Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ina a gidan nan ban ganshi ba kuma na duba jakar da yake tafiya da ita duk basa nan,
anty amarya tace yanzu kika tashi kika ce, wace matar aurece mai neman martaba a gurin mijinta zata kai har sha biyu tana bacci,
ashe sanah baki ji fadan da nayi miki ba, bazaki taba canzawa ba dan haka makomarki wallhy, karki kara nemana tunda kin maida ni mutuniyar banza ta kashe wayar ranta a bace,
ta mike ta wuce kitchen tana mita a zuciyarta dan sanah tana neman ta wargaza mata plans dinta gashi har yanzu babu labarin daukar ciki bare har ta samu dan da zai zame musu garkuwa,
taja tsaki ta bude fridge ta kwankaďi ruwan sanyi ko hankalinta zai kwanta...

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: [20:09, 31/01/2016] Aysha Ya'u Kurah: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 4⃣5⃣
BY Aysha Ya'u Kurah

Zulfa'u zaune a daki ita da jalila suna duba prizes din da ta samu ranar speech dinsu, suka dinga budesu cikin nishadi suna hirah, gift din da uncle majeed ya aiko a bata ta bude cards ne da turaruka sai wata guntuwar letter, da sauri jalila ta dauki letter tana dariya ta bude, ta karanta, kai ta girgiza cikin tausayinshi da ta gama karantawa, ta kalli zulfa dake karanta cards tace uncle majeed yasan kinada aure ne, zulfa ta ajiye cards din tace a'a, jalila tace ya akayi ya sani, gashi karanta, wai yana miki fatan alkhairi a rayuwar aurenki, zulfah ta karba ta karanta a zuciyarta tace to waye ya fada mishi, kenan wannan shine dalilin canjin da yayi mata har suka gama exams baya ko bari su hadu, jalila ta katse mata tunanin da takeyi tace Allah sarki majeed ba tun yau nasan ya kamu da sonki ba, tun ranar inter house na dinga lura da yadda yake miki, walhy badan ke matar aure bace da na shige mishi gaba saboda sai macen dake very lucky ita zata iya sace zuciyar irin su, zulfah jikinta yayi sanyi a zuciyarta tace aure ko so called aure, ita yanzu bata daukar kanta macen aure walhy badan tana ganin darajar mummy ba da ta nemi mummy tasa ya sauwake mata itama tayi rayuwarta ta zabi wanda zai sota itama ta soshi, wayar jalila ita ta katse mata zancen zucin da takeyi, jalila tayi murmushi ta dauki wayar ta shiga hira da saurayinta wanda aka sa musu rana tare, sai da ta kusa minti goma tana waya sannan ta kashe ta kalli zulfah da ke kara kallon letter, ta fisge tace haramun yarinya, kina tunanin wani namiji kuma kinada miji, gara ma muje mu kwanta saboda gobe da wuri ishaq zaizo mu tafi rabon I.v da ashoebi, zulfah ta tattare kayanta jikinta a sanyaye ta zuba cikin wardrbe, sannan ta kwanta tana tunane tunane aranta,

Watan sadeeq biyu bai waiwaiyi 9ja ba,
daga ka ganshi kasan yana cikin matsananciyar damuwa, ya rame sosai saidai yayi fresh fatarshi ta kara haske, baya waya da kowa a gida sai daddy da yayi ma karyar wasu takardu yaje amsowa,
mummy ma ta dan damu da rashin sadeeq,
hankalinta kan kwanta ne in daddy yace mata suna waya,

Sanah kuwa ko a jikinta dan harka ce ta bude mata na tara kawaye da maza abokan harkarta, ko tunanin sadeeq ma batayi bare tayi kewarshi tunda ta samu wadanda take ganin sun fishi iya harka, (wa iyazubillah)

A cikin satin ne yaji gaba daya bazai iya cigaba da zaman dubai ba,
abinda yakeji game da Zulfa'u ya karu matuka a zuciyarshi fiye da kwanakin baya, tunanin da ke hanashi komawa bai wuce abinda zai ce ma mummy ba,
yasan tana kan bakarta na sai ya saki zulfa,
dafe kanshi yayi idonshi ya ciko da kwalla yace zai hakura kawai ya rubuta mata sakin ya bata ko da kuwa hakan zai zama ajalinshi,
dan bazai kara tafiya ko ina ba kuma bazai kara nunawa mummy bazai rubuta ba saboda kar su ga kamar sonta yakeyi, shi kuwa a ganinshi ba sonta yakeyi ba kawai dai zuciyarshi ce ke matukar bashi wahala akan tunaninta,

Karfe 8 na dare ya isa gida dan yaso ya kwana a abuja saboda dare amma sam zuciyarshi taki bashi hadin kai,
a bude ya tarar da kofar parlon dan haka ya shiga ya rufo kofar ya wuce dakinshi ba tare da ya kalli dakin sanah ba,
sai da yayi wanka sannan ya fito ya shiga dakin sanah, kwance ya sameta cikin bargo kanta a ya mutse,
tana ganinshi ta mike zaune daure da zanin gado a kirjinta, zaro ido tayi cikin firgici tace yaushe ka dawo, ya harareta ba tare da yace mata komai ba ya juya saboda wani irin wari da yakeji a dakin,
ta mike da sauri ta fada bayin ta samu Nasir dake wankan tsarki tace shikenan mun shiga tara ma ba uku ba nasir,
yace lafiya me ya faru, tace shi ne ya dawo, yace shi wa,? tace sadeeq mana, ya wurgar da sosan hannunshi yace wayyo Allah na, saida nace miki muje hotel kika ki, gashi yanzu kin sani cikin matsalar da zata iya shafar career ta, tace kai career ka kakeji ni da aure na zai mutu fa,
kasan yadda nakeson wannan auren kuwa, nasir ya harareta zaiyi magana muryar sadeeq ta hana shi, kwala kiran sanah yakeyi kamar zai tsaga gidan, da gudu ta fito tace ma nasir ya sa key a kofar,
towel ta daura ta fito parlon tayi hanyar kitchen ta ganshi tsaye fuskar nan a hade kamar hadari, ta tsaya a gabanshi jikinta na rawa tace gani,
ya harareta yace kalli kitchen dinnan, yanzu ke tsakaninki da Allah zaki iya cin abinda ya fito a kitchen dinnan, wannan wace irin kazanta ce kitchen sai wari yakeyi abinci sun fara rubewa,
kalli,, ya fara bude kulolin yana nuna mata, wani irin kara yayi da ya bude wata kular amala da ta fara tsutsotsi,
fita yayi a kitchen din yana masifa kamar zai ari baki,
ya dauki key din motarshi yace wallhy taallhi in na dawo baki gama gyaran kitchen din nan da parlo ba wallhy sai dai ki nemi wani gurin ki kwana amma ba nan ba, kazama kawai, ya fita yana tsaki hade da tsirtar da miyau,
Ajiyar zuciya sanah tayi ta koma daki tace ma nasir ya shirya ya tafi da sauri tunda sadeeq ya fita,
da sauri ya gama sa kaya ya fita har yana karo da kofa,
saida ya fita sannan ta koma kitchen ta tattara duk kulolin da abinci ya rube tana yatsina fuska ta fita ta zubar dasu a cewarta zata siyo wasu gobe dan bazata iya sa hannu a cikin kulolin ba,
ta wahala sosai gurin gyaran kitchen da parlon duk da haka bai bada wani qamshi mai dadi ba haka ta wuce bayi tayi wanka,,

Sadeeq gidansu ya nufa ranshi na baci da irin kazantar sanah, har ciki ya shigo da motarshi yayi parking, daga cikin mota ya hango farouk da zulfah tsaye a hanyar shiga parlor sai hira sukeyi tana dariya harda kyakyatawa,
a hankali ya fito daga motar ya kasa dauke idonshi a kansu zuciyarshi na bugawa sosai saboda ta hango abinda take tunani dare da rana,
farouk ne ya fara ganinshi yace yaya abba ya matso kusa dashi yana murmushi yace yaushe ka dawo, sadeeq idonshi na kan zulfah da ta dukar da kanta gashinta da yasha ribbons ya kwanta a gefen wuyanta yace yanzu na dawo farouk,
welcm farouk yace sannan ya kalli zulfah yace bari in shiga in fito,
ta dago kanta tace to, ta kalli sadeeq tace ina wuni,
ya amsa yana tafiya ciki kamar baya son amsawa, tabe bakinta tayi saboda kiyayyarshi yanzu ta daina damunta tunda itama ta daina jin masifaffen sonshi da take kiranshi da kaddara,

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: Mrs tijjani shattima...
[20:20, 31/01/2016] Aysha Ya'u Kurah: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 4⃣6⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Cikin faduwar gaba sadeeq ya karasa cikin parlon ya tsuguna ya gaisar da su mummy, mummy da anty amarya suka amsa a tare daddy yace yaushe ka shigo, sadeeq yace yanzu daddy ina wuni, lafiya lau daddy yace, sannan yace Allah yasa ka samu takardun,
sadeeq ya sosa keya yace a'a zan dai koma in an gama kammalawa,
yace to madallah, suna dan hira sadeeq na satan kallon mummy ko zatayi mishi maganar zulfah, har ya gama zamanshi yaci abinci bata ce mishi komai game da zulfah ba,
shi kam hankalinshi ya kwanta dan ya dauka ta hakura ne, sai aftr 10 ya bar gidan cike da farin ciki...

an fara bikin "jalila da captain ishaq tambuwal" kwana biyu da dawowar sadeeq,
tsaftataccen biki akeyi sosai na masu nairah, anyi kamu ranar thursdy,
ranar friday da xa ayi "sword crossing" tun safe suke preparation ankon su material army green da maroon head,
wani irin dinki akayi musu iri daya ita da zabba'u kanwar hilal saboda sune manyan kawaye,
suna zaune suna cin abinci farouk na gefensu shima abincin yakeci gidan cike yake da baki,
zabba'u ce ta shigo da silk dinsu a hannunta ta zauna tana maida numfashi tace dakyar ya dawo ya bani head dinnan wallahy, jalila tace ay yaya hilal sai a slow shi a sanshi ma wai kar ayi wasu kide2, zabba'u tasa hannu a abincin tace rabu dashi dalla auren zamani ay dole sai mun chashe ko yaya farouk,
ya mike yace ba ruwana karku sani a ciki mudai yan zuwa kallo ne,
zulfah ta harareshi tace kallon ma kar ku je tunda duk daya ne ay, yayi murmushi yace in dai kawar nan taki xata zo to babu abinda zai hanani zuwa,
jalila ta kwashe da dariya tace wai yaya farouk da gaske kake san rolex kakeyi,
yace ban sani ba, ya fita suka kwashe da dariya zabba'u tace su umaran mummy an girma,
zulfah tace lallai ma, to ke da haka kike, ku kyale min angona ya sakata ya wala, sukayi dariya jalila zatayi magana sukaji karar wayarshi a gurin da ya tashi,
zulfah ta kalli wayar tace manta ta yayi bari in kai mishi,
ta mike da sauri dan kar wayar ta tsinke, kofar dakin ta tura hade da sallama tace gashi da sauri kiranka akeyi,
tasa mishi a kunne tace na riga nayi picking,
shurun da taji ne yasata kallonshi da kyau ta firgita dan kusan kaya iri dayane a jikinsu na farouk milk wannan white,
ta mudubi ta kalleshi ta saki wayar lokacin da suka hada ido, ahankali ta fara zare hannunta ,
da sauri zuciyarshi ta ingiza shi ya riko hannunta ya juyo yana kallonta jikinta na rawa,
tace walhy gurin yaya farouk nazo bansan kai bane dan Allah kayi hakuri,
ya lumshe idonshi ya bude yana kallonta sama da kasa idonshi ya tsaya kan hadadden lallen kafarta,
gefen hagu da dama na zuciyarshi suka dinga kokawa akan ka saketa ta tafi kar ta raina ka,
dayar tace ka rungumeta zaka samu saukin radadin dakake ji game da ita,
zulfah ta fara kokarin kwace hannunta tana ja baya kar wani yazo ya gansu ga kofa a bude,
da kafarshi ya tura kofar ya rufeta tasa daya hannunta jikinta ya tsananta rawa zata bude kofar ya matseta sosai,
yana iya jiyo bugun zuciyarta, takalmin kafarshi ya cire yasa kafarshi yana shafar kafarta a hankali, ta runtse idonta ta daga kanta sama numfashinta na neman daukewa,
kallonta yakeyi zuciyarshi na tunzurashi tana fada mishi tunda mallakinka ce komai kayi mata lada zaka samu ba zunubi ba, kara matse hannunta yayi cikin nashi yana murzawa nan da nan idonshi ya kada ya kai bakinshi wuyanta yayi mata kiss a hankali, kuka ta fashe dashi a hankali jikinta na rawa sosai tana kokarin kaucewa daga jikin kofar saboda abinda yake mata yafi karfin daukar kwakwalwarta, rungumeta yayi sosai a jikinshi yana shafar bayanta,
ko kadan hankalinshi baya jikinshi,
turashi takeyi iya karfinta tana fadin ka rufa min asiri, wallhy mummy na kirana dan Allah ka bar-- ya daura bakinshi kan nata ta kara runtse idonta ta datse bakinta sosai, bin fuskarta yayi da kallo zuciyarshi cike da nishadi,
bude idonta tayi a hankali ya sauka cikin nashi ta kara runtse su tana kokarin yin wani kukan,
tsintar kanshi yayi yana murmushi ya kara maida kanta cikin kirjinshi zuciyarshi tayi tass kamar babu wata damuwa da tayi katutu acikinta,
jin an murda kofar yasa shi sakinta ya maida idonshi kan kofar,
farouk ne ya shigo ciki yana waka,
a bakin kofar ya tsaya yana kallonsu,
zulfah ta kasa hada ido dashi tace wayarka ake kira gata can ta nuna mishi ta bi ta gefenshi zuciyarta a dagule babu wani farin ciki a cikinta,,
farouk yayi murmushi ya karasa ya dauki wayarshi yace yaushe ka shigo yaya abba, sadeeq yace tun dazu, na kira wayarka ay hilal yace ya baka sako ka bani,
farouk yace eh na dauka ma ba yanzu zaka zo ba yana gurin mummy, sadeeq yace okk sannan ya fita farouk ya bishi da kallo yace Allah ka dai2ta wadannan bayin naka dan sunyi matukar dacewa da juna,,

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ZULFAH ◆◆ 4⃣7⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Dakin mummy ya wuce yana gaisawa da bakin da suka cika gidan,
zaune ya sameta da wasu bakin ya tsuguna ya gaishesu suka amsa mishi da fara'arsu sannan ya kalli mummy yace mummy farouk ya baki sako ko? ta mike tace eh dama ina son ganinka,
gaban sadeeq ya fadi sosai ya mike ya bi bayanta yana adduoi cikin zuciyarshi, dayan dakin suka shiga ta mika mishi sakon da hilal ya bayar a bashi sannan ta mika hannu tace bani,,
gabanshi ya tsananta faduwa ya dake yace me zan baki mummy? Ta harareshi tace baka ma san abinda zaka bani ba ko?, to takaddar zulfah nake nufi, saboda inason tunda babu idda akanta a hada bikinta gobe dana jalila Allah cikin ikonsa yasa ta samu mai kaunarta har na ma bashi saboda haka rubuta kawai ka bani kafin ya kawo sadakin,
gumi ya shiga tsatstsafo wa sadeeq tsayuwa ta gagari kafarshi, ya zauna a kasa ya dukar da kanshi cikin sarkakakkiyar murya yace mummy Allah baya son saki,
da sauri tace amma ya halasta shi ko?, yayi shuru ya kasa bata amsa,
tace tunda dama babu wanda yasan matarka ce sai mu,
kaga sai ka saukake mata saboda abincin wani gubar wani kuma hilal tun tana yar aikinta da ka fada mishi yake sonta dan haka maza rubuta karka bata min lokaci ina da abubuwan yi,
shuru sadeeq yayi yana share zufar da ta jika ko ina a jikinshi zuciyarshi kamar zata buga saboda tsananin tashin hankali, mummy taji shurun yayi yawa tace abba a tsaye nake fa,
ya rike kafarta ya dago jajayen idonshi ya kalleta yace ki yi min rai mummy,
, dan Allah dan son annabin Allah ki bar wannan maganar, tace kamar yaya in bar wannan maganar, kana nufin zan cigaba da zama da ita a gabana ne kamar hoto,
itama tana feelns ay ba dutse bace, bazan taba cigaba da cutar da ita ba,
gara ka saketa ta samu mahaďinta itama kamar yadda kaima kake da mahaďi,
ga dukkan alamu mummy so takeyi ya mutu a wannan lokacin,
kara rike kafarta yayi yace Alla--- ka daina hadani da Allah abba, ya zaka dinga hadani da Allah muna cutar yarinya,
ta kusa shekara uku a gidan nan baka taba maganarta ba, baka taba cewa yau wannan matata ce bari in sauke nauyiyyikanta da ya rataya a wuyana ba, yanzu dinma bansan me kake nufi ba tunda har yanzu ba sonta kakeyi ba, dan Allah abba ka rubuta sakin nan ka bata gobe in maye gurbinka da hilal dan Allah,
wani irin kuka ya fashe ma mummy dashi zuciyarshi kamar zata tarwatse saboda kalamanta na karshe gashi shi ya kasa gasgata sonta yakeyi ko kuwa,
shidai yasan yana jinta a dukkan ilahirin gabobinshi da jinin jikinshi,,
Mummy taja baya da sauri tace kuka kuma abba, me nayi maka, cikin kuka ya mike yace wallahy mutuwa zanyi mummy,
wallhy bazan iya sakinta ba in kuma kika matsa wallhy zan mutu,
cikin halin ko in kula tace duk wanda ya mutu lokacinshi ne yayi Allah ya jikanka in ka mutu amma sai ka rubuta,
na shiga uku ya shiga fadi kamar karamin yaro yana ta yarfe hannu hawaye na bin idonshi,
mummy tace baka shiga ba tukunna dai abba,
ya kasa magana sai kuka yakeyi sosai mummy ta matso kusa dashi a hankali tace abba sonta kakeyi?
Ya dago kanshi ya shiga girgizawa yace bana sonta amma bazan iya rabuwa da ita ba,
mtswwwwww mummy ta fadi saboda takaici tace kaji na rantse idan baka rubuta min takardarta ka bani ba yanzu sai tsine maka, ya mike tsaye kamar zararre yace ki rufa min asiri mummy, wallhy bazan rayu ba in na rabu da ita, dan Allah mummy ki taimakeni,
ta daka mishi tsawa tace wallhy bazan bari aurenka ya kai gobe a kanta ba abba,
dole ka saketa gobe a daura mata wani auren itama,
yace mummy ki bari in tambayeta ko ita tana sona mana, ki bari mu zauna tare dasu daddy in bata sona na yarda zan saketa,
mummy tayi kwafa tace Allah ya kaimu yau komin dare sai ka rubuta,
kuma ko tana sonka bazan bari ba sai ka saketa saboda ka cika son kanka dawa,
tayi tsaki ta fita tana masifa tabar sadeeq tsaye sai kuka yakeyi yana nemowa kanshi mafita,
saida ya kusan minti talatin sannan ya fito bayan ya gama yanke shawarar daura mata iddar da mummy ke tutiyar bata dashi,
motarshi ya shiga zuciyarshi a dagule yana tunanin rabuwa da zulfa'u,
sam bazai iya rabuwa da ita ba,
gurin hilal ya yanke shawarar fara zuwa yaci mutuncin shi kafin ya wuce gurin da suke sword crossing din,
har ya kama hanya wata zuciya ta kwabeshi akan in kaje me zaka cewa hilal, kana ma sonta kenan, kuma kai shikenan akan mace sai kayi ta fada amininka,
tunanin irin fadan da sukayi akan sanah da yadda suka dau lokaci kafin su shirya shi ya hanashi zuwa gurin hilal,
to amma meyasa hilal zaiso matarshi why,??
yayi tsaki ya juya ya nufi sde rsrt,,
a harabar gurin yayi parking ya zauna cikin motar zuciyarshi na zafi saboda mummy na neman daura mishi ciwon da baisan wani bangare bane zai fara kamuwa da ciwon saboda yadda yakeji,,
yana cikin tunanin ya hangosu ita da zabba'u sun fito daga ciki da jakar kayan waleed din anty laila a hannunta sunyi kyau har sun gaji,
zabba'u ta juya ciki sakamakon kiranta da akayi ,
zulfah ta fara takawa a hankali ta karaso kusa da motar anty lailah tasa key ta bude,
tunda take tahowa yake kallonta baya ko kiftawa fitowa yayi da sauri lokacin da ta tura kanta cikin motar,
tana dagowa taga inuwar mutum a bayanta ta juyo da sauri cikin firgici,
suna hada ido ta maza ta kauda kanta ta kama murfin motar zata rufe ya rike hannunta hade da murfin yana bin ko ina na jikinta da kallo,
, janyota yayi ya rike kugunta sosai ya tura motar,
ta dinga waige2 tana kokarin kwace jikinta kara riketa yayi ya bude motarshi a hankali kamar mai raďa yace shiga muje, ta juyo cikin rashin fahimta tace ina zani, ni dan All---- ya turata cikin motar yayi lockn dinta yana jinta tana bubbuga glass din motar ya koma ya rufe ma anty laila tata motar sannan ya dawo ya shiga ya ja suka wuce,
duk irin ihun da takeyi bai saurareta ba har suka kai kofar gidanshi tana kuka.....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 4⃣8⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Horn yayi mai gadi ya bude mishi da sauri yana sara mishi,
yayi parking motar ya kalleta ta hada kanta da murfin motar tana kuka harda shashsheka,
ya bude motar yana shawara da zuciyarshi akan ya maida ita kawai karta rainashi, ya tsaya jimm kusa da kofar motar yace to ay in ya maida ita ba tare da ya daura mata idda ba tabbas gobe mummy xata bawa hilal,
gara ya daura mata idda ya saketa,
yasan zai iya maida ita tunda har sai tayi wata uku,
"(hmmmm) "
bude motar yayi ya tsuguno da kanshi cikin rarrashi yace kukan me kikeyi,
bata dago kanta ba tace ni ka maida ni gida,
yace to sakko zan dauki wani abu ne sai mu tafi,
ta kara matse kanta tace um um kaje ina jiranka,
ya shafo gashin kanta yace kina biye ma jalila kina matar aure kina barin jikinki a bude kina kwasar zunubi ko,
ranta ya fara baci tace ni ba matar aure bace, dan Allah kazo ka maida ni gida,
yayi murmushi yace lallai ma yarinyar nan wato baki daukar kanki matar aure ko,
tayi banza dashi,
da yaga yana lallabata tana bata mishi lokaci ya dauketa cak tanata ihu tana zillo,
riketa yayi sosai bai damu da ihun da ta cika mishi kunne dashi ba har saida ya shiga parlor ya wuce dakinshi da ita, kwantar da ita yayi kan makeken gadonshi,
ta mike da sauri ta diro tana ihu jikinta ko ina rawa yakeyi,
kafin ta kai kofar ya rigata ya murdeta da key,
, ta matsa jikin kofar tana ihu tana girgizawa ko zata iya budewa ta jingina jikinta jikin kofar tana kuka kamar ranta zai fita,
dariya yayi ya karaso kusa da ita yace ki daina kukan nan dan ba wanda zai ji ki, gara ki zo ki zauna muyi magana,
tace ni a'a wallhy bazan zauna ba, kuma duk abinda kamin saina fadawa mummy,
yayi murmushi yace ita tace inje in dauko ki ay,
ya kamo hannunta yace kuma kinsan meye,
ta kwace hannunta tace dan Allah ka bude min kofa in tafi gida banason sanin komai,, shuru yayi yana kallonta,
ta karkatar da kanta idonta na zubar da ruwa tace Allah fa nace,
yayi dariya ya janyota ya rungumeta yace nima Allah nace,
Tace to me kakeso inyi maka,
yace yauwa maganar da zakiyi kenan kin tsaya munata bata lokaci,
ya dago fuskarta ya share mata hawayen fuskarta yace karki kara kuka kinji,
ta gyada kanta tana kokarin shanye hawayen dake kokarin zubo mata, yace au wani kukan ma zakiyi, ta girgiza kanta tana boye fuskarta saboda hawaye ya riga ya zubo a kan kumatunta,
Yayi murmushi ya kara share mata hawayen, ya jata suka zauna gefen gado,
a hankali ya fara magana, yace kinga yanzu shida ta wuce ko,
ta gyada kanta, yace gud,
to idan kika bani hadin kai cikin mintina kadan zan maida ki gida kinji,
da sauri tace to,, yayi murmushin jin dadi dan yasan bazai sha wahalar yi mata wayau ba,
ya matso sosai kusa da ita ya dago kanta yana kallon cikin idonta,
a kunne ya rada mata abinda yakeso ta matsa da sauri tana girgiza kai tace wallhy bazan iya ba, na shiga uku na, dan Allah ka taimakeni ka mayar dani gida, ya mike yana mika yace kina son kwana a gidan nan kenan,
tace a'a, yace to zabi ya rage naki, ta kara sa kuka tace wayyo Allahna nasan yanzu ana can ana nemana,
ya ciro wayarshi a aljihu yace haka ne kin tuna min bari in kira mummy in fada mata gaki nan kin kawo kanki gidana kince ke a gidan mijinki zaki kwana,
ihu tayi sosai ta sa hannu zata kwace wayar ya rike wayar hade da hannunta, cikin kuka tace karya haramun ne kuma walhy wutar jahannama Allah zai saka in har kamin sharri,
ya janyota ya rungumeta yana dariya sosai harda rike ciki,
ya fara shafar gashinta har wuyanta yace dagaske kikeyi wuta za'a sani,
ta ture hannunshi tace ban sani ba, ya dago kanta yace ni kika ture ma hannu, muryarta na rawa tace to ka mayar dani gi--- shigar bakinshi taji cikin nata cikin wani irin rikitaccen salo,
kuka takeyi tana kokarin kwacewa ta kasa,
sadeeq ya riga ya shagala, kukan da takeyi ma kamar tana kara ingizashi
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment