Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

barrister "Lailah Isah Ameh" nice lauyar wacce ake kara,
bayan dan gejeren lokaci alkali yace barrister Tahir bismillah,
tahir ya mike ya isa kusa da zulfah yace baiwar Allah ko zaki iya fadawa kotu sunanki,
kan zulfah a sunkuye taki dagowa ta bashi amsa,
ya kara wurga mata tambayar,
nan ma shuru tayi, anty laila ta dafe kanta cikin bacin rai,
alkali ya tausasa murya yace baiwar Allah ya kamata kisan nan ba gurin wasa ko taurin kai bane,
ki bamu duk wata amsar da aka tambayeki ba tare da kin bata mana lokaci ba,
tayi shuru bata dago kai ta kalleshi ba, tahir yace ko zaki iya fadawa kotu sunanki,
a hankali ba tare da ta dago kanta ba tace sunan zulfa'u adam, zan takaice muku shariar nan ba tare da kowa yasha wahala ba,
ni na kashe shi, nice na kashe shi da hannuna,
ta dago kanta tana kuka sosai tace dan Allah mai shari'a ka yanke min hukunci ba tare da bincike ba,
duk hujjojn da aka kafa na daukesu,
ta rage kukanta a hankali tace meye a cikin duniyar nan da mutum zaiyi sha'awar ta, menene burin wadanda suka daura min wannan KAZAFIN (littafin kawalliya ta), burinsu shine su zauna a duniya suji dadinsu ni kuma in mutu da yarfen kisan kai ko,
ta daga hannunta tace dan Allah mai sharia ka cika musu burinsu ka yanke min hukuncin kisa,
nasan ko yau ko gobe ko jibi ko nan da shekara dari ne zasu zo inda zanje anan ne za'ayi shariar karshe lokacin da nake da mafita su basu dashi, dan son annabin Allah karka barni in kara kwana a wannan duniyar, ka yanke min hukuncin kisa kamar yadda ubangiji ya fadi a alqurani, ta kara fashewa da kuka mai tsuma zuciya,
kalaman zulfah sun sanyaya gwiwar dukkan mutanen dake gurin,
sadeeq da sauri ya tashi ya fita yana kuka shima kamar kwakwalrshi zata buga,
alkali ya dan dukar da kanshi kasa yasa hannu cikin glass dinshi ya share kwallar da ta taru a idonshi, ya dago kanshi ya kalli tahir da ya tsaya kamar gunki yace barr tahir baka da tambayar da zakayi mata,
barr tahir yace duk wata tambaya da zan mata ta riga ta bada amsa da bakinta saboda she's guilty,
zan gabatar da hujjojin da nake dasu duk da ta fadi da bakinta but saboda kotu ta kara gamsuwa zan gabatar mata da kwararan hujjoji,
wayar da ke hannun police din aka amsa aka mika ma alkali bayan an budo mishi txes din sannan ya bukaci a shigo mishi da wasu shedun da zasu tabbatarwa da kotu itace ta kasheshi, bamba aka fara shigowa da shi ya fadi duk karyar da ya fadi rannan,
sannan aka shigo da maimzy itama ta fadi duk karyar da ta fadi a gidan,
alkali ya tambayi laila ko tanada tambayar da zatayi ma maimzy, laila ta share hawayen idonta ta mike tace eh, ta matsa kusa da maimzy bayan ta gama gyara hular kanta,
tace malama maimzy tun yaushe kika san zulfa'u,
zufa ta fara tsatstsafo ma maimzy tace wata rana a hamdala hotel, laila tace gudd tun daga lokacin kuka zama kawaye kenan, maimzy tace eh,
laila ta kafeta da ido tace kuma a statement dinki kince fada kike ma zulfah akan shashancin da takeyi kenan daukar karatu kikaje yi hamdala har kuka hadu da zulfah,
maimzy iya tsurewa tayi tace ammm.... eh naje... naje,,, Objection mai girma mai shari'a tahir ya fadi hade da mikewa tsaye ya kamata barr, laila tasan irin tambayar da zata dingayi,
bai kamata ta dinga ruda wanda take tambaya ba,
alkali yace barr laila a kiyaye,
tace okk my lord,
tace maimzy ko zan iya ganin wayar da zulfah tayi miki text a ciki,
da sauri jikinta na rawa saboda laila ta gama rudata tace eh gata nan,
laila ta karbi wayar sannan ta amshi wayar zulfah tace ya mai girma mai shari'a, a ranar 3 ga september karfe 4:45pm text ya shigo wayar zulfah sannan at dat very tym wani text din ya fita daga wayarta, kuma a statement din maimzy tace tun kafin mutuwar marigayi zulfah ta turo mata da text din,
ya akayi text ya shiga kuma ya fita lokaci daya a ranar mutuwar marigayi,
ko daga nan ma zamu gane cewa wannan shiryayen abune,
ta mika wayoyin aka mika ma mishi,
sannan ta dakko takarda tace ya mai girma mai shari'a wannan takardar bin diddigin layi ne wanda aka tabbatar min da a rana daya aka fara amfani da wadnnan layikan,
kuma wannan layin da maimzy ke ikirarin tana amfani dashi layi ne da ko sau daya ba'a taba kira dashi ba kuma tace mana suna waya da zulfah har ma suna shirya gurin da zasu hadu duk ta wayar,,
sannan dayan ma sau daya takk akayi kira dashi, dayan shine ke cike da rudu saboda an rubuta AMINIYA kururu a jiki,
kuma in aka duba wayar zulfah bata taba kiran layin ba ko sau daya, haka text,
in har zulfah ta shirya plan din kisa dole mu samu numbers din nan a kan dialled calls dinta,
wannan shine shaida ta ta biyu da zan tabbatar muku da wannan plan ne shiryayye,
jikin maimzy ya fara rawa cikinta ya duri ruwa ta maida kallonta gurin da sanah dake zaune itama a tsuree.....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 6⃣0⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Anty laila ta cigaba da cewa ya mai shari'a ya kamata a duba wannan lamarin da kyau,
a daura shi a kan mizani a aunashi sannan ayi wa wacce ake tuhuma adalci, "nagode ya mai shari'a",
alkali ya gama rubuce rubucen shi, ya dago kai ya kalli barr tahir yace barr tahir ko kana da abin cewa,
tahir ya mike yace eh ranka ya dade, ya fito ya tsaya yace ya mai shari'a wadannan hujjojin da barr laila ta fada yayi kama da labarin kanzon kurege, hujjojinta basuyi karfin da har zai iya sawa a kori wannan shariar ba,
barr laila tace a wayar makashiyar babu kiran numbr da suka hada plan din akan dialld calls,
shin ko barr ta manta cewa ko wace wayar duniya akwai gurin da ake share abubuwan da ba'a bukatar wani ya gansu musamman ma abin nan in na sirri ne,
ko ma wanene in har yasan bashi da gaskiya zai iya yin duk abunda xaiyi dan ya ga asirin shi ya rufu, saboda haka ina rokon wannan kotun mai alfarma da tayi watsi da wannan shaidar in akayi la'akari da rashin karfi da ingancinta, sannan shaida ta biyu barr tace a mtn office an bi mata diddigin layin kuma an gano sababbi ne,
yayi murmushi yace ya mai shari'a mutumin da har yake da fasahar kisan kai har zai rasa dabarun da zai batar da mutane akan layikan waya, barr laila da bakinta tace lokaci daya aka siya layin nan,
ta yiwu makashiyar ita ta siya layukan ta rabasu ga aminanta saboda su gama komai ba tare da an gano su ba,
text kuma da take cewa lokaci daya aka turo kuma aka fitar, wannan kowa yaji yasan ita ta kitsa abinta saboda ko da an kamata ta samu mafaka akan bata san komai ba,
mutum mai wayau zai iya yin text shekara biyar ma da suka wuce, dan ya sabunta text din zai iya copying dinshi ya goge wancan ya tura wani a lokacin kaga anan ya mai shari'a an sabunta date din da tym din,
da wannan nake rokon wannan kotu mai alfarma akan tayi watsi da wadannan hujjoji ta biwa marayun da suka rasa ubansu da kuma matan da suka rasa mijinsu hakkinsu da gaggawa saboda rashin kwakwarar shaida da za'a gabatar da ita a gaban kotu,,
ya numfasa sannan yayi godiya ya koma ya zauna,
sai a sannan sanah ta gyara zama ta share zufar dake kwance a kan fuskarta,
alkali ya gama nazarin bangarorin duka biyu sannan yace shaidu sun gabata a gaban mu, amma saboda rashin karfin shaidar dayan bangaren zamu ďaga wannan shari'ar har 10 ga watan October dan a taro gamsassun hujjoji saboda yin adalci ga kowane bangare,

nan hayaniya ta kaure a cikin gurin anty laila taji dadin adalcin da akayi musu dan yanzu ne take da lokacin fara bincike saboda samun karin lokaci,
bayan an tashi daga kotun anty laila da farouk suka bukaci a basu belinta amma samm aka ki saboda karfin laifin da ake zarginta dashi,
haka suka hakura suka wuce gida suna tattauna yadda zasu sake bullowa alamarin,

sanah kuwa da ta koma gida ita da amarya dake takaba suka kule can daki cikin rashin jin dadin rashin yanke hukunci tun yau,
amma sai suka shagala saboda a ganinsu sun ma abun daurin da dakyar za'a iya warwareshi,
da wannan tunanin hankulansu yayi daya suka cigaba da harkokinsu....

Kwance yake akan resting chair a gidan yake,
wani littafin addini yake dubawa yana kara zurfafa iliminshi akan karfafa gaskiya a cikin aikinshi,
gaba daya ya maida hankalinshi akan littafin, burinshi kawai duk shariar dake gabanshi ya aiwatar da ita bisa gaskiya da amana,,
wannan dalilin ne yasa wata kotu mai zaman kanta a kasar singapore suka rikeshi aikin dindindin saboda kwazonshi da nutsuwarshi, sam wasu kyalekyalen duniya basu dameshi ba,
aikinshi kadai yasa a gaba kuma cikin ikon Allah duk wani aiki da akazo mishi dashi sai ya samu nasara akanshi saboda tsayuwar da yayi akan ibadarshi da kuma rikon amana,
muryar abokinshi naji yana fitowa daga kitchen rike da glass cup din juice a hannunshi yana cewa ya ustaz yau dai we are free rabon da mu zauna mu samu hutu yafi sati uku saboda wannan shari'ar,,.
yau daya dai sai ka ajiye littafin hannunka muyi hira mu kira gida muji lafiyarsu anjima kuma mu fita yawo muyi murna saboda samun nasara akan wannan shariar da ta kara daga sunanka a cika da batsewar singapore,
SALEEM ya rufe littafin ya mike ya zauna ya karbi cup din ya kora juice yace amma ay ansha bakar wahala kafin samun nasarar,
ni dai kam babu inda zani gara in zauna abuna a gida in huta in samu lokacin da nayi sati biyu ban samu ba mu gana da ubangiji na,
Isma'il yayi murmushi yace Allah taimaki ustaz ina son halin nan naka nima Allah ya koyar dani kyawawan dabiunka,
saleem yace ya koyar da kai kyawawan dabiun da manzon mu,,
ya rage namu mu bi ko mu bi san ranmu, amma ko wani muslmi Allah ya koyar dashi dabi'u na gari in har xaiyi koyi da sunnar manzo s.a.w,
isma'il yace hakane saleem Allah ya ganar damu,
ya dauki wayarshi da ya bude data tun dazu yana jiran ya gama komai ya hau ya sada zumunci da yan uwa da abokan arziki,
saleem kuwa komawa yayi ya kwanta ya lumshe idonshi zuciyarshi na tasbihi ga Allah,
Isma'il ya gama gaishe gaishen da xaiyi a whatsapp ya dan bata lokaci yana hira da budurwarshi da sukayi missing juna,
facbk ya hau,,
news feed barkatai ya gani ya shiga binsu yana girgiza kai da Allah wadai da shuwagabannin mu na Nigeria,
Rariya, Sahara, naija report da sauransu a gurin yaga abubuwan da suka girgizashi, duba date din yayi yaga tun on 3rd sept abin ya faru,
sannan yaga har an shiga kotu 12 sept, a zuciyarshi yace wannan kisan ya kusa 3wks kenan ma, innalillahi wa inna ilair rajiun shi ya fadi da karfi,
saleem ya bude idonshi yace lafiya ismo me ya faru, isma'il yace wani alamari nagani mai ban tausayi gashi nan a rubuce wai an kashe "Air- marshal Hasheem abubakar marafa",
saleem ya zabura ya mike zaune yace watt,?? isma'il ya mika mishi wayar yace kalli kagani kuma surikarshi ake zargin ta kashe shi,
saleem ya karbi wayar da sauri, hoton zulfa da sunanta da yagani shi ya sashi mikewa tsaye ko ina na jikinshi na rawa,
isma'il ya mike shima yace kaga rashin imanin mutane ko, yanzu yar wannan yarinyar har tana da dabarar kisan babban mutum haka,
yaran yanzu duniya kadai suka sanya a gaba,.
saleem cikin rawar murya yace "allahumma ajirni fi musibtn wa akhlifni khairan minha, la haulu wala kuwwat illah billah"",
ya koma dabas ya zauna, isma'il yace saleem lafiya,
saleem idonshi yayi jajur yace isma'il zulfah bazata iya kisan kai ba,
isma'il ya dafashi yace u mean zulfar da ka taba bani labarinta ce wannan,
saleem ya daga mishi kai,
ismo yace ya Salam kaga tsiyar rashin xama current ko,
kai kullum sai kace mu daina shagala akan waya ko wasu abubuwan more rayuwa kuma wallhy saleem nwadys sai ta waya aka fi jin duk wani abun da ke yawo a fadin duniya,
yanzu gashi abu har ya kai three wks har an shiga kotu za"a kuma shiga on d 10th, saleem dai bai ma san me ismo yake cewa ba,
mikewa yayi ya shiga ciki ya kunna wayarshi,
texes ne suka fara kara kainin shigowa cikinta, dan har ya manta rabon da yayi amfani da ita,
text din yayanshi malam labaran shi ya bude ya karanta magana ce yayi mishi akan mutuwar da yarfen da akayi ma zulfah,
bai bude sauran ba ya shiga kai kawo cikin dakin,
ismo ya shigo ciki yace saleem yanzu ya za"ayi kenan,
saleem murya can ciki yace abin da nake tunani kenan isma'il, yarinyar nan tana cikin matsala babba,
dole in nemi tafiya cikin kwana uku ismo, wannan hakkin ya rataya a wuyana dole in san yadda xanyi in fitar da ita daga cikin kangin da take ciki, kuma dole a gano koma waye yayi wannan kisan in shaa Allahu zan tsaya kai da fata sai an gano ko waye an hukuntashi,
ismo ya dafa shi yace tare zamu tafi saleem, duk wani aiki tare muke yinshi wannan ma tare zamuyi in Allah ya yarda sai munga karshen shari'ar nan cikin kankanin lokaci duk da tana da zafi amma a gurin Allah mai sanyi ce,
saleem yace nagode sosai ismo ya kamata tun yanxu mu fara shirya shiryren tafiya, ismo yace hakane bari inyi wanka mu tafi.....

Mrs tijjani shattima ...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 6⃣1⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Ranar laraba karfe 6 na yamma jirginsu ya sauka a abuja,
ismo nata raba ido a airport din ko zaiga yayanshi har suka kusa minti goma bai hango kowa da ya sani ba,
can yaji anyi ihu a bayanshi an dane kanshi ya juyo da sauri yaga kanwarshi Nafeesah,
yayi dariya yace feenah bakya girma ke ko,
so kike ki ballani, ta shagwabe fuska ta turo baki tace kai yaya iloli dan ma kaga ina murna shine zaka cemin haka ko,
yace to am sorry sis baki gaisar da bako na ba,
ta matsa kusa da saleem ta tsuguna tace ina wuni,
saleem yace lafiya lau, ismo ya kalleta yace yaya bai zo ba ko,
tace ay baya nan shine ya kira anty tasa driver yazo ya daukoka,
ta dauki wata jaka a kasa tace muje yaya dare nayi,
ya kamo hannun saleem suka wuce, suna karasawa gidan su dake sun city anan cikin garin abuja ismo yasa aka kwaso musu kaya suka shiga ciki bayan sun gaisa da Anty husaina suka wuce dakin ismo nan suka huta suka ci abinci suna hirarsu cikin nutsuwa akan ta inda xasu fara binciken tunda yau kwana 8 ya rage a shiga kotu..

Karfe 11 na ranar alhamis a kofar gidan su sadeeq tayi ma su saleem,
bayan gajerun tambayoyi da masu gadi sukayi musu, sannan suka bude musu kofa suka shiga ciki,
sallama saleem ya tsaya yayi kafin ya danna bell,
farouk dake gyara agogo suna shirin fita shi da anty laila shi ya bude musu kofar, saleem yayi mishi sallama ya mika mishi hannu suka gaisah sannan yace dan Allah hajiya na nan,
farouk yace eh ku shigo mana, suka shigo suka zauna farouk ya hau sama ya kira mummy, tare suka sakko tana ganin malam saleem ta fadada fara'arta, ta nemi guri ta zauna suka gaisa sukayi mata gaisuwar rasuwar mijinta,
hira suka taba kadan akan nasorarin da ya samu tayi mishi murna sosai shima yayi mata godiya saboda itace silar cigaban shi, ,
anty laila ta fito daga daki suka gaisa dasu saleem, ta kawo musu dan abin tabawa, saleem ya fara tambayar mummy maganar zulfah, ta gyara zamanta fuska cike da damuwa ta kwashe komai ta fada mishi,
shi da ismo dai sukayi tsamm cikin tunani, barr saleem yace hajiya kiyi hakuri, karki ce na karyata hujjojin da aka gabatar,
kuma karki ga kamar ko zan goyi bayan zulfah ne amma zan tsaya inyi bincike har agano gaskiyar wannan lamarin,
in zulfah nada hannu a ciki zan tsaya kai da fata inga anyi mata hukuncin da ya dace, mummy tayi ajiyar zuciya ta rage muryarta tace,
saleem zuciyata ta kasa gasgata wannan alamarin,
amma bani da yadda zanyi saboda kwararan hujjojin da sukayi ma alamarin nan kawanya,,,
yanzu dai kasan abin da nake so da kai, ka tashi ka fita waje zan turo maka laila dan itace lawyern dake bincike akan alamarin, banason ko kadan mu sake tattauna wasu maganganu a cikin gidan nan,
saboda zuciyata bata aminta da mutanen dake cikin gidan ba, Allah ya gaggauta bayyana gaskiya, suka ce amin,,
suka mike cikin farin cikin mummy bata yarda ba ita ma saleem yace to nagode hajiya sannan suka fita shi da ismo suna tattauna karamci irin na mummy,

A dakin sadeeq mummy ta samu laila suna zaune ya dafe kanshi da ruwan lipton a gabanshi, tana lallabashi ya dan sha sannan ya danyi mata bayani akan abinda yace daddy ma ya kirashi ya fada mishi, ya dan kurbi lipton din yace ehh daddy ya kirani ana gobe zai dawo ya fada mata duk tambayoyin da daddy yayi mishi,
mummy dake tsaye a kansu tace laila kira farouk kuje ga baki can a waje suna jiranku, anty laila tace to mummy,
ta mike ta fita tabar mummy gurin sadeeq itama tana rarrashinshi akan yaci wani abu...

Mota daya suka shiga dukkansu su hudun suna tafe suna tattaunawa suka wuce gurin zulfah,
anty laila tace wallhy malam yarinyar nan bazata taba yi maka magana ba,
ita kullum burinta a barta a yanke mata hukuncin kisa shiyasa bana bi ta kanta yanxu a bincike na,,
saleem yace to bari mu je in jarraba in gani,
suna karasawa anty laila tayi zamanta a mota dan ji takeyi kamar ta shaketa ta huta,

Zaune take kamar kullum a takure kanta na cikin cinyoyinta, karasawa sukayi suka tsuguna kusa da ita, saleem ne ya fara mata magana,
ta gane muryarshi tsaff amma taki dago kanta ta kalleshi,
cikin dabara ya kara mata magana,
zulfa'u ki saurareni da kyau kiji abinda zan fada miki,
ruwanki ne ki dauka ruwanki ki zubar ni dai na fita hakkinki kuma na sauke alkawarin da na daukarwa kaina cewar duk lokacin da kika shiga cikin wani hali zan taimaka miki,
rayuwar dan adam tana da matukar muhimmaci zulfa,
dan adam duk tsanani baya ma kanshi fatan mutuwa,
me kika tanada yanzu idan kin tafi lahira,?
wa kika ajiye a duniya da zai miki addua ko bayan ba ranki,
ko kina tunanin wannan taurin kan da kikeyi in har aka kasheki zaki je ki samu rahamar ubangiji,
to bari kiji in fada miki, ubangiji na baiwa dan adam dama a rayuwar shi,
kinga wadannan damomin da kika samu ubangiji shi ya turo miki su,kinga anan rashin maganarki ya nuna cewar bakya farin ciki da abinda Allah ya turo miki dashi,
shin kina tunanin mahaifinki kuwa, ashe bazaki godewa Allah da ya baki gida irin wannan da har suke tunanin taimaka miki duk da irin karfin hujjojin da aka kafa akanki ba,
zan barki yanzu babu wanda zai sake dawowa gareki,
amma ki sani har a nade duniya sunanki bazai taba goguwa akan wacce bata da imani mai kisan ba, kuma ko a lahira shaidar mutane na iya cetonka ka shiga aljanna,
kinga anan kin rasa wannan shaidar, sannan zunde da maganganun da za'ayi tayi akanki zai iya daurawa mahaifinki ciwon mutuwa kinga kenan laifin kisan kai biyu kenan da naki da na mahaifinki,
dan haka na barki lafiya in an kasheki zan miki adduar samun rahama, maganganun malam saleem sun sanyaya gwiwar zulfah,
jin takun tafiyarshi yasa ta kara fashewa da kuka mai tsuma zuciya,
farouk idonshi ya ciko da kwalla yace zulfah dan Allah dan annabi ki yi mana magana wallhy mutane da yawa suna cikin halin kunci akan wannan alamarin kuma rashin maganarki zata cutar da rayuka da dama ciki harda dan mala'ikan Allah dake cikinki,
da sauri ta dago kanta idonta kamar nama ta shafa cikinta tace yaya farouk me kukeso ince, me kukeso in fada muku,
kome zan fada muku baida karfin da zai fitar dani daga wannan kazafin da akayi min, saleem da ya kusa kaiwa kofa ya dawo rai a bace yace kalma daya ta gaskiya zata iya tarwatsa kalmomi dubu na karya, saboda haka ki bude baki ki bada amsar tambayoyin da zamuyi miki,
ta gyada kanta tana kuka sosai,
farouk baisan sanda murmushin jin dadi ya kubuce mishi ba,,
ismo yace ki nutsu sosai duk abinda aka tambayeki ki yi tunani da kyau kafin ki bada amsa,
tace to,,
saleem yace a ranar da abin ya faru ance babu kowa a cikin gidan sai ke ko,
tace eh,
yace to amma ance wai wata tazo gurinki a lokacin,
zulfah tace ni babu wacce tazo guri na, ismo yace kuma babu wanda kika gani ko kuma kikaji muryarshi kodai wani abu makancin haka,
ya kalli saleem yace kasan meyasa na tambayeta haka, saboda wanda ya shirya wannan plan din a tym din ya shirya shi tunda har masu gadi sun ga mutum biyu sun shiga cikin gidan, kaga dole wanda yake cikin gidan yaji ko yaga wanda ya shigo,

zulfah tayi shuru tana tuno sanda ta fito wanka taji buruntu a gurin dining da kuma ganin da tayi ma beeba,
da sauri tace ehh wallhy na ganta lokacin da na fito wanka naji kamar ana taba wani abu a gurin dining da na fito banga kowa ba ta window na hangota,
kuma wayata ma na kan dining sai a lokacin na dauketa, jikinta ya fara rawa tace wallhy na ganta....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 6⃣2⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Saleem cikin farin ciki yace wacece ita,
Zulfa tace kawar sanah ce,, wallhy ita na gani kuma itama ta ganni,
farouk yace kawar sanah wacce a ciki, tayi shuru tana nazari can tace Beebah ce ita nagani,
farouk yace Habiba Garba kike nufi, tace eh ita wacce suke zuwa gida tare da sanah gurin anty amarya, farouk ya tashi ya fita da sauri,
gurin anty laila ya nufa dake zaune cikin mota ya bude motar yana sauke numfashi yace anty tunaninki ya zama gaskiya,
zulfah tayi magana tace taga beeba a cikin gidan mu on dat vry day, anty laila da sauri ta fara maida takalmanta kafarta ta bude motar suka fito ita da farouk suka koma ciki,
suna shiga anty laila ta dafa ta tace haba zulfah kinsan da wannan shaidar kikayi shuru kika bari munata wahala,
ta kalli su malam saleem tace alhamdullah yanzu komai zai tafi da sauki ay ko gobe ma a shiga kotu,
saleem da isma'il suka kwashe da dariya suka ce da wace hujjar,
anty laila tace wannan hujjar mana ay wannan hujjar mai karfi ce tunda me ya kawota gidan a wannan tym din gurin wa tazo,
saleem ya mike yayi murmushi yace anty wannan hujjar bata karfi ko kadan mu ne zamu maida hujjar ta zama mai karfi,
a yanzu in muka shiga kotu da wannan shaidar to tabbas zamu rikito,
beeba nada access da gidan ko ba haka ba, duk suka gyada kansu, saleem yace xata iya denying flat tace aiko ta akayi ko kuma tace tare suke da anty
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment