Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a hankali  ya  dinga  masa nasiha mai ratsa jiki  sai kusan  shida  na yamma suka  bar  gidan zuciyar Safiyya  cunkushe da bakinciki  duk   abinda mijinta   ya  fa?a  bata dauki komai  ba , ita dai tasan  Aliyu  ya taho da diyar  mutane  ne ?an kawai  ya cutar  daita ".a mota  tsokano maganar  ta  dinga yi dan nasir  ya fa?a  mata abinda ya faru tsakanin kisna da Aliyu  amman yaki  ,dan  baya son tasan  komai  dangane da rayuwar Aliyu , ganin haka  ta  kudurta  a ranta zata  dawo musamman  domin  taji  komai  abakin kisna"
Ranar  haka kisna  ta kasance  da  zazza?i , ko falon  bata sake fitowa ba , ya  shigo d'akin kallo ?aya  yayi  mata ya fahimci  zazza?i ne ke d'awainiyya daita "kin shigo  daki  dan bakin munafurci  kin boye  ,to ki bu?e  kunnuwanki da kyau , duk abinda kika san  nawa ne acikin gidan  karki yi ganganci ta'bawa idan ba haka ba wallahi  wallahi  ......"
qarar  wayarsa ce ta katseshi  ya ?auka  ya  juya  ya  fita daga d'akin  kunneshi  manne da wayar  har  ya  fita  bata san  ya  fita ba wani sabon  tashin hankali da faduwar  gaba  da wani irin  tsoronsa ne suka d'arsu a zuciyarta "yanzu irin  rayuwar da zata yi kenan  "?
"a she Aliyu bai san darajan  dan adam ba kamar yadda tai tsammanin   ? " mutumin  da kullum take  wa kallon yafi kowani  ?an  adam kirki da nagarta a duniya  shine yau  yake kokarin kasheta  da ranta  ta share  hawayen daya wanke  mata fuska ta tashi  ta soma ha?a kayanta  a jaka  tana cikin  zubawa cikin jakarta  ya  shigo sai da gabanta yayi  wani mumnunar faduwa  da ganinsa ,  da sauri tayi  jefa da  kayan da  yake hannunta  sakamakon kallon  da yayi mata ta matsa  baya  da sauri  "kashina ya bushe ta furta hakan  a kasan ranta " cikin matsananci mamaki  yake kallonta "a kwana  biyu kacal har ta gaji dashi  ya furta a ransa  dariyar  mugunta na  kokarin  subuce masa  yayi saurin had'iyewa  yana watsa mata  harara, tausayin kanta ya ka mata "a kwana  biyu  kacal har kin  gaji  da aliyunki kin  soma  nemanwa  kanki mafuta ba ?"
"haba  yarinya har yaushe daren yayi?  "ai yanzu  aka  fara  buga wasan  ,ina  irin naki wasan  yake ?"yayi  magana  yana  tsareta da idanushi  tare da tsuke ?aramin  bakinsa  "Okay a she  fa yanzu son Aliyu ake  baza'a  iya aikata komai  ba , amman zan so  ki fito da salon  iskanci  da kika iya kala kala  sai  mu buga wasan mugani  cikin ni dake waye  zai yi nasara ".
"babu abinda zanyi  har kullum  hakuri   zan cigaba da  baka saboda nasan ...... " yi  min shiru  munafukar Allah kawai  hakurin  ubanki zaki cigada da bani  ? tayi saurin  girgiza masa kai jikinta  na rawa  wallahi kika sake bude wannan rubabben bakin naki da zumar bani hakuri sai Kin  dawo ball a gidan nan , dan na dinga kwallo da kanki kenan har sai kin mutu  .."Tsit tayi tare da sunkuyar da  kanta kasa  tana sauke numfashi ,"mai mugun hali kawai ya fada yana fad'awa saman gadon ya talla'be kanshi da hannunwansa duka  ya runtse idanunshi gam yana jan dogon  tsaki ..."
Tun   daga   rana  bata sake  samun  canji rayuwa daga Aliyu   ba, tsananin  yafi  na wanda take  ciki , kuskure ka?an duka  da  zagi  ga azabar yunwar  da yake mata, sai ya  fita tun  safe ya barta  babu abinci , sai idan ta roki mai  gadi  ya taimaka  mata dashi  a rana sau daya take cin abinci ,  kafin   kace  me ta  zabge  tayi wata ?atuwar  rama sai dogon hanci da wuya  ,a qalla sai  datayi  sati  biyu a kasar , sannan wata ranar lahadi  yace ta shirya  dan   shiga  kasuwa shima  darajan  nasir taci if not  haka  zai barta tayi rayuwar yunwa   daga karshe ta mutu ya huta  ..
yana  zaune  cikin motarsa  kiran  beaz  330   hannuwansa   akan  stearing , ganinsa cikin mota ya hana escout dinsa harama biyosa dan duk sanda yayi haka baya nufin yana da bukatar rakiyarsu , ta fito jikinta  sanye cikin doguwar riga marun colour  har kasa mai zanen  fulawa  milk colour tun   daga wuyar rigar har zuwa shashin dukiyar fulaninta ,rigar tayi mata kyau sosai ,kafafunta sanye cikin flat shoe masu matukar kyau , babu  kwalliya a fuskarta sai  powder data dan shafa, ta shafawa lip's d'inta  Whit lipstick
duk da ta rame sai dai hakan bai hana kyawun da Allah yayi mata fitowa ba ,ta fito haraban gidan tana taku  a natse kamar koda yaushe  ta  bude murfin mota ta  shiga cikin dari dari ta  zauna  batare da ta sa seatbelt  ba , ya murza stearing  din motar  ,  take mai gadi ya bude musu makeken get din gidan  suka  fita .
a hankali motar ke gudu akan titi  ta ?an juyo inda yake   ta kallesa yayi kyau  sosai , komai nashi irin  nasu  aryan ne babu abinda  suka bari nasa , ya ?an  juyo ya kalleta ya ?auke  idanunshi  yana jan  tsaki "mayya kawai ji yadda  ta kurawa mutu ido kamar zata cinye mutu  ,burki  yaja  aiko gabad'aya  ta gigice ta zubo   jikinsa dole yasa ya tsaya ba dan ya shiryawa hakan ba  yana kallonta , a fusace yace  "kina hauka ne  ,ki sanya seatbelt  mana "am sorry ta  fada tare da janyo seatbelt  ta sanya tana kallon  wani bangare "komai  yayi kyau yake masa  zan cigaba da hakuri  da  kai nasan wata rana zaka sauko ka  soni ?"
  Duk  wani  abun bukata a gida  bangaren abinci babu  wanda  bai siyo ba sai  daya  cika bayan  Boot d'insa  sannan suka ?auki  hanyar dawowa gida , akan hanyarsu   tace "ina bukatar waya da  sabon layi  ina son nayi waya  da mummy ".
banza  yayi mata cikin haka  taga wani guri da'ake  siyar da  waya da layin  waya tace "yauwa dan Allah ka tsaya ka  siya  min , ya tsayar da motar  kamar abun arziki yana  gama tsayar da motar  ya sauke mata  yatsunsa biyar  a fuskarta "shiga hankalinki  baki isa kisani yin  abinda banyi niyya ba, duk abinda kika ga nayi  na gadama ne wawiya  mara  kamun kai kawai , kina wani hauka kamar tinkiya  , ke din da bakowa bace , ba matsayi  gareki  a zuciyata ba ,dake da jaka  daya  kuke  agurina , ya kai  hannunsa ya murza stearing  ya cigaba da tuki  har suka karaso gida kuka  take  kamar wacce akace uwarta da ubanta  sun mutu yana gama  daidai tsayuwar motarsa  ya bude boot  ya  fito ya shige ciki abunsa ya barta ..
yana zaune a parlou'n ta shigo  fuskarta tayi jajur  kwayar idanunta sunyi luhu  luhu sun kod'e har ta  kusan gifta shi ya hard'e  kafarta tayi kasa  luuuuuuuu  zata fa?o   jikinsa  , bai san yadda  akayi  ya   tarota  ba aikuwa  hannuwansa duka suka  sauka akan  dukiyar fulaninta  wani irin shock yaji a gabad'aya jikinsa  , idanuwanta ta tsura masa tana kallonsa a tsorace ,  hakan yasa yayi saurin cire hannunsa "ya'akayi hannuna ya kai jikinki "? 
yayi maganar cikin ?acin rai  zuciyarsa  na wani iri  zafi ,mikewa  tsaye yayi  jikinsa na rawa  yana mata  wani  irin  kaskantacce kallo mai razana  duk wanda aka yiwa shi   "ba  tambayarki nayi  ba kika min shiru" ya'akayi  hanuna ya kai wannan banzar jikin naki  "wallahi  ban bansani ba nasan dai san  zaka taimaka min ne  hakan ta faru "
"meye shi hakan ya faru yanzu  ?  tayi saurin girgiza masa kai idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye ta samu guri zata zauna" uban wa zai  kwaso miki kayan ?" ta kalleshi da sauri hawaye na zubo mata . "oh kina tunanin ni ne zan shigo miki da kayan  bayan naje nayi wahala na siyo da kudina ?"
"bance   ka  shigo dashi  ba amman dan Allah ka bawa  mai gadi umarni ya  shigo dashi jikina ciwo yake "ubanki da ciwon jiki  dan Allah malama tashi kije ki kwaso  ,"  sai na maidake kaskantacciyar baiwa a gidan nan  , duk wata babbudewa da cikar iskar  da kike takama  dashi sai na sauke  miki shi  ,ya  zira hannunsa   cikin aljihun wandonsa  ya zaro  wayarsa ya soma danne  danne .... ...."
   Juyawa  tayi  jiki a matukar sanyaye  ta  koma  haraban  gidan ta k'arasa bayan  motar ta bu?e  ta soma fito da caton din monster  fury  energy, lamunsa ne  yana bala'in son  shi  ya kusan carton goma , ta fito dashi ta kai kitchen  ta  dawo ta  ?auki  carton din ruwa  shima  guda goma ,sai kayayyakin  amfani shikafa  manja mangyada   da dai sauransu , gabad'aya ta ha?a  gumi  tana cikin aikin  Safiyya  ta shigo gidan da sauri ta karaso gareta , ta dafa kafad'unta a tsorace ta juyo  ganin Safiyya  ta sauke naunauyen ajiyar zuciya  tana fad'ad'a fuskarta da murmushi "
a she kice ?" ta gyada mata  kai ",abinda zaki saka  mai gadi ya  shigar miki  dashi shine kike yi da kanki  ,"kai  ai babu komai zan iya ai ne shiyasa  "zaki iya ko wannan  mugun mijin naki  ya sakaki , kalli idanunki kamar ma  duka yayi miki , kai bama kamar bane marinki yayi ko? "
"Karki damu dani plz mu shiga ciki ta ?auki  wani kwali  guda biyu muje ko "bari  na tayaki safiya  ta ?auki wani  kwali  tare suka shiga parlou'n basu iske  Aliyu ba ya hau sama  tare suka kwashe kaya  sannan ta tayata ajiye  komai a mazauninsa  ,suna aikin Safiyya  na zargin Aliyu"Allah yana sama yana  kallon abinda Aliyu yake miki shi zai kwatar miki  hakinki   ,kuma inshallahu  nan ba dadewa  ba sai ya girbi abinda  ya shuka  ,mugu azalumi  kawai ,kisna tayi dariya tace ayya Safiyya ki daina fadar haka babu abinda zai sameshi inshallahu , mijina mutumin kirki ne wallahi wannan abinda  ya faru a tsakaninmu ki ?auka qaddarata  ce haka , tayi  tsaki  "lallai yanzu har wani yabonsa kike ? "To ai bashi da laifi wallahi, bana ganin laifinsa hasalima zuciyata sake qaunarsa take "tab gaskiya zuciyarki bata miki adalci ba " ......
Har kusan shida Aliyu bai sauko ba, tare da  Safiyya  suka da dafa soyayyiyar taliya wacce taji salad garbage da carote da soyayyen nama kaza sai dataci sannan  tayi mata sallama ta wuce.
bayan   safiyya ta wuce ya sauko yana mika ha?e da  salati ,ko kallon inda take  bai yi ba , ya zauna ya dauki remut ya kunna tv  ya janyo jakarsa ya fito da  computer  d'insa ya kunna  ya soma duba sakonnin mutanen dake kaunarsa  wasu yayi maida martani wasu kuma ya wuce , ganin haka  yasa  ta mike ta shiga kitchen ta dauko kular   data  zuba  masa abincinsa , ta daura a tire da ruwa da fury  ta  dauko  ta  fito , ta ajiye akan  table din da computer  dinsa ke kai.
ya d'ago  kyawawan idanunshi ya zuba mata yana  kallonta, murumushi tayi masa mai narkar da zuciya tamkar ba ita ce ta gama cin azaba a hannunsa ba  dumple d'inta ya lotsa hakan yasa ta ?ara kyau  "kaci  abinci  sannan ka cigaba da aikin "baza'a ci ba , ki  ?auke  abincinki  yanzu  kafin nayi miki rashin mutunci "dan Allah ni da  kaci  idan ka gama ci sai ka min rashin mutunci ,kalli yadda ka  rame kaima, kaki  kwantar da hankalinka  kaci abinci mai nauyi  kullum daga cake sai snaks ...."
Ai ko   gama  rufe bakinta bata yi ba taji gabad'aya kular  abinci  ajikinta , a firgice  take kallonsa tana kakkabe abincin , duk jikinta  ya  baci da  taliya    cigaba  kakkabe jikinta tai  Allah yasa abinci ya ?an sanyi "bana bukatar komai daga gareki ke ce  mayar abinci  gashin nan kiyita fama , duk ranar da kika sake min tayi  abinciki da bai  dadi    ,dan nasa ba iyawa  kika  yi ba , yawon gantali bai bari an  tsaya an koya ba , sai na kasheki da duka stupid Kawai mai kama da siffar  maciji "...
"duk yawon gantalina dai da  darajata  ka ........"
Saurin katse  maganarta  tayi ta kwasa aguje saboda ?o?arin  mikewa da yayi  "da ki tsaya mana kiga yadda zanyi dake ?aramar mara kunya  ? "Kuma wallahi  ki dawo ki gyara gurin nan  minti goma kacal  na baki  ,ya dauki computersa  ya fita zuwa haraban gidan  ya  bu?e motarsa  ya shiga ya cigaba da aikinsa ....
Bayan ta gama aikin gyara  garin daya abinci  ya 'bata  d'aki ta koma  tayi  wanka ta sako wata doguwar riga milk colour kusan yanayinsu daya data safe data saka sai dai ita wannan  mai karamin hannu  ce ,kuma shara shara dan kana iya hango jikinta bata d'aure gashin kanta ba tabarshi  ya zubo gadon bayanta  ta koma parlou'n ta tsurawa  tv ido  wanda a zahiri ba kallon take ba hankalinta na gareshi  ,
bai shigo parlou'n  ba sai bayan  isha'i  , ?auke kanshi  yayi ya hayewarsa  sama ,yau ma  bacci suka yi kamar yadda suka saba, tana kan gado yana kan kujera yayinda baccin nata ya kasance rabi da rabi tana yi tana bu?e idanunta akan shi ,shi kuwa tsakaninaa da Allah  yake sharar baccinsa  sai tayi kamar ta sauko ta kwanta ajikinsa sai  zuciyarta ta gargadeta a haka har bacci bawon yayi awon gaba daita.."
*****
Washegari
Tsaye  yake a gaban dress mirrow ,jikinsa  sanye da rigar  wanka   yayinda hannunsa ke  rike  da  towel , ya cire rigar wanka ya  goge sumar  kanshi da   fuskarshi  yabi jikinsa  da lotion sannan ya feshe jikinsa da turaruka masu sanyi kanshi  ya tsuke cikin  suit  baki masu matukar da tsada , ya da'ura  agogon  dimond a tsintsiyar  hannunsa ,ya dauki culmb ya  gyara sumar  kanshi  ,yana   ?o?arin ?aukar briefcase  dinsa   ta  shigo d'akin  tana  rausaya wanda ya zame mata jiki  dan  idan basaninta  kayi tun asali ba  ,zaka ?auka yanga take  ,wata hadaddiyar riga ce har kasa ajikinta rigar tayi matukar yi mata kyau sosai kamar dan  ita akayi , abunka ga farar mace sai rigar ta  haskakata sai kamshi take zubawa " fuskarta ?auke da murmushi tace amincin Allah ya tabbata a gareka mijina  barka da Safiyya ,ina ta sauri nazo na shiryaka shine har ka shirya ko ? " ta fad'i hakan tana kallonsa tabe baki  yayi yana jan  dogon tsaki yana tare da d'aga  mata hannu yana mata  gargadi sannan  ya  maida hankalinsa ga kofo  ta kai hannu zata amshi briefcase din hannunsa "bana  bukatar hauka plz   yabi gefenta zai  wuce , tabi bayansa da kallo "ka?an kadan dai tunda ka sauke ra'ayin  barin wutan lantarki a kunne ka siyo kayan abinci yau gashi ka manta baka kulle kofa ba  wata rana zaka canza tana cikin zance zuci  ya dawo d'akin , gyaran murya  taji  har ta tsorata ", dauki  abinda zaki ?auka  zan kulle d'akina  ....."

Mmn sudais
????????????
  CUTAR DA KAI
     ????????
????????????
~TRUE LIFE STORY~
Free Page 4
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da  kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalmi, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ?aya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096,
yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ..."????
.....tsuru  tsuru  tayi kamar  mara gaskiya tana  kallonsa "ki  fito  mana    saboda  baki da manners   kin   wani tsareni  da  wadannan  shegun   idanuwan naki  masu  kama dana  aku  common  get out  ya  fada a fusace kamar zai dauketa da mari  , k'arasawa   tayi  inda  hijab  d'inta  yake  ta d'auka  don   gabatar  da  sallah  ,dan bata  san lokacin  da zai ?auka  ba  kafin  ya  dawo gidan  ."
     cike  da  sanyi  jiki  take d'aga zara zaran yatsun  kafafunta     ta fito  daga  d'akin ta tsaya tana ci-gaba da kallonsa ,ya janyo  kofar da  karfi  ya kulle  ha?e  da  murd'a key  "meye  na wani tsayamin  akai kamar kina bina  bashi ?  "dan  Allah  malama ki  wuce  banason  ganin wannan  banzar fuskar taki   ,kin  wani  tsareni da ido  kamar  zaki cinyeni  ko  zaki  cinye  ni ne?" Yayi maganar a fusace yana zaro mata  idanu ,Tayi saurin  girgiza masa kai alamun  "a'a  "ko  wani  naga  zai cinyeka  ai  sai  inda  karfina ya ..."...
"ya isa  dan  Allah malama  bance ki  qara  da  dogon sharhi ba  dan bana bukatar jin komai  daga  gareki hasalima  na tsani ganinki a kuda dani  bare wannan shrgiyar muryarta ki  ,yana gama  fa?ar  haka ya   raba ta  gefenta  ya wuce yana  d'aga  kafafunsa kamar  baya  son  taka kasa , wani  sabon abin mamaki  suna isa parlou'n  kasa  ya canza wuta  kamar  yadda ya saba a tun farkon zuwansu  "bance  karki  yi  changeover  ba , kiyi   duk yadda kike so   jikinki  ne zai gaya  miki   idan na dawo ,ya kama hanya  ya  fita yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa ."
  Naunayen  ajiyar  zuciya ta  sauke  da karfi tana dafe  goshinta  "daman haka  Aliyu yake ?"  "daman zai  iya rashin mutunci  da rashin imani haka ?" shiru  tayi  tare da  kwanciya  akan doguwar  kujera , ta shiga tunanin  rayuwa  idan akace  mata  akwai wata rana  da zata zo rayuwarta  ta  dawo  haka zata  karyata ,sai gashi  tazo  mata  fiyye da  tunaninta, nasan halinsa  tunda na zauna dashi  ban ta?a  samun matsala dashi  ba ,bai ta?a  aikata min laifin komai ba,  yasan duk abinda  zai yi  ya faranta min  rai  , idan    nace   wannan abun   baki  ne  ,to muradi   zai ce  bakinkirin ne , bai ta?a   sa'bawa umarnina ba, duk  abinda  ya  biyo baya   daga gareki ne kisna ,  ba  kuma zan lamunta  ba ......" wannan shine maganganun mahaifiyarta a lokacin da zasu baro Nigeria .
  ta sauke numfashi "zan  d'aure  mummy ,Kuma  zan sanyawa zuciyata hakuri sannan zanyi ?o?arin  na nasan  yadda zan  janyo hankalinsa gareni."
Shi  kuwa Aliyu   tunda  ya bar gidan  zuciyarsa  a cukunshe  take   da  bakinciki mara misaltuwa , ya kasa manta  abinda  tayi  masa  a baya  "ka manta  komai   aliyu  ko dan  darajan  iyayenta, sunyi  maka  komai arayuwa  , mutun  kan ci daraja  wani  nasa mai imani  inji cewar wankakkiyar  zuciyarsa "surukina  kuma d'ana  muradi  , kai kasan  halakar qaunar  da take tsakanina  da kai , ina sonka fiyye da komai a rayuwata ,ina rokon   alfarmarka    ka  kasance  tare da kisna   muddin  rai , kasan  yadda  nayi fama daita  a can  baya  ,gashi a karo  na  biyu zata dawo hannunka , wannan  abu bakaramin  faranta min zuciyata  yayi  ba , bazan iya  kwatanta maka  farinciki  da  nake  ciki ba , ada ta kasa fahimta komai   ,amman a yanzu ta fahimci komai   zaka ji dadin   rayuwa daita, nasan  kai  mutun ne da d'aukaka   ko matsayi bazai  ta?a  canzaka ba, ada  tayi   kuskure , a yanzu  kuma  tana son gyara  kuskurenta na baya  kayi hakuri ka bata dama  " nasihan mahaifiyarsa  kuma mahaifiyar  kisna  kenan gareshi  har ya isa ma'aikata  tunanin magangagun  mummy ne  ke  yawo a cikin kwakwaluwarsa "

"Wunin  ranar  kwance tayi sa  tana saka da warwara , sallah ne kawai  ke  taddaita, yamma  nayi  ta shiga Kitchen  domin  girka  abinci  dare , bubbud'e wundunan Kitchen din  tayi domin taga  hasken  aiwatar  da aikinta ,abincin da tasan yafi so shi tayi ?o?arin d'aurawa ,  tuwon  shikafa   da miyar  wake   "Yau  mijina  zai  ji dadi  abinda  yake so zan  girka  masa tayi maganar a kasan zuciyarta  , shiru tayi  bayan  ta d'and'ana miyar ,   jikinta yayi sanyi sosai saboda  tuno  baudadden   halinsa da tayi, "ban  sani  ba  ko  zai ci abincin  nan  ko bazai ci ba ? " Tayiwa kanta tambayar ..
   "komai  nayi  masa sai ya  gwasaleni ya kama fa?a da  zagina alhalin yasan banason daya daga ciki  , ya zakiyi  kisna haka  zaki  cigaba da hakuri  dashi har zuwa  sanda Allah  zai  sauko miki  dashi , ta gama komai a tsanake  ta shirya dinning  ta shiga bayin dake manne da parloun tayi wanka ta sake maida kayan jikinta data cire  tazo ta   raku'be    guri  daya tana jiran  dawowarsa   ".
*****
Karfe  takwas  daidai ya shigo  gidan  a gajiye  hannunsa  rike  da jakar laptop  d'insa , ya zaro wayarsa  ya kunna sannan  ya  d'aga idanunshi  da suka koma ja , ya  sauke  akan abun canza  wuta , ya canza  haske  ya haska  gidan gabad'aya  sannan  ya soma  daga kafafunsa  da kyar saboda kanshi dake masa  wani aza?a??en ciwo  , ta mike da sauri ta  karaso  gurinsa "sannu da  zuwa  zata amsa jakar hannunsa   ya watsa  mata  wani  mugun kallo batare  daya  amsa mata sannu  da zuwan data yi masa  ba , ya wuceta ya ajiye jakar computer dinsa  akan kujera  dan akwai aikin da zai yi a daren , ya  furzar da iska  kana   a hankali ya nufi step yana takawa ?aya bayan ?aya  cikin izza tamkar wani jinin sarauta ."
tsayawa  tayi cak tare da  bin  bayansa  da kallo  tana tunani abun yi  "aliyu na tozartata dayawa  yana wulakantata tamkar bai san daga inda ta fito ba   ,ada can  baya ba  haka  yake  ba, ba haka tasan shi ba ,ta ina zata fara irin  wannan rayuwar da yake muradi daita?  bazata  iya ba  gaskiya ,dan  haka  duk  yadda zatayi  sai tayi ta shawo kanshi su zauna lafiya , sannan  zata  lalla'bashi yaci  abincin data dafa masa koda kuwa  zata samu  tukuncin duka da mari  ne  daga garesa zata d'aure   tayi  iya kokarinta,  bayansa ta biyo  da hanzari  koda ta shiga d'akin yana  zaune  a kan doguwar  kujera ya rike kanshi  dake sarawa  da duka  hannuwansa ,sosai zuciyarta  ke bugawa da ganin yanayinsa ,ta karaso  garesa  ta kudurce aranta komai zai faru  sai dai ya faru amman  zata jure duk wata  azaba daga garesa  , tsugunawa  tayi  a gabansa ta zuba masa narkakkun idanunta  tana jin zallar qaunarsa  na ratsata "meke  damunka aliyu ko baka  da lafiya ne ?"  tayi masa tambayar hawaye nabin kuncinta ji take duk duniya babu abinda take qauna sama dashi, ta kai hannu  zata  riko hannunsa yayi saurin fixge hannusa    yana jan tsaki "karki  ta?ani  wai dan  Allah me yasa kike son kawowa rayuwata hari  ne  alhalin kinsan bana son kusancimu tare ?"   shiru tayi  tana ci-gaba da  kallon yadda yake  motsa lip's d'insa " kamar baya son magana komai nashi a natse kuma a yangance , "Baka  son kusancimu gashi  kuma  Allah ya had'amu  tare ,kuma ina Sa rai mutuwa ce zata rabamu ......."
    Mtsssss ya ja dogon tsaki   yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa "wannan  kuma damuwarki  ce dan Allah ki  fita daga d'akin nan  banason  damuwa  kuma bana son  Kallon fuskarki  yana  gama fadar haka  ya mike  ya soma cire kayan  jikinsa yana ajiyewa  a saman  gado bata daddara ba  ta dinga   bin kayan daya bayan daya  tana ?aukewa  tare da kai su ma'ajinsu , ya saura daga shi sai  boxcer  ya janyo towel ya da'ura a wuyansa   zai  shiga bathorrom tayi saurin  rungumeshi  tsam  ta baya "ka  bar zuciyata da rashin sonta  da bakayi dan  Allah , ka daina hukuntani  haka  ya Aliyu ,ka tausaya min idan kana careles dani zuciyata zata iya bugawa".
"kece  da kanki kika *CUTAR DA KANKI* "nasani   wallahi  nice, nasan nice , na *CUTAR DA KAINA*  nasan ka d'and'ani  damuwa mai yawa a tare dani , amman  ka  yafe min abinda nayi maka  ,nasan nayi kuskure , dumin jikinsa ya ratsata tayi saurin runtse idanunta  "jikinka da  zafi ya Ali  , "da alamun baka da lafiya ,  juyowa yayi  tare daita ajikinsa suna fuskantar juna  sannan ya  zareta a jikinsa ya shige bathoroom batare daya bata amsar tambayarta ba ".
Bathtube  ya shiga  yai having  shower ya dade yana  sakarwa kanshi ruwa   tukunna ya fito tana  tsaye  tana jiran fitowarsa , yana goge jikinsa ta karaso  ta soma  taya shi ",dakata dan Allah malama   bana  son kina ta'ba  min jiki   "amman da....."enough I don't want to hear anything from you  ,cire hannuwanta tayi ta ajiye ?aramin  towel a mazauninsa  ta ja ta tsaya rungume da hannuwanta duka a qirji tana kallonsa  yana  goge ko'ina ajikinsa ya d'auko kayan shan iska  ya saka   farin wando  da farar  riga , ya fesa turare mai sanyi kamshi , ya zo ya  wuceta  ya  sauko zuwa falon  kasa ta sake biyo bayansa da

Please Login or Register in order to submit comment