Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

  Muryarta   a  dake tace "bawan  Allah  kayi hakuri ni  din  matar aure ce  fa" wani irin kallon raunin wayo   yayi  mata sannan ya   gyara  tsayuwarsa tare  da zube hannuwansa  duka cikin aljihun wandonsa yana wata   irin   dariya har ya neman  d'aga  murya , cike  da  matsanancin tsoro  ta matsa baya da sauri  ha?e da rike hannun  d'anta  gam  dan ba karamin tsoro ya bata ba , a zahiri ake iya  hango  tsananin tashin hankalinta  waige waige ta soma yi  tana neman  hanyar  guduwa ciki  zolaya  yace "dakata ! dakata!!  mana Karki  gudu  dan  duk inda  kika shiga a kasar nan wallahi   sai na zakuloki  matsawar  kina cikin garin  nan  na mallakawa zuciyata ke  ".Yayi maganar hankalinsa kwance yana nuna ta da ?an yatsansa yayinda idanunshi ke tsaye kyam akanta yana mata wani irin kallo  yana cigaba da dariyar da yake dan shi karya ya dauki maganarta ...
"a matukar tsoroce ta dubeshi   kamar  zatayi kuka tace   "dan  Allah malam ka daina  kallona haka  wallahil azim  ni matar aure ce har ma da yara biyu ..." ta karasa maganar idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye .
Cak  dariyar dake kwance akan fuskarshi ta 'bace  zuwa mummunar ?acin rai  sannan  yayi  shiru yana kare mata  kallo sama da kasa  zuciyarsa na wani irin tsalle da bugawa ,  sam bazakace  matar aure bace  komai na jikinta  irin na yammata ne  hatta shigar jikinta  yammata dayawa  suna yi irinta  yayi maganar acikin  ranshi "oh my goodness  ya furta a fili  yana  dafe goshinsa  ,"amman ko waye wannan mutumin  daya aureki  ya cuceni ya cuci rayuwata  ya gama dani  kalar  matar dana dade ina  nema na  aura wayyo Allah  naga samu naga rashi  tawa ta sameni  a fili  yayi maganar yana Kallonta da narkakkun idanunshi , hankalin kisna ya sake tashi  ita   ba maganarsa tafi daga mata hankali  ba  zuwan ahlinta tafi jin tsoro   dube  dube ta soma  tana addur  kar Allah ya kawo Aliyu ko  ya samir  guri, numfashi  ta sauke saboda  babu    alamunsu  hatta su anty zee bata ga kyallinsu a gurin  ba dan haka  ta  sanyawa jikinta natsuwa tare da gyara tsayuwar ta   ,bangaren Aliyu kuwa gabad'aya  ya manta da wata halitta kisna suka zo  tsabgar  gabansa kawai  yake yana gwadawa  areef takalma  , duk wanda ya daukar masa sai ya d'aukarwa aryan .."
Mutumin  ya lumshe idanunshi  yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa akan jin abinda ta fa?a masa yanzu ,cikin murya mai cike da kasala ya cigaba da  fadin "gaskiya  gaskiya wanda ya aureki ya kassara min  rayuwa ,  ina ji ajikina koma waye ya aureki  baya sonki sai dai kasancewar mata nada   raunin  zuciya zaki iya son shi dan baku  san  mutanen da suka dace da rayuwarku ba ..."bata san sanda  dariyar maganarsa ta subuce mata ba  tayi  murumushi   tana   toshe bakinta  da hannuta,  aryan ya d'ago kanshi  ya kalleta ya sake maida idanunsa akan mutumin  dake tsaye ,"kin san wani abu"?ya tambayeta yana tsareta da idanunsa ,taki cewa komai saboda  qirjinta dake  bugawa da sauri "idan ace ni na aureki bazan Iya barin ki fita  ko'ina batare dani ba, irin kulawa da soyayyar da zan baki sai kin ce na rage  yayi yawa zan  lalla'ba....." saurin  katseshi tayi ta hanyar fadin "dan Allah ka wuce tare da mijina muke fa idan ya gamu  komai zai iya faru  ".ya zaro ido waje cike da mamaki "shine ya barki haka gaskiya hasashena ya tabbatar  gaskiya, wallahi baya sonki "hasashenka bai tabbata  gaskiya ba ni dai dan Allah ka rufa min asiri ka bar bibiyata hakan zai iya haifar min  da babban  matsala da mijina wanda bazan so faruwar haka ba ".

