Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

,amman  tun jiya suke nacin kisna har d'azu    da suka dawo daga makaranta , na fa?a musu muyi magana da mamansu  shine suka samin kuka ......"
saurin  runtse idanunshi yayi "kenan sun fi son mamansu dashi ?"ta yaya bazasu sota ba bayan sun rayu daita sama da shekara uku zuciyarsa ta fa?a masa haka "daita suka saba duka wata nawa kayi tare dasu ka barosu?". numfasawa yayi sannan ya bu?e idanunsa akanta tana kallonsa ya katse kiran batare daya bata  sun yi waya da mahaifiyarta ba ya ajiye wayar  akan bedside ya koma ya kwanta ruf da ciki  tare da rufe rabin jikinsa da bargo yana tunanin rayuwarsa .."
  "A cikin kwana ?aya da yayi  rashin lafiya zaka fahimci  yadda  ciwon yaci  jikinsa baya  wani cin  abinci sosai sai kisna ta matsa masa sannan yaci" Kwanaki shadaya kenan da samun saukinsa wanda yayi daidai da sauran sati biyu   mummuy da Samir da matarsa  zainab da aryan  areef  su sauka a kasar sai dai har zuwa  wannan lokacin suna  gidan  jiya  ita da Aliyu babu wani cigaba da'aka  samu a zamantakewar rayuwarsu , duk abinda kisna  tasan  zata yi domin  ta karkato da hankalinsa garesa tayi ,amman  yaki  sakin jiki daita  , yana dai  iyakacin ?o?arin  kyautata mata ta bangaren   bata abincin barin  wuta a kunne daina kulle gida  da daidai sauransu  ,
bangaren  aurattaya ,hira a tsakaninsu  wannan ma ba'a  maganarsa, mari kuwa sai dai idan bata masa  kuskure ba ,kuskure  ka?an zata yi masa  yanzu ne zai  ?auketa  da mahaukacin  mari  ,zamansu babu wani  sha'awa tamkar ba ma'aurata ba,  duk da ita kam   tana  iyakacin bakin   kokarinta na  ganin wani abu ya shiga tsakaninsu  amman shi sai ya hauta da bala'i da zagi  ,sai dai duk inda yake tana makale dashi wani  lokacin ta rungumeshi ajikinta  ta manna  masa kiss a wuya ko d'aura hannunta akan jijiyarsa idan zai hauta da bala'i ta marairaice ta nuna bata sani bane , duk sanda ta rungumeshi kuwa  haka zai zareta ajikinsa tare da nuna kyama da  nuna  mata  ta fita hanyarsa "dan shi a yanzu bashi da lokacinta  ,damarta ta rigada ta wuce kuma har abada bazata dawo ba  yanzu ma yana zaune daita ne kawai saboda  darajan iyayen ."
Sanye  yake  cikin black jeans  with  white t shirt kwantaccen  sumar kanshi  dake kwance har bayan wuyansa ya sha  gyara  sai sheki yake, hannunsa daure da agogon dimond sannan rike   da wasu file  ya kalli kisna  dake sanye cikin  abaya mai sharara sai  dai acikin abayar  wasu had'ad'd'un kananan  kaya ne wondo da riga wanda a zahiri ake iya ganin kayan dake sanye ajikinta  , ta nade  kanta da mayafin kayan tamkar yadda indiyawan Pakistan suke yi , fuskan nata tar kamar wacce take shafa mata madara , wuya da azabar da Aliyu ke ganamata sam basu nuna ba, sai dai ta zabge ta rame sosai amman hakan bai sa tayi muni ba."
Ganin yana ?o?arin barin d'akin ta  sha gabansa da sauri  tana fuskantar shi hancinsa ya shaki kamshin turarenta saurin lumshe   ido yayi na second biyu  sannan ya bud'esu tar akanta "nima za... zani gidan nasir   wata uwar harara ya watsa mata sannan yace "daman nasan sai kinyi min shishigi  tunda ke  uwar yan neman gindin zama ce da cusa kai babu kwarjini ya fada yana jan tsaki tare da tsareta da kyawawan idanunsa , shiru tayi tana mamakinsa  ita da  duk abinda zatayi  sai ya gwaleta   duk wannan maganar da suke idanunta na kan jijiyarsa yayinda yanayinta ke sauyawa  sake motsoshi tayi sosai kamar zata shige jikinsa kirjinta na dukan uku uku  on-expecting yaji  ta kai hannunta daidai saitin jijiyarsa dake kwance  wani  irin ?auke numfashi yayi da sauri  yana kallonta take tsigar jikinsa ya tashi ya dinga jin wani iri a Gabadaya ilahirin jikinsa mai kama da shocking , murmushi ta sakar masa mai narkar da zuciya  tace "kana bukatar matarka Aliyu mai  yasa zaka tauye kanka "? Cike da zafin rai ya buge mata hannu ya juya  da sauri tayi saurin riko  laulausan tafin hannunsa ya juyo a fusace "Are You mad "?. Ta fada yana zaro mata ido ,
ta kashe masa idonta ?aya  idan dai akanka  ne tuni na amshi certificate , ta karasa maganar tana rungumeshi ajikinta ta fara shafasa numfashi ya sauke da karfin gaske ya zareta a jikinsa ya bar da'kin yana jan tsaki "aikin banza kawai duk abinda zakiyi a banza .
tana jinsa ta kwashe da dariya "kana so kana cutar kanka ,tun daya fita bai dawo gidan ba  sai kwanciyar  bacci , lokacin tana  kwance akan gado ta ha?e  pillows gabad'aya ta d'aura kanta akai  haka  bargon lullu'ba  ta hadesu duka ta lullu'be  gashi jikinta babu  komai sai wata yar yololuwar rigar bacci iya gwiwa mai shara shara kai tsaye agogon hannunsa ya soma cirewa ya da'ura  a gaban mirrow sannan ya soma balbale botiran gaban rigarsa ya cire ya zame wondonsa ya  zauna akan kujera  ya k'arasa zarewa ya shiga bathoroom ya soma wanka tana jin motsin shigowarsa ta share ta ci-gaba da baccin karyanta bayan kamar minti goma ya fito ya goge jikinsa ya sauya wasu kaya ya kira nawal suka sha  hirarsu duk tana jinsa zuciyarta kamar ta kama da wuta , amman ta kudurta aranta zatayi hakuri ita yanzu har Allah Allah take ya aurota ma  a wuce gurin sai daya gama abinda yake hankalinsa ya koma kanta ,a ransa ya furta matsala wallahi wannan yarinyar matsefa ce arayuwata ,k'arasowa yayi inda take kwance"ke..! Ke!! Shiru  yaji  ya kai hannunsa ya dafe goshinsa yana tunanin yadda zai ?auki pillow da bargo  kusan minti  biyar  yana tunanin abun  yi kafin daga baya ya kai hannunsa daga saman kanta inda tayi double din pillow ya fara ja a hankali batare daya bari hannunsa ya ta?a jikinta  ba , daman abinda baya so kenan jikinsa ya ha?u da nata , murmushi tayi ta sake danne pillow sosai   da kanta ya ciza lip's d'insa da karfi yana kokarin zaro pillow  tayi wani  juyi har  bargon jikinta ya zame kayan baccin dake sanye a jikinta  suka  bayyana   fuskanta na kallon nasa  tana sauke numfashi  a hankali, cak ya bar abinda yake ya tsura  mata  ido yana kallonta  babu abinda baya  gani ajikinta, tun daga kan dukiyar fulaninta  dake  tsaye cak tamkar  ba'a ta?a sarrafasu  ba  har zuwa lafaffen cikinta wani wahalallen  miyo ya had'iye  ha?e da lumshe idanunsa  .
  sake  gyara  kwanciya tayi  ta matso jikinsa  sosai  nan rigar tayi sama ka?an cibiyar ta ta bayyana ",inna lillahi ya furta a fili  tare da saurin runtse idaunshi  yana k'arasa  zare  pillow ya ajiye kasa yana sauke numfashi .wata irin mika tayi tare da  juya masa baya nan take   bombom d'inta   suka  bayyana   makale da  wani siririn  pent Wanda  shi da babu duk ?aya ,  a hankali ya ?an bude idanunsa daya "subhanallahi ya furta qirjinsa na wani  bugawa da matsanancin karfi ya dauko  pillow daya  ciro ya  kare bombom d'inta  yana sauke numfashi  da ajiyar zuciya a tare a hankali ya soma jan bargo yayinda ita kuma ta rigada ta rike bargon gam yana ja madadin bargon ya dinga dawowa  garesa sai itace ke dawo masa kafin ya ankare ta zubo jikinsa gabad'aya tare da d'aura hannuta  daya a kan  qirjinshi daidai nipple d'insa  tana cigaba da baccinta na karya .runtse ido yayi  yana ?o?arin zare hannuta daga qirjinsa  ya fado jikinta  gbdy   jin tudun dukiyar  fulaninta yasa jikinsa ya kama rawa tamkar mazari , shigewa jikinsa tai tana zagaye hannunwanta  duka ajikinsa a firgice ya kalli fuskarta  muryarsa a kausashe yace "ke ke .....!!! yana marin fuskarta  da sauri ta cire hannunta  tana dafe goshinta  "aikin banza kawai  ace mutun ko baccin  arziki bai iya ba  saboda rashin natsuwa". yayi  maganar yana jan bargo  da karfi ya k'arasa  kan kujera ya ajiye pillow Yana ?o?arin kwanciya yaji sautin muryarta "kai me ya kawoka  inda nake da har ka kwanto jikina  da zaka wani  Kirani da kalmar rashin natsuwa "?
  Wata irin zabura yayi ya dawo  gareta yana girgiza  kai sannan yace "lallai  to me kike expecting  zanyi da wannan  jikin naki? " yayi maganar a fusace yana huci tamkar mayunwacin zaki , tayi  shiru jikinta na daukar rawa "sauko nan sai naji dalilin da yasa kika fa?a min wannan maganar  "ganin zata 'bata masa lokaci  yayi gaggawa fincikota  daga kan gadon ya sauko daita sauran ka?an kirjinsu ta ha?e yayi saurin ja baya yana furzar da iska   , eye's  dinsu suka ha?u cikin juna  take zuciyarsu yai mummunar baguwa a tare  "ance miki ni maye ne irinki  ? "ko  jikinki  zinari ne da har zan kwadaitu dashi bare ki samu damar fa?a min magana "?
  A hankali ta soma ja da  baya  saboda  ganin jijiyoyin  kansa sun mike kar ya ?auketa da mari dan gashi  zuciyarsa tazo wuya  tasan  ka?an da aikinsa ya narkar mata mugun duka ko mari ,   ganin ya kara taku  ta juya da sauri   zata gudu aiko bai tsaya wata wata ba ya sa  mata kafa sai gata ta fadi kasa dummmmmm   wata irin razananniyar  kara ta saki tare da kokarin   mikewa   ,ya sake saka mata kafa cikin tsantsar ?acin rai "yar iska kawai mai muguwar  zuciya kuma na rantse da Allah idan kika sake fa?a min makamancin maganar da kika fa?a min yanzu  sai na miki azaban da ba'a taba miki  irinta ba ya k'arasa maganar yana murje mata kafa, ita ba faduwar datayi kasa ko take mata kafarta  yafi damunta ba kamar mugayen kalamansa, a tarihi babu wani mahalukin daya ta?a fa?a mata irin kalamansa  rarrafawa tayi ta koma kan gado ta rakube  jikinta tana kuka  mai cin raina  .
Shima Kwanciya yayi bugun zuciyarsa na karuwa sai dai  bai damu da abinda yayi mata ba ,hasalima  ko ajiinsa lalubo wayarsa ma yayi yashiga danne danne har bacci ya daukeshi ita kuwa kasa runtsawa tayi yadda taga rana haka taga dare har gari ya waye zuciyarta cunkushe take da bakincinsa ,Itace ta rigashi tashi kasancewar bata samu isasshen bacci kai tsaye bayi ta shiga tayi alwala ta fito ta dauki zani ta daura a saman rigar jikinta , ta sanya hijab  ta tada sallah bayan ta idar ma bata koma ba zama tayi tana lazimi da kaiwa Allah kukanta har sai da gari ya waye ta waiga inda yake kwance a lullu'be so take ta tashesa saboda ya makara sallah  amman tana jin tsoron tashinsa  ,mikewa tayi ta sauko kasa domin ha?a masa break fast bayan ta gama ta shirya dining table dawo dakin  domin tayi  wanka ta sauya kaya  wanda zuwa lokacin tuni ya tashi  yai sallah yana zaune akan kujerar kushin ya da'ura kafarsa daya a kan daya yana girgizawa tare da yin shiru yana tunani , har ta gama abinda take bai daga kai  ya kalleta ba,  ta tsaya nesa da ka?an dashi tana kallonsa taba son ganinsa  cikin damuwa barin kuma ace itace silar damuwar  dan tunaninta ko abinda ya faru jiya yake tunawa  .
dan dawo dashi cikin walwalarsa yasa ta kaskantar da kanta da muryarta tace "kayi wanka kayi  breakfast ina jiranka "bana ci a gidan nawal zan ci"? yayi mata maganar muryarsa a dake da kuma zumar ya 'bata rai  ai kuwa  yayi nasara dan wani abu taji ya tsaya mata akahon zuciyarta mai kama da dalma  ,kusan sai da kafafunta suka gaza d'aukarta Allah yasa a kusa da jikin bango take dan haka ta tsaya da kyar  qirjinta na bugawa  da karfi  ..
   a qalla ta ?auki sama da minti talatin bayan tayi masa tayin abinci   ya fada a gidan nawal zai ci batare daya damu da halin da zata shiga ba ,
wani  lokacin gabadaya yanayinsa sauyawa yake  kamar hawainiya .
tayi shiru tana  kallonsa zuciyarta na mata wani irin zafi ,tunda take baa ta'ba mata cin fuska irin Wanda yake mata ba, sai dai ta danne zuciyarta ta nuna kamar abun bai dameni ba ya kalleta yaga kamar bata damu ba dan babu alamun damuwa a tattare daita shiru yai yana nazarin abinda zai sake mata da zai d'aga mata hankali ."
tana  kallonsa ya tashi ya bude wardrobe d'insa  ya dauki kayan da yake son sakawa ya dawo  hannusa rike da iron da Kaya wando da riga duk bakake ya soma kokarin jona iron a wuta   "jiki a sanyaye ta karaso inda yake tsaye a daidai lokacin daya Kai hannusa ya ta?a kasan iron din, yaji ko ya dauki zafi "kana jina ko  kawo kayan na goge maka kayan da zaka saka kaje gurin nawal din ai bana kishi daita hasalima ma nafika son ayi auren  ,yayi shiru kwakwaluwarsa na sake maimata masa abinda yace  "  kawo ta sake magana a marairaice a matukar tsawace yace "bana so ko dole ne ?
"Dole mana   gani   bana aikin  komai ai  ni yafi dacewa nayi maka komai ta Kai hannu  ta janyo kayan gabanta zata d'auki iron yayi sauri rike tsintsiyar hannunta "banaso nace  da ke  kike  min da zaki wani ce na kawo ?ya fadi haka tare da wurgi da hannunta ya  soma guga .
Ta sake matsoshi ya kalleta a wulakance bata damu ba tace "Da dabam yanzu dabam da baka da mata  kusa da kai yanxu Kuma kana da ita to me zai sa kayi guga da kanka ? "duk fa yadda kake son zareni cikin rayuwarka dole ka hakura ka barni  tunda ba iya rabuwa zakayi dani ba."
Cak ya bar abinda yake ya waigo inda take tsaye kusa dashi  a matukar firgice ya tsura mata ido yana kallonta  itama idanunta ta tsura masa tana kallon cikin  kwayar idanunsa tana jin zuciyarta na harbawa da sauri   "Dan girman Allah banace ki fita rayuwata ba  kiyi naki  nayi nawa ba "? "Kace sai dai bazan iya ba dole ina na kasance  da rayuwarka har zuwa sanda zan daina numfashi  "ki daina shiga tsabgata ,  bari na fada Miki abinda baki sani ba kawai kina zaune a gidan nan just for nothing  dan haka ki  daina shiga rayuwata " abu na biyu ni aliyu bana bukatar duk wani taimako ko kyautatawa daga gareki ,  dan   bazaki  taba samun cigaba  a zuciyarta Aliyu  ba  muddin rai haka zaki kare rayuwarki a gidan nan baki da wani amfani agurina  ".
wani irin yanayin mai wuyar misaltuwa ta tsinci kanta ciki take yanayita ya sauya zuciyarta ta dinga bugawa da sauri tana mata zafi ,Aliyu na jin dadin  cin   mutuncinta   , wannan shine   karo na sau babu adadin dayake tozartata   yana fa?a mata duk abinda ya fito daga bakinsa hawayen dake makale a kwayar idanunta ne suka samu nasarar zubowa, kusan minti goma zuciyarta na wata  duniyar da jin rad'ad'i da zafin zantuttukansa , yayinda shi Kuma ya cigaba da gugansa hankali kwance tamkar bai san da wata halitta a kusa dashi ba hasalima dadi yaji saboda fahimtar da yayi ya bata mata rai ".
Muryarta cike da kuka ta soma magana "duk da  nasan kana yin haka ne dan ka kasheni da bakincikika  amman zan cigaba da yi maka komai har sanda bakincikika zai kasheni  ka huta  ,zan maka komai koda kuwa bazakayi appreciate dinsa ba "kawo nayi maka gugan   ta  sake Kai hannu zata amsa iron din  tana kuka , ?auke iron din yayi da sauri  yana mata wani mugun   kallo mai cike da gargadi  "kiyi duk abinda zakiyi a gidan nan babu ruwana amman idan yazo kaina karki yi saboda bana bukata,dan  zukatanmu bazasu taba kasancewa tare ba kamar yadda kike tunani  ".  ya cigaba da abinda yake
Matsoshi tayi sosai hawaye na cigaba da gangaro mata  " babu ruwana da duk wani  abinda zaka ce, zan tabbatar dana sauki hakkinka dake kaina ba wai  kafi karfina bane kawai  Ina kyaleka  ne sabida abinda nayi maka amman ya kamata nayi abinda zai sa ka shiga hankalinka  "komai zan maka sai ka gwaleni ,kaki ka bani dama na gyara kuskurena na baya , bansan me ye matsalarka ba "....
Kallon inda take yayi yace "da kyau yar hannu  an zo gurin  ai  nasan zaki kasa jurewa    ,sai dai matsalarki  shine baki iya komai ba, sannan bakisan daidai ko akasinsa  ba, komai kina yinsa ne  tamkar na mahaukata  .
zaro  duka idanunta tai da sauri  tana kallonsa hawaye na sake gangaro mata "yes ki daina  wani zaro ido kamar am miki karya  halinki na fada ,komai na dabbanci kike yi idan kin manta na tuna miki , shiyasa nake Allah Allah nawal ta shigo gidana dan ke daita  akwai bambamci mai yawa, nawal  ta fiki komai idan ma kyau kike takama dashi ta fiki ,haka idan ilimi ne tafiki phd gareta  ke fa ?"Yayi mata tambayar yana  cigaba da  guga "just digre gareki amman Kika damu rayuwarki, bazaki taba kamo kafar nawal dina  a komai ba ,dan haka na rokeki ki daina bata min lokaci kina batawa kanki,sannan matakin da zaki ?auka wanda zai sa na shiga hankalina ina jiranshi karki canza ra'ayiki  fa ...... ".
tayi sororo tsaye  gabadaya jikinta yayi sanyi da kyar take janyo numfashi tana fesarwa ta juya  a hankali kanta na jujjuya mata da kyar ta  dinga daga  kafafunta "jina nan ......"ya fadi haka yana kallon bayanta   ta tsaya cak batare data juyowa ba "  abokan  aikina  zasu zo  anjima da yamma dan Allah ki yi wani Abu wanda zai nuna masu cewar ke din  mahaukaciya ce   kiga yadda zanyi dake stupid Kawai  mai siffar aljanu ".
  Tafiya ta cigaba yi  har ta fita daga dakin hawaye na gangaro mata   ",ya Allah ta  furta cikin tsananin tashin hankali " yanxu haka rayuwata zata cigaba da kasancewa "? ina zan   shiga acikin gidan taji sanyi arana  dan har wani duhu duhu take gani ,rasa inda zata  shiga yasa ta fada bayi ta zauna aciki  ta dinga risgar kuka  kamar ranta  zai fita yayinda kwakwaluwarta ke  sake tariyo mata magangunsa masu kuna da ciwo " wani hanya zan bi yanzu kafin ya kasheni  .."?
Mmn Sudais
????????????
CUTAR DA KAI
     ????????
????????????
~TRUE LIFE STORY~
Free Page 8
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa  wannan  number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma , getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ?aya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar  cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...????
"Kuka  take  sosai  tana  tunanin  rayuwarta  data gabata  , isa  izza  da  jiji da  kai  ko  yar  sarauta  iyakarta   kenan  , dayawa  mutane  ada can  baya  sun sha  fa?a mata cewar da  gidan  sarauta  aka  haife ta  ba'a  san  abinda zatayi ba,ita kanta tasan gidan sarauta ne   yafi  dacewa daita  saboda karfin  mulkin dake tattare  daita, taja numfashi a hankali  ta  sauke tana ciza gefen labenta na kasa sai ga wasu sababbin hawaye masu zafi  sun gangaro mata  ."
"har  ga  Allah  bata  marmarin   sake  yi masa  rashin   mutunci  saboda ta  horo iya horowa akanshi ,  tana  tsoron sake  faruwar  wani abu sa?anin  zaman lafiya , shiyasa  da zasu zo kasar   aunty  ummi  bata  so  ta  biyosa ba  , taso  ya  barta a kasarta  ne  ta cigaba da rayuwarta  a gaban iyayenta  domin  tasan  zasu  taimaka mata ,dan bazasu  yarda wani  mummunar  abu ya sameta  ba, duk lalacewar  itace din rayuwarsu ce amman ta nace lallai sai ta biyosa wanda ita a tunaninta kasancewarsu guri daya  zai sa ta  janyo hankalinsa gareta a she bata sani ba  cikin ukuba ta jefe  kanta     ta  karasa  maganar cikin wani  sabon kuka ."
wani  kullin tashin hankali   ta dinga  ji a cikin  zuciyarta  ,a ranta tace  "Aliyu  baya qaunata  sai wasu hawayen sharrrrrrr tamkar an bude famfo , tana  jin motsin saukowarsa  amman taki fitowa daga bayi  dan tasan  idan ta fito ma  wani  sabon  bakinciki zai kusan  mata , kuma  tasan wannan fitowar da yayi    gidan nawal    zashi  dan   ya kuntata mata , sai  data tabbatar da ya  bar gidan gabadaya  sannan ta mike ta isa bakin fomfo ,ta kusan minti biyar a jikin famfo tana wanke fuskarta , addur kariya da zaman lafiya a tsakaninsu tayi yafi sau babu adadi sannan ta  fito parlour  ,ta cigaba da sheshekar  kuka, ranta na wani  irin quna  ta zauna  hawaye na sake bin kuncinta ,da zarar ta runtse idanunta babu abinda take gani sai  kyakkyawar  miskilalliyar fuskarsa mai nuni da babu wani abu da ke damunsa . "
tana  cikin  wannan halin taji  motsin  bu?e  kofar falo  da  sauri ta bude idanunta ta  soma ?o?arin  goge   hawayenta  da  hanzari safiyya  ta karaso cikin filin falon  tana  tambayarta  "lafiya me kike  ma  kuka  kisna "?wani  matsanancin kuka ne  ya  sake  kufce mata haka  yasa hankalin safiyya  sake tashi "wai meke  faruwa  ne  kisna ki  fa?a  min me ya faru  kike kuka "?
cikin dasashiyar muryarta  da bata fitowa  sosai  tace "ba abinda ya sameni  juyin duniya safiyya  tayi da kisna domin  jin abinda ke faruwa  amman  taki fa?a  mata  dan haka Safiyya  ta bige  da rarrashi  har ta samu tayi shiru  "kin ma ci abinci kuwa  ta d'aga mata kai  ba dan  ta sakawa cikin komai  ba , ruwa safiyya ta tsiyaya mata a glass cup  ta mika mata  ,ta amsa ta  sha  kadan sai lokacin taji zuciyarta  ta ?an yi mata sanyi  ,cikin natsuwa safiyya tace "ki ?ara hakuri kisna duk da kina boye  min abinda ke damunki  amman zuciyata  na fa?a min kina cikin damuwa mai tsanani wanda kusan ina ganin hakan  a zahiri ,dan duk sanda zan zo gidan nan sai na iskeki cikin tashin hankali da damuwa ".
"abinda nake son dake  Ki ?ara  hakuri kowace mace da kika gani  yanzu hakuri  take a gidanta ,ba wai  wani dadi take ji  ba, kowani  ma'aurata da irin  tasu matsalar , idan kikaji matsalar  wata  zakice naki  ba komai bane, sannan idan  kina
lura zaki ga  kowace mace  a gidan aurenta tana  da katuwar matsala ,  idan  aka tara miki  matan duniya babu mace  guda  daya da za'a  cire  wacce bata da matsala  a rayuwar aurenta, haka idan aka tara mazan duniya kowane  dana shi matsalar , abinda  ya kamata  muyi  shine hakuri  ,ki karfafa zuciyarki  ki  daina wannan  kuka  babu abinda Aliyu yake so a rayuwarsa  kamar ya ganki cikin damuwa da tashin  hankali  , mai yasa  bazaki d'aurewa zuciyarki  ki  fita lamarinsa ba , duk abinda kika san hakinsa ne ki sauke masa kiyi  lamuran  gabanki , wallahi  muddin yaga kin fita hanyarsa kin sharesa  zai dawo hankalinsa dan yaga kina yawon  damuwa   idan ya bata miki   ."
  "Kin gani shekarata   biyar  kenan  da aure ban ta?a haihuwa ba ko batan wata ban taba yi ba  kuma  ina tunanin ko ni ko    mijina ne ke da  matsalar  rashin  haihuwar   nayi  juyin duniya  muje muga doctor  ko daya mu samu nasir  yaki  a cewarsa wai shishigi  za'a  wa Allah ".Kisna ta numfasa kana  tace   " idan baku je kunga likita  ba ya zaku fahimci matsalarku  ? Safiya tayi shiru ha?e da tagumi tana kallon kisna batare data ce uffan ba , " Shi bai  yi tunani mai kyau ba ke kuma  kika biye masa ta karasa maganar tana duban Safiyya  ."
Safiyya  tayi  murmushi  saboda taji  maganar  kisna akwai zallar  kuruciya a ciki  kusan second biyu Safiyya  tana dubanta tana murmushi sannan tace  "to  ya zanyi  kisna tunda ina sonshi, bugu da kari maganarsa akwai  gaskiya kar muyiwa Allah shishigi akwai ma'auratan da sun yi sama da shekaru kuma daga baya sun samu haihuwa "an san da haka   sai dai kuma Allah ya bawa likita sani akan abinda ya danganci rayuwar dan adam ku daure kija ra'ayinsa domin ya'ya rahma ne ."
Safiyya ta sauke numfashi tace " zan cigaba da addu'a kema ki tayani da addu'a " kisna tace " Allah  ya  canza masa ra'ayinsa  "ameen kisna na

Please Login or Register in order to submit comment