Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

wani qamshi da yaji a iskar, jalila ta jata suka dauki akwati suka wuce ciki, saida ta gama frshup cikin wata karuwar doguwar riga sannan suka fito parlor, anty amarya baki sake tace sanah yaushe kika shigo, mummy tace ay bazaki ganta ba tunda taga kawarta, sanah tayi dariya tace anty "dee" ya kike, tayi murmushi ta amsa tana cigaba da gyaran dining, sadeeq da yayi mutuwar zaune saboda kallon sanah, ya kara gyara kwayar idonshi ya tsaida su a kanta sosai, gaskiya yarinyar ta fisgeshi lokaci daya, wani irin sonta yakeji a can cikin ranshi, ta dace da irin matan da ya dade yana mafarki, shidai bai santa ba to a ina kowa yasanta a gidan su,
"SANAH HAMEED" yar yayar anty amarya ce dake zaune a abuja, mahaifiyarta yar siyasa ce babba, mahaifinta kuma custom ne, sanah ta tashi cikin gata da sangarta saboda ita kadai Allah ya ba iyayenta, rayuwar sanah gaba daya babu No a cikinta komai tayi dai2 ne, iyayenta sam basu kula da tarbiyyarta dan su a ganinsu komai tana yinshi bisa tsari, irin kayan da sana ke sawa in ka ganta zaka rantse ba musulma bace, kyakywace sosai doguwa ga kyan jiki ta hada komai na mace mai aji, sai dai hali daya mata cikas, Allah ya zuba ma sanah son kyawawan maza ko namiji baida kudi in dai kyakkyawa ne to ya gama da ita, dan sai tasan duk yadda tayi suka zama masoya, daga ta hadu da wani wanda yafi wancan zata yar dashi ta kama wani,
in dai akan namiji ne to sanah bata da alqibla ita kanta bazata iya kirga mazan da tayi mu'amala dasu ba tun tana js3 har kawo yanzu,, sadeeq yana makaranta lokacin da sanah ke zuwa hutu gidansu, har ta gama hutunta ta tafi basu taba haduwa ba, amma ita tasanshi sosai dan har hotonshi gareta....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ●● ZULFAH ●● 5⃣
By Aysha Ya'u Kurah

A hankali take leķen gidan da ganin idonta a firgice take, ganin babu kowa a tsakar gidan yasa ta karanta addu'a tashiga ciki tana waige, ta kai dai2 dakinta taji an fisgota da karfi har saida hijab dinta ya yage sosai a wuya, fitsari ta saki a wando saboda yanda taga idon goggo marka babu imani a cikinsu hannunta rike da wani murďaďďen sanda wanda ta saba dukanta dashi, durkushewa zulfa tayi idonta yanata ambaliyan ruwa, cikin sanyin muryar kuka tace goggo dan girman Allah kiyi---- saukar sanda taji a bakinta ta fara ihun neman taimako, dukanta marka takeyi babu ko digon tausayi a ranta, saida ta tabbatar ta mata liss sannan ta kyaleta ta wurga sandar gefe tana huci, tace dan kutumar ubanki har ni zan saki aiki saboda ke tabbatacciya ce tsinanniyya, har kinada karfin gwiwar wurgo min bokiti daga waje, to tsaya kiji in kina ganin kin fara balaga nonuwa sun tsuro miki kina ganin yanzu kin ri'ka kamar rikakkiyar kubewa, tashen balaga zai fara bayyana kanshi, to bari kiji in fada miki wallhy kinji na rantse da Allah daga yau karfe hudu zaki dinga tashi a gidan nan, waina ma na daina zaman suyanta ke zaki dinga soyawa kina siyarmin, islamiyya kuma sai dai kiyi a lahira in anayi, haka boko ko kun koma hutu na haramta miki shi, duk ranar da kika kuskure abu daya cikin abinda na lissafa miki hummm"" zulfa'u ki kira kanki gawa kinaji na, eh ta fadi a hankali jikinta ciwo yake mata sosai, zafin da takeji a zuciyarta yafi wanda takeji a jikinta, yanzu shikenan an hanata zuwa islamiyyar da saura kwanaki tayi sauka, kuka ta dingayi a gurin taji an sa kafa anyi ball da ita, a tsorace ta fara rarrafawa tana kuka har ta kai ďakinta, hada kanta tayi da gwiwa ta cigaba kukan da babu mai rarrashi, yanzu shikenan babu wanda zai kwatar mata yancinta, shikenan ita haka zata kare cikin wahala, ta dade tana kuka kiran sallar azahar ne yasa ta ta mike dan taje tayi sallah, tana kokarin mikewa kafarta tace bata san zancen ba, ta koma da baya ta xauna hawaye na bin idonta, targade goggo tayi mata a hannu da kafa, da jan jiki ta fito ta shiga bayi ta dauraye jikinta ta canza kaya, tayi alwala ta koma daki tayi sallah, ta dan kwanta dan taga fitar su goggo da salaha, bacci ne yayi gaba da ita, bata san lokaci yaja har haka ba saboda baccin yayi mata dadi ko ba komai ta dan huta, ruwa taji an sheka mata a jiki, ta farka tana waige2 a firgice, ga warin da ya ishi hancinta, ta kalli jikinta cikin kyankyami ta kalli salaha, tace ruwan kwata kika watsa min, innalillahi kadai take fadi a ranta ga wani amai daya taso mata, salaha ta wurgo mata bokitin jikinta tace an watsa miki ko kina da abinda zakiyi ne, zulfa ta girgiza kanta tace babu,, Allah ya isar min, salaha tace kambuu lallai yarinyar nan, ni kike ma Allah ya isa, zulfa ta mike da kyar tana dingishi salaha ta kara tare kofar dakin rike da kugu tace dan uwarki wa kike ma Allah ya isa, zulfa tayi banza da ita zata bi ta gefe ta fita salaha ta hankada ta da karfi kanta ya bugu da bango, rike kanta dake juya mata tayi kwata2 bata iya gane zagin da salaha ke mata saboda azaba, ta dade a durkushe tana kuka kafin nan ta fita ta cire kayan jikinta tayi wanka ta yi alwala da kyar tayi sallah, ta fito jiri na ďibanta ta fara iza murhu har ya kama ta daura ruwan talge, a daddafe take aikin har ta gama abinci goggo marka bata dawo ba, ta gyara ko ina ta dauraye kayanta, sannan ta shiga daki ta dan kwanta idonta kamar an daura dutse, sallamar babanta taji a hankali bayan magriba ya dauka marka ta dawo daga gidan biki ne, ďakinta ya leka yaga bata nan, da sauri ya fito ya shiga ďakin zulfa, a hankali ya ďan bubbugata ta mike a firgice, yace zulfa'u ni ne, ta mike a hankali ta zauna tace ina wuni baba, idonshi ya ciko da kwalla saboda yadda yaga jikin yar tashi yace dukanki sukayi ko, ta fashe da kukan da take boyewa ya rike hannunta yaji zafi rau yace kiyi hakuri zulfau, nasan komai ake miki a gidan nan nine sanadi, ki yi ta addu'a komai na duniya mai wucewa ne, kuma wata rana sai labari, zuciyar zulfa ta kara zafi a ranta tace kullum sai ace mata wata rana sai labari wai ita yaushe labarin nan zai zo har ya wuce ne,, cikin muryar kuka tace baba" goggo tace bazan kara zuwa islamiyya ba kuma jarabawar sauka mukeyi, dan Allah baba ka taimakeni kar a katse min karatuna, ya rungumeta sosai ajikinshi shima kukan yakeyi dan yasan marka baxata taba janye kudirinta ba, yace kiyi hakuri zanyi miki kokari zulfa share hawayenki, ya dagota yana share mata hawaye itama ta share mishi nashi, da sauri yasa hannu a aljihunshi jikinshi har rawa yakeyi ya dauko leda ya bude nama ne yanka biyu ya fito dashi yace dazu aka kawo naman walimar sunan y'ar datti shine aka raba mana kowa bibbyu shine na kullo miki nawa, karbi kici yakai bakinta, ta rike hannunshi tana kuka tace baba kaci daya nima inci daya ya kara share mata hawaye yana girgiza kai yace kinfi ni bukatarshi cinye duka kinji, tasa hannu zata karba taji an warce naman ana huci kamar kura, suka dago kai suka kalleta tana kallon naman tana huci kamar bata taba cin nama ba, tace nama, nama ne fa salaha ta fadi tana nuna ma 'yarta, tabdi lallai ado ka cika munafuki, yaushe rabon da muci nama a gidan nan shine yanzu dan kaga bana nan ka kullo ka kawo mata, tayi kan zulfa da jikinta ke rawa tace dan ubanki nawa kikaci, yau sai kin amayar dashi duka, ta danneta zulfa na kakari tace wallhy ko daya banci ba goggo, da kyar malam yayi ta maza dan yaga ana kokarin raba yarshi da ranta ya tura marka da karfi, cikin zafin nama kamar namiji tayi kanshi tana dukanshi har saida ta yaga mishi riga, hakuri kawai yake bata tana kara turashi tana masifa, kabiru ne ya shigo da sauri saboda yaji hayaniyar tayi yawa, dakyar ya iya rabasu yana kuka yace haba goggo wai meyasa kike irin wannan abun ne, ji yadda---- mari ta kai mishi har biyu tana huci tace to sallamame watsatstse wanda baya kishin uwarshi, wallhy ka kara fadin kalma daya anan saina daga maga nono shege dan iska, kabiru ya rike kuncinshi ya fita ranshi a bace, zuciyarshi na kara jin tsanar mace, ya kudira aranshi bazai taba yin aure ba har ya mutu in dai haka mata suke, a cikin gida kuwa marka nata masifa,, abinda zai baku mamaki bai wuce duk damben da marka tayi baisa ta saki naman ba yana nan makale a cikin hannunta, saida ta gaji dan kanta tayi shuru ta wuce daki, salaha ta bita tace goggo ina naman, ta harari salaha tace yana can a waje na watsar, salaha ta fita da sauri harda daukar fitila, tana fita goggo marka ta watsa naman a bakinta duka biyu, salaha tayi ta neman naman harda dakin zulfa saida ta duba ko ina kamar mayya, daki ta koma tana nishi tace ban gani ba goggo babu mamaki wani a cikinsu ya dauke, ummm goggo tace saboda naman na bakinta bata gama taune shi ba, salaha tace goggo dazu kinsan yarinyar nan zagina ta dinga yi, goggo dai ta kasa cewa komai saboda kar salaha ta gane abinda ke bakinta, salaha tace goggo kinajina kuwa, uhumm goggo tace tana kokarin kwanciya, salaha ta matso kusa da ita ta dafata tace wai goggo me yasameki ne, goggo ta kifa kanta a katifa tafara kukan karya tana ummmm, salaha tace to goggo meye na kuka, ay tunda kin musu laga2 xasu shiga taitayinsu goggo bata dago ba tana kokarin hadiye naman ta kware sosai ta dago da sauri tana tari ragowar da bata hadiye ba suka zubo ta dinga tari tana kakarin amai, salaha ta debo ruwa da sauri ta bata ta sha zata ajiye kofin a kasa taga naman da goggo ta fito dashi, salaha ta kara haskawa ta tabbatar nama ne, ta dago kai ta kalli goggo, ta tabe baki tace walhy gogg---- cikin sarkakakkiyar murya tace Allah ya tsine ma wanda yayi min magana ta juya bayanta ta kwanta idonta zuru2, salaha ta tashi ta fita tana girgiza kanta aranta tace mugunta fitsarin fako, lallai goggo ta shahara a mugunta, dama hausawa sunce bazaka taba kwarewa a mugunta ba har sai kama naka, walhy saina rama abinda goggo tamin tayi kwafa ta fita daga gidan gaba daya.........

Mrs tijjani shattima....
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ●● ZULFAH ●● 6⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Washe gari ta tashi da wuri kamar yadda goggo ta umurceta, aikin gidan tayi gaba daya tana yi tana hutawa saboda hannunta, karfe shida da kwata ta iza wutar waina, tana zaune hayaqi ya turnuke gurin idonta ya cika da ruwa tana ta fiffita ga yunwa tanaji sosai,,, saida tandar ta dau zafi sannan ta fara suyar wainar, maza da yara suka fara shigowa cikin gidan, ta na suya tana siyarwa,,,

sallamar wani wanda a kullum idan yazo gurin ke kaurewa da ihu saboda siyan ma duk wanda yake gurin yakeyi,, hannu ya daga musu yana zukar wiwi, ya kalli zulfa da ke iza wuta ya shafo gefen kunnenta, tayi maza ta ja baya ta dago kai tana kallonshi, yayi murmushi yace kuce yau yar kyakykyawa ce ke mana waina, ya daga murya da karfi yace a kira yara a basu waina yau waina ko daya bazata rage ba,,, wani yaro a gefe ya fita yana ihu yana fadin sai baban house Allah yaja zamanin baba uban baba, ya kara kallon zulfa ya matso kusa da ita sosai zai rike hannun ta, ta watsa mishi kullun wainar a fuskarshi, ta mike tsaye tace wani irin iskanci ne wannan, yan tashan dake gurin suka fara ihu suna bangis din kikayi wa haka, tayi tsaki ta cigaba da zuba kullun cikin tanda, sunata hayaniyar su, bangis bai kallesu bare ya tanka musu, hayaniyarsu ita ta fito da goggo da sauri tana hamma tace lafiya dai kuka cika min gida da ihu, ta kalli bangis da ya cika ya batse, ta dunkule hannu tace Allah yaja zamanin ka mai gidan masu gida, laminu dan koranshi yace dalla matsa can da wannan kirarin naki, in ba iskanci ba wannan kazamar yarinyar ta rasa wanda zata watsa ma kullu sai bangis, yau sai munga wanda ya tsaya mata dan uwarta, goggo ranta ya baci matuka saboda in bangis ya daina zuwa gurinta siyan waina ay ta kaďe, ta matso kusa da zulfa gadan2 har tana gurďe kafa, wani katon ice ta dauka zata buga mata, zulfa ta rintse idonta haďe ihu mai karfin gaske, da sauri bangis ya rike icen, cikin muryar kauraye yace haba haj markus, irin wadannan kayan masu tsada ay ba'a dukansu, barta taci bashi, zata biyashi nan bada dadewa ba, ya wurgar da icen gefe ya goge fuskarshi ya zaro dubu uku ya mika ma goggo yace ki raba ma yara wainar yau, ya shafi gefen hannun zulfa ya rintse idonshi hade da zukar wiwi, yasa kai zai fita goggo dai sai kallonshi takeyi cikin mamaki dan tasan bangis ba'a takashi a kwana lafiya, har ya kai kofa ya juyo yace zan auri yar nan taki markus nan da sati biyu, sai ku fara shirye2, ihu mutanen gurin suka Sá sunata fadin sai kayi wallhy,,
Goggo marka ta kasa dauke idonta daga kofar waje, tana mamaki aranta, ta waiga ta kalli salaha dake tsaye bakin kofa ta kumbura tayi fammm, dan ba karamin so takeyi ma babangida BBG ba, daki ta fada da gudu tana kuka, zulfa ma kuka sosai takeyi kamar ranta zai fita, ya za'ayi ta auri bangis, innalillahi wa inna ilaihir rajiun shi ta dinga faďi, a ďaki kuwa baban zulfa ne ya dafe kanshi saboda jin furucin babangida, dan ba a unguwar "babbar saura" ba ko ina an sanshi a unguwar rimi da kewayenta, ya ďaga hannunshi sama idonshi na zubar da hawaye yace ya Allah kaine kake da hanyoyi da yawa wanda bamu san dasu ba, Allah ka kawo mana hanyar da take billewa cikin gaggawarka ni da ďiyata zulfa'u.....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ●● ZULFAH ●● 7⃣
By Aysha Ya'u kurah

Zulfa na zaune ta gama suyar waina goggo ta rarraba ma yara, amma ita ko ďaya ba'a bata ba, fa'ee ta shigo da sauri dan sunyi latti, turus" tayi saboda ganin zulfa a gaban tanda tana kuka, ta dafa ta tace ke lafiyarki baki shirya ba, zulfa zatayi magana goggo ta ce bazata ba kinibabba uwar tsari, fita ki bar min gida muha'ina kawai, in kara ganin shegiyar kafarki a gidan nan kiga yadda zanyi dake, fa'ee ta murguda mata baki tace zanga uban da zai hanata zuwa makaranta, goggo tayo kanta da gudu ta fita da karfi tace karki damu zulfa babu wanda zai katse miki makaranta, goggo ta kulu matuka ta juyo ciki bata ce ma zulfah komai ba, kuma batayi mata magana kan babangida ba saboda kar maganar ta koma kunnenshi, jira takeyi ragowar yan tashan su fita ta ci ubanta, ta shiga ďaki tana rarrashin salaha dake faman kuka, salaha tace haba goggo, shikenan ni babu wanda zaice yana sona, na fa girmi zulfa da kusan shekara hudu amma kullum sai ita samari ke zuwa nema, haka nura telan bakin titi saboda zulfa baki ga wulakancin da yayi min ba, yanzu ga bangis da na kwallafa raina akanshi shima ya fara sonta, ya kike so inyi da raina, ta kara fashewa da kuka, goggo ta dinga rarrashinta akan tasha kuruminta indai bangis ne kamar ta aureshi ta gama,
Malam ado a ranshi yace ko meye abin sha'awa a auren mashayi dan tasha oho, ya ce marka ni na fita, ta yi mishi kallon banza tayi tsaki tace kafi ruwa gudu, matsiyacin banza, ta juya ta cigaba da rarrashin yarta,

A kofar gida ya tarar da liman da salim da wani dattijo, cikin girmamawa ya mika musu hannu sukayi musabaha, liman yace malam ado yanzu salim yazo ya sameni da wata magana, shine naga muna tare ya kamata inzo inyi muku magana tunda ay "ďa" na kowa ne, malam ado yace Allah dai yasa lafiya liman, liman yace lafiyar kenan, kawar yarka zulfa'u ce take fada ma salim wai ance zulfa'u bazata kara zuwa makaranta ba, haba malam ado sanin kanka ne saukar yaran nan bata wuce yan kwanaki ba, kuma ana yabon kokarin zulfa a ko'ina babu adalci ace za'a hana yaro mai hazaka yin saukar alkurani saboda wannan ranar yara da yawa suna ďokinta badan komai ba sai dan su nuna bajintar su a gaban alumma, wanda yayi kokari yaji dadi a yaba mishi ayi mishi kyaututuka su dawo gidajensu cikin farin ciki, zan iya takaice maka cewar yara suna sanya wannan ranar ta zama tarihi a cikin rayuwarsu, saboda haka na rokeka kayi hakuri ka barta ta cigaba da zuwa makaranta kwanaki kadan suka rage,,
malam ado yayi jugum cikin tunani yace to liman nidai ban hanata zuwa makaranta ba, ku shigo daga ciki sai inyi muku magana da marka ku roketa nasan zata ga girmanka, liman suka shiga kallon kallo, suka maida numfashi sannan suka shiga suka zauna a dan karamin zauren,
Marka ta fito kamar mutuniyar kwarai ta nemi guri a gefe ta gaishesu, suka amsa mata da fara'arsu, sannan suka koro mata abinda ya kawo su, bata nuna musu komai ba, tace au to to to, ba komai zata cigaba da zuwa, saleem yaji dadi sosai suka dinga mata godiya, tace babu komai ay ba saikun gode ba, har sun mike zasu tafi tace,,,

Ammmm nace ba, suka waigo dukansu, tana dan murmushi ta kalli liman tace tun mutuwar saude buhun masara nawa ma ka taba kawowa gidan nan kace a ciyar da zulfa'u, cikin rashin fahimta liman yace ban gane ba, tace da hausa fa nayi magana, inaga kanada matsalar ji ne, ta kalli salim da ya haďe rai sosai tace ay kai ka fahimta ko, bata jira ya bata amsa ba ta kalli dattijon dake tsaye a gurin tace malam tanimu, sau nawa ma ka taba dinkawa zulfa'u kaya tunda muke tare dakai, , ran saleem ya baci sosai dan ya gane inda ta dosa, yace kinga malama bawai munzo kici mana mutunci bane, ta katseshi cikin masifa tace nidai kuka shigo kuci min mutunci har gidana, ku fada min uban da na taba shiga gidanshi sulhu ko rabon fada wato shine ni dan kun raina ni kun wani taso zugwi2 kunzo wai a bar zulfa tayi makaranta, in akwai uban da ke ciyar da ita sai ya fada min, ko kunya bakuji ba, wai kuma a haka kuna da ilimi, to lallai iliminku bai amfana muku komai ba, haka goggo tayita surfa musu ruwan bala'i malam ado na basu hakuri, saleem ya fita a fusace yace yau zan ganar da matar nan kurenta, zata gane taba zulfa'u kamar taba raina ne, bai zame ko ina ba sai police station, yan sanda uku ya bukaci a bashi suka taho tare har kofar gidan, lokacin goggo da salaha suna kan zulfa suna mata izayar da suka saba, sallama yansandn suka yi da karfi, goggo ta fito babu ko mayafi tace uban waye yake min sallama haka kamar gidan uban--- maganarta ta koma ciki saboda ganin masu bakin kaya,
murya na rawa tace la-fiya daga ina, salim yace ku kamata itace nake fada muku, kuma ku tabbatar kun mata azabar da wani ma in yaganta bazai ganeta ba, durkushewa goggo tayi ta fara kuka ta rike rigar salim tace kayi wa Allah da manzonsa kayi hakuri, islamiyya ce zulfa yanzu zata tafi kuma ko za'a shekara a can wallhy bazan damu ba, dazu din ma wasa nake muku dan gata can ma tayi shirin makaranta, ya fisge rigarshi yace karya takeyi yallabai ku kamata kawai ku rufeta har sai dan kaina na sa a sakota,
in kunga irin azabar da take ma yarinyar nan wallahy sai kun tausaya mata, kuma anjima kadan zan tafi gurin human ryt dole a kwato mata yancinta, da karfi yace take her out, zamuyi sharia dake daganan har lagos, wayyyyyyyyyyo Allah na abinda goggo ta fada kenan saboda "human ryt" din da yace da kuma "take her out" kuma ya ambaci shari'a lagos ta dauka wasu nau'ikan azaba ne da za'ayi mata ko ma akasheta, ihu takeyi tana crolln da gwiwinta tana rokon salim da ya daga kanshi sama,
ihunta ne ya fito da salaha ganin yan sanda yasa ta zubewa a gurin itama tana ihu, ya raďa ma police din magana a kunne sannan yace duk ku tafi dasu azzalumai kawai, ya wuce ya shiga cikin gidan, hangota yayi a daki kanta a kasa tana kuka, sai da ya ķare ma dakin kallo sannan ya girgiza kanshi ya tsuguna yana mata magana a hankali, ta dago kumburarren idonta ta kalleshi, yace tashi kije ki shirya mu wuce makaranta, tace to, ta mike a hankali tana ďingishi jiri na neman yar da ita, dakewa tayi saboda tana son zuwa makaranta, uniform dinta ta hango can kasa duk anyi tsumma dashi, ta kwaso su tana kuka, zatayi magana yace ki sa ko wani irin kaya muje tara ta wuce ya fita waje yana kara jin tausayinta, a zaure ya tsaya yana kallon dramar goggo da yan sanda, bindiga daya ya saita a kanta nan take goggo ta saki fitsari, ta sulale a kasa ita bata suma ba kuma bata tashi ba, jikinta sai rawa yakeyi, saleem yace yallabai barta muje kawai kukan kurciya jawabi ne, yau in mun barta gobe in ta kuma wallhy babu lamuni, suka fita salim ya durkusa yace "karen bana goggo," wannan gargadi ne, ya fita ya sallami yan sandan yayi ta musu godiya......

Mrs tijjani shattima.....
[15/12 14:47] Anty aisha ya'u kura: ●● ZULFAH ●● 8⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Mummy me yake damunki, kwana biyun nan naga kina yawan shiga damuwa, mummy tayi murmushi ta kalli jalila tace babu abinda ke damuna jalila, me zai dameni ina da Allah da manzonsa, sannan inada miji mai kaunata kuma inada nutsatsun ya'ya kamarku ta karasa faďi tana shafa kan jalila, jalila tayi dariyar jindadi tace hakene mummy, suka cigaba da hirarsu ta ďa da mahaifi, a cikin hikima mummy ta jefo ma jalila tambaya akan abinda ke damunta tace jalila wai niko ina abba ya tafi tun dazu, tayi murmushi tace sun fita da sanah na manta ne ban fada miki ba ya shigo kina wanka, uhumm kawai mummy tace ta cigaba da kallon tv amma da gani hankalinta baya gurin kwata2,, kwanan sanah hudu da zuwa gidannan gaba daya ta canza mata sadeeq dinta, ko dayaushe yana like da ita kamar kaska wannan itace damuwar da tayi ma mummy katutu a zuciyarta, shigowarsu rungume da juna shi ya katse ma mummy zancen zucin da ta keyi, ko kadan basu san su mummy na parlon ba, sanah na narke a cikin kirjinshi sai shagwaba take mishi, shi kuma yana biye mata kamar wani dolo, gaba daya sanah ta gama da zuciyarshi, bayajin zai iya kara son wata mace a irin sonta da yakeji a zuciyarshi, bakinshi ya daura kan goshinta ya manna mata kiss yace sorry babie muje in taya ki ajiye kayan sai ki rakani, ta yi murmushi tace yanzu naji magana, suka karaso cikin parlon suna dariya, a hankali ya zare jikinshi da na sanah yana sosa kai saboda ganin mummy zaune a gurin, ko kallonsu batayi ba ta cigaba da kallon tv, sanah ta zo ta dafata tace mummy sannu da gida, yauwa kawai tace ba tare da
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment