Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

gafararshi ki tuba ki koma ga Allah,
babu mahaifin da zaiso raba danshi da matarshi menene aibu a cikinshi in kika tuba kika koma ga Allah kika rungumi mijinki da gidanki kikayi watsi da duk wasu abubuwa da kikeyi marasa kyau, meyasa kika zabi maida yayanshi marayu,
meyasa??
Sanah ta fashe da kuka ta hada hannunta guri daya tace wallhy sharrin shaidan ne da rudin zuciya,
dan Allah kuyi hakuri,
hayaniyya ta kaure a gurin duk kokarin da alkali yayi akan ayi shuru amma abun yaci tura saboda masu Allah wadai da halin sanah,
saleem ya kalli alkali yace ya mai shari'a shaidun sun gabata a gaban ka kuma sannan itama ta amsa da bakinta,
yanzu kawai abun da ya rage min daga shi zan barka kayi naka shine a gayyato min wacce tayi ikirarin ita kawar zulfah ce da kuma saurayin nata,
anty amarya ta sulale kasa saboda tsananin rudu tace yau na shiga uku,
ganin an shigo da su maimzy suma suna zare ido yasata boye kanta a kasan kujera, saleem ya kalli maimzy yace aminiyar zulfah barkanki da warhaka,
murya na rawa tace barka dai,
yayi murmushi yace tooo maimzy yanzu dai kinji yadda sharia ta juya ko,
maimzy ta hadiye miyau tace eh, saleem yace to yaya abun yake kiyi min bayanin yadda akayi shariar ta juye yanzu,
kafin ki ce komai ina so in tunatar dake wani abu,
rayuwar duniya ba matabbata bace, yanzu nan gaki a gabana in lokacinki yayi zaki mutu, karki ga Allah na ara miki lokaci kice zakiyi duk abinda kikaga dama,
zaki iya gama fadin abinda zaki ce yanzu Allah ya amshi rayuwarki kinga kinyi pleasn wasu a duniya zaki je lahira ki tadda azaba mai radadi,
kiji tsoron haduwarki da Allah ki fadi abinda kika sani saboda shaidarki bata da wani tasiri a wannan shariar ko kin fadi karya ko gaskiya bazaki canza shaidun baya ba saboda haka gara ma ki fadi gaskiya ko Allah zai yafe miki sharrin da kikayi a baya,
jikin maimzy yayi sanyi sosai a hankali tace wallhy ban taba ganin zulfah ba tun da nake a rayuwata,
ina zaune a daki bamba yazo min da kudi yace wai zamuyi wani aiki,
ganin zunzurutun kudi har 200k yasa na amince ya fada min so yakeyi muje wani gida mu bada shaidar karya akan wata yarinya, bayan ya gama min bayani ya dauko ni ya kawoni gidan lokacin ana zaman makoki, muka shiga dakin matar da tasa shi aikin tayi min bayanin komai sannan suka yi waya da bamba,
ni dai waya kawai suka bani da hoton da suka hada nawa ni da bamba aka cire fuskata aka sa ta zulfah,
anan ta kara min dubu 100 tace in aiki ya gama kammala zatayi mana kyauta ta musamman,
dan Allah ya mai shari'a kuyi min afuwa wallhy ba yin kaina bane,
saleem ya juya ya kalli bamba da gumi ya jikashi yana hararar maimzy yace malam bamba yi hakuri ka daina harararta taji tsoron Allah ne ta fadi gaskiya, ka sani ko wannan ya zama sillar shigarta aljanna, yanzu ya rage naka ka karasa mana ka tafi ko kayi karya ka dawwama a prison har mahadi ya bayyana,
murya dashe bamba yace duk abinda maimzy ta fadi gaskiya ne,
hajiya hadiza amaryar marigayi ita ta sani, dalili kuwa shine,,
ni dai kawali ne ina nemo ma manyan maza masu mulki mata in kai musu,
to a wata ranar alhamis ne karfe uku na rana na kirata a waya dan ranar ne minister umar marke zai shigo kaduna dama sun saba haduwa da ita, da na kirata nake sanar da ita isowarshi nace mata muna 17 hotel, nan da nan tace gata nan zuwa to muna tare dashi da wani ashe mijinta ne ni bansani ba,
bayan ta iso muka shiga dakin hotel din lokacin hon umar yana bawa mijinta labarinta, tana shigowa suka hadu da mijinta,
cikin rudewa ta fita da sauri tana kuka sosai ta wuce gida shi kuma saida ya kusan awa a zaune kafin ya iya mikewa hon umar na bashi hakuri har ya rakoshi bakin mota bai iya ce mishi komai ba,
bansan ya suka kare ba a gida, ni dai washe gari na kirata take cemin ay an fitar dashi england bashi da lafiya, kuma ta shiga dakinshi taga takaddar da ya rubuta mata na saki amma bai bata da hannunta ba,
shine tace bazata yarda ya dawo ya bata takaddar ba saboda zata tashi a tutar babu duk irin bautar da tayi ma gidanshi,
nan ta ce inzo in rakata wani guri,
Gurin boka na rakata ya bata wani magani dan cewa tayi kasheshi zatayi, saboda tasan yana dawowa zai bata takaddar,
a hanya ta sauke ni tace duk yadda ake ciki zata nemeni, kwana uku tsakani ta kirani da daddare tace aiki yayi kuma yanzu ta daura zargin akan wata yarinya saboda haka gobe muzo dan musan yadda zamu daure yarinya saboda binciken ya tsaya a kanta kadai,
ya fara kuka yace nayi kuskuren biye ma zuciyata in aikata wannan aikin dan Allah ku yafemin,

Innalillahi wa inna ilaihir rajiun shi kadai kake ji a cikin kotun, sadeeq dake zaune kanshi a daure hawaye na bin idonshi yace guba biyu kenan daddy yaci,,,
sanah ma ta girgiza sosai da jin wannan jawabin,,
saleem kuwa dafe kanshi yayi cikin rudun jin zancen bamba....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 6⃣8⃣
By Aysha Ya'u kurah

Kan anty amarya kallo ya koma,
jalila ta mike daga kusa da ita da sauri tana kallonta, anty amarya dake durkushe a kasa tace sharri yake min jalila karku yarda da zancen shi,
ya za'ayi in kashe daddy me yayi min?
Magana taji a bayanta ta waiga da sauri taga wani dansanda, cikin firgici ta mike tace wallhy karya yake min, dan sandan yace karaso muje kiyi bayani a gaban kotu,
anty amarya ta shiga gaba tana kuka har ta kai gaban alkali ta hade hannayenta gurin daya tace ya mai shari'a wannan mutumin karya yake min wallhy hada baki sukayi dan suyi min sharri,
anty laila ta mike da sauri tace su waye suka hada baki dan su miki sharri,
kin dauka kowa irinki ne wacce kullum zuciyarta ke saka sharri, waye ya kawo mana maimzy da bamba cikin gida,
daga dakinki kuka fito tare kina kuka kamar dagaske, abunda baki sani ba anty shine shi sharri fa dan aike ne wallhy duk inda yaje sai ya dawo gurin wacce ta aikeshi, kawai yanzu ki saukakewa kanki kiyi ma kotu bayanin gaskiyar abinda ya faru dan da gaskiyarki da karyarki duk daya ce tunda shaidu sun gabata a gaban alkali gara ma ki fadi gaskiyar ko zaki samu sassaucin azabar da Allah zaiyi miki,

Anty amarya ta durkushe tana kuka mai sauti tace na cuci kaina,
nabi son zuciya na aikata ba dai2 ba, ban taba tunanin zuwan wannan ranar ba, lallai duk wanda ya dauki duniya da zafi yana cikin masifa kamar yadda na fada cikin ta yanzu,
tabbas abinda bamba ya fadi gaskiyane,
domin da zulfau ta gama aikin abincin sai na faki idonta kamar na fita,
saida na bari ta shiga wanka sannan na fito na zuba maganin na fita daga gidan gaba daya,
washe gari da naga ana bincike kuma babu mamakin bincikensu ya dawo kaina shiyasa na sa bamba ya kara dabaibaye zulfau a ciki saboda binciken ya tsaya a kanta ita kadai,
sannan maganar saki tabbas nasan ya sakeni lokacin da na shiga dakinshi yana bacci naga takaddar, kafin in kai ga yagawa ya bude idonshi ya ganni da sauri ya mike yace gara da Allah yasa kika gani da kanki dauka kije Allah ya isa tsakanina dake,
nan na fara gaya mishi bakaken maganganun da suka kara tayar mishi da ciwo,,
da naga ya kwanta yana kuka sai na fita na yaga takaddar da niyar bazan fada ma kowa ba kuma bazan yarda yasan ina gidan ba,
sai na fara tunanin in kawar dashi kawai saboda nasan in iyalinshi suka san mun rabu bazan ci wani abu daga cikin dukiyarshi ba,
ta fashe da kuka tace sai gashi yanzu na tashi a tutar babu, babu kudi babu kima,
"sannan kuma babu rayuwa nurain ya fadi da karfi idonshi na zubar da kwalla, ya karaso kamar zaki ya dagota ya shaketa yace wallhy yau saina kasheku dukanku, babu wanda zan bari da rai in har na barku to tabbas ban cika dan mahaifina ba,
da kyar aka banbare hannunshi a wuyan anty amarya ya durkushe yana kuka mai tsuma zuciya, farouk, laila da jalila suka karaso gurinshi suna bashi hakuri suna kukan suma,
babu wanda a gurin bai zubda hawayen tausayinsu ba,
sadeeq ya mike ya fita da sauri kamar mahaukaci,
hilal ya bi bayanshi yana kiranshi amma ina sadeeq har ya shiga mota ya tada ta ya fita,
da sauri hilal ya shiga tashi ya bi bayanshi wani irin mahaukacin gudu sadeeq yakeyi ya doshi wani daji yana keta bishiyu yana kuka sosai dan a ganinshi duk shi ne silar mutuwan mahaifinshi, duk irin gudun da hilal keyi baisa ya cimma sadeeq ba,
haka mutanen dake hanya wasun su suka biyosu dan ganin abinda ke faruwa, saida ya isa daidai wani katon rami sannan yaja baya hilal ya sauko da sauri ba tare da ya kashe motarshi ba yana ihu yana kiran sunanshi amma inaa sadeeq ya riga yayi nisa baya jin kira,
runtse ido hilal yayi hade ihuuu ya durkushe a gurin sakamakon fadawar sadeeq wannan katon ramin,
da sauri mutane sukayi dafifi a gurin ana kallon ikon Allah dan yadda motar ta tarwatse sunsan dakyar rai zai fita a ciki sai dai wani ikon Allah,,
hilal kasa motsi yayi Idonshi ya kafe hawaye suka ki fitowa a cikinsu saboda tsananin tashin hankali,
sai mutanen dake gurin ne sukayi iya kokarinsu dakyar aka janyo sadeeq da yayi paca2 da da jini babu alamar numfashi a tare dashi,,
a rude mutanen da suka rikeshi sukayi motar hilal dashi baya hilal ya shiga ya rungume sadeeq sai a lokacin hawaye suka fara zuba a idonshi yana kuka yana fadin why marafa, meyasa zaka kashe kanka da gangan, kuka yakeyi sosai da kyar suka rarrashe shi wani a gurin ya shiga motar ya tuka suka wuce Mends specialist hospital...

A kotu kuwa bayan an tsagaita da koke koke alkali ya tattara shaidu sannan ya kalli barr tahir yace ko yanada jaa, barr tahir jiki a sanyaye yace a'a ya mai shari'a,,
alkali yace to bisa kammaluwar gabatar da shaidu kotu ta gamsu da shaidun da aka kawo mata saboda la'akari da karfinsu sannan kuma masu laifi sun saukakewa kotu ta hanyar amsa laifinsu da sukayi,
saboda haka kotu ta wanke zulfa'u Adam daga zargin da ake mata da kuma tarar miliyan goma sha biyar saboda kazafin da akayi mata da zaman matsi da takura da tayi a police station,,
sannan kotu ta yanke wa maimzy shekara biyu bamba kuma shekara sha uku a gidan yari saboda harda shi aka je aka karbo maganin da aka zubawa marigayi ya mutu dan da ya fadi da wuri hakan bazai faru ba,
sannan bisa adalcin kotu da kuma saukake ma kotu da sukayi ta hanyar fadin gaskiya kotu ta yanke ma hadiza matar marigayi da sanah matar danshi hukunci ta kisa hanyar rataya,,
sai kuma beeba da ta taimaka gurin nemo guba, kotu ta yanke mata hukuncin daurin rai da rai,
ihuu suka dingayi suna kuka suna fadin a yafe musu, babu wanda yaji tausayinsu sai yar uwarsu aneesah dake kuka ta kira maman sanah ta fadi mata kuka ta dingayi itma a wayar kamar tababbiya,,

alkali yace alhamdulillah mun gode ma Allah da ya kawo mana karshen wannan shari'ar kuma ya bayyana gaskiyar dake cikinta cikin kankanin lokaci,

yaku mutanen dake zaune a gurin nan,
shin me wannan shari'ar ta koyar daku,
babu wanda yayi magana shuru kotun tayi saboda suna son jin kalaman hikima daga bakin alkali,
alkali yace tabbas Allah mai girma da daukaka ya koyar da darasi cikin zamanmu na farko,,,
a shariar karshe kuma ayah ce ta sakko daga gurin Allah swt,
shin akwai wanda yayi tunanin fitar zulfah daga cikin wannan rikitaccan dabaibayin da akayi mata,
sai gashi cikin watanin da basu kai biyu ba Allah ya wanketa da shaidu masu karfin gaske saboda gaskiyarta da kuma tsaftataciyar zuciyarta,
shaida ta farko yadda karya ta shigo cikin tafiyar sanah wanda ta fadi ma mutane uku kasar da take,
ta fadi ma mijinta taje india jinya, sannan saboda toshewar basira ta fadi ma kanwar mahaifiyarta taje dubai sarin kaya, sannan tayi ma mahaifiyarta karyar suna england ita da mijinta,
ikon Allah kenan zai ta ara maka lokaci amma in yaso a lokaci guda alakadarinka zai karye,
shaida ta biyu mukhtar yayan ismail wanda ikon Allah ne ya hada ismail da saleem har Allah ya kawosu taimakonta;, cikin labarinsu mukhtar ya gane akwai makarkashiya har Allah yasa yaga jawabin beeba ya tabbatar da gaskiyar abunda yake tunani har ya fada musu sirrinshi,
shin in ba Allah ba waye zaiyi wannan, gurin ya rude da cewar Babuuu,,,
sannan shaida ta uku shine mati drivern taxi wanda mutuwar mahaifinshi yasa shi barin tukin taxi ya siya napep Allah cikin ikonsa yasa a ranar da motar laila zata lalace shi kuma a lokacin Allah ya turoshi domin ya daukesu har yaji jawabinsu shima Allah ya matsi bakinshi ya fadi saboda dai yana son wanke baiwar shi mai yawan bauta mishi in banda Allah wanene zai iya wannan hadin cikin lokacin da ake bukatar taimako,
nan ma kowa yace babuuu,
sai kuma shaidar beeba da Allah ya toshe basirarta ya rufe mata ido da son kudi wanda har soyayyar su ya sakata yin SUBUL DA BAKA ( littafin my one nd only zeedee) ba tare da tayi tunanin abinda fadin zai jawo mata ba, lallai wanda ya yarda da Allah to tabbas baxai taba tabewa ba kuma babu wanda ya isa yaga bayanshi cikin sauki, sannan shaidar da tafi bani mamaki bai wuce shaidun mutane biyu ba wanda a farko suke bayan karya a karshe kuma suka ji tsoron Allah suka fadi gaskiya cikin gaskiyar har aka gano rikitaccan alamari wanda akayi shi bisa dodewar basira,
dan da bata sako su cikin shaidu ba bincike bazai taba hawa kanta ba saboda babu wanda ya ganta sai Allahn da ya dode mata kwakwalwa ya sanyata sakosu ciki saboda ya tona mata asiri,
lallai Allah mabuwayi ne gagara misali,
ya yan uwana muji tsoron Allah, mu tuna da ranar da uwa bazata iya ceton danta ba,
ranar da aikinka na lada zai taimakeka, ranar da babu wata inuwa sai inuwar alarshi,
shin muna yiwa kanmu hisabi a kullum idan mukaje yin bacci, shin akwai wanda yake tuna in ya kwanta ba lallai bane ya bude idonshi gobe ta riskeshi,
shin muna tuna akwai babban tashin hankali a gaban mu bayan an gama hisabi wanda shine tsallake siradi, duk musulmi mai hankali tabbas baya cikin kwanciyar hankali saboda bai san ina ne makomar shi, ya kamata dukkanmu nan da ma wanda baya nan yasan ba aikinmu bane zai kaimu aljanna rahamar Allah ita kadai ce zata kaimu aljanna,
dan haka ya yan uwa mu yawaita tasbihi, istigfari da hailala, da kuma salatin fiyayyen halitta annabi muhammad sallalahu alaihi wasallam,
bakin ciki bazai taba riskar wanda yayi riko da alkur'ani ba saboda shi alkur'ani jagora ne kuma ginshikine a cikin rayuwar mu baki daya,
ina rokon Allah da ya hane mu duk wani aiki na sabo a gareshi yasanya mana tsananin son yin aikin da zai kusanto mu gareshi,
ya Allah ya hadamu cikin aljanna firdausi baki dayanmu, ameen thumma ameen,

jinjina gareka barrister saleem da kuma ismail da laila da ta tsaya kai da fata gurin binciken gano gaskiyar wannan alamarin saboda kyakyawar zuciyarta,
wadanda suka mutu Allah ya jikansu mu kuma Allah ya sa mucika da kalmar shahada,,,
ameen mutanen gurin suka fadi sannan kotu ta tashi kowa ya mike masu murna suna murna rolex da jalila da zabba'u suka rungume zulfa'u dake kuka sosai can kuma su anty amarya ce ke kuka yan sanda sun sakasu a gaba sun tafi dasu,
barr saleem suka fita waje shida su ismo mutane sai sam barka ake musu cikin farin ciki, baban zulfa kamar zai durkusawa laila da saleem saboda murna yanata godiya babu kakkautawa, gurin motocinsu suka wuce sunata hirarsu cikin jin dadi,
nurain na bude motarshi yaji wayarshi na ringing, kafin ya daga ta katse ya duba yaga misd cals da yawa,
yace hilal lafiya, yana waige2 dan yasan ya ganshi a cikin court, kiranshi yayi, hilal ya dauka cikin kuka ya fada mishi abinda ya faru,
a gigice yace whattt, innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
laila da su farouk suka ce lafiya yaya, ya fada musu abinda ya faru cikin rudu yace laila ku wuce gida bari inje asibitin, tace a'a mudai je tare farouk dauke su ka kaisu gida amma fa kar ka fada ma mummy komai sai munje mun ga jikin nashi kaji,
farouk jiki a sanyayye yace too, suka wuce gida, anty laila da su malam saleem da baban zulfah suka wuce asibitin...

Mrs tijjani shattima....
[15/12 14:48] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ ZULFAH ◆◆ 6⃣9⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Hankali a tashe suka karasa asibitin har lokacin likitoci na kan sadeeq da ya ji ciwo sosai a jikinshi, Allah ya taimaka babu karaya da buguwa amma har lokacin bai farfado ba,
saida suka kusa awa akanshi suna dressing ciwukan jikinshi, sannan suka fita bayan an daura mishi drip,
doctor na fitowa suka karasa gurinshi a rude suna tambayarshi, doctor yace su kwantar da hankakinsu babu abinda zai sameshi yayi musu bayanin komai yazo da sauki at any mmnt xai iya farkawa,
suka tambayeshi zasu iya shiga yace ehh amma banda hayaniya,
shiga sukayi da sauri suka ga gurin da yaji ciwukan goshinshi sai hannunshi da kafadunshi, alhamdulillah suka dinga fadi saboda Allah ya kiyaye sannan suka zauna jiran ya farfado...

Suna karasawa gida mummy na parlor tana kuka sosai kamar ranta zai fita saboda ganin da tayi ma shariar a ait,
afrah da amrah na kewaye da ita suma kukan sukeyi ayda na share ma mummy hawaye tana bata hakuri,
ganin shigowarsu yasata mikewa ta rungeme zulfah tana fadin ki yafe min zulfah,
zulfah na kuka itama tana share ma mummy hawaye tace wallhy ban taba kullatarki ba mummy, babu abinda kikayi min dan Allah ki daina kuka,
mummy ta janyota suka zauna tana kallon ta cikin kuka tace tashi kije kiyi wanka kici abinci kizo ku tafi asibiti da farouk a duba lafiyar jikinki, zulfah ta mike suka wuce ciki Ita da jalila da zabba'u,
wanka sosai tayi ta wanke kanta da yayi mugun datti tayi alwala ta fito tayi sallah tana godewa ubangiji da ya wanketa daga wannan zargin da ake mata,

Abinci aka loda a gabanta kamar jaka ta bude baki tana hararar jalila tace ko jaki kika zubawa abincin nan banjin zai iya cinyeshi,
jalila tace bansan iskanci kinsan wahalar da nasha kafin in gama miki girkin nan, gobe ma ranace in na tafi zanga wanda zai cigaba da dafa miki irin me dadin nawa, ta ajiye spoon din zata wuce zulfah ta janyo hannunta tace dan Allah anty jalila ki yi hakuri,
haba amaryar isiyaku, zabba'u ta kwashe da dariya tace ay fa sai isiyaku,
jalila ta zauna tace duk zaku sani wallahy zan rama ne in na tafi gobe baku kara ganina sai haihuwarki,
zulfah tayi murmushi tace wai ku wa ya fada muku ina da ciki, jalila ta shafo cikin tace mummy mana,
dan Allah ki haifo min takwara, zabba'u ta harareta tace ko kuma sakwara ba,
kinji ta hannun daman ni zaki haifo ma takwara ko, ita dai abincinta take ci bata ko kallesu ba dan ita gani takeyi duk wasa suke mata,
saida suka gama cin abinci sannan suka wuce asibiti, dubata dr balogun yayi da kyau sannan ya bata magunguna ya dibi jininta akayi test, doctorn na dawowa daga lab yace mata am happy 4 u kina da cikin wata biyu da kwanaki,
shuru zulfah tayi bayan ta karbi takaddar ta fito ta sami farouk suka wuce asibitin sadeeq a mota sai murna farouk yakeyi kamar matarshi aka ce tana cikin, ita kuwa har suka karasa sukuku take dan har ga Allah bata son abinda zai kara hadata da sadeeq da a yanzu ta gama tabbatar da jikinta yake so zuciyarshi sam babu ita cikinshi,
ta riga ta kudira a ranta zata rabu dashi ko da kuwa rabuwar zai haifar da bacin rai, suna karasawa farouk yayi2 ta shiga taki tace ya shiga ya fito, haka ya kyaleta ya shiga ya barta tanata sake sake,

Kwanan sadeeq tara a asibiti jikinshi yayi sauki sosai sai dai ciwonshi da bai warke ba saboda zufinsu, da kuma karfin jiki,
fada sosai nurain yayi mishi kamar zai ari baki,
haka mummy da taji tayi kuka sosai itama tai mishi fada a waya dan bata fita saboda takaba, kullum in za'aje duba sadeeq zulfah excuses take bayarwa ko tace bata da lafiya ko kuma tayi baccin karya ko in sunje tace su shiga zata shigo,,,
farouk da laila ne kadai suka dagota suma kuma sun yarda ta garashi din tunda zuciyarshi sam bata fada mishi gaskiya, in ya hau dokinta baya sauka sai da dana sani ...
Satinshi biyu aka sallameshi ciwukan sun warke kadan ya rage su gama heeln kuma ya samu karfin jiki sosai,
damuwarshi a kullum itace yasa zulfah a idonshi, yayi mamakin da ko sau daya bata zo duba shi,
kafin su tafi ran da aka sallemeshi farouk na rike da bargo suna fitowa yace farouk wai ina zulfah ne,
farouk ya hade rai yace jiya ta dawo gida kasan tabi babanta sai jiya barr saleem ya dawo da ita gida,
ya kauda kanshi yace yaya abba barr akwai kirki wallahi,
jiranka ma mummy takeyi akan takaddar zulfah saboda in ta haihu mummy da mahaifinta sun yanke hukuncin bawa saleem aurenta ay ya cancanci hakan ko yaya tunda kai da kyar zuciyarka zata kara baka hadin kan kasota,,,
sadeeq sai da ya kusa faduwa saboda karo da yayi da kujerar reception din, da sauri farouk ya rikeshi yace sannu yaya ka dinga kallon gabanka ko sai na rikeka ne,
sadeeq dai bai ce mishi komai ba zuciyarshi na suya har suka shiga motar suka wuce bai ce mishi komai ba,
farouk ya dinga gimtse dariyarshi saboda yadda yanayin sadeeq ya canza har suka kai gida sadeeq baisan sun kawo ba, saida farouk ya tabashi yace mun kawo yaya,sannan ya bude motar jikinshi a sanyaye ya fito a kofar parlon ya tadda mummy tsaye tana jiran karasowar shi, yana shigowa suka rungume juna idonta ya ciko da kwalla tace karka kara irin wannan gangancin abba na, shima idonshi yayi ja yace yi hakuri mummy in shaa Allahu bazan kara ba,
tace yawwa abbana ka dinga addua akan wannan zuciyar taka dan Allah dan ko kadan zuciyarka tana da rauni kuma kana biye mata ka dinga yawaita maimaita ""Allahumma ya muqallibal qulubi sabbit qalbi ana deenika""
kaji,,
ya gyada mata kanshi tace to maza muje kaci abinci sai kayi wanka ka huta kaji, jikinshi a sanyaye ya mike,, kenan mummy da gaske takeyi zata rabashi da zulfah tunda da ba haka ba ay da ce mishi zatayi yaje dakinshi matarshi ta bashi abinci,
yana isa dining room ya zauna mummy ta zuba mishi abinci, yana ci tana mishi hirah,
fitowa zulfah tayi cikin wata doguwar rigar light orange silk material kanta ba dankwali sam bata kula dashi ba tace mummy gashi malam saleem ne,
mummy tayi murmushi tace har sun isa ne, zulfa tace ehh tana murmushi, juyowar da zatayi suka hada ido da sadeeq ta dauke kanta tayi wucewarta tana tafiyarta mai jan hankali,
binta sadeeq yayi da ido zuciyarshi kamar zata faso kirjinshi saboda tsananin kishi, mummy ta kalleshi bayan ta gama waya tace saleem akwai mutunci wallhy yaron kirki,
sai yau suka tafi Singapore, mikewa
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment