Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ne,
bai ankara ba yaji cizon da ya gigita shi a harshenshi,
cire bakinshi yayi da sauri yana fadin "aushhhh",
ya kalleta idonta a runtse ta datse bakinta yace yau zan nuna miki na fiki iya mugunta,
tunda na biki ta lalama kinki,
cak ya dauketa ya daurata akan gado duk ihun da takeyi baisashi ya daina abinda yakeyi ba,
zulfa taga duk ihu da dukan da take mishi baisahi ya kyaleta ba,
ta shiga hadashi da Allah akan ya kyaleta, inaaa sadeeq bai ma san tanayi ba shima hakurin yake bata cikin rudewa dan sam hankalinshi baya jikinshi,
saida ya cire mata kaya sannan ya shiga aika mata da sakonni masu rikitarwa,
ihun da naji cikin dashashshiyar yasa na gane sadeeq ya maida zulfa'u cikakkiyar mace,
sambatu kawai yakeyi cikin ficewar hayyaci, shi kanshi baisan abinda yake fadi ba saboda bai taba tsintar kanshi cikin wannan ni'imtaccen yanayin ba...

Mrs tijjani shattima..
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: [11:08, 02/02/2016] Aysha Ya'u Kurah: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 4⃣9⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Kuka zulfah takeyi muryarta bata fita saboda azaba a zuciyarta tana jin haushin sadeeq saboda ya gama bata mata rayuwa kuma ba sonta yakeyi ba,
shi kuwa sadeeq gefe ya mirgina ya rungumeta tsamm a jikinshi hawaye na fita a idonshi,
gaba daya ya rasa ta inda zai fara fada mata irin tsananin kaunar da yake mata ta yarda dashi,
sai yanzu yasan meye ainihin kalmar da ake kira so,
ashe shirme yayi lokacin da yayi haukar son sanah,
yanzu ne ya gane dimbin kaunar da yake ma zulfah,
da wani baki zai fara fada mata yana sonta, in ya tuno abubuwan da yayi mata a baya sai yayi tsaki a hankali yaji ya tsani zuciyarshi da bata mishi nuni da irin wannan ranar ba lokacin da idonshi ya rufe,
kenan wannan ranar ita ce ranar da anty laila ke nusar dashi a kullum,
runtse idonshi yayi hawaye masu zafi suka zuba a goshin zulfah,
a hankali ya fara magana kamar mara gaskiya,
kiyi hakuri I don't mn to hurt u,
ki yafe min plss karki hukuntani akan kurakuraina,
zan iya jure komai amma banda hukuncin da zaki min, nasan ni mai laifi ne, dan Allah kiyi hakuri,
Dan Allah ka kaini gida ta fadi tana ajiyar zuciya,
yace nan ma gida ne, babu wanda zai zarge ki in kika kwana gidan mijinki,
ta runtse idonta tana kukan takaici dan tasan jikinta kawai sadeeq ke so ba ita ba, ya matseta sosai yana rarrashinta yace zan maida ke gida amma sai kin daina kukan nan,
ita dai babu abinda tace mishi,
ya juyo fuskarta ya goga hancinshi kan nata yace kinga yadda fuskarki tayi,
ya fara lashe hawayen dake kwance a kan kyakykyawar fuskarta,
"I LOVE U" taji ya fada mata a kunnenta,
ta bude idonta da sauri tana kallonshi, ya lumshe idonshi yana shafa mararta yace I love u so much,
ta kauda kanta tana kukan jin karyar da ta fito daga bakin sadeeq, bakin da yace bazai taba sonta ba har abada wai shine yake fada mata wannan kalmar,
ya marairace murya can kasa yace ki daina tunanin komai wallhy ina sonki son da bazan iya ma misalta miki shi ba,
dan Allah ka rabu dani da kalaman nan naka nagaji da jinsu nidai ka maida ni gida,
yayi murmushi ya dauketa ya kaita bayi ya taimaka mata tayi wanka sannan suka fita har lokacin idonta bai bar zubar da hawaye ba,
taimaka mata yayi ta shirya yana kallonta yana tausayin kanshi in har mummy tayi yunkurin rabashi da ita,
jallabiya yasa yayi sallar magriba yayi adduoi sosai akan Allah ya sanya ma mummy hakuri yasa tabarshi da matarshi da yake jinta har cikin bargon shi,
mikewa yayi ya kalleta yace har yanzu kuka, to bari in jiraki ki gama sai mu tafi,
da kyar ta iya mikewa saboda azaba tace ni ba kuka nakeyi ba,
yayi murmushi ya kamata suka fito parlon, yaso ta zauna tasha tea amma fir taķi,
har sun kusa fita yaji wani ihu a bayanshi ya waiga yaga sanah tsaye idonta ya rine saboda kishi,
da sauri ta matso kusa dasu tace zina har cikin gida sadeeq,
ta fara ihu tana daura dankwali a kugunta,
ya kara rungumo zulfah yace ke dakata2 kalleta da kyau wannan matata ce, Allah ya tsare ni da yin zina da matan banza kema shaida ce tunda ban taba kusantar ki ba har saida na aureki so ki dinga sanin abinda zaki fada,
da karfi tace kan bala'i mata fa kace,
yaushe ka dauketa a matsayin matarka, ta kalli zulfah dake kuka tace munafuka wallhy kinji kunya ba"a sanki amma saboda kulafuci da shegen son maza sai da kika biyoshi har gida,
kinyi asara wall--- sadeeq ya dauketa da mari yana huci, ta rike kuncinta tana kururuwa, tace wallhy yau sai na kashe yarinyar nan, wallhy saidai ko ni ko ita,
ta ruga kitchen kamar tababbiya, sadeeq ya dauki zulfah saboda tafiyar da takeyi ya kaita mota da sauri ya shiga ya ja baya yana hangota ta fito da wuka tana ihu tana tsalle kamar mahaukaciyya..

Zabba'u ta fito daga cikin hall din tana neman ta inda zulfah tayi bata ganta ba, taja ta tsaya tana jiranta ta dawo suje su fara rabon souvenirs, shuru Zabba'u taji har kusan minti talatin, tayi gurin parking motoci ta dinga dubawa babu zulfah ba alamarta,
cikin kidima ta koma hall din tana dubawa ko tana ciki nan ma bata ganta,
har kusan 1hour tana dubata, share zufar fuskarta tayi taje kusa da anty laila tace anty zulfah ta maido maki da key ne,
anty laila tace yanzu na gama maganarta wallhy tana ina, Zabba'u tace wallhy ban ganta ba anty kuma na duba ko ina, anty laila ta mike tace saidai ko wani gurin ta shiga suka cigaba da dubata bata ba alamarta,
Zabba'u ta kira farouk ko ya tafi da ita gida, yace a'a kuma gashi a gida bata nan, har aka tashi a gurin hankalinsu a tashe yake saboda ko alamunta basu gani ba,
kuka jalila ta fashe dashi suka dinga bin layin kaff babu zulfah, to ina ta shiga haka wasu suka dinga fadi, laila ta kira nurain ta fada mishi yayi salati yace garin yaya, tace aikenta mota nayi ban kara ganinta ba, innalillahi kadai yake fadi sannan ya kashe wayar ya shiga ya fadawa mummy, mummy ta rude sosai dan ko mayafi babu akanta ta fito tana salati,
nurain yace mummy ki kwantar da hankalinki, tace ta yaya hankalina zai kwanta ba'a ga yar mutane ba, ta zauna a parlor tana kuka tana jiran dawowar su jalila,
suna shigowa ta mike tace an ganta,
jalila cikin kuka tace wallhy babu inda bamu duba ba;, mummy ta koma ta zauna hawaye na bin idonta tana fadin ta shiga uku waye ya sace yar mutane, aka dinga ba mummy hakuri amma bata ko kallonsu dan tana tunanin abinda zata fadawa mahaifin zulfah,
sam basu kawo su kira sadeeq ba saboda sun san zaiyi wuya ya dauketa tunda ko magana basu yi to me zai mata ma in ya dauketa haka zuciyoyinsu suka dinga sakawa,
har kusan 8 babu labarinta, daddy ma ya shiga tashin hankali yasa nurain ya fita yaje ya sanar ma yan sanda, anty amarya na zaune itama tana kukan munafurci tana rarrashin mummy..

Gasashshiyar kaza ya biya ya siyo da madara,
yana kallonta tana kuka bai ce mata komai ba suka wuce,
a zuciyarta tana tunanin me zata ce ma su mummy, shima yana tunanin karyar da zaima mummy dan yasan hankalinsu a tashe yake,
yana isa kofar gidan ya shiga ciki ya bude mata mota ta fito tana share hawayen da yake zubo mata ya rikota suka kama hanyar shiga cikin gidan,,
da nurain suka fara karo lokacin ya fito zai kai report, tsayawa yayi yana kallonsu baki sake,
sadeeq ya kalleshi yace ina wuni, nurain bai amsa ba ya juya ya kalli zulfah da fuskarta ke kumbure yace me ya sameki, ta girgiza kanta hawaye na ambaliya a idonta, tace bakomai, cikin rashin gamsuwa yace okk ya wuce ciki suna binshi a baya....

Mrs tijjani shattima...
[13:39, 02/02/2016] Aysha Ya'u Kurah: ◆◆ ZULFAH ◆◆
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ♢♢50♢♢
By Aysha Ya'u Kurah

Mikewa mummy tayi da ta hango zulfah ta karasa kusa da ita ta rungumeta tana shafa fuskarta, tace meya sameki, ina kika shiga, zulfah ta fashe da kuka ta kasa magana, mummy ta kalli sadeeq da kanshi ke sunkuye tace me ya sameta abba, fadamin abinda kayi mata, daddy yace Aisha ki nutsu mana su zauna sai muji abinda ya sameta tunda Allah yasa an ganta, tayi kwafa tana hararar sadeeq ta ja zulfah suka zauna, daddy ya kalli zulfah a hankali yace ina kikaje, ta dago kanta cikin muryar kuka tace nnn.. a... sadeeq ya amshe da sauri yace daddy naje gurin bikin ne sai na ganta a waje a haka tana hira da wani shine ni kuma naga zunubi take ďiba saboda ba muharraminta bane shine na dauketa muka tafi gida kafin a tashi sai in dawo da ita gida dan nasan in na maidota gida a wannan lokacin zata iya komawa gurin,, zulfah ta kwalolo ido tana kallon sadeeq yadda yake sharo karya,
mummy cikin fushi tace kai za a rubutawa zunubi ko ita, ina ma ruwanka da ita dan ka ganta da wani, wllhy ka fita idona in rufe in dai baso kakeyi ranka ya baci ba, kuma ka miko min takardarta yanzun nan,,
kowa a gurin saida ya girgiza da jin kalaman mummy, daddy ya kalleta yace wace takadda kike nufi Aisha,
tace takardar saki nake nufi, gobe in shaa Allahu za'a daura mata aure da hilal har na karbi sadakinshi,
"innalillahi wa inna ilaihi rajiun" abinda daddy ya fadi kenan yace kina da hankali kuwa Aisha, kin taba ganin inda aka karbi sadakin wani da auren wani akan yarinya, tace an fara daga kan zulfah saboda ina da tabbacin nata auren zai kare yau,
daddy yayi ajiyar zuciya ya kalli sadeeq yace abba kunyi da mahaifiyarka zaka rabu da matarka ne,
ka fa daina cewa matarshi dan ta kusa zama ba tashi ba mummy ta fada tana gyara zama,
sadeeq yace daddy dan Allah ka bawa mummy hakuri wallhy bazan iya sakinta ba, mummy tace wallhy sai ka saketa tunda ni na aura maka ita dama,
yau babu abinda zaisa ta kara kwana da aurenka a kanta,
Nurain ya kalli mummy yace mummy kiyi hakuri muji meye nufinshi na kin sakinta tunda baya sonta,
da sauri sadeeq yace ni bance bana sonta ba dan Allah daddy ka fadama mummy haramcin tursasa saki, anty amarya ta mike tayi daki rai a bace saboda yadda taga alamun sadeeq yana mutuwar son yarinyar nan,
masifa mummy ta shiga yi ma sadeeq kamar zata dakeshi sannan tace wallhy ya biyota da takaddar har daki in baso yakeyi ta sa wando daya dashi ba,
ta mike ta daga zulfah dake kuka sosai suka kama hanyar daki, tsayawa mummy tayi da taga yadda zulfah ke tafiya, ta janyota da sauri suka shiga daki, gefen gado ta zaunar ita tace fada min abinda abba yayi miki, zulfah ta kara fashewa da kuka ta kasa yi ma mummy magana, zama mummy tayi kusa da ita tayi tagumi tana kallon bango, hankalin zulfah ya tashi sosai ta tsuguna a kasa tace wallhy tallahy mummy shi ya daukeni da kanshi ya kaini gidanshi ya..... ya.... ta kasa karasawa tana kuka sosai,
mummy tayi murmushi ta dagota ta rungumota tace kwantar da hankalinki ki daina kuka,
zulfah ta hadiye kukanta tana share hawayenta, mummy ta kalleta tace kina son abba? Zulfa ta sunkuyar da kanta idonta taff da kwalla a zuciyarta tace so na hakika wanda na boyeshi acan cikin zuciyata na danneshi da tunanin kiyayyar da yayi min,
mummy ta kara dago kanta tace kar ki cuci kanki zulfah ki fada min wallhy in baki sonshi dole in kwato miki yancinki ki auri wanda kikeso,
zulfah ta kara sunkuyar da kanta ya za'ayi tace bata son dan mummy matar da ko rayuwarta ta bukata zata iya bata inda hali, ta yaya bakinta zai iya furta ki ga jinin baiwar Allahr da ta maida ita cikakkiyar mace mai yanci,
ay ko bata son sadeeq bazata iya kin zama dashi ba, bare tana matukar kaunarshi tun bata san kamanninshi ba ma,
mummy tayi murmushin jin dadi tace nagode zulfah kin gama min komai shurunki amsa ce mai girma a gareni wallhy bani da kamarku ke da laila dan daya kuke da yayan da na haifa, nagode sosa-- zulfah ta katseta tace mummy ni ya kamata inyi miki godiya, bani da wata uwa a duk duniya da ta wuce ke, kin daukoni gidanki kin bani komai na rayuwa kin sa nasan abubuwa da yawa kin yi min abinda babu wanda zai iya min shi a rayuwata, babu abinda zan iya biyanki dashi,,
mummy tace kin gama biyana tunda kika jure komai saboda ni, Allah yayi miki albarka tashi ki shiga bayi kiyi wanka, ta mike tana tafiya da kyar mummy ta fito mata da magunguna tana mai jin dadi cikin zuciyarta ta dinga adduar dorewar farin cikin nan na har abada,,
Parlon ta koma ta zauna ta kalli sadeeq da idonshi yayi ja daddy da nurain suna mishi fada tace duk fadan da kuke mishi na banza ne dan kunnen abba na kashi ne,
so yakeyi mu bashi ita yanzu ya wulakanta ta in ya samu wata saboda har yanzu baisan me yake so ba, baima san me kalmar so take nufi ba,
ya dago kai kamar maraya yace wallhy mummy ina sonta na rantse da Allah mummy gaskiya na fada miki,
tace to ita bata sonka kaje can ka karasa tsufanka da matarka,
nurain yayi dariya yana kallon mummy yace mummy dan Allah ki bashi dama kadan in bai canza ba sai ki dau mataki, mummy tace to shi hilal din fa da yake sonta tuntuni,
sadeeq cikin daga murya yace karya yakeyi mummy wallhy na fishi sonta,
farouk ya kwashe da dariya harda tsugunawa kasa,
ran sadeeq ya baci ya dauki remote ya wurgo mishi mummy ta danne dariyarta tace karka illata min ďa, haka kawai zaka hanashi dariya,
sadeeq kamar zaiyi kuka yace to ni sa'anshi ne,
daddy yayi dariya yace kai ba sa'anshi bane babana,
ya kalli farouk yace fita ka bamu guri ana maganar manya ka wani zo kana mishi dariya,
farouk ya mike ya fita yana dariya sosai, daddy ya kalli mummy yace ya isheki haka Aisha,
ki daina susuta min uba dan ma kinga yanzu yana sonta shine kike neman ki haukatar min dashi,
to ko ki janye wannan maganar taki ko kuma muyi fushi mu nemi wata ko babana, sadeeq ya girgiza kanshi kamar karamin yaro yace ni ita nake so daddy,
mummy tace to ita kuma bata sonka kayi hakuri kawai ka nemi wata, yace wallhy tana sona, ni nasan tana sona, mummy tace to tunda tana sonka sai muga yadda zaku zauna tare,
nurain tashi ka wuce gurin iyalinka kaji, ya mike ya wuce yana dariyar dramar mummy da sadeeq,
ta kalli sadeeq tace tashi kaje gida kaima ka huta ko,
yayi narai2 da ido yace haba mummy wai yanzu kin daina sona ne,
tace soyayyar ce tasa na ke son rabaka da abinda baka so, KWAILAH ce fa kai kuma ay sai HIGH CLASS BEB ko, ya kalleta yace ki yi hakuri Allah ma muna mishi laifi fa mummy, tace ni ay ba laifi kayi min ba, daddy yace dan Allah ki kyaleshi haka yaje ya huta ay kin bashi wahala ya isa haka tunda kin rama, tace ay ban yi mishi komai ba ma,,
sadeeq yace wannan ay yafi komai mummy wallhy kadan ya rage in samu "strk" tayi dariya sosai tace to naji tashi kaje,
yace to mummy.... ammm... menene kuma ta fadi tana harararshi ya sosa kanshi yace ta.... taz.. babu inda zata ko zan baka ita sa nan da wata daya in naga yanayinka kuma na gasgata gaskiyarka,
ya mike dan kar ya harzuka ta duk da ba haka yaso ba yace to Allah ya kaimu tace ameen....

Mrs tijjani shattima...


: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 5⃣1⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Sai kai kawo anty amarya takeyi a tsakar parlonta,
hankalinta in yayi dubu to ya tashi, tana kallon wayarta dake faman ruri taki dagawa, ya akayi abba ya fara son yarinyar nan, lallai sanah ta cika yar iska da har tayi sake hakan ta faru, zama tayi tana huci kamar zaki ta dau wayarta taga kusan 10msd calls kuma duk na sanah ne, tsaki tayi tayi dialing numbr maman sanah, sau uku tana kira ba"a daga ba a na hudun ne ta daga murya can kasa tace ina meeting ne "deee" in na fito zan kiraki,
anty amarya tayi tsaki tace at dis tym ake meeting, me zaisa ďan da ka haifa ma ka bashi tarbiyya kai kanka baka da lokacin kanka,
tayi tsaki bayan ta yar da wayar ta dinga sambatun maganganunta ita kadai ta kasa samo mafita,
meyasa sanah zata yi mata haka, meyasa? Wayarta ta shiga ringing ta duba tym taga afta 11 ta girgiza kanta ta dauka maman sanah tace dee ya akayi ne, yanxu na dawo gida wallhy duk na gaji,
anty amarya tace baki gaji ba yanzu ne zaki gaji in kikaji abinda zan fada miki,
maman sanah cikin firgici tace meya faru? Anty amarya tace komai ma ya faru, ta bata labarin duk abinda yake faruwa a gidan sanah, sannan ta cigaba da fada mata irin son da ta gani na zulfah a idanun sadeeq, maman sanah ta zame dankwalin kanta ta ya mutsa kitson attch din dake kanta cikin tashin hankali tace kina nufin sanah bata canza halinta ba,
anty amarya cikin fushi tace ay kinji abinda nace yanzu mafita kawai zaki kawo meye mafita,
maman sanah ta furzar da iska mai zafi a bakinta tace ay ni hadiza bansan me zance miki ba, gaba daya ji nake kamar zuciyata zata buga,
anty amarya tace xata ay lokacin da yarki ta zama bora, lokacin da zata dinga ganin yaran sadeeq amma ba ita ta haifesu ba,
ni ban taba ganin kaxamar karya irin sanah ba a rayuwata, maman sanah ranta ya kara baci sosai tace dakata hadiza yar tawa ce karya, anty amarya tace wallhy tama fi karya, in ba isk-- ya isheki maman sanah ta katseta da karfi, da wanne zanji da halin da sanah take ciki ko da cin mutuncin da kike min yanzu, ko mutuwa tana jin kunyar mahaifi a kunne na kike zagin yata da karya saboda baki san dadinsu ba ke kin gama watsar da naki a titi ko,
in sanah karya ce ke kuma kare ko kuma me zan kiraki,
sannu gwano wacce bata jin warin jikinta sai na wani, in kin manta bari in tuna miki, halinki sanah ta dakko na bin mazan da ba nasu ba, ko kin dauka bansan har yanzu kina pipn idan hasheem yayi tafiya ba,
to wallhy ki fita idona in rufe kuma wallhy kinji na rantse da Allah kika kuskura wata matsala ta gifta tsakanin auren sanah da sadeeq ki tabbatar naki kema zai samu matsala,
gara ku hada hannu ke da ita ku sama ma kanku mafita,
tunda ta fara masifa anty amarya ke kuka kamar ranta zai fita saboda takaicin kalaman yar uwarta, saida maman sanah tayi masifa mai isarta sannan ta kashe wayar ta bar anty amarya na shashshekar kuka,

Washe gari karfe 11 aka daura auren Jalila da Ishaq,
hidima ake tayi babu kakkautawa a cikin gidan, ko ina ka xaga mata ne zaka gani masu ji da kansu saboda naira ta zauna a gurinsu, daga can ciki kuma zulfa'u ce kwance a dakin farouk saboda nan ne babu mutane,
jalila na gefenta ana mata makup, zabba'u ta kara taba kan zulfah tace ohh wannan zazzabin xai kwafsa mana sai yau zai wani tashi ya hana mana sukuni kuma yaki sauka kamar yazo gidan ubanshi,
jalila tayi dariya tace ay ko ya sauka ko kar ya sauka yau bani barin garin nan sai da
"Z-square," zabba'u tayi dariya tace sunan da kika rada mana kenan, tayi tsaki tace nima da sunana da z ya fara da kinga shikenan sai komai ya tafi dai2, zabba'u tace ay bai baci ba baby rago kadai zaki siyo sai a yanka miki da sunan '"Zankaďaziyya", duk suka kwashe da dariya meenah me makup tace ay kuwa sunan ya dace dake,
zulfah dai na kwance tana murmushi tana kallonsu, ciwon da jikinta da kanta ke mata shi yafi komai damunta,
wayar jalila aka kira ta dauka tace yaya abba gud a.m,
yace morning amarya ya kuke, tace fyn, yace good,
ya rage muryarshi yace kina kusa da zulfa'u ne,
tace eh, yace plss sa mata wayar a kunnenta inji muryarta, tayi murmushi tace to, ta sa ma zulfah wayar a kunne ta rike tana kallonta,
runtse idonta tayi da taji muryarshi a cikin kunnenta,
magana yake mata a hankali kamar baison yi har ya gama bata ce mishi komai ba,
jalila ta cire hannunta ta mayar da wayar kunnenta tace yaya abba hannuna,
yace jalila bata min magana ba,
jalila tace wallhy bata da lafiya ne yaya a dukunkune ma take tun jiya,
yace subhanallah me ya sameta,
cikin wasa tace zazzabin rabuwa dani mana,
yace bansan shirme dan Allah ki tasheta tasha magani yanzuu, tace okk baka da matsala,
yace gidan duk a cike yake ko hayaniya ma ay zai sa mata ciwon kai dan Allah kuyi sauri a daukeki a kaiki gidanki mu huta,
tayi dariya tace ay tare zamu tafi da ita sai tayi min shekara daya sannan zata dawo,
yace shekara 1 ay yayi kadan why not tayi spndn rayuwarta a gidanki har ki tsufa, jalila ta yar da wayar tana dariya sosai kamar tababbiya....

Mrs tijjani shattima....
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 5⃣2⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Wasa wasa saida zulfa'u tayi sati daya tana ciwo tasha allurai da magunguna,
kullum sadeeq yana tafe zuwa duba ta mummy sam bata barinshi ya ganta ko ya ganta saidai daga nesa,
a bangaren sanah kuwa tunda tayi haukanta a wannan daren sadeeq bai kulata ba shikenan itama ta daina kulashi ko hanyar dakinshi bata bi saidai in yana parlor tayi shigar da a tunaninta zai ďaga mishi hankali tayi ta karkaďa jikinta dan in yazo ta samu damar wulakanta shi,
tsaki yakeyi ya kauda kanshi saboda ko kadan sanah bata bashi sha'awa,
sam baijin dadin tarayya da ita,
a kullum in ya tuna tarayyarshi da zulfa'u sai yayi ta murmushi shi kadai wani lokacin ma daurewa yakeyi da tsananin da mummy tayi mishi akanta saboda shi kadai yasan dadďar zumar da ya lasa a jikinta...

Yana zaune a dakinshi da daddare yana duba wasu aiyuka,
yayi kusan 1hr yana dubawa ga yunwa ta addabeshi,
tsaki yayi a hankali ya mike ya kashe lptp din ya fito zai shiga kitchen ya hada tea, zaune ya samu sanah ita da kawarta beeba suna hira suna shewa,
beeba na ganinshi ta tsuguna har kasa ta gaishe shi ya amsa mata ciki2 ya wuce,
sanah taja tsaki tace dan wulaknci, ke kika ma gaida shi wallhy ni bai isheni kallo ba,
beeba ta dan bugeta kadan tace ke wawiya ce, da dabara ake cin ribar zama da mutane, ta matso kusa da kunnenta ta raďa mata wasu maganganu sanah ta watse da dariya suka tafa,
beeba ta mike ta dauki jakarta tace maza ki tashi kije inji feedbc a waya komin dare kinji,
Sanah tace karki damu kawas ta mike tana karairaya ta karasa kitchen din,
yana tsaye ya gama hada tea zai dauka sanah tayi wuff ta dauke,
ta marairaice fuska tace haba dear wai laifin me nayi maka ne duk kabi ka canza min, ta shige jikinshi tace nice fa sanarka wacce take tsananin kaunarka,
ya matsar da ita a jikinshi ya murtuke fuska yace miko min tea dinnan ki bace
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment