Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

tare da sanah yace Hilal kana duniya, dayan saurayin ya mika mishi hannu yace ina nan Hafiz 2dys ka buya, rabona da kai zai kai 3yrs fa, hafiz yace hakane kam ya kake ya su baba, hilal yace suna nan lafiya tare muke dashi ma suna ciki shi da abokinshi,
ya kalli sanah dake makale jikin hafiz tana kallonshi, yace sannu ko yammata, tayi fari da ido tace yauwa,
hilal yace hafiz sauri nakeyi zanje in dauko ma su baba abinci a gida bani numbrka, yace to ya karbi wayar ya sa mishi numbr,
yace ma sanah ta jirashi ya rakashi****

Hilal ya kalle shi da suka fita yace hafiz kana nan da neman mata har yanzu, hafiz yayi dariya yace sune ginshikin rayuwa mutumina,
wannan ma yau na hadu da ita, dama ina tunanin kwana ni daya a hotel kasan a kano nake yanzu, hilal yace Allah ya shirya to ai gara ka riketa ka aureta dan ta hadu sosai, hafiz yayi tsaki yace wannan ba ta aure bace mutumina macen da daga haduwa ta yarda da kai ai ba irinsu ake aure ba, hilal yayi murmushi yace ka dai ji tsoron Allah ni bari in wuce sai na kiraka, hafiz yace okk sai na jika abokina,,,

Satin zulfa'u uku a gidansu mummy, fatarta ta murje saboda mayukan da take shafawa, ta koyi komai na gidan cikin kankanin lokaci, kullum ita ke karawa mummy karatun qur'ani da littafai, haka wasu ayukan girki tare sukeyi da laila,,

Wata ranar jumma'a suna tsaye dukkansu a kitchen suna girkin jumma'a kamar yadda aka saba yi a gidan, kowa da aikin da yakeyi suna hira, jalila ta kalli zulfah dake haďa salad,
cikin tsokana tace anty laila kinga matar yaya abba an dan fara murjewa ji yadda ta daddage tana hada salad,
zulfa tayi murmushi bata kalleta ba dan ta saba da tsokanar jalila, anty laila tace kedai jalila baki da kunya walhy,, matar yayan naki kike ma iskanci, bari in gama foiln zaki sani dan da mummy zan hada ki, ko kuma in kira abban in fada mishi,
jalila tace yauwa anty yaya abba na kiranki kuwa,
tace a'a kuma ko na kirashi ma baya ďauka,
jiya ma abban ayda ke min korafin baya kiranshi, jalila tace umm ko mummy baya kira kuma kinsan bai san maganar auren nan ba,
laila tace eh ina ganin akwai abin da ya tsareshi ne,
jalila ta tabe baki tace babu wani abun da ya tsare shi ay yana kiran anty amarya, laila tace kai jalila bansan sharri, jalila tace Allah anty ba sharri bane, naga missd call dinshi har 7 a wayarta, anty laila tayi jugumm sannan tace to Allah ya kyauta amma baki fada ma mummy ba ko, tace eh ban fada mata ba, tace to kiyi shuru da bakinki,,
zulfah ta mika ma anty laila salad din ta kama wani aikin, anty laila ta kalleta tace baki gajiya ne ke, kije kiyi wanka fatsin zata karasa gyara kitchen din, zulfah tace to anty, ta wanke hannunta ta kalli jalila dake mata wani irin kallon tsokana kasa2 tana murmushi, ta yarfa mata ruwan hannunta tace kyaji dashi ta fita da gudu, jalila ta kwashe da dariya tana goge fuskarta tace lallai yarinyar nan taci abinci, laila tace ay tamin dai2, jalila tace zan rama ne ay tasan hali na,

Zulfah na fita daga kitchen tayi karo sosai da mutum wayar dake hannunshi ta faďi,,
da sauri taja da baya jikinta ya fara rawa ta dago kai ta kalleshi yana tsaye shima kallonta yakeyi sanye yake da red top da ta karbi fatar jikinshi gashin kanshi a kwance da ganinshi kasan hutu ya gama ratsa shi kamarshi daya da Nurain sai dai yafi nurain kyau,
ta tsuguna da sauri ta dauki wayar tace dan Allah kayi hakuri wallhy bansani ba, bai amsa mata ba ya mika hannu ya karba, ta bi ta gefenshi ta wuce ya bita da kallo har ta bace ma ganinshi sannan yayi ajiyar zuciya ya shiga kitchen ......

Mrs tijjani shattima..
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 1⃣7⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Laila ce ta fara ganinshi ta fadada fara'arta tace farouk yaushe ka dawo, yace yanzun nan anty,
ya rankwashi kan jalila dake shan fruit salad yace acici,
ta ajiye spoon din ta rungumeshi tace yaya farouk oyoyo,
shine baka fada azo a dauke ka ba,
ya harareta yace sai kace wani yaro,
anty ina mummyna, anty laila tace suna skool nasan yanzu zaka gansu,
sannu dan autan mijin yau kai zanyi yayi fadi duk abinda kakeso in kawo maka, yayi dariya yace I trust u anty ki kawo min kome kuka dafa,
jalila cikin murna tace to broo,
ta kwaso ragowar kayan da basu jera a dining ba ta jera, sannan ta zuba mishi abinci tana mishi hira dan taji dadin dawowarshi,
yace to parrot barni in ci abinci,
ta turo baki tace kai yaya dan ma kaga ina murna ka dawo shine kake min wulakanci ko, yace sorry sis surutunki ne yayi yawa,
tace to shikenan da naso in baka labarai amma na fasa, yace yi hakuri kanwata zauna ki tayani cin abinci in mun gama sai ki bani ko,
ta zauna ta zuba abinci suka ci tare tana mishi hira..

Zulfah na daki tsoro ya hanata fitowa duk tunaninta shine wanda aka daura mata aure dashi, afrah ce ta shigo dakin ta tsaya gabanta tace antie zage min zip mummy tana sallah kuma anty jalila tace bazata zage min ba saboda naki bata ice cream din da daddyn ayda ya siyo mana,
zulfah ta janyota ta zage mata zip tace me yasa kika hanata rowa babu kyau,
, afrah tace ba kowa yasha nashi muna bacci ba, ni bazan bata nawa ba, zulfa tace to muje in miki wanka sai ki kira amrah ma in mata ko,
afrah tace ay anty jalila ta mata saboda ita ta bata nata,
zulfah tayi dariya tace to muje in miki, suka shiga bayin ta mata wanka suka fito ta shafa mata mai, tace je ki dakko kayanki in sa miki,
ta fita da gudu taje daki ta dakko kayanta da mummy ta fito musu dashi,
tama jalila dake ma amrah kwalliya gwalo ta ruga da gudu jalila tabi bayanta itama da gudu,
ihuu afrah ta dinga yi saboda jalila ta kusa kamota, a tare zulfah da farouk suka fito a firgice sun dauka wani abun ne ya sameta, jikin zulfa afrah ta fada tana maida numfashi tana dariya,
jalila ta karaso ta daga hannu zata kai mata duka,
farouk dake tsaye yana kallon zulfah ya daka mata tsawa, yace baki da hankali ne, me ta miki,
jalila tace wallhy yaya yarinyar nan ta raina ni,
da ta miki me ya fadi yana kallonta,.
afrah tayi saurin guduwa bayanshi tace (yaya umara sunan da mummy ke kiranshi suma haka suke kiranshi ita da amrah)
babu abinda na mata wai dan tace in tsammata ice cream naki shine taki min wanka kuma ta biyoni zata duke ni,
jalila tace wallhy karya take min gwalo fa ta min ni sa'arta ce da zata min gwalo,
farouk yace kusan sa'arta dince ke tunda bakinki ya iya kwadayin abun yara komai kika gani sai kinsha,,
ta turo baki kamar xatayi kuka tace wallhy yau Allah ne kadai zai kwaceki,
afrah ta kara mata gwalo tana dariya,
jalila tace yaya kana ganin abinda takemin ko wallahy yau sai naji ma yarinyar nan ciwo, ta wuce daki ranta a bace,
zulfah ta dauki kayan afrah tace zo muje in shiryaki, afrah ta rugo gurin zulfah suka wuce daki suka bar farouk baki sake yana kallonta,
wai wacece wannan, ya fadi a fili, yarinyar is so cute, ya daga kafadunshi ya juya daki yana siffanta yanayin zulfah a zuciyarshi,,

Da safe bayan ya dawo sallar asuba ya shiga dakin mummy, zaune ya samesu tare da zulfa'u tana kara ma mummy karatu,
gefensu ya zauna yana sauraron kira'arta yana bin karatun idonshi a lumshe,
sai da suka idar sannan ya bude idonshi ya kalli zulfah da ke kwashe qur'anai, ta sunkuya tace ina kwana,
yace lafiya lau malama, ta ajiye qur'anan gurin da suke ta fita,
ya dawo kusa da mummy yace ina kwana mummy,
tace lafy lau umara ya gajiyar hanya, yace tabi lafiya mummy, nan suka fara hirar skool dinshi, har gurin karfe takwas suna hira, har ya tashi zai tafi ya dawo yace wai mummy a ina kika samo wannan kyakykyawar malamar, mummy tayi dariya tace malama ce amma tá gida,
ya zauna yace ban gane ba, tace Amaryar Abba ce,
gaban farouk ya fadi sosai yace wane abban, mummy tace na nan gidan yayanka, abinda yasa bamu fada muku ba saboda muna son muyi muku surprise, ko shi abban bai sani ba,
farouk yayi ajiyar zuciya yace gaskiya yaya abba ya dace sosai,
Allah ya basu zaman lafiya, mummy ta bude murya cikin farin ciki tace ameen umara cika daji,
yayi murmushi ya tashi ya fita jikinshi a sanyaye.....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: [3:40PM, 20/01/2016] Mrs Tijjani shattima💏: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 1⃣8⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Dakinshi ya wuce ya kwanta yana ta juyi,
Astaghfirullah...
Astagfirullah......
Astagfirullah......
Kalmar da ya dinga fadi kenan a bayyane,
saboda farat daya zuciyarshi ta kamu da son macen da ta haramta a gareshi har abada,,
ya dinga godiya ga Allah da yasa ya sani da wuri,
tabbas kallo ďaya yayi mata yaji wani abu game da ita,
a kallon da yayi mata na biyu zuciyarshi ta fara kitsa mishi wani sabon al'amari mai wuyar faďuwa,
hannunshi ya daga sama yace Allah na gode maka daka sanar dani wacece ita a kallon da nayi mata na uku,
Ya lumshe idonshi a hankali yana neman tsari daga sharrin shaidan dan yasan duk aikinshi ne wannan, cikin ikon Allah har bacci yayi gaba dashi....

Kuka sosai anty amarya keyi a gaban daddy,
duk wanda ya ganta a wannan lokacin zai dauka daga can cikin zuciyarta take kukan,
hankalin daddy ya tashi matuka,
yace subhanalhi hadiza lafiya me ya faru, cikin muryar kuka tace babu komai,
da sauri yace kamar yaya babu komai, fada min abinda ke faruwa mana,
ta kara narke murya tace banason ace na fara kawo kara,
duk abinda akeyi min a cikin gidan nan ina shanye wa na dauki yaya tamkar ita ta haifeni shiyasa kome zatayi min bana daukarshi da zafi, amma bazan jure gaba da ita ba,
ina matukar shan wahala saboda rashin kulani da bata yi kwata2 bata amsa gaisuwata,
haka ta hana su jalila gaisheni,
yau kwanan farouk hudu a gidan nan ko sau daya bai je inda nake ba bare yayi tunanin gaisheni, dan Allah ka bata hakuri in nayi ma wani l-a-i-f-i ta karasa fadi tana sheshshekar kuka kamar da gaske,
ran daddy ya baci sosai yace ita Aishan ce bata kulaki,
anty amarya ta gyada kai tana share hawaye, yace me kikayi mata to,
cikin sanyin murya tace babu abinda na mata,,
daddy ya mike a fusace zai fita tayi maza ta riko shi,
tace kayi hakuri daddy bazan juri inga kana ma yaya fada ba dan Allah karka mata magana zata ce kararta na kawo gurinka kuma zai kara zame mana matsala, nidai inason ka lura da kanka idan kaga yadda muke tafiyar da alamuran mu sai kayi mata magana,
amna yanzu in ka sameta ay komai baci zaiyi,
Daddy yayi ajiyar zuciya yace wallhy da kin barni naje na sameta, suma su farouk din sai naci mutuncinsu,
anty amarya tace kayi hakuri yara ne,
kuma ni duk abinda zasu min bazan taba rikeshi ba saboda son da nake musu ko da dan da na haifa banajin zan iya mishi irinshi,
ta dangwabe a jikinshi tace ina matukar kaunar jininka fiye da yadda nakeson kaina ma,
dadi daddy yaji har cikin ranshi ya rungumota sosai yana rarrashinta nan ta kasheshi da kissarta mai zafi wacce take ma mummy zagon kasa da ita....

Mrs tijjani shattima....
[7:12PM, 20/01/2016] Mrs Tijjani shattima💏: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 1⃣9⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Zaune suke kewaye da mummy a parlor bayan isha'i,
farouk na zaune yana latsa waya,
jalila da zulfah suna duba wani littafin adduo'i suna musu akanshi,
Anty amarya ta fito cikin daguwar riga mai kyau da tsari,
ta gabansu tazo ta wuce duk suka gaisheta daya bayan daya,
ta amsa tana yatsina mummy ko kallon inda take batayi ba,
fridge din palour ta bude ta dakko juice ta koma daki,

tana jin hon ďin motar daddy tayi maza ta mike ta kara gyara jikinta ta feshe jikinta da ni'imtaccen turare,
sai da taji ya shigo sannan ta fito tana tafiyar hawainiya,
ta karaso cikin parlon ta dan durkusa tace sannu yaya,
mummy da mamaki ya isheta ko kallon inda take batayi ba,
daddy ya lura tsaff da mummy sannan yabi dukka yaran da kallo dan baiji sun gaisheta ba,
haba nan da nan ranshi ya baci sosai ya kalli mummy da ta haďe girar sama da ta kasa yace Aisha bakiji ana gaisheki bane,
mummy tace banji ba ta cigaba da kallon tv,
daddy ya kalli farouk yace kai dan ubanka baka iya gaisuwa bane,
cikin rashin fahimta yace dad-- bai bari ya karasa ba ya shiga surfa musu ruwan bala'i anty amarya na gefenshi tana kukan munafurci tana bashi hakuri,
ya kalli zulfah da kanta ke sukunye yace harda ke zuwan jiya har an koya miki rashin kunya an nuna miki karki daraja matata to wallhi babu wanda ya isa ya taka min mata ina kallo haka ya dinga masifa mummy bata kalli inda yake ba bare tasan abinda yake fadi,
zagin da taji anty amarya tayi ma zulfah ne yasata mikewa a fusace, kuma dama tayi hakan ne dan ta harzuka mummy,
Cikin fushi mummy ta janyo zulfah dake rakube a kusa da jalila duk kuka sukeyi, tace Hadiza kika mata ce yar matsiyata,
kinsan waye matsiyaci,
to ki bude kunnenki dakyau kijini,,
matsiyaci shine wanda duk abinda ake bashi baya isar shi sai ya hada da haram,
matsayaci shine wanda yake siyar da mutuncinshi dan ya samu kudi a kirashi da mai arziki,
matsiyaci shine mai arzikin dake nuna halin tsiya kamar yadda kikeyi,
kuma yanada daga cikin siffofin matsiyaci mutum ya zama munafuki algungumi kamar yadda kike,
sai kiyi alkalanci tsakanin ke da ita waye matsiyaci?
kinga wannan yarinyar, ta fi min ke da duk wani wanda ya rabeki,
haushi kikeji saboda na aurawa abba ita ko, to bari kiji ko bayan raina jinina bazai taba haduwa da jinin fasikai irin---- wawan marin da daddy ya dauketa dashi ne ya hanata karasa maganar da takeyi, farouk ya mike da sauri jikinshi na rawa ya fita daga gidan gaba daya idonshi jawur,
daddy yace a gabana kike fifita wata banza akan matata,
a gabana kike kiran matata fasika, lallai Aisha kin cika marar mutunci me manta alkhairi, duk irin biyayyar da hadiza take miki baki gani, yanzu dama akan wannan yarinyar gidana yake neman kamawa wuta, wallhi badan nasan darajar aure ba da a yau sai yarinyar nan ta bar min gidana, amma kisa a ranki, duk ranar da abba ya dawo yace baya son yarinyar nan, wallhy tallahi zan goya mishi baya dari bisa dari ya auri wacce yakeso,
dan kinga na kyaleki kina yadda kikeso da ya'yana to komai yazo karshe,
ya cigaba da masifarshi mummy dake tsaye rike da kunci hawaye na zuba akansu ta juya ta barshi a gurin yanata masifa, daki suka wuce ita da jalila da zulfah, dukkansu kuka sukeyi,,

Daddy ya zauna bayan yayi masifar mai isarshi muryarshi har ta fara dashewa saboda bai iya masifar ba, ya shiga rarrashin anty amarya dake kuka sosai, yace ya isa hadiza,
cikin kuka ta tureshi tace me yasa zaka mareta,
wallhy zafin marin a jikina najishi, wata rana zata gane kuskurenta tasan ni mai kaunarta ce, amma yanxu ka kara goga min bakin jini,
yaya ta kasa gane irin son da nake mata, amma da sannu zata gane ""ta kara rushewa da kuka,
ya dinga rarrashinta yanajin tausayinta a zuciyarshi dan yasan tana kaunarsu dukkansu har cikin ranta,
to me ya canza Aisha ta tsaneta lokaci daya,
me ya canzata take neman rushe farin cikin gidanshi magana yakeyi a zuci baisan ta fito ba,
anty amarya tayi saurin mikewa tace Zulfa'u,
shigowar Zulfa'u gidan nan yana neman rusa da farin cikin daya ginu lokaci mai tsaho,
irin yaran nan burinsu su auri mutum ya mutu suci gado amma yaya ta kasa ganewa,
ni tausayi ma take bani saboda makashinka yana jikinta,,
daddy ya gyada kanshi ya daura duk akalar tunaninshi akan Zulfa'u baiwar Allah

(kissa tafi magani sunan wani littafi)

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 2⃣0⃣
By Aysha Ya'u Kurah

A daren ranar bacci ya kauracewa idanuwan bayin Allahn musamman zulfah dake kuka kamar ranta zai fita,
daddy kuwa yana can gurin anty amarya itama kukan takeyi yana rarrashinta sam baiyi tunanin mummy ba dan gani yakeyi duk laifin nata ne,

Haka gidan ya kasance har tsawon kwana hudu mummy sam bata fitowa daga ďaki,
bata kaunar abinda zai haďata da daddy bare anty amarya,
Kullum nurain da farouk ke zama su tausheta da kalamai masu dadi, abinci ma a daki suke zama suci duk da ba wani cin kirki suke ma abincin ba,

alamarin mummy ya fara damun daddy dan yasan halinta sarai in tana fushi bata ki sufi shekara a haka ba,
ranar kwana na biyar ne daddy ya yanke shawarar zuwa ya sameta su sasanta kansu dan Aisha itace shi itace rayuwarshi baki ďaya duk wani ci gaba da yasamu a sanadiyyarta ne,

Zaune ya sameta a kan dadduma tana karatu,,
jalila da zulfah suka gaisheshi suka fita da sauri,
a gefenta ya zauna yana jiran ta idar,
, ya kusa awa zaune bata idar ba yasan da gayya ta kara janyo sura mai tsaho,
rufe al Qur'anin yayi ya daukeshi a gabanta,
bata ďago kai ta kalleshi ba ta cigaba da karatunta da ka,
cikin muryar lallashi yace kiyi hakuri Aisha, dan Allah ki saurareni, ko kallon inda yake batayi ba ta fara kokarin mikewa, rike hannunta yayi yace mu ba yara bane Aisha,
cikin fushi tace kace ni ba yarinya bace, dan kai yarone karami ma, ka sakeni kar in fada maka maganar da zata sa Allahna yayi fushi dani,
banason hakurinka ka koma can gurin matarka ka cigaba da rarrashinta,
janyota jikinshi yayi sosai yana murmushi yace kece matata uwar ya'yana,
kece silar cigaban Hasheem,
ke kika zauna dani daga ba kowa ba har na zama wani,
bai kamata mu dinga samun sabani ba in kikayi la'akari da shekarun da muka dauka muna tare,
kinsan duk duniya bani da wata sama da ke,
ta katseshi da sauri tace kanada hadiza, dan hadiza tafimu daraja dani da ya'yana tunda har akanta zaka iya daukar hannu ka mareni,
ka bani mamaki hashimu, babu ranar da zan manta wannan cin mutuncin,
Cikin damuwa yace ki zama mai yafiya Aisha, so nakeyi gidana ya dauwama cikin farin ciki, banason yarana su raina hadiza dan zataga kamar dan bata haihu bane,
in zakuyi fada kuyi tsakaninku amma banason yara su dinga shiga,
cikin fushi mummy tace wai wane fada kake magana,,
yace ki fadamin me ya hadaki da hadiza da bakya kulata, ko ta gaisheki baki amsawa, meyasa su farouk basa gaisheta,
mamaki ya hana mummy magana kallonshi kawai ta tsaya yi,
ya cigaba da cewa kinga ko ranar a gabana ta gaisheki baki amsa ba, kuma babu ko daya a cikin yaran nan da ya gaisheta, kinga bazanji dadi ba,
kuma naga ba haka kuka saba ba, tun zuwan yarin--- mummy da ta gama gano makirci ne shiryayye ta katseshi da sauri tace dakata kar ka kira min zulfa cikin maganata,
naji na dauki laifi kuma yara ma zan musu fada,
in shaa Allahu komai zai daidaita,
cikin jindadi daddy yace kin hakura kenan, tayi murmushi tace ay kasan ni da kai bama iya fushi da juna kuma wanda ya shiga tsakanin mu shi zaiji kunya,,
yayi dariyar jindadi yace kwarai kuwa Aisha abin alfaharina,,
nan suka cigaba da hirarsu cikin hikima ta cire mishi duk wata damuwa da kokwanton da yake da shi akan zamansu da zulfah,
ya dade a dakinta kafin ya fita ta mishi alkawarin yanxu zata fito ta sameshi,
Dariya tayi da gama nazarin duk kalaman daddy,
tace kinyi kuskure hadiza,
zaki gane kissar bariki kadai kika iya, yanzu ne za'a fito salon kissa kala2 muga wanda zai ci riba....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 2⃣1⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Sati ďaya bayan wucewar wannan, mummy a gaban daddy tana nuna ma anty amarya kulawa ta musamman wacce take bata mamaki ita kanta dan in daddy baya nan ko A bata ce mata,
duk yadda taso ta kara samun wani gurbi na haddasa fitina mummy ta toshe shi, kullum ran anty amarya a bace yake musamman yadda taga mummy da daddy nayi a gabanta,

Zaune take a daki tana tufka da warwara dan da a tunaninta ta samo kan daddy saura abba yanzu gashi kwabarta tayi ruwa, tunanin hanyoyin da zata kara bi cikin hikima ba tare da daddy ya gano ta ba takeyi,
wayar daddy ce ta shigo wayarta ta daga bayan ta gama hararar wayar,
a hankali take magana kamar wacce taci kuka ta koshi, daddy yace lafiya hadiza,
ta kara kwantar da murya tace lafy lau, daddy bayason yawan zurfafa bincike saboda bayason jin abinda ke faruwa har ya dame shi ko ya harzukashi ya aikata ba dai2 ba, dan haka yace to alhamdulillah tunda lafiya lau,
yau zan dawo na kira wayar Aisha bata dauka ba dan Allah kice tayi min danwake da kunun gyaďa dan zan kashe wayata yanzu ne,
anty amarya tace to zan fada mata, sukayi sallama ta kashe wayar, kwanciya tayi a kan gado tana dariyar mugunta dan tasan ya tsani yace ayi mishi abinci aki yi musamman danwake, ta riga ta gama haďa plan dinta ta dinga murmushi bacin rai ya ragu sosai a zuciyarta..

Farouk tsaye a kitchen yana hira da su zulfa dake kwashe tuwo jalila na fere dankali dan bata cin tuwo, cikin tsokana yace amaryar yaya ni fa bana cin tuwo,
tayi murmushi tace to me kake ci,
jalila tace wahala kawai zai baki dan yanzu zaice danwake da kunun gyada daddy ya koya musu cin danwake na tsaneshi walhy tayi tsaki ta cigaba da fere dankali,
farouk yace ina ruwanki ko kinji na fadi abin da nakeso, nidai bazanci tuwo ba kuma bazanci dankali ba, asan yadda za'ayi dani ya fadi kamar karamin yaro,
zulfah tayi dariya sosai tace to kayi hakuri yanzu zanyi maka abinda kakeso, yayi murmushi ya kalleta yace wasa nake miki ki dafa min ko indomie ne dan nasan kin gaji, tace kai dai jeka zanyi maka abinda kake so,
yaji dadi sosai dan ya dade baici danwake ba, yace to amma karki sha wahalar yin kun--- kai dai jeka tunda yi maka za'ayi bamason iyayi jalila tafadi tana dariya, yace kin raina ni fa jalila wallhy zan murde shegen bakin nan naki, ya kalli zulfah dake daura ruwan zafi yace zanje u/dosa in dawo kinji tace to adawo lafiya ta wuce store ta debo flour, cikin mintuna talatin ta gama danwaken da kunun gyadan saukinta ma akwai nikakken gyada irin na maiduguri a fridge,
a cooler tasa danwaken ta diban mishi miyar alayyahu da yaji kayan ciki da naman rago, ta zuba kunun a flask ta deban ma amrah da afrah dan suma suna son kunun gyada,
Mummy ta kalleta da ta kai ma su afrah tace kunu kika dama, tace eh yaya farouk yace a dama mishi, tace lallai kina shagwaba yaran nan, laila ta baki kewa da tare zakuyi sannu kinji Allah ya miki albarka ameen tace cikin jin dadi ta fita ta koma kitchen ta tadda jalila na shan kunu, tana ganinta ta ajiye kopin da sauri tace ko iya damawa ma bakiyi ba da kyar na iya shanye wannan,
zulfah ta kure ta ido tace ance dole kisha ne, ko
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment