Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

...."
Man zafi ya lakato ya soma murza mata a gurin yana tsuke ?aramin bakinsa mai matukar kyau ,  ta runtse idanunta  gam jikinta na sake ?aukar  kyarrrma "wayyo zafi  nake ji dan Allah ka min a hankali , jin yadda yake murzawa da karfi, yasa ta kwace ?afarta tana haki  "ka barshi  kawai na gode  ."duka lip's d'insa ya tura cikin bakinsa ya ciza yana Kallonta yana tunanin yadda zai ja mata kafar, wani tunani yayi samo mafutar yadda zai yi  yasa ya  sake kamo kafar a hankali  wani irin zirrrrrrrrr  taji tana fidda numfashi da kyar  saboda ji tayi kamar yana mata tafiyar tsutsa ne ,muryarsa a  kasanlance yace  ",kalli bayanki  kinga yadda sautin muryar ki  ya tashi aryan da reef  tana juyawa ya ciza lip's d'insa tare da  jan kafar da karfi  ji kake kassssss ........
Wani  razananniyar qara ta saki tare zubowa  jikinsa yayi saurin toshe mata baki da ....
Mmn sudais
????????????
CUTAR DA KAI
????????
????????????
~TRUE LIFE STORY~
Free page 10
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalmi, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ?aya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...????
Yayi saurin toshe mata baki da hannunsa yana zaro mata ido "kina hauka ne salon kisa yara su farka su ?auka wani mugun abu nake miki "? Wani irin harbawa zuciyarta tayi a sanda ta jita kwance a saman faffad'an qirjinsa dake kwance da laulausan  gashi , hannunsa ta cire tare da  marairaice murya  kamar zatayi kuka tace "to ai kaine kasani ihun".yaja tsaki yana furzar da iska mai zafi "zaki iya yin  komai dan ki kusanta kanki dani ya fada yana harararta ha?e da zareta a jikinsa dan kusancin da suka samu ya soma canza yanayinsa zuwa wanda baya so a tsakaninsu , mikewa tayi tana d'aga kafafuwanta da kyar, madadin ta kwanta sai ta fita a d'akin taje tayiwa mumy sai da safe bata jima ba ta dawo ta nufi gurin shimfid'anta ta kwanta taja bargo ta lullu'be rabin jikinta ta zuba masa narkakkun idanunta tana jin kamar ta fixgoshi jikinta su kwanta tare  ."
a natse  ya  maida idanunsa kan aikinsa yana yi yana hamma da zarar taga zai kallo inda take sai tayi saurin runtse idanunta , ta ?an bude idonta daya taga ya mike ya dauki plet din data shigo masa dashi ya ajiye akan table ya koma ya zauna yana aiki yana ci tun tana jiran taga tashinsa a aiki har bacci yayi nasarar d'aukarta , misalin karfe biyu  na dare ta farka taga yayi bacci ga system dinsa a bude ta mike tsam ta isa inda yake ta rufe masa system din tare da ajiyewa akan table ta  kamoshi ta kwantar dashi akan  kujerar sosai dan kar jikinsa yayi ciwo , tana kokarin zare hannunta ya farka idanunshi akanta "me kike ?o?arin yi ?
"Uhmmm ammmmm babu komai naga kayi bacci ne shine nayi tunanin "kika yi tunanin me "?yayi mata tambayar cikin tsananin ?acin rai "Wai ke dan Allah mai yasa baki da kai sai na daukar kaya bance kar hannunki ko wani sashi na jikinki ya gogi nawa ba "? Muryarta a sanyaye tace "Kayi hakuri inshallahu na daina "Kina da bala'i shishigi da takura wallahi ,ki daina 'bata lokacinki akan Aliyu , yana gama fadar haka ya soma ?o?arin  mike wa tsaye " dan Allah malama ki bani hanya na wuce ya karasa maganar yana harararta da sauri ta matsa ta bashi hanya tana kallon bayansa ."
Cike da jarumta tace "ko bata lokacin nayi akanka ya Aliyu daidai ne bare ni nasan ba batawa kaina lokaci nake ba,dan na  kasance  tare da kai zanyi duk abinda ya dace ,kuma nasan yadda nake mutuwar sonka kaima kana mutuwar sona kawai kana takura zuciyarka ne bisa wani dalili naka bancin haka da an ga haukan soyayya a gurinka ..........."
cak ya tsaya ya kasa cigaba da d'aga kafafunsa "ya Aliyu i love you  more than word's a hankali ya juyo da idanunshi dake cike da mayen bacci ya tsura mata yaji kamar ya ?auketa da mahaukacin mari tsabar takaicin abinda tace a natse yayi taku biyu ya tsaya a gabanta har lokacin kwayan idanunshi na kanta , gabanta ne ya shiga dokawa da sauri da sauri saboda tsoro da fargaban abinda zai aikata mata "kinsan wani abu ? tayi saurin girgiza masa kai zuciyarta na wani irin tsalle "wallahi wannan abun kunya kike aikatawa kanki kar ma ki bari wani kunnen yaji wannan kalmar a bakinki "babu komai barni na cigaba da aikata abun kunya nifa a halin yanzu bana fahimtar komai sai yadda nake sonka ".wani dogon tsaki yaja tare da juyawa ya hau saman gado ya kwanta kusa da yaransa ya janyo bargon data lullubesu dashi ya rufe rabin jikinsa ta zauna akan kujerar daya tashi ta zuba tagumi tana cigaba da kallonsa ,ta rasa yadda zatayi da rayuwarta ,bata san me Aliyu yake son tayi masa ba duk abinda tayi bata burgeshi ,komai tayi masa  daga hantara sai zagi da harara "ya Allah ka duba halin da nake ciki kasa mijina ya fahimceni "zaman me kike ki tashi kije kiyi alwala ki kaiwa Allah kukanki mana wankakkiyar zuciyarta ta sanar daita zumbur ta mike ta shiga bayi ta d'auro alwala tazo tayi raka goma da wutiri byn  ta sallame ta zauna tana addu'a akan Allah ya karkato mata da hankalin mijinta Ta dade zaune tana kaiwa Allah kukanta sannan ta mike ta nad'e sallaya dan lokacin sallar asuba da saura madadin ta koma ta kwanta a kasa sai ta koma dayan bangaren da yaran ke kwance ta kwanta suka sa yaran a tsakiya ita da Aliyu ,ta kashe wutar dakin ta kunna mara haske ta kai hannuta tana shafa kan areef dake kusa daita a hankali bacci yayi awon gaba daita ...."

Kiran  sallahr karshe  ne ya tada ita ta bude idanunta a hankali  tana mika ha?e da sallati ta kunna wutar dakin ta tsura masa ido yana kwance sai faman sauke numfashi yake , yayinda hannunsa daya ke rungume da yaransa matsowa tayi ta kai hannunta ta shafa gefen fuskarshi tana lumshe ido fuskarta dauke da murmushin jin dadi ,duk da yana kinta amman baya kin ya'yan data haifa masa wannan kadai ma wani alfarma ce daga Allah, a kullum bazata daina godiya ga Allah da aunty Zainab ba bancin ita data hanata cire cikinsu a wancan lokaci daya yanzu matsaloli sun mamaye rayuwarta ,saukowa tayi ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito ta gabatar da sallah ,a natse take yin komai dan karsu aryan farka su tashi babansu  .."
Karfe bakwai  saura ta shiga Kitchen dan hada musu  break fast, tana kitchen  tana aiki ta jiyo motsin saukowarsu suna wasa da  magana da juna daman kuma haka suke suna son wasa akan step ko akan karfen step su hau suna lilo a hankali ta liko tace "maza ku koma dakin mumy  ku kwanta , gabad'ayasu  suka tsaya suna kallonta suna  mata dariya "bazaku koma ba tayi maganar tana kokarin fitowa suka kwasa a guje suna dariya "areef ga momy na zuwa zo mu gudu." tayi saurin  dafe qirjinta "kubi a hankali dan Allah karku fadi ,ta biyosu sama ta shiga dakin mumy taga basa ciki dan haka ta nufi dakinsu  ta iske su kwance a bayan Aliyu suna faman kyalkyale dariya."
tayi saurin kama bakinta tare da daukar areef ta sauko dashi aryan na ganin haka ya makalkale Aliyu yana dariya "zo nan aryan ku kwanta anan karku tashi papa daga bacci yayi aiki jiya ya gaji sosai yana bukatar bacci juyi duniya tayi da dabaru dan su koma bacci amman suka ki dole ta koma  dasu  kasa ta cigaba da hada breakfast  sun so su makale mata a kitchen taki yarda tace su tsaya a parloun dan suna da mugun wasa sosai ,a parlou'n ma tana aiki tana lekosu .."
Basu dade da barin dakin ba Aliyu ya tashi dan duk abinda suke yana jinsu , sallah yayi ya koma karfe tara  daidai ta kammala da komai ta shirya dining table ta kamo hannun yaranta suka nufi dakin momy anan tayi musu wanka ta shiryasu cikin wasu had'ad'd'un kaya sabbin riga light green da wando blue black "aryan ya kalleta yana murmushi yace momy I love this clothes are you the one  brought it for us or grandma "?
"No it's grandma brought it say thanks to her ya washe baki  yana kallon mumy dake zaune tana bare tafarnuwa yace "thanks you grandma kisna ta karasa shiryarsa yazo ya tsuguna a gaban mumy yana surutu irin nasu na yara tare da ?o?arin ?aukar tafarnuwa,mumy tayi saurin rike  masa hannu tana cewa "uhmmm aryan ,kisna ta kamo areef yayinda aryan ya haye saman gado ya rungume mumy ta bayanta " I love you so much grandma tayi murmushin jin dadi "love more my boy tana tsananin qaunarsu akan sauran jikokinta ,amman tasan hakan bai rasa nasaba da kasancewarsu ya'yan Aliyu da kisna ba .."
Aryan ya mike ya tsaya a tsakiyar katifa ya kalli areef yana murmushi yace "mommy kayan sunfi min kyau akan areef ko ? aiko take areef ya sa kuka , kisna ta rungumoshi rabu dashi world best kaima sun maka kyau sosai kamar dan kai akayisu  sai da ta gama dasu sannan ta nufi d'akinta , koda ta shiga Aliyu baya dakin jin motsin saukar ruwa yasa ta fahimci wanka yake dan haka ta soma gyara dakin ta feshe ko'ina da turare yana fitowa ta fada bathorrom tayi wanka ta fito ta tsaya gaban madubi tana goge jikinta da karamin  towel ita cinyarta yayinda rabin dukiyar Fulaninta suka bayyana , wani irin duba yayi mata sama da kasa sannan ya ?auke idanunshi akanta ya soma  daura agogo a tsintsiyar hannunsa.
Muryarsa a tsarke yace "karki sake fitowa daga ke sai towel idan ina guri".wani kalar juyowa tayi tana masa wani irin kallo mai cike da takaici da mamaki wanda ka?an ya rage towel din jikinta ya subuce tayi saurin kamoshi gam ta rike , iya towel ma yayi complain ina ga jikinta ya bayyana ai sai dai taji saukan duka ko mari da fada mata bakaken maganganu".
"hope kinji abinda nace bana son ganinki d'aure da towel idan ina guri bana son karuwanci dan kin wani tsareni da ido kina kallona kamar mayya idan kuma bazaki yi abinda nace bane na sani ".saurin girgiza masa kai tayi tare da cewa "zanyi ."
ya sa kai ya fita zuwa dakin mommy ita kuma ta gaugauta goge jikinta ta sanya kaya ta fito ta shiga dakin mommy ta zauna kusa dashi akan kujera ,areef na zaune akan ciyarsa yayinda aryan ke tsaye a bayansa yana ?o?arin hawa wuyansa mommy ta Kallesu sun burgeta sosai ,sun dace da junansu , bata ta?a ganin halittar da suka dace da juna ba kamar Aliyu da kisna ko dan kamar da suke da juna ne batasani ba ,a ranta ta dinga masu addu'ar akan Allah ya zaunar dasu lafiya ,kisna ta dubeta "mommy abinci fa yayi ready "to kisna sannu da ?o?ari Allah yayiwa rayuwa albarka amman gaskiya kinyi sauri kammalawa , haka ake so bari na fito.
"Ki bari a kawo miki nan mana ba sai kin sha wahalar saukowa ba saboda kafafunki inji cewar Aliyu, "haka ne amman dai muje kasan gabad'aya zai fi ya dauki areef ya sabashi a kafad'ansa aryan na rike a hannunsa suka fito . "
Mommy  ce  ta  soma yin gaba sannan suka biyota a baya kisna  na kokarin jerawa dashi ya dakatar daita muryarsa can kasa ta yadda mommy bazataji ba "karki sake ki jera dani bana bukata  ".aryan najin abinda yace yayi saurin  saki hannunsa ya rike na kisna muryarta a sanyaye tace "Okya babu matsala idan da hali ka kira su ya Samir a waya suzo suyi break fast banza yayi mata kamar bai ji abinda tace ba ,Suna saukowa  parloun Samir da aunty zee suka shigo aunty zee ta karasa gaban mommy ta durkusa har kasa cike da girmamawa "mommy Ina kwana kin tashi lafiya"?
Mumy tayi murmushi tace "Lafiya lau zainab ya kika tashi ya gajiya? "alhamdulillahi mommy ta fada tana mike wa tsaye tare da mikawa kisna hannu "ya'akayi autar momy kinyi kyau fa sosai "na gode aunty zee Ina kwana suka gaisa cike da kulawa, Aliyu ya mikawa Samir hannu suka gaisa ya dauki aryan ya daga shi sama "wooooowwww my dad you look  so beautiful ,aryan ya wangale masa baki yana kyalkyale dariya dan yana son yaji an ce masa yayi kyau ,zama sukayi akan dinning kisna tayi saving dinsu tare ajiyewa kowanensu plet a gabansa da ruwan tea Mai kauri sannan ta zubawa Aliyu nashi ta zagayo inda yake ta ajiye masa ,
ta zauna a kusa dashi ji yayi kamar ya tashi  ya canza gurin zama amman babu dama gashi  yana jin idanun mumy ajikinsa   , spoon ya dauka ya dinga feeding din yaransa batare daya ci abincin ba  sai daga karshe ya    curbi tea  kadan ..."
Bayan sun gana break suka dawo kan kujera nan hira ta barke mommy tace kisna  ta d'auko babba jakar dake ?ar?ashin step wanda suka zo dashi tsaraban kisna ne acikin makil  ,kisna ta mike ta janyo jakar ta bude had'ad'd'un kaya ta gani atamfofi da lace duk a dinke kusan kala goma ta soma d'agawa daya bayan daya tana murmushin jin dadi duk wannan kayan nawa ne mumy ? "Naki ne ke kadai mamana ".
kisna ta daga wani lace guda biyu wanda akalla kudinsu zai kai dubu dari dari tace" kai mommy wannan lace din sun min kyau sosai wallahi duk sunfi shiga raina murmushi mumy tayi "tana tuna yadda aka yi ta samu kayan Alhaji realwan ne ya siyo mata a wata tafiyar  da yayi zuwa kasar  hollond " ya kika ga kayan nan uwar marayu da yake haka yake kiranta dashi ? "gaskiya sunyi kyau sosai dady ,"shiyasa na siyo miki dan nasan zasu miki kyau ,ta sake kallon kaya sosai "gaskiya sunyi kyau amman zasu fi yiwa kisna kyau akaina kuma zata so kalarsa gaskiya ita ma zanbawasu sun shiga cikin tsarabanta "what na siyo miki abu kice wata kisna wacece haka "? yayi maganar yana bata rai ."Mutun ce  ita zanbawa kuma bana son ka sake cewa komai ni ka siyowa ni kuma na bawa diyata shikenan " shiru yayi bai sake cewa komai ba har ta bar dakin.."
"Momy na gode sosai me dady ya bayar ki kawo min "bai bayar da komai ba ya ce idan zan dawo ki fa?a min abinda kike bukata idan na koma na fa?a masa  zai aiko miki ta  fadi haka dan ta kwantar mata da hankali amman a zahiri cewa yayi bai da abinda zai bada a kawo mata dan har yanzu bai gama yarda daita ba .
"okay mumy zanyi tunani ta kwashe kayan ta kai su d'akinta ta jera cikin wardrobe ta dawo suka ci-gaba da hira har rana tayi suka shiga Kitchen tare da aunty zee ,"me zamu dafa ne kisna "?
Kisna ta rausayar da kwayar idanunta sannan tace    "mu  dafa predrice da coslow saboda ya Aliyu zai so . ..."
"Lallai kisna kina shagwa'ba muradi dayawa fa shiyasa gashi nan yayi bulbu ke kuma duk kin zuke sam na lura mumy bata ji dadin ganinki  haka ba "ajiyar zuciya kisna ta sauke da karfi  tace " wallahi  kamar kinsani dan  har sai  da tayi  magana  amman na fada mata babu komai "Allah yasa babu din to ko ciki  gareki ne ?Kisna tayi murmushi har dumple d'inta na lobawa tace "kai aunty zee ciki fa ..."?
"Kai aunty ko gaskiya tunda nasan muradi shapshuter ne  nan da nan yayi ajiya a mararki  dariya suka kwashe dashi gbdy sannan suka fara aikinsu suna tsaka da aiki Samir ya shigo kitchen hannunsa rike da farar leda aunty zee ta kalleshi tace "me muka samu ne ranka ya dade ? Cikin jin dadi ya gyara tsayuwarsa yana cewa "Kayan dadin da gimbiyar muradi ta kawowa  mumy ne shine na dauko leda daya na kawo muku "Gabadaya kisna ta maida hankalinta da natsuwarta  kan Samir qirjinta na wani irin dokawa da matsanancin karfin gaske " wace irin mata ce wannan  wato  sai data sake dawowa gidan nan  ? Bata gama tunani ba ta sake jin muryar ya Samir "yarinyar nan fa tana mutuwar son Aliyu kinga yadda take wa mumy kamar zata yi  mata sujjada dan ladabi abun ya burgeni sosai shiyasa nace mata idan akwai ta aure a gidansu ta gaugauta sanar min ya karasa maganar yana nuna aunty zee da baki alamun tsokanar , take aunty zee  ta sakar masa hararan wasa ya shigo  cikin kitchen din sosai ya ajiye laidar hannunsa  ya tsaya a bayan aunty zee Kamar zai shige jikinta "gimbiya Ki amince min mana na sake shiga daga ciki kamar yadda dan'uwana zai yi ?
shiru dukkaninsu sukayi kafin daga bisani tace "ai zuciyarka bazata iya son Abu biyu ba bare soyayya , shi kansa d'anuwan naka zuciyarsa mace daya take so ya dai ki yarda da hakan ne amman nasan da sannu zai fahimci haka idan lokaci yayi.."
numfashi Samir ya sauke ya ?an saci kallon kisna dake aikinta ganin kamar bata damu da maganar ba  yace "muje ku gaisa da ita ko ?  ya fada yana barin kitchen din ,aunty zee ta kalli  kisna "muje ko " 
" gaskiya bazani ko'ina ba kije kawai duk yadda kisna   taso kin zuwa amman  aunty zee tace  dole sai sun suje , a durkushe suka isketa a gaban mumy kanta a kasa tana rike da hannu aryan tana kokarin kamo hannun areef yaki yarda daita daman kuma shi muguwar kiyuwa garesa baya yarda da kowa sai yan gidansu ...
Nawal na ganinsu ta sake fad'ad'a fuskarta da murmushi ta maida hankalinta sosai a kan aunty zee tace "aunty zee sannuku da zuwa kun zo lafiya ya kuka baro mutanen gida ?
"Alhamdulillah aunty zee ta amsa mata atakaice ,nawal ta ?an saci kallon kisna wacce gabad'aya yanayinta ya sauya sam bazaka ce ta ta?a dariya ba ,yanayin fuskarta yasa gaban nawal ya dinga faduwa amman ta sanyawa jikinta jarumta tace maman twins ina wuni ?
Sai da kisna ta gama shan kamshinta dan har nawal da Aliyu sun fidda rai zata amsa suka ji sautin zazzakar muryarta "lafiya " atakaice .
shiru dukkaninsu sukayi ,daga kisna har nawal babu wacce numfashinta bai fita da matsanancin sauri ,wani irin kishin Aliyu ne ya mamaye zuciyar kisna ,duk da a yanzu tafi kowa maraba da shigowar nawal gidanta a matsayin kishiya ta huta da wasu daga cikin iskanci Aliyu amman wani lokaci sai taji kamar ta kashe nawal din akan tsananin kishin mijinta dan Allah ne ka?ai yasan irin ciwo da rad'ad'in da take ji a zuciyarta a duk sanda ta tuna da aurensu , sai dai tana kokarin danne kishinta saboda bata son zubarwa Kanta da mutunci a idanun nawal din da Kuma idanun duniya dan ta lura da tsoronta dake tattare da zuciyar nawal din kuma tasan hakan bai rasa nasaba da kashedin data mata a wancan ranar ba  , ita kuwa nawal gbdy jinta tayi duk a takure a gurin , mikewa tayi cikin sanyi jiki tayiwa mumy sallama ta wuce zuciyarta cike da matsanancin tsoron kisna , Aliyu ya so  bita sai dai kunyar mumy yasa ya kasa Binta suka ci-gaba da hira da mumy da zumar anjima zashi gurinta ,yayinda kisna da aunty zee suka koma kitchen ..
"Kinji wani sabon salo kiran sallah da husir wai aunty zee a bakin guzuma abun ma babu dadin ji aunty zee ta karashe maganar tana kwashewa da dariya "ai naga yadda kika shaka dan gaisuwar ma da kyar kika amsa kisna ta fada tana dariyar mugunta  "ba dole na bata rai ba mata ta girmeni nesa ba kusa ba amman ta bige da ce min  wani aunty kinji kuwa yadda raina ya ?aci  ,dan wallahi ko shi ya  Aliyu a girme zata iya girmansa idan kuwa bata girmesa ba zasuyi daidai daita amman tsabar iyayi wai aunty zee  ta fadi tana jan tsaki "ke kuwa meye abun jin haushi bayan gindin zama take nema sgurinki  "
"Ai kuwa idan dai agurina zata samu bazata taba samu ba sai dai gaisuwar fatan baki ,kisna tace "to ai shima aunty data kiraki dashi ba wani abu bane fa normal ne yanzu da wanda ka girma da wanda ya girmeka duk zaku iya kiran junanku da aunty Kawai dai ke baki son girma ne shiyasa kikaji haushi  ",gaskiya bana son gara ma idan nasan na girmeka ina iya hakurin wannan amnan ita datayi kanwa ta biyu ko uku dani ta wani  ce min aunty ..." Dariya suka yi  suka ci-gaba hirarsu suna aiki batare da sun bi ta kan laidar da Samir ya kawo musu ba  .."
******"
Tunda su mommy suka zo wasu abubuwa suka ragu kasancewar basa zama a gidan kullum sai sun fita yawo har da kukan murna kisna tayi saboda tun zuwanta kasar sau daya ta fita zuwa kasuwa sai gashi yanzu kullum sai sun fita , sai dai duk daren duniya sai Aliyu  yasan yadda yayi  ya bata mata rai har ya kai ta ga yin kuka , satinsu mommy uku a kasar  suka fara shirin komawa Nigeria ita da yara ban da  aunty zee  zata zauna tare da mijinta duk abinda ya dace mommy tayi tsaraba dashi Aliyu ya siya mata  Ana jibi jirginsu zai daga tace  zata shiga  kasuwa ta duba ta gani ko akwai abinda zata bukata dan haka washegari ta shirya da misalin karfe biyu na rana direban Aliyu ya bar gidan ita."
Aliyu da samir da nasir na zaune a haraban gidan akan fararen kujeru suna tautaunawa akan business da buga wasa dan wani sati zasu wuce spain domin buga wasa yayinda safiyya da aunty zee da kisna suke dakin mommy zaune akan gado suna kimtsa mata kayanta aryan da areef suna wasa a kasan tayis da kayan wasa, can aryan ya fita daga dakin ya tsaya abakin kofa kasancewar safiyya data shigo dakin bata rufe ba, mikowa areef hannu yayi alamun suje parlou'n kasa babu mutsu areef ya mika masa hannu suka fice daga dakin da kayan wasansu .
Suna saka da hira kisna taji gabanta yayi wan irin mumnunar faduwa sakamakon tunowa datayi ta daura ruwan zafi kafin ta hawo sama qara ta saki tare da durowa daga saman gadon ta sauko da sauri "lafiya kisna  "?Safiyya ta tambayeta cikin tsananin tashin hankali "wallahi ruwan zafi na daura tun dazu na manta sai yanzu na tuna tayi maganar tana karasa  barin dakin da sauri ,tana taka step taji qara areef da gudu ta karasa saukowa jikinta na wani irin rawa kamar mazari  ,ganinsa jikin hot plet jikinsa na rawa yasa ta saki qara ta fito da gudu dan ta kashe wutan gidan gbdy sai dai rudewar datayi yasa ta kasa hada kujera  , ta dawo zata rungumeshi ajikinta adaidai lokacin da safiyya da aunty zee suka shigo kitchen sakamakon ihunta da suka jiyo safiyya tayi sauri riketa  cikin tashin hankali tana furta " inna  lillahi wa inna ilaihi raji'un  Samir da nasir ne suka shigo atare ban da Aliyu dake amsa wayar wani abokin harkallarsa hankalin samir a matukar tashe ya kai hannu ya kashe meter gidan gbdy yana kashe meter arif ya zube kasa a sume kisna ta fixge jikinta  ta karasa rungumeshi tana kuka da kiran ta shiga uku.."
samir  ya dawo  kitchen din da hanzari ya amshe  areef a hannuta yana tambayarta yadda abun ya kasance ta biyosa tana yi masa bayani tana kuka  ,Gaba-daya Samir

Please Login or Register in order to submit comment