Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

danneki akayi akace sai kin shanye, jalila ta juya tana murmushi tace ay dan nasan bazaki ji dadi bane idan bansha ba shiyasa, zulfa ta kwashe da dariya tace walhy baki da dama, ta cigaba da aikinta..

Bayan isha'i daddy ya dawo lokacin mummy na daki ta idar da sallah tana addua,
a gajiye ya shigo parlon ga matsananciyar yunwa yanaji anty amarya ta fito ta taryeshi tana mishi sannu da zuwa, ya zauna ya amsa yana maida numfashi, tace sannu kasha hanya, yace wallhy kuwa yunwa ma nakeji sosai, ina Aisha kin fada mata sakona, tayi murmushi tace kwarai na fada mata kace ayi maka danwake da kunun gyada, dai2 lokacin mummy tafito kuma taji duk abinda anty amarya tace, abin bai bata mamaki ba saboda tasan iya bariki irin na hadiza, to yanzu a ina zata samu danwake, dan tasan zulfah ta dama ma farouk kunu kuma bai dawo ba, addua tayi a zuciyarta sannan ta karaso cikin parlon tana murmushi ta zauna gefenshi tace sannu kunsha hanya, yayi murmushi yace kedai bari tafiya yankin azaba, tayi dariya tace sai kace wanda yayi tafiyar kasa bari a kawo maka abinci, yace yauwa Aisha ta mike tayi hanyar kitchen tana ma anty amarya murmushi mai alamar baki da wayau, itama anty amarya ta mayar mata da murmushin yau zaki sani,
kitchen mummy ta shiga ta dauko flask din kunu, tasan zai fara shan kunu har agama dan waken, jalila da zulfah ta kwala ma kira da sauri suka shigo kitchen din, mummy tace kuyi sauri ku kwaba garin danwake ku daura ma daddy,
jalila tace mummy har zai jira ga wanda zulfah tayi ma yaya farouk a kai mishi sai ayi ma yaya farouk wani, ajiyar zuciya tayi da taga kulolin ta bude taga danwake yana turiri da miyar da daddy keso, da sauri tace ma jalila dauka ki kai parlor ta mika ma zulfah flask din kunun suka kai komai na bukata anty amarya na murmushi dan ta dauka tuwo ne, mummy ta zauna a kasa ta zuba mishi kunun sai kamshi yakeyi, ya amsa yana sha yana lumshe ido, ta bude kular danwakn nan anty amarya ta kirne fuskarta ta dinga bin danwaken da kallo, mummy ta gama ta zuba mishi miyar da kayan ciki kamshi ya cika ko ina daddy ya fara cin danwake cikin jindadi dan ya samu abinda yakeso, har yagama ci anty amarya bata kara cewa komai ba, to ya akayi tasan abin da yace yanaso, kodai ya kirata ne?
To ay da ya kirata bazai tambayeta ba da ya dawo,
daddy ya wanke hannunshi bayan ya gama yanata shi ma mummy albarka, suka yi yar hira kadan sannan ya mike yace tazo ta taimaka mishi yayi wanka, tace to,
ta kira su zulfah suzo su gyara gurin,
saida ta tabbatar ya shiga daki,
sannan ta kalli anty amarya, tace "nace Allah hadiza" babu mai cin galaba akaina,
kina kuskuren ja dani, baki san Allahna ya tsaya min ba, bakiyi mamakin yadda danwake ya fito nan da nan ba,
Allah nagode maka da ka shigo da zulfah cikin rayuwata, da bansan me zai faru ba yau saboda makircin makirar mace,
dama kin yarda makaman ki da yafi maki dan bazaki taba cin galaba akaina ba, tayi murmushi mai kyau ta wuce side din daddy ta bar anty amrya kamar zata kurma ihu dan takaici..

Mrs tijjani shattima..
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 2⃣2⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Wata daya sadeeq yayi baiji muryar sanah ba,
hankalinshi a tashe yake matuka, ya rame sosai saboda ba karamin so yake mata,
ya riga ya gama shirye shiryenshi na dawowa gida,
ranar lahadi da safe jirginsu ya ďaga zuwa nigeria bai sanar ma kowa a gida zai zo ba dan ba kiransu yakeyi ba ko sun kira ma ba dagawa yakeyi ba,
Karfe 3 jirginsu ya sauka a abuja,
yayi niyyar fara biyawa gurin sanah amma baisan takamaimai adress dinsu ba,
drop ya dauka zuwa kaduna, sai 5 suka iso ya kaishi har kofar gida ya biyashi ya dauki yar karamar jakar kayanshi ya fito,
Masu gadi na hangoshi suka maza suka bude mishi kofa suna gaisheshi ya amsa babu walwala a fuskarshi,
ciki ya shiga babu kowa a parlon direct ya wuce dakinshi yayi wanka,

Zulfa'u na zaune a parlo tana gyarawa ayda kanta, jalila na skool dan ta fara zuwa "kasu" sati daya kenan,
twins na gefenta suna mata surutu,, karar rufe kofar dakin da ba'a taba budewa ba taji tayi maza ta daga kanta sama taga mutum tsaye cikin kananun kaya da bakin glass a idonshi,
wannan ba farouk bane dan yafi farouk jiki da tsaho,
ihun twins ne ya katse mata zancen zucin da takeyi, yaya abba oyoyo suka ruga da gudu suna rige rigen zuwa gurinshi,
ya rungumesu ya daga ayda yace mummyna kece kikayi katuwa haka fada min me ake baki kici, ta kwanta a jikinshi tana dariya,
ina wuni yaji an fadi a bayanshi ya kalleta daga sama har kasa ya maza ya dauke kanshi ya wuce side din anty amarya yana adduar Allah yasa ba wannan kucakar yarinyar mummy ta dauko mishi ba,

waya takeyi sanda ya shigo tana jin muryarshi ta katse wayar ta fadada fara'arta tace ango ango, yaushe a garin, yayi tsaki yace dan Allah ki bari anty, tayi dariya tace kamar yaya in bari, baka hadu da amaryar taka bane, yace ohh my God ban shiga dakin kowa ba sai nan babu ma wanda yasan na dawo sai wata yarinya may be ma yar aiki ce,
anty amarya ta kirne fuska tana kallon twins dake kallon fuskar abba, tace ban san iskanci wace irin yar aiki, afrah ku da waye a parlo, afrah tace anty zulfa'u ce,
tayi murmushi tace to ku tashi maza kuje kuyi wasa, suka tashi suka fita, anty amarya tace amaryarka ce ai,
da karfi yace wattt? Ta gimtse dariyar da tazo mata Ta hade rai tace meye na ihu, kyau ne bata da ko me,
innalillahi wa inna ilaihir rajiun abinda sadeeq ke fadi kenan, lokaci daya yaji muguwar tsanar yarinyar daya gani a parlor wacce aka kirata da zulfa'u,

Yace haba anty wake maganar kyau anan, ay persnlty din zaki duba, kamar ni a dauko wannan kwailar yarinyar ace matata ce, meyasa mummy zata min haka, yanzu ta ina zan fara nuna wannan yarinyar a matsayin matata , wayyo Allah na,
ya fadi yana matse hannunshi,
Anty amarya tace hmmm gata munafuka abba ga shegen hada fada,
ko kasan rannan saboda ita mukayi fada sosai da yaya, ta fara share kwallar gulma tace yaya harda mari na a gabanta, yanzu haka bama gaisawa da ita kuma duk saboda yarinyar, saukin da zaka samu shine daddy yace in baka sonta zai goya maka baya ka saketa,
nan ta cigaba da kitsa mishi karya da gaskiya, bai bar gurin ba sai da tsanar zulfa mai tsanani a zuciyarshi kuma zuciyarshi ta kangare akan kome zai faru sai dai ya faru amma bazai zauna da zulfah ba....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH◆◆ 2⃣3⃣
BY Aysha Ya'u Kurah

Da gudu su afrah suka fada kan mummy tace wayyo yaran nan Allah ya shirya,
suna haki suka hada baki dukansu sukace mummy yaya abban daddy ya dawo yana can dakin anty amarya yace wai anty zulfa yar aikin mu ce shine mukace mishi a'a sunanta anty zulfa kuma naji anty amar--- shigowar laila ce ta katse su tare suka shigo da sadeeq itama a hanya suka hadu,
mummy tace to naji kyautar Allah kuje maza kuyi wasa suka fita da gudu,
sadeeq ya zauna gefenta a kasa yace ina wuni, da kamar bazata amsa ba sai taga kar ta biye mishi ya kara dilmiyewa, tace lafiya lau, yayi shuru anty laila tace mummy na gama dambun yanzu zaki ci ko sai anjima, mummy tace zuwa anjima sannu kinji, tace yauwa mummy, har ta kai kofar fita mummy tace ki turomin zulfa'u,,
jin haka yasa sadeeq ya tashi ya fita da sauri dan baiso yaji ma mai zata ce,,,
tayi murmushi tace duk ka gama yinka abba baka isa ka rabu da yarinyar nan ba, dan ina ji ajikina zata xame maka silar shiga aljanna..

Bayan isha'i duk suna parlor ana hira banda zulfah da tun ganin da tayi ma abba ta fara jin tsoron irin kallon da yayi mata,
Nurain, farouk da daddy suka shigo duk suka zauna anata hira, sadeeq ya fito daga dakin anty amarya ya gama mata magiyar ta bashi adress din sanah sai gwarashi takeyi,
ganin su daddy da yayi a parlor ne yasa shi karasowa parlon, daddy cikin murna yace babana yaushe ka dawo,
ya zaune kusa dashi yace dazu daddy,
Yace ikon Allah to ya skull din, yace lafiya lau daddy, ya gaida yaya nurain, farouk ma ya gaisheshi,
daddy yace ka dan rame abba ko dai akwai wahala ne karatu, yace um um daddy kawai dai nayi missing dinku ne, daddy yayi dariya yace kai dai fadi gaskiya,
sai kuma ka dawo ka tarar da abin farin ciki, sadeeq ya maida dariyarshi yace wane abin farin ciki,
daddy yayi dariya ya kalli mummy yace au baki mishi albishir ba,
tayi dariya cikin dabara tace ay mamanshi ta fada mishi,
amrah kirah min zulfah,
amrah ta mike da gudu taje ta kira zulfah, tare suka fito tana sanye da hijab har kasa,
sadeeq fuskarshi kamar bata taba dariya ba ya kauda kanshi idonshi jawur, daddy yace abbana!!!
wannan itace matar da aka daura maka aure da ita, da fatan bazaka bamu kunya ba zaka riketa tsakani da Allah,

Sadeeq murya can kasa yace aure kuma daddy, gaskiya kuyi hakuri, Allah yasani bazan iya daukar alkawarin da bazan cika ba, haba daddy kalleta fa ya fadi yana nuna zulfa yace God forbid, gaskiya ni inada wacce nakeso sai dai kuyi hakuri ya fadi yana mikewa,
Nurain ya daka mishi tsawa yace uban wa kake fada ma saidai yayi hakuri, dan ma kasamu ana lallabaka, meye aibun yarinyar da zaka tashi kana fada ma mutane magana,
sadeeq yace dole kace meye aibunta saboda selfishness irin naka, wato kai saboda an aura maka wayayyar mace high class beb shiyasa ni ka yarda aka dauko min wannan kuchakar a matsayin matat--- wawan mari nurain ya kai mishi wanda ba sadeeq ba har wadanda ke gurin saida suka ji shi a jikinsu,
zulfah da tunda sadeeq ya fara magana ta bishi da ido muryarshi nata mata yawo a dodon kunne, babu kalmar da ya fada da tayi mata zafi saboda dadin jin muryar da ta dade bataji ba,
Sadeeq ya rike kuncinshi yace ni ka mara, mummy ta mike ta kara daukeshi da mari tace ya mareka nace ya mareka marar mutunci ko kanada abinda zakayi,
idon sadeeq ya kada babu alamun fari a ciki yace wallhy bazan zauna da ita ba, narantse da Allah natsaneta, ya koma kusa da daddy da ya dafe kanshi yace daddy ka taimakeni wallhy inada wacce nakeso,
dan Allah karka bari su ruguza min farin cikina, kuka sosai yakeyi saboda zafin da zuciyarshi takeyi,
daddy ya dafa shi yace kayi shuru ya isa haka komai zaizo da sauki,
farouk dake gefe ya kalli zulfah dake kuka yaji tausayinta sosai a ranshi yace wannan wace irin muguwar tsana ce, ya kalli mummy da idonta ya ciko da kwalla yace mummy kiyi hakuri dan Allah ki barshi ya auri wacce yakeso din ko ya zauna da zulfah cutar da ita zaiyi,
mummy cikin kuka tace wallhy na rantse ko bayan raina abba ya saki zulfa'u ban yafe mishi ba,

Daddy ya daka mata tsawa yace wai Aisha meyasa kike da taurin zuciya ne,
meyasa baki da feelns ne ki duba kiga yadda yaron nan ke kuka kinsan ba karamin abu kesa shi kuka ba, ki daina saurin yanke hukunci kai tsaye har ya kaiki dayin mummunan furuci irin wannan,
Nurain cikin fushi yace daddy ka daina biye mishi iskanci ne yasa shi kuka saboda ya raina mutane sakarai kawai wanda ko kadan baisan kanshi ba bare yasan inda yake mishi ciwo,,
ya kalli jalila da zulfah yace su tashi su wuce daki, ya kama mummy dake kuka suka wuce daki yana rarrshinta, daddy ya shiga rarrashin abba yace ya kwantar da hankalinshi zai aura mishi wacce mishi wacce yakeso, anty amarya ta fito itama tasa baki cikin kissa ta nuna batasan me ke faruwa ba kuma ta rufe abba da fada kamar da gaske tace ya tashi maza yaje ya bawa mummy hakuri, suka dinga tausar shi da alkawarin duk randa yake so za'a aura mishi sanah,
daddy Allah yasani bai so jin sanah danshi ke so ba, amma saboda kunyar idon anty amarya yasa ya amince amma sam dabi'uta da rawar kanta basu mishi ba....

Mrs tijjani shattima....
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 2⃣4⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Daren wannan ranar ya zama dare mai zafi a gurin zulfa'u,
ko kadan bata runtsa ba, in ta tuno kalaman mutumin da ta dade cikin kogin sonshi da son ganinshi sai kuka mai tsanani ya kufce mata,
da taga zuciyarta na neman bugawa ta mike ta shiga bayi tayi alwala tayi sallah ta dinga adduar neman zabin Allah...

Bayan sallar asuba ta fito ta nufi kitchen dan hada ma twins breakfast da lunchbox, ta zauna tana fere dankali,
farouk ya shigo kitchen din, tsugunawa yayi agabanta, ta dago kumburarrun idanuwanta tace ina kwana yaya farouk,
ya kafeta da ido yace lafy lau,
ya kwanan kuka? tayi murmushi tace ni banyi kuka ba, yace nasan bakiyi kuka ba, bacci kikayi ya maida fuskarki haka ko?
ta sunkuyar da kanta idonta ya ciko da kwalla,
Cikin tausayi yace kiyi hakuri zulfah, komai zai wuce, wata rana sai labari, komai ya faru dake rubutacce ne bazaki taba tsallakeshi ba,
kiyi ta addua idan aurenki da abba akwai alkhairi Allah ya daidaita ku,
idan babu alkhairi Allah ya kawo rabuwarku cikin sauki ba tare da wata fitina ba,
""AMEEEEEN'" sukaji an fadi da karfi, suka daga kansu suka ga sadeeq da ya dawo daga masallaci a bakin kofar kitchen,
zulfa'u ta sunkuyar da kanta da sauri ta cigaba da fere dankali, ya harareta cikin tsana da kyama yace da ko kin kyautawa kanki in har kikayi wannan adduar dan ko kadan aurena dake babu alkhairi,
kema kinsan a yadda nake dinnan ban kamaci mace irinki ba, ki taimaki kanki kije ki samu mummy ku warware duk wani kullin da kukayi dan wallahi bazan taba sonki ba yaja dogon tsaki ya fita,

Kukan dake makale a makoshin zulfah ya fito da karfinshi, zuciyarta ta kasa jure muggan kalaman sadeeq,
tabbas da wani ke bata labarin cewa sadeeq din da take matukar kaunar ganinshi zaiyi irin wannan halin bazata yadda ba, kuka ta dingayi,,
farouk ya kasa jurewa idonshi ya ciko da kwalla ya tashi ya fita da sauri,,,
Saida tayi kuka mai isarta sannan ta cigaba da aikinta....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 2⃣5⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Tunda ya shiga daki ya kwanta bacci ya daukeshi sai after 12 ya tashi yayi mika ya shiga wanka,
yana fitowa ya dauki wayarshi dake ta faman ruri tun yana bayi,
ya daga yace mutumina ya akayi ne, daga daya bangaren yace baka da kirki marafa ashe dama da gaske ka shigo gari, jiya zabba'u ke fada min ta ganka ban yarda ba saboda I clld u a kashe ashe da gaske kai din ta gani, sadeeq yayi dariya yace Hilal complainer, walhy shigowar yamma nayi kuma banje ko ina ba ina gida dama ina shirin kiranka zaka dan rakani abuja,
hilal yace ok gurin karfe nawa,
sadeeq yace gurin 4 haka dan acan zamu kwana, hilal yace kwana marafa,
sadeeq yace yess please karka ce bazaka je ba gobe zamu dawo in shaaa Allah, hilal yace to bari in gani zanzo arnd 3, sadeeq yace yauwa abokina ko kaifa sai kazo akwai gist, suka dan taba hira kafin su aje wayar...

Karfe uku da kwata hilal yaxo gidan lokacin sadeeq na zaune yana shan farfesun da anty amarya ta mishi,
yana ganin hilal ya mike cikin farin ciki yace dadi na dakai cika alkawari suka tafa, a tare suka zauna cikin jindadi dan sunyi missing juna,
hilal yace mummy na ciki ne, sadeeq yace eh tana ciki bari in gama muje ka gaisheta, saida suka gama sannan suka mike sukayi hanyar dakin mummy sadeeq yana adduar Allah yasa kar ta mishi abinda ta mishi dazu da yaje gaisheta,,
yana murda kofar sukayi karo da zulfah bowl din farfesu ya fadi kasa romon ya dan fallatsan ma hilal,
ta ja baya da sauri ta tsuguna tace dan Allah kuyi hakuri wallahy bansan zaku shigo ba,, sadeeq yayi tsaki a hankali saboda idon mummy,
hilal yayi murmushi yace babu komai tashi kije ta mike da sauri ta fita hilal ya bita da kallo ta gefen idonshi, mummy ta kalli hilal tace kayanka sun baci sosai ko hilal, yayi murmushi yace a'a mummy kadan ne zanje in canza wasu, ina wuni?
Tayi murmushi tace lafy lau ya ummanka, yace tana nan lafiya tace in gaisheki, tace ina amsawa zabba'u ta guje mu kwana2, yace wallhy makaranta ce ta boyeta,
tace ayya Allah ya bada sa"a,
yace ameen mummy,, saida shuru yadan ratsa na tsawon minti biyu sannan sadeeq da kanshi ke kasa tun shigowar su ya dago kai yace mummy zanyi tafiya xanje abuja,
saida ta dau lokaci dan kar hilal ya gane wani abu ta maida kallonta gurinshi tace hilal da kai xa"ayi tafiyar kenan yace eh mummy,
tace to Allah ya tsare a dawo lafiya, sukace ameen dukansu sannan suka tashi suka fita,,

Sadeeq ya kalli hilal yace muje ka canza kaya wadannan sun baci,
hilal yace no muje sai in biya ta gida in canza mu wuce,
amma bansan yarinyr nan ba marafa yar uwarku ce,
sadeeq ya harareshi yace yar aiki ce, hilal yace kaiii haba, amma tanada kyau ni da zaka shige min gaba a bani ita in aura ai da naji dadi,
sadeeq da karfi yace wannan karamar yarinyar hilal yadda kake dinnan,
hilal yace kaifa banza ne, irinsu ake aure ay,
wallhy wannan nan da 2yrs bazaka ganeta ba, ay ni nafison irinsu, da wayayyun matan nan na zamani wanda suka gama zama fanko, gara in auri sweet16 muyi zamanmu lafiya batasan wani ba in ba ni ba,,
Sadeeq yaja dogon tsaki yace lallai abincin wani gubar wani ni banga abinda zanyi da wannan kwailar ba wallahy,
hilal yace kai kace ay, kai ay dama daban ne kafi dealn da manyan mata niko irin wadannan sun isheni in mori kuruciyata a gurin mai kuruciya,
sadeeq yace dalla tafi can ni wuce muje kar muyi dare,
hilal ya dan waiga yace to dan kirata mana in ganta da kyau,
sadeeq yaja tsaki ya dauki keyn mota ya fita yace ka shiga ka kirata da kanka,
hilal ya fito yana dariya suka shiga mota suka wuce....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 2⃣6⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Tun bayan isha'i suke kofar gidansu sanah har gurin tarah sanah bata dawo ba,
hilal cikin kosawa yace nagaji da zama anan marafa,
ko yar gold ce wannan ay sai ka bari gobe ka dawo ko, wace macen kirki ce zata kai wannan lokacin a waje, ni dai na gaji wallhy!!
Sadeeq ya kalli agogon hannunshi yace kayi hakuri mu kara mata 5mins in har bata dawo ba sai mu wuce, hilal yayi tsaki yace yau zanga wannan yarinyar da ta ruda min marafa,
sadeeq ya lumshe idonshi yace aiko zaka ganta abokina, ta hadu karshen haduwa, ni kaina na kagu in ganta,
hilal zaiyi magana ganin wata bakar land crusher da tayi parking a kofar gidan ta hana shi,
Sanah ce ta fito daga cikin motar da wani matsatstsen wando da rigar da dakyar ta kai mata cibiya,
saida ta tsaya ta gama magana da mutumin dake motar sannan ta dago tana dariya tana daga mishi hannu,
Fulll light sadeeq ya saki cikin kunan rai ya haskata sosai, hilal ya kalleta sosai yace subhallahi marafa badai wannan bace sanah??

Sadeeq bai bashi amsa ba ya bude motar ya fita cikin bacin rai,
sanah ta karaso gurin cike da masifa, tace malam wani irin iskancine wannan zaka has--- maganar ta makale a makoshinta saboda ganin sadeeq, taji tsoro a can cikin zuciyarta saboda ganin da yayi mata da wani,
amma da ta tuna abinda ke tsakaninsu sai ta dake taja tsaki ta juya tayi hanyar shiga gida da sauri har yana tuntube yabi bayanta,
ta kara sauri ta shige gida, har ta kama kofar parlor zata bude ya cimmata,
ya janyota da karfi kamar zai cire mata hannu, tayi yar kara tana ture hannunshi, ya kara matse hannunta yace uban waye ya saukeki a wannan lokacin,
ta harareshi tace ban sani ba, ni dalla malam ka sakeni,
zuciyarshi kamar wuta yake jinta ya kalleta daga sama har kasa yayi tsaki yace kalli yanda kika fita duniya suka gama ganinki a haka wasu irin matsiyatan kaya ne wannan,,
ta daka mishi tsawa tace nasa din in ma nayi yawo tsirara Ina ruwanka, dan Allah ka sakeni kafita harkata kaje can ka zauna da zabin mahaifiyarka ka barni in auri wanda zai soni familynshi ma su soni,
ya murde hannunta cikin fushi yace ni kike fada ma wannan maganar,
ta fashe da kuka sosai tace na fada maka din, dan Allah ka rabu dani karka fama min ciwon da ya fara warkewa a zuciyata,,
kayi nesa dani ko zan samu saukin abinda nakeji game da kai,
jikinshi yayi sanyi ya
rungumeta sosai a jikinshi,
murya kasa2 yace haba sanah ya kike so inyi da raina, kinsan irin wahalar da nake sha a kanki, kinsan irin matsalar da nake fuskanta yanzu a gida kuma duk a kanki, plss karki kawo karshen soyayyarmu saboda auren da ban daukeshi aure ba,
kinsan ke nakeso kuma bazan taba iya hada sanki da wata ba,,
ajiyar xuciya tayi saboda dadin jinta jikin sadeeq, wani irin sonshi takeji yana ratsa ko ina na jikinta, amma dole ta dan wana shi kadan, cikin muryar kuka tace nidai na fada maka ka rabu dani bazan iya aurenka ba, bazan iya kallon wata mace na amsa sunan matarka ba bare har in iya sharn dinka
, na rokeka ka kya--- da sauri ya katseta yace karki min haka sanah,
wallahy zuciyata zata iya bugawa, dan Allah kar kiya punishn dina da laifin da bansan dashi ba,
ta dago kanta tace amma ay kasan yadda zakayi dashi,
cikin rashin fahimta yace ban gane ba,
tace ay ba daura maka ita akayi a kafa ba, kana da ikon sakinta tunda ikon a hannunka yake,
cikin rawar murya yace "saki "fa kikace, ta daure fuska tace kwarai kuwa,
ko bazaka iya bane, ya kara matseta ajikinshi, yace zan iya mana baby, lokaci nake jira, dan yanzu mummy na cikin fushi zata iya aikata komai in na sake ta, amma kisa aranki bani da aure dan ban dauki auren nan a bakin komai ba wallhy,
taji dadi sosai, ta dago kanta tace haka dai kace,
yace I mean it "sajna", "kasam se!" Ki yarda dani,
ta dan bugi kirjinshi tace ni ban iya yaren india ba,
yayi murmushin jindadi yace dole ki koya cwthrt,
nan suka cigaba da soyayyarsu ta mantar dashi bacin ran da ya shiga na ganinta da wani,
Hilal da ya gaji da zaman jirah ya bude motar ya fito yana tsaki yace lallai wannan dan iskan ya raina min hankali,
kofar gate din ya shiga ya hango su manne da juna, ya karasa ranshi a bace, saida yayi magana kusan sau uku sannan suka dawo hayyacinsu,
yayi tsaki cikin kyama ya kalli sadeeq yace wani irin iskanci ne zaka barni a waje kamar wani driver, wallhy inda nasan haka zaka min da babu abinda zaisa in baro abubuwa masu muhimmaci in rakoka,
sadeeq ya matso kusa dashi
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment