Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

cikin tsawa tace wallhy bazai tafi ba sai ya gama bincike an gano azzalumin da ya kashe min miji,
sadeeq ya harareta yace to sai ki zauna a bincike ki amma ni babu wanda ya isa ya cigaba da firgita min mata,
nan hayaniya ta kaure tsakanin sadeeq da anty amarya, zulfah dai kara kankameshi tayi saboda tsabar tsoron da take ji dakyar nurain ya lafar da kurar da ta taso yace ma sadeeq ya barsu suyi duk abinda zasuyi gaskiya zata bayyana,
sai da ya dade yana bata baki sannan suka zauna,,

police din ya cigaba da magana, yace babu wanda ya shigo gidan lokacin da kika gama aikin,,
gaban sanah dake zaune rai a bace saboda yadda sadeeq ya kankame zulfa ya fadi saboda beeba tace mata zulfah ta ganta,
tayi saurin yi mata flashing,
kafin zulfa'u ta bada amsa wayar dake hannunta tayi ringing, AMINIYATA ta gani kururu,
ta shiga zare ido to wacece aminiyata abin da ta dinga tunani kenan,
har wayar ta kusa tsinkewa sadeeq yayi answern yasa speaker saboda taji da kyau, dariya sosai akayi a wayar sannan akace aminiyata komai yayi dai2 ashe shine baki kirani kin fadamin aiki yayi ba,
na miki text jiya da na koma gida kin gani,
zulfah murya a sarke tace waye?, aka sake yin dariya sosai akace ohh na gane kina cikin mutane zan kiraki anjima nidai kar amanta dani in GADO ya shigo hannu,
kafin zulfah ta sake magana har an kashe wayar,
sadeeq cikin rudu ya kalli zulfah yana matsawa daga jikinta, innalillahi wa inna ilaihir rajiun shi suka dinga maimaitawa shida su mummy zulfah ta mike jikinta na rawa tace wallhy bansan ta ba,
karar shigiwar text wayar yasata yin shuru,
sadeeq ya bude text din da ya kara gigita shi,
yayi scrolln na jiya ma,
wurgi yayi da wayar ya mike tsaye da sauri yana ma zulfah kallon tsana sosai, police din ya dauki wayar ya bude text din farko kamar haka,

(aminiya gani nan zuwa na samu gubar sharp sharp wanda ko minti biyar bazaiyi ba zai sheka barzahu, kinga daga nan sai musan yadda zamuyi da sadeeq in kin haifa mishi ya'ya shima a shekeshi gida ya zama naki dan naji kince baya bi takan tsinanniyar kishiyar nan taki itama nan gaba waje zamuyi da ita)

sai text na biyu

(Aminiya na gane kina cikin mutane,,
ko'ina ka zaga yau mutuwar sirikinki kadai akeji gaskiya u are very smart da kikayi tunanin kasheshi kafin ya tona miki asiri, zuwa anjima ina nan zuwa)

Faduwa kasa zulfah tayi sumammiya da ta gama jin maganganun dake cikin text din, yayin da duk mutanen gurin suka dauki salati......

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 5⃣6⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Babu wanda yaje kanta sai anty laila, kuka takeyi sosai tana girgixa ta tace mummy wallhy sharri akayi mata, wallhy zulfah bazata aikata wannan aikin ba,
frmn dinta akayi, mummy dai banda kuka babu abinda takeyi haka nurain, sadeeq kuwa hanyar waje yayi kamar zararre hawaye sun kafe a idonshi, wani iri ya dinga ji a cikin zuciyarshi,
meyasa zulfah zata kashe daddy, why why?? Ya fadi yana buga kanshi a bango, hilal ya taso da sauri ya rikeshi yace haba marafa ya zaka kashe kanka saboda mutuwar daddy,
kayi tawakkali mana kasan duk mai rai fa mamaci ne,
sadeeq ya tsuguna ya rike kanshi sosai yace hilal zulfah ce ta zuba ma daddy guba yaci ya mutu,
hilal ya mike tsaye yana girgiza kanshi yace karyane,
karyane wallhy, ya shiga cikin parlorn da sauri inda ake kokarin yayyafa ma zulfah ruwa dan ta tashi,
gurin mummy ya tsuguna idonshi duk ya canja yace mummy kin zauna da yarinyar nan na tsawon lokaci, kinsan abinda zatayi da wanda bazatayi ba, wannan maganar daga jinta ansan shiryayya ce wallhy zulfah bazata iya kisan kai ba,
anty amarya ta mike cike da masifa tace sannu sarkin shishshigi ga abu nan a zahiri mun gani kuma mun ji zaka zo kana neman kareta to kodai da kai ta hada baki ne in taci dukiyar ta gudu kuje kuyi aure, hilal ya daka mata tsawa cikin bacin rai zaiyi magana jalila ta shigo da gudu tana kuka ta rungume mummy,
kukan jalila da hayaniyar da anty amarya sukeyi da hilal shi ya farfado da zulfah cikin firgici tace wallahy bani bace dan Allah mummy ku yarda dani, anty laila ta dagota ta karasa goga mata ruwan adduar dake kofi, zulfa tayi crolln ta karasa kusa da mummy ta dafata tace mummy ki yarda dani,
wallhy tallahi bansan wacce ta kirani ba, wallhy babu wanda yazo nemana gidan nan ku tambayi masu gadi ma zasu fada muku,
mummy dai kallonta kawai takeyi tana kuka jalila ta rungumeta tace nasan bazaki iya kisa ba zulfa, akwai dai wani abu boyayye a kasa,
dan sandan ya mike da wayar zulfa a hannunshi ya kalli anty amarya dan itace ke bashi full attention dinta, yace hajiya bari muyi binciken mu na karshe sai musan abin yi, tace go on kuyi duk abinda kuka san ya dace, yace good yasa aka kira masu gadin, yayi musu tambayar shin akwai wani wanda yazo gidan nan jiya da misalin hudu da wani abu lokacin mutanen gidan basa nan,
mai gadin yace ehh wasu mata su biyu sunzo daya ta rufe fuskarta da wani bakin abu, sunce mana sun zo gurin small madam, zulfah ta mike da sauri ta karasa gabansu tace ku fadi gaskiya, karkuyi min sharri da kudin zai kare ya barku da zunubi,
dayan mai gadin yace I swear gaskiya muke fada dan basu dade a gidan ba ma suka tafi, zaman dirshan zulfah tayi a gurin gaba daya ta nemi kuka a idonta ta rasa, sai bin su mummy dake kuka takeyi da ido,
ta runtse idonta tace ya Allah kai kadai ne shaidata akan wannan daurin zato da akayi min, Allah dan isarka da ikonka kafitar dani daga cikin halin da nake ciki da gaggawarka ba ta shaidan,. ameen anty laila tace tana sheshsheka,
hilal ya tsuguna a gabanta yace tabbas wanda yayi miki wannan sharrin yayi nisa sosai cikin tsanarki, ki sa a ranki Allah zai fitar dake daga wannan musibar da kika shiga ko ba anan duniya ba zai wanke ki a lahira,
yana kaiwa nan yafita yana share hawaye masu zafi..
Bayan yan sanda sun gama rubuce2 suka bukaci tafiya da zulfah station,
sai a lokacin mummy ta mike tana kuka ta matso kusa da zulfah, tace har yanzun zuciyata ta kasa yadda zaki iya aikata wannan danyen aikin, amma kuma wani sashi na zuciyata yana gasgata kwararan hujojin da suka fito cikin kankanin lokaci, kuje zan cigaba da yi miki addua Allah ya bayyana gaskiya,
ta juya tayi hanyar daki tana kuka nurain da jalila suka bita suna rarrashinta,
sadeeq kuwa daki ya wuce yana kuka, wanda ke waje ma zai iya jiyoshi, sanah na tsaye tana bashi hakuri amma kamar kara zugashi takeyi, ta zauna itama tana matsar kwalla tace ashe mafarkin da ka tabayi zai zama gaskiya,
kayi mafarkin faruwar wannan alamarin duk tunanina aikin mafarki ne ashe zai zama gaske, gaskiya yarinyar nan ta cutar damu matuka,
sadeeq ya juya yayi ruf da ciki yace tashi ki fita plsss inason kadaici yanzu, bana bukatar yawan magana, ta mike sum2 ta fita tana gimtse dariyarta, yanzu kokari kawai zatayi taga ta dauki ciki ta haihu da sadeeq tunda yanzu ita kadai ce dashi...

Labarin wannan mutuwar ko ina ka zaga a fadin nigeria zaka jita,
news papers, gidan radio da tv kowa yasamu aikin yi ,
daga ka kunna kafafen yada labarai zakaji ana fadin mutuwar,
sunan zulfah da hotonta babu inda bai zaga ba mutane sai Allah wadai sukeyi da halinta,
labari ya iske goggo marka tana zaune tayi tagumi tana kallon ya'yan salaha dake raba mata kashi a tsakar gida,
cikin tsawa tace ma salaha tazo maza ta tsaftace mata guri, bazai yiwu kazanta ta koroki daga gidan mijinki ba ki zo nan kuma ki dira min wata, haba!! ko waina an daina siya tun dawkwarku gida saboda bakar kazantarku,
gashi abinci ma da kyar muke samun ci sau daya, maza gyareshi wallhy, shigowar wani yaro wanda yake siyan waina a gurinta ne ya katse masifar da takeyi, yaron yace markus kinsan abinda ke faruwa kuwa a kasar nan,
marka sarkin son jin gulma tace a'a me yafaru, yace hmm an kashe surikin zulfa kuma kinsan waye ya kasheshi,
tace a'a Allahn misiru gareni, yace zulfa ce ta samishi guba a abinci, goggo marka gabanta ya fadi tasan zulfah ko kyankyaso tana jin tausayin kashewa bare dan adam,
amma a fili saboda tsabar hassada da kiyayya tace ay kadan ma suka gani,
yarinyar da ni kaina tasha kawo min hari zata kasheni, Allah ya kyauta gaba ta fadi ta mike da kuzari da murna saboda taji zulfah ta shiga tsaka mai wuya.
Goggo amina ma sunci kuka ita da fa'e dake da da daya da wani cikin, kuka sosai sukeyi suna rokon Allah ya fitar da zulfah daga cikin wannan bala'in.... .

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆5⃣7⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Ranar da daddy ya cika kwana uku bayan gabatar da adduoi da sadaka mutane sun watse cikin jimamin mutuwar bawan Allah mai taimakon talakawa,,

Zaune suke a parlo dukkansu kowa yayi tagumi daga ka gansu kasan suna cikin matsananciyar damuwa,
afrah ta kalli mummy da hawaye ke fita a gefen idonta tace mummy dan Allah kisa su yaya nurain suje su fito da anty zulfa'u wallhy kinsan bazata iya kashe mana daddy ba,
Nurain ya kalli mummy ko zata ce wani abu dan shima zuciyarshi ta kasa yadda da wannan sarkakaken alamarin,
ya maida kallonshi gurin sadeeq da ya takure kanshi guri daya yace abba tashi muje station muga inda suka tsaya a binciken,
sadeeq bai kalleshi ba ya girgiza mishi kai kawai, anty laila ta mike tsaye tace muje abban ayda dan Allah muje inga halin da zulfah take ciki,
anty amarya ta fito daga daki tana kuka sosai wata matashiyar yarinya na biye da ita, cikin kuka tace duk wani bincike ya gama tabbata yaya,
kalli wannan hoton, mummy ta share kwalla a idonta ta karbi hoton, fuskar zulfah ta gani muraran kwance tsirara da wani saurayi,
runtse idonta tayi ta wurgar da wayar tana salati,
anty amarya tace yanzun nan yarinyar nan tazo ta kawo hoton ashe abun da daddy ya kamata tanayi kenan shiyasa tayi saurin kasheshi dan kar ya tona mata asiri,
mummy ta mike tsaye jiri ya debe ta tafi luuu ta fadi kasa sumammiya,
da sauri dukka yan gidan suka yi kanta suna kuka aka shafa mata ruwa,
saida tayi kusan minti 5 sannan ta farfado tana kuka sosai, anty laila dake rike da wayar tace wallhy wannan ba zulfa'u bace mummy,
wai meyasa kowa baya fahimtar abinda nake fahimta a kwakwalwata ne,
ta matso kusa nurain kamar zararriya tace abban ayda nasan zaka fahimce ni, wallhy wannan sharrin computer ne,
yarinyar dake tsaye tayi saurin cewa zakiyi kaffara kuwa, ni ko alqurani za'a bani zan rantse da cewar wannan zulfa'u ce, ranar da abun nan ya faru kunga text din da tayi min,
suka duba text din da numbr duk na zulfa ne, lokacin da muka hadu da ita na rakata hotel din na jirata a reception ta gama ta fito suna fada da shi wannan da kuka gani mai suna Bamba akan kudin da ya bata kadan ne,
sunata zage2 lokacin shi kuma marigayi ya fito da abokanshi ya ganta,
tun daga lokacin da ya ganta take fada min ya fara ciwo har an fita dashi waje, tace min bai fada ma sadeeq ba amma tasan yana dawowa zai fada mishi saboda haka zata san abun yi kafin ya dawowa ashe kasheshi zatayi yarinyar ta karasa fadi tana kuka sosai,
anty laila ta harareta cikin kuka tace munji tatsuniyarki yanxu imani ne ya shigeki kika zo kika tona ma kawar shashancin taki asiri, yarinyar ta dake saboda kwarewa a iya sharri tace ni bana biye mata kullum fada nake mata kuma wallhy in baku yarda ba yanzu sai in shigo muku da Bamba dan shima yace sai ya tona mata asirin abun da takeyi a boye,
anty amarya tace je ki shigo dashi,
sadeeq dai tunda ya kalli hoton ya runtse idonshi bai sake budewa ba, har suka gama karyarsu da karairayi,
zuciyarshi ta zama kamar dutse saboda duk yadda yaso ya tankwarata taki tankwaruwa,
fashewa yayi da wani irin kuka mai tsuma zuciya yana tambayar zuciyarshi whyy ta damu da his father murdrr,
meyasa bazata daina tunanin zulfa'u ba a wannan lokacin da ya kamata ta tayashi tsanarta,
meyasa har yanzu zuciyarshi take kallon zulfa'u innocent,
kukan da yakeyi ya ba dukka yan parlon tausayi jalila ta rungumeshi tana rarrashinshi tana kukan itama,
Bamba da maimzy basu bar gurin ba saida sukayi ma zulfah qullin da babu mai warwareshi sai Allah, duk gurin sun yarda saboda hujjojin da suka kawo musu ciki harda warwaron zulfah da mummy ta siyo musu tare da jalila wanda nata ya bace kwana biyar kafin faruwar wannan lamarin anty laila ce kadai bata yarda ba, tirkashi....

Nurain yaa dafe kanshi da ya dau zafi yace laila ki daina kukan nan haka mana,
hujjoji nawa aka kawo kuma duk masu karfi, shi kanshi daddy kafin a kasheshi saida yayi ma mummy tsokaci akan hakan,
tsokacin me yayi mata ta fadi rai bace, tace matan abba nawa ne, abban ayda bakasan sharrin mutum ba ko, babu abinda zance maka yanzu saboda ko nace bani da shaida amma ol wat I knw shine zan koma aiki saboda zulfah, in shaa Allahu sai na gano azzalumin da ya daura mata wannan sharrin, nooo nurain ya fadi yana kallon cikin idonta,
bazaki koma aiki ba laila, babu abinda zakiyi da case din wacce ta kashe min mahaifi,
ka daina cewa ta kasheshi ta fadi da karfii, wallhy zaka tsaya shaida ranar gobe kiyama,, kuma aiki sai na koma ko da kuwa hakan zai kawo karshen auren mu, tana kaiwa nan tasa kai ta fita daga dakin, dafe kanshi yayi idonshi yayi jawur saboda kalaman laila, ya za'ayi laila tayi mishi haka, yanzu da wani baki zai fara fada ma mummy laila zata tsaya ma zulfa'u, dole ya dakatar da laila kar ta karama mummy wani ciwon...

mrs tijjani shattima...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 5⃣8⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Tun safe laila ta gama shirin tafiya gurin zulfah,
duk irin tataburzar da sukayi cikin dare da Nurain bai sa ta karaya ba,
ita dai abin da tasani shine xata fara bincike daga yau kuma ita kadai tasan inda ta karkata akalar bincikenta,,
dakin mummy taje ta gaisheta da jiki sannan tayi mata sallama tace zata je asibiti ta dawo, mummy tayi murmushi dan jalila ta gaya mata duk yadda sukayi da nurain cikin dare kuma ta goyi bayanta dari bisa dari baza dai ta nuna ma kowa bane dan kar mutane su dauka mutuwar bata dameta ba,
ta kalleta tayi mata Allah ya tsare kuma Allah ya taimaka,
anty laila tace Ameen mummy, ta fita ta dauki motarta bata yarda wani driver ya kaita ba,

Baban zulfah ne tsaye shi da kabiru a waje sai sharar hawaye yakeyi kabiru na rarrashinshi, tun jiya suke tsaye a gurin an hanasu ganin zulfa, saboda tana kebabban dakin masu manyan laifuffuka,
laila nayin parking ta fito tayi hanyar shiga ciki, ganin baban zulfah ya dakatar da ita,
ta karasa gurinsu ta gaishesu, baban zulfa yayi saurin tsugunawa saboda ya ganeta, cikin kuka yace hajiya walhy zulfah bazata aikata kisan kai ba, an samu sabani dai gurin bincike amma ni nasan bazata aikata ba dan Allah ku taimaka ku fito min da ita,
anty laila ta share hawayen da ya zubo mata a idonta tace karka damu baba, ka daina wannan kukan addua ita kadai ce zata fitar da ita daga wannan mugun kullin da akayi mata, adduarka muke bukata Allah zai bayyana gaskiya,
malam ado yace to nagode hajiya Allah ya bayyana gaskiyyar nan cikin gaggawa, ameen anty laila tace sannan ta wuce ciki suna binta a baya,
Da kyar aka barta ta shiga gurin zulfah saida ta nuna musu itama bata da mutunci sannan suka barta ta shiga dakin da akayi mishi kewaye da mukullan tsaro masu matukar tsauri,
can lungu inda ta hango zulfah a dukunkune ta karasa, dafata tayi sannan ta tsuguna tana fuskantarta,
a hankali ta fara mata magana,
zulfah taki dago kanta sai sheshshekar kuka da takeyi, anty laila tace zulfa kiyi shuru ki dago ki bani hadin kai in fitar dake daga cikin wannan zargin da ake miki,
nan ma zulfah bata dago ba, anty laila tayi maganar duniya zulfah taki dago kanta ta kalleta bare ta bata amsa,
gaba daya ta cire rayuwar duniya a ranta gara ta mutu da ta cigaba da rayuwa a wannan rudun dake cikin wannan kazamar duniyar mai cike da sarkakiya,
ran anty laila yayi matukar baci ta mike tace kinsan shurun nan naki zai iya haifar da munanan abubuwa kuwa,
kinsan mutanen dake bukatar ki a rayuwarsu kuwa, shin kin manta da mahaifinki wanda kike fada min a kullum burinki ki yanta shi daga wahalar da ya dade yanayi in har kika tsaya da kafafuwanki, ta matso kusa da ita ta girgizata tace meyasa bazaki bamu hadin kai ki fada mana abinda kika sani ba,
ta fita waje da sauri ta kira mahaifin zulfa suka shigo tare suka hadu suka dinga yi mata magana harda kukansu amma zulfah bata dago kanta ta kallesu ba saboda bata da wata kalmar da zata fada wacce zata iya fitar da ita daga sharrin kisan kai da zinah,
har lokacinsu ya cika basuyi nasarar jin komai daga bakinta ba,
tashi sukayi suka fita cikin bakin ciki,,
kwana uku anty laila tayi tana zuwa gurin zulfah amma kullum da bacin rai take komawa gida,
gashi su anty amarya sun matsa sosai akan a shigar da kara kotu a yanke mata hukuncin da ya dace, ramewa sosai laila tayi saboda bata da kuxarin cin abinci,

Ranar akayi bakwai ranar farouk ya dawo, tun a makaranta ya shiga matsanancin tasshin hankali jarabawar da yakeyi ita ta hanashi dawowa, yayi mamakin ganin duk su mummy sun yarda da cewar zulfah zata iya kashe daddy, har daki yaje ya samu sadeeq da ya kauracewa fita ko nan da bakin kofa,
ya zauna yana mishi magana akan su san yadda zasuyi su fitar da zulfah tun kafin a shiga kotu,
hararar shi sadeeq yayi murya a dashe yace farouk ka daina min wannan maganar wace hujja kake da ita da zaka ce bazata iya kashe daddy ba,
hujjoji sun nuna itace farouk,
idonshi ya fara fitar da ruwa yace farouk zuciyata taki bani hadin kan cireta a raina,
ka fada min yadda zanyi inji na tsaneta farouk, ka fada min dan Allah,
farouk ya tsuguna kasa shima yana kuka yace yaya abba zuciyarka tasan gaskiya kaine kaki bata hadin kai, shawarar da zan baka shine mu dage da addua ba dare ba rana har Allah ya fito da gaskiyar wannan alamarin...

Hada hannu farouk da laila sukayi gurin bincike, babu yadda farouk ma baiyi ba akan zulfa ta fada mishi abinda ta sani, da kyar ya shawo kanta tace yaya farouk bani da wata kalmar da zata fitar dani, duk yadda zanyi in kare kaina bazai yiwu ba, kawai ku barni in mutu in huta da wahalhalun dake cikin duniya, daga haka bata kara ce mishi komai ba har ya tafi shima cikin kunan rai..

Ana gobe za'a shiga kotu anty laila a susuce take saboda rashin shaida ko daya, tun asuba ta tashi tayi tagumi tana tunanin ta inda zata bullo, wayar zulfah dake gurin police ta fado mata a rai, ta mike da sauri tayi wanka nurain dai na kallonta baice mata komai ba saboda mummy tace ya barta tayi kuma ya bita da addua,
tana fitowa wanka ta wuce station din, bata bukaci ganin zulfah ba saboda tana matukar bata mata rai,
saida ta jira police din da case din ke hannunshi ya iso sannan ta karbi wayar, tun a gurin ta fara duba wayar,
dialled calls ta duba tun na kwana uku kafin rasuwar, daga na jalila sai na sadeeq sai kawayenta Rolex da Frisky, haka ma recieved cals sai wannan number "aminiya" din da akasa kuma sau daya takk aka taba kira da ita, ta shiga mesges ta duba recvd shima na sadeeq ne kadai sai na numbr aminiya,
a send kuma wata numbr ce akayi ma sending text din da su maimzy suka kawo, ta duba tym din da date din,
taayi mamaki matuka saboda lokaci daya akayi su da wanda akayi sending na aminiya,
ta dunga binsu tana dubawa saboda ta gasgata idonta,
saida ta gama tabbatar wa sannan ta mika ma police din wayar bayan ta copy numbrs din ta mike tayi mishi godiya ta fita,
a mota ta dinga kiran layikan duk a kashe mtn office ta nufa dan ayi mata binciken layikan,
abunda ya kara girgixa anty laila da aka gama bin diddigin layin bai wuce cewar duk sababbin layi ne da ake siyar dasu da register su,
sannan dayan ko kira ba'a taba yi dashi ba,
dayan kuma sau daya tak aka taba amfani dashi,
da sauri jikinta har yana rawa tace ayi mata printing informatns din,
nan sukayi mata ta fita tana musu godiya dan tana ganin kamar komai zai zo da sauki, To Allah yasa.....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 5⃣9⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Ranar monday 12 ga watan sept,
ranar ce aka shirya shiga kotu,
a daren ranar daukacin masoyan zulfah basu runtsa ba, addua ce suke ta yinta gurin ubangijin talikai akan Allah ya bayyana gaskiyar wannan alamarin,
dakin sadeeq na shiga yana zaune kan dadduma yana kuka mai sauti, haka kawai ya tsinci kanshi da yin addu'a akan Allah ya bayyana gaskiyar wannan alamarin a yanke hukunci kowa ya huta,
sanah da ta tare a gidan saboda mutuwar tana tsaye jikin kofar dakin tana hararashi a zuciyarta tana ba ameen ba,
gaskiya bazata taba bayyana ba tunda babu wani mai shaida a hannu,
tayi murmushin mugunta da ta tuna irin kullin da sukayi ma alamarin ta juya ta shiga daki ta kwanta tayi baccinta cikin kwanciyar hankali...

Tun tara mutane suka fara dafifi dan jin hukuncin da za'a yanke ma matar da ta kashe surikinta,
duk inda ka kewaya a gurin zaka ga mutane gungu2 suna tattaunawa game da rashin imanin mutanen wannan zamanin,
Goma dai2 kotun ta cika makill wasu ma a tsaye suka tsaya saboda cikowar gurin, shigowar alkali ne ya sa kotun tayi tsitt kamar babu rayuka a ciki,
nan suka gabatar da abinda suka saba yi kafin daga bisani a fara gabatar da shari'u, mai gabatarwa ya mike ya gabatar da case din dake gabanshi na farko, na zulfa'u Adam wacce ake zarginta da kashe mahaifin mijinta, alkali ya gyara glass dinshi da alkalminshi,
ya fara da sunan Allah mai rahama mai jin kai, sannan ya bukaci a shigo da wacce ake tuhuma,
Mutane suka maida kallonsu gurin kofa dan ganin wacce suke ma kallon mara imani mai son duniya, shigowar zulfah cikin hijab da ankwa a hannunta yasa kotun ta dauki hayaniya sosai,jalila dake rakube gefe daya ta kalleta idonta ya ciko da kwalla saboda yadda duk ta zube cikin yan kwanaki,
rolex da frisky na hango suna kuka mai sauti suna kallon zulfah,
bayan ta tsaya a inda aka bukaci ta tsaya yan sanda na tsaye gefenta,
alkali ya bukaci ayi shuru a kotun,
nan ya kalli barristers din ya dan sauke glass dinshi,
nan da nan wani bakin handsome ya mike cikin girmamawa yace sunana barrister "Tahir Kurah" nine lauyan wanda suke kara,
ya koma ya zauna, anty laila ta mike itama cikin girmamawa tace sunan Sunana
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment