Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rayuwata dashi ba�� saboda darajan� ya'yana, bazan� iya kallon idanun uban ya'yana nace banason shi bana bukatarsa arayuwata� ko bana bukatar had'uwa dashi a lahira ba kamar yadda ya fada min� � ".
A� matukar fusace yace "kinji ba kinji� abinda wannan wawiyar take� cewa ko zainab� wato ma� darajan ?a?anta takewa komai ?� "ai daman� nasan abinda ke zuciyarki kenan shi yasa nake son rabaki da su gaba-daya na canza musu wa.........."tayi saurin katse masa hanzari ta hanyar cewa " duk abinda zaka fa?a ya� Aliyu� ka fada amman bazaka� taba canzani agurinsu arayan ba� saboda nice nan na dauki cikinsu na tsawon�� wata tara da kwanaki kuma� nayi na kudarsu� ...." Ni yanzu�� Abinda zaka min�� tunda baka bukatar zamana� da kai� ka taimaka ka wankeni� agurin mahaifina�� tunda nayi iyakar ?o?arina naga mun sasantar kanmu muyi�� zaman lafiya da juna�� amman kaki ," ba dai baka son zama� da kisna ba� ? yayi shiru tare da jan tsaki� "to� ka taimakawa rayuwata� ka� wankeni� agurin iyayena kafin ka sawakemin aurenka dake kaina��wallahil azim ina bukatar takardar saki daga gareka ,ka sake ni ka huta rayuwarka nima na huta� " .
tunda ta fara magana ya dauke kanshi akanta sai dai� jin maganarta ta karshe�� yasa Ya� d'agowa idanunshi� a hankali yayi mata wani� � kallon banza sannan� ya� ?auke kanshi ya cigaba da kallon areef zuciyarsa na masa wani irin tuttukin bakincikin, sosai aunty zee ta tausayawa halin da kisna� take ciki gashi dai a shirye take data sadaukar masa da rayuwarta amman ya kasa fahimtar kisnar� da data yanzu akwai bambamci� "ya Aliyu karka biyewa zuciyarka kayi hakuri dan Allah,� karka biyewa maganar kisna tana cikin ?acin rai ne , karkayiwa rayuwar aurenku nakasu� alhalin kuna bukatar juna ,ka tsaya ka duba rayuwar ?a?ansu uwar wani da ?an wani sai Allah babu wanda zai iya kula dasu Aryan kamar kisna, ka barta a gindin ?a?anta da ita kadai suka saba� sannan ina kake tunanin zata� idan ka saketa tunda kasan abinda dady yace mata kayi hakuri dan Allah� ta tarkashe maganar kamar zata yi kuka ...."
d'akin ya dauki shiru na wani� lokaci� sannan sautin muryar kisna ya karade dakin " aunty zee ki daina bashi hakuri dan girman Allah �� ki bar shi yayi� duk abinda zuciyarsa� ta yanke masa� akaina� ko dady da mommy sun ki amsata amatsayinsu na iyayena� zan bi duniya ,zan kwashe� yarana mubi duniya� tare dan bazan bar ko daya ba� ya sake d'agowa�� a� matukar fusace yana kallonta da jajayen idanunshi da suka canza kala� "da wasu yaran zaki bi duniya� ?� Yayi maganar kamar zai cinye ta "idan zaki bi duniya ki bi duniya� ke kadai kar ma ki tsaya� a iya duniyar� mutane� ki zarce zuwa wata� duniyar� daban i dont fucking� care� amman� ban da ya'ya na ...." ya karasa maganar a zuciye yana baro inda yake ya iso gabanta ya tsaya suna fuskantar juna� "idan� kin shirya� yawon duniya ki tafi ke kadai karki sake ambato� ya'yana a ciki� okay idan ba haka ba zan kasheki da kai kaina ya karashe maganar yana nuna mata yadda zai yi daita� ".
��a hassale tace� "lokacin dana yi d'awainiyya da cikinsu kana ina "?� ta kai hannuta� qirjinshi tana nuna shi� jijiyon wuyanta� na mikewa� sabida tsananin� tashin hankali da jin dacin maganarsa " kana ina� nace ? " kana� ina na� ?auki tsawon kwanaki �� ina nakudarsu� sannan na haifeshi kana ina "? "kasan yadda ake daukar� ciki ko kasan yadda ake nakuda bare ka fa?a min magana�� akan ya'yana � ka bani amsa� tambayarka nake�?� ta dinga zuba masa� magana tana nuna qirjinsa tare da� turesa tamkar mahaukaciya sabuwar kamu shi kuma� yana ja baya ganin kamar ta soma fita haiyacinta� yasa a� zuciye� ya damki kafad'unta ya ha?eta da bango� dakin "shut up kisna !!!! I said shut up or� else I will get you lost on second are you insane ? ya cigaba da� magana cikin zafin rai� "ko kina hauka ne kike ture ni� " ?"Ko� kin� soma shaye shaye ne� ko kuma� tsohon haukan� rashin mutuncinki ne ya motsa "? " alright ai nasan bazaki taba� canzawa ba dan idan kayi shekara dari baka ha?u da mutun ba duk ranar daka ha?u dashi karka tambayi halinsa dan halinsa na nan� bai canza ba , da wannan halin� kike tunani zaki� mallaki zuciyar Aliyu� never in history? " Aliyu yafi karfinki yayi miki nisa da.....
"Papa Me yasa kake sa mommy� Kuka� ?� Suka jiyo sautin Muryar aryan yana kuka har da shesheka " kullum kana sa mommy� kuka bana sonka tunda kana sa mommy kuka� daga yau kai ba papa dina� bane, babu ni� babu kai ".ya riko hannun aryan da niyyar rungumeshi� yaron ya� fixge� hannunsa ya karasa� jikin kisna� yana goge mata hawaye "stop crying� mommy ,I will� tell Grandma to punish him wasu hawaye suka zobo mata ya sake goge mata ta karasa ta dauki areef� ta saba shi a kafad'anta ta rike� hannun aryan suka bar d'akin ."
� "kaga abinda kake kokarin haddasawa� ko ?" wannan karamin�� yaron�� da bai san� meye damuwa ba amman yau � saboda ganin uwarsa cikin damu...........
"ya damu ko kuma ana son gurbata min tunanin yaro ya dauka ni din mugu ne "dan girman Allah kayi hakuri ya Aliyu komai ya wuce karka sake tada maganar� nan plz numfashi ya sauke jikinsa yayi� matukar yin sanyi saboda ganin yadda aryan ya nuna reaction dinsa akan kisna �� ya juya� ya fita zuwa haraban gidan kanshi kamar zai kama da wuta nasir ya dake zaune ya kalli samir "tashi mu bishi mu shawo kanshi , Samir� ya masa banza ganin haka yasa� nasir ya� mike ya� fita,Aliyu� yana tsaye hannunsa daya dafe da goshinsa� dayan hannunsa� yana cikin aljihunsa nasir� ya karaso�� ya rike hannunsa ya nufi lambun gidan� dashi� batare da yace masa uffan ba shima ya bishi a baya har suka shiga ya zaunar dashi ya koma�� ya dauko ruwa mai dan sanyi� ya ?alle murfi ya mika masa "ka sha kaji sanyi a hankali� ya amsa ya� kafa bakinsa a bakin goran bai sauke ba sai daya shanye tasssss� .
Yana� ajiye goron nasir� ya fara magana cikin fushi� ta inda yake shiga bata nan yake fita ba "karka ?auka ko na shigarwa kisna ne a'a ina fada maka gaskiya ne� a matsayina na d'anuwanka� kuma abokinka saboda� bai dace ba ko wata kayiwa haka� ba kisna ba zan tsaya tsayin� daka naga na fa?a maka gaskiya shima Samir sam bai ji dadin abinda kayi ba�� ya� dai� kasa saka� bakinsa ne�� bisa wani dalili nashi� ,ko� baka duba darajan kowa ba ka duba Samir mutumin da rayuwarsa ne kawai bazai iya baka ba ,mutumin da kai da kanka ka sha fada min yadda kuka yi rayuwa tare haba muradi ai ko mutuwa tana jin kunyar� idon iyaye ,ya'yan nan fa ?a?anta ne bazata so abinda zai cutar dasu ba sannan duk sonka dasu bazaka Kai ta ba, nasir ya dade yana masa magana� jikin Aliyu ya sake yin� sanyi sai lokacin ya fara tunanin yanayin da Samir ya shiga a lokacin da yake wa kisna tujara "kenan haushinsa Samir � yaji� ko me� .."? Yayiwa kansa� tmbayar yana duban nasir ?wa?walwarsa na sake shiga� caji� "Idan kuwa haushinsa Samir� yaji lallai jini ba karya ba "amman har an zo lokacin da samir zai yi fushi� atsakaninsa da kisna ?� � sun dade zaune�� a lambu� nasir na nusar da Aliyu� gaskiya� bai dai kula sa ba haka bai ce masa ya hakura ba illa iskan da yake furzarwa .."
Misalin ?arfe biyar� mommy ta shigo parloun� aunty zee ce da safiyya�suna� zaune " assalamu alaikum ta furta a hankali tana karasa shigowa gabad'aya suka maida hankalinsu gareta "wa'alaiki salam tare da mikewa suka amshi� laidodi dake� rike a hannunta ta zauna akan kujera "ya Allah ta� furta a hankali ina wa?an sojojin� suke ban ji motsinsu ba"?
Safiyya da aunty zee suka kalli juna sannan aunty zee tace "suna sama tare da mammansu bari na kawo miki ruwa ki sha sai naje na dauko miki su ta karasa maganar tana shiga Kitchen bayan kamar second biyar ta fito hannuta rike da jug da glass cup ta tsiyaya ruwa� ta mika mata ta ajiye sauran a saman table� sannan ta juya ta hau sama mommy ta kalli safiyya "ina nasir ko� suna� bangaren Samir ne ko suna� lambu� "?
"Eh suna lambu "ta bata amsa da haka� suna zaune aunty Zee ta dawo "mumy bacci suke daga su har mammansu ta fadi haka ne� dan kar mommy ta d'ago komai "bacci a daidai wannan lokacin ki koma ki tasota� ga waya nan na siyo mata�� ta bude ladar data shigo dashi ta mikawa aunty zee wayar� "gashi nan ki�� tasheta� ki bata� "kai mommy gaskiya ta gode� kisna zata dawo online� kenan ? "Gaskiya wayar tayi kyau sosai " dubu ?ari biyar�� kenan a kudinmu na nigeria zaro ido aunty zee tayi "haka waya yake da tsada anan ?"sosai kuwa ai wayoyi sunfi sauki a Nigeria nan dai� aunty zee ta dinga jan mumy da hira daga karshe nasir ya kira safiyya a waya tayi musu sallama ta wuce aunty zeey ta shiga Kitchen domin� daura abincin dare .."
Haka nan jikin mommy ya dinga bata akwai abinda ya faru a gidan da bata nan� dan har kusan takwas din dare bata ga yaran ba� haka bata ga kisna ba hankalinta yaki kwanciya gashi ita ta kalli abincin da� aunty zee ta kawo mata bata jin zata iya sanyawa cikin komai batare da ta daura idanunta akan jikokinta mafi soyuwa acikin ranta ba ,ta mike ta sanya silifas ta fito daga d'akin ta karasa bakin kofar dakinsu har zata tura sai tayi tunanin watakilla Aliyu yana ciki�� tayi knowking� tare da sallama ......"
Aliyu ne ya taso sanye da jallabiya� dan maroko� kalar dark blue jallabiyar tayi masa kyau sosai abunka ga fari sol �� ya bude kofar ganin mommy� tsaye� ya sha jinin jikinsa sai dai yayi kokarin sanyawa jikinsa jarunta cike da girmamawa yace "barka da dare� mommy , kina bukatar� wani abu ne "?Girgiza masa kai tayi kana tace "yaran nan� nazo dubawa tunda na dawo daga kasuwa ban sanya� idanuna akansu ba daga su har uwarsu shiru yayi dan shi kansa baya son mommy tasan abinda ya faru ,idan ya hanata ganinsu zata fahimci wani abu idan ya barta ta ga hannun areef hankalinta zai iya tashi fiyye dana yanzu� duk da bawani ciwo bane ,hannu dai yayi sanyi ne saboda shock din daya samu , matsawa yayi gefe ya bata hanya ta shigo d'akin akan gado ta hago su kwance lullu'be cikin bargo kisna na zaune a gefensu jingine da gado ta tafka tagumi� tana ganin mommy ta sauko tana wayancewa ",mommy kiyi hakuri kin jini shiru ko wallahi tunda kika fita kaina ke ciwo shine na kwanta har yanzu ma ban daina jin ciwon kan ba momy� ta zuba mata ido tana nazarinta sannan ta karasa gurin yaran ta shafa kansu� tayi kasa da hannuwanta zuwa kirjinsu taji numfashinsu na sauka yadda ya kamata�� ta rankwafo� ta sunbuci� goshinsu ta dawo ga kisna "kiyi kokari kiga likita kada ki tsaya gida shan magani a tare kisna da Aliyu suka d'ago suka kalli juna qirjinsu na mahaukacin� bugawa da wani�� sauri mommy kuwa tana gama magana tayi musu sai da safe ta fita Aliyu ya kulle kofar ya� hau saman katifa ya yi rigingine rungume da hannuwansa duka a qirji� yana tunanin maganar mumy da alamun ta dauka ko ciki ke ga kisna ..?
� � Har kusan dayan dare kisna bata runtsa ba tana kwance kusa da ya'yanta shima ba� runtsawa yayi ba tunani ne ya sha kanshi ta kai hannu ta janyo laidar da aunty zee ta shigo mata dashi d'azu tana dubawa wasu zafafan hawaye ne suka zo mata "uwa kenan "hakika duk wanda ya rasa uwa yayi kuka tasan� ta siya mata wayar ne� a matsayinta na yarta da kuma kwantar mata da hankali dan ta zauna da Aliyu gashi wanda ake wa dan shi yaki kwantar da kai su zauna lafiya ta mike dan saka wayar a caji�� motsin laidar ya tadda areef ya Mike zaune Aliyu yayi saurin kamoshi jikinsa� ya rungume shi� "zaka ci abinci ne?Yaron ya girgiza masa� kai yana cewa� ",papa tea "
da sauri ya sauko yana ?o?arin fita kisna� ta rigashi fita� dole ya dawo ya zauna rike dashi bata dade ba ta dawo hannunta rike da cup din tea ta amshesa a hannun Aliyu� ta soma bashi� can shima Aryan ya farka� ta dauko shi ta bashi sauran tea din da areef ya sha� ta kwantar dashi� ta shiga bayi dan bata jin zata iya runtsawa ta d'auro alwala ta fito wanda zuwa lokacin ya kwantar da areef a kusa da aryan sai dai idanunsu biyu yana lallabasu dan su koma bacci�� .."
Tana zaune byn ta idar da sallah ta fashe da kuka yaranta dake kwance suka sauko a gigice� suka karaso gareta suka rungumeta kuka take suma suna� � kuka�� kamar ana zarar ransu kuka yaran suke sosai saboda ganin halin da take ciki gashi dai� � basu da cikakken wayon da zasu ce ga dalilin kukanta sai dai suna jin zafin halin kunci da mahaifiyarsu take ciki a hankali ta rungumesu ajikinta tana ci-gaba da kuka "Allah kasa papa ya daina saka mommy kuka� kasa ya bata farinciki� , ki daina kuka kinji� mommy duk aryan yake magana shi areef ganin mamansa da d'an'uwansa na kuka ne� yasashi kuka "na gode d'ana� na daina kuka� kaji�babana� Allah yayi muku albarka na gode muku ,kuma na godewa� Allah daya azurtani da samu ya'ya irinku masu tausayi Allah� yayi muku albarka ta karasa maganar tana shafa kansu ....."
Mmn sudais

????????????
CUTAR DA KAI
????????
????????????
~TRUE LIFE STORY~
Free page 12
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ?aya ko sari yayi magana ta wannan number08059623096,
yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...????
Shiru yayi yana kallonsu suna kuka zuciyarsa cike da matsanancin takaici , haka kawai tana neman d'agawa yaransa hankali a karon banza da kukanta ,qirjinsa sai faman tafasa yake , babu abinda ya tsana a rayuwarsa kamar yaga uwa da ya'yanta suna kuka rungume da juna wannan abu na bala'in d'aga masa hankali .. "wannan wacce irin tarbiyya ce yayi maganar a zafafe zuciyarsa na kuna "? "kin wani rungume yara kina ?o?arin gur'bata musu tunanin da wannan dakikancin naki "kina son nuna musu zalintarki nake saboda su tsane kou me "? yayi maganar a tsawa ce gaba-daya yaran suka sake makalewa jikinta suna kyarma
"kiyi kokarin yin duk abinda zai sa su tsane a cikin zuciyarsu wallahi kece zaki kwana a ciki dan nan kusa zan samu wasu ya'yan da zasu maye min gurbinsu aikin banza kawai komai kuka kamar wata matar mamaci ,da yarda Allah sai Allah ya maida miki mugun nufinki akanki ni bazan ga kuka a rayuwata ba ". ya k'arasa maganar tare d'aura hannunsa ?aya akan sumar kansa dake kwance luf luf gwanin ban sha'awa kamar irin na areef da aryan ."
D'akin ya dauki shiru bata sake yunkurin yin kuka ba bare yaranta su tayata ,shima kuma bai sake cewa komai ba sai aikin jan tsakin da yake aika aika zuciyarsa na bugawa da karfi , a hankali ya runtse idanunshi da sukai jawur yana Allah wadai da irin halayyar wasu matan , ya furzar da iska sannan ya gyara kwanciyarsa cike da takaicinta yayi rigingine yana ?ara jin tsanarta a cikin zuciyarsa , ai muddin bai nika abinda tayi masa ba to bai kyautawa rayuwarsa ba, tamkar ya rako maza duniya ne , gara ya rama itama ta d'and'ani irin abinda yaji ."
Har goshin asuba kisna bata runtsa ba tana tsaye bisa kafafunta ta dukufa gurin kaiwa Allah kukanta , tasan abinda tayi masa yayi muni da yawa ,amman abinda yake mata a yanzu har duniya ta nad'e bazata ta?a mantawa ba, ta d'aga hannuwanta duka sama tana rokan Allah akan ya sanyaya zuciyarsa ,"Allah Kasanyawa Aliyu hakuri a cikin zuciyarsa , Allah kasan ina cikin tsananin damuwa akanshi , kasan yadda nake sonsa a halin yanzu karka bari zafin zuciyarsa ya rabamu alhalin ina tsananin son shi , Allah na tuba bazan sake aikata abinda nayi masa ba , Allah ka yafe min bisa kuskuren dana aikata ya Allah Aliyu bawanka ne kai kake da karfin ikon akansa ka gaugauta sanyaya zuciyarsa akaina ,Allah na rokeka da sunayenka tsarkaka ka sanyaya zuciyar aliyu yayi min afuwa Allah kasan ina son aliyu saboda kai ,Allah ka tausaya min saboda darajan fiyyayen halitta ,Allah kafi kowa sanin zuciyata nada rauni a kan bawanka Aliyu , Allah idan soyayyar da nake wa Aliyu alkhairi ne a rayuwata da addinina kasa Aliyu ya hakura ya dauki al'amarinmu da sauki idan babu alkhairi Allah ka cire min son ka raba tsakaninmu cikin sauki batare da tashin hankali ba sannan ka k'arawa mahaifiyata lafiya dan tayi namijin kokari akaina dan ganin rayuwarta ta inganta ba kowace uwa ce zatayi irin abinda mahaifiyata tayi min ba a ganiyar kuruciyata ta karashe addurta tare da ha?awa da yiwa yaranta akan Allah ya albarkaci rayuwar su sannan ta shafa addu'ar tare da shafawa akan yaranta da bacci yayi awon gaba dasu tuni ,bata tashi ba har sai data ji ana ?o?arin gabatar da sallar asuba sannan ta mike ta shiga bayi ta d'auro sabon alwala ta fito ta gabatar da sallah tayi azkar din safe sannan ta kwanta a kasa kusa da yaranta ta rungumesu ajikinta ..."

Washegari sai gurin karfe tara na safe ta tashi shima sautin zazzakar muryarsa ce ta dinga shiga kunnuwanta yana waya da coch dinsu , ta yunkura da kyar ta mike cikin sanyin jiki tana kallonsa suka hada ido shine yayi saurin janye kwayar idanunsa akanta yana yatsina fuska kamar yaga mugun abu , yaranta ta kamo ta soma yiwa wanka ta shiryasu cikin kananan kaya ta kai su dakin mumy sannan ta fa?a wanka ta jima acikin bayi tana sa?a jikinta da turarukan wanka masu kamshi sannan ta fito ta shirya cikin wata had'add'iyar doguwar riga wacce take da adon fulawa tun daga kasa har sama cikin kayan da mommy ta siyo mata ne jiya tayi tunanin ta saka ta gani kafin su bar kasar , ?aramin gyale tasa ta nad'e kanta dashi kafarta na sanye da takalmi kalar kayan tayi matukar kyau kwarai babu wanda zai ganta bai sake Kallonta ba, gashi daman jikinta akwai shi da daukar kaya ,babu kayan da zata saka basu amshi jikinta ba , ta shafa hoda kadai a fuskarta dan bata damu da yin fente fenten a fuskarta ba sannan ta feshe duk ilahirin jikinta da ruwan turare .."
Aliyu dake tsaye sanye da kananan kaya wanda daka Kallesu kaga kalar kudi bama sai an fa?a maka adadin kudin kayan ba zaka fahimci iya tsadarsu ,ga tsabar kyau da kwarjini sai kace shi yayi kanshi ga siffarsa kamar dan larabawa , Allah dai yayi a kasar Nigeria za'a haifosa kuma acikin jinsin *zarma* amman idan ba fa?a maka aka yi ba bazakace asalinsa dan nigeria bane ."
kallon kasa da sama yayi mata hakan yasa tayi saurin durkushewa kasa a gabansa dan tasan ma'anar kallon cikin rawar murya tace "ina..ina kwana"? yaja dogon tsaki yana kawar da fuskarshi a ranshi yace "mai zan yi da ina kwananki "? jiki a sanyaye ta mike tana ?o?arin barin d'akin ba dai ta gaishesa ba kar ya amsa ita dai tayi , dan gaisuwar na cikin dokokin daya kafa mata ko ta sha mahaukacin mari , tana daf da barin d'akin tana rausaya taji sautin muryarsa mai shegen dadi da tsuma zuciya wanda tsautsayi yasa ya fa?a kunnuwansa koda kuwa bakar magana zai fa?a sai mutun yaji tasirinsa ajikinsa "tunda nake a rayuwata ban ta?a ganin mace mai tsananin muni irin ki ba ......"
cak ta ja ta tsaya ta kasa cigaba da tafiya sannan ta kasa juyowa , sai dai take jikinta ya ?auki rawa kamar mazari ta dinga bin jikinta da kallo gabanta na faduwa "ban taba ganin mace mara kyan fasali irinki ba yanzu ke nan har wani kyau kika yi da kike wani tafiya kina rausaya kamar wata gurguwa ..... "?
wannan karon da hanzarinta ta juyo gaba-daya ta zuba masa narkakkun idanunta tana kallonsa, ido cikin ido suke kallon juna zuciyarta na rawa cike da tsananin mamaki jin furucinsa " ya rabbi mai kuma nayi masa da safiyar nan yake aibantani haka ? ta yiwa kanta tambayar har lokacin idanunta na cikin nashi , take idanunta suka kad'a suka yi ja tsabar ?acin rai da yake son haddasa mata . "me ke laifinna da sassafen nan da zai muzani haka wato dai Aliyu ba zai bar rayuwarta ta huta ba duk yadda zai yi ya dagula mata lissafi sai yayi daga wannan balain sai wannan
Allah ma yasa daga ita sai shi ne a dakin dan tasan ko agaban mutane haka zai mata dan ya kuntatawa rayuwarta ,bafa tsoronsa take ji ba kawai dai tana son gyara kuskurenta ne yasa take had'iye abubuwansa "
Ranta yayi bala'in 'bace akan abinda yayi mata yanzu a cikin ranta tace "lokaci ya kusa da zan taka maka burki akan abubuwan da yake mata ,a zahiri kuwa cewa tayi "wannan shine lokacin da zangargadeka matukar kana son zaman lafiya a gidan nan to ka fita hanyata kamar yadda kace na fita naka , idan ba haka ba zan rikeka a matsayin gawurtaccen makiyina da yake son kassara min rayuwa ,wai dole ne sai ka min magana ma tunda kace baka bukatar hakan a tsakaninmu " ai kace baka bukatar zama dani to ka sawwake min saboda nima yanzu ba bukatar zama nake da kai ba ka bani takardata dan Allah kaga aiki da cikawa ta k'arasa maganar tana sakar masa harara gabanta na faduwa dan karfin hali tayi kawai amman zuciyarta a matukar tsorace take da kalmar ya bata takardanta cikin sanyi jiki ta dinga daga kafafunta zuciyarta na zafi tana data sanin furta masa haka dan tasan halin zuciyarsa kadan da halinsa ya maka saki .."
Murmushin mugunta yayi dan abinda yafi bukatar gani kenan akan fuskarta damuwa da tashin hankali sannan ta bukaci rabuwa dashi da kanta kuma duk yayi nasarar haifar mata ,bai barta iya haka ba yace "ayi gaba dai zuciyata ta huta da tashi saboda ganin wannan mumnunar banzar fuskartaki mai mugun hali kawai ai nasan duk abinda kike fa?a akan kin canza karya ne dan ba zaki ta?a canzawa ba maganar zaki rikeni a matsayin gawurtaccen makiyinki ai nafi son haka , ke na ma fi makiyinki tasiri a rayuwarki idan baki manta ba ni dake makiyan juna ne baza mu ta?a sauyawa daga matakin da muke ba saki kuma tunda kin bukata sha kuruminki sa ido kiyi kallo kina zaune zai sameki saboda zama dake bashi da wani amfani dan bana sonki i really hate you ..........." abinda kunnuwanta suka jiyo mata kenan a lokacin da zata karasa ficewa daga d'akin kafafunta kawai take dagawa zuciyarta na zafi da rad'ad'i idan shi bai sonta ai ita tana son shi , dole ne sai ya furta baya sonta ko sai ya saketa ya barwa zuciyarsa mana har sanda zai aiwatar da niyyarsa akanta, Allah kaga bawanka Aliyu ko allah ka kawo min ?auki ,kasa min dauriya amsar duk abinda zai zo

Please Login or Register in order to submit comment