Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maganar kisna  ta fito daga bayi gabanta ne ya shiga  faduwa da karfi  ko ba'a fa?a mata ba tasan  da wacce  yake  magana "?"Karki damu zaki ganni nima ina son ganinki ta sake maimaitawa kanta na  kanta kalmar  ,  ta dawo kusa dashi ta durkusa bisa gwiwowinta tana kallonsa kasancewarta  agurin bai sa ya katse kiran ba sai ma cigaba da wayarsa da yayi daga karshe yace" me too tasan duk yadda akayi  kalmar  i love You aka furta masa idanunta yayi raurau da hawaye "dan Allah  kace ka  yafe min laifin dana maka sannan ka   sake bani dama  Ina sonka Aliyu mai yasa bazaka soni ba "?
"Bani da ra'ayin  sonki , ko yin wata muamula dake ,ki rayu dani cikin wannan rayuwar ko ki rabu dani ki auri wanda zuciyarki ta kafu  akan  soyayyarsa tun farko ba damuwata bace  , wannan da kika  ji muna waya  daita sunanta nawal  nasan kina da labarinta itace matar da zan aura  sai ki shirya zama daita idan fa zaki  iya idan bazaki iya kofar gidan Aliyu a bude take  ". yana gama fadar haka ya juya mata baya ta mike tsaye hawaye ya gangarowa  daga  idanunta kafafunta take d'agawa a hankali tamkar bata da laka ajiki  "nawal ta furta sunan  a fili  dan Allah karki shigo rayuwarmu nida mijina yanzu ma yaya aka kare  ,nasan idan kin  shigo  ko kallona bazai  ba , har ta hau kan step zance zuci take ta shiga Kitchen ta soma  kwabin fulawa dan yi masa  samosa   haka ta dinga aikin tana zance  zuci tana hawaye  tamkar wata mahaukaciya sabuwar kamu  ,hawayen idanunta  yaki tsayawa bayan ta gama samosa ta dibo arish ta bere ta soya da kwai sannan ta d'aura ruwan zafi ."
Tana  tsaye a kitchen  ya sauko  parloun  kasa fitowarsa kenan daga bayi  jikinsa sanye da gajeren wando baki da farin  singlet   ,wuyansa  rataye da farin towel yana goge fuskarsa zuwa wuyansa , yayinda  kafafunsa  ke sanye da bakin  silifas  yana tafiya yana goge jikinsa ,  kai tsaye   kofar Kitchen ya nufa  dan ?aukar fury  har  ya  kawo bakin kofa yaji  sautin  qarar dayan  wayarsa   dake  ajiye a parlour tun  jiya  ,ya juyo ya  dawo ya ?auki  wayar ya manna a kunnen "hello  Samir ya garin"? " da fatan komai lafiya ko ? lafiyata qalau na gaya maka  fever ne kawai  kuma  anyi  maganinta  kaine  aji farko fa  ,daga can bangaren dady ya amshi  wayar suka gaisa  ya masa  ya jiki "dan zazza?i  ne kawai fa dady me yasa zai fa?a maka dan kawai ya tadda maka  hankali  "to ya saukin jikin "?"Yanzu  lafiyata  qalau inshallahu  ma gobe zan fita  zuwa  office "okay naji dadin  abinda kace ba  damuwa  za'a yi komai  yadda ya dace samir   ma  zai shigo karshen  wata tare  da mummynku   dole  ayi  tafiyar  dashi  gashi Samir din yace zaku je buga wasa   spain ko ".?
"Eh haka ne dady ".
"to shikenan  Allah yayi jagora  idan kun dawo sai kuje hollond  da Austaraliya ayi abinda ya dace "to shikenan  dady sai anjima ya katse kiran ya shiga Kitchen kamshi  ne ya bugi hancinsa ya zagayeta ya bu?e  fridge ya ?auki  abinda  ya shigo dashi ya fita .."
shadaya  da  rabi na safe  ta gama  komai har da  break  fast ta gyara gidan  ta hau sama tayi wanka  dan zuwa lokacin tuni  ya sauya kaya zuwa na  gado wato kanana kaya zuwa  wando da riga duk blue  Black , tun ganiyar kuruciya bata sake  ganinsa da manya kaya ba  ,sai ranar daurin aurensu ,kuma  tun daga lokacin bata sake ganinsa dashi  ba, daga suit  sai  wondo da riga".
wardrobe  ta bude inda ta jera  kayanta ta tsaya tana karewa kayan kallo  ta dauki doguwar  riga ja wanda  aka tsaga bangaren kafarta ?aya har zuwa cinyarta  hannun  riga daya dan tsiriri ne yayinda d'ayan hannun ya zamanto dogo ta  taje gashinta ta fakashi  a tsikiyar kanta tasa ribbon ta kama ta fito ta zuba masa chips da  soyayyen kwai  da tea Mai kauri ta kawo masa inda yake zaune yana danne danne a system  ta ajiye "kayi break kasha magani " gyaran murya  kawai yayi ya cigaba da abinda yake ta  juya zata bar gurin "ummmmm ummmmm ummmmm yayi sound din Kamar Waka ta juyo da sauri tana murmushi "kana magana ne "?
Ya d'ago ya bar abinda yake ha?e da  tsura mata idanunshi  "tana da  damuwa a rayuwarta  , daman haka take shi bai sani ba , shi  da yake daukarta mai mugun girman kai da taurin kai da rashin son shiga lamarin mutane, a she abun ba haka bane shegen rawar kai ne daita kamar farar kura da surutun  tsiya , yatsun hannunta ta kamo ta soma  wasa dashi tana kallonsa , kawar da kanshi yayi yana jan tsaki bai gama takaicinta ba yaji ta soma waka har da dan  rawa  ..,"
"Omo  walai  if them pont gun  to  my head say make  I deny you I go tell them  say  lallai Ni be lie.
"I fit spen all of my money  on you (oh ho)
"Speed a couple million you  (yeah yeah )
"Give you loving tell you say  e don do (yeye)
Special type of felling that  I feel when am with .......
" Enough  dan Allah Malama  bana son hauka anan ya fada a tsawace yana watsa mata kallon banza   " shiru tayi tana dubansa  kamar ruwa ya  cinyeta ganin ya hassale  tace "kayi hakuri dan......  " jeki dan Allah banason hayaniya kin wani cika min kunne da   banzar waka da wata  muraryarki gangarin da bata   dadin sauraro  ,tsimi tsimi ta bar gun  tana tabe baki  ,yace " mahaukaciya kawai ji yadda take faman wangale  baki kamar wata  shasha  ya yaja tsaki tare da  maida  kanshi a kan computer..
Tunda ta koma sama ta kwanta lamo tana tunanin rayuwa  bata   sake yunkurin saukowa kasa  ba , sai misalin karfe  hu?u  na yamma , shima gabanta taji  yana ta faman  faduwa  da bugawa ,ta  sauko  a natse  take  daga kafafunta  , aiko idanunta suka ci karo da mugun abu ,dan kuwa wata matashiyar mace  ta gani  zaune  a gefen mijinta ,sanye cikin doguwar riga blue black wacce aka yiwa aiki da zare  milk colour a gaban rigar  da hannun rigar ,  ta nad'e  kanta da mayafi milk colour  ,haka kafafunta sanye da takalmi blue black da ratsin milk colour  , shekarunta  zasu zarta nata  a haihuwa, tana rike da yatsun hannun Aliyu  cikin nata  tana murzawa tare da yi  masa sannu .
a hankali ta dinga takowa jiri na dibanta har ta karasa saukowa "Allah sarki my love sannu kaji Allah ya baka lafiya kaga da muyi aure bazan taba barinka kai kadai ba ,dole ina tare da kai  a cikin wannan yanayin , kusan abinda tafi  furta masa kenan   ,yayinda  kisna ke binsu  da wani irin kallon mamaki "a gidan aurenta wannan film din ke faruwa ?" Take zuciyarta ta dinga tuttukin tana zafi da ciwo taji kamar taje ta rufeta da duka har sai taga bata mosti, sai dai sanin cewa bata da wani power agurinsa  yasa ta d'auke Kanta akansu  ta nufi kofar shiga  kitchen  zuciyarta na wani irin tsalle da rad'ad'i , tana gama shiga ta danne lip's d'inta na kasa da hakorinta da karfi  tamkar zata fasa lebanta  "ya Allah me ya kamata nayi yanzu "?"Na ?auki  mataki akanta ne ko kuwa na hakura na kama  girmana ?"Ki hakura ki kama girmanki  kisna  idan abu mai kyau tayi miki da sannu zata ga sakamako, idan ma akasin haka ne shima zata girbi abinda tayi tunda itama macece  "mai yasa kika zo gidana ?" Ta sake furtawa a fili
"Mai yasa bazaki bari har sai  kin kasance mata a garesa ba ?"
"Mai yasa na sauko? " da nayi zamana a sama da ban ha?u da wannan tashin hankalin ba ,  cikin sheshekar kuka take wa?an zantuttukan "mai yasa Aliyu  ?kasan ina tsananin  sonka dole zanji babu dadi a raina idan naganka tare da wata ". "mai yasa ka bata dama zuwa inda kake alhalin kasan  kana da mata  ?"Mai yasa zaka min haka Aliyu  ?"Why! why!! why !!!do you this to me Aliyu ?".
"A cikin soyayyar da nake maka har yanzu ban bayyana  maka rabi daga ciki ba, ka tausaya min kar zuciyata ta tarwatse akanka  " na fita sonka da bukatarka , zan sadaukar maka da dukkanin   farincikina , ka yarda dani dan Allah ka bani dama akwai sauran lokaci da zan gyara zamantakewar mu ,Aliyu duk abinda nayi maka ba yin kaina bane , zugar aunty afra ne gashi tasa na dasa kiyayyata acikin zuciyarka tun daga zamanin kuruciyata har zuwa auremu  ,plz forgive me and forget what I did to you ,nasan kayi tsananin fushi dani ne shiyasa  baka shayin  aikata mummunar abu gareni  ,sai dai bazan iya ?aukar  zuwan  wannan matar gurinka ba ,I will  be able to handle this situation tana cikin wannan halin ya shigo kamar an jihosa bataji motsin shigowarsa ba sai tsayuwarsa a gabanta taji  yana huci tamkar mayunwacin zaki"uban me kike yi ?
"Ko  baki ga anyi bakuwa bane da zaki wani tsaya batawa kanki lokaci  ki kawo mata wani abu ta sha ".
Tayi saurin gyada masa kai tana goge hawayen dake kwance akan kuncinta "da kyau kuka ba ?".  ya  fada yana kai hannunsa  ya dago ha'barta Yana kallon cikin kwayar idanunta tayi saurin girgiza masa kai alamun "a'a ".
"uban meye wannan idan ba hawaye ba da zaki ?aryatani   ?"Shine amman kayi hakuri  bazan sake ba ta fada muryarta na rawa  ya ingiza ta baya da iyakacin karfinsa  tayi taga zata fa?a tayi saurin rike Kitchen cabinet ta tsaya bisa kafafunta tana sauke numfashi da kyar "haka nake so kullum nayita ganin zubarsu har zuwa sanda zuciyarki zata buga ki mutu ......".Ya karasa maganar yana sakar mata tsadadden
murmushinsa ,"minti  a shirin na baki ki  shirya mata abinda zata ci yayi baya ka?an yana kallon falon "my nawal mai zaki ci ?".....
Mmn Sudais
????????????
 CUTAR DA KAI
     ????????
????????????
~TRUE LIFE STORY~
Free Page 7
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalmi, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga bukatar  siyan ?aya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ..."????
Tambayar    da  yayiwa  nawal   yasa   ta mike tsaye  cike   da yauki da  rausaya  ta  soma takowa   zuwa    bakin kofar  Kitchen  din  ,ta tsaya  a gabansa tare da  rungume   hannuwanta  duka  a saman  qirjinta ta  tsura  masa  idanunta tana kare masa kallo ,ganinta   tsaye  a gabansa  yasa   kisna juyawa  da  sauri  tana danne   kukan dake shirin kufce mata  dan babban  abun  kunya  ne gareta  ta  bar  nawal  taga hawayenta  ko damuwarta   "me   zaki ci a  dafa miki  my nawal ?".  sautin  muryarsa   ta   doki  dodon  kunnen kisna  ,take  zuciyarta  ta cigaba   da  dokawar  da take   a  tun sanda  ya  shigo  kitchen  din , cike da  sihirtaccen  kaunar da  nawal take wa Aliyu ta  sake  matsowa  jikinsa  tamkar  zata shige  masa   ta kai hannunta  ?aya  ta shafi gefen  fuskarshi cikin shaukin  son shi  tare da jin  dadin kulawarsa gareta "tabbas Aliyu na matukar  sonta   tunda  har  zai iya  mata  irin wannan karramawar  a gidansa".
"i love  You so much my love ta fa?a tana kashe masa  idonta ?aya   "I love you  too my nawal ki fa?a  min  abinda kike son ci "?nawal ta saki murmushin  jin dadi  tace "my  love  karka takura min  kanka da auntyna  banason wahalar da....."
Aliyu  bai  barta  ta k'arasa maganarta  ba ya katse  mata hanzari  "nasan  halinki  da rashin son cin  abinci  just tell me  what you ... .."
itama  saurin  katse shi tayi  ta hanyar  sakala hannunta  cikin tafin hannunsa ta soma masa tafiyar tsutsa  yayinda idanunta  ke  kanshi ta soma   tafiya  da baya da baya  dashi , tana masa  magana  a shagwa'be   .
"Cikina  akoshe yake  my love  if not da  zan so naci wani abu a gidanka  kodan na sake faranta maka  ". wani irin yanayi na zallar sha'awa ya tsinci kanshi ciki gabad'aya tsigar jikinsa ta mike gabadaya mazantakarsa ta motsa abunka ga lafiyayyen  namiji   ya sausauta  muryarsa sosai kana   yace"ok my nawal " .
a sukwane kisna ta juyo  idanunta ya sauka a cikin na nawal sakamakon fuskarta na kallon  kofar Kitchen  , murmushin gefen  baki kisna  ta sakar  mata  tana mai danne  abinda taji ya sauka  a tsokar dake makale  da qirjinta ,itama nawal  din  murmushin barikanci  ta sakarwa  kisna tana sake shigewa Aliyu kamar zata ratsa gangar jikinsa .
  "Yau naga abinda yafi karfina , anya kuwa  rayuwata  zata d'aure  a gidan nan idan wannan  yarinyar ta shigo ? ta yiwa kanta tamvayar  ha?e da  kawar da fuskarta  hawayen  bakinciki na gangaro  mata ."inna lillahi wa inna ilaihi rajiun kawai ta shiga furtawa tana maimatawa domin neman sausauci daga gurin Allah ..."
Nawal ta zaunar da Aliyu  sannan   ta zauna suna fuskantar   juna  ta matso  da  fuskarta  sosai  suna  sha?ar  numfashin  juna  bai  an  kara  ba  yaji  saukan  lip's d'inta  akan lip's  d'insa  tana  yawo dashi a daidai  lokacin da kisna ta sake  juyowa gabanta yayi  wani  irin mummunar  fad'uwa ,ta dinga jin kamar zuciyarta zata kama da wuta, Gabadaya yanayinta ya sauya  , numfashi  ma da kyar  take  janyowa tana fitarwa  zuciyarta na wani irin tuttukin bakincikin , ta ?auki wuka  tana kallonsu "naje na  tsoka mata wukar nan  a kahon zuciya na kashe shegiya  na huta  ."No  no  karki yi haka wannan ai  haukan kishi ne  ,"to  bari na d'aura ruwan  zafi  nayi mata wanka  dashi  ta soma ?o?arin  kunna gas "kai shima  wannan ba mafuta bane   gara ki nemo  abinda zaki mata cikin sauki ki  korata  ta  sake  maida  idanunta  akansu  zuciyarta na wani irin  zafi da ciwo  ."
   
Aliyu na  shirin kawar da  fuskarshi  yaji ta cafki  bakinsa  ta soma tsatsa kamar ta samu sweet , kisna   tayi  saurin  runtse  idanunta tare da yin kasa dafe da kirjinta dake tafarfasa tamkar an daura mata wuta , Aliyu ya kasa hana nawal aiwatar da abinda take so akanshi saboda feeling din da yake ji yana ratsa sansar jikinsa ,  batare  daya ce mata  uffan ba ta cigaba da  sha bakinsa tana sauke numfashi dan wani irin  sanyin dadi taji yana ratsata  da kai wa kwalkwaluwarta  sako na musamman ,wannan  shine karo na farko da suka fara musanyawar  yawu a tsakaninsu kuma kowanensu yaji sauyi na dabam ajikinsa shiru yayi ya cigaba da amsar sakon nawal bisa ra'ayinsa guda biyu na  farko  ragewa kanshi  feeling , na biyu kuma   dan  ya sake tarwatsa zuciyar  kisna  tasan yana da martaba da darajan da za'a so shi......"
sai  data  tsotsi  bakinsa sosai kafin  daga baya ta saki tana sauke numfashi  ,  shi  kuwa komawa yayi ya  jingina bayansa da  kujera yana fidda numfashi  "na matsu sosai  my  love , burina bai  wuce mu kasance ma'aurata  ba , yayi mata shiru  yana lumshe mata  ido dan shi kadai yasan yanayin daya tsinci kanshi a lokacin  da take tsotsan bakinsa a hankali  ya bude idanunshi akanta ya lura gabad'aya  yanayinta ya sauya da gani da  za'a wuce  shan baki bazata hana ba  ,shima ya kai zuciyarsa nesa ne bancin haka da yaso ya  murza dukiyar  fulaninta a tare suka  sauke numfashi suna kallon juna yayinda kisna Ke kai  sosai  har da shesheka  zuciyarta na  zafi "mai yasa bazai soni ba  ,bayan ina da duk abinda yake so ...?"Dan Allah ya Aliyu  ka tausaya min  wallahi zan kasance maka yadda kake so ,zan baka farinciki da kwantar maka da hankali ,zan kula da kai ,zan baka rayuwata hatta numfashina zan iya sadaukar maka dashi ka tausaya min ta   karashe maganar tana wani irin kuka mai ban tausayi ".
bayan   kamar   minti  biyar  kisna ta goge hawayen dake kwance akan kuncinta   ta  fito a natse tamkar bata tare da wani damuwa  hannunta  rike da  jug  ?auke da ruwan sanyi  ta ajiye a  gaban nawal   batare  data kalli  inda  take ba hatta aliyun bata kalleshi ba ,ta juya a hankali tana taku tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta  haye saman d'akinsu ,  zariya ta shiga yi  a cikin d'akinta tana zance zuci  kanta kamar zai  tsage gida biyu tsabar bakinciki, kwakwaluwarta ta shiga  cajin da tunanin neman   mafuta  ,dan  dole tasan abunyi  tun lokaci bai mure mata , idan  ta bari wannan yar iskar  matar  nayi  mata karuwanci  a gida tun  yanzu  shinkenan zata rainata  kuma kashinta ya bushe  , tana  tsaye  ya  shigo d'akin kallo ?aya yayi mata ya dauke kanshi   aranshi yace "wahallaliyar banza kawai baki ga komai sai nayi nasanadin da zuciyarki ta buga  ya soma cire kayan  jikinsa ya ?auki  towel  ya taraya a wuyansa  da alamun wanka  zai  shiga  ,take ta sauke  wani wahalallen numfashi , wani dadi ya lullu'beta  ta  samu damar da zata   fattakar wannan yar iskar  mata  a gidanta  ,yana gama  shiga bayi  ta fito daga  d'akin  ta kulle kofar  ta bar key ajikin ta dawo parlou'n kasa inda nawal take zaune  , wani  irin mugun kallo mai  ha?e da harara ta sakar  nawal dake zaune kafarta  ?aya  akan ?aya tana girgizawa tana sake karewa falon kallo ,  gabanta  ne yayi mummunar  fad'uwa da  ganin  irin kallon da kisna tai mata , a hankali ta motsa  bakinta "sannu da .......".Kisna  tayi saurin katse mata  hanzari ta hanyar d'aga  mata hannu "sannun uwarki da ubanki zaki min amman  dai  ke anyi tsohuwar   kilaki tsohuwar yar tasha    ,jaka  shasha  ballagaza   da bata  san ciwon  da darajan kanta ba , yanzu har  rashin  kamun kanki ya  kai  ki kwaso wa?an nan  tsilla tsillan kafafun naki kamar na jemage  ki zo  gidan saurayi  ? nawal  ta  cika da tsananin   mamakin kisna  ta bu?e  baki  zatai magana kisna ta sake d'aga mata hannu "dakata malama bana bukatar jin komai daga  bakinki  ,idan  ki kayi ganganci  bude  wannan dan iskan bakin  naki  sai na lahira yafiki  jin  dadi dan sai zubar miki da ha?ora  , maza maza second  biyu kacal na  baki  ki tashi ki bar min  gidana   kafin na  tura miki  wannan  abun a gidan  kashinki dakikiya mai fuskar  alade  ta nunata  da sekundireba ...........
"an  gama  yawon tazubar  da karuwanci  an rasa mashin shini  shine za'a lekewa mijina  ,na  sake ganin wa?an  kafafun naki masu  kama  dana jemage  sai na lalata miki rayuwa  , ai wallahi Allah ya  taimakeki  da kinci abincin  gidana  da kin  tabbatarwa  kanki mutuwa, domin  guba zaki   ci  oya out ta kai hannu  ta  janyo  wuyan rigarta  ta soma tafiya daita bata tsaya a ko'ina ba sai a  haraban gidan  ta saida ita a jikin motarta  "to  be your first and  last warning  da zaki tako zuwa   gidana  a matsayinki na karuwa ,ki tabbatar da aure ne zai kawoki gidan nan   ba karuwanci   ba  ta karasa maganar tana buga mata sikundireban  hannuta a baki .
nawal ta saki  ?ara mai sauti  tare  da rike  bakinta cikin azaban zafi   ta  juya  ta bu?e motarta  ta shiga ta zauna zata maida murfin motar  ta rufe ,kisna ta rike "bance  karki fa?a masa  ba  ki fa?a masa dan girman Allah kiga yadda zanyi dake  , wallahi  sai  kinga kudi kince kashi ne shashar tumakiya   sannan kuma  zaki iya   cigaba da zuwa gidan bazan ce karki zo  ."cikin rawar jiki nawal ta  bar  gidan tana zubar da hawaye "
kisna na  ganin tafiyar  motarta ta saki murmushin  jin dadi "kadan kika gani wawiya   ta  juya da  sauri taje ta bu?e  kofar  ta dawo parlou'n  kasa ta zauna tana kallon tv qirjinta na bugawa da karfi   a  natse ya sauko falon   yaga wayam babu nawal babu alamun , yace" ke ina yarinyar nan "?.
"Wacece haka ? Ta tambayesa tana hura hanci "Banason iskanci nasan kinsa wacce nake nufi  yayi maganar a zafafe yana tsareta da idanunshi  "to ni ina zansan inda take   tayi maganar a shagwa'be mutumin dake zaman kansa har a tambayi inda yaje "wacece ke zaman kanta ? yayi maganar yana ?o?arin damkar makoshinta ta goce ha?e da mikewa tsaye tayi nesa dashi kirjinta na bugawa ..."Wallahi ki kiyayeni idan ba haka ba zan bata miki rai "to ni me na maka  kodan  ban da gata shi yasa kake min abinda kaga dama  ? Ko Zaman  daduro  muke  da  kai ya dace ka  gayyato budurwarka gidan nan har   ma ku zauna kuna iskanci alhalin  ga matarka sunanh a gidan ?
"Da wa kike wannan Maganar ya kara taku biyu zai cafkota ta buge hannunsa ta  zura aguje "ni ka kyaleni karka dokeni  bata tsaya a ko'ina ba sai a karshen step tana haki tana hura masa hanci ..."
"Zaki sani ne  kuma zan kamaki cikin ruwan sanyi , zaki san baki da kunya dan wallahi  sai na fasa bakin rashin kunya, kuma  ki bari na kira nawal naji tace kin mata wani abu sai kin gane baki da wayo kamewa tayi guri daya ta rungume hannuwanta tana kallonsa tana  fargaba, tasan idan nawal ta fada masa abinda tayi mata sai ya mata dukan mutuwa dan haka ta tsaya  jira  ya kirata taji yadda abun zai kaya ,idan taga dukan zai yi ta shige daki ta kulle   ta barshi yayi  kwanan  falo  .."
Tana kallonsa  ya dauki wayarsa  yana ?o?arin neman  layin nawal  kiran cochi dinsu  ya shigo ya zauna  yana amsa wayar  " hello Mrs birsat kwana biyu  bamuyi waya ba, ya kake ya kwana biyu ?". "yanzu kake nufi to  shikenna  ka dan bani lokaci zan kiraka back   ..."ya katse kiran yana  neman  na Samir...
Bayan sun gama waya da Samir ya sake kiran mr birsat yayi masa bayani komai a natse sannan ya soma neman nawal ,tana ?auka yaji gabad'aya muryata ta sauya "me yasa kika wuce bayan nace ki jirani ?
"Kayi hakuri dan Allah na samu kiran gaugauwa ne "akwai kiran gaugauwan daya fi dokata mahimmanci? " kin fa san banason saba doka "kayi hakuri bazan sake ba yayi shiru yana kallon kisna dake tsaye tana kallonsa   can yace "me yasa muryarki ya sauka kamar ma kuka kika yi ?"No babu komai fa wallahi mura ce ke son kamani Kuma  nasha magani "ke dai ki fa?a min gaskiya idan akwai wani abu "babu komai ta fada a takaice tana danne kukanta duk yadda Aliyu yayi daita ta fada masa abinda ke damunta taki saboda taji tsoron gargadin kisna ..
******
Kwance  yake  akan gado hannunsa  rungumeta  da  pillow  yayinda  idanunshi ke  kallon celling d'akin, sosai  yayi zurfi cikin  tunani  wayarsa  ce  ta ?auki  qara  ya kai hannunsa ya lalubo wayar yana dubawa sunan daya gani yasa ya ?an mike  ya jingina bayansa da abun gado "assalamu alaikum "
"Wa'alaiki salam mummuy  anyini  lafiya "lafiya ya jikin naka jiya  samir yake fa?a min  baka da lafiya ? Cikin kwantar da murya yace "jiki alhamdulillah mumy naji sauki sosai "Allah ya qara sauki ka kular min da kanka fa ,ya amsa mata da "inshallahu mamana ya mutanen gidan ? "Duk muna lafiya ina ita kisna take  ya d'ago ya kalli  inda take kwance akan  doguwar  kujera  idanunta na kallonsa, tun sanda  daya ambaci sunan mummuy  tayi shiru  tana sauraronsa tana  jin kamar tazo ta fixge  wayar  a hannunsa ta  sake  jin muryar mahaifiyarta ."
muryarsa a raunane yace" tayi  bacci "okay inshallahu  gobe zan kira ka  ha?ani daita su aryan sun damu suna   ina  son magana daita "okay suna kusa  ne yanzu ko sunyi bacci "?
"Ai  tun takwas sukayi baccin dole ,ya gyara zamansa sosai yana son jin dalilin baccin  "mai ya  samesu mumy  "? yayi maganar hankalinsa a matukar tashe " kasansu da kiriniya d'azu ne suna wasa a parlour daf da magariba  sukai  karo da juna , aryan ya fasa  baki shi kuma areef  goshi  ,sai da  muka dangana  da asibiti shine fa muna dawowa sukai  bacci 

Please Login or Register in order to submit comment