Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ta kalleta ba, sanah bata kawo komai a ranta ba saboda ita a gurinta ba wani abu sukayi ba, hannun jalila taja suka wuce ďaki,
sadeeq ya zauna gefen mummy yace sannu da hutawa mummy, ko kallonshi batayi ba, Allah ne kadai yasan irin bakin cikin dake ranta, in har aka cigaba da tafiya a haka to tabbas sanah zata jefa mata danta cikin halaka, gara tun wuri ta nemi kimtsatsiyar yarinya irin laila ta aura mishi,
Sadeeq ya dukar da kanshi kasa yace mummy magana nake miki, nan ma banza ta bawa ajiyarshi,
laila ce ta shigo twins da ayda na biye da ita suna cin apple, tace sannu da hutawa mummy,
Mummy tayi murmushi tace sannu maman yara, ta kalli sadeeq da baya cikin walwala, tace abba lafiya, ko dai cikinka bai dauka bane, nasan dai babu abinda zai saka damuwa sai maganar gas, yayi yake yace kaii anty laila wato ma sharrin da kike min kenan ko, tace ba wani sharri sai gaskiya, ka dai kusa tafiya kaje ka dinga cin jagajaga mukuma mu huta, murmushi kawai yayi yana kallon mummy da ta kara hade fuskarta, laila tace mummy me zan dafa ma daddy?,
Mummy tace ki dafa kome kika ga ya dace, ay kinsan abubuwan da yafi so, laila tace to mummy ta tashi tana tsokanar sadeeq, sanah ta fito cikin matsatsatsun kaya kamar zasu yage in tayi nishi mai karfi, tace anty laila ashe kina nan, laila ta kalleta sosai tace eh yanzu na fito ina zuwa haka, tace zamu dan kara fita ne, mummy ta mike ta wuce daki ta barsu a parlon, anty laila tace a haka zaki fita, ko dankwali babu, sanah ta yatsine fuska tace wallhy zafi2 nakeji, ta zauna kusa da abba tace muje ko dear, ya kalli anty laila dake musu kallon mamaki ya dan matsa kaďan yace to muje, laila taja hannun su twins suka wuce ciki zuciyarta cike da tambayoyi, matsowa kusa dashi tayi ta fara shafa fuskarshi, murya can kasa yace no sanah ki bari mana baki ganin a gida mu--- bata bari ya karasa magana ba ta tura harshenta cikin bakinshi, irin waďannan abubuwan da sanah ke mishi su ke kara tsumashi cikin kaunarta, nan da nan ya mance damuwar da ya gani a fuskar mummy, kuma ya kasa hana sanah sarrafashi a wannan lokacin, saida ya ji motsin taba kofa sannan ya maza ya janye daga jikinta yana maida numfashi, Nurain ne ya shigo drivern shi na biye dashi da kaya kallon su yayi yadda suke a kasalance a yamutse yasa shi zargin wani abu, cikin sauri ya kauda zargi saboda yasan sadiq bazai taba aikata wani abu na sabon Allah ba,
sadiq ya taso yace yaya sannu da dawowa, yayi murmushi yace yauwa abba, yau baka fita ba kenan, yace na fita ban dade da dawowa ba, sanah ta gaisheshi ya amsa mata a dakile dan nurain ya tsani mace mara kamun kai, ga shegen son maza dan shi kanshi tasha kawo mishi hari, amma bai taba barin wani ya sani ba saboda shima ya iya maganin mata irinta, dauke kanshi yayi hade da dan tsaki da ya tuno abinda ta mishi last zuwan da tayi, dakin mummy ya wuce,
zaune ya sameta tayi tagumi, ko sallamar shi bata ji ba, saida ya dan taba ta ta ďago ta kalleshi ta kirkiro murmushi tace a'a yaushe ka dawo, ya tsuguna a gabanta yace ban dade da dawo ba mummy,
fada min damuwarki dan fuskarki ta bayyana min abinda ke ranki, fada min ko menene in dai har bai fi karfina ba zan nemo miki,, mummy ta kara kirkiro murmushi tace babu abinda ke damuna Nurain me ka gani a fuskata, cikin damuwa yace abubuwa da yawa mummy, ki daina kirkiro murmushi kina daura shi kan fuskarki, komin kankantar damuwa ina ganeta musamman a gurinki mummy, dan Allah fada min damuwarki, tayi ajiyar zuciya, tace ba wata damuwa bace Nurain, kawai dai ina son in sama ma abba matar aure ne, mace nakeso kamar laila ko ma wacce tafita Nurain, banason abba ya auri macen da zata kaishi ga jahannama, wannan ita kadai ce damuwata, Nurain yace wannan ba damuwar da zata dameki bane mummy, ki kwantar da hankalinki kiyita addua, kuma bazamuyi gaggawa ba domin samun natsatsiyyar mace a wannan zamanin sai an nutsu, nima nayi matukar sa'ar dacewa da uwa irinki wacce ta iya dubawa ta hango min mace kamila kamar laila,
mummy tayi murmushi tace ai laila daban take Nurain Allah ya bamu wacce zatayi hali ko bai kai nata ba, dan nasan samun mace kamarta akwai matukar wahala, Nurain yace zamu samu mummy wacce ta fita ma,,
in shaa Allahu daga abba har farouk sai sun auri kamilallun mata mummy mudai cigaba da addu'a, Ameeen mummy tace sannan addua ay kullum munayi saidai mu kara Allah ya bamu sa'a......

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ●● ZULFAH ●● 9⃣
By Aysha Ya'u kurah

Shiri sosai zulfa takeyi, saboda tsabar farin cikin da take ciki yau ko kadan aikin gidan bai mata wahala ba, tun kafin 4 ta tashi ta gyara ko ina, dan yanzu da taimakon Allah da taimakon malam saleem goggo bata yi mata komai, tsakaninsu harara ce daga nesa amma bata gigin dukanta saboda tsabar tsoron abinda kaje yazo,
abinci ne dai yanzu ko loma basa bata, sai dai goggo ameena ta bata in ta shiga gidansu ,
ledar da malam saleem ya aiko mata dashi jiya ita ta dauko ta kwance ta fara fito da kayan ciki,
sababin uniform ne da takalmi mai kyau sai turaren tony mantana, cikin murna ta sa kayan bayan ta gama shafa man da ta roko gurinsu fa'ee, uniform din yayi mata kyau sosai tasa takalminta ta feshe jikinta da turare ta kimtsa dakinta ta tsaya tayi addu'oi kafin ta fito, goggo na zaune tana tuyar waina maza sun fara shigowa ta tsugunna ta gaishe ta, goggo ta kalleta sama da kasa cikin bakin cikin da ya kasa boyuwa a fuskarta, ta debo ruwan miya a ludayi tace uban waye dinka miki uniform,
salaha dake zaune tace ai harda takalmi goggo,
zulfa taga goggo na neman bata mata kaya da ruwan miya, tace jiya malam saleem ya aiko min dashi,
gaban goggo ya fadi amma sai ta dake tace ko uban malam salim ne sai in watsa miki ruwan miyan nan inga wace tsiyar za'ayi dan ni bana tsoron uban kowa, ta ajiye ludayin miyar tace Allah ya taimakeki yau banjin bala'i da wallhy bazaki fita ko nan da can ba, rabani da wannan koďaďďiyar fuskar taki ta fadi tana harararta,
tayi maza ta tashi ta fita, a zaure tayi karo da bangis,
innalillahi kawai take fadi a ranta saboda yadda yayi mata katanga, alamarin BBG shine yanzu babbar matsalarta a rayuwa dan ba karamin matsa mata yayi ba, gyaran murya yayi yace amarya amarya, ta dago kanta ta kalleshi, yace kinsan yau ne daurin aurenmu, jiya nazo tambayarki abinda kike bukata ban sameki ba, marka ta baki sako?
Na bata dubu hamsin ayi miki siyayya saboda kurewar lokaci,
idon zulfa ya ciko da kwalla, ta kalleshi tana girgiza kanta tayi waje da gudu, gidan su fa'ee ta shiga tana kuka sosai, goggo ameena tace me yasameki zulfa,

Zulfa cikin kuka ta fada mata abinda ke faruwa tsakaninta da babangida goggo tasa salati, tace Allah ya kyauta ki auri wannan yaron, ay share hawayenki yanzun nan zanje in samu ado, zulfa tace goggo ko kin sameshi babu abinda zai iyayi, tunda goggo ta karbi kudinshi nasan Allah ne kadai zai kubutar dani daga aurenshi,
fa'ee ta gama shirinta ta fito suka haďa baki da goggo sunata rarrashinta, goggo ta basu kosai da koko zulfa ko kadan bata hango ta inda abinci zai bi bakinta har ya wuce makoshinta ba, da kyar suka lallabata taci kosai daya goggo ta kawo mata kwalli tace maza kisa kuma ki nutsu kiyi karatun saukarki, ta daga ma goggo kanta, suka gama shirinsu delu na gefe tana musu habaici, saboda babangida saurayin hanne ne, jiya ma a dakinshi ta kwana, ya gayamata dalilinshi na auren zulfa'u dan ya bata mata rayuwa ne ba wai dan yana sonta ba, wannan dalilin shi ya kwantar da hankalin su hanne dasu goggo marka,

A kofar islamiyya suka ga malam salim cikin farar shadda mai kyan gaske, tsugunawa sukayi suka gaisheshi, ya amsa yana kallon zulfa'u, bai taba ganin tayi kyau ba irin yau,
yace malamai kuma ďalibai har kun iso, suka daga mishi kansu sama suna murmushi,
yace to maza a shiga ciki ayita bitar karatu kafin lokaci yayi, zulfa ta wuce ciki fa'ee ta tsaya ta labarta mishi komai dake faruwa,
Fuskar saleem ita zata nuna miki ainihin tashin hankalin dake zuciyarshi,, ya daga kai ya kwala ma zulfa da ke tafiya kamar wacce kwai ya fashe ma a ciki, ta karaso gurin tace gani malam, yace dagaske ne abinda fa'iza ta faďa min, ta kalli fa'iza sannan ta daga kanta tace eh malam, innalillahi wa inna ilaihir rajiun abinda malam ke fadi kenan a bayyane, cikin tsawa yace me yasa baki fada min ba tuntuni, muryarta na rawa tace ban dauka dagaske yakeyi ba,
yayi huci mai zafi a zuciyarshi yace ta ina zan fara, lokaci ya riga ya kure, kuma aure ba wasan yara bane,
ga mugun sonta da yakeji kamar zai kasheshi ya kasa fada mata, gashi yanzu ko ya aureta bashi da gurin ajiyeta dan matar babanshi azzaluma ce zai iya cewa gara ma goggo marka dan ma shi namiji ne shiyasa
kuma bawai zai zauna a gari bane karatu zai tafi, dama ya riga ya tsara musu rayuwarsu tana js3 yanzu yasan zai gama law skull har Allah yasa ya samu aiki yazo ya aureta lokacin ta gama makaranta, yanzu duk plan dinshi sun rushe kenan, idonshi ya kaďa sosai yanata karanto adduoi cikin ranshi,
kauda kanshi yayi yace ku wuce ciki, har sun fara tafiya ya kira zulfa, ta dawo,
yace dago idonki ki kalleni, a hankali ta ďago kanta suka hada ido tayi maza ta saukesu yace kisa a ranki duk wata matsala da zata dameki to Allah da kuma ni saleem Abdulrahman muna tare dake, wannan issue din ki fitar dashi a ranki ki nutsu kiyi karatunki ta yadda zai gamsar,
ki manta da anyi wannan maganar saboda zata zama tarihi in shaa Allah,,

Zulfah taji wani dadi a ranta ta tabbatr zai shawo mata kan matsalar,, tace nagode malam ta ruga cikin makaranta tana murna, kallo ya bita dashi, to yanzu ta ina zai fara, yasan halin bbg sarai tunda ya fada sai ya cika, shi kuwa ya dau alkawarin bazai zuba ido yaga wanda zai cutar da zulfa'u ba, ko bai aureta ba zaiso ta sami wanda zai kula da ita sosai, "to waye shi kuma a ina yake,"
wani sashi na zuciyarshi ya tambaya,
, yayi addu'oi sosai sannan yaji duk wata damuwa ta yaye mishi yasan in shaa Allahu kafin karfe biyu ya samu mafita.....

Mrs tijjani shattima..
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ●● ZULFAH ●● 1⃣0⃣
By Aysha Ya'u Kurah

A nutse ta gama shiryawa cikin rantsatstsen lace mai matukar kyau ta dauko milk hijab ta saka , parlor ta fito anan ta tarar da nurain yana zaman jiran fitowarta, mikewa yayi, ya dan tsuguna ya gaisheta, ta amsa tace ka dade kana jira ko, yace a'a mummy, laila ta fito ta gaisheta itama ta shirya cikin java holland tasa hijab dinta , yara duk suna islamiyya, anty amarya ta fito daga kitchen suka gaisa da mummy, tace har kun gama shiri, mummy tace walhy ai mun ma kusa makara, tace to sai kun dawo, ta koma kitchen, su mummy suka fita suka wuce, tun suna cikin gida wayar mummy ke kara taki dagawa sai danna reject takeyi, kiran karshe ne anty laila ta kalli screen din taga abba, ta juyar da kanta dan tana sane da irin fushin da mummy keyi dashi tun kafin ya tafi, kuma duk a dalilin sanah,
wayar nurain ya kira ya dauka yace abba ya kake,
cikin damuwa sadeeq yace lafiya lau yaya, yayi dan tsaki kamar zaiyi kuka yace yaya mummy fushi takeyi dani ko na kirata bata dagawa dan Allah ka bata hakuri ni bansan me nayi mata ba, Nurain yace ok ka bari zan tambayeta sai in kiraka ka bata hakuri, cikin farin ciki yace to yaya nagode sosai, suka danyi hira akan school dinshi sannan ya kashe wayar,
Nurain ya waigo ya kalli mummy cikin girmamawa yace mummy abba yayi miki laifi ne, kanta kawai ta girgiza ba tare da ta kalleshi ba tace wani abu yace maka, Nurain yace eh yace wai baki daukar wayarshi kuma baisan abinda yayi miki ba, mummy tace uhumm tunda bai san abinda yayi ba shikenan nima bansan meyasa bana daukar wayar shi,
laila ta kyafta ma mijinta ido saboda yadda taga yadda ran mummy ya fara baci, tayi mishi alama da yayi shuru,
hakuri kawai ya bata ya juya yana kallon titi, mummy kuwa ta tsunduma cikin tunanin yadda sanah tayi ma ďanta qawanya cikin zuciyarshi da kissarta da yaudararta, in ta tuno abinda ta kamasu sunayi ana gobe zai tafi har kuka takeyi, wai sadeeq dinta ke rungumar mace har saboda ficewar hayyaci yake fada mata duk duniya babu macen da yakeso kamarta kuma bayajin zai iya son wata bayan ita,
sanah harda kuka tana fadin to idan mummy ta nemo maka mata kamar yadda tayi ma yaya nurain fa, ni gaskiya inada kishi sosai in har kayi aure to walhy bazan aureka ba, ya kara rungumeta yace ni ba yaya nurain bane baby, babu wanda ya isa yayi min aure bada son raina ba, kima daina wannan maganar, mummy ta runtse idonta cikin bacin rai tace zaka ga isata akanka abba, idonta ya soma canzawa kuma ya ciko da kwalla, dai2 lokacin sukayi parking a islamiyyar
"Abdulrahman bin Auff"
Nurain ya fito da sauri ya bude ma mummy ta fito ta boye bacin ranta ta kirkiro murmushi tace sannu Nurain yayi murmushi yace yauwa,
malam saleem ta hango yana tahowa kusa dasu da sauri yana murmushi, ya karaso ya tsuguna ya gaisheta ta amsa tana murmushi suka karasa cikin makaranatar lokacin har ďalibai sun fara karatu, guri na musamman aka bawa mummy suka zauna tare da anty laila,
Dalibai aka dinga kira suna karatunsu kowa cikin kwarewa, kirarsu ma mai dadi dukansu, daga wata "Amina rabi'u"
sai aka kira ZULFA'U ADAM, da sauri malam saleem ya xagoyo ya tsaya saitin munbarin, ta fito cikin nutsuwa ta hau kan mumbari, hada ido sukayi dashi yayi mata murmushin da ya kara mata karfin gwiwa, cikin sanyin murya tayi "mukaddma" sannan ta fara karatunta cikin kira'a mai dadi, sanyin muryarta da yadda take bawa ko wani harafi hakkinshi shi ya burge duk wanda yake gurin, mummy gaba daya ta kasa dauke idonta akan yarinyar, duk wadanda sukayi karatu a gurin babu wanda ya burge ta kamar yarinyar, gashi an bata surar da mummy keso kuma take bitarta a kullum suratul Nisa'i, mummy bata san lokacin da yarinyar ta sauka a kan mumbari ba, sai jin karatun wata tayi itama cikin nutsuwa takeyi, gaba daya daliban sun burge mummy, har aka gama karatun aka rabawa yaran shahadarsu mummy na yabawa yaran a ranta,
Kiran dalibin da yazo na farko a maza akayi mai suna "Musa Ahmed"
yaron yasha kyaututtuka sosai,
sannan aka kira wadanda sukazo na farko a mata su biyu ne Marks dinsu daya,
Zulfa'u Adam Da Bilkisu Nabayi, a tare suka fito cikin murna suma sun sha kyaututtuka harda envlp din kudi aka basu,
zulfa ta kasa boye murnarta sai dariya takeyi,
Mummy nata kallonta, laila ta lura da mummy sosai, dan ta faranta mata rai yasa tace yarinyar can ta burge ni mummy, mummy ta washe baki tace ashe dai bani kadai ta burge ba, yarinyar ta shiga raina laila,
muryar wasu mata a bayansu sukaji suna maganar irin wahalar da marka ke ba zulfa, dayar tace ay laifin duk na ado ne dama mace in taga gida nata ne kuma kana zaune baka tabuka komai sai dai tayi sana'a ta ciyar da kai ai dole ta rainaka, dayar tace Allah sarki dije ai halin marka sai wadanda suka santa, ta rage murya tace bakusan da kudinshi ta siya gidan ba, ita fa ta sace kudinshi lokacin da ya tara zai siya gida, kuma tasa aka rufe mishi baki, shima ba a son ranshi yake zaune a gidan ba dan dai tafi karfinshi ne, Amara tace ni fatana ma Zulfa'u tasamu miji tayi aure tabar musu gidan taje ta huta da wahalar marka,
mummy ta nutsu ta gama sauraronsu, tausayin yarinyar ya shigeta sosai, tana hangota tana dariya da ganinta tana cikin farin ciki, ta mika ma saleem komai na hannunta shima sai murna yakeyi, kusa da malam ado salim yaje ya mika mishi shahadarta da kudin, kuka ya fashe dashi saboda kofar gidanshi na can cike da su bangis da mahaukatan iyayenshi suna jiranshi yazo a daura aure; salim yace baba murna zakayi ba kuka ba, malam ado yace kukan rayuwar da Zulfa'u zata fada nakeyi, ka taimakeni salim, ka taimakeni a cikin malamanku kayi ma wani magana a daura mata aure dashi yanzun nan kafin jama"a su watse, kaga idan aka daura aurenta dole su Alhaji mati su hakura su tafi,
saleem ya shiga cikin tashin hankali, ya kalli mahaifinshi dake zaune a gefe shima cikin damuwa, mummy ce ta karaso gurin lokacin da taji furucin mahaifin zulfa, ta kalli saleem tace malam, in har banyi muku katsalandan ba, inaso a aurawa sadeeq dina yarinyar da naji kuna magana,
saleem gabanshi ya tsananta bugawa zuciyarshi ta karye, ya zaiyi da son da yake ma Zulfa'u, da ya tuno da gidan da zata je kuma yasan wacece Haj Aisha nan da nan ya kauda duk damuwar dake fuskarshi ya kirkiro murmushi yace Alhamdulillah hajiya mun gode wallhy kin taimakemu a lokacin da muke bukata,
malam ado ya kalleta kamar an mishi albishir da gidan aljanna, suka dinga mata godiya tace ay nice zanyi muku godiya, yanzu bari in kira yayanshi yazo ayi magana a daura auren ko, liman yace kwarai kuwa ay bazamu bata lokaci ba,
Mummy tasa laila ta kira nurain, da sauri ya fito daga mota ya shiga cikin makaranatar,
mummy tana murmushi ta fada mishi abinda ke faruwa, yayi ajyar zuciya yace to mummy bari in kira daddy in fada mishi, tace to maza ka fada mishi, ya kira daddy ya fada mishi, daddy yayi dariya yace Aisha case,
to ni me zance kaima uba ne a gurin shi, Allah ya sa alkhairi ce a cikin familyn mu, nurain ya ji dadi sosai yace Ameen daddy sukayi sallama ya kashe wayar, ya fada ma mummy abinda yace, mummy tace to madalla muje ka basu sadaki sai a daura auren mu wuce da amaryar mu,
Nurain yayi mamakin yawan farin cikin da ya gani kan fuskar mummy, ya karasa kusa dasu liman ya zaro dubu 100 ya mika musu yace ga sadakin nan, suka amsa liman yayi adduoi duk malaman dake gurin suka taru guri daya aka gabatar da daurin auren kamar yadda musulunci ya tanadar,
bakin mummy ya kasa rufuwa ta dinga rabon kudi a gurin,
ana gama daurin auren wani malami ya je kusa da speaker ya sanar ma da mutane, dukka mutanen gurin mamaki ne a kan fuskokinsu,
saleem office ya shiga ya daura kanshi a kan table zuciyarshi kamar zata buga,
har aka gama komai zulfah bata san wainar da ake toyawa ba tanacan cikin kawayensu,,

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ●● ZULFAH ●● 1⃣1⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Labari tuni ya cika "babbar saura," murna yan unguwar suka dinga yi, barin goggo ameena har sujjada tayi tasan duk wata wahalar zulfah ta kare tunda an ce mata masu kudi ne ko babu komai zulfah ta shiga daular duniya,
ta dinga jero mata adduo'i kamar tana gabanta,
Marka na zaune dasu delu an ci gayu cikin kayan da ta ragargazo cikin kudin bangis suna zaune suna kulla mugun abu shewa kadai ke tashi suna zaman jiran dawowar malam ado da zulfah a daura aure,
shigowar bangis gidan kamar zaki shi ya katse musu shewar da sukeyi, marka ta tashi da sauri ta matsa kusa dashi tace ango lafiya na ganka haka, wani gigitaccen mari ya kai mata wanda ya dauke jinta na yan sakwanni, tayi ihu taja da baya rike da kunci, delu tace innalillahi babangida me ya faru ne, saida yayi mata mugun kallo sannan ya fara magana cikin karaji, ni za'a raina ma wayau, kun sanni marka kunsan bana ďaukar rainin hankali, wallhy tun wuri ki fito min da duk kudaden da na baki ko kuma inyi miki abinda babu wanda zai ganeki,
Marka da har yanzun zafin mari bai saketa ba tace ni bangane abinda kake nufi ba, bangis yace yanzun nan zaki gane, ya karbi wata karamar wuka a hannun laminu yayo kanta suka sa ihu dukansu suka arce daki, mazan dake kofar gidan su suka shigo da sauri suka bi bangis da kamar ba'a hayyacinshi yake ba, har daki ya bisu mazan suka rikeshi ya dinga tirjiya yana zagezage, dakyar aka fita dashi zaure, marka dasu delu gaba dayansu sun fita a hayyacinsu, saida aka fitar dashi sannan delu ta ďago a hankali ta kalli mutanen dake dakin a hankali tace wai me ya faru ne mu kun barmu cikin duhu,
wani a cikin mazan yace ai yau marka kun tabo babangida ya za'ayi ya biya kudin aure ya tara jama'a sannan aje a daura mata aure saboda tsabar kun raina mishi hankali,
goggo marka ta mike da sauri tace aureee?
Mutumin yace kwarai kuwa aure ga labari nan ya zaga ko ina, saboda haka tun kafin bangis yayi miki rashin mutunci ki bashi kudinshi in ba haka ba wallahi zai muku iya wuya,,,
Marka tasa salati hade da kuka tace ado ya cuceni, wallhy bansan an shirya wannan munafurcin ba,
na shiga uku ni marka yanxu ta ina zan fara bawa bangis kudinshi, kuka sosai takeyi tana aibata malam ado tana fadin har abada shi da gidan nan wallhy yau sai ya rabu da ita, ta dinga tsine mishi,
ai marka bata kara haukacewa ba saida aka fada mata zulfa a gidan masu kudi tayi aure, wani yaron dake gurin saukar ya fito da dubu uku a aljihunshi yace sirikarta tanata raba kudi marka, nima kinga wanda nasamu, sannan naji ance ďan shugaban sojojin sama na nigeria gaba daya ta aura,
Marka da hassada ya mai da idonta kanana, kirjinta yayi nauyi tana masifa karshe ta fashe da kuka sosai, zuciyarta kamar zata buga lallai ado ya munafurceta, ga salaha a gida bai bada aurenta ga masu kudi ba sai zulfa yarinya karama, lallai yau ta kara tabbatar da ado baya kaunarsu yafi son saude da yarta,
bangis ne ya sake shigowa tare da zugarshi da suka gama bashi baki da shawarar ya auri salaha a madadin kudinshi, ya na shigowa marka ta katse kukan da takeyi ta boye bayan delu da ke zaune kamar matacciya,
Wani abokin bangis yace marka ki fito kizo ki sa wani yayi wakilcin yarki salaha, bangis zai aureta a madadin kudinshi, marka ta kalli fuskar bangis taga irin mugun kallon da yake musu, salaha kuwa murna ta cikata kamar anyi wata wahayi zata shiga aljanna, hanne ta mike da sauri tace wace salahar, laminu ya harareta yace salaha nawa ne anan gurin, hanne idonta yayi jawur tace walhy bazai yiwu ba, ni zaka ci amana bangis, to wallhy tallahi yau za'a uwar watsi a gidan nan sai dai kowa ya rasa ta daura dankwalli a kugu tana girgirza,
Sai a lokacin marka ta samu karfin gwiwar mikewa dan taga hanne na neman yi musu salalar tsiya,
(sai kace bangis din mutumin kwarai ne mtswww)
tace ke hanne kinci ubanki bangis din kike fadawa magana, dan yace
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment