Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

bangis in ka ganta bazaka taba ganeta ba.

A mota suna tafiya yana ta janta da hira saboda yaga duk zuciyarta a jagule take, tunanin su goggo kawai takeyi,
lallai duniya ba matabbata bace ji yadda Allah ya maida marka da su delu da ada suke ganin kamar sun fi kowa ita kuma da suka kaskantar da ita sai Allah ya daukaka ta,
ikon Allah kenan,
sadeeq ya dafa ta yace wannan tunanin ya isa haka shi dama Allah babu yadda bai iya ba, mudai cigaba da addua Allah ya tsarkake mana zuciyarmu, tace haka ne ameen,
yasha kwanar wata unguwa mai kyau anan cikin Gra, ta kalleshi cikin rashin fahimta tace ba gidan su zabba'u ake bikin ba,
yayi shuru har saida suka kai wani dankareran gida ya tsaya a waje ya kalleta yace ziyara muka kawo,
tace gurin wa, yayi murmushi ya latsa hon yace "Anty Aisha Dangusau" ce ta kirani tace ya kamata muje mu sada zumunci, cikin kosawa tace to wai gurin wa,
yace Gurin ""Captain Mus'ab Abdulhameed da Anty Nuwairah Ahmed Shattima"",
zulfah ta fadada fara'arta tace badai na cikin littafin SIRRIN BOYE ba,
sadeeq yace uhumm yess su,
mai gadi ya wangame gate din zulfah cike da murna tace dama anan suke,
wayyo Allah na kana nufin zan gansu kenan, yace a'a bazaki gansu ba hotonsu zaki gani cike da gidan, ta turo baki zatayi magana suka hango Aman da Amal sun fito da gudu sun nufo motarsu,
zulfah ta kasa rufe baki saboda murna ta bude kofar tana kallon twins din da basu wuce shekara 11 ba,
suka rungumeta amal ta karbi daddy zulfah cikin jindadi tabi bayansu tana murnan ganin fuskokin mutanen da ta dade da karanta labarinsu, sadeeq ya fito yace au wucewa zakiyi ki barni to jeki,
ta dawo da sauri tace am sorry plss in na shiga ince musu ni wacece,
ya rike hannunta yace kice sunanki "Zulfa'u Adam" wacce "anty Aisha kurah" bata gama basu labarinki ba har yanzu,
tayi dariya tace nasan zata gama gajen hakurinka ne yasa baka jira ta gama ba ka dauko ni ka kawoni, yajata suka bi bayan su aman dake fada akan daukar daddy,
da sallama suka shiga katafaren parlon gidan, Nuwairah na zaune da tsohon cikinta tana kallo,
can gefe kuma mus'ab ne ke raba Hanan da junior fada akan kayan wasa,
da sauri Nuwairah ta mike tana musu sannu da zuwa, ta rungume zulfah ta jata suka zauna mus'ab ya karaso gurinsu shima yana murmushi suka gaisa da sadeeq sannan suka zauna, hira sukeyi sosai Nuwairah taja zulfah ciki suka cigaba da hirarsu tana ta bata shawarwari akan zamantakewar aure sannan ta hada ta da magunguna masu kyan gaske,
da gudu hanan ta shigo tana ihu kamar wacce aka yankata, Nuwairah ta dafe kanta tace yau na shiga uku, me kuma aka miki,
tace ba anty amal bace taki bani baby in daukeshi,
zulfah tayi murmushi ta janyota tace yi hakuri zan bar miki shi ma duka kina so ko, hanan ta daga kanta tana murmushin jindadi ta fita ta da gudu tana kiran sunan junior ita adole zata fada mishi,
Nuwairah tayi tsaki suka cigaba da hirarsu, saida suka ci abinci sannan suka fara shirin tafiya gurin karfe uku,
kayayyaki ne cike da leda mai aikin Nuwairah ta kai musu mota suka rakosu suna tafe suna hira, mus'ab yace ma Nuwairah kinji bikin barr saleem gobe ne ko,
tace ehh yanzu nakeji in shaa Allahu jibi zamuje abujan muma daga nan sai mu hadu mu kai ziyara gidan su "Marwah da doctor Abdallah,"
zulfah tace gaskiya da naji dadi sosai in muka hadu dukanmu, daga nan sai muje gidansu "barr Abdulmaleek sawaba" saboda in ga kaka,
Nuwairah tayi dariya tace kaka problem Allah ya kaimu yar kanwarmu, kuma ya kara hada kawunan mu,
Ameen suka ce dukkansu sannan suka shiga mota yaran na daga musu hannu suka wuce cike da murnar karrama su da familyn capt Mus'ab sukayi.....

Mrs tijjani shattima...
[12:33PM, 10/02/2016] Aysha Ya'u Kurah: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 7⃣3⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Washe garin daurin aure aka dauki amarya zabba'u aka kaita abuja,
bikine aka yishi na nutsatsun masu ilimi ya kayatar matuka aka dau amare aka kaisu gidajensu,
Karfe hudu bayan an gama budan kai zulfa da sadeeq suka fito suka wuce gidan Anty zarah inda Nuwairah tayi musu kwatance can suka hadu saida suka dan dade acan sannan suka shirya tafiya gidan su MARWAH dake maitama,

Tun kafin su karaso Marwah ke kiran Nuwairah a waya saboda ta kosa suzo, suna karasowa mai gadi ya wangale musu gate din gidan saboda yasan da zuwansu,
a waje suka tarar dasu, suna ganinsu suka karaso gurinsu cike da farin cikin re unioun din da sukayi yau, Abdallah ya mika musu hannu suka gaisa sannan suka shiga ciki,
Marwah ma rugumesu tayi cikin farin ciki ta karbi daddy tace anty Nuwairah ina yaran ko hanan baki taho min da ita ba,
Nuwairah tace wannan fitinaniyar ay da bazata barni in huta ba suna can gurin ummi,
karasawa ciki sukayi cikin farin ciki suka zauna nan da nan aka cike gabansu da kayan dadi,
sunaci suna hirah zulfah tace wai ni anty Marwah ina yaran ne, banga ko daya ba, Marwah tace suna can gurin kaka yau hutu nakeyi,
zulfah tace ay ko yanzu muna gamawa zamuje in gansu dan inason ganin meenal da fatan ta daina wasan ruwa,
abdallah yayi dariya yace ay yanzu ta girma dama gado ne kuma dole yaro sai yayi daga baya kuma ya sakeshi,
Marwah ta harareshi tace me kake nufi,
ya kalli mus'ab da sadeeq yace kunji na kira sunanta,
duk suka kwashe da dariya, Marwah tace wallhy zan rama, nan suka cigaba da hirah har kusan 6 sannan suka shirya suka wuce Gimbiya street, abdallah ya kira abdulmaleek ko yana gida yace eh yanzu ma ya shigo, yace to gamu nan zuwa, cikin farin ciki yace to sai kun karaso,
suna karasawa kowa ya fito a motarshi suka wuce ciki, suna shiga ciki suka tarar gidan a jike ko ina meenal da beebi yar lubna sunata tsalle cikin ruwa,
abdallah ya dafe kanshi yace oh ni wannan gadon ashe bai saki diyata ba har yanzu,
marwah tayi tsaki ko kallonshi batayi ba taja hannun Nuwairah da zulfah dake dariya suka shiga ciki suka barsu a waje,
tun kafin su shiga ciki suke jiyo hayaniya suna murda kofar lubna ta hankada su zata fita kaka na tsaye rike da ludayin miya a hannunta tana masifa tace dan ubanki kizo ki tafi gidanki; haka kawai ke duk kika zo gidan nan sai kin sani magana, marwah ta janyota tana dariya tace wallhy buga mata kaka har yanzu taki ta girma,
kaka ta ajiye ludayin tace yaushe zata girma ta hadu da sahoramin mijin da baya kwaba mata, lubna tace wallyy mijina ba sahorami bane haushin rashi ne dan ba ke kika sameshi ba, abdulmaleek da suka fito tare da haffy yace ohh ya Allah, wai ku bakinku baya gajiya ne,
haffy tayi murmushi ta rungume su zulfah dake tsaye suna dariya tace sannunku da zuwa,
kaka tace baki lale2 wannan jarababbiyar ta hana mu gaisa, lubna tace oho dai naci dubu sai ceto, abdulmaleek ya karasa waje inda abdallah suke tsaye yana ma su meenal fada, ya mika ma su mus'ab da sadeeq hannu ya kalli abdallah yace in dai wadannan yaran ne wallhy bakinka sai ya gaji, abdallah ya mika mishi hannu yace kuma sai sunxo gidan kaka sukeyi saboda sangarta,
suka karasa ciki suka zauna aka gaggaisa cikin farin ciki sunata hirah dasu kaka da baki ya kasa rufuwa sai labarin dariya take basu,
basheer ne ya shigo da sallama shima ya zauna anata hirar dashi kaka nata mishi masifa akan ya dauki jarababbiyar matarshi da mabarnaciyar yarshi su tafi, basheer dai dariya kawai yakeyi saboda ya riga ya saba da jarabar kaka, sai kusan tara suka fara shirin tafiya dan anan sukayi sallar magrib da isha, har waje suka rakosu suna sallama tare da adduar Allah ya barsu tare....

Four years ltr

Zulfah ce driving ta dawo daga skool kanta ciwo sosai yakeyi saboda karatun exams kuma bata samun yin baccin dare,
tunaninta daya yanzu tana shiga gida su daddy da kanwarshi Nour zasu dameta dan ko ta korasu cikin gida gurin su mummy dawo mata sukeyi dukkansu har su waleed kuma so takeyi tayi bacci kafin ta tashi tayi girkin dare,
farouk ne ya fado mata a rai wanda ake shirin bikinshi nan da wata daya, kiranshi tayi ya dauka yace madam ya akayine,
tayi tsaki tace kaidai bari tace yanzu zan dawo skull umara ka taimakeni ka kwashi yarannan dukansu ku fita yawo wallhy bana jin dadi kuma bazasu barni in huta ba,
yayj dariya yace gaskiya kin takurani da yawa amma zanyi anytn 4u tayi dariya tace godiya dubu ango, yayi murmushi ya ajiye wayar ya kwashesu suka fita suna murna sosai,

Sai gab da la'asar ta farka ta shiga bayi tayi alwala tayi sallah taji kanta ya rage ciwo, kitchen ta shiga ta fara sarrafa abinci kala kala,
sai gurin magriba ta gama ta shiryasu ta kimtsa ko ina taje tayi wanka, tana tsaye tana goge kanta da karamin towel sadeeq ya shigo da ruwan sanyi a hannunshi,
rungumeta yayi sosai sannan ya juyota yace babyna ya skool, tayi tsaki ta karkatar da kanta gefe tace boko ba dadi,
ya ajiye ruwan a kan mudubi yace ay dama daurewa akeyi hope exams din da sauki ko, ta gyada mishi kai, yace gud Allah bada saa, tace ameen, wayarshi ta fara kara zainab ta gani akan wayar ta juyar da kanta ta fara kokarin cire jikinta cikin nashi, ya kara matseta sosai ya dauka yace gayu ya akayi ne,
tace fyn marafa kuma kai na jika shuru bayan nagama shirya program din, gashi nan masoya sai kira sukeyi,
yace goshh wallhy sweety na ce ta mantar dani komai amma zamu zo tare yanzun nan,
zee tace zaka sani yanzu da tym ya tafi ne zaka zo, sai dai kayi promisn dina zaku zo gobe,
yace in shaa Allahu tace to Allah ya kaimu, yace ameen sannan sukayi sallama ya kashe wayar,
ya kalli zulfah yace kishina akeyi, ta runtse idonta ta girgiza kanta, yasa hannu yana shafa wuyanta yace karya kikeyi,
ta noke wuyanta ta danne hannunshi tace ni dan Allah ka bari, ya matseta a jikinshi yace bazan bari ba gobe zaki raka ni wani guri, ta noke wuyanta, yayi murmushi yace gulma ko, an fada miki banji labarin da kike bawa anty laila bane,
ya kara rungumeta yace ashe ni dan gata ne ma an dade ana sona tun kafin a ganni, ta kara boye kanta cikin kirjinshi tace wallhy sharri zaka min, labe ka koma kana mana kan jin sirrin mu ko, ya fara goga kanshi cikin gashinta yace na labe din ba gashi najiyo abinda ya kwantar min da hankali ba,
ya dago fuskarta yace Alhamdulillah nagode ma Allah da ya bani mace mai kamala wacce ta hada komai da komai,
tayi murmushi itama tana shafo fuskarshi tace kace mun gode ma Allah dai, sai dai muyi adduar Allah ya barmu tare, Ameen thumma ameen ya fadi hade da yi mata wasu abubuwa masu wuyan fadi,
Haka rayuwar familyn marigayi daddy ta kasance cikin farin ciki da kaunar juna tabbas adduar daddy ta bisu domin kuwa Allah ya fitar mishi da bata gari cikin iyalinshi,
kullum cikin mishi addua suke, haka duk wata sai an sauke alkurani an sadaukar zuwa kabarinshi,
Allah ya jikan dukkan musulman duniya ameen ya Allah...

Tammat bi hamdulillah

Alhamdulillah Allah nagode maka da ka bani iko da damar karasa littafin nan, kurakuren da nayi a ciki Allah ka yafe min su, Allah ka shige mana gaba a dukkan alamuranmu,

Godiya ta musamman ga mijina uban ya'yana Allah ya barmu tare..
Ina muku addu'a a kullum ya'yana abin alfaharina
Nuwairah Shattima
Nour Shattima
Anwar shattima
Allah ya raya min ku kan tafarkin addinin musulunci,

Jinjina gareku masoyana na Facebook da WhatsApp Allah ya bar kauna ina son duk musulmin dake cikin duniyar nan, Allah ya sadamu da alkhairi a ko yaushe kuma ya hada fuskokin mu a aljanna firdausi,

Jinjinar ban girma zuwa gareki Hadiza isah Ameh mrs Jabeer Allah ya barmu tare kawata ya raya mana yaranmu,
sai kuma kawalli Ummu abdool Allah ya barmu tare,

Sannan zan mika godiyata da gaisuwa zuwa ga masoyana wayyo ina ma zan iya kiran sunanku dukkanku, Badiyya, Aneesah, Huris da Aysha dangusau kuzo ku tayani lissafosu dan Allah,
kalmar godiya tayi kadan zuwa ga masu min addu'a wadanda nasani da wanda ban sani ba Sai dai kawai ince Allah yasa aljanna ce makomarmu..

Ga naku godiyar yan uwana masu kaunata dukka yan group dina na
World of hausa novel amma banda NO SHAKING da HANNE CILLARE Allah ya barmu tare yan uwana..

Lovely sisters
Rufaida umar fans
Classic ladies novels
Feenat jafar novels
Hausa novel na Raff mukhtar
Da kuma Hausa novel na dearest Sheedat
Da novel's one
Kai da duk ma sauran groups din ma da ban fada ba Allah ya barmu tare.. ameen

Aysha Ya'u Kurah na muku fatan alkhairi

Mrs tijjani shattima.....

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment