Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kyakkywar fuskar da kike takama dashi ya karasa maganar yana kwafa da kyar ta samu ta sauke ajiyar zuciya da karfi ta rike wuyanta da har lokacin take jin rad'ad'i wani sanyi taji yana tsiyoyawa daga hancinta ta kai hannu ta tabo tana dubawa jini ta gani "ka?an kika gani muddin bazaki fita daga rayuwata kiyi rayuwarki ba irin wannan izayar sune hukuncinki ,kiyi rayuwarki nayi rayuwata shine zaman lafiyarki a cikin gidan sabanin haka kuma kinsani ". yana gama magana yayi parlou'n kasa ya kwanta yayi pillow da hannunwansa duka ya daura ?afarsa daya akan daya yana girgizawa baya jin zai iya fita zuwa ko'ina saboda zazza?i da yake ji itama kwanciya tayi akan gado wasu zafafan hawaye na bin kuncinta "na *cutar da kaina* me yasa nayi masa abinda nayi ?"Me yasa banji maganar Samir ba a lokacin da yake nuna min illar abinda nake ? me yasa baji maganar aunty Aysha ba "? yar'uwata ta fada min gaskiya tayi min nasiha ta fada min wata rana zanyi dana sani gashi ina yi ..."
" mai yasa na biyewa aunty Afra gashi ta Kai ni ta baro ta barni Ina girban abinda na shukawa zuciyarsa ni ?aya , kuka take sosai har da shesheka ta mike zaune tana tunanin abinda zai ci "ko kinyi masa tayin abinci bai zama lallai yaci ba zuciyarta ta fa?a mata haka "amman ai bashi da lafiya ? ta yiwa zuciyarta tambaya "ki rabu dashi har zuwa sanda zai huce umarnin zuciyarta tabi ta koma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya tana tunanin kalmamin daya fa?a a sakwanin da suka gaba "babu soyayyar kowa a cikin zuciyarsa kenan itama nawal din ba sonta yake ba ? ba sonta yake ba zai aureta yana duk sonta "ina ma zai zamo da gaske babu soyayyar kowa a zuciyarsa kamar yadda ya fada haka ta dai dinga saka da warwara a hankali har bacci ya ?auketa ."
sai kusan karfe ?aya na rana ta farka ,taji fuskarta tayi mata nauyi ta zuro kafafunta ta sauko ta tsaya gaban mirrow gabanta ya fadi ganin bakinta da hancinta sun kumbura har ma da idanunta girgiza kai tayi ta shige bayi tayi wanka ta d'auro alwala ta fito ta sauya kaya zuwa doguwar riga pinky colour tayi sallah ta sauko kasa dan shiga Kitchen mamaki ganinsa kwance tayi hannunsa daya da abun qarin ruwa yayinda likita ke gabansa yana ?o?arin bashi kulawa daga gefe guda kuma nasir ne zaune yana kallonsa sam hankalinta bai kai ga nasir ba har ta karasa saukowa idanunta na kanshi kunnensa manne da waya daga jin yadda yake wayan tasan da Samir ne ,da sauri ta karasa zuwa inda yake kwance jikinta na rawa "sannu a she zazza?i yayi karfi haka ?" sannu Allah ya baka lafiya ina ke maka ciwo ? "Ya tsani jin sautin muryarta duniya da lahira " kai hannunta daidai saitin wuyansa tai ,ta shafa zafi taji ya ratsa tafin hannunta shi kuwa saurin runtse idanunshi yayi yana jan tsaki sai dai ya kasa dakatar daita saboda ya badamasi daya amshi wayar a hannun Samir , kanshi ta d'aga ta d'aura a saman cinyarta tana shafa sumar kanshi "doctor meke damunsa plz "?"Fever ne amman nan da zuwa wani lokaci zai ji sauki tunda anyi masa allura ta cigaba da shafa sumar kanshi tana sauke numfashi"sannu Allah ya baka lafiya gaba-daya duk ta rud'e shi kuwa wani tuttukin bakincikin ne ya tokare masa kahon zuciya, yana gama wayar yace " ke maza ki tashi ki bar nan.." yayi maganar a dan zafafe , babu mutsu ta d'aga kansa ta maida kan pillow ta Mike tsaye sai lokacin taga nasir dake zaune , jiki a sanyaye ta gaishesa ya amsa mata cikin sakin fuska "ya gida kisna ? "Lafiya ta furta masa a hankali tana tambayarsa safiyya yace" tana gida zuwa anjima zata zo, ta gyada masa kai sannan ta nufi hanyar Kitchen har ta kusan shiga likita yace "madam akawo masa abinci ya ci ya sha magani .."
"No likita ba sai naci komai ba ka bari na sha maganin kawai "ba zai yiwu ba ,idan ma bazaka ci ci abinci ba kasha ko ruwan zafi ne , ki kawo masa tea "okay ta fa?a tana karasa shigewa kitchen ,bayan kamar second biyar ta fito hannunta rike da cup ta karaso gabansa ta durkusa wanda zuwa lokacin ya mike zaune "ga tea "ki ajiye a kaina mana " ya fada a zafafe yana nuna kansa "ban ta?a ganin sakariyar dakikiyar mace irinki ba komai baki iya ba ". ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ajiye cup din akan table din dake gabansa ta sake juyawa ta koma kitchen zuciyarta na wani irin zafi .."
A tsanake ta fara ha?a priderice tana cikin aikin safiyya ta shigo bayan ta gaishe da Aliyu tare da yi masa ya jiki ta shiga Kitchen saboda jin motsin kisna da tai "har kin karaso? Kisna tayi magana tana kawar da fuskarta gefe dan bata son safiyya ta fahimci wani abu amman sai data fahimta ,ta dawo gabanta ta tsaya tana kare mata kallo fuskarta dauke da tambaya sake kawar da fuska kisna tayi tana juyawa gurin wanke wanke Safiyya ta biyota tare da juyo daita suka fuskanci juna "me ya samu fuskarki haka naga ta kumbura ?"
"babu komai ta bata amsa atakaice" babu komai fa kikace ko dai uncle Aliyu ne ya 'bata miki fuska haka "? tayi saurin girgiza mata kai "ko daya faduwa dai nayi a bayi d'azu da safe ta bar gurin ta karasa jiki frizer ta bu?e ta dauko naman kaza tana juyowa taga safiyya a gabanta tana kallonta idanunta sun cicciko da ruwan hawaye kafin kace me har sun fara zubowa "meye abun kuka babu komai fa faduwa nayi "babu wani faduwa da kikayi wallahi kina dai boye min ne kawai, amman dagani fuskarki mari ne" ta karasa maganar cikin rawar murya , "tam shikenan kije parloun ki jirani ina zuwa ta fa?a tare da ra'bawa ta gefenta ta wuce duk yadda safiyya take son su tautauna akan lamarin zamanta da aliyu kisna taki, aikinta kawai take tana dauko mata wani zance dabam , daman kuma ita ba mai yawon magana bace ."
A parlour ma magana nasir yake wa Aliyu "kayi hakuri Aliyu hakuri ake da mata haka kowa yake fama dan Allah ka manta komai sannan ka daina dukanta, da iyayenta sunsan irin wannan zaman zakayi daita da basu sake baka ita a karo na biyu ba , ka saka wa zuciyarka damuwa, kullum kana cikin damuwa da zubar da hawaye nasan kana son kisna duk da baka ta?a furta min hakan ba amman wallahi ko rantsuwa nayi bazan yi karfafa ba kana sonta kuma so mai tsanani laifinta ne ya hana soyayyar tasiri ".
"zaka yi kaffara kuwa abdul-nasir saboda ban taba sonta a cikin zuciyata ba ,muyi zama ne ba irin zaman da zamu so juna daita ba, nasir ya karaso inda Aliyu yake zaune ya dafa kafad'ansa "naji amman kayi hakuri dan Allah taci darajan iyayenta ka saukaka mata ba dole sai ka sota ba amman ka daina wulakantata kana dukanta akan abinda bai kai ya kawo ba ,kalli yadda ka mayar mata da kyakkyawar fuskarta akan ta rike hannuka kawai ....."
Aliyu ya ja tsaki ka?an yace "gaskiya nasir ka cika min ido dayawa ,nasir yayi dariya mai nuna cin nasara akansa yace "na gode duk abinda zatayi ka barta dan Allah ka daina dukanta kisna da safiyya suka karaso parlour'n hannunsu rike da manya manyan kuloli suka ajiye akan dining tare da plet kisna ta karaso gaban Aliyu ta na cewa "ranka shi dade abinci yayi ready nasir yayi dariya yace "an gaishe da uwar gidan Aliyu sannu da ?o?arin zubo masa kawai ki kawo masa nan "murmushin jin dadi tayi taje ta zubo masa ta dawo ta ajiye a saman table din gabansa taje ta dauko masa lemunsa na gado da ruwa ta dawo nasir ya mike ya koma mazauninsa "sannu yaya kake jin jikin naka yanzu"? Yayi mata banza tamkar ba dashi take magana ba , ta dauki plet din abinci ta dibo had'ad'd'en priderice ta kai bakinsa "kallon cikin kwayar idanunta yayi yana jin zallar ?acin rai "ka bude baki kaji , kaga baka da lafiya rashin cin abinci yana bari ciwo ya samu matsuguni ajikin mutun".tayi maganar tana lumshe masa idanuwanta , fuskarta data dan kumbura yake kallo ta dan bashi tausayi kadan "ka bude baki " ta sake maimaitawa "jikinsa a sanyaye ya bu?e ba dan yaso ba ta soma bashi abinci abaki spoon uku yayi ya kawar da kanshi, ta ajiye plet ta tsiyaya masa lemun ta kai bakinsa ya bu?e ya sha ta jiye cup din, kallonsa tayi taga gumi ya ?an tsatsafo masa a fuska tasan gumin abinci mai zafin daya ci ne, tasa gefen rigarta ta soma goge masa "ba muna da towel ba "? Yayi maganar muryarsa can kasa kamar baya son magana , ta gyada masa kai sannan ta mike cikin sauri ta hau sama."
bayanta safiyya tabi da kallo dan gabad'aya dawowa tayi kamar wata wawiya ta kasa zubawa mijinta abinci tana kallon kisna dake rawar jiki akan mutumin da bai san darajanta ba ,ko cikakken minti biyu batai ba ta dauko towel ta dawo ta zauna kusa dashi zata goge masa ya amsa "zanyi da kai numfashi ta sauke ta cigaba da kallonsa ,yadda safiyya ke Kallonsu haka nasir ke Kallonsu kisna ta bala'in burgeshi kuma yaji dadin yadda ta sauya ta rusunar da kanta ta zubar da makan yakinta domin kyautatawa mijinta sai gurin yamma su nasir suka bar gidan ."
A cikin mota safiyya ta waigo inda nasir yake zaune yana tuki "sweet heart Wai me ka fahimta yau ne a gidan aliyu "? "Kamar me kenan ?shima ya tambayeta yana sake maida hankalinsa ga tukin da yake "kamar duka yayiwa yarinyar mutune fa , wallahi ban ta?a tunanin haka daga Aliyu ,ban san haka halin aliyu yake ba ,mutumin da nake ganin ya fika kyawawan halaiya ,mutumin da nake ganin babu kamarsa a fadin duniyar nan ,mutumin da nake kismawa a raina duk matar data sameshi a matsayin miji tayi sa'a duniya da lahira, mutumin da nayiwa kanwata kwadayin aurensa saboda kyawawan halaiyensa yau shine yake musgunawa matar aurensa kuma uwar ya'yansa why nasir "?
"Duk abinda kika lissafa akan Aliyu gaskiya ne domin kuwa Aliyu mutumin arziki ne mutumin Karki ne ,muyi karatu dashi a kasar nan tunda muka zauna bamu ta?a samun matsala dashi ba, mutun ne na gari bai ta?a aikata laifin komai ba ,mutun ne shiru shiru wanda yasan darajan dan adam da duk wani hukunci da'aka tanada domin mu'amula ."
"ita kuma kisna da kike ganinta yar ta'adda ce kamar yadda duk wani dake cikin danginsu ya san da haka ,duk wannan tashin hankalin da take fuskanta ita tajawa kanta da taimakon Afra ,wannan halin da yake nuna mata tayi masa fiyye dashi , wallahi idan na fa?a miki abinda tayi masa har duniya ta nade bazaki sake ganin kima da girmanta ba yanzu ma wannan ladab din da kikaga tayi na wuya ne , saboda taga babu wanda zai iya rufawa rayuwarta asiri sai shi .....
" dan haka ki daina magangun bazan akan abinda baki sani ba ,naki kiyi kokarin kwantar mata da hankali tunda yanzu tayi nadama ki nuna mata ta cigaba da hakuri wata rana zai dawo mata yadda take so . numfashi Safiyya ta sauke tace "kenan shiyasa bata son ana fadar laifinsa saboda tasan itace bata da gaskiya? "eh ya bata amsa a takaice dan duk ya gaji da tammayoyinta "shikenan zan tayata da addu'a Allah ya daidaita tsakaninsu "ameen addu'a mai kyau kenan ."

Mmn Sudais
????????????
CUTAR DA KAI
     ????????
????????????
Free Page 6
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalmi, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga bukatar  siyan ?aya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...????
"Tunda  nasir  da matarsa   suka  bar  gidan  ta bashi  magani  ya sha  ta kwantar da  kanshi   akan  cinyarta  ta  d'aura  hannunta ?aya a qirjinshi   tana shafawa a hankali  zuwa  fuskarsa  tana  yi masa sannu tana jin kamar ta cire masa ciwon ta dawo dashi kanta  ,   idanunshi ya runtse gam  yana sauke numfashi  sama sama batare  daya amsa mata ba "
    
  "wani iri  ya dinga ji a gaba-daya  sansar  jikinsa  a lokacin daya tsinci  laulausan  tafin hannunta  a saman  qirjinshi tana shafawa ga kamshin  turaren jikinta dake   gauraye  dana parlou'n duk  sun  buwayi  hancinsa , itama  hakan  ce ta kasance   gareta kamshinsa  ya buwayi hancinta   ji  take tamkar su  kasance   haka  har abada  , sake  runtse    idanunsa  yayi  sosai har  bacci  mai nauyi yayi nasarar  d'aukarsa a cikin  mintunan  da ba su wuce  goma  ba, ya d'aura laulausan  hannunsa a saman  nata  yana sauke numfashi  a hankali .
kyawawan  idanunta ta zuba   masa  tana kare masa  kallo tsab  wani  irin yanayin  ta dinga ji a jikinta, da  kyar take janyo  numfashi  tana fesarwa , dayan hannunta  ta  kai gefen  wuyansa ta shafa   har lokacin jikinsa  da sauran hucin  zafi  ,kanta  ta rankwafo ka?an   daidai fuskarshi tayi  shiru  tana sha?ar  numfashinsa  ,abinda ta tsani shakarsa ada shine yanzu ya zama muradin ranta , ko iya sha?ar numfashinsa ka?ai ya bata dama ya isheta k'arasa sauran rayuwarta  da tai saura a duniya .
   " a hankali take  addu'ar akan  Allah ya sausauto  mata da  zuciyarsa tare da fatan samun  soyayyarsa koda bai kai wanda take masa ba  , kusan minti talatin tana zaune tana kallonsa  yana sharar  bacci da alamun   kamar akwai maganin bacci acikin magungunan daya sha dan ko daga hannunsa  bai iya wa  , sosai suke musaya numfashi juna batare daya sani ba , mutuwar da jikinta yayi ne yasa ta sake kusanta kanta dashi har lip's dinsu na had'uwa da juna  ,
tsawon lokaci ta ?auka  tana zaune tana kallonsa tana sha?ar
numfashinsa tana jin kamar ta kamo lip's d'insa ta tsotsa  ko ka?an ne ,dan  tana kwadayin sake jinsu cikin bakinta sai dai tsoro da tsananin  fargaban  abinda zai faru idan ya bude idanunshi  ya kamata ya  hanata aiwatarwa."
 
   da kyar ta daidaita  natsuwarta cikin sanyi jiki ta  zare jikinta ta d'aura  kanshi akan pillow  ta hau sama ta d'auko  bargo mai taushi ta lullu'beshi  sannan ta koma  d'aki  ta shiga bayi ta tsalla wanka ha?e da alwala ta fito ta goge jikinta ta  bu?e wordrobe ta ?auki  wasu kayan ta canza tayi sallah ta sake gyara  ko'ina a d'akinta ta  d'auko turaren da  take amfani dashi ajikinta ta feshe  ko'ina , duk inda tasan  yana  kwanciya  a cikin dakin sai data fesa turarenta  har cikin bayi, ko'ina  ya  ?auki  kamshi turare  sannan ta ajiye kwalban  turaren ta sake dawowa  parloun."

A  gabansa  ta tsaya tana kallon  yadda yake sauke numfashi  yayinda a hankali  zuciyarta  ke  bugawa tamkar  zata fasa qirjinta ta fito waje    ta ?auke  idanunta akanshi sakamakon  wayarsa dake  ringin  cikin  sanyi jikin  nan nata ta  kai hannu ta ?auki wayar tana dubawa  sunan Samir ta gani   yana yawo akan  screen  ?in  wayar da  sauri  ta d'auka "hello ya samir  barka da  warhaka" ?
"Yes my  lovely sweet  sister   ya  kike   ya  mai  jiki fatan ya samu sauki"?
"Alhamdulillah ya samu  sauki gashi nan  yana bacci  ,"jikin dai nashi da  sauki sosai  ko"? "da sauki  yaya  mummy  ta amshi wayar "kisna  ya  jikin d'ana "? kisna ta kwa'be  fuska  kamar zatai kuka  "mummy ai ni fushi nake dake tunda na sauka a kasar nan baki kira kin nemi ba kullum sai dai kiyi waya da muradi   "kinga  sarkin shagwa'ba  ajiye  batun fushi nan muyi maganar jikin d'ana  , ya jikin dana ? "ya ji sauki  doctor yazo ya dubasa  Kuma yace da zarar  ya tashi a bacci zai sake  samun  sauki yanzu haka bacci yake" "okay  naji dadi sosai dan nasan wannan mayatattacen ciwon kan nashi  zai  iya kai shi ga kwanciya asibiti Allah dai ya bashi lafiya ,ya dai zaman naku fatan  dai babu wata   matsala babu  damuwa  "?"Yes my sweet mummy babu  damuwar komai  , muna zaune lafiya  dashi ,d'anki  yana matukar  bani kulawar data dace , baya son ganin  ?acin raina  ,duk  abinda  nake so shi  yake min  ina jin dadin zama dashi sosai  ,ko'ina zashi idan ba gurin aiki ba tare muke  zuwa  ,tare muke zuwa  tsiyaya , babu abinda  zance miki   mummy  sai godiya Allah ya qara nisan kwana na gode bisa ?o?arinki  gareni, hakika samun uwa irinki a waannan duniyar  tamu da kamar wuya ta karasa maganar tana sauke   numfashi da ajiyar zuciya a tare ".
dariya mumuy tayi  tace "iye  lallai kin zama yar gatan haka  muradi   yake ji dake ni ina can  cikin damuwar yanayin zamanku , duk da nasan zaki samu kulawa  fiyye da haka daga garesa," muradi yaron kirki ne ya fita dabam acikin  mutane. " "a saninki da tunaninki  ba amman wannan dan naki mugu a duniya babu kamarsa tayi maganar a kasan zuciyarta tana jan numfashi da kyar .
  "hello kisna  kina jina "?
Numfashi ta sauke da karfi  tace "ina jinki  mummy , maganarki  haka  ne samun  mai kyawun hali irin nasa da wuya  ta fada tana dariya.
  "ki zauna lafiya da mijinki kiyi  masa  biyayya kiyi masa duk abinda kika san zai faranta  masa, yanzu muna wani zamani ne da ake   lalla'ba maza  bare miji irin naki mai tsananin tsada da   samun  irinsa  da  wahala, shiyasa kikaga bana son ki bar karkashinsa,  dan Allah   ki zauna lafiya da mijinki , ki rike shi amana sannan ki rike sirrin gidanki nasan kina da zurfin ciki ki  ?ara  akan  wanda nasanki  dashi  muma inshallahu  zuwa karshen wata  ko  sabon wata  zamu  shigo Cairo".
wata   irin  qara  ta  saki na  farinciki  tare da furta  "dan  Allah mummy nah ?"inshallahu  kuwa  "kai  amman  mummy   naji dadin  wannan maganar sosai  kamar ance ta d'ago  idanunta  inda yake  kwance  taga idanunshi  fesa  akanta ya  bala'in  ha?e rai  tamkar  wanda aka aikowa  da  sakon mutuwa  tunda ta soma wayar  ya  bude mayatattun  idanunshi akanta  rungume  da hannyensa a  qirji yana kallonta, duk maganarta  babu wanda bai yi  nasarar shiga kunne  shi ba ,haka  nan ya  tsinci kanshi da jin dadin  abinda ta fad'awa mummy  ko babu komai ta rufe wani  sirri  dake tsakaninsu   "lallai  kisna ta  canza irin canzawar da'ake  so, ina ma zai iya  daya  bata  wani gurbi a cikin  zuciyarsa kamar yadda ta bukuta  sai dai ba  zai  iya  ba  dan shi yanzu  burinsa  bai wuce  ya   auri   nawal  ba  saboda  zamansa haka without  having sex ya soma   damunsa , kuma nawal itace matar data fi dacewa  da rayuwarsa duk  da  bai tsananin sonta  amman haka zai aureta ".
Idanunshi  dake  tsaye kyam  akanta  yasa gaba-daya  ta rud'e , ta gigice a matukar tsorace tayiwa  mummy  sallama  ta katse kiran ta mike tsaye jikinta na rawa  ta  k'arasa  inda yake kwance  ta ajiye wayar a inda ta ?auka   taja ta tsaya   gabanta na faduwa da matsanancin karfi  "ka....kayi  hakuri dan Allah  mummy  ce ta kira  kana bacci  shine  na  ?auka  tana gaisheka " ta  karasa maganar a matukar  tsorace  ."
?auke  kanshi  yayi batare da ya ce komai ba  yana  ?o?arin  mikewa tsaye  , tayi  saurin  rikoshi  ta karasa mikar dashi   tsaye ta sanya hannuta  daya a kugunsa  sannan   ta zagaye   hannunta   ?aya  a  wuyansa  wani irin shock suka  ji a tare ,  a hankali
suka  fara  takawa suka    nufi   hanyar  sama  akan step  taji ya dafa kafad'anta  sosai ?an ya samu  damar  takawa ta tsaya  cak  tare da    waigowa  a tsorace suka ha?a  ido fuskarsa babu walwala ya d'age mata girarsa ?aya alamun tambayar kallon mai take masa ?  kawar da idannunta  tayi da sauri ,yayinda shi kuma ya daga ?afarsa ?aya  da kyar wani sanyin dadi taji yana ratsata  kamar wata  wawiya  ta dinga daga kafafunta har suka shiga daki , kai tsaye   bayi ta nufa  dashi saboda tasan bai  yi Sallar magrib ba ga  isha'i ta karato ta taimaka  masa yayi alwala suka fito ta kaishi gurin sallah "ka zauna kayi  sallah  a zaune saboda  jikinki babu kwari".
banza  yayi mata ya tsaya  bisa kafafunsa ya soma  tada ikama ita kuma ta koma falon  kasa ta  gyara ko'ina ta shiga  Kitchen ta wanke plet din da suka yi amfani dashi ,ta goge ko'ina  dan tasan halinsa da rashin son kazanta sannan  ta  dawo parlou'n  ta  tattara  kan magungunsa ta dawo sama  wanda zuwa lokacin  har sallar  isha'i yayi  yana ?o?arin tashi ta shigo  d'akin  ta karaso da sauri  ta taimaka masa ta kwantar dashi akan  gado  tana yi masa sannu "sallar isha'i tayi ta dawo   gefen gadon ta zauna   tana  sake jin tausayin  kanta dan batasan  ranar da zata fita daga  cikin wannan kangin  damuwar ba, ganin  sai  faman mika yake  yana juyi  alamun  jikinsa  yayi masa  tsami , ya juya a hankali  ya kife yayi  ruf da ciki  ,hakan  yasa ta hau  gadon sosai, hannunta na tsananin   rawa ta kai bayansa  ta fara shafawa a hankali   jin   bai yi magana  ba , yasa ta canza salo  zuwa massaging   a  natse  ta dinga  mammatsa  masa sansar  jiki   tun daga  bayan  wuyansa da tsakiyar bayan kanshi har zuwa    kasa   gurin gwiwowinsa  zuwa kafafunsa  da tafin ?afarsa  "ya salam ya furta a kasan ransa  dan sakonta yaje masa inda bai yi expecting  ba , jin reaction din jikinsa ya fara sauyawa yayinda zuciyarsa ta fara bugawa da  tsalle na kaiwa  kololuwar sha'awa , cikin dakakkiyar muryarsa  yace  "stop......"
ya  fada tare da sauke wani  wahalallen numfashi."ka bari nayi maka  massagin zaka ji dadin jikinka ya juyo a zuciye   cikin rashin  sani  gaba-daya ya zubo jikinta  sai  gashi a saman ruwan  cikinta  ita kuma tana  kasan shi hannunta duka a saman qirjinsa daidai kan nipple's d'insa ,  ya tsura mata idanunshi  tare da   ha?e rai , a tsorace ta  cire hannuwanta ajikinsa  ta  zuba masa ido tana kallonsa , ya  lumshe idanunsa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa kusan minti goma suna kallon juna tare da sha?ar numfashin juna  batare da yayi  magana  ba,  ya
kai hannu ya ?auki pillow yayi  cilli dashi kasa  ya  lalubo bargo ya jefar sannan ya  gyara kwanciyarsa ya lullube jikinsa tun tana ganin motsinsa  har  bacci yayi awon  gaba dashi ta lalla'ba ta d'auko bargo da pillow ta kwanta a dayan  gefen , ta lullu'be jikinta ta runtse idanunta itama bata ?auki dogon  lokaci ba bacci ya ?auketa ..
Washegari
A hankali ya  soma bu?e idanunshi  kawai ya jishi  ajikinta  da sauri ya k'arasa  bu?e  idanunshi yaji  ?afarsa  akan kafafunta ya kanainayeta yayinda hannunsa daya ke saman kirjinta daidai dukiyar fulaninta da sauri ya cire hannunsa da ?afarsa ya mike tare da matsawa baya ,yaji kamar ya sakar mata mari dan bakinciki ," shiyasa fa  baya son su kwanta guri daya waya sani ma ko yayi wasanin da jikinta  "?
"Oh my goodness yarinyar nan tana son damun rayuwata saukowa yayi ya shiga   yayi  alwala yazo yayi Sallah  ya koma  kan doguwar  kujera ya kwanta bata  tashi ba sai gurin tara wanda wayarsa ce ta tasheta a bacci,  ya kasa tashi ya ?auki  wayar har ta katse wani kiran ya shigo  ta sauko  ta dauki wayar ta mika masa ta shige bayi "hello my  love  aka fa?a daga can bangaren da kyar ya iya bude bakinsa yace  "nawal ya kike "?
" Sorry na tasheka a bacci  ko ya karfin jikin "?"Naji sauki ya za'a yi nazo na ganka ina son ganinka plz naga yanayin jikinka  "
"Karki  damu zaki gani dan  nima ina  son ganinki akwai abinda nake son muyi magana akai  yana cikin

Please Login or Register in order to submit comment