Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gode  ta fada ha?e da kamo hannu kisna cikin nata  "dan Allah kema ki saki ranki ki daina saka damuwa  aranki kalli yadda  kika rame gaba-daya  kin canza kamar bake ba  ,kin fi  kyau a sanda naga hotonki  gashi  naji uncle Aliyu  yace next week family  dinki zasu zo ? Kisna  ta d'aga  mata kai alamun "eh . "kinga kuwa ya kamata ki natsu  ki kwantar da hankalinki  ta yadda idan sunzo su  ganki  fess  a cike,  idan mahaifiyarki ta ganki   haka a rame  bazataji dadi ba  "ni dai shawarata  komai Aliyu yake miki kiyi hakuri tunda  bazaki iya fa?a wa kowa  ba  bare ki  ragewa zuciyarki rad'ad'i , ki sharesa  ki cigaba da rayuwarki ."zanyi hakuri na cigaba da rayuwata kamar yadda kikace amman bazan iya sharesa ba  ."to shikenan sai ki zauna kina  kunsawa kanki  bakinciki har wani ciwo ya kamaki koda yake baki  ga  wahala bane idan  kikaga wahala da kanki  zaki nemi mafuta nan  suka  cigaba da tautaunawa  har kusan karfe  biyu  sukayi sallar tayiwa safiya tayi   abinci    tace a koshi take   tayi mata sallama ta tafi."
komawa  sama tayi ta  cigaba  da kukan zuci dana  zahiri , ta shiga zagaye  d'akin  kafin tana   zance zuci hawaye na cigaba da  gangaro mata  "kisna  dole  ki nemawa kanki mafita  to  me zanyi "?  dole ina bukatar waya  gashi  bani dashi a hannuna  ina  zan samu waya ? "Ta yiwa kanta tambayar "babu hanyar da zaki samu waya  muddin ba Aliyu ne  ya baki ba  shi kuma  gashi bashi da niyyar  sai  ta tsagwaron  rashin mutunci ." shiru tayi hannunta na tsarke  cikin juna ta karasa  ta  kwanta akan katifa  tana sauke numfashi a hankali ta kai hannunta  cikin sumar kanta  ta yamutsa tana sauke  ajiyar zuciya "baki da  abun yi dole kawai ki kwantar  da hankalinki ki rike  sirrin gidanki ki ?auki wannan  abu a matsayin  kaddararki tana  kwance lamo ya shigo d'akin  da sauri yana  waya  ta d'ago ta kalleshi aka ci sa'ar shima  idanunshi sun kai gareta   suka  ha?a ido, kallo  ?aya yayi mata ya ?auke  kanshi  yana jan tsaki "eh gasu nan  muna  tare ma yanzu ,okay to shikenan yayi  maganar cikin harshen  tsadadden turancinsa  sannan ya katse  wayar ya ?auki jakar  laptop d'insa ya fita."
Jin hayaninyarsu a kasa tayi  tunanin  ta sauka ko ruwa  ne  ta basu tunda sun  san yana da mata a gidan  bai  kamata  ta biyewa  halinsa ba , a hankali ta yunkura ta fito  zuwa  parloun tana tuku  akan step cike da  natsuwa , a hankali  ya d'ago  ya kalleta ya tabe baki yana yatsina fuska kamar yaga wani mugun abu  a karshe yayi  mata   kallon banza tare da ?auke kansa ya  d'aure fuska tamau tamkar hadari  ,suna zaune gabad'ayansu suka d'ago idanunsu saboda daddad'an kamshin turarenta da ziyaci hancinsu duk da ba sawar yanzu bace tun wanda tasa da safe ne makale ajikinta idanunsu na kanta har sanda ta karasa  saukowa   muryarta a raunane tace "sannku da zuwa ina yininku  cikin  harshen turanci?Gabad'ayasu suka washe baki suna sakar mata murmushi kafin daga baya suka amsa  "amarya  a she idonki biyu  ai  dana  ji shiru baki fito mun  gaisa ba na ?auka bacci kike yi   nasir  ya fadi  haka yana kallonta.?
girgiza  masa kai kawai tayi  tace "idona biyu na dai  dan  kwanta ne Aliyu daya dago yanata faman   harararta   tun data  tsaya yace "tsabar koshi da   samun  guri  ne yayi mata yawa  " yayi maganar  da hausa sannan  ya  kalli nasir "kai yanzu malam   mai ruwanka da fitowarta ne ? "Kuma idan ta fito uwar  me wannan wawiyar  zata maka da kake ta wani faman washe mata ha?ora  ?"  Ya k'arasa  maganar yana jan   tsaki .
shiru Kisna  tayi , jikinta ya sake yin sanyi da lamarin Aliyu,  wato dai komai sai ya rama  ,a hankali  ta soma daga kafarta  ta shiga Kitchen domin kawo musu abun sha ."
Nasir ya tsina fuska "gaskiya Aliyu ba'a haka abinda kakewa yarinyar nan fa bai dace ba ,bafa Allah ne zai sauko daga sama ya baka hakuri ba, mutane dai irinmu ne zasu baka hakuri komai fa yana da lokaci tunda gashi ta sauya ta dawo yadda kake so gaskiya ni dai ka daina abinda kake mata   idan ba haka ba zance ta fara ramawa ka dai san itama ai ba kanwar lasa bace duniya ce ta maidaita haka  ya k'arasa  maganar yana kwashewa da  dariya .
"ka dade  wallahi ai abinda nake so kenan ta nuna  halinta kowa ya gani  daga nan su sake bukatar  takardan sakinta  a karo na biyu  na rabu daita na  huta  da naci mayyar  yarinyar  nan ,yarinya  kawai ta like min tana takurawa rayuwata  har ta fito  Aliyu bai daina zaginta ba , ta ajiye ruwan  lemu da ruwan sanyi   yana cigaba da  zaginta  yayinda abokan aikinsa ke faman satar Kallonta tamkar zasu cinyeta , tayi matukar yi musu kyau tamkar ba hausa ba , komai na jikinta cassss  cassss rohan wanda ya kasance dan kasar India shi yafi Kallonta yana lasar lip's d'insa matsayinta na matar abokinsa ne kawai yasa zai daga kafa amman da a waje ya ganta babu abinda zai hana ya kulata har ma da kulla mu'amula mai karfi a tsakaninsu .  "sannu Kisna  mun gode fa  , ba tace masa komai ba ta juya a hankali   ta haye sama  ta shige d'aki tana kuka  ranta na mata zafi "daman sai daya gargadeni ......"me ma ya kaini sauka ?tayiwa kanta tambayar hawaye na gangaro mata.
"yanzu dan Allah mutanen nan  da suna  jin  hausa haka zakayita magana agabansu "? "Dan Allah malam kayi abinda ke gabanka banason damuwa da kumfar baki  ...Har kusan la'asar suna nan suna aiki , bata daddara ba ta  sake saukowa  domin  ta d'aura musu  abinci dare  ,karfe bakwai  daidai ta kamala da komai  ta zuba a kula ta d'aura a tire da plet da spoon ta fito daga kitchen ta ajiye agabansu ta kawo musu ruwa  tunda ta soma kai kawo rohon ya tsaida abinda yake ya zuba mata ido yana faman Kallonta sai ma yaga kamar tafi dazu kyau ,Aliyu ya lura da irin kallon da rohon ke binta dashi sai dai   bai bi ta kanshi ba ,haka abincin data ajiye bai kalla ba  bare wacce tayi abincin, nasir yace "gaskiya yunwa nake ji fa bari naci ka?an idan naje gida na qara dan idan na cika cikina anan  akwai katuwar matsala idan na koma gida , tsaki aliyu yaja yaki kallon inda yake  ."
  anan gabad'aya abokan Aliyu  suka ci abinci  suka sha ,nasir da sauran  abokansa nata santi da yaba girkinta barin rohan yafi kowa zakewa dan har cewa yayi a tambayar masa ko tana da kanwa da bata yi aure ba a bashi yana so Aliyu ya yatsina fuska yana zabga masa ?atuwar harara  "kai dan  Allah ko dan  girkin nan nata bazaka sauko ka rungumi matarka ba ku ci-gaba da rayuwa mai dadi ba  "?
"a wannan zamani fa bakowace mace ta iya girki irin haka ba ya d'ago a sukwane ya kira sunansa  " Abdul nasir ........."
"Na'am abokina mai zuciya da  taurin kai kamar mutanen farko "tashi ka wuce gidanka   dan Allah  na sallaneka  bana son damuwa "ko bakace ba wucewa zanyi gurin matata yar albarka mai kyautata min ina jin dadi ina godiya  nasan ma yanzu tana can tana jirana   ya mike ya kama gabansa yana murmushi  ".
****
Daren ranar ma irin baccin da suka saba shi sukayi yana kan kujera yana waya da masoyiyarsa nawal  ita kuma  tana kan gado tana kukan zuci ta rasa yadda zatai dashi ita bata hana shi yin wayarsa da nawal  ba amman ya dinga yi a waje ba sai suna tare ba, kwana yayi yana waya itama kwana tayi tana juyi  har goshin asuba  ta mike ta shiga bayi  ta d'auro alwala ta fito ta soma gabatar da nafilfili  har aka kira sallah ta tashi ta gabatar da sallah ta dade zaune tana lazimi tana kaiwa Allah kukanta da neman sausauci ..."
"Yana tsaye a saman gidan  sanye cikin farar riga da  wando baki   ya  hangota  sanye cikin doguwar riga pinky colour sanye da k'aramin hijab  tana  share palo, shiru yayi  yana kallon  bayanta duk da bai ga fuskarta ba yasan tana cikin damuwa dan yana jin haka ajikinsa, tabbas abinda yake tunani din shine tattare daita dan  hawaye ne  ke tsiyoyowa daga cikin kwayar idanunta tana gogewa da bayan hannunta  ,aikin da  sai  dai ta  farka taga anyi  komai, ko  tabawa masu aiki  umarnin  aiwatar  da duk  abinda take so kuma dole subi umarninta  suyi yadda take so yau itace take yi hawaye ya ci-gaba da zobo mata tasa hannu ta sake  gogewa  ta tattara sharan  guri daya ta kwashe ta shiga Kitchen duk akan idanunsa, numfashi ya sauke   yana furzar da iska mai zafi da ga bakinsa sannan ya juya ya koma d'aki  ya rike kugunsa da hannunsa ?aya yayinda d'ayan hannun ke saman goshinsa yana tunanin yadda yake  musguna mata ,duk sanda  ya ganta cikin damuwa sai   yaji kamar ya  yafe mata sai  kuma zuciyarsa  ta hau tuno masa  komai  ".
*******
Ana gobe su mummy zasu  sauka a kasar  taji yana waya dasu har dasu aryan yana gama wayar    tace " zan bika  airport   d'aukosu mumy   gobe ya watsa  mata kallon  banza  yayi tamkar ba dashi  take maganar  ba ,washegari tun data idar da sallar asuba bata koma bacci ba ta shiga Kitchen  ta soma ha?a musu abinci ,abinci kala uku tayi musu ha?e da cak  ta gama  ta gyara ko'ina ta feshe gidan da kanshi duk abinda tasan mumy zata gani tayi magana  sai data kawar dashi sannan ta hau sama ta shiga wanka  ta shirya  cikin  atamafa  super exlusive mai ruwan ja da zanen fulawa baki  dinki riga da siket ne sun karbi jikinta  ga wani sihirtaccen kamshi na musamman  dake  fita ajikinta  ta d'aura    doguwar  riga abaya akan kayan  tayi rooling  kanta da mayafin abayar   duk da ta zabge ta rame  amman hakan  bai hanata kyau ba , shi kanshi  har mamaki yake duk yadda take cikin damuwa kyawunta baya  dusashewa ,  tana nan kamar yadda ya santa da tsananin kyau da kamshi mai dadi , dake wa mutune  iso a duk sanda suka kusanto inda take, hakika  yabon gwani ya zama dole duk da  bai jinta acikin  ranshi amman  yana jinjinawa kamshinta  ,mace ce tamkar mahaifiyarta mai tsananin  tsabta da iya tsara  kwaliya tun bata kai  haka ba gwana ce gurin ado  ?auke kanshi yayi akanta    ya soma  ?o?arin shiryawa   cikin kanana kaya kamar koda yaushe har ya gama narkakkun idanunta na kanshi ,tana kallonsa  ya ?auki mukulin mota zai fita batare daya mata magana ba ,ganin yana ?o?arin fita tayi saurin shan gabansa tana fuskantar shi hancinsa ya shaki kamshin turarenta itama hancinta ya zuko  mata kamshin turarensa atare suka lumshe idanunsu zuciyarsu na wani irin bugawa da matsanancin karfin gaske ......"
a hankali ta rigashi bude  baki  "haba  aliyu kaji fa nace  maka zani d'aukosu  mumy  shine zaka wuce  ka barni " wata uwar harara ya watsa  mata sannan yace "na sha gaya miki bana son shishigi ko amman da yake ke uwar yan shishigi ce sai da kika yi ,dole ne sai kin nemi gindin zama "?ya fa?a  yana jan tsaki tare da tsareta da kyawawan idanunshi masu narkar mata da zuciya ."
shiru tayi tana kallonsa tana mamakinsa ita da mahaifiyarta amman kullum sai ya  dinga nuna mata  ya fita sonta  ,ko da yake itama mumy haka take nuna wa tafi sonshi  akan ya'yan cikinta sannan tafi yarda dashi fiyye da kowa dake cikin gidansu sake matsoshi  tayi ta shige masa jiki har tana gogo jijiyarsa "karka 'bata min rai  yau  zan ha?u da mahaifiyata bayan wani lokaci dana ?auka ban ganta ba "karki 'bata ranki a banza dan  babu inda zani dake na bar nawal   dina   dan tare daita zamu yayi maganar tamkar bashi yayi ba ya  soma ?o?arin fita daga d'akin .
zama tayi a bakin gadon ta zuba tagumi tana mamakinsa "yanzu na sake tabbatarwa kaina cewa baka kaunata Aliyu ta fada tana nuna qirjinta da yatsa , tsayawa yayi cak tare da juyowa ya natse ya sake tsareta da idanunshi , idanunta sun  ciko da hawaye ta runtse idanunta sai gasu sharrrrrrr sun gangaro  "da kyau kiyi kuka sosai  zan fi bu?atar haka wallahi babu abinda nake so kamar naga wannan ya tako ya  kai yatsan hannunsa ya dangwalo hawayenta  yana kallo murmushin farinciki ya bayyana akan kyakkywar  fuskarsa "abinda nafi bukata kenan  ranar farinciki ya zame miki ranar bakinciki  yana gama fadar haka ya juya ya bar d'akin cike da farinciki " .
Yana fitowa direbansa ya bude  masa bayan mota ya shiga suka bar gidan motar escout dinsa suka saka shi a tsakiya  kai tsaye hanyar airport suka ?auka daman babu wata nawal din  da zata shi daita kawai dan ya kuntata mata ne ya fadi haka  kuma yayi nasara bata mata rai  ,  akan  hanya ya  kira   number nasir  ya ?auka yace "ya'akayi,?
Aliyu yace  " ka shirya ne ? "Eh kai kawai nake jira "  okay ka  biyomu da motarka mu hadu a  airport  , kusan a tare suka karaso guri  direbansa ya   samu guri  yayi parking Shima Nasir yayi parking  sannan suka fito ,Aliyu ya jingina da mota,  nasir ya karaso ya tsaya kusa dashi "dan Allah abokina karka yi abinda zai taba ran kisna a gaban mahaifiyarta kasan tsakanin uwa da d'a sai Allah ba'a shiga tsakaninsu , duk son da mumy take maka bai  kai na kisna ba "a ganinka  ba , kai ne kake ganin haka amman ni a zuciyata ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba nasan  tafi son akanta ,idan ka manta na  tuna maka a yanzu ma tana samun  kulawa ne agurin mumy  saboda  tana karkashina ,da a  karkashin wani take wallahi bazasu ta?a had'uwa daita   ba bare wata maganar fatan baki ta had'asu    "duk da haka dai  karka yi abinda za'a yi Allah wadai da kai  taci darajan mahaifiyarta "naji plz abar maganar nan   .."
A hankali  cikin natsuwa fasinjojin  dake cikin jirgi  suke saukowa daya bayan daya  ciki  kuwa har da ahlina kisna   mumy ce a gaba tana taka mattatakala hannunta rike da aryan har suka sauko farfajiyar gurin inda idanunta bai sauka akan kowa ba sai kan Aliyu shima da sauri ya tura wayar dake rike a hannunsa cikin aljihun wandonsa ya nufo inda take ya rungumeta  ajikinsa "i really miss you mummuy  ,itama rungumeshi tayi tare da sakin hannun aryan "i miss You too muradi , "sannu da zuwa mamana maganin kukana ."
  " yauwa d'ana  mai tausayina yau ina cike da farinciki  ,"nima haka mamana "dady ......"..
aryan  ya furta yana rike masa gefen  riga  a hankali ya saki mummy ya ?auki aryan  ya rungumeshi "babana   i miss you so much  tare  da kissing din  goshinsa daya bayan daya ya rungume yaransa  cikin tsananin farin ciki sannan  ya rungume Samir "ai na  ?auka ni baza'a min sannu da zuwan ba ?  "ni na Isa bayan kai din na dabam ne kuma ajikin farko a zuciyata  "zainab  ya akayi ne  me  wannan dan'uwan nawa yake baki naga kinyi bulbul  haka ?"
dariya suka sukayi  gbdy suka  jero har gurin  mota nasir ya durkusa har kasa ya gaishe  da mummuy cikin girmamawa ta amsa tana tambayarsa matarsa ."
Aliyu  yasa hannu ya budewa mumy murfin Mota Yana tsaye ta shiga ta zauna tare dasu areef  su kuma Samir da zainab suka shiga motar nasir suka dauki hanyar gida  ,Hayaniyarsu ce ta fito da kisna da sauri   biyu biyu ta dinga taka step tare da  ihun murna ganin mahaifiyarta tana faman kiran  sunanta mommy!mumy !! Oyoyo  daidai  tsakiyar parloun  suka ha?e  ta  rungumeta  tana sauke numfashi da ajiyar zuciyarta mumy ta daura hannunta a kanta tana shafawa cike da matsanancin tausayin yarinyarta wacce kallo ?aya tayi mata tasan tana cikin tsananin damuwa ,kusan minti biyar suna rungume da juna sannan Kisna  ta zare jikinta ta durkusa   har kasa ta gaishe daita tana murmushi ganinta  mumy  ta mikar daita  ta sake  rungumeta  tsam   ajikinta  itama Kisna  rungumeta tayi sosai ,mumy ta cigaba  da  shafa kanta zuwa bayanta " fatan na sameki lafiya diyata "?
"Lafiya qalau mommy  "da kyau  Allah yayi miki albarka "ameen mommy
fuskarta ?auke da matsananci farinciki ta sake  rungume  mahaifiyarta tana jin  wani sanyin dadi  yana ratsata "lallai uwa dabam ce arayuwar  ya'ya bata qara sanin mahimancinta ba sai datayi  nisa daita ,ita kuwa mommy   tunda ta rungume  diyarta  dumin jikinta da yanayinta ya tabbatar mata da tana cikin tsananin  damuwa ta zareta daga  jikinta a daidai lokacin da hawaye ya cicciko a idanun Kisna   tayi saurin zare jikinta ta  rungume aunty Zainab "oyoyo aunty zee  sannuku da zuwa kunzo lafiya ?"lafiya qalau auta mumy  fatan kina lafiya "?"lafiya lau  nake aunty zee .
  mummy tayi shiru ta  kasa zama sai kallon bayan kisna take tana son ta sake kallonta Dan ta karewa  yanayinta  kallon  tsab , sai  dai tana juyowa murmushi ta gani kwance akan fuskarta "mumy Ki zauna mana Aliyu ya fa?a yana soso keya  , zama mommy tayi kamar yadda ya umarceta , dukkaninsu suka  zauna aryan da areef suka zube a jikin mamansu  suna zuba mata surutu  "mumy shine kika gudu kika bar mu ko kullum sai ni da areef muyi kuka" ?
Ta Kallesu tausayin yaranta ya kamata , bata san sanda hawaye ya gangaro mata ba," ta bar su ne saboda mahaifinsu gashi bata tsinci komai a zamanta dashi ba sai tarin damuwa da bakinciki ".
"Allah sarki babana ban gudu na barku ba  ,  na zo gurin   dad dinku ne amman very son zamu kasance tare kunji yarana i love You  so much do you love's me "?"yes mommy suka hada baki gurin furta mata  haka sannan suka  kwanta ajikinta , ta kai  hannuwanta duka  tana shafa kansu  tare da manna  musu kiss , sannan ta mike ta shiga  Kitchen  manya manyan kuloli ta shiga fitowa dashi tana ajiye wa a gabansu tare da plet tana fadar "ranki shi  dade hajiya mommy ga abinci  .
mommy tayi dariya tare da cewa "yau kuma har da ?arin girma na samu  ? tayi maganar tana dariya suma dariya suka yi gaba-daya "ai dole mummy kin ma fi ranki shi dade din ai  Samir ya janyo kuloli "bari muga  irin abinci da dan'uwana ke ci ya narka kiba haka yayinda  kanwata take ramewa....."
tsam Aliyu ya sha jinin jikinsa har kisna,Samir  ya bude kula miyar stew Wanda yaji kayan kamshi da soyayyiyar  naman kaza da  kuma kamshin romon  jelar sa  dake tashi a cikin wata kular , sai wani plet da aka jera  cake  wanda  yaji kayan hadi, ya saki murmushin jin dadi yana fadar "lallai dole danuwana ya dinga narka kiba har da wani fresh na musamman idan na soma cin abinci nan kar wanda ya rike min hannu dariya suka saka gabad'ayasu banda Aliyu dake wasa da yaransa kisna ta mike a ranta tace "dama yana wani cin abinci ne mutumin da sai akai ruwa rana yake ci shima yana ci yana zagin mutane  ,
saman kujera da mumny take zaune ta zauna gefenta ta d'aura kanta a saman kafad'anta "mumumy me za'a zubo miki ko duk abinda na dafa zakici?Mummuy  ta  ?an kalleta "ai ban ga gurin cin abinci ba sai naji dalilin  wannan ramar  ? tayi maganar can kasa kasa ta yadda babu mai ji "gaskiya banji dadin ganin yadda kika dawo ba, kinki kwantar da hankalinki ko har yanzu zuciyarki na wani guri ko"?Tunda  mumy ta soma magana qirjinta ke bugawa tayi saurin kawar da damuwarta ta mike  dan bata son ta fahimci komai cikin sanyi jiki   ta shiga zuba mata abinci ta mika mata sannan tai saving sauran har Aliyu  bai ce komai ba ya amsa dan babu yadda zai yi ya soma ci har suka gama hankali mummy yaki kwanciya  tana son Jin dalilin ramar Kisna ..
ha?a  kuloli da plet plet din  da suka yi amfani dashi   ta bar gurin  zuwa kitchen , bayan Wasu sakonnin ta dawo wanda zuwa lokacin tuni Samir da matarsa zainab da Aliyu da yaran sun fita zuwa gidan Samir dake cikin haraban gidan ,Kisna  ta zauna kusa da  mummy ta ?an kwanta a jikinta cikin shagwa'ba tace
"Mummy nah duk naga kinyi wani iri   karki damu da ramata   dan babu abinda ke damuna .. ....."
Mmn  sudais
????????????
CUTAR DA  KAI
     ????????
????????????
~TRUE LIFE STORY~
Free Page 9
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ?aya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...????
.....Shiru  ne  ya biyo baya ,  parlou'n  ya  ?auki  shiru   kamar  babu mutane  a  cikinsa , yadda  kisna  bata  sake cewa  komai  ba   haka ma momy  har  tsawon  minti  goma  sannan  sautin  muryar   momy   ta  doki  dodon kunneta,  "dole  zan  damu  da ramarki mamana  ,ni   dai  fatana  ki  kwantar da  hankalinki , ki  kasance cikin   farinciki  , ki  zauna da  mijinki  lafiya bana son  rayuwarki  tare  da  wani  mutun  bayan muradi  a nan duniya  saboda nagartarshi , gashi  mutumin  kirki,  mai dattako wanda kowace uwa zata yi alfahari dashi a matsayinsa na surukinta ".
"haka  ne mommy duk abinda  kika  fa?a akan shi  gaskiya ne , duk inda ake neman  mutumin kirki dole  a ambaci shi , kisa a  ranki  a gidan ya  aliyu  zan k'arasa  sauran rayuwata data  saura bani da burin rayuwa da kowa a halin yanzu  sai shi ,  tana  gama  fadar haka ta mike  tsaye   tare da  kamo   hannun mahaifiyarta "muje  sama  mumy  an gyara miki  daki".
"zan so na zauna a bangaren dadynku  " no no mummy  dan  Allah ki  zauna  a  nan   nafi son na jiki  a kusa  dani ta karasa maganar cike da shagwa'ba ,momy  tayi murmushi kawai batare da ta  sake cewa komai ba  saboda  farincikin diyarta  shine nata ,ta mike   suka  nufi  sama madadin  ta kai ta dakin da zata zauna   kai  tsaye d'akin baccinsu ta shiga   daita  ta  zaunar  daita  akan  kujera  zata juya   momy  tayi saurin   riko  hannuwanta  duka  cikin nata  tana sake  kallon  cikin kwayar idanunta   tana  sake karewa jikinta kallon kallo ,wuyanta duk kashi ,tayi wata    irin ramar    kamar  bata cin abinci  "ina son ganinki  cikin   farincikinki  mamana  sai  dai  ban ga alamun kina cikin  kwanciyar hankali ba , kin  rame sosai  mamana ko baki  da  lafiya  ne?"  ko  kuma  akwai abinda  ke damunki "?
  Numfashi  kisna  ta sauke  zuciyarta na wani irin rawa da tsinkewa Wanda kallo daya zaka mata ka fahimci tana cikin damuwa  da kyar ta sanyawa jikinya jarumta  tace   "mommy  na fa?a miki  babu abinda   ke  damuna   , ina cikin koshin lafiya, ina  farinciki  a gidan nan , bani  da  damuwar komai  ,duk  abinda nake so shi nake yi , shima ya  Aliyu  duk abinda ya gani zai  siyo min,  ga tsantsar kulawa  da  soyayyar da yake  bani  ,baya qaunar abinda  zai  nisantashi dani yana bani kulawa  sosai ...."tayi  maganar  hawayen da  take ?o?arin  boyewa ya  cika idanunta  tayi  saurin zare hannuwanta  cikin na mumy   ta    mike  ta juyawa momy  baya dan  bata son taga zubar hawayenta ,  ta k'arasa jikin   wordrobe  ta bude inda  kayanta suke  ta  ciro   dogayen   riguna guda    uku    da nasir ya   siyo musu  ita da safiyya   ta  juyo a sukwane  tana nunawa  momy tana takowa  zuwa gareta   "momy  kinga wad'an  nan dogayen  rigunan duk  shi  ya siya min  ta d'aura  akan cinyar  mommy  ita dai momy binta  Kawai  take da Idanunta da suka cika da ruwan  hawaye  ta sake juyawa  ta d'auko agogo" wannan  ma shi ya  siyo min   ta d'aura  mata akan

Please Login or Register in order to submit comment