    "shikenan ya zanyi da rayuwata   zanyi  duk yadda kuke so sannan zanyi   addu'ar Allah  ya kawo  tsautsayin da mijinki  zai  sakar min ke  na aureki cikin kankanin lokaci dan bana son a dauki lokaci batare dana mallake ki ba  yayi maganar tare da mika mata badir din kudin kasar  "ga wannan ki sha ice cream ke da boy  taki  amsa tace  " bana  bukatar  haka daga gareka   , sannan ba Ameen ba  akan addur da kayi yanzu  saboda ina tsananin  son mijina duk runtsi bazan so rabuwa dashi ba  .."
Tabe  baki yayi kawai yana Kallonta sannan ya mika wa aryan hannu alamun yazo gareshi aryan   yayi saurin  makale kafad'a   ,"har yanzu  jikina yana  bani baki da aure sai dai  musamman  zan sa a binciko min komai naki   ina tabbatar miki nan da wani lokaci  zan san komai akanki   ya kamo hannun aryan da dabara ya daga shi sama yana masa wasa "ya sunanka boy "? Aryan daya jishi a sama yana yawo  daman abinda yake so kenan ya wangale  masa baki yana cewa  "aryan     ..." "Wooooowwww   nice name "  aryan   kace  auntynka ta fad'a min gaskiya  kada ta wahalar da zuciyata  idan kuma bazata  amince min ba ta bari mu zama friend's daita ..... "."wayyo Allah na shiga uku  shikenan kasani a matsala  ta furta a matukar  tsorace sakamakon  idanunta  daya  ha?u  dana Aliyu dake tsaye   "dan Allah ka rufa  min asiri  ka sauke min  yaro kuma  ka  bar gurin nan yanzu  tayi maganar kamar zatayi kuka a hankali mutumin ya sauke aryan domin ganin wanda ta kira da sunan mijinta ...."
A  natse  idanunshi ya sauka akan  Aliyu  daya soma takowa   da kyawawan zara zaran  yatsun kafafunsa masu matukar kyau cike da jarumta  irin na karfaffan namiji mai tattare  da  natsuwa da haiba    zuwa inda suke   tsaye ,yayinda kisna dake tsaye  qirjinta ya cigaba da bugawa da matsanancin karfin gaske  hankalinta yayi mugun  tashi   take gumi ya shiga tsatsafo mata a goshinta da sansar  jikinta   ,ta tsura  masa narkakkun idanunta  da suke a  matukar tsorace  domin son tabbatar  da yanayinsa ,
Irin na d'azu zai yi musu   ya sharesu  ya basar kamar bai ga komai ba ko kuwa zai yi magana ne a matsayinsa na mijinta "?yana daf da k'arasowa inda suke wayarsa ta soma ringing kafin  ya d'auka  kiran ya  katse a hankali  ya ciro wayar daga gaban aljihunsa ya duba ganin mai kiran ya soma neman layin yana cigaba da daga kafafunsa yana ciza gefen  lip's dinsa yayinda hannunsa daga ke cikin aljihun wandonsa dan tunanin maganar da zai fadawa mr birsat dake bukatar zantawa dashi ta musamman a gobe    .."
  Ta daura laulausan tafin  hannunta akan goshinta ta goge gumin dake tsatsafo  mata  zuciyarta na rawa  yayinda har wannan lokacin tana cigaba  da kallonsa  jikinta  na  wani irin  rawa , tana kallonsa ya soma wayar bata ji yace komai ba  illa "to shikenan naji  zamu yi magana  later cikin tsadaddan turancinsa   ya cire hannusa cikin aljihunsa ya   riko hannu areef  dake tsartsarfa yana  biye  dashi  ,bakinta na rawa ta dinga furta kalmar " ka  wuce ! Ka wuce dan Allah !! Allah ya gani bata so Aliyu ya ganta ba  saboda gudun tozarcinsa da wulakancinsa  dan tasan duk abinda zai yi dan  tozartata yana so saboda baya kaunar ganinta cikin farinciki  sai dai  babu yadda zatayi yanzu aikin gama ya gama sai ta jira taga sakamakonta , mutumin  ya  kallesa  ya ganesa sarai realwan Aliyu  muradi ne  da suka ha?u  d'azu  nan take ya shiga  wasi wasi acikin ranshi  anya kuwa gaskiya ta fa?a masa?  tunda ganin idanunshi suka yi    karo dashi babu  wanda  yayiwa  d'an'uwansa magana ko nuna alamun  sun san juna  idan kuwa har mijinta ne ta yaya zasu ha?u da juna batare da sun nuna alamun su din ma'aurata bane ?  "ganin  Aliyu yana ?o?arin nufo inda  suke yasa jikinta ya sake ?aukar kyarma gumi ya sake wanke mata jiki wani irin tashin hankali ne ke sake kawowa gangar jikinta ziyara a hankali  ta cigaba da  maimaitawa  mutumin kalmar  "ka rufa min asiri ka  tafi  dan girman  Allah, amman ko gezai  yaki  tafiya ya tsaya kyam kamar mashi yana jiran karasowarsa yaga mai zai yi ," dan tabbas idan  matar aurensa ce  dole ne ya dauki mataki  ......"
Sunkuyar da kanta kasa tayi   tana kallonsa ta  kasan idanunta ,  yana takowa qirjinta  na  luguden bugawa da matsanancin karfin gaske, saurin fixge hannu aryan tayi ta rike gam  a hannunta  ganin yana cigaba da karasowa "momy look at papa ......sororo mutumin yayi kar dai gaskiya ta fa?a masa ita din matar aure ce ,matar ma ta  Aliyu muradi  ,gaskiya ta cancanci ta kasance matarsa sun dace matuka, tana da kyau sosai kamar yadda shima yake da tsananin  kyau na bugawa a jarida daman irinsu sai irin wadan nan matan masu tsananin kyau kamar su sukayi kansu ..."
yana gama k'arasowa ya fixge hannu aryan  a hannunta ta  d'ago idanunta a gigice  ta kalleshi ,hanunusa ya mika baya tunaninta  marin mutumin  zai yi  dan  haka tayi saurin durkushewa kafin ya gama dashi ya dawo kanta ga mamakinta sai gani  tayi ya riko hannu samir ya zagaye kanta  dashi tare da mika masa hannu aryan suka juya suka soma ?o?arin barin gurin ,wani wahalallen numfashi ta sauke ta mike tsaye a firgice "da alamun kina matukar son wannan dan wasan kallon ba dai mijin aurenki ba ? " ki duba kiga yadda ya nuna ko in kula  akanki babu mutumin da zai ga matarsa ta sunah tsaye da wani reaction d'insa bai  canza ba kina son maso  wani wannan da shafukan sadarwarsa hotonsa dana wata buduwar ne wanda ake rade raden zai aureta me yasa zaki 'batawa kanki lokaci akan mutumin da bai sonki kuma  bai damu dake ba ki bawa yusif modibo  dama ya zamo abokin rayuwarki zan kula dake da duk abinda na mallaka a duniya  zan baki   .. .."
  "Enough  dan  Allah ka  dameni da surutunka na  banza shasha kawai sai wani  zuba kake kamar fanfo  babu class babu aji babu mannes ," kasani koda ni din ba matar aure bace bazan taba kula ka ba saboda baka daga cikin tsarina tana gama fadar haka taja tsaki ta barshi tsaye ...."
Bayanta yabi da kallo a ransa yace duk abinda zakiyi sai dai kiyi amman bazan hakura ba sai na mallakawa zuciyata ke "..
Jiki a sanyaye ta k'arasa inda suke wanda zuwa lokacin numfashi ma da kyar take fitarwa  "lafiya me ne ne  ka wani  fixge  hannu yarona  a hannuna    ai  ba kai kadai ka haifeshi ba   tayi maganar cike  da dakiyar zuciya  Aliyu ya  bu?e  baki zai fara magana cikin sanyayiyyar murya  Samir ya dakatar dashi dan haka ya juya a fusace ya tsaya nesa ka?an dasu "wato daman kina da wata manufa   a cikin ranki  shiyasa kika ce  a fito  dan ki samu damar kula maza ko "? tsayawa tayi kawai tana masa wani irin  kallon ,ya  kalleta kamar zai ?auketa da mari saboda kallon raunin hankalin da  tayi masa "wuce muje gida  "kayi hakuri dan Allah yanzu fa muka fito inji cewar aunty zee  "lafiya kisna mai ya faru yayanki ya dauki zafi haka  "?"Babu komai tayi magana muryarta can kasa hawaye na zubo mata ita ba fadan da yayi mata ne yafi damunta ba kamar yadda Aliyu ya wulakanta aurensa dake kanta "tabbas yanzu ta sake fahimtar Aliyu bazai sota ba  "me ye  babu komai ki fa?a mata wani kato kika kula da aurenki  saboda bakinsa darajar kanki  ba yana fa?a yana  kara d'aure fuska nan take kisna ta sake  tsoronta motar da suka zo daita ya nuna mata duk abinda Samir yake fa?a mata yana shiga kunnen Aliyu   amman ko ajikinsa bai nuna ya damu ba dan shi ko yawo zatayi   tsirara  tayi ba  zai damu ba bare kula wani kato  ..."
A hankali su aunty zee suka karaso gurinsa tun daga  nesa take kallon Aliyu so take ta fahimci   reaction d'insa akan kisna amman taga babu alamar haka hasalima wasa da yaransa yake ya daga ariyan sama  ya daga areef"Hannu areef ya rike aryan na saman fad'ansa  ya nufi inda ya paka mota ya  shiga ya sanya aryan a gabansa  ,su aunty zeey suka shiga mota ya ja , gabad'aya hankalin kisan  yana kan Aliyu dake zaune yana tuki  "ya Allah ka taimakeni ka nuna min hanyar da zan shawo hankalin mijina gareni ...
  Gudu yake sosai akan titi duk maganar da Samir yake masa yana bashi hakuri akan abinda kisna  tayi bai ce uffan ba haka zalika bai waigo inda  yake zaune ba yana karaasowa  get din gidan ya danna hon da karfi mai gadi ya taso da sauri  ya bude masa get ya sanya hancin motarsa cikin haraban gidan madadin ya karasa inda aka tanada domin ajiye motoci sai  ya tsaya a tsakiyar  gidan ya fito ya nufi  kofar parlou'n gidan Samir   ma ya fito da sauri ya biyo bayansa Aliyu  na kokarin  hawa  step samir ya shigo yana masa magana "ina son na kasance ni ka?ai  i will see you later samir ,  samir   ya gyada kai ya  zauna akan doguwar  kujerar  parlou'n  yana furzar da iska mommy dake zaune tace "wani abu ya faru ne da kuka fita "?
Girgiza mata kai yayi  "babu komai momy ya fada mata haka dan kwantar mata da hankali  "karka  min karya fa samir  ? babu komai mommy idan akwai ai zan  fa?a miki "Allah yasa ta fada hk  tana jiran shigowar jikokinta a guje suka shigo suna kiran sunanta "granny  ta ware musu hannuwanta  "oyayo sannuku  da dawowa  me kuka kawo min my dear"?  "Ni yunwa nake ji inji cewar aryan  yayi magana yana yatsuna fuska tare da shafa ciki Samir ya kalleshi "babana ban da karya fa duk cire ciye da kuka yi amman kace yunwa kake ? Turo masa karamin bakinsa yayi yana sake kwabe fuska mumy tayi murmushi Tace "karku damu   yarana  I have oredy cook delicious  for you ta fada tare rungumesu ajikinta "really granny ?  "sure my grandchildren's babu abinda ban muku ba  "yeeeeeeee suka soma  tsalle  suna sake rungumeta  a daidai lokacin da kisna da aunty zee suka shigo hannunsu rike da kaya "iyeeee kunga yan gatan granny  areef ya mike ya amshi farar ledar da Aliyu ya siyo musu takalma ya dawo gurin mommy "granny  I want to show  you  something ya bude ledar takalma suka zubo   masu yawa  "papa ne ya siya mana nida aryan "iye lallai papa na ji daku ,aryan ya cire takalmin  dake sanye da ?afarsa  ya matso ya dauki guda daya acikin wanda aka siyo   "ki samin granny  ina son nasa sabon takalmi  " ka bari zuwa gobe kaji my sweet heart  ya kwasa takalman da gudu  ya hau sama shima areef ya kwashi wasu ya bishi a baya  "sannu da gida mommy aunty zee da kisna suka hada baki ."
"sannuku kun sha yawo "wallahi ai kasar akwai tsari gasu da dogayen riguna da kananan kaya  ai ina ganin sai na sake komawa tayi maganar tana nuna samir da baki ya juyo ya kalleta  "aikuwa sai dai ki nemi mai kai ki dan duk kwananki nan zamuyi busy "haka zaka daure ka kaita "Allah mommy kina shagwa'ba yaran nan  da yawa  ya fadi haka tare da mikewa ya fita domin gabatar da sallah ,  Kisna ta mike" bari nayi sallah nima  nazo na daura mana girki "huta abunki  mamana na  dafa muku had'ad'd'en girki kala dabam dabam "thats why I love you mommy ta kai mata pick a kumatu ita kuma mumy ta shafa kanta .."
Sama ta hau zuciyarta cunkushe  da bakincikin nuna ko in kulan da Aliyu ya nuna mata  lokacin daya gatan da wani kato wannan abu ya bala'i taba mata zuciya tana kan step ya sauko sanye cikin wasu kayan  kunnensa manne da waya yana  magana kasa kasa  ",okay ka fito da  marcende kawai   yana ganinta yayi saurin  ?auke  kanshi , idanunta ta lumshe tare da sake bashi hanya qirjinta na bugawa cikin natsuwa ya raba ta gefenta yana  sake janye jikinsa dan kar jikinsu ya ha?u kamshin turarensa dake tashi ne ya cika mata hanci da zuciya hakan yasa ta ?an ji sanyi acikin ranta har taji kashi dari na ?acin ran daya haddasa mata kashi goma ya kau  a cikin zuciyata , ta gefen idanunta take kallonsa har ya gotata  sannan  ta cigaba da tafiya , kofar fita ya nufa muryarsa a ?ausashe yace  " mommy  zan ?an  fita amman ba jima zanyi  ba zan dawo "
  "Muradi  ......"Mommy ta kira sunansa  ya juyo tare da tsurawa momy idanunsa da suke a rikici sun yi jawur tamkar garwashin wuta bama  zaka ta?a  cewa farare bane sannan cike suke da matsanancin maseefa ya kasa amsawa mumy illa tsura mata ido   "amman naji kacewa Samir  zaka huta  ina kuma zaka yanzu da alamun ma akwai abinda ke damunka , murmushin gefe baki yayi mata wanda yafi kuka ciwo yana girgiza mata kai alamun babu komai, bata fuska tayi "karkawa mommynka karya mana zaka iya k'arasowa ka fa?a min damuwarka koni na taso na sameka"?murmushi ya sake yi yasan komai zai yi mommy Sai taso  tasan abinda ke damunsa ko abinda zai fitar dashi a daidai wannan lokacin yasan  yadda mommy take matukar sonshi bata ha?a shi da komai ba a rayuwarta , uwa ce data amsa sunanta shi kuma  yana tsananin sonta zai iya mallaka mata  komai daya mallaka  a duniya koda kuwa rayuwarsa ce  koda kuwa  ba  itace sila inganta rayuwarsa ba  ,bashi da wata uwa kaf duniya  data wuce ta, itace  uwarsa itace ubansa itace komai nasa  k'arasowa yayi ya zauna kusa daita  ya kamo hannuwanta duka  cikin nashi  aunty zee na ganin haka  ta mike  tsaye "uhmmm bari na bawa uwa da d'a guri  ta nufi sama mommy tayi murmushi "gara ki tashi kam .
bakinsa ya kai daidai kunnen mommy yayi mata magana a hankali , murmushi ne ya sake  bayyana akan fuskarta ta ja kunnensa ya ?an saki qara mara sauti yana kai hannunsa kan na mommy "ashhh mommy  akwai zafi fa  "kabi a hankali muradi  bana son kana damun kanka dayawa  Allah ya tsare min kai  sai ka dawo amman karka dade sannan karka  yi abinda zai ....."  Hannunsa ya d'aura a saman bakinta "mommy babu abinda zai faru kin rigada kin min addu'a ya mike ya fito zuwa haraban gidan yana waya "okay na gane unguwar ,no karka damu zani  ni ka?ai ya katse kiran ya karasa inda direbansa  ke jiransa har ya bude masa murfin  gidan  baya amman yaga ya bude gaban mota ya shiga direban ya  karaso da hanzari ya bude mazaunin direba ya shiga ya tada motar mai gadi ya wangale musu get din gida...
Jingina bayansa yayi da kujerar motar da yake zaune , zuciyarsa na wani irin zafi da tuttukin bakincikin mara misaltuwa ,shi kadai yasan yadda yake jin kanshi da zuciyarsa da yake jin  kamar zata kama da wuta, runtse sexy eye's d'insa  yayi yana dukan cinyarsa da hannunsa daya "ina muka nufa ne boos"? direba ya tambayesa yana dubansa  *"madinaty*  ya bashi amsa a takaice ...."
Zaune a bakin gado aunty zee ta iske kisna  ta rafka  tagumi  yayinda aryan da areef ke guje guje a dakin  ta karaso  ta zauna a gefenta tana dafa kafad'anta "me yayi zafi kisna komai yayi zafi  fa maganinsa   addu'a ".
  Naunauyen ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe idanunta "zuciyata aunty zee ina jin ajikina  bazan dade a duniya ba na  kusan mutuwa dan Allah ko bayan raina ga ....
  "dan damuwar datayi miki yawa ne yasa kika fadi haka bai zama lallai damuwar tayi sanadin barinki  duniya ba ,idan Allah ya ga dama kina cikin damuwa zai rayaki na tsawon shekaru abinda zakiyi shine addu'a Karki gaji da kaiwa Allah kukanki "ina addu'a sosai aunty har na fara ga..."  "Karki gaji  ,ba'a gajiya da  addu'a kisna  , Allah na amsa addu'armu sai dai ana jinkirtawa bawa ne amman kisawa ranki duk abinda kika roki Allah ya amsa wai ma meye abun damuwa yanzu "?
  "Damuwata da bakincikina aunty zeey Bai wuce yadda ya  Aliyu ya nunawa mutumin nan ni din bawata  tsiya bace agurinsa alhalin na sheida masa ni din matarsa ce wallahi dana san wannan wulakanci zai min dana ce masa ni din ba matar aure ba kai dana ma  bishi mun wuce gidansa ..........
  Aunty zee ta kwashe da dariya har da rike ciki "ai kuwa da kin haukata  ya  Aliyu kinsa wani abu ?Kisna ta girgiza mata kai "sai kin fada min " wallahil azim  yaji mugun  haushin  ganinku  tare da wannan mutumin Samir ma yaji haushi bare shi mai mata "karki  fa?a min haka  aunty zee dan ba yarda zanyi ba " kinsan Allah ko ki yarda ko Karki yarda Aliyu yaji haushi ya dai ki nunawa ne dan karki ?auka ya damu dake   "yaushe ne zai damu dani aunty wallahi na gaji dashi zama dashi ya fita raina banki ya sakeni ba   ......"?  Tayi maganar hawaye na gangaro mata "karki fidda sautin kukanki kinga yara suna gurin nan shiru sukayi gabad'aya yayinda kisna ke kokarin maida kukanta  "nasan yadda kike jin wannan situation din da kike ciki sai dai bani da abinda zan fa?a miki daya wuce ki zauna da mijinki  lafiya ki ci-gaba da ?o?arin janyo hankalinsa shiyasa ma na siyo miki kananan kaya domin ki dinga sakawa kina daga masa hankali" .
"Wannan mai zuciyar dutsen ai ina fada miki ko tsirara zanyi yawo a gabansa  bazai taba nuna ya ji wani abu ba bare wasu  kaya , na dai sawa jikina naji dadi  "karki  gaji   kisa tun bai damuwa  zai zo ya fara nuna sha'awarsa tunda shi ba dutse ba "kai aunty  bazan iya ba fa   Kuma bazan cigaba da  miki alkwari ba at any time  zan iya barin rayuwarsa dan wallahi na gaji dana mutu nayiwa yayana hasara wallahi gara na bar rayuwarsa ,na dawo rayuwarsa ne dan na gyara kuskurena amman yaki bani dama  sai faman wwulakantani yake , me ye amfani dawowata ?
" da amfani sosai bazaki gane ba sai nan gaba abinda nake so da Ke   ki kara  hakuri ki bar maganar rabuwa wai bana ce miki ma'aikun rahma na tsinewa matar dake neman saki daga mijinta ba kema fa kinsa furta hakan haramun ne shiru Kisna tayi kirjinta na buga ita fa ta kudurcewa ranta zata sanarwa  mumy  tana bukatar rabuwa dashi gara ta rungume rayuwar ?a?anta   " bari naje na bar yayanki shi kadai gashi banyi sallah ba Kisna ta sauke ajiyar zuciya  "Okya shikenan nima bari nayi sallah na sauko an bar mommy ita kadai ..."
Sai wurin karfe goma  da minti  goma shabiyar Aliyu  ya shigo gidan  yana  haki kamar wani zaki ,suna  zaune gabadayansu  akan  dinnig table suna cin  abinci   kallo ?aya yayi  musu ya dauke  kanshi  ya haye step momy na ganin yadda ya shigo ta biyo  bayansa  da sauri  kallon kallo suka bi juna dashi batare da sunce wa juna  komai ba kisna kuwa  kasa cigaba da cin abinci tayi  duk taji komai ya fita akanta  kawai ta cigaba da bawa areef zuciyarta na tsinkewa saboda hukunci  zuciyarta  yayinda  aunty zee ke bawa  aryan abinci , kasa zama kisna tayi ta biyo byn mumuy  domin son aiwatar da kudirin ta .."
A tsakiyar dakin mommy   ta iskeshi yana ?o?arin cire rigar jikinsa  jin motsin shigowa dakin yasa ya juyo yana zare rigarsa ya saura daga shi sai farar vest da dogon wando a hankali ya shiga fifita da rigarsa  yana furzar  da iska mai zafi daga bakinsa  yayinda hannunsa daya ke rike da kugunsa sai zufa yake yi ,jijiyon kanshi duk sun mika sun yi rudu rudu   tamkar wanda ya shiga  fagen  yaki   " bana ce kabi komai a hankali ba me yasa zaka ........."shigowar kisna ya katsewa mumy   hanzari ,kisna  ta karasa  shigowa  jikinta a sanyaye idanunta na kanshi a kallon da take masa ta fahimci yana cikin  tsananin damuwa "to me kuma  ya sameshi"? tayi  Maganar akasan ranta tana takowa  inda jug din ruwa yake ta tsiyaya a glass cup ta karaso inda yake yana fidda numfashi ta mika masa kin amsa yayi sai da mommy tasa baki sannan ya amsa sai dai ya kasa  kai cup din bakinsa yana jin tamkar ya saki  cup  din kasa   ,babu  zato babu  tsammani  suka ga ya  matse   glass  cup din a hannunsa take cup din ya  soma tarwatsewa ruwa da fasassasun glss suka yi kasa kisna da momy suka tsura masa ido hankalinsu a tashe cikin tsananin tashin hankali mumy ta rike hannunsa tana furta  "menene haka

Please Login or Register in order to submit comment