Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

amarya,
ka tsoraci sharrin mai sharri inji hausawa, haka in baka iya kama barawo ba to tabbas shi zai kamaka,
wanda duk ya iya kulla wannan sharrin to ba karamin devil bane sai da dabara za'a iya kayar da ko ma waye, anty laila tace haka ne to yanzu ya za'ayi mu maida wannan shaidar ta zama mai karfi,
good saleem ya fadi yana gyyara tsayuwar hularshi,
yace wannan maganar a kebantaccen guri zamuyi yanzu muna fita daga nan dan zuwa gobe in shaa Allahu zamu fara aiwatar da aikin ...

Farouk ne tsaye kofar dakin sadeeq sanah na zaune tana jefo mishi hira jefi jefi saboda rashin sabon da basuyi ba,
shigowa dakin yayi gaba daya ya zauna suna hirah cikin dabara,
can ya shafa cikinshi yace wallhy yunwa nakeji anty sanah, ran sanah yayi fari kal dan a tunaninta yanzu sun fara sonta saboda abinda zulfah ta aikata,
mikewa tayi tana murmushi tace bari in dafa maka ko indomie ce,
ya gyara zama sosai yace aiko da kin kyauta min,
ta wuce kitchen tana murmushi, farouk ya saci kallon sadeeq dake kwance idonshi a lumshe ya mika hannunshi gefen da sanah ta tashi ya dauki wayarta cikin sauri ya shiga contact dinta yayi searching sunan "Beeba Gee" ya gani ya dauka da sauri sannan ya mayar da wayar ya ajiye,
kwala mata kira yayi da karfi har saida sadeeq ya dan razana ya bude idonshi yana tsaki yace tashi ka fitar min a daki,
farouk ya mike bai mishi magana ba ya deka yace bari inje in dawo ki ajiye min,
tooo sanah ta fadi da karfi itama,
farouk ya fita yana waka yana murmushi dan ya gama abinda ya kawoshi,
tsakii sadeeq yaja ya mike ya wuce ciki dan ya kwanta ya huta,
Farouk da sauri ya karasa dakin anty lailah yace angama anty, komai yayi dai2, anty laila ta karbi wayarshi tana dariya tace yauwa dan kanina shiyasa nake sonka wallhy duk kafi manyan banzan can hankali,
ta kirah saleem tace ga numbr nan an samu,
yace to ta turo mishi da ita "Asap" tace yanzu kuwa ay ba maganar sanya,
ta kashe wayar ta tura mishi number suka cigaba da tattaunawa da farouk har saida nurain ya dawo sannan ya bar dakin...

Oh my God khady zo kiga wani abun ala'ajabi,
khady ta mike daga kwanciyar da tayi daga ita sai daurin kirji tace lafiya beeba,
beeba ta mika mata wayarta tace kati ne kin ganshi nan na 20k aka turo min,
khady ta karbi wayar da sauri tace waye wannan,
beeba tace wallhy ban sani ba, ko ma waye ay zai biyo baya, dama yanzu na gama maular katin 400 sai gashi na samu wannan a bagas, ay ko mistake din numbr akayi wallhy bazan mayar ba yanda nake jin garin nan, yanzu ma zan samu in siyar da na 15k wallhy, khady tace gaskiya ki siyar ko zamu samu nacin abinci,
beeba tace kwarai kuwa ay wannan tsuntsune daga sama gasashshe dama tun jiya nake kiran wannan yar iskar taki dagawa, wallhy sanah tana wasa dani,
khady ta tabe baki tace ay wannan yar akuya ce,
matar da kuna tare tana cikin daula har yanxu ta kasa baki jarin 500k ma, me akeyi da ita, ni wallhy ko kadan bata raina tunda maza kadai ke cin moriyarta,
beeba tayi kwafa cikin bacin rai tace kedai bari ashe dai bani kadai ce ke wannan tunanin ba,
ki bari kawai tym nake jira wallhy in naso samun milyan ma sai na sameshi a gurinta, khady zatayi magana wayar beeba ta fara ringing,
beeba tace ke numbr da aka turo min da katin nan ne aka kira da ita,,
tayi jimm kamar bazata dauka ba dan kar yace ta dawo mishi da katin,
sai da ya kira sau biyu sannan ta dauka taji ance heeyyy cutie how are u,
cikin rawar murya tace fyn, yace sunana Nurah Aliyu majeh,
ta mike tsaye tace Nurah aliyu majeh, yace yess, tace u mean kai dan ministern abuja ne Hon Aliyu Majeh,
yace yesss dear murya na rawa tace ina wuni,
yace lafiya lau ya kike ya 2days, tace lafiya lau,
yace gaba daya yanzu kun daina shigowa abuja, ina kawarki sanah,
tace tana gidan mijinta, yace ohhh so tayi aure kai am happy 4 her,
dazu na karbi numberki a gurin wani guy da yake kawo min mata in na dawo nigeria so da naga hotonki sai naji kinyi min kuma dama ina yawan ganinku a sharaton ke da kawarki,
Allah yasa u are ready to spend dis wknd wv me,
jiki na rawa tace why not, ko yanxu kakeso inzo ay zaka ganni, isma'il sukayi murmushi shi da saleem sannan yace no ba yau ba kin ga yamma tayi,
ki bari gobe zan turo miki da transport sai kizo ko,
tace ehh to Allah ya kaimu,
yace ameen ina jiran account numbr bye, tace ok bye,
tana kashewa ta daka tsalle ta tura mishi accnt no,
murna suka dinga yi da khady, beeba ta dinga godewa Allah da yasa tace sanah tayi aure da tasan sanah zaice yana so saboda kyanta,
tana cikin wannan tunanin taji alert na 30k, wani ihun sukayi ita da khady harda rawa dan a ganinsu banza ta fadi,
wanka tayi ta dau atm zata banki da kasuwa siyo turaruka da kayan mata,

su beeba anga masu gidan rana

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: Aysha Ya'u Kurah: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 6⃣3⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Zaune suke a harabar cikin gidan cikin wata yar bukka suna hirah, feenah ta fito musu da juice ta zauna itama suna hirar tare tanata basu labarin ban dariya,
horn sukaji anyi da sauri mai gadi ya wangame gate din wata bakar glk350 ta kunno kai cikin gidan, da sauri feenah ta mike ta karasa gurin tana fadin yaya mukhtar oyoyo ya karasa parking ya fito ya rungumeta yana murmushi yace feenah ya kk,
tace am fyn broo ta dauki jakarshi dake cikin motar ta wuce ciki tana murna, saleem da isma'il suka gaisheshi ya amsa suna shiga cikin gida yace irin wannan zuwan na bazata iloli, isma'il ya sosa kanshi yace wallhy kuwa aiki ne ya kawo mu, dai2 lokacin suka shiga parlor, yace aikin me kuma,
suka zauna isma'il yace wani case muka zo yi a kaduna, muna sa ran komawa daga an gama in shaa Allahu,
Mukhtar yace okk Allah ya taimaka case din menene, isma'il yace wallhy case din kisan kai ne yau saura 5dys a koma kotu amma har yanzu bamu da kwakwarr shaida ko guda, mukhtar yace Allah ya fitar daku, kwanan nan kisan kai kawai akeyi ko ina a fadin nigeria last three weeks da suka wuce ma an kashe alhj hasheem marafa,
mutuwarshi tayi touching dina sosai saboda ana gobe zai mutu we met a england yaje duba lafiyarshi ranar ma na fara ganinshi, mutumin kirki wallhy,
saleem ya kalli isma'il suka hada ido, ismo yace yaya case din da mukeyi kenan abun akwai rikitarwa sosai, yanzu haka wacce ake zargin ta kashe shi ita muke karewa,
ya gyara zamanshi yace wallhy yaya abun akwai rudu a cikinshi nan suka warware mishi komai har dawowar da yayi mummy ta tambayeshi yace damuwarshi akan matar danshi ne,
da kuma wayar da yayi wa sadeeq duk saida suka fada mishi, mukhtar ya gyara zamanshi cikin rudu yace wait isma'il u mean matan shi dan nashi biyu ne, saleem yace eh biyu ne amma bai fadi wacce yake nufi ba, kuma sai akayi sara a akan gaba dan a ranar aka samu nasarar kashe shi abin da yasa aka karkata abun kanta saboda ita tayi girkin kuma dayar matar tashi bata kasar wannan dalilin ne yasa gaba daya aka daura kisan a kanta,
sann-- wayar isma'il ta shiga kara numbr beeba ya gani ya mike dan ya tabbatar ta iso yayi ma saleem alama da ido yace bari inje in dawo yaya dan aramin motarka,
mukhtar ya mika mishi keyn da sauri yana son jin karashen labarin, isma'il ya karbi keyn har ya fita ya dawo ya wuce daki ya fito da jaridar da suka sa aka nemo musu ita saboda zata taimaka musu yasa kai ya fita daga gidan,
mukhtar ya kalli saleem yace ina jinka, saleem ya cigaba da bashi labarin yadda akayi mata sharrin zinah kuma aka ce dan ya kamata tanayi ne yasa ta kasheshi,, mukhtar ya share gumin da ke fita a fuskarshi yace yanzu ita dayar matar dan nashi fa, sun rabu ne ko kuwa,
saleem yace a'a suna tare, mukhtar ya boye tashin hankalinshi yace to Allah ya bayyana gaskiya bari in dan huta inci abinci dan madam tun dazu take ta safa da Marwah saboda ta janyeni daga sauraron hira,
anty husaina dake tsaye a dining room tace karka min sharri malam in zaka koma ka koma, yayi dariya ya wuce ciki...

Kwanan beeba biyu a abuja banda kisan kudi babu abinda ismo ke mata,
bai taba kusantarta ba saboda mugun kyamar ta da yake ji, duk lokacin da ta bijiro mishi da bukata zaisan yadda yayi ya kauce,
abinda yasa abun bai damunta saboda makudan kudaden da yake narka mata,

a daren ranar da suka cika kwana uku ya shigo hotel room din ya zauna yana maida numfashi, mikewa tayi cikin karairaya ta isa gabanshi ta durkuso tana shashshafashi, yayi dan tsaki ya ture hannunta,
cikin tashin hankali tace lafiya kuwa, wallhy raina ne yake a bace saboda wani aikin da ya kamata ace ni nayi shi wata ta rigani ya fadi yana duba jaridar hannunshi, kallon jaridar beeba keyi itama
kafin tayi magana wayarshi ta yi kara, yasa hannu ya dauka yace dad yanxu na karasa gida,
daga daya bangaren saleem ya kaurara muryarshi kamar ta babban mutum yace Nurah goben ka shirya ka tafi kadunan duk yadda ake ciki ka nemi mahaifin yarinyar nan dan naji ance shi kadai gareta ka tabbatar ka bashi 100milion din da nace maka, isma'il ya ce dad nima zan kara mishi 50m saboda jin dadin abinda daughtern shi tayi, naso ace ni na kashe chief hasheem da hannuna saboda in samu ladan kawar da bata gari irinsu,
ay wannan yarinyar ba karamin jihadi tayi ba dad ta rage mugun iri kaga ko an kasheta aljanna direct saboda su kansu masu shariar basu san waye hasheem marafa ba, mutumin da zai yanka jariri ba tausayi yaci namanshi,
ay da tun da wuri nasani bazan taba yarda a kama yarinyar ba amma gobe da kudi masu tarin yawa zansa a kori shariar kuma in bata makudan kudi na ban mamaki wanda ba tun yau ba nayi alkawarin duk wanda ya kashe alhj hasheem zan bashi, daga daya bangaren akace goben ka fita da wuri dan mu samu nasarar korar karar kafin a shiga kotu, sannan ka fada ma mahaifinta su bar kasar nan gaba daya, nan suka cigaba da ruda beeba da fadin kudade masu yawan gaske sannan suka kashe wayar,
ta wutsiyar ido ya kalli beeba duk yanayinta ya canza saboda jin nairah,
ya dan tallabo fuskarta a hankali yace baby gobe zan je kaduna,
ta hadiye miyan dake bakinta tace tare zamu tafi kenan,
yace anya jirana zakiyi dan so nakeyi jibi in samu full tym a jikinki dama wannan alamarin shi ya tsare ni na kasa samun lokacinki,
yayi murmushn jin dadi yace yau daddyna na cikin farin ciki har yayi kyautar kudi masu yawa beeba, ni kaina saboda farin cikin da yake ciki zanyi signing blank check in bawa yarinyar nan da mahaifinta ko da kuwa 1blin zasu cire,
tace waiiii gaskiya sun gama arziki wadannan, ismo yace kwarai kuwa ay burinmu ni da dad shine mu ga bayan hasheem in kuma wani ya rigamu mu bashi kudin da yafi karfin ganinshi dan ni sau uku ina atmptn kashe shi ban samu dama ba,, beeba ta shiga rudun ganin zulfah zatayi gaining akan abunda suka aikata,
na farko za'a fito da ita, na biyu zunubin kisan nasu ne ita da sanah, na uku kuma shi yafi komai daga hankalinta jin irin makudan kudin da zulfah zata caska,
nan da nan idanun beeba suka rufe tace nura da gaske kakeyi akan maganar kudin nan?,
yace haba baby ay kinsan dai ni bana karya bari ma ki gani, ya dauki biro da check book yace kinga wannan account din akwai fin 1bln a ciki shine mafi karanci a kudade na na bankuna, signing yayi ya nuna mata sannan yace gobe ana fito da yarinyar zan mika mata muje tare in ciro mata alkawarinta,
beeba taga blank check muraran gaba daya basirarta ta toshe,
can wata kasa take hangota tana fantamawa cikin naira, a zuciyarta tace to meye ma na jin tsoron fadi tunda waccan ma fito da ita za'ayi a kori karar gaba daya,
tayi ajiyar zuciya ta kalle shi sosai tace wata magana nake son muyi dakai, bai kalleta ba yana kallon waya yace ina jinki baby,
tace to ai bansan yadda zaka dauki maganar bane ta yiwu ka karyata ni,
ya mike tsaye ya isa wata kusurwa a cikin dakin yace ina zuwa baby,
yana zuwa ya manna camera ya saita ta sosai inda suke, ya dawo ya zauna ba tare da tasan abun da yayi ba saboda kankatar camerr,
dagota yayi sosai ta inda fuskarta zata haska sosai,
sannan yace ina jinki baby, tace amm dama sai kuma tayi shuru, yayi mata peck a kumatunta yace go ahead fadi koma meye kinsan zanyi miki,
tace maganar wadannan kudin da kake cewa zaka bawa yarinyar da tayi kisan nan,
ya yi murmushi yace kwarai zan bata ke in takaice miki goben nan ni da lawyern dad dina zamu tafi kaduna ko nawa ne sai mun kashe yarinyar nan ta fito kuma mu bata kudin da zasu bar kasar nan ita da dad dinta,
beeba tayi murmushi tace yanzu fa in nace maka ina da hannu a kisan nan sai kace karya nakeyi dan kudin da zaku bayar ne ko, yace yess karyata ki zanyi mana tunda me zai kaiki gidan har ki samu damar zuba mishi guba,
beeba tayi murmushi tace to bari dai in daina kumbiya kumbiya wallahi kaji na rantse maka ko, yace eh, tace ko alqurani aka bani zan dafa ba karya zan fada ba, yace uhum inajinki, tace wallhy akwai hannuna a cikin wannan kisan,
yayi dariya yace babyna bansanki da kar ya ba ya akayi har kika shiga gidan duk irin tsaron dake ciki, tayi murmushi tace ni kawar matar danshi ce,
yace u mean ke kawar wacce tayi kisan ne, tace a'a ba ita ba kawata sunanta sanah, wallhy waccan bata san komai ba,
isma'il dake Zaune a gurin da saleem dake kallo tru laptp suka dinga adduar Allah ya cigaba da ingiza zuciyarta ta fada, Allah ya kara dode mata basira ta fadi komai, isma'il yace yanzu baby kina nufin kune kuka kashe shi, ta kara gyara zama tace yess, yace wow kuma yayi ruining life dinku kenan kamar yadda yake ma mutane,
tace eh to kawata yaso yasa a koreta a gidan, kuma sannan she hate wannan kishiyar tata saboda mijinta ya juya mata baya saboda ita, nan ta fara rattafo labarai bata rage komai a ciki ba sai na wayar da aka kawo hoton zulfah tsirara dan bata da idea akan wanda ya aikata,
nan da nan saleem ya katse camerar daga lptop dinshi,
shi kuma isma'il rungumeta yayi yace wow gaskiya kin biya ni baby,
ya dauki blank check ya mika mata jikinta na rawa ta karba,,
ya kira saleem yace dad ashe ba yarinyar da ake zargi bace tayi kisan yanzu haka ma muna tare da wacce tayi kisan,
saleem cikin fada yace haba nurah ya zaka yarda da maganar mace alhalin ga wacce kowa yasan ita tayi kisan,
beeba jikinta ya fara rawa dan taga samu kuma zata ga rashi ta bude murya tace wallhy dad mune wallhy bazan yi maka karya ba,
isma'il yace sune dad tunda ta fada baza tayi karya ba, saleem yace to indai tanaso in yarda sai na ga evidence a gurinta tace wallhy zan kawo maka nurah wallhy akwai wayar da nayi text da ita ko ita zata gasgata zance na,
isma'il yace dad ka yarda da ita dan baza tayi min karya ba, yanxu dai muyi watsi da maganar yarinyar da ke kulle a yanke mata hukunci kawai kaga sai mu ba su beeba kudin ko,
yace ohk to ba matsala yanxu dai zuwa gobe sai kuje da ita ka ciro mata na wajen nawa,
isma'il yace ohk dad yanzu haka ma na bata blank check bari in bata 50k kafin goben,
beeba ta tafi duniyar tunanin wai itace yau a dare daya ta mallaki makudan kudi, tayi murmushi tace wallhy ko sanah bazan fada mawa ba sai dai taga ina juya dala,
ta dinga tunanin kasar da zata ta sakata ta wala,
isma'il ya kalleta yace baby gashi bari inje in dawo zuwa gobe sai muje in ciro miki na gurin dad ko, beeba tace to gaskiya nagode da ka yarda dani,
yace ay mu ke da godiya saboda u hlpd us alt,
tayi murmushi ta raka shi bakin kofa ta juyo tana ihu ita kadai...

Mrs tijjani shattima....
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: [20:27, 06/02/2016] Aysha Ya'u Kurah: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 6⃣4⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Murda kofar taji anyi ta juyo da sauri ta kalleshi,
yayi hanyar gurin da ya manna camera yace baby irin wannan ihun ay sai ki tara yan hotel dinnan su dauka wani abun nayi miki, tayi dariyar jin dadi tace duk cikin murna ne,
ya kai bakin kofa yace ay ni yau na fiki farin ciki, ya fita yana murmushi itama ta juya tana rawa hade da tsalle,
gida ya wuce yana parking motarshi mukhtar ma ya shigo da tashi, tare suka shiga cikin gidan suna hirah,
zama sukayi a parlo ya dauki wayarshi ya kira saleem,
ko minti biyar ba'ayi ba sai gasu sun shigo tare da feenah,
ismo ya kalleshi yace wannan sarkin surutun ta dameka ko, saleem yayi murmushi ya suka gaisa da mukhtar, saida suka gama cin abinci sannan suka koma cikin parlon suna hira cikin nishadi, ismo yace yaya alhamdulillah yau Allah ya kawo mana saukin binciken nan da mukeyi,
mukhtar yayi murmushin jin dadi yace kai gaskiya na muku murna, an gano wanda yayi kisan kenan,
ismo yace wallhy kuwa yaya da bakinta ta fada, plan muka hada mata, nan ya kwashe labarin yadda suka hada mata plan din da yadda ta auka cikin sauki ya fada mishi,,
laptp ismo ya aiki feenah ta dauko ta mike taje ta dauko ta kawo, saleem ya amsa ya kunna maganganun da beebah tayi,
cikin gigita mukhtar yace sai da nayi wannan tunanin wallhy, ismo da saleem suka kalleshi cikin rashin fahimta wane irin tunani,suka hada baki suka tambaya, ya kallesu dan baisan ma maganar ta fito ba,
ya dafe kanshi ya kalli feenah yace Nafee tashi ki shiga ciki, ta mike ta wuce daki, ya juyo ya kallesu yace tun ranar da kuka bani labarin nan saida nayi tunanin sanah ce wallhy,
dan dai bani da wata hujjar da zan nuna muku ne shiyasa nayi shuru da bakina, saleem ya gyara zamanshi yace yaya kasan ta ne,
yace farin sani ma kuwa, ya rage muryarshi saboda kar anty husaina taji shi, yace na dade ina sabawa Allah ba tare da kowa ya sani ba isma'il, kunsan dama ance komai yana da silar shiryuwarshi, to ni silar shiryuwata marigayi ne,
ya fara basu labarin tun haduwarshi da beeba da sanah a kaduna har tafiyarshi england business da yayi da ita da abin da ya faru ranar da ya kamata da wani,

Innalillahi wa inna ilaihir rajiun abinda saleem da ismo suka dinga fadi kenan a ransu,
mukhtar yace ranar da naji mutuwarshi wallhy na girgiza matuka har mutuwar ma ta zame min ayah, na dinga tunanin yanzu da na mutu ina sabon Allah in je ince mishi me, tun daga lokacin mata suka daina burgeni duk ko da irin kawo min kansu da sukeyi, ni dai burina a kullum bai wuce Allah ya yafe min ba,
saleem yayi ajiyar zuciyah yace alhamdulillah tunda har ka gane gaskiya kuma ita kofar tuba kullum a bude take ka cigaba da rokon Allah shi gafurur raheem ne, ismo yace haka ne Allah ya yafe mana baki dayan mu, ameen suka ce dukkansu sannan suka cigaba da hada shaidunsu dan tun gobe zasu tafi mukhtar kuma jibi zai iso saboda aikinshi...

Lailah ce tsaye ita da farouk a kan titin waff road motarta ta samu matsala farouk ya dago kanshi yace anty bari mu bar motar nan gurin mechanics din can gurin dan pelpon dinta ya tsinke zuwa gobe sai inzo in karba, tace oh my God yanzu sai ka samo mana napep mu karasa gida dan in muka ce zamu kira a kawo mana mota zamu dade ga su saleem sun karaso ga kuma waleed yayi bacci,
yace wannan ba matsala bane rufe motar sai in samo, ta karbi key din ta rufe motar ta kwantar da waleed a kafadunta ta tsaya jiran farouk, ko 3mints baiyi ba sai gashi ya dawo da me napep shiga ciki tayi shima ya shiga yace bari suje tare sai ya juyo ya mika gyaran motar,
a hankali suke tafiya suna hirar nasarar da saleem da ismo suka samu, me keke napep din yayi tsam yana jinsu yanata tunanin anya kuwa ba gidan da ya taba sauke wasu yan mata biyu bane da suke ta sake saken sa ma wani guba, shuru yayi musu har suka kai kofar gidan, anty laila ta fito daga napep din tana ma saleem da ya fito daga cikin mota magana,.
farouk ya fito suka gaisa ya koma napep din yace malam mayar dani muje mu dawo dan Allah, me keke napep din yace to muje, suna tafiya shuru zuciyar me napep din na kitsa mishi yayi ma farouk magana,
da kyar dai suna shan kwanan layinsu me napep din yace ranka ya dade gidan nan da na saukeku rasuwa akayi a cikinshi,
farouk yace eh babana ne ya rasu,
yace ayya Allah ya jikanshi da rahama, amma kamar naji kuna maganar kashe shi akayi ko
, farouk ya kalleshi tsaff sannan yace eh, mutumin yace Allah ya bayyana wanda ya aikata, farouk yace ameen kawai ya cigaba da kallon titi, can me napep din yace lokacin da nake drivern taxi kuwa na taba sauke wasu mata anan kofar gidan,
tun daga abuja na dakko ta tazo ta dauki kawarta suna ta hirar su nidai ina jinsu, har na sauke su suna hira daga jin hirar tasu ba alkhairi bace, dan harda maganar guba naji sunayi, duk da ban gama saurarar su ba nadai san wani suke son kashewa, dan suna sauka dayar ta mika ma dayar bakin nikab tace tasa a fuskarta, in dai takaice maka har suka fito ina gefe ina kallonsu suna dariya,
naso dawowa washe gari gida inji abinda ya faru a gidan dan in fadi abun da nasani saboda nasan inda na daukesu dukkansu dayar a airport din abuja tunda muka taho take waya, dayar kuma anan hayin banki, kwatsam na samu labarin mutuwar mahaifina a ranar, wucewa kauyenmu kawai nayi bayan na kaiwa me mota motarshi,
saida mahifina yayi sati biyu sannan aka raba gadon mu na dawo nan kaduna na siya wannan machine din dan inci gashin kaina,
ko da na dawo na bi ta kofar gidan har sau biyu to in tsoron shiga in tambaya saboda sojoji da nake yawan gani a tsaye, kar ace min dan boko haram shiyasa kawai na bar zancen,
dai2 lokacin suka isa waff road yayi parking ya juyo ya kalli farouk da ya zama kamar mutum mutumi saboda mamaki, mutumin yace dazu da naji kuna magana kuma saida jikina ya bani kuma Allah cikin ikonshi sai gamu a kofar gidan, farouk yayi ajiyar zuciya yace
"Hukumul lahu la azabun"
a zuciyarshi yace
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment