Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

zai auri salaha shine kike bakin ciki to sai ya aure ta din,
haba ay nan delu ta kara kaiwa bango ta mike suka dinga cacar baki kamar zasu ci kansu, duk irin hakurin da ake basu a gurin suka ki yin shiru sai tonetone sukeyi ma junansu, salaha dai ko ajikinta dan waje ma ta fita neman babanta ko yaya kabiru, lokacin da suka shigo tare da kabiru da ta ganoshi gurin mai shayi, bangis na tsaye a tsakar gida yana rarrashin hanne rarrashi na musamman wanda ya kwantar mata da hankali, yace kiyi hakuri ay kinsan duk duniya babu wacce nakeso kamarki, ki bari in aureta in ci kudina kema sai in aureki mu hadu muci kudin tare ta hanyar bata wahala, salaha taji kamar zata mutu dan takaici amma saboda zuciyar kare da kwakwalwar kifi gareta sai ta basar a ranta tace ai in na aureka dole in koyar da kai yadda zaka soni, ta wuce ciki tana ma hanne gwaloo,
Bayan kurar fadace2 ta lafa duk mazan suka fita waje aka je aka gabatar da daurin aure hanne da delu gida suka wuce suna kulle kullensu,
goggo amina dai ko kallonsu batayi ba ta cigaba da gyaran kazar da ta siyo a kudin da aka bawa fa'ee tana yi tana wakar da ya kara kular dasu amma sun kasa tanka mata,,

Malam ado bai dawo gida ba sai bayan magriba lokacin motar daukar amarya tazo har sun wuce ya bi motar da kallo, kabiru ya fito daga cikin gida yace baba yanzu ka karaso ya kalleshi yace eh kabiru, motar waye waccan ta bar kofar gida, kabiru yace uhunm salaha aka daura ma aure da bangis shine suka zo daukarta, ya bawa babanshi labarin duk yadda abin ya faru, malam ado yayi ajiyar zuciya yace to Allah ya basu zaman lafiya, kabiru yace ameen, suka danyi hira ya bashi labarin yadda akayi auren zulfah kabiru yayita murna yace itama Allah ya basu zaman lafiya gaskiya naji dadi baba, malam ado yayi murmushi yace nima haka kabiru suka karasa ciki,
Sun sako kafarsu kenan marka cikin tsawa tace dakata2 ta mike da sauri ta isa gabanshi ta nuna shi da yatsa, tace yanzu ado kai har kana da idon da zaka kalleni, har kanada kwarin gwiwar da zaka shigo min gida, to wallhy kaji na rantse tunda har baka kaunata nima bana kaunarka, ka sauwake min aurenka kaje can ka karata da wahalarka, in ma gidan zulfan zaka koma su baka mazauni to amma dai kai da zama a gidannan har abada tunda ba tare da kai muka siya ba, ta wurgo mishi ledar kayanshi tace ban takadda, kabiru ya tsuguna cikin bacin rai yace haba gog-- ta katseshi tace zan tsine maka albarka dan ubanka, malam ado yace yi shiru kabiru, ya karbi ledar kayanshi yace to zan tafi marka in har na zalunceki Allah ya saka miki, in kuma ke kika zalunceni Allah ya sa hakkina ya hanaki sukuni, yasa kai zai fita ta biyoshi tana masifa tace takaddar fa, yace zan bayar a kawo miki, tayi shewa tace tafi nono fari matsiyacin banza kawai, har sukayi nisa da kabiru suna jiyo masifarta,
A dai2 masallaci suka zauna kabiru yana kuka yace to baba ina zaka je, malam ado yace zan kwana cikin masallaci da safe in wuce kano ina son in cigaba da sana'ar da na bari ne, kabiru yace to baba kanada kudi ne, malam ado yace eh ina dashi ya fito mishi da dubu 200 yace dubu dari sadakin zulfa ne, sai wannan kyauta sirikarta ta bani, kaga ya isheni in yi duk sana'ar da zanyi, kabiru yace kwarai kuwa baba amma tare zamu tafi in dinga taimaka maka dan zaman bazai yiwu mana ba gara mu hada hannu, malam ado yaji dadi sosai yace gaskiya kayi tunani sai kaje ka kwaso kayanka kuma ka sallami mahaifiyarka ya bashi dubu 5 ya kai mata, kabiru ya tashi ya wuce cikin farin ciki dan dama ya gaji da zaman banza.....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ●● ZULFAH ●● 1⃣2⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Zulfa'u na zaune cikin mota a takure, anty laila na dan janta da hira jefi2, sai dai tayi murmushi kadan, amma a tsorace take sosai saboda rashin sanin inda zasu, in ta tuno malam saleem yasan su sai hankalinta ya dan kwanta,
Mummy ta kalli laila tace yamma tayi laila da kunje shopping kin siyo mata duk abun da bata dashi amma gobe da wuri sai ku fita ko, cikin girmamawa laila tace Allah ya kaimu mummy,
Kallon unguwar zulfa takeyi tsoronta ya kara zurfi saboda bude wani tankamemen gate da akayi tun daga waje taketa kalle2, hankalinta a tashe sojoji suka bude musu kofa suna sara musu, idon zulfa ya ciko da kwalla anty laila tace fito muje mana, ta fito a hankali suka jera suna tafiya har cikin gida, sanyin kamshi ne ya daki hancin zulfa da aka bude kofar, anty laila ta kamota suka bi bayan mummy suka shiga da sallama,
twins suka rugo da gudu suka dane jikin mummy, ayda na bacci a gefen anty amarya, mummy ta saukesu tace nagaji dayawa ku bari in huta ko sweeries,
suka daga kansu suka koma jikin anty laila suna bata labarai na shirme,
Anty amarya ta kalli mummy da ta zauna tana maida numfashi tace kun dade yaya, da har zan bi sahu ta fadi cikin zolaya,
laila suka karasa cikin parlon zulfa ta tsuguna ta gaida anty amarya, ta amsa tana murmushi tace wannan yar kyakyawar fa laila a ina kuka samota,
mummy tayi murmushi ta kalli laila tace kuje ciki laila, ki kaita ďaki daya a bangarena kisata tayi wanka, anty laila tace mummy wai da mu tafi side dina in tayi wanka sai taci abinci anjima sai in kawota dakinki, mummy tace to ba laifi duk yadda kikayi Allah miki albarka, tace ameen taja zulfa suka wuce bangarenta tare da twins,
Mummy ta kalli anty amarya tace yarinya na samo a gurin sauka, yarinya marainiya kuma mai hankali, gata abin tausayi, ta kwashe duk labarin zulfah wanda taji ta fada mata,
anty amarya ta dinga gyada kai cikin tausayi tace Allah sarki har naji tausayinta, mummy tace kedai bari yarinyar ta shiga raina lokaci guda shiyasa na nema wa abba aurenta saboda nutsuwarta kuma an bashi har an daura auren,
ba anty amarya dake zaune ba hatta jalila da sanah da suka dawo daga garden lokacin saida suka girgiza,
jalila ta kalli sanah da idonta yayi ja sannan ta zagayo ta gaban mummy, tace mummy wani abban, mummy ta harareta tace inada wani abba da ya wuce sadeeq ne,
sanah ta ruga daki da gudu zuciyarta na tsananin bugawa gaba daya ta nemi kuka ta rasa,
Anty amarya tayi kokari matuka ganin ta boye bacin ranta amma ta kasa, saboda sau biyu kenan mummy tanayi mata haka, tun akan nurain da taso kanwarta Aneesah ta aura har sun gama magana da daddy, kawai washe gari mummy taje ta auro mishi yar aminiyarta,
anty amarya ta kalli mummy ta kirkiro yake tace Allah ya sanya alkhairi,
mummy tayi murmushi tace ameen a fili amma a zuciyarta tace sai dai ranki yayita baci, ta mike tace bari in dan watsa ruwa bata jira jin amsar ta ba ta wuce hanyar sama tana kwala ma jalila da tabi sanah daki kira, jalila ta fito da gudu tabi mummy samah,,,

Anty amarya zaune a dakinta tana rarrashin sanah dake kuka kamar ranta zai fita, dan mummy ta rikirkita mata plans dinta,
wayarta dake gefe tanata faman kuka tasan sadeeq ne amma ko kallon wayar batayi ba, kiran ya ishi anty amarya ta dauki wayar,,
'"Hello" tace babu dariya a fuskarta, daga daya bangaren jikin sadeeq har rawa yakeyi ya dauka sanah ce ta dauka, yace sweet baby menayi haka kika zabi ki yi min irin wannan ukubar, kinsan in banji mur--- anty amarya ta katse shi da cewa ba ita bace abba nice, yayi murmushin jin kunya yace anty ina wuni, lafiya kadai tace mishi, yace anty sanah bata da lafiya ne, cikin kissa anty amarya tace lafiyarta kalau, ka saurareni da kyau abba, daga yau karka kara kiran layin sanah, kayi biyayya ga zabin mahaifiyarka, ka bar sanah itama Allah ya hada ta da mai sonta,
cikin kidimewa yace anty ban gane abinda kike nufi ba, ta rage muryarta ta fara ďan kukan munafurci tace abba bansan me yasa yaya bata kaunata ba, duk irin biyayyar da nake mata bata gani,
a kullum burina in hada zuria daku amma yaya sam bata kaunar hakan, anyi na aneesah ya wuce ban damu ba, saboda shi dama nurain bai ce yana sonta ba, amma yanzu kowa yasan irin soyayyar da kukeyi da sanah har muna fatan kuyi aure shine yaya tayi ma sanah wulakanci sosai akanka har karshe taje ta auro maka wata yarinya yar talakawa wanda basu gaji arziki ba, irin yaran da burinsu su aureka ka mutu suci dukiya, ta kara fashewa da kuka tace Allah ya sani inason jinin yaya Aisha da jini na, saboda ban haihu a cikinku ba shiyasa nakeson wani ya auri jinina in ya haihu ko na mutu baza'a manta dani ba, sadeeq ya kara rudewa yace anty dan Allah kiyi shuru waye ya fada miki wannan maganar, ya za'ayi ayi min aure ba tare da sanina ba,
anty amarya tace walhy da gaske ne abba, amma kayi hakuri kayi ma mahai--- karki ce inyi mata biyayya anty ya fadi cikin daga murya kamar zautacce, yace wallhy bazanyi biyayya akan abinda zai cutar dani ba,
yanzun nan zan kira mummy ta warware auren da ta dauko ma kanta,
da sauri anty amarya ta katse shi cikin kwarewa a iya bariki tace karkayi haka, ka nuna musu bakasan zancen ba in ba su suka tare ka dashi ba, in ba haka ba ni zaka jawa masifa kasan banason duk abinda zai bata ran yaya ta karasa fadi tana kanne ma sanah ido, dan tasan sadeeq ya shiga tarkonta....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ●● ZULFAH ●● 1⃣3⃣
By Aysha Ya'u Kurah

A hankali yace to anty amma dan Allah kuyi hakuri,
tace babu komai kaima Allah ya baka hakurin juriyar rashin sanah dan tausayi kuke bani dukkanku, gata nan banda kuka babu abinda takeyi,
kuka ne kadai sadeeq baiyi ba, yace bazan iya rabuwa da ita ba anty, ko me za'ayi sai dai ayi wallhy dan sanah ta zama wani bangare a zuciyata dan haka ki ma daina wannan maganar,
anty amarya tace dole kayi hakuri da ita ab-- ya katseta da sauri yace anty bani sanah pls,
tayi murmushi dan tasan sanah ta diga mishi dafinta mai wuyar goguwa lallai ta samu damar aiwatar da kudirinta ta hanyar sadeeq,
ta kwantar da murya tace bazai yiwu kayi magana da ita ba kayi hakuri kawai Allah ya hada kowa da rabonshi tayi saurin kashe wayar tana murmushin mugunta,
ta kashe wayar gaba dayanta, ta kalli sanah tace mun kama sadeeq sanah, tabbas zai bijire ma mahaifiyar shi, ni kuma zanyi ta hura wuta ta a can kasa tsakanin dukansu ukun, daddy, mummy da shi sadeeq,
wannan karan sai nayi nasara akanta dan haka gobe ki shirya ki tafi kuma karki kara daukar wayarshi ke kima canza layi nasan bazai jure ba zai biyoki, ke kuma sai kisan yadda zakiyi ki rikita shi ya dawo ya saki waccen sauran yunwar,
kinga anan komai zai dagule sai insan yadda zanyi in jawo abba jikina ta yadda zamu cin ma burin mu,
sanah ta share hawayenta tayi murmushin jindadi zuciyarta tayi sanyi dan bata jin zata iya rayuwa ba tare da sadeeq ba...

******
Sadeeq juyi kawai yakeyi wani abu ya tokare mishi maqogoranshi,
kuka
kawai yakeson yi amma ya kasa, meyasa mummy zatayi mishi haka, wace irin mace mummy ta aura mishi?
Tambayoyin da ya dinga yi kenan ya kasa samun amsoshinsu,
yayi huci ya daga murya yace gaskiya mummy sai dai kiyi hakuri amma bazan iya zama da macen da bana so ba,
shi a tsarinshi yafi son mace wayayya mai aji amma shi sam bazai iya zama da irin macen da mummy ke kwaso musu ba,
yayi tsaki ya kara kiran layin sanah karo na na ashirin da uku ya kara jinta a kashe,
ya wurgar da wayar ta fadi ta fashe ya buga hannunshi a bango yanajin wani irin zafi a ranshi,
bazan iya jure wannan punishment dinba bazan iya baaaa ya fadi da karfi,
dole ya nemi hutu ya dawo gida yayi solving problems dinshi, dole ya ganar da mummy kowa yanada yancin yin abinda ya keso, ya wuce bayi a fusace ya sakar ma kanshi ruwa yanajin tsanar duka yan gidansu saboda suna neman rabashi da ruhinshi, bazai kara nemansu ba sai dai kawai su ganshi...

lailah tsaye gaban mudubi tana tsefewa zulfa kanta da yayi mugun datti, tanayi tana goge hannunta saboda dauďar tayi yawa,
tace ke kuwa yaushe rabonki da tsifa kinga kanki yanda yayi datti ya cukurkuďe, zulfa tayi murmushi cikin kunya tace hmmm kawai,
laila na gama mata tsifa ta taje mata tayi mata parking dinshi a tsakiyar kai, laila tace gaki da gashi amma saboda rashin gyara ya dunkule guri ďaya, shi kanshi ya galabaita ta fadi tana dariya,
zulfa tayi murmushi a ranta tace inata kaina wake ta gashin da na manta rabona da budeshi,
anty laila tace tashi ki cire uniform din nan muje in nuna miki komai na bayi sai kiyi wanka a kaiki saloon, ta mike tace to, sun kusa da bayin jalila ta shigo da sallama, anty laila ta amsa tace jalee ina kuka shiga ne, jalila ta ajiye doguwar rigar da mummy ta bata bayan ta gama mata tatass kuma tace tazo gurinsu lailan ta dinga Jan zulfa'u a jiki,
ta kalli anty laila tace muna garden ne,
tayi murmushi tace amaryar yaya abba sannu,
zulfa ta tsuguna tace ina wuni, jalila ta kwashe da dariya tace tashi ni ba ruwana kar ki kara tsuguna min kisa mummy ta yi punishing dina da fushinta,
laila tayi dariya tace ai fa, ta ďago zulfa suka wuce bayi,

jalila ta rike baki tana mamakin mummy, yarinyar tana da kyau amma tayi karama da yawa, yadda yaya abba keji da kanshi, yan mata masu aji ke kawo kansu ya kare a wannan kucakar, lallai akwai bala'i in ya dawo, ta kwantar da kanta kan kujera.....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ●● ZULFAH ●● 1⃣4⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Washe gari tun kafin asuba zulfah ta farka saboda ta riga ta saba lokacin nayi bacci zai kauracewa idonta, ta dinga bin dakin da aka kaita ta kwana da kallo karo barkatai dan tun da aka shigo da ita take kare ma dakin kallo barin toilet din da yaji kayan gyara,

Tashi tayi a hankali ta shiga bayin tayi tsarki ta kunna ruwa kamar yadda jalila ta nuna mata tayi alwala, tsayawa tayi gaban mudubin bayin tana kare ma kanta kallo, sai da ta dan dade sannan ta fito ta shimfida dadduma tayi nafila kafin a kira sallar asuba,, karantun qur'ani ta dinga yi da "ka" batare da ta duba qur'ani ba,
har aka kira sallah tana karatu tana idarwa ta mike tayi sallah, ta zauna tana addu'oi tana tuno rayuwarta ta baya, ko yanzu me goggo takeyi tasan tana can tana aikin waina, haka ta dinga tunanin su goggo da salaha da babanta, ta share kwallar da ta digo mata a idonta ta karasa adduointa ta nade daddumar ta maida ita mazauninta,
Kofar dakin taji an bude ta waigo suka hada ido da mummy,
ta karaso ciki itama da hijab da carbi a hannunta tana murmushi,
zulfah ta durkusa da sauri tace ina kwana, mummy ta dagota tace lafiya lau zulfa'u ya kwanan bakon guri, zulfah ta sunne kanta tace lafiya lau,
mummy tace to alhamdulillah ki saki jikinki kema yar gida ce, banason wannan dari darin da kikeyi, da ke da laila da jalila duk daya kuke a gurina, saboda haka ki daukeni matsayin uwa kinji,
Zulfah tace to in shaa Allah, mummy tace yauwa diyata, bari inje daki kema ki kwanta ki huta kafin a kawo miki abin kari,
zulfah tace to, amma babu wani aikin da zanyi, mummy tace a'a je ki kwanta ki huta kinji, zulfa ta gyada kanta ta koma ta zauna bakin gado,

Gurin karfe 9 jalila ta turo kofar dakin, lokacin zulfah na tsaye tana goge jiki, ta juyo da sauri zata tsuguna jalila ta hade rai tace tashi2, wai so kikeyi kija min bala'i ne, na fada miki karki kara tsuguna min bakiji ba ko, ki rufamin asiri mu dinga gaisawa daga tsaye,
kuma ki saki jikinki kinji? Zulfah tace to, jalila tace yauwa, yanzu ki shirya ki fito mu karya ta ajiye mata doguwar riga a kan gado ta fita,
zulfah ta duba rigar taga katuwa ce irin ta jiya, har kasa take kai mata, ta koma gaban madubi, mai kadai ta shafa ta dauki rigar ta saka ta rufe kanta da gyalen ta sakko parlon, a bangaren dining taga mummy da jalila suna zaune suna hira, karasawa tayi ta tsuguna ta kara gaida mummy,
mummy tayi murmushi tace ai mun gaisa zulfa'u tashi ki zauna anan, ta nuna mata kujerar kusa da ita, zulfa ta zauna cikin jin kunya tana ta sinne kai, jalila tayi srvn dinsu mummy da kanta ta hada ma zulfa tea mai kauri ta tura gabanta tace maza ki shanye duka, zulfa tace to, da kyar kunya ta barta ta fara cin dankali da sauce din hanta, a tare suka gama karyawa dukkansu, mummy ta koma cikin parlon ta zauna, zulfa ta taya jalila kai kaya tsaftataccen kitchen din da kamar ba anan ake girki ba,
fatsin ce tsaye a ciki tana wanke2, zulfah ta karasa kusa da fatsin tace kawo in tayaki, fatsin ta wage baki tace a'a jeki abinki ay na kusa gamawa, zata kara magana jalila taja hannunta tace zo mu tafi ciki mummy zatayi fada in taga kina aiki,
parlor suka wuce zulfa ta rabe gefen kujera, mummy tayi murmushi a ranta tace da sannu zaki saki jiki,

sai da suka dan dade sannan mummy tace zulfah ajinki nawa a school, zulfa tace js3 nake zan shiga ss1, mummy tace wace makaranta kikayi, ta kara sunkui da kanta tace nayi l.g.e.a unguwar rimi dana gama malam salim ya samo min capital school,
mummy tace gud, kina sha'awar cigaba daga ss1 din,
jalila tayi dariya tace haba mummy me zai hana tayi sha'awa, ai kawai gara in anyi resuming ta dinga zuwa ko,
mummy zatayi magana shewar da taji ta katseta, daga kanta tayi taga sanah janye da trolley anty amarya rike da jaka, har suka karaso cikin parlon basu kalli inda su mummy suke ba sai hirarsu sukeyi suna dariya,
sai da suka zo dapp dasu anty amarya tayi murmushn rainin wayau tace yaya ina kwana, mummy da mamaki ya cika ta tace lafy lau,
sanah ta kara gyara dankwalinta tana kallon zulfa'u tana kas kas da cingam,
ina kwana zulfah ta fadi hade da kara tankwashe kafa, suka mata kallon uku saura kwata, sannan sanah ta kwashe da dariya harda rike ciki,
anty amarya ta dake cikin kissa tace banason iskanci wuce mota gani nan, ran mummy ya baci sosai da abinda sanah tayi mata dan ko gaishe ta batayi ba,
anty amarya tace yaya bari in kai sanah gidan aneesah,
mummy tace to a dawo lafiya, bata jira jin abinda zata ce ba ta kalli jalila tace tashi kuje gurin laila in ta gama kuzo ku tafi shopping din, jalila tace to mummy suka mike suke wuce side din laila, mummy ta mike tayi hanyar sama ta bar anty amarya tsaye tana hararar bayanta, sai da ta gaji dan kanta tayi kwafa ta wuce waje tana sakar zuci....

Mrs tijjani shattima....
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 1⃣5⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Sai gurin 11 suka fita, saloon suka fara zuwa aka wanke mata kanta da kafa,
daga nan suka wuce kasuwa sukayi siyayya sosai, atamfofi, laces da material takalma sai sarkoki, sun kashe kudi sosai a kasuwa,
a hanyarsu ta komawa gida suka biya passion trust suka kwaso mayuka da turaruka masu kyau da tsada, zulfa dai kallonsu kawai takeyi kamar basu jin zafin kudin haka take fadi a ranta,
"senegls" nan suka je karshe inda tela ya gwada zulfah,
jalila tace kayi mata styles masu kyau fa,
ina material dina, yace saura kadan kinsan aikin akwai wahala, tace haka dai ka ke cewa ka iya yawa wollah,
yaushe zaka kawo wadannan to, yayi jumm sannan yace tunda express ne kuma kunce Inji mummy zan gama nan da 1mnt, anty laila ta rike baki tace lallai Hayatu baka da m, ka bari sai nan da shekara daya ma wannan kai da mummy,
Hayatu yayi dariya yace anty kayan da yawa zanyi kokarin gamawa cikin 1wk in shaa Allah, anty laila tace now u r talkn,
jalila tace Allah yasa dan ban yadda ba, hayatu yace aiko zan baki kunya,
tace da dai wani ne bakai ba, ta fita tana dariya...

Sai yamma likis suka dawo gida a gajiye, anty amarya suka tarar zaune a parlo tana waya da sadeeq itama dawowarta gidan kenan, sannu da gida suka ce mata gaba dayansu sannan sukayi hanyar dakin mummy,
tayi tsaki mai karfi ta cigaba da wayar da takeyi,
sadeeq yace anty ke da wa kike tsaki kuma, tace ni da wadannan kitifaffun mana, wai daukar wannan yar kauyen sukayi suka yo mata shoppn, jalila harda rungumeta saboda munafurci,
yayi tsaki yace duk zasu gane kurensu anty, ina nan dawowa nan kusa zan warware duk kullin su, ni dai dan Allah ki taimakeni ki fadamin numbr da zan sami sanah, wallhy ina cikin tsananin damuwa,

Tayi murmushin mugunta tace abba kayi hakuri da maganar sanah, ni banason tashin hankali, karka kara kirana ma bare ayi tunanin ni ke zuga ka, cikin damuwa yace haba anty, so kikeyi in mutu ko kuma wani ciwo ya kamani, wallhy na kasa maida hankalina a karatu, kirjina zafi yake min, meyasa sanah zata hukunta ni akan laifin da bansan dashi ba,

Anty amarya zuciyarta wasai dan taga alamun daga zuciyarshi yake fadin wadannan kalaman, a hankali tace dukkanku hakuri zakuyi, dan itama sanah tana can bata ko iya cin abinci,
Cikin damuwa yace can ina anty, tace ta tafi ay, muryarta ta dan fara rawa tace yau tun safe yaya tayita zaginta akan yarinyar nan,
zagi sosai tayi mata har jalila na sa baki,

Sadeeq ya dafe kanshi yama rasa me zece, shurun da anty taji ne yasa tace kana jina abba, uhmm kawai yace mata, tace kayi hakuri kayi ma yaya biyayya, ka cire---- sallamar nurain ce ta katse mata maganar, tayi saurin kashe wayar suka gaisa cikin sakin fuska, sai da yayi gaba tabi bayanshi da harara, aladar anty amarya kenan kowa a gidan haka take mishi sai kun gaisa ko kun gama magana da ita cikin sakin fuska sai tabi bayanka da harara, ta tsani yaran gidan da mahaifiyarsu amma saboda tsabar iya bariki da kissa babu wanda yake ganewa dan nunawa takeyi tafi son su akan mahaifansu, wannan dalilin yasa daddy yake girmamata saboda tana nuna ma ya'yanshi da matarshi so da kulawa ta karya, ta dade tana neman dalilin da zai haddasa fada a gidan sai yanzu ta samu wannan damar daga gurin sakarai sadeeq....

Mrs tijjani shattima..
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 1⃣6⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Tavern hotel nan naga motar da sanah ta shiga a bakin titin governr rd tayi parking,
Wani hadadden gaye ne ya fito daga cikin motar ya zagayo gefen sanah ya bude mata kofa,
ya rungumota suna tafe suna hira har suka kai ciki,
a kofar shiga ne sukayi karo da wani saurayi shima kyakykyawa, baya ya koma da sauri yana fadin sorry pls, suka hada ido da saurayin da suka shigo tare da sanah, bude baki sukayi dukkansu suna dariya, saurayin dake
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment