Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ta sa hijab ta tada kabbarar sallar walha...

Mrs tijjani shattima..
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 3⃣6⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Wow
Wow
Wow
abinda yan hostel dinsu keta fadi kenan tunda ta gama shiryawa,,
linda okoro tace smiling beauty u luk take awy,
rolex tace kamar queen din gaske danyi tafiya muga,
ta fara takawa a hankali anata ihu da tafi a hostel din,
gashin kanta ya kwanto a bayanta yaji gyara da ribbons da wasu kyalkyali wanda aka watsasu a flowrs,,
sai qamshi takeyi gashi makeup din da akayi mata babu wani hayaniya,
tun 8:30 suka fito, Rolex da Abdulhi su suke rike da bannr,
sai wata yarinya dake ma queen fiffita a bayanta prince nd princess na watsa flowers a duk inda queen zata taka, suna zaune dukkansu queens din,
suma sauran sunyi kyau amma basu kamo kafar zulfa'u adam ba, sai kuma Wasila kamba da itama tayi sosai..

Tsaki yayi da yaji ringing din wayar jalila a motar shi dan ya saukesu in sun gama zai dawo ya maida su gida,
juya kan motarshi yayi dan har ya wuce katsina rd,
yana shigowa makarantar yayi hanyar field can gaba dab da su principal ya hango jalila tsaye kusa da uncle majeed, tsaki yayi yace shegen rawan kan tsiya,
ya dinga kutsawa saboda cikowar mutane sam idonshi bai gane mishi masu matching ba,
ya kusa da jalila yaji wasu maza tsaye hankalinsu na kan abinda akeyi dayan yace wayyo cizo mubarak kaga wata andar oh my God mubarak yace kaidai bari jamal tun kafin azo kansu nake kallonta wallhy ban taba ganin kyakykyawar mace kamarta ba,
daga kanshi yayi yana son kwalawa jalila kira yaga sun kara matsawa gaba tana daga hannunta tana murmushi,
daga kan da yayi idonshi yayi arba da kyakykyawar halitta, ganin abin yakeyi kamar gizo, murmushin dake kan fuskarta shi ya kara mata nuri,
tafiya takeyi kamar batason taka kasa yaran na watsa mata flowers dai2 gurin principal ta tsaya idonta ya sauka akan jalila da uncle majeed,
murmushi tayi musu mai kashe zuciya sannan ta fara taka step din table din,
kidin band na tashi ko ina matchers na yin style din da aka koya musu mai ban sha'awa,
ihu kawai kakeji lokacin da zulfah ta gaida principal da mutanen dake kewaye da ita sannan ta dauki flowern dake tray ta rataya mata a wuya ta mika mata hannu suka gaisa ta dan rungumeta,
snow spray wani yaro dake tsaye bayanta a matsayin bodyguard ya fara fesawa,
zulfah ta juyo tana murmushi zata fara sakkowa har lokacin yana biye da ita da spray din, juyowarta yayi dai2 da karasowar sadeeq gurin shima ita yake kallo ta kasa dauke idonta cikin nashi, gaba daya gabobin jikin sadeeq sun tsaya chakk basa aiki,
wani abu yaji yana tsarga mishi a jinin jikinshi,
dauke idonta tayi da sauri jikinta na rawa ta fara sakkowa a hankali takalmin kafarta ya gurde ta tafi da baya zata fadi ta runtse idonta hade da yar kara saboda ta sadakar zata fadi kasa kuma tabbas zata ji ciwo,
jinta tayi jikin mutum ya riketa sosai,
ta bude idonta a hankali tana kallonshi,
uncle majid yayi ma bodyguard alamar ya cigaba da fesa spray din saboda kar suyi failn dan abin ya bada wani style na daban,
da sauri ya cigaba yaran suka shiga watsa flowers,
kida hade da ihu na tashi sosai,
dagota yayi hannunshi na cikin nata har lokcin yana kallonta,
Da kyar ta saita kanta ta cire hannunta ta koma ciki jikinta na rawa suka cigaba da matching har suka wuce idonshi bai daina kallonta ba,
dafashi jalila tayi tace yaya abba baka wuce ba,
yayi tsaki ya harareta ya kalli jakarta da ya yar a kasa lokacin da zai taimaki zulfah yace dauki jakarki, abinda ya kawoni kenan,
ya juya ya wuce dan kar jalila ta fahimci halin da yake ciki,,,
zama yayi a mota zuciyarshi cike tambayoyi,
lumshe idonshi yayi ya dinga tuno abin da ya faru,
oh my Goshh ya fadi hade da kifa kanshi, addua yakeyi akan Allah kar yasa sonta ne zai kamashi farat daya,
wani irin abu yaji yana taso mishi yana nukurkusarshi,
wayyo ya fadi yana girgiza kanshi,
dole in yi nesa da duk abin da zai kara hadani da yarinyar nan,
meyasa ma ya riketa da ya barta ta fadi abinda zuciyarshi keta kitsa mishi kenan,
tada motarshi yayi ya tafi da niyyar bazai dawo ba dan baisan kara haduwa da ita, me yake shirin faruwa dashi,
in ya tuna shock din da yaji sanda ya riketa sai ya runtse idonshi ya rage gudun motarshi,
ya rike mata kala2 ya taba su sosai amma bai taba jin abinda yaji a gurin yarinyar nan ba,
ko sanah da yake mutuwar so bai jin wannan abun akanta, gida ya wuce direct dan ya samu relief...

Anya kuwa sadeeq hmmm.. mudai je zuwa...

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 3⃣7⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Yana isa gida ya tarar da mata cike da gidan anata ciye2 ko ina a hargitse,
basusan ya shigo ba hirarsu sukeyi kuma duk akan samari, Beebah da tazo ma sanah hutu daga abuja tana kwance daga ita sai daurin kirji sai musu sukeyi suna mikewa suna girgiza jiki,
dogon tsaki yaja ya wuce daki cike da kyamar halin sanah, nan ya tarar da wani bacin ran,,
dan kuwa shiga yayi da niyyar ya watsa ruwa ya kwanta ko zaiji sanyi a ranshi ya tarar da dakin kaca2 anci abinci saman gadon plate din indomien ma na can gadon da gwangawanin kan juice,
ranshi ya baci matuka ya fito parlorn yana kwalawa sanah kira, ta mike tana yatsina fuska ta karaso inda yake tace lafiya,
ya harareta ya riko hannunta yana janta da karfi har suka kai dakin,
yace uban waye yace ki shigo min daki ki batamin,
ke kike gyara min daki?
Ki bata naki ki bata nawa saboda ke kazama ce mara hankali ,
kallon mamaki ta tsaya tana ma sadeeq, tace iyyye kai har kanada karfin gwiwar yi mani masifa, kai har ka isa dan na shigo dakinka kace zaka daga min murya, ta nuna shi da yatsa tace wallhy ka maida hank--- mahaukatan mari ya kai mata a duka kuncinta zuciyarshi na tafarfasa da halin sanah,
gashi duk abinda take mishi ya kasa daukan mataki akanta,
kuka sosai ta fashe dashi tace ni ka mara, wallhy ka mari aurenka mugu kawai,
ta fita tana kuka duk ta cika gidan da hayagaga,
kawayenta suka taso suka rungumeta suna rarrashinta ta wuce dakinta ta dauko keyn mota tasa jallabiyya suka fita daga gidan ita da kawayenta,

zama sadeeq yayi a kasa ya rasa me ke mishi dadi,
idonshi nan da nan ya kada yayi jawur saboda damuwa, tunanin zulfah shi ya toshe duk wani lungu da sako na zuciyarshi, gani yakeyi ma kamar duk shakar numfashin da yakeyi hade suke tahowa da tunaninta,
ya Allah karka horeni da abinda bazan iya ba akan laifuffuka na,
tashi yayi ya shiga wanka ko zaiji sanyi a zuciyarshi da yakejin kamar dutse mai nauyi ne a cikinta yana fitowa ya kwanta yanata juyi da kyar ya samu baccin damuwa yayi gaba dashi....

Gurin alpha Demola suka nufa kowa na fadin albarkacin bakinshi akan abinda sadeeq yayi mata, suna shiga sanah ta fashe mishi da kuka, yace oooo me ya faru kuma sanah,
ta rushe da wani kukan tace aiki ya baci alpha yau sadeeq har marina yayi yanata zagina, saida yayi min dukan tsiya ka taimakeni a daura wani aikin kan wancan dan banaso in rasa sadeeq plss alpha,
demola ya kalleta yace aah bari muyi istahara inaga akwai wani da yake bata mana aikin da munayi,
ya fara"
"incantion" cikin yaren yarbanci yanayi yana kiran sadeeq,
can ya gama, ya kalli sanah yace tashi kije wani gurin xai nemeki a gigice duk inda kike, ay sadeeq naki ne babu wata mace da zaiso bayan ke tashi kije,
ta ajiye mishi damin kudi ta mike ta fita cikin jindadi dan tun aurenta da sadeeq take harka dashi bata taba samun failure ba, shurun da sadeeq yayi ya kasa mata magana akan daren farkonsu da
yadda take juyashi da yadda yake tsoronta ma wannan duk aikin demola ne,
ko anty amarya bata san tana zuwa gurinshi ba dan wata kawartace ta bata shawarar yanzu mata basa zama haka duk son da namiji yake maka wata rana sai ya juya maka baya bare ita da bata kai virginity dinta gidan aure ba dole ta mike tsaye,, wannan dalilin yasa ta fara zuwa gurin demola dan bata son rabuwa da sadeeq ko a mafarki bare a zahiri, ta ja motarta suka wuce sheke ayarsu ita da kawayenta,

Firgigit sadeeq ya mike daga gajeren baccin da ya daukeshi, abin da ya faru tsakaninshi da sanah ya shiga dawo mishi,
ya mike a firgice yace ya salam, meyasa na mareta meyasa ban taushi zuciyata ba,,,
to yanzu in zan fara bi in nemota,
wayarshi ya dauko ya shiga kiranta, ya kirata yafi a kirga tana kallon wayar amma taki dauka sai dai su sheke da dariya ita da kawayenta,
kamar zaiyi kuka ya mike gaba daya ya manta da tunanin zulfah da abinda ya faru tsakaninsu dazu,,
waje ya fita ya shiga motarshi ji yayi duk duniyar ma zafi take mishi saboda sanah bata kusa dashi,
gidan aneesah ya fara zuwa tace bata zo ba,, yaje duk gidan da yasan tana zuwa amma bata can,
dafe kanshi yayi da ya karaso kofar gidansu ya rasa me yake mishi dadi, kuka kawai yakeson yi dan shine toshe a makogoronshi, yanayin da ya tsinci kanshi dazu yake son tunowa amma kamar an shafe abin a kwakwalwarshi,
saida ya kusan minti biyar sannan ya shiga cikin gida,
jalila ya tarar a parlor tana zaune, tace yaya shine kaki dawowa sai kiranka nakeyi baka dauka ba,,
kanshi ya sara mishi sosai yace ina zan dawo,
tace au ka ma manta ko,
shikenan ta cigaba da latsa wayarta, sama ya wuce dakin mummy, saida ta gama abinda takeyi sannan ta kalleshi tace me yake damunka abba,
ya dago jajayen idonshi ya kalleta yace wallhy bansani ba mummy, zuciyata na min zafi sosai dan Allah ki taimakeni, tace dame zan taimakeka? Idonshi ya ciko da kwalla yace nima bansani ba amma ina cikin wani hali dan Allah mummy ki taimakeni, ya fashe da kuka mai ban tausayi dan zuciyarshi kamar zata buga haka yakejinta,
tayi ajiyar zuciya ta karanto adduoi a zuciyarta, zata fara mishi magana afrah ta shigo dakin tace yaya abba wai kazo inji anty amarya, anty sanah ma tana can naga tana kuka, wai kayi mata duk-- mummy ta buge bakinta tace wa ya tambayeki ko abinda aka aikoki ki fadi kenan, ta turo baki fita tana kuka,
mummy ta kalli inda sadeeq yake taga wayam babu kowa, bata san tunda afrah tace sanah na dakin anty amarya ya fita ya nufi dakin,
mikewa tayi ta sakko ta nufi dakin anty amarya,
Mummy ta gigita sosai da taga sadeeq durkushe gaban sanah sai zazzaga mishi masifa sukeyi ita da anty amarya yana bada hakuri muryarshi har rawa takeyi,
da sauri ta karasa ta daukeshi da mari, ta juya ta dauke sanah ma da mari sadeeq ya mike da sauri ya rike sanah dake kukan marin da mummy tayi mata, ,
ran mummy yariga yagama baci, tace saketa abba, saketa ka wuce muje, jikinshi na rawa cikin muryar kuka kamar wawa yace mummy kiyi hakuri kinga kuka takeyi kuma ke kika sata kuka kalli yadda fuskarta tayi jaaa,
mummy tayi salati idonta ya ciko da kwalla tace shikenan abinda nake gudar maka abba ya faru, Allah ya isa tsakanina daku hadiza, bazan taba yafe muku ba da kuka mayar min da ďa mace,
in shaa Allahu bazaku ga da kyau ba, anty amarya ta kalleta shekeke tace saidai in kece bazaki ga da kyau ba tunda babu abinda muka ma danki,
so ne yakeyi ma sanah na tsakani da Allah ba komai ba kuma ke baki isa ki raba abinda Allah ya hada ba, saboda haka ki fita harkar yara indai baso kikeyi kiji kunya ba, sanah ta buge hannun sadeeq tace wallhy bazan koma gidanka ba kaje ka zauna da mahaifiyarka,
cikin gigita sadeeq ya rikota yace ki rufa min asiri wallhy zan iya mutuwa in har kika rabu dani,
zan iya rabuwa da kowa akanki sanah, ya tsuguna yana kuka kamar karamin yaro yana rokonta,
mummy da kukanta ya tsananta ta fita da sauri tayi dakinta tana kukan halin da sadeeq ke ciki...

Mrs tijjani shattima....
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 3⃣8⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Duk sunah zaune a dakin shuru in banda gunjin kukan mummy babu abinda ake ji,
Nurain da hankalinshi yake a tashe tun shigowarshi, ya dafa gwiwowinta cikin damuwa, yace mummy dan Allah ki daina kukan nan haka, in shaa Allah komai zaiyi sauki,
cikin kuka tace yaushe zaiyi sauki, abba ya riga ya fada tarkon su hadiza,
sun rabani da dana, sun rabani dashi nurain,
ta kara fashewa da kuka, anty laila tace dan Allah mummy kiyi hakuri duk tsanani yana tare da sauki, in shaa Allahu zai fita daga cikin halin da yake ciki mu dage da addu'a komai zaizo mana da sauki,
Nurain yace hakane mummy mu dukufa kai kukanmu gurin Allah da yardarshi komai zai wuce,
yanzu zanje insa ayita sauke alqurani da adduoi akanshi,
dan Allah ki cire duk wata damuwa aranki kar wani ciwon ya kamaki mu dage da addua,
nan suka dinga rarrashinta har hankalinta ya kwanta sannan suka barta ta dan huta,,,,

Gosshhh!!
gaskiya bantaba ganin cool guy kamar wannan ba,
Hmm walhy Rolex baki kare mishi kallo bane saboda kuna matching ba karamin cizo na yayi ba frisky ke magana rike da towel a hannunta,
zulfah ta amshi towel din ta daura tace humm kawai ta bude drawer ta dakko bath cse dinta, rolex tace smilley yayan nan naki ya zama topic of d town a skull dinnan, duk inda ka wuce maganar shi kawai akeyi,
zulfah tace wai bazakuyi wankan bane ko in wuce ne in kun gama muhawarar kwa taho,
rolex tayi dariya tace wato muhawara ma mukeyi ko,
suka wuce suna ta mata magana duk akan sadeeq ita dai jinsu kawai takeyi, dan tun dazu take kokarin yakice abun da ya faru a zuciyarta ko kadan bata tuno shi bare ya dameta,
suna gama wanka suka dawo suka shirya cikin nyt wear kowa ya kwanta gurin kwanciyarshi suna jefo ma juna hira kadan2 har bacci yayi gaba da rolex da frisky,
zulfah taja bargon jikinta har kanta, tiryan2 abubuwan suka shiga dawo mata kamar lokacin suka faru,
runtse idonta tayi tana kokarin kawar dasu amma abin ya faskara, bazata iya cewa ga yanayin da take ciki ba a wannan daren, ita dai abinda ta sani shine tunani yaki barinta ta samu hutu har bacci ya samu damar sace kwayar idonta,
to wai meyasa take tunanin mutumin da ya tsaneta fiye da komai a rayuwarshi, meyasa zuciyarta zatayi rinjaye gurin tunanin wanda baya kaunar ganinta, tambayarta ta karshe wacce ta samo amsarta nan da nan itace meyasa sadeeq ya taimaketa,? zuciyarta tace abinda ko wane musulmi zaiyi kenan in yaga dan uwanshi musulmi zai cutu,
kwarai haka ne sadeeq ya taimaketa daga faduwa a gurinne saboda zuciyar musulnci amma badan komai ba,
kuma ko baizo gurin ba tasan Allah zai turo wani ya taimaketa, da wannan tunanin ta kauda duk wani abu a ranta har bacci yayi gaba da ita...


Watan sadeeq biyu ko hanyar gidansu baya bi,
duk da ba mazauni bane saboda aiki duk wkend yake samun hutu,
ya tare a gurin sanah dake cin karanta babu babbaka,
gani yakeyi duk duniya babu mai kaunarshi kamarta, duk wknd in ya dawo bata barinshi yaje ko ina har wayoyinshi kashesu takeyi saboda kar a damesu a cewarta,
duk wasu abokan shedancinta sun san ta daina fitowa wknd saboda sadeeq na gida,
hakan yayi ma sadeeq dadi ya dauka ta canza ne ta daina yawo, ga gidan ta samo wata mai aiki da take gyareshi, matsalarshi daya gurin abinci,
sai dai yaje restaurant yaci,

ranar wata friday ya dawo da ciwon kai mai zafi sosai,
rungumeshi sanah tayi tana mishi sannu da zuwa, dishi2 yake ganin idonshi dan haka suka wuce daki, kwanciya yayi a kan gado ko zaiji saukin kan amma juyawa kawai yakeyi kamar ana burga wani abu a cikinshi,
da kyar ya mike ya shiga wanka, yana gamawa bai iya yin komai ba saboda azaba ya kwanta cikin ikon Allah bacci yayi gaba dashi a cikin baccin sai ya dingajin kamar ana buga mishi wani abun a cikin kwakwarwarshi,

Tashi yayi da sauri yana salati saboda mummunan mafarkin da yayi, wai ga mummy nan tana kuka jalila da nurain sun riketa suma suna kuka, gefensu kuma gawa ce ta mutum kwance dayan gefen kuma wata yarinyace da bai gane kamanninta ba itama kukan takeyi da yan sanda akanta, sosai mafarkin nan ya ruda sadeeq,
ya mike yayi sallah sannan ya fito parlor nan ya tarar da sanah tana kallo ya zauna gefenta ta shige jikinshi tace my dear har ka tashi ya kanka, , yace umm na tashi ya dan rage ciwo,
wani mummunan mafarki nayi baby , sanah tace ya salam wane irin mafarki nan ya kwashe duk mafarkin ya fada mata, tayi murmushi tace wani abu sai mafarki, ka kwantar da hankalinka kowa na gida na lafiya, anjima ma ka shirya muje ka gaishesu tunda ka dade bakaje ba,
ya kalleta sosai yace are u crious, ta gyada mishi kanta tace yess ka kusa three mnth fa ay ya kamata muje ko, yayi murmushi yace hope dai ba takura kanki kikayi ba, kinsan bana son abinda zai matsa miki kin yarda muje,,
tayi dariya cikin jindadi tace eh ai ni nace muje so ba wani matsala dear,
ya mike yana jindadi dan yau sanah ta barshi ya ziyarci mahaifanshi da ko waya tace kar ya kara musu, kuma shi a ganinshi dai2 tayi saboda duk so ne ya jawo hakan...

Mrs tijjani shattima..
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 3⃣9⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Tunda ya karyo kwanan gidansu gabanshi ke faduwa, ya rasa dalilin wannan faduwar gaban da yakeji,.
horn yayi masu gadi suka bude mishi kofa suna sara mishi,
yayi parking suka fito shi da sanah, amrah da afrah suna wasa a tsakar gida suna ganinshi amrah ta taho da gudu ta rungumeshi tana kiran sunanshi,
afrah tayi tsaki ta wuce ciki tana gunguni ita a dole bata sonshi yanzu saboda kullum mummy na kuka tana kiran sunanshi ko cikin dare inta farka fitsari sai taga mummy zaune tana kuka kuma duk shi yasata kukan, da sauri mummy ta fito jin sunan da amrah ta fadi, haka laila da jalila dake rike da babyn laila dan wata biyu suka fito dan suga ta inda abban zai shigo,
afrah taje gurin mummy tace mummy kinga amrah taje ta rungume yaya abba harda mishi dariya bayan tasan kullum sai kinyi kuka akanshi, karki kara mata magana tunda bata jin haushin abinda ke saki kuka,
mummy da idonta ya ciko da kwalla ta tsuguna zata ma afrah magana sadeeq ya murda kofar suka shigo,
idon mummy kyar akanshi shima ya kasa dauke nashi akanta, gurinta ya nufa yana tafiya kamar wanda bashi da laka,
har ya kusa kaiwa inda take sanah ta daka mishi tsawa,
ya tsaya chak bai waigo ba kuma bai daina kallon inda mummy take ba, sanah tace ina zakaje, kazo kawuce muje ka gaida anty dee tukunna sai ka dawo ka gaidata,
ko ka manta da marin rashin mutuncin da tayi min a gabanka, jalila da anty laila zuciyoyinsu cike da adduoi,
mummy ta runtse idonta hawaye na binsu a zuciyarta tace Allah kaine mai karfin iko ka nuna ikonka anan gurin,
ya Allah kai kace duk adduar uwa karbabiya ce akan danta Allah ka dawo da hankalin dana gurina ka fitar dashi daga jarabtar da yake ciki ya zuljalali wal ikram,
cikin fushi afrah ta matsa kusa dashi ta jawo hannunshi tace yaya abba meyasa kullum kake sa mummy kuka ne, meyasa baka jin zafi a jikinka in mummy na kuka, meyasa zaka dinga hana mummy baccin dare, saboda kai mummy bata cin abinci sosai kullum sai tayi kuka, kaje ka rarrasheta ta daina kuka in haka ba babu ruwana da kai I will hate u to d coo in mummy bata daina kuka akanka ba,
sanah tace iyyye lallai sadeeq tsayawa kayi, bakaji abinda nace maka ba ko, kuma ka tsaya kanajin rashin kunyar da wannan yar cikin taka take maka ka kasa tabuka komai,
sadeeq da kirjinshi ke bugawa har lokacin yana kallon mummy na zubda hawaye,
mummy ta kasa jurewa ta tashi ta shige daki tana kuka, jalila ma ta ruga daki tana kuka sosai kamar ranta zai fita,
sanah taga sadeeq bai motsa ba ta karasa kusa dashi cikin fushi tasa hannu zata janyoshi, zulfah dake tsaye jikin kofah itama shigowarta kenan da uniform ajikinta kuma ta gama gani da jin duk abinda ya faru ta karaso da sauri ta shiga tsakani ta rike hannun,
wani abu sadeeq yaji tun daga yatsun kafarshi har kanshi ya waigo da sauri yana kallonta,
kallon cikin idonshi takeyi itama tana murmushi mai kyau ta juya rike gam da hannunshi ta fara tafiya,
a hankali kafarshi ta fara dagawa yana binta kuma yana karewa duk ilahirin jinkinta kallo,
duk masifar da sanah keyi baisa zulfah ta sakeshi ba duk da a tsorace take amma ta dake saida ta kai kofar dakin mummy sannan ta tsaya a hankali tana kallon cikin kwayar idonshi tace ka shiga ciki yaya abba,
ka shiga gurin mahaifiyarka dan aljannarka tana karkashin kafarta, karka tuna da komai da kowa a lokacin da kake gabanta,
ka bata duk wata kulawar da zai sata farin ci--- janyota yayi tafada kirjinshi ya juya baya da sauri glass din da sanah tazo bugawa zulfah ya sameshi a gefen hannunshi,
kofar dakin ya bude ya turata da karfi sannan ya dauke sanah da mahaukatan mari, ihu ta saki ya dinga dukanta yana fadin maganganun da baisan daga inda suke fitowa ba,
da gudu anty amarya ta fito saboda jin ihun tayi a cikin baccinta, cikin firgici tace kasheta zakayi abba na shiga uku, ta rikeshi itama ya turata ta fadi ya cigaba da dukan sanah dake kuka kamar mahaukaciya da kyar suka gudu daki suka datso ya tsaya yana buga kofar kamar zai ballata,
ga jini na bin hannunshi shi kanshi ya rasa abinda ya harzukashi haka,
can dakin mummy kuma mikewa tayi da taga zulfah ta rungumota tana kuka sosai,
anty laila ta shigo tace mummy alhamdulillah Allah ya karbi adduarmu, in shaa Allahu komai yazo karshe da ikon Allah ta fada ma mummy duk yadda akayi ta cigaba da cewa kuma gashi can sai dukanta yakeyi, ta dafa zulfah tace Allah ya taimakemu bata sameki ba da mun shiga uku,
mummy sujjada tayi tana godewa Allah tana tawassali da manzo Allah s.a.w....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 4⃣0⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Zama sadeeq yayi a parlon yanaa kuka sosai,
ya rasa me ke damunshi,,
zuciyarshi sai zafi takeyi, kuka sosai yakeyi harda sheshsheka yaji an dafashi ya waiga ya kalleta itama kukan takeyi ya rungumeta yana kuka yace jalila me yake faruwa dani dnt kn waz wrng wv me, dan Allah ku taimakeni,,
plss ki bawa mummy hakuri,
cikin kuka tace mummy bata kullaceka ba yaya kazo muje ka bata hakuri,
ya girgiza kanshi yace bazan iya haďa ido da ita ba jalila,
tace karka ce haka yaya ka tashi muje mummy zata yafe maka,
ya mike sukayi dakin mummy da kyar ya iya shiga kanshi na kasa ya karasa kusa da kafarta ya fashe da kuka,
ta dagoshi tana hawayen farin ciki ta rungumeshi,
cikin kuka yace ki yafemin mummy
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment