Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

a gabana,
ta kara shigewa jikinshi tana kuka kasa2 tana magana kamar marainiya, wa'azin karya ta shiga yi mishi akan yaji tsoron Allah ya dinga sauke hakkinta akanshi wa'azi sosai take mishi wanda itama zuwar mata yayi a baki saboda ta samu biyan bukatunta, jikinshi yayi sanyi kadan dan yasan gaskiya ta fada shi rabon da su hada shimfida da sanah har ya manta,
kuma yasan baya kula da duk wasu needs dinta, share mata hawaye ya shiga yi yana bata hakuri ya jata suka wuce daki shima ya shiga yi mata nasiha akan abubuwan da takeyi marasa kyau,
narkewa tayi a jikinshi tana bashi hakuri kamar da gaske,
nan ta shiga aika mishi da salonta dake rikita maza,
sun lula can wata duniya idon sadeeq babu abinda yake hange da wuce zulfah gani yakeyi kamar tare suke tarayya da ita a wannan daren,
ina ma ita ke mishi irin wadannan abubuwan da sanah ke mishi abin da ya dinga aiyyanawa a cikin ranshi kenan,
saida ta gamsu dan kanta sannan suka mike suka shiga wanka tare,,
ta riga shi fitowa ta zauna a bakin gado tayi tagumi,
yana fitowa ya zauna kusa da ita yace meya faru kuma, ta kwanto da kanshi jikinta tace waalhy dazu na samu waya wai momy na bata da lafiya shine nake jin tsoron tambayarka ko zaka barni inje,
ya salam ya fadi cikin damuwa yace ciwo ay ya wuce komai gobe ki shirya da wuri muje mu dubata,
gabanta ya fadi amma sai ta dake tace a'a bari dai In fara zuwa saboda naji ance india za'a fitar da ita goben, kuma kaga dole ni zanyi jinyarta a can din,
yace hakane to Allah ya bata lafiya ya kuma kaimu goben,
ameen ta fadi hade da rungumeshi tace tnk u so much swthrt,
yayi murmushi ya mike yana karasa goge jikinshi,
dakinta ta wuce ta kira beeba tace ya faďa beeba,
wallhy komai ya daidaita kawata,
gaskiya samun kawaye irinki sai an tona,
beeba tace yauwa ko kefa yanzu kinga zakije ki sheke ayarki babu wanda ya sani, sanah tace hakene kawata,
bari in kirah Mukhtar in fada mishi ina tafe gobe yayi min shiri na musamman,
beeba tace ay kema kinsan a shirye yake tunda har ya matsu kuje yawon bude ido kinsan kasashe hudu yace zaku,
tace yeyyy ai zamu hole kawata ke dai Allah ya saka miki, tace ameen suka cigaba da hirarsu ta karuwan mata masu neman mazan mutane,
Allah ka tsare mana mazajenmu
"ameem thumma Ameen"
....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 5⃣3⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Kwance take safiyar asabar a daki ta dukunkuna cikin bargo saboda sanyin da akeyi,
waya ta gama yi da jalila ta ajiye wayar tana lumlumshe ido ko zata koma bacci,
tun daga parlor yake sallama shuru babu wanda ya amsa ya hau sama ya murda dakin mummy ya ganta kwance tana bacci,
a hankali ya janyo kofar ya wuce dakin zulfa'u cikin farin cikin samun damar ganinta, a hankali ya murda kofar ya mayar ya rufe, karasawa yayi ya zauna gefen gadon ya bude fuskarta dake cikin bargon, bude idonta tayi da sauri suka hada ido, ta runtsesu sosai tana jan bargon dan ta kara rufe fuskarta,
rike bargon yayi sosai yana dariya yace ki saki bargon nan ko in cireshi gaba daya,
ta maza ta saki bargon ta rufe fuskarta da hannunta,
kwanto da kanshi yayi dai2 fuskarta yasa hannunshi yana shafar yatsun hannunta, ciresu tayi da sauri zata juya kanta cikin pillow,
da sauri ya tallabo habarta da hannunshi, ta kara runtse idonta jikinta na rawa ta ko ina, a hankali yayi mata peck a kuncinta yace bude idonki ki kalleni,
um um ta fadi kamar me shirin yin kuka, ya daura bakinshi kan nata ta kauda kanta da sauri ta bude idonta, yayi mumushi yana kallon cikin kwayar idonta daga ganinta a tsorace take a hankali yace baki iya gaisuwa ba ko? Ta girgiza kanta tace ina kwana, ya kama kunnenta yace bazan amsa ba tunda saida na roka,
ta noke gefen fuskarta kan hannunshi saboda yadda yake mata waiwayi a kunnenta cikin rawar murya tace dan Allah ka daina,
yace to daga min hannuna sai in daina, ta juya da fuskarta cikin muryar shagwaba tace to ka tashi,
ya kara matsowa sosai yana shafar fuskarta,
hawayen tsoro suka shiga tsere a fuskarta, a kasalance yace wannan hawayen dama nakeson gani,
ya fara lashesu a hankali, ta bude baki zatayi magana ya hanata yin maganar da bakinshi saida ya dan rage ma kanshi wahalar da yakesha akan tunaninta sannan ya kyaleta,
ta juyar da kanta tana kuka tana tsoron ya sake bata wahalar da bata rannan,
kamar ya karanto abinda ke zuciyarta yace ki daina jin tsoro babyna babu abinda zan miki rannan ma tsautsayi ne, ta ji dadi sosai ta dan share hawayen fuskarta,
a hankali yace ya kamata ki saki jikinki dani ki cire kunya ki nuna min tsantsar son da kike mini,
ta juyo fuskarta da sauri suka hada ido, ya kashe mata ido yace ko bakya sona,
ta turo baki ta juyar da kanta gefe,
yayi dariya yana jan bargon jikinta yace nasan kina sona in ma bakya sona zan gane yanzu in har baki fada min da bakinki ba,
tayi shuru kirjinta na bugawa da sauri2, yace baxaki fada ba kenan,
to bari in tambayi zuciyarki, ya fara yaye bargon ta rike da sauri saboda nyt gown din dake jikinta,
tace na hadaka da Allah ka tashi ka tafi, yayi murmushi yana kallon hannunta yace in kinga na fita a dakin nan to naji labarin da ke cikin zuciyarki,
tace wayyo Allah na, dan Allah to ka bari in fada maka da bakina, ya girgiza kanshi yace bana so nafison inji a gurin da baza'a min karya ba,
ta kara cukuikuiye bargon tace nima bazan yi maka karya ba wallahy,
ya karkatar da kanshi gefe yace ni kuma bana son jin ta bakinki, ya fara jan bargon? tana ja itama tana rokonshi tana kuka, sakin bargon yayi yana murmushi yace oyaa ina jinki zo ki fada min a kunne,
ta marairaice tace me zan fada maka,
yace ohhh tambayata ma kikeyi ko,
ya rike bargo tayi yar kara tace na tuna zan fada, yace matso da sauri ki fada min yadda kike sona, ta kai bakinta kunnenshi ta runtse idonta, a hankali tace I love u saboda ka matsa min in fada,
ya kauda kanshi yace auuu ni ma na matsa miki ko? Ta riko hannunshi tace um umm kayi hakuri, yace to kara fada min kina kallon cikin idona, ta girgiza kanta ta runtse idonta tace I love u, ya rungumeta sosai yace luv u more more more baby
, dan Allah ki saki jikinki dani ki manta da komai da ya faru a baya mu gina rayuwarmu cikin farin ciki kinji,
ta daga mishi kanta a zuciyarta tana jin dadi da godewa Allah da ya bata wanda take matukar so kuma shima yake sonta, saida ya dade rungume da ita shima zuciyarshi tayi fari kal saboda kasancewar shi da abin kaunarshi,! (To Allah yasa farin cikin na wadannan masoyan ya daure ameen)
cikin yan kwanaki kadan ta saba da mijinta har ya zamana in bata ganshi ba ko bata ji muryarshi ba bata jindadi ko kadan, mummy na hankalce dasu haka anty lailah dan kullum in yana gari suna tare a dakinta, wannan abu yayi ma su mummy dadi saboda dama abinda take jira kenan taga sun daidaita kansu,,

Daddy zaune a hotel din da ya sauka a England wani doctor na kanshi yana mishi aune2 saboda baya jin dadi tun zuwanshi, magunguna ya bashi suka yi sallama daddy ya rakashi har waje ya juyo dan komawa daki idonshi na mishi nauyi sosai,
hayaniya yaji a dakin kusa dashi harda ihu da kuka kuma muryar hausawa ce,
ya bude kofar ya shiga, wani saurayi ne tsaye rike da wani saurayin ya shake mishi wuya daddy yayi saurin rabasu dayan saurayin ya rarumi kayanshi ya fita da gudu yana haki, shi kuma dayan ya koma kan yarinyar dake duke tana kuka daga ita sai towel,
zai fara dukanta daddy ya rikeshi yace kayi hakuri samari mata rauni garesu karka duketa ka lallabata har ku koma gida babu mamaki ma akwai ya'ya a tsakaninku, kaga bazai yi kyau ba ace ka duki uwar ya'yanka,
yaron tofar da miyau yace Allah ya kyauta wannan karyar ta xama matata,
macen da duk namijin da ta gani burinta ta kwanta dashi ,
inaga alhakin mijinta ne ma ya kamani saboda da mijinta tayi mishi karya ta biyoni wata kasa,
shine yau daya dan naje wasu ayyuka ta kasa hakuri ta nemo wani dan ya biya mata bukatunta,
tirrr da halinki,
daddy ya girgiza kai cikin kyama da tausayin mijin yarinyar, yace yarinya kiji tsoron Allah,
ta dago kanta cikin masifa tace dakata mal-- muryarta ta makale saboda ganin daddy da tayi, daddy yaja da baya da sauri jiri na dibanshi yace s..a..n..ah, ta juya bayanta da sauri jikinta na rawa tace yau na shiga uku,
taro daddy saurayin yayi dan ya kusa kaiwa kasa saboda tashin hankali, yace baba kasanta ne, sanah ta tattara yan komatsan kayanta da jakarta dake cike da kudi ta fita da sauri tana kuka,
daddy yace ma saurayin matar ďana ce,
innalillahi wa inna ilaihir rajiun, abinda saurayin ke fadi kenan ya rike daddy yace dan Allah kayi hakuri, daddy yace ba laifinka bane yaro sai dai zan baka shawara kaji tsoron Allah, ka tuna da ranar karshe, ranar da babu wata sauran nadama, ranar da kana gani ranka zai fita daga jikinka ba tare da ka tuba ba, jikin saurayin da ya kira kanshi da mukhtar ya mutu sosai, yana hawaye yana bawa daddy hakuri,
daddy yayi mishi nasiha sosai sannan ya kaishi dakinshi ya kwantar dashi,
kuka daddy yakeyi jikinshi na rawa ta ko ina, ya daga waya ya kira tawagar da suka taho tare yace su shirya tafiya yau in shaa Allah,
sannan ya kira sadeeq, sadeeq ya dauka ya gaida daddy yace ya jikinka, daddy yace da sauki abbana, ina matarka, ya shafo kan zulfa'u dake kwance a jikinshi yace gata nan daddy tana gaisheka,
daddy yace dayar fa, sadeeq yayi jimm yana tsoron kar daddy yayi mishi fadan rashin zuwa duba mahaifiyarta,
yace daddy tana india tana jinya mamanta bata da lafiya, jikin daddy ya mutu sosai yaga bazai iya fadama danshi abinda ke faruwa a waya ba, yace to Allah ya kara sauki, sadeeq yace ameen daddy sukayi sallama suka kashe wayoyin,
daddy wani irin yanayi ya dinga ji a jikinshi gaba daya tun daga kan jininshi har gabobinshi duk sun saki,
a zuciyarshi yace ya Allah ko bayan raina ka fitar da gurbatattu daga cikin zuriata kuma karka bawa wani gurbatatacce daman shiga cikinsu...

""Ameen daddy amma da ka fada ma sadeeq dan rashin fadar da wuri bamusan me zai haifar ba, tabbas akwai wanda zai shiga gaggarumar matsala a gidanka saboda rashin fadin da bakayi ba da wuri""'

Mrs tijjani shattima....
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 5⃣4⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Sanah airport ta nufa da sauri tana kuka ta kira beeba ta fada mata duk abinda ke faruwa,
beeba tayi salati tace yau mun shiga uku yanzu ya zakiyi sanah, sanah cikin kuka tace ko ma meye zanyi dan inga daddy bai fadawa sadeeq ba,
koda kuwa kasheshi zanyi wallhy,
dan da in rabu da sadeeq gara in mutu, beeba ta harari bango a zuciyarta tace kinsan kina sonshi kike bin mazan banza, amma a wayar ce mata tayi kiyi sauri ki taho mu san abin yi kafin ya dawo,
sanah tace yanzu kuwa dan ina airport, kuma karki bari kowa yasan ina gari ma, beeba tace trust me dear, suka gama hada plans dinsu suka kashe wayar sai a sannan sanah ta samu nutsuwa,
karfe biyu na rana jirginsu ya sauka a abuja da hanzari ta dauki drop ta fada ma beeba ta iso,
beeba tace to sai kin karaso sanah,

a motar ta dinga sake sake , can ta dauki waya ta kira anty amarya, ta dauka suka gaisa anty amarya tace kwana biyu kina garin nan kuwa,
sanah tace wallhy naje dubai sarin kaya anty,
anty amarya tace manya to yaushe zaki dawo, tace inaga jibi, da England ma naso zuwa,
anty amarya tace aiko da kinje can dan daddy ma na can da ya cika miki jakarki da kudi, sanah tace gaskiya nayi missn ko dai zan wuce can ne,
anty amarya tace kin makaro yarinya ya riga ya taso inaga magriba ma a gida zaiyi ta, sanah tayi murmushi cikin faduwar gaba tace kice yanzu ana can an hada mishi delicious,
Anty amarya tayi tsaki tace inaa ay bani bace da girki nasan yanzu wannan bazan yarinyar tana can tana iyayin girki a kitchen dan yaya da laila ma suna biki sai dare zasu dawo,
nima fita zanyi ita kadai zamu bari a gida tayita iyayinta shegiyar,
sanah cikin farin cikin ta samo satar amsah ta taya anty amarya tsine ma zulfa'u dake can tana kici kicin faranta ran uban mijinta da daddan girkinta,
saida suka dade sannan suka kashe wayar,

karfe uku da rabi ta shigo kaduna ta wuce ta dakko beeba da tayi mata guzurin muguwar gubar dake gurbata ya'yan hanji, sunata plans dinsu a mota kasa2 suna dariya babu imani a zuciyarsu,
dan a ganin sanah zata jefi tsunsu biyu da dutse daya,
suna karasawa suka biya dan texi din sanah tasa nikab din da beeba ta dakko mata suka shiga ciki, masu gadi suka tambayesu inda zasu beeba tace nazo gurin aminyata ne sunanta zulfah, suka ce to ku shiga, suka wuce ciki suna murmushi,

zulfah na daki tana shiryawa dan a yau ne mummy tayi ma sadeeq alkawarin zata bashi matarshi saboda farin cikin gano boyayyen karamin cikin dake jikin zulfah wanda babu wanda ya sani sai ita,
buruntu taji a gurin dining ta fito da sauri taga bata ga kowa,
ta deko ta windo ta hango fuskar beeba,
ta daga kafadarta ta juya tace may be gurin anty amarya tazo dan ta taba ganinsu tare da sanah, ta dauki wayarta dake gurin dining ta koma daki ta cigaba da shirinta...

Karfe takwas da yan mintina daddy ya shigo gidan,
mummy ta fito ta taryeshi cikin farin ciki ta karbi jakar hannunshi tace muje a ci abinci sai ayi wanka ko,
ya zauna bai ce mata komai ba,
cikin damuwa ta zauna kusa dashi tace yallabai me yake damunka ko jikin ne, ya girgiza kanshi yace damuwata Aisha tafi karfin ciwo, ina cikin matsananciyar damuwar da idan kuka ji ta ku kanku sai kun shiga cikin damuwar da tafi tawa,
tace subhanallahi wace irin damuwa ce wannan?
Yace damuwar matar abba,
wacce daga ciki mummy ta fadi cikin kagauta,
yace kedai kawo min abinci inci sai muyi magana,
ta je dining ta kwaso mishi abincin, babu abinda ya iya ci a abincin sai kunun gyada, gaba daya kunun ya shanye sannan ya mike yace zaiyi wanka tukunna sai ta kira kowa yazo a zauna ayi magana,,
mummy dai cikin zulumi daddy ya barta saboda taso ya fada mata wacce a ciki matan abba,
ta zauna tayi jimm tana jiran fitowarshi, mummy taga awa daya ta gota daddy bai fito ba, ta mike tace yau inaga canza fata kakeson yi ko, wannan irin dade---- maganar ta makale a makoshinta saboda ganin daddy da tayi kwance bakinshi duk kumfa, karasawa kusa dashi tayi da sauri tana salati, ta shiga girgizashi babu alamar motsi, da sauri ta fito tana kuka tayi dakin nurain,
Nurain yana ganinta cikin wannan yanayin ya mike dan yasan ba lafiya,
tace nurain fito muje ka gani tana magana kamar tababbiya nurain yabi bayanta laila ma ta fito da gudu tabi bayansu,
ihu nurain yayi shima hade da salati ya shiga girgiza daddy, ya dago kai yana kuka yace shikenan mummy daddy babu,
ya kwanta jikinshi yanata gunjin kuka kamar karamin yaro, laila kuwa zama tayi dabas a bayin tana kuka sosai ta kalli mummy wacce take kamar a sankare ta kasa yin komai saboda shock,
sun kusa minti talatin a haka kafin nurain yayi ta maza ya tallabo daddy da kyar ya fito dashi daga bayin...

Sadeeq kwance a side dinshi na gidan da aka gyareshi tun satin da wuce,
rungume yake da zulfa'u bayan sun idar da sallar godiya ga Allah,
yanata mata hira cikin so da kulawa suna aikawa juna sakonni, gaba daya ta cire kunya a wannan lokacin tana mishi duk abinda yakeso amma zuciyarta na tsoron abin da yayi mata a ranarsu ta farko,
cikin kasala ya matseta jikinshi ya dinga rada mata kalamai a kunne cikin so da kauna,
yanata nusar da ita akan bazata ji zafi ba dan Allah ta bashi hadin kai su raya sunnar manzon Allah s.a.w,
cikin hikima ya lallabata har ta yarda suka shiga faranta ran junansu,
iya ficcewar hayyaci sadeeq yayi dan gaba daya bai san duniya da yake ciki ba,
yana gab da shiga "koramar zuma" yaji bugun kofar parlonsu babu kakkautawa, tsaki yaja ya mike jikinshi a mace yasa kaya ya fita da sauri dan har lokacin ba'a bar bugun kofar ba,
yana budewa yaga nurain idonshi jawur,
a firgice yace yaya nurain lafiya me ya faru,
nurain cikin muryar kuka yace ka biyo ni muje,
sadeeq gabanshi na faduwa yabi bayanshi a tsakar parlor ya hango daddy kwance babu rai,
mummy da anty amarya na gefenshi suna kuka,
sadeeq ya karasa da sauri yace me ya sameshi,
ya fara girgizashi yana kuka yace ka tashi daddy, dan Allah ka tashi karka tafi ka barmu,
me yasameshi ku fada min dan Allah,
anty amarya cikin kuka tace wannan kumfar ta bakinshi ta guba ce wallhy guba aka bashi yaci dan ya mutu,
gaban mummy ya fadi ta sauko dan bata kawo guba a ranta ba, taba kumfar tayi taji tana yauki ta fashe da kuka tace waye ya gaji da rayuwarka ya baka guba, wanene ya cuci rayuka da yawa ssboda bukatar kanshi, ta dinga magana kamar zautacciya, anty amarya ta dago kanta ta hango zulfah dake tahowa cikin hijab da sauri, itama ta fito jin abinda ke faruwa ne saboda dadewar da mijinta yayi, harararta tayi ta kauda kai tace koma wanene ya zuba maka guba wallhy bazamu kyaleshi ba sai mun dauki fansa a kan mutuwarka tana magana tana kuka,
zulfah ta shigo ciki da sauri ta zauna gefen mummy tace mummy lafiya,
mummy ta rungumeta tace an kashe shi zulfah an kasheshi, bansan me yayi ba aka kashe shi, bansan wace irin tsana bace tsakaninshi da wanda ya kashe shi, zulfa ta fashe da kuka ta toshe bakinta da hijab dinta tana kallon daddy a tsorace,
a daren akayi mishi wanka aka suturce shi yayi kwanan keso.. duk iyalan gidan suna kewaye dashi suna mishi addua da kuka sosai.....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 5⃣5⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Washe gari tun safe police da manyan sojoji suka kewaye gawar chief of air staff,
bincike sosai akeyi akan gawarshi inda aka tabbatar da guba ce yaci ta mai saurin illata yayan hanji,, cikin kwarewa manyan yansanda suka fara aiwatar da bincikensu tun daga kan wadanda sukayi tafiya tare da irin abincin da yaci a hanya,
har kawo cikin gidanshi inda kowa ke zaune cikin tsananin tashin hankali, ta kan mummy aka fara, tambayoyi wani police yake mata cikin muryar kuka take bashi amsa,
tace tunda ya shigo dama ranshi a bace yake yace zai fada min damuwarshi, kuma damuwar tashi akan matar dana ne gashi can abba,
amma bai fada min wacce aciki ba, kunu kadai yasha ya shiga wanka shine na iske shi a kwance babu rai,
police din yace hajiya an duba ingancin kunun kuma an tabbatar da tsaftarshi kafin a bashi,
tace kwarai kuwa dan matar dana keyi mishi kunu yama fi son kununta fiye da na kowa a cikin gidan nan,
police din yace ko zamu iya samun flask din da aka zuba kunun in ba"a wanke ba,
tace kwarai kuwa zulfa je ki dakko, zulfah ta mike taje ta dakko ta kawo musu,
ya bude flask din babu kunu a ciki sai dan kadan daya kwanta a can kasan flask din, dan sandan yayi mata godiya ya koma kan sauran duk yayi musu tambayoyi,
duk suka amsa mishi, fita waje sukayi da flask din suna tunanin yin bincike akan ragowar kunun ciki tunda ance shi yasha karshe,
daya ya basu shawarar su hada kunun da madara asamu mage a bata tasha in dai har wani abu ya samu magen to tabbas a kunun gubar take,
haka kuwa sukayi suka wanko flask din da ruwa kadan suka dama madarar dashi, mage suka bawa tashanye tasss ko minti biyar ba'ayi ba magen ta fara shure2, cikin kankanin lokaci ta cika,
police din sun tsorata matuka da ganin wannan alamarin,
cikin minti kadan suka isa gidan, lokacin mutane sun cika makil ciki harda sanah da tayi ikirarin dawowarta kasar kenan,
police din na shigowa parlon suka bukaci ganin mummy, mummy ta tashi ta bisu karamin parlon yara,
nan suka fada mata komai game da kunun sannan suka bukaci ganin wacce ta dama shi,
mummy ta fara kuka tana girgixa kai tace wallhy zulfau bazata kasheshi ba, kudai sake bincikowa,
saboda me zaki ce bazata kasheshi ba, haihuwarta yayi ko rainonta muryar anty amarya sukaji tana karasowa cikin parlon ay ni biri yayi kama da mutum dama tun ganin gubar nan nasan wallhy itace zata kasheshi ta fashe da kuka tace dama saida ya fada yace kin shigo mishi da matsala cikin gida gashi ta kasheshi kowa ya huta,
mummy jikinta ya fara rawa tace wallhy inspector zulfa bazata iya kisan kai ba, inspectorn yace hajiya bincike ne zai fadi koma zata iya ko baxata iya ba,
kedai ki bamu hadin kai muyi mata tambayoyi, a statement dinki na dazu kince yace damuwarshi akan matar danshi ne abba ko, ta iya yiwuwa yanada wata boyayyar damuwa akanta, mummy tace ay ba ita kadai bace matar tashi,
anty amarya tayi wuff tace ay sanah ba'a gidan nan take ba kuma bata ma kasar sanda abun ya faru, police din yace duk a tsayar da wannan cece kucen a kira mishi zulfa'un,
mummy ta mike hawaye na bin idanunta ta kira zulfa'u da laila sannan tasa aka kira mata sadeeq da nurain a waje..

Zulfa'u zaune gaban police din dukka mutanen dake gurin sun tsura mata ido, police din yace malama zulfa'u ki fada mana gaskiya duk abinda kika fada shi zamuyi amfani dashi a gaban shari'a,
cikin rawar murya tace to, yace kunun da kika dama jiya kin sha?
Tace eh nasha,
yace ke da waye a cikin gidan nan lokacin da kika gama aikin,
tace ni kadai ce,
kin duba ingancin ruwan da kika dama kunun dashi, kuma kin duba kullun babu wani abu da zai cutar a ciki,
tace eh na duba,,,
yace kinsan kunun da kika dama na dauke da guba a ciki,
ta mike tsaye da sauri ta dafe kirji jikinta ko ina sai rawa yakeyi, tace wallhy tallahy bani bace na zuba, police din ya mike yace relaxx nasan bake bace kika zuba, babu mamaki wani ne yayi miki barazana akan zai kasheki in baki zuba ba ko?
Ta rike cikinta dake murda mata tana girgixa kanta kamar zata fadi,
sadeeq ya mike ya rungumeta da sauri yana bubbuga bayanta yace wace irin banzar tambaya kakeyi mata haka,
ta kankame sadeeq tace wallhy ban zuba komai a ciki ba, wayyo Allahna na shiga uku,
rarrashinta ya shiga yi yace nasan bazaki zuba komai a ciki ba u r innocent ki daina kuka,
police din yace mr man ka barni inyi aikina,
sadeeq cikin fushi yace ka gama yi mata tambayoyin da zasu dinga firgita ta,
ka tashi ka tafi kawai bamu bukatar ka,
anty amarya
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment