina tare da lalura,
a hankali ya fara shafa katon cikinta ya kwantar da kanshi kan kafadunta murya can ciki yace nayi tolerating punishment dinki na gaji haka,
duk dan adam ajiizi ne babu wanda baya kuskure dan Allah ki daina bani wahala haka,
idonta a runtse saboda duk ya sakar mata kasala tace nidai dan Allah ka barni bana son jin kalamanka,
ya juyota ya rungumeta sosai yace babyna nason jin kalamaina kuma yanzun nan zamu gana cos I msd him or her alot,
ta turo baki ta fara kukan shagwaba tace ni ka kyaleni wayyo cikina,
yace ay ko mararki ce yau saina nayi magana da baby na saboda shi ay baya fushi dani,
da sauri tace wallhy yama fi yin fushi dakai dan he htes you,
yayi dariya ya dago kanta yace hakuri zan bashi karki kara cemin komai,
ta bige hannunshi tace wallhy sai nayi ma---- tura bakinshi cikin nata yayi ya hanata karasa maganar da takeyi,
cikin rudewa sadeeq ke sarrafata ko kadan baiyi duba da tsohon cikin da take dashi ba, bazai iya jurewa ba ko kadan saboda yayi missing dinta matuka gashi dai sau daya ya taba kusantarta amma wannan tarayyar ganinta yakeyi tafi dare dubu saboda taki gogewa a cikin zuciyarshi,
rawa kafarshi takeyi saboda tsabar rudu har suka kusa kaiwa kasa,
daukarta yayi tana ihu tana kuka tana mishi nuni da cikinta amma sam sadeeq bai saurareta ba dan bai ma san tanayi ba, kasancewar gidan babu kowa yasa babu wanda ya jiyo muryar sadeeq,
addu'a ya dinga rada ma zulfa da karfi yana kuka yana rokonta Allah da Annabi akan kar ta rabu dashi, itama kukan takeyi saboda azabar ciwon marar da takejinta kamar zata fita,
tabbas sadeeq yayi musabaha da danshi a wannan rana musabahar da ta kara dasa mishi soyayyar zulfah da abun dake cikinta mai yawan gaske,
razanannen ihun da zulfah tayi ne ya dawo da sadeeq cikin hayyacinshi,
da sauri ya dagota ganin zufa na keto mata ta ko ina yace lafiya menene, da karfi tace dole ka tambayeni mana wayyo bayana,
ta rike bayanta tana kuka sosai,
tsarki kadai yashiga yayi a bayi da sauri ya maida kayan jikinshi ya daura mata zani da hijab ya dauketa chakk yayi waje da ita yana shirin sata a mota motar nurain ta shigo shi da laila da sauri suka fito suna tambayarshi,
cikin rudewa yace bayanta ne ko mara anty shiga muje plss, ta mika ma nurain waleed suka shiga motar nurain ma yashiga gaba suka wuce asibiti cikn tashin hankali dan kuka takeyi sosai saboda azaba,
diamond hospital suka je nan da nan akayi labour room da ita,
sadeeq sai kai kawo yakeyi yana adduar Allah yasa ba wani illa yayi mata ba,
duk ya surkuce saboda tashin hankali,
ta kusa awa a cikin dakin sannan wata nurse ta fito musu da katon yaro kyakkyawa kamar ubanshi a gyare cikin sweater,
nurain ya karbeshi da sauri bayan ya ajiye waleed, sadeeq yace nurse ya jikinta,
nurse tace da sauki ana mata dressing ne, sadeeq yace alhamdullilah,
anty laila ta kira mummy dake gidan suna ta fadi mata cikin farin ciki ta mike da sauri ta tattara su afrah tayi sallama da mai jegon ta wuce ta shiga mota farouk yaja su suka wuce shima cikin farin ciki,

Dakin da aka bata cike yake da familyn marigayi daddy in ka dauke jalila dake gidan aurenta,
kowa cikin murna yake daukar yaron harda su afrah,
farouk ya kalli sadeeq da bakinshi yaki rufuwa yace congrat yaya abba wannan babyn ni za"a bawa in nayi aure in rike ko mummy,
anty laila tace ay dama namu ne dan autan mummy,
yayi murmushi yace bari in fara ma saleem albishir dan nasan baku fada mishi ba ya fito da wayarshi ya fara neman layin saleem,,
a zuciye sadeeq yayi kanshi ya kwace wayar yayi wurgi da ita ta tarwatse ya kai mishi mari da sauri ya goce yana ihu yana dariya,
nurain da mummy suka mike da sauri suka rike sadeeq da yake shirin bin farouk waje yana masifa,
mummy tace haba abba to yanzu me ya maka da ka fasa mishi waya harda kai mari, sadeeq ya kara hade rai yace mummy ni sa'anshi ne da zai fada ma wani haihuwar dana,
ya bari shi in ya haifi nashi ya kirashi yayi mishi albishir din, wallhy mummy kija mishi kunne in ba haka saina ji mishi ciwo, anty laila ta kasa boye dariyarta sai da tayi mai isarta sannan tace to meye dan an fada ma saleem ay naga mun zama daya dashi ko,
da ku dai sadeeq ya fadi kamar me shirin yin kuka yace wallhy mummy ki fada musu su fita harkata dan yaga anty na goyon bayanshi shiyasa ya raina ni,
mummy tace hakilo, to yanzu wai kai duk dan za'a kira saleem ne yasa kake wannan masifar,
ay ko saleem dole yaji tunda yanada muhimmaci a rayuwar zulfah,
sadeeq yace rayuwarta kikace mummy nidai kar wanda ya fada mishi haihuwar dana,
nurain yace to fah to yi hakuri abban daddy babu wanda zai kirashi zan musu fada kaji, farouk dake tsaye daga waje yace wallhy yaya kace ya biyani abubuwan cikin wayata in ba haka ba,
in ba haka me zai faru sadeeq ya fadi yana karasowa kofar,
farouk ya ruga da gudu yana dariya,
mummy ta zauna tana dariya tace Allah ya shirya,,
sai washe gari aka sallameta suka dawo gida,
baki ko ta ina zuwa sukeyi mata barka harda su goggo amina anan take bata labarin marka na kwance hawan jini ya kwantar da ita sosai saboda damuwar salaha da ta maida ma bangis yara ta shiga karuwanci,
zulfah taji tausayinta sosai tace Allah ya bata lafiya in shaa Allahu zanje duba ta bayan arba'in,
jalila ma tun ana jibi suna taxo itama da tsohon cikinta,

ranar suna yaro yaci sunan daddy HASHEEM ABUBAKAR MARAFA, (Daddy) mutane sun zo sunan sosai ciki harda su feenah dake soyayya da malam saleem sosai dan har an fara maganar aure,
sadeeq kuwa ba karamin barin kudi yayi ba a sunan dan walima biyu yayi saboda tsabar farin ciki,
haka akaci suna aka watse cikin farin ciki...

Mrs tijjani shattima......
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: [10:37AM, 10/02/2016] Aysha Ya'u Kurah: ◆◆ ZULFAH ◆◆7⃣2⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Satin zulfah uku da haihuwa sunyi kyau sosai ita da babynta saboda kulawar da suke samu gurin mummy da anty laila, sadeeq ma na iya bakin kokarinshi akansu in yana gari duk da har yanzu bata gama sakewa da shi ba, shi kuwa ko ajikinshi dan koda yaushe in yana gari yana tare dasu yayita mata hirah wani ta basar wani kuma ta amsa mishi..

Kwance take a daki idonta a lumshe dan bacci takeji sosai saboda daddy baya barinta ta rintsa da daddare sai dai da rana,
muryar afrah taji tana bubbuga pillown da take kai tace anty wai kizo inji mummy tana parlon baki kuma wai ki bani daddy in daukeshi,
zulfa ta mike zaune tace afrah bazaki iya ba,
afrah tasa hannu kan daddy tace Allah anty zan iya,
ta daukeshi ta fita dashi kanshi na rawa dan bata iya rikon sosai ba,
zulfah ta sauko da sauri ta dauki hijab tasa ta bi bayan afrah, sakkowa afrah keyi daga kan stps da kyar ga skirt dinta na hardeta,
rikeshi tayi da hannu daya tana kokarin gyara skirt dinta, kukan da daddy ya tsanyara yayi dai2 da shigowar sadeeq da sauri ya ajiye jakarshi yayi gurinsu da gudu dan saura kadan ta sakeshi,
cikin masifa yace uban waye ya baki yaronnan,
tace mummy tace in dauko shi a kaiwa baki,
sadeeq yace duk gidan nan babu wanda zai dauko shi sai ke wallhy idan na kara ganinki da yaron nan saina babbala ki,
zulfa ta karaso da sauri tace afrah meya faru,
ta mika hannu zata dauki daddy sadeeq ya kauda hannun ya harareta yayi tsaki ya wuce side dinshi yana jijjiga daddy,
afrah tace anty fa mummy ce tace a dauko mata shi baki zasu ganshi kuma kinga ya tafi dashi,
ta kama hannunta tace muje rabu dashi kinji, suka wuce parlon,
da sallama suka shiga parlon ta karasa da murmushi ta tsuguna ta gaida malam saleem dasu ismo da mukhtar,
suka amsa mata cikin fara'a sukayi mata barka,
mummy tace ina daddyn yake, afrah tace yaya abba ne ya kwace shi a hannuna, mummy ta kalli zulfah tace je ki karboshi su ganshi ko,,
ta mike ta fita tayi side dinsu da rabonta da shiga ta dade, can ciki ta shiga dan baya parlon, kwance ta sameshi ya daura daddy kan kirjinshi yana shafa bayanshi, ta karasa tace wai mummy tace ka bani shi a kai mata,
idonshi a runtse bai bude ba yace sai ki daukeshi in kinada karfi,
tace wallhy zance mata kaki bani shi fa,
yace wa ya rikeki anan yi sauri kije ki fada mata mana,
tasa hannu a kan daddy tace dan Allah ka bani shi baki ne fa zasu ganshi,
sai a lokacin ya bude ido yace ay ba dole bane bakin su ganshi, fita anan kafin ranmu ya baci dukkanmu,,
in kina son kaiwa bakin shi kuma kin damu dashi ay bazaki ba afrah ta kaishi ba, amma saboda kina saurin kije ki ga saleem shiyasa kika bata shi dan ki tsaya ki shirya da kyau,
zulfah ta zaro ido zatayi magana mummy ta turo kofar tace wani irin wulakanci ne wannan zaku bar baki zaune sun zo tun daga wani gari ganin da,
sadeeq yace mummy afrah fa ta ba shi saura kadan su fadi kuma ni gaskiya sai dai suyi hakuri dan har yanzu kin ga bai daina kuka ba,
mummy ta rike baki cikin mamaki tace zanci mutuncinka wallhy in baka miko min yaron nan ba, sadeeq ya kara hade rai ya mika mata shi tayi tsaki ta fita da shi,, zulfah ta mishi gwaloo ta fita ta sauri tana dariya,
ya koma gefen gado ya dafe kanshi zuciyarshi na zafi dan a tunaninshi saleem yazo da magana akan zulfah ne, saida ya dan jima a zaune sannan ya mike ya fita da sauri harda tuntube ya nufi parlon dan jin abinda suke tattaunawa,
tun kafin ya karasa yaji mummy nata Allah ya sanya alkhairi Allah sa ayi damu mun gode sosai,
zulfah ma na gefe tana murmushi tana godiya, karasowa yayi lokacin da yaji sun rufe kofar alamar sun fita,
kusa da mummy yaje ya zauna kamar zaiyi kuka yace mummy sun gama ganinshi, ta harareshi tace bansani ba, wallhy abba ka fita idona in rufe,
yace wai mummy ina kika taba ganin an daki mutum kuna an hanashi kuka, ni kawai ki bani ďana tunda bani kadai kukeson sawa cikin kunci ba harda shi saboda haka ki bani shi mu bar gidan gaba daya,,,
zulfah ta gimtse dariyarta tayi ciki ya bita da muguwar harara,
mummy tace kuncin me kuma zamu saku, ya kara narke fuska yace ba gashi kuna maganar aure da saleem ba,
haba mummy kin fa san hukunci neman aure akan aure, wallhy badan akwai abinda nake hange ba wallhy da saina kulleshi tunda shi bashi da hankali,
mummy tayi murmushi tace saidai kayi hakuri abba amma mun riga mun gama magana gara ta auri wanda ke sonta da zuciya daya babu kokwanto a zuciyarshi, yace to ni da zuciya uku nake sonta,
ta mike tsaye tace waya sani ta wurga mishi katinan biki da yawa tace kayi gaggawar bata takarddarta dan ga kati nan har sun buga, tayi ciki ta barshi baki sake ya kasa bata amsa,
saida ya dade da katin a jikinshi sannan ya mike idonshi jajur ya zubar da katin har yayi gaba kuma sai ya dawo ya dauki daya ya bude,
murmushin da baisan daga inda ya fito ba ya bayyana a kan fuskarshi,
ya kwashe sauran katin yayi sama dasu da sauri,
dakin mummy ya shiga yana dariya yace wallhy mummy yanzu kin daina sona so kikeyi zuciyata ta buga,
tayi dariya itama tace ay gara ta buga a kara dasa maka wacce tasan abin da ya dace, ya zauna gefenta ya daura kanshi kan cinyarta yace mummy I promise u bazan kara wani abun da zakuyi fushi ba in shaa Allah, tayi murmushi ta dafa kanshi tace Allah yasa abba nah, yace ameen...

Bikin su saleem ya rage kwana uku lokacin tayi arbain har jalila ma ta haihu ta sami baby gal,
shirin bikin sukeyi sosai saboda sai an daura na zabba'u in sun kaita abuja su tsaya na saleem,
ana gobe daurin auren ne ta shirya zuwa gaida goggo marka, tun safe ta gama shiri saboda daga can zata wuce gurin bikin,
wani rantsatstan lace ta sa ash nd red tayi kyau sosai haka daddy shima ta shiryashi yayi kyau sosai,
tana tsaye gaban mudubi tana daura dankwali taji an rungumeta ta baya, ta kalleshi ta cikin mudubin tayi murmushi tace kayi kyau sosai,
ya juyota yana kallon cikin idonta yace har na kaiki,
ta shige jikinshi ta lumshe idonta tana shakar kamshin jikinshi tace kaima kasan kafini,
ya matseta sosai ajikinshi yace kedai kike ganin hakan amma ni duk duniya ban ga wacce ta kaiki kyau ba,
tace ummm dadin baki kawai zaka ma KWAILAH,
yayi murmushi ya dan buge bakinta yace wannan maganar bance kar a kara min ita ba,
ta turo baki tace sai an fada din ay ba karya nayi ba,
ya dauki daddy yace to naji gama shiryawa ki same mu a dakin mummy, ta dauki red gyalenta tana fesa turare tace to mijin kwaila,
ya fita yana girgiza kai yana dariya...

Zaune suke kan tabarma, goggo marka na kwance ta zama kamar mujiya ta rame sosai saboda azabar ciwo,
kuka takeyi sosai tana rokon zulfah gafara, zulfah ta share hawayen idonta tace na yafe miki goggo Allah ya baki lafiya, tace ameen kabiru ma jiya yazo ya gaisheni dan Allah ku hadu ku rokor min gafara gurin malam nasan na musguna mishi sosai dan Allah ku bashi hakuri,
zulfah tace shima ya yafe miki goggo Allah ya yafewa duk musulmin duniya,
in shaa Allahu zaki samu sauki,
goggo marka ta kara rushewa da kuka tace ay ni yanzu gara in mutu zulfah, kinji labarin salaha da sukayi fada da wata akan saurayi tsautsayi ya ratsa ta buga mata kwalba yarinyar ta mutu yanzu haka tana an yanke mata hukuncin kisa ta karasa fadi tana kuka sosai,
zulfa tace kiyi hakuri goggo dan Allah ki daina kuka Allah yasa hukuncin da aka yanke mata ya zame mata rahama,
sadeeq yace ameen nan suka dan dade sannan da zasu tafi sadeeq ya bata kudi masu yawa da alkawarin zasu dawo su kaita asibiti...
Gidan goggo amina suka shiga itama suka gaisheta sukayi mata alheri sosai, delu ma ta roki gafararta dan hanne na can gidan
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment