Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dana  turarenta   ita kanta  a tsaftace take   tayi  kyau sosai cikin  doguwar riga kamar  an  tsinkareta  ta motsa  ha?e da  bude idanunta   taga mutun tsaye a gabanta   wani  irin  mummunar faduwar gaba  taji  sai dai bata nuna masa   ba  tayi masa kallon  sama da kasa tace  "sannu   da zuwa ta dauke  kanta  akanshi  ya ajiye  jakar  hannusa yana  cigaba  da kallonta cike da takaicinta "wato  ma  dan  samun  dama taci ta koshi  ta hau  bacci   ganin yadda yake kallonta  kuma bata manta da yadda suka rabu dashi ba  ta mike tsam tana kokarin  bawa kafarta iska  sautin muryarsa  taji  "tunda  nake  ban taba ganin   wawiyar  yarinya irinki  ba....."
  da hanzari ta tsaya  tana dubansa da  idanuwanta   da suka kada  zai sake magana  ta katseshi ta hanyar daga masa hannu "enough muradi   ya kamata  zuwa yanzu  kana sanin irin maganar  da  zaka dinga fada min, karka   manta  nifa ba yarka  bace  matakar ce ita kuma mata  ba kowace magana zaa  dinga  fada mata ba, ka lura   ka  hankalta  kuma gane  kisna  tafi  ?arfin wannan  tozarci  dan haka  kayi  ka dawo taitayinka , idan ba haka nan kusa  zaka  tantance tsakanin  aya da tsakuwa taja  tsaki tana  sakar masa  harara tayi gaba  abinta  tana  rausaya abinda yafi tsana  kenan a rayuwarsa ayi masa tsaki a wuce shi  ji yake kamar ya mutu  ya  gwamaci shi yayi  da ayi masa ,  biyota yayi cikin zafin nama aiko   ta  kara sauri sai dai akan  step  ya  cafkota ya damki  naman cikinta  zuciyarta   ta  soma sarewa da lamarinsa daga  dawowarsa    abin nasa  yafi  karfinta    hawaye suka   gangaro  mata "wannan  wace irin tsana  ce haka" ?
Da  kyar  ta fixge jikinta tana  masa harararsa da yi masa  Allah  ya isa ta  shige  dakin  mumy  tun kafin ta saka key  ya banko dakin ya ?auketa da mari  "bayan tsaki har da Allah  ya isa ni  sa'anki  ne dukan tsiya mata ,sai da   yayi  mata   lilis  sannan  ya samu guri akan  kujera ya  kallonta tana kuka "muddin  zai fada ta fada bazai raga mata  ba  ya dinga gallazawa rayuwarta  kenan har sai ta shiga  hankalinta"  zaki  yiwa mutane shiru ko sai na an kawo min kyankyasai  ?tana jin haka tayi shiru ta daina zubar da hawaye sai shesheka "shima sheshekan  kuka  bana son jinsa dan kin cika min kunne kuma na sake jin kin kirani da muradi sai zubar miki da ha?ora  wawiya  kawai ". tashi tayi gbdy ta shige bayi , tunda   ya dawo  bata sake  bari sun  hadu dashi ba ,shima bai fiyye zama  a  gida  ba  kullum sai ya fita acikin  kwananki harkoki  sun masa yawa  training da office saboda zasu sake  fita    German   buga  wasa  yadda  ya  fita tsabgarta   haka itama ta  sharesa  babu  mai  shiga tsabgar wani  sai ya wuce ta wuce .."
*********
da  wani yammaci  da misalin  karfe   hudu   tana  zaune akan  doguwar kujerar hannunta  rike  da waya tana  magana da mommy   yayinda idanunta  ke lumshe ,kamshi turarensa  ne yasa ta bude  idanunta suka sauka  akan  shi  yana  saukowa  daga mattatakala  sanye da gajeren  wando  baki  da karamar   riga fara  irin ta yan  kwallon hannusa rike da  kwallo   yana bugawa   har ya sauko daga step  ya  fita zuwa wajen  idanunta na kanshi , sake  lumshe kyawawan idanunta tayi" Aliyu ba dai kyau  ba komai  kyau yake masa cigaba  da waya sukayi da  mommy daga karshe ta  hadata dasu areef ..
Shi  kuwa aliyu  kai tsaye  field din   gidan ya nufa  inda  Samir ke jiransa  shima sanye  cikin irin kayan  dake jikinsa tun kafin  ya karaso zee ta hura  husir tana karfafawa  mijinta gwiwa "karka  yarda ya cinyeka kamar  sauran lokuta  "Kima  daina bata bakinki yarinya  dan kamar na cinyesa  na gama idan dai  wannan mijin naki ne da bashi da momora sai aiki cin tsiya   Samir  yayi dariya yana tafa  hannu yace " sharesa   baby  duk ya gama  cika bakinsa daga karshe  Allah ya bani Sa'a akanshi ba".  Aliyu ya saki  kwallo aunty zee ta sake  hura husir suka fara  wasa da kwallo.."
Ganin  har kusan minti goma  suna fafatawa a tsakaninsu kuma har lokacin babu wanda yayi nasara  cinye d'an'uwansa, sai dariya take  ita kadai, idan taga Aliyu  zai  cinye mijinta da sauri zata sa ihu  kamar zatayi  kuka ha?e da daura hannuwanta saman  kanta ,idan kuma mijinta ke kokarin cinye Aliyu sai tayi ta bashi kwarin  gwiwa tana kiran "Samir !Samir !!Samir !!!
Haka  nan  tayi tunanin taje ta  fito da  kisna itama tayi kallo koda   aunty zee  ta shiga parloun   ta isketa  zaune ta tallafe  gwiwar hannuta  da filo data daura a saman cinyarta ta tallafe kumatunta da tafukan hannuwanta  tana tunanin  mijinta da auren da zai yi  "kisna stop  overthinking "me ke damunki  mai yasa  kike wannan dogon tunanin"? "Idan kika kashe kanki da tunanin ya  Aliyu babu ruwansa ya'yanki zakiyiwa hasara ".
Taja numfashi ta fesar tana sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ta  kalleta "tunanin auren ya  Aliyu nake aunty  bansan ya  komawar rayuwata zata koma ba idan nawal ta shigo gidan nan wallahi har na fara tausayin kaina saboda ba karamin so yake wa yarinyar ba "Mai  nawal ta fiki ilimi kyau ko nasaba ko kudi da zaki shiga damuwa akan shigowarta  "?"Ki bani amsar tambayoyina  numfashi ta sake  saukewa  ta tsurawa yar'uwata kuma matar yayanta uwa guda uba guda ido sannan ta girgiza mata kai "bata  fini  ko daya ba sai da munanan  kalamansa gareni  yana sani jin kamar tafi ni komai  tunda ita yana sonta "
"Ciwon rashin sonki shine babbar matsala da zai kawowa rayuwarki shamaki sai dai kisani kowa ne dan adam akwai ciwo acikin rayuwarsa kawo kunnenki kiji wani abu kisna ta mika mata  kunnenta murmushi ne ya subuce mata "babu abinda ban masa ba aunty  har takai ta kawo ma daidai towel baya son ganina dashi hatta kwanciya guri daya baya yi dani duk abinda nasan zanyi dan na janyosa gareni nayi amman  yaki ni gara kawai ayi ayi auren  na  cigaba da  zaman biyayyar da   naki yiwa iyayena a tun farko".
"Ai duk kece kika cutar da kanki  kisna "uhmmm ta sauke  numfashi karki tuna min abinda ya faru aunty  wallahi nasani shiyasa  wani lokacin idan yayi min wani abu konaji  haushinsa  sai na dawo  na huce "Kinga share tunaninsa da tunanin aurensa   taso muje  muyi  kallon kwallo ta  kamo hannunta suka fito  zuwa filin kwallo ."
Tun kafin  su karaso  kisna ta hango  Aliyu da Samir sun hada gumi da sauri  ta juya" ina kuma zaki ?  inji cewar aunty zee "ruwa zan dauko musu  ko cikakken minti biyar batayi ba ta dawo hannuta rike da roban ruwa guda biyu da kananan towel  ta mikawa aunty zee daya sannan suka  karaso gurin  a daidai lokacin da Samir ke kokarin cinye  Aliyu yayi saurin kwance kwallon da ?afarsa  Aunty zee ta dauki   husir ta hura tana murmushi  "to ku huta haka dan da alamun babu wanda yaci suka tsaya suna fidda  numfashi  rike da kugu, aunty  zeey ta karasa kusa da mijinta ta  shiga goge masa fuska zuwa wuyansa ..."
Hakan yasa  kisna  cikin sanyi jiki ta karasa kusa da Aliyu ta  kai hannu daidai kunnesa  zata goge masa fuskarsa dake tsiysyar gumi  ya juyo ya watsa mata idanunsa  masu matukar kyau  da haske take gabanta ya shiga dokawa duk ta daburce taji kamar ta saki towel din ta falla da gudu . hannu ya kai ya  amshi towel din hannunta idanunshi na kanta  ya soma   goge fuskarsa bayan ya gama ya mika mata , ita kuma ta mika masa roban  ruwa sa?anin aunty zee da a baki ta bawa ya Samir ya sha.
tun daya d'aura bakinsa akan goran ruwan  bai sauke ba sai daya sha rabi sannan ya mika mata sauran   suka ci-gaba da buga kwallo yayinda  su kuma suka samu guri suka  zauna a gefe akan fararen kujeru suna Kallonsu  a hankali kisna ta tsurawa mijinta ido tana kallon yadda yake sarrafa   kwallo  kamar  dan shi Allah ya haliccesa  duk wani  siffar karfi dake jikinsa ta gama  bayyana burinsa kawai  ya  cinye Samir cikin sauki , yadda surar  jikinsa take cike da karfi haka yake da mazakunta, karfi garesa kamar doki , sautin muryar aunty zee da ya  karade gurin  ya dawo da kisna  daga duniyar  tunani" Samir  isa goal ta rungumeshi ajikinta   tana murna "Allah  yayi yau Samir ya cinye  ya Aliyu ...."
Aliyu  dake tsaye rike da kugunsa da hannunwansa  duka yaja dogon   tsaki  yana kallon kisna  dake dafe da goshinta tana kallonsa  dan sam bata ji dadin cinyesa da Samir yayi ba shi da yake bugawa wasa  kasa da kasa  kuma ya cinye har yanzu da yake kan ganiyar buga kwallo babu kasar datayi nasarar cinyesa sai  wannan karon da Samir ya lashe   aunty  zee ta sake hura husir "baby ka  kara  masa daya dan Allah  "aliyu ya ha?e rai bazan  yi ba  ,a tunda kika  dad'd'ako min wannan   nasan bazan yi nasara  ba ya juya fuuuuuu a zuciye  ya soma  tafiya Kisna tayi saurin  d'agowa tare da dafe kirjinta idanunta suka cicciko da ruwan hawaye "ke dan Allah meye abun kuka "? "Ki barta hawayen ne suka mata yawa inji ya Samir  take ta maida kukanta tana sauke  numfashi  tare da   tsuke karamin bakinta tana shesheka  sannan ta mike  ,tare suka jero suka fito daga filin  kwallo suna fitowa haraban gidan ya fito sanye da riga pink da gajeren wando iya gwiwar ya nufi gurin motarsa escort d'insa na ganinsa suka taso yayi saurin daga musu hannu take suka kame ya danna mukulin mota ha?e da bude murfin ya shiga mai gadi ya bude masa ya fita a guje  ..
Ganin yadda ya  fige motar da gudun maseefa  Yasa kisna    fashewa  da wani  kukan mai cin  ranta  , hankalinta yayi matukar  tashi tsoro tattare  da fargaba ne sukayi nasarar   lullube  ilahirin jikinta, abubuwan da yake mata sun fara isarta amman ta rasa yadda za'tayi dashi ita meye laifinta ita tace samir  ya cinyesa ko me"?  takaicin haka yasa ta durkushe bisa gwiwowinta ta  kife kanta bisa cinyoyinta tana sake risgar kuka mai cin rai da  suma zuciyar ma'abocin sauraro  har aunty zee zata mata magana Samir ya dakatar daita  "ki tashi  ki shiga ciki kin dai san halin zuciyarsa ba karamin aikinsa bane ya dawo ya sameki agurin nan ya kara miki da duka , yana gama fadar haka  ya ja hannun aunty zee sukayi  bangarensu .."
A hankali ta mike ta shiga part d'inta tana goge hawaye  kai tsaye kitchen ta shiga   ranar ma bai ci abincinta ba haka  bai yarda ta kusanci  inda yake ba  dan har gargadi yayi ma tare da rantsuwa "wallahil azim idan na farka na jiki ajikina ko kusa dani  sai na miki  abinda har ki mutu bazaki manta  dani ba tasan shi tasan halinsa shiyasa tana kammala abubuwanta ta kama kanta ta kwanta akan kujera.."
********
Bayan wata uku
Duk  wani abinda za'a bukata na  kayan auren  nawal  Aliyu yayi ya sakarwa  aunty zee kudi masu yawa domin   hada  kayan lefe koda ta tambayeshi na kisna cewa yayi bazai mata  ba har zatace bazata ha?a masa ba sai taga rashin dacewar hakan , duk abinda ya kama  tun daga kan dogayen rigunan da takalma da jakakkuna turaruka anan egypt  ta siya ,ta tura kudin atamfofi  da  lesina da wasu abubuwan  daza'a bukata  negeria  tunda can za'a tura kayan lefen   dan amarya ma tuni tana Nigeria safy tazo ganin kayan lefe  tayi mamakin   bata  ga na kisna ba, ba  tayi kwaron  baki ba ta tambaya aunty zee "ina kayan kisna  na fadar kishiya  .. "?shiru sukahi mata gabadaya  dan rasa abinda zasu fa?a mata "tambayarku nake kun min shiru ina kayan kisna ko ita bazai mata  komai ba "?Kisna dake kwance tana  tunani ta  yunkura ta mike zaune  "bai min ba kuma ban damu ba saboda har yanzu ina da tarin kayan da ban yi amfani dashi ba "gaskiya wannan ba adalci bane ke kuma  ba hujja bane dan kina da kayan da zakiyi amfani dasu ,yau  ace Aliyu bashi da kudin da zai siya muku ku  biyu ne sai ki ?auki hakuri amman yana da ninkisu da ko mata dari zai aura a rana daya zai iya hada musu kayan lefe, gaskiya   aunty zee ban ji dadi ba  ya kuna kallon yadda  Aliyu ke wulakanta  kisna amman ku  kasa  ?aukar mataki akanshi  sai ma wani lalla'bashi kuke  sai ya kasheta kuce zakuyi kuka " idanun kisna ya cika da hawaye , aunty  zee ta sauke numfashi tana cewa "safy kenan bazaki fahimta ba, lallashinsa shine mafi alkhairi idan aka yi wani abu  na  ?acin rai idan  dady  ji zai iya janyo gagarumar matsala  wannan auren iyayenmu na murna dashi fiyye da kowani aure  babu yadda zamuyi duk yadda ya tsara  lamarin gidansa haka zata hakura  .."
"Hakuri hakuri hakuri kullum shi ke kashe mata ko saka su kamuwa da wata mummunar cuta safy ta fada cikin ?acin rai "karki manta hakuri shine jigon rayuwar duniya Allah yace kuyi hakuri lallai ni ina tare da masu hakuri ,hakurin shi karan kanshi aikin lada ne ba kuma  kowa  allah yake bawa baiwar hakuri ba inji cewar aunty zee.
"Haka ne Allah ya qara mana hakuri  sai dai na dade dasanin kisan na cikin damuwa dan Allah ko zaki iya fa?a min abinda tahi masa har yasa yayi mata irin wannan muguwar tsanar "?
Shiru parloun ya ?auka babu wanda ya sake furta komai ",ko kuwa ban kai matsayin da  zamu iya sanin sirrin juna bane "?Kisna ta kalli  aunty zee fuskarta dauke da damuwa safy ta kamo hannu kisna "dan Allah ki daukeni tamkar yaruwarki  ina son sani abinda kika wa aliyu da har ya rikeki a zuciyarsa ya kasa hakuri ya kasa manta komai "?"Shiru still tayi ta kasa  magana hawaye na kokarin zubo mata bata jin zata iya fadawa wani tahirinta da abinda yasa Aliyu yake mata wulakanci daya ga dama  ."

"Ni da zuciya  daya nake  zaune  da mutum kuma Allah ya sakamun jin damuwarki  a ciki raina , bana zama da mutum don in yaudareshi ko qin fada mishi damuwata, abu daya na dauka cewan mutunci ya hadaka da mutum tou kuyi zaman haka. Mutunci na kawo yarda da juna  wani zubin tana bada amana ma, kuma amana babban amincewa da mutum kesa aba mutum , kuma baya zama me kar6an amana alhalin bashi da kamala, dattaku, girmama na gaba, girmama na qasa, gaskia da haquri da halin mutane , Ina zaune dake tsakanin da Allah  ba wai dan mazajenmu na matsayin aminai  ba, amma wariyar da kike ta nunamun yau ya qureni wacce ni a wajenki? Shasha? Ko kuwa sakariya wanda zaki dinga 6ata lokaci daita ? Ko kuwa banza kike kallona? Ko mara illimi? Ko mara tunani? Ko mara sanin ya kamata? Ko kuwa yarinya qarama wacce  bata san komai ba? Ko wacce  bata san meye rayuwa ba? Duk abin da kike nunamin yana kunshe da wannan sannan rashin daukata yadda na daukeki yasa bazaki fadamun ba saboda kila bazan fada miki kiji ba ko bazan baki shawarar da ta dace ba ko kuma zan fallasa sirrinki ga wasu  saboda kina mun kallon wawiya wacce  bata san me take ba.
"A yau na yarda  zaman da muke  bashi da anfani kuma zaman da muke bana amana bane  in dai bazamu ji damuwar juna  ba ,mu bawa juna sharawa ba  zaman munafurci ne.
",Wallahi idan   na tambayeki damuwarki kika ki  fadamun   bakisan zafin da nakeji ba amma sai in barki sbd kar in daga miki hankali ko takura miki, babu komai sabon sanayya game da rayuwa dama nasan irinta ,kuma bazan daina aminta da aminta dake ba  , kuma  bazan daina jin zafin ciwon dake damunki ba a kan Aliyu  nagode  sosai da yadda kika nunamun matsayina da kuma yadda kike zaune dani na rashin yarda , na hakura da son jin komai dan ko kin bude bakinki   qarshe  bai wuce kice "bazan gane abinda ya hadaki da mijinki ba "  Nagode sosai wlh tunda ta soma magana kisna take kukan zuci dana zahiri safy ta mike tsaye ta dauki jakarta ta rataya zata wuce kisna tayi saurin riko hannunta cikin zafin nama tana kallon aunty zee hawaye na gangaro mata.."
"alamar tayi  magana  aunty zee tayi mata dan haka a hankali tace " kiyi hakuri ki  zauna safy ba wai naki fada miki labarina ba ne  dan ina tunanin wani abu  ko zaki fallasawa wani illa bana son  Tina abubuwan da suka faru dani sannan asalina ni mai zurfin ciki ce bana fadawa kowa damuwata idan ba mutun ne da kanshi ya fuskanci haka ba  safy ta zauna tana kallonta cike da tausayawa " safy abinda ya faru dani  ciwo ne dake cin zuciya ,ni kaina na kasa yafewa kaina abinda nayi  bare ya  Aliyu ,damuwa kuwa muddin Aliyu bai sauko daga dokin nakin  daya hau ba haka zan kare rayuwata cikin damuwa da garari  tunda nasan dan ra'ayin kanshi bazai sakeni ba sai dai idan iyayena ne suka bashi umarni "safy Kowane dan adam akwai  ciwon da Allah ke daura masa wani gurgu wani makaho wani kurma da sauran ciwuka da dama amman ni  Allah da ya tashi sai ya jarabeni da ciwon kaunar wani halittan mutun  a   sheakaru   goma sha  biyar data gabata a lokacin ina jss one ......."
Waiwaye.....
Mmn sudais
????????????
 CUTAR DA KAI
     ????????
????????????
Page 17
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ?aya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096.
"Aunty   zee ,  aliyu  sakina  wato  ni  iyayenmu  abu  daya  ne ,uncle garba  shine   mahaifin  aunty  zee , sai  uncle   yahaya   wanda  ake kira da  bature  shima yana  da   ya'yansa  ,sai  haroon   wanda   ya  kasance  mahaifin   Aliyu   sai  salaha   wacce  ta   kasance   mahaifiyata    , dukkaninsu   uwa ?aya uba  ?aya  suke   gabad'ayasu  hajiya  sakina  ce  ta  haifesu wacce  muke  kira da hajiya   kayi   sanadin aure  ne  ya kawota  garin lagos  da  zama  ita da mijinta   alhaji sani  sai  dai  asalinsu ita  da  mijinta   zarma  ne  wato  yaren  zabarmawa ,   haifaffun   kauyen   ilo  ne  dake ?ar?ashin    hukumar   bagudo  dake  jahar  Kebbi , sunan  kakata  ta  gurin  uwa nace  shiyasa  ake  kirana  da   kisna  dan  boye  sunan  ."
    Alhaji   Sani   dan canji ne  a   unguwar   yaba  dake  kusa  da ojuelegba a garin Lagos  ,yayi  rawar  ganin    gurin   bawa  yaransa   ilimi addinin dana  boko  sai  dai karatun  nasu  baya wuce iya   secondary  school yake  dakatar  dasu  ya sanyasu  cikin  irin  sanar da  yake  wato canji, yaransa  maza guda biyu  aikin   canji   suke  ban da  mahaifin   Aliyu  wanda  ya  sakawa ransa son  karya  da son  cin  rayuwar  duniya ,  baya  zuwa  aiki  kamar yadda sauran  yan'uwansa  ke ?o?arin  ganin sun gina kansu  ,  kullum  shikenan  kwanciya a d'aki  kusa da hajiya kayi ."
Duk  da  wannan kwanciyar  da  yake  baya  rasa   kudin  kashewa daga  hannu  yammatan  da  yake dasu   kala dabam  dabam   yoroba, Igbo  , hausa  har ma da yarensa  saboda    Allah yayisa  da tsananin  farinjinin    yammata saboda    shararraren kyawun   da  Allah yayi masa   na bugawa a jarida  da  ?aukar  hankali  kusan kyawunsa Aliyu  ya  d'auko  shi din  fari  ne   sol    shi da mahaifiyata   sa?anin  jinsin  zarma da mafi yawancinsu  bakake ne , suma  asalin   kyawunsu   sun  dauko   ne daga  mahaifiyarsu   dan   hajiya kayi   fara  ce  sol  ko digon  baki babu ajikinta haka  shima alhaji sani   fari  ne  sai dai  ba sol kamar  hajiya  kayi ba  ,bayan  kyau da Allah yayiwa haroon  har da tarin ilimin  boko  domin kuwa  ?wa?walwarsa naja  sosai   dan  har schoolaship  ya  samu  zuwa  uniLag   shi  da abokinsa  damilola  , sai  dai Alhaji sani ya hanashi  , hatta  mahaifin dami sai daya  saka  baki  yace   "idan rashin ku?i   ne  yasa  zai  dakatar da karatunsa  gwamnatin ce zata dauki nauyin  komai amman Alhaji sani  yaki  yarda yace "shi iya secondary School  kawai yake  da bukatan  yaransa  suyi  tunda  sun iya karatu da rubutu shikenan , haka mahaifin dami  ya hakura ya tura d'ansa ."
Hajiya   kayi   tayi fama da   haroon   akan ya tashi  ya  nemi na kanshi  kamar  yadda yan'uwansa  ke yi tunda bai samu damar  cigaba da karatunsa ba  amman   yayi  kunnen uwar  shegu  daita  har daga  karshe  itama ta dinga  biye  masa tana  bashi  cikin  kudin   da    manyan  ya'yanta  ke  bata hakan  yasa  kyawun haroon  sake  fitowa  saboda tsadaddun  kayan da yake  sakawa  jikinsa  ya famtama  gari  gurin abokai ,  duk  sanda uncle garba  yayi  masa maganar  aiki  kuwa  ranar babu zaman lafiya  a gidan ya  dinga  nunkurfici kenan  yana  cewa "shifa  ba zai iya  harkan  canji  ba  ci  baya ne agurinsa    dan  ba zai iya tsayuwa  a bakin titi yana kiran  mutane suna masa wulakanci   ba  su da sukaji  zasu  iya  su cigaba   da  tsayuwa akan   titi  bai  zai hanasu ba  amman shi bazai iya  ba , iya gata hajiya  kayi  ta  nunawa haroon  , duk abinda  yake so tana masa  saboda kasancewarsa   mai sunan kanin  mahaifinta  kuma shi ya riketa har aure tana ji dashi sosai   .."

"  Mahaifina    kuwa   asalin  iyayensa   yan  kano  ne a karamar hukumar  kiru  , sai  dai shima  zama ne ya kawo iyayensa  lagos   ,  anan  cikin  garin lagos aka haifeshi  a unguwar agege shi  da sauran yan'uwansa   ,kakana  na  gurin  uba  alhaji lukman shararraren   mai  arziki ne   wanda  sunansa ya shahara  a  jahar  lagos sannan  ya karad'e   sauran  garuruwan dake cikin  nigeria kasancewarsa  ?an siyasa , Alhaji  lukman   yana  da  tarin ya'ya da yawa   wajen su a shirin da  shida  ya haifa , ya mallaki  maza da mata  ,maza  shabiyar mata  goma  amman gabad'ayansu  kansu a ha?e  yake duk da wasu daga  cikinsu  sun mutu sauran  ashirin a raye  , mahaifina  yana  da yawon  yan'uwa  sai dai yawansu  bai sa kansu ya  rabu ba ,  hakan  kuma  ya  samo asalin ne agurin  mahaifinsu  shi ya  ha?a  kan ya'yansa  ,hakan  yasa  yaran suka taso  kansu  a  ha?e  cikin tsananin son juna babu   ruwansu da wannan  uwarsu  ?aya ubansu  ?aya,  wannan uba  daya ne , suma  haka  zalika  iyayen ma  kansu  a  ha?e  yake  haka  ma   jikoki  muna matukar  qaunar junanmu   .."
" mahaifiyata  salaha da mahaifina Alhaji  realwan sun   ha?u ne a wani zuwa bikin  abokinsa  idiaraba  soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu  ,sunyi   aure   bayan gwagwarmayar   rayuwa da  mahaifina  ya   sha kafin  mahaifin mahaifiyata  Alhaji sani  ya  yarda da aurensu  a cewarsa  ba zai ?auki tilon  diyarsa mace ya bawa    bare   kuma  yare  da ban  ba zarma d'an'uwansa ba , dan asalin  zarma  basa bada auren  ?a?ansu ga wani yare  baya  ga yarensu bisa  nasu ra'ayin ,dan har  yanzu  ba kowane bazabarme  ke  daukan ya'yansa  mata  ya aurawa   bahaushe ba , sai dai zabarmawan  dake   zaune  a garin  lagos suna  kokarin su bawa bahaushe   idan sun san asalin   daga  ina yake  kuma  sun san halinsa amman  yawancin na kauye  basa bada yaransu  saboda suna ganin  hausawa basa rike aure  ga saurin saki , har yanzu  har kwana gobe ba  kowani  zarma ke daukan  d'ansa ya bawa bahaushe  ba  sai dai su kan  yarda ?a?ansu maza  su auro  ya'yan hausawa  mata  ."
 
   Tun   bayan  da'akayi auren  iyayena  Allah bai nufesu  da  samun haihuwa  ba  sai da suka kai  kimanin  shekaru goma  da aurensu sannan  Allah ya basu haihuwar ya badamasi , yayinda  a wannan lokacin  tuni   uncle  garba  da uncle bature sun yi aure kuma a rana daya  kuma  duk yaren  zarma  suka  aura  mazauna  Idiaraba .
   bayan  bikinsu  bada jimawa  ba  hajiya kayi ta koma  ilo  da zama ita da mijinta  kasancewar girma  ya  soma zuwan musu  wanda  kusan al'adar  zamar ne basa karashe  rayuwarsu a wani  guri sa'banin garinsu  na haihuwa , duk yadda suka kai ga neman kudi  aguri  da

Please Login or Register in order to submit comment