Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zarar girma  yazo musu zasu tattara  su koma jaharsu su  cigaba da rayuwa  ..."
  A  wannan  lokacin kamar  yadda muka samu  labari  uncle haroon  bai bi bayan iyayensa  zuwa ilo ba acewarsa  mai zai yi a kauye  babu  wuta  babu network   babu jin dadin rayuwa  tsakaninsa da kauye  sai  dai kallo ya tattara  ya bi wani abokinsa  farhan  zuwa  jos  ,duk sanda  mommy  taje ilo  gurin   mahaifiyarta  dan kai mata  ziyara ta dinga mata  kuka kenan akan uncle  haroon  tare da bar mata wasiyya  iri iri akanshi  ,  "Idan  garba da bature sun  juya masa baya  salaha  karki  juyawa d'anuwanki  baya " ina son  babakarami  tamkar raina ,dan Allah  kema ki so shi kamar yadda nake son shi  ki  janyosa  jikinki  ko bayan  raina  idan Allah yasa  ya  dawo kuka hajiya  kayi  keyi sosai wanda  har  yasa mommy  kuka   suka   rungume  juna gam  suna  kuka yayinda Alhaji sani  yayi  shiru yana Kallonsu  cike da takaici da bakinciki  dan duk  tautaunawarsu yana shiga  kunnuwansa , kuka  suke kamar ransu zai  fita  ,   cike da zafin zuciya    alhj sani  ya    tako  zuwa inda  suke rungume da juna   ya  fara  magana cikin zafin  zuciya  yana cewa" momy    karki  kuskura  ki ?auki maganar  mahaifiyarki  da  mahimmancin  da zai sai  ki damu rayuwarki  akan   takwaran Alhaji   dan  ko ya dawo garemu   bashi da muhalli    acikin   gidan  nan,  ban ciresa  a cikin  ya'yana ba amman na ciresa a cikin  zuciyata dan bazan   amshesa ba  ,ba  dai yana gudun zama damu bane  saboda bamu da arziki yaje  duniya ce gashi nan gata wanda bai zo ma tana jiransa "hajiya  kayi  ta zabura  ta  mike  tsaye  tana fuskantar shi  cike  da mamakin  jin furucinsa sannan   tace  "saboda  me  zaka fadi  haka  alhalin  d'anmu ne babakarami  bashi  da iyayen da suka fimu ",ana ki tunanin  ba ai shi bai daukemu  a matsayin iyaye ba  , kafin kace me gurin ya hargitse da magana  da rudani  tsakanin hajiya kayi da Alhaji sani  zuciyar hajiya  kayi ta tsinci  kanta  cikin  rashin natsuwa  da jin hukuncin  mijinta  , ranar tamkar mutuwa  akayiwa  a gidan   mommy  da  hajiya   kayi   babu  abinda suke sai  aikin zubar da hawaye yayinda  shi  kuwa a lokacin  haroon  yana can  yawon duniya bashi wannan  gari bashi wancan  gari  duk garin da yasan zai ji dadi zashi ,kullum kuma  cikin  samun sabbin  abokai da yammata  yake  kuma har  wannan lokaci mata basu  daina kashe masa kudi ba  , a hankali  har  ya  shiga  harkan  neman  mata  da smoking  kamar yadda  momy   ta  samu  labari   mata na biyansa  kudi dan  ya  kwana  dasu , ranar  kuwa momy  tayi kuka  tamkar ranta zai bar  gangar  jikinta  bata fadawa kowa ba ranar da  zazza?i ta kwana a jikinta ta aika masa sako  ya dawo gida  ya bar harakar da yake duk abinda  yake so zata masa  amman yaki yace shi yanzu bazai iya rayuwar gida ba   ..."
Numfashi   kisna ta sauke a lokacin data zo nan  sannan  ta fuskanci safy fuskarta  cike  da tsananin damuwa tace   "a  iya  nan zan dakata  bazan  iya cigaba  da bakin labarin ba  saboda  akwai  wani  boyayyen sirri  akan  ya aliyu ba kuma zan  so wannan sirrin ya fito  daga bakina ba  ta karasa maganar wasu hawaye na gangaro mata  safy ta numfasa  tace ,"to ai baki  fa?a  min yadda kuka  yi aure da Aliyu  ba dangantakanku kawai kika fada min ni rayuwar aurenku nake son ji " "Muddin  zan fa?a miki  yadda muka yi aure  dashi dole  zan bayyana wannan  sirri   " .
murmushi safy  tayi sannan tace" kisna  kenan  ba dai zurfin  ciki  ba  sai naji kin  sake  shiga raina ina matu?a  son mutun mai rike  sirri wanda samun irinku  yanzu kuke da matukar  wuya, kisna  ta gyada mata  kai  kwayar idanunta na kallon sama dan  ita  ka?ai  tasan  yadda take  jin zuciyarta a  hankali  ta mayar da idanunta   zuwa ga safy  ta cigaba da magana "ciki   ba'a yisa  dan  abinci kawai  ba duk mutumin daya  kasa rike sirrinsa karka  yi  tunanin zai iya rike na  waninsa ta karasa  maganar hawaye na  sake  gangarowa daga cikin kwarnin  idanunta  "wannan  magana   taki haka take amman   naso  naji yadda  kuka yi aure da Aliyu gaskiya " parlou'n  ya d'auki shiru  babu  wanda ya sake  yin magana har aunty  zee wacce ke aikin mayar  da  kayan lefe cikin  jakunkuna, " Kisna  kiyi hakuri ki daina kuka  bana son  ganin hawayenki yana sani jin wani iri wallahi  "ai  indai kisna  ce yanzu  haka take  abu kankani ke sata  kuka  sa?anin da  ta mike ta karaso kusa da kisna ta rungumeta suna kukan tare wani abu ya tokare makoshin Kisna dan komai  daya faru ya shiga dawo mata daki daki  suna cikin kukan muradi ya shigo parlou'n ya iske su
cikin  wannan  halin  suna kuka safy na basu hakuri   saurin katse sallamar yayi   daidai  lokacin da aunty zee ke magana murya can kasa  tana gogewa Kisna  hawayen " .
kyawawan  idanunshi masu  matukar kyau da haske  ya sauka akan kisna  dake zaune tana matso ruwan hawaye tamkar wacce aka yiwa mutuwa   tare da  kare mata kallon tsab  idanunta sun canza daga  fari zuwa kore , a hankali ta d'ago idanunta suka  hade da nashi wani irin mummunar faduwar gaba  taji  ,take  gaba-daya ilahirin jikinta ya dauki rawa  lokacin da kwayar idanunta ya ha?e da  nashi kallonsa ka?ai nasata jin  abu biyu a lokaci  daya, faduwar gaba  tare da alfahari   kasancewarsa   uban   ya'yanta  .
kusan minti   biyar   ya   dauka  tsaye a bakin kofar dakin  yana Kallonta sannan  ya  soma takowa a hankali yana mata kallon kasan ido ,nazarin yanayinta  yake, wannan yanayin daya gani a tattare daita yanayi ne na damuwa dan kuwa idanunta sun tabbatar masa da haka guri ya samu ya zauna akan kujera  yana kallon safy  dake faman zuba sannan yana kallon  kisna  ta  gefen  idanu muryarsa  a kasalance ya soma magana  cikin  tsigar  tsokanar  safy    "ya   kika ga   kayan  amaryarta sun bugeki   ko "?"Sosai  kuwa duk  sun   burgeni   sai  dai  gabad'aya kayan sunfi dacewa  da kisna ba wannan  mai  kama da busashen bishiya ba, ko ka taba ganinta da irin wannan wa?an kaya"?ta karashe maganar cikin tsigar wasa tare da yunkurawa ta tashi "wannan  kuma son ranki kika   fa?a   saboda     kina  da wata manufar     munafurci          a ranki  ai sai   na     zuga  mijinki ya qara  aure  " kalmar munafurcin  daya dangantata dashi    ya mugun bata rai  murmushin    takaici  tayi   tana rataya  jakarta  "kai ma daka hakura mai mata kamar kisna mai zai yi da wata nawal din banza mai siffar munafuka   "? Ta fada tare da    nufi kofar  fita tun kafin ya antayo mata bakar  magana data fi na farko  tana cewa "sai anjimanku " aunty zee ce  ta mike tayi mata rakiya  har haraban gidan kalmar ta bala'in bata masa rai zuciya  tazo  wuya a hankali ya  dinga girgiza  ?afarsa   daya   ...."
Kisna   ta  mike  tsaye ta karasa inda yake   ta   durkusa  muryarta  cike da rauni tace "sannu da zuwa " ta'be baki yayi batare daya amsa mata ba , bata damu  da rashin amsawarsa ba tunda idan da  sabo  ta saba da halinsa  .
  ta    soma  cire masa  canves din dake sanye  da kafafunsa hawaye na ziraro mata sanda ta karasa cire masa kafafunsa ya saura da  safa kawai  , ita kanta  aunty zee data dawo parlou'n  ta  ganta    durkushe a gabansa kasa daurewa tayi sai da wasu suka qwalla zubo  mata  ta  kawar   da kanta  tare da danne abinda taji bawai shishige masa da kisna  take bane yafi damunta irin banzatar da rayuwarta da yake   kai  tsaye  juyawa tayi ta nufi kofar fita    tana  goge    hawaye  "zainab  ya  kira  sunanta   muryarsa a dake cike da  ?acin  rai    tsayawa   tayi  cak  batare data  juyo ba   "kowa  murna   yake  akan  auren  nan da zanyi  banda ke   da wannan yar iskar  me  yasa kika   manta abinda  yar iskar nan  ta  aikata  ga rayuwata kunnuwan  Kisna   suka jiyo mata sautin muryarsa  yana fadar haka a can kasan makoshi , kamar  ta cigaba  da durkuso a gabansa ta cigaba da sauraronsa tare da  rarrashinsa da bashi hakuri sai zuciyarta ta haneta dan haka ta mike hannuta  rike  ta canves dinsa  tana kokarin hawa  sama  kamar zai mata magana sai kuma ya fasa  ya cigaba da magana "wallahi  kina biyewa son zuciyarki dana wannan abar sai dai bata isa bakincikinta ya kasheni ni kadai ba kamar  yadda taso faruwar hakan  kafin taga mutuwata  ina tabbatar miki ni ne zan soma ganin nata duk da  nima nasan  bazan cigaba da zama ba amman wallahi tallahi ba zan barta tayi rayuwa mai dadi ba ina nan akan bakana har sai nayi magani iskancin data min numfashin Kisna ya soma fita da sauri da sauri , ta kasa cigaba da daga kafafunta aunty zee ta gigice ta juyo tana kallonsa cikin tsananin damuwa itama  Kisna ta juyo tare da tsura masa ido canves din hannunta ya subuce  shima kallonta yake  cikin  tsana muryar a zafafe Kisna ta soma magana  cikin kunar rai   "kai  cika   mutun  mara imani     hakika  na soma danasanin kasamcewa  mata kuma uwar yayanka  a rayuwata  ,alfaharin da nake na kkasancewarka ubansu Aryan reef  da janye domin sun yi hasarar  uba wallahi  ,kasani  wani  bakincikin ne dabam  zai kasheni ba sanadin   ciwon zuciyar da kake kokarin haifa min ba kuma  duk abinda kake yi Allah yana kallonka zai saka min sannan auren nawal da kake ganin yana cikin bakinciki da zaka kunsa min wallahi  ko  ajikina  saboda banga  abinda zai sa na daga hankalina akan matar da tsinannu kadangarun bariki suka gama da rayuwarta  yar iska da kowa yasan ba yar mutunci bace kawai bakar zuciyarka ce ta hanaka ka fuskanci komai ni kuma da kake kira da yar iska duk iskancina ban bari yan iskan kadangaru bariki sun .........."
shiru tayi sakamakon toshe mata baki da aunty zee tayi tana girgiza mata alamun tayi shiru  saurin cire hannu aunty zee tayi a bakinta  "ki bari na fadi   abinda ke raina ta yaya zai dinga dangantani da kalmar iskanci wallahi duk  matakin da kake shirin dauka akaina ka dauka amman ka kwana da sanin cewa Allah bazai barka ba saboda ina da hakki akanka kuma babu inda Allah yace dan nayi maka  laifi ka tauye hakina daya rataya a wuyanka ya mike a zuciye yayi kanta yana huci  ya daga hannunsa   zai doketa  yana auna mata zagi aunty zee ta kare  "haka zaki  kare cikin tsananin  bakin ciki a gida nan rayuwar farinciki sai dai kiga ana yinsa a wani gida .."
  "da ikon Allah sai Allah ya kunyataka,   karewa cikin   bakinciki tana gurinka mutumin da baya yafiya tunda har nadamata bata sanya kaji zaka iya hakura da abinda nayi ba hakika zaka ga yadda rayuwa zatayi da kai hakina dana yayana bazai barka ka zauna lafiya ba aunty da zee ta rikesa  gam da hannuwanta duka tabashi hakuri   saboda jikinsa dake tsuma   da kyar ta samu ya zauna yana huci  duk cikin maganganun ta babu wanda ya taba zuciyarsa da tsaya masa arai kamar kalmar data danganta nawal daita take gumi ya rufeshi gabadaya ya nemi natsuwarsa ya rasa ji yake kamar zuciyarsa zata buga a yanzu da ya soma  jin soyayyar  nawal na dan  shigarsa shine zata fadi mummunar kalma akanta yasan tayi haka ne dan kawai ta bakanta masa amman bazai yi sakacin da zuciyarsa zata amince da kalamanta ba,cikin tsananin zafin rai Kisna ta  juya  cikin sauri   ta hayewarta  sama zuciyarta kamar zata  buga ,itama aunty  zee  ta fita ko  dan  rarrashin data saba yi  masa  a duk sanda ya hau sama bakinciki yasa ta kasa sannan taki masa magana akan yadda za'a yi da kayan lefe dan nan ta barsu yasan yadda zai yi dasu ai ta gama mai wuyar , duk yadda zuciyarsa taso ya yarda da kalaman Kisna akan nawal  kin yarda yayi domin ganinsa  yana   yin  nasara akan komai dan tun daya taso yake samun nasara arayuwarsa yana da tabbacin zai yi nasarar samun nawal cikakkiyar mace a gidansa  kamar yadda ya saba nasara  dogon   tsaki  yaja  wayarsa dake qara ya ciro yanayin yadda ya soma magana kasan shi da mommy ne.."
Tana  tsaye a dakin  tana datasanin abinda tayi ya shigo dakin   yana  cire yar  saman   rigarsa  ya ajiye akan gado ta karasa zata tayashi cire sauran ya dakatar daita yana zabga mata harara taja ta tsaya tana kallonsa ta madubi gabanta na cigaba da faduwa ",sannu tantiriya Kinga ma ci min mutunci  ke da wancan yar rainin hankalin yanzu  shine ?an iskanci zaki wani nuna ke mutuniyar arziki ce  yayi maganar yana  ajiye rigar  akan  wanda ya cire ya ?alle agogon diamon din  dake daure a tsintsiyar hannunsa ya ajiye "bai kamata kaji ciwo ba , babu inda  maganata ta shafi ta safy data  biyayyar aurena da  kai  ,magana ka fada na baka amsa daidai da maganarka meye abun daukar zafi? "shiyasa fa idan baki yasan abinda zai fada bai san abinda za'a maida masa ba idan baka son ina fada maka babu dadi akan komai kaima ka canza dan Allah ma daya haliccemu  muna saba masa kuma mu dawo mu rokeshi ya yafemana bare mu yan adam yakamata ka canza ka manta abinda ya faru mu rungumi rayuwarmu idan kuma rayuwar daka zaba mana kenan shikenan sai mu cigaba tunda ta soma magana bai kulata ba haka bai dago ya kalli inda take ba  zai shiga bayi  tace "ranka shi dade akawo  coffe ko akwai abinda  kake .. ....?"
Bai  tsaya  jin abinda zata fada  ba ya shige bayi ya rufo kofar da karfi ya  shiga bathtube ya  tsaya tare da kuna showel  a hankali ruwa ke tsiyaya ajikinsa a hankali komai ke dawo masa tun daga maganar     safy   har zuwa wanda  Kisna ta   furta  masa tsaki yaja yana furzar da iska safy  tana   yiwa rayuwar  gidansa shishigi kafin ya dauki mataki zai fara  fadawa mijinta daya ja mata kunneta sannan ya dakatar daita daga zuwa  gidansa har  ya kammala zuciyarsa na masa zafi da tuttukin bakincikin "ko ina ruwan ta da rayuwar gidansa "?
Ya fito kungunsa daure da towel fari hannunsa rike da wani ,ga gabobin kirjinsa da damtsen hannunsa sun bude kana ganinsa kaga dan kallo dan alamun motsa jiki ya bayyana ajikinsa saurin ?auke idanunta tayi dan kallonsa na haifar mata da damuwa muryar a sanyaye tace   "me zaki ci "?yayi mata banza ya wuce ta ya karasa ya bude wardrobe kayan shan iska ya dauka gucci farare  tass  wando da riga   ya saka  rigar ta kama jikinsa sosai  dam ana iya hango murdewar jikinsa da yadda karfin jikinsa yayi tasiri  sumar kanshi sai kyalli  take ya sanya fillifas  fari  da facing cap fari  ya dawo gaban madubi yana kallon jikinsa yana fesa turare ya ajiye kwalban turaren ya dauki system dinsa  zai  fita ta sake sanyawa jikinta jarumta  tace "inda ka dawo mai zaka ci  ?"   dan  ina  son na dafa maka abinda zaka  ...... .."katseta  yayi ta hanyar ce mata "enough kisna kinsan  bana son damuwa da yawan naci ko ? " dole sai na fadi abinda zanci  "? Ke baki san abinda ya dace ba saboda hauka ne acikin tunaninki   kike tambayata ya karasa maganar yana  k  nufar kofar dakin . "
"Allah ya huci zuciyarka
ta hanzarta bude masa kofar fuskarta babu alamun damuwa  tayi masa rakiya tana tsaye har  sai  da taga tashin motarsa  sannan ta dawo zuciyarta  cike da tunanin ,  sosai  take  jinsa  ajinin jikinta bazata iya rabuwa da shi ba sai dai ta daina daukar duk wani iskanshi yana mata zatayi masa zata bashi mamaki dan bazata  saba alkawarin da tayiwa kanta ba sai ya dawo ya rusuna mata kafin wata biyar dinsu ya cika ..."
Bayan muradi ya bar gidan gidan nasir ya nufa   bai shiga  cikin gidan ba ya tura mai gadi tare da mai gadi nasir ya dawo nasir na sanye da kananan kaya wando tree quater sai shirt yaja ya tsaya yana binsa da mugun kallo cikin tsananin zafin rai "muradi lafiya ka tsaya daga waje kamar wani bako?a fusace muradi ya  katseshi nazo in sanar da kai kajawa matarka kunne ta daina yiwa rayuwar gidana shishigi idan ba haka sanadin ta'adancinta zai haddasa gagarumar matsala a tsakaninmu "haba muradi me yasa zaka fadi haka bayan ba ita bace silar haduwarmu tare fa matanmu suka bude ido suka ganmu bai dace ka fadi haka  ba na maka alkawarin zan dauki mataki akanta  da kyar nasir ya shawo kanshi sai dai yaki shiga gidan daga nan yayi masa sallama ya wuce inda zashi
A daren kasa runtsawa yayi  duk yadda zuciyarsa ke  bukatar natsuwa, gashi yanayin garin yayi sanyi zai yi dadin bacci  amman  ya kasa samu ajiyar zuciya ya dinga saukewa wanda duk Kisna tana iya juyowa , abubuwa zuciyarsa ke tunawa zuciyarsa ta jagule kamar ya daura hannu aka yasa ihu ko zai ji sau?in zafin da take masa gani zai juyo inda take tayi saurin kawar da idanunta tare da runtsewa sai da yayi mata duban tsanake  ya tabbatar da bacci take sannan ya mike ya karasa inda yake ajiyar abubuwansa masu mahimmanci  ciki har da sirrin daya shafi rayuwarsa  tun daga kan mahaifiyarsa  har zuwa rayuwarsa da Kisna    bude karamin akwatin zinarin yayi wanda agurin gasar kwallon duniya yaci ya cire wani kyakkyawan diary mai tsananin kyau ya mike ya fito daga dakin ya nufi parlou'n sama ya zauna  idanunshi na kan diary yadda yake kallon diary haka komai ke dawo masa  a hankali  kamar yanzu abun ya faru ya bude  ya soma bin komai daki daki  har yazo inda mahaifiyarsa ta hadu da mahaifinsa mutumin da yake jin tsanarsa fiyye da kowa a duniya, bayan shi sai Kisna da afra wadan nan  mutanen bazai taba manta su a rayuwarsa ba domin kuwa sune mutanen da suka hujijiga rayuwarsa ..."
BENUE
  daga   garin  jos benue haroon  mahaifin Aliyu ya nufa ya cigaba da fantamawa  yadda ransa ke  so ga mata ga kudin holewa  da yake samu daga gurin yammatansa dan ta kai ta kawo  baya kula ya'yan talakawa sai ya'yan masu kudi ,yayan talaka sai dai su kalleshi su kyasa amman babu fuskar da zasu  kusanci  inda yake ba dan suna  jin  tsoro ko bazai  saurarensu ba kawai kwarjinin yake  musu  cikin haka ya hadu da wata yarinya mai suna Benedicter  gebrel   asalinta  yar  kauyen  gishiri ce amman suna zaune acikin benue  ,
benedicter  dai diyar  mai  kudi  ce sosai  a garin  Benue  wacce ta kammala  da karatunta na gaba da secondary a kasar enugu  tana   aiki  ne a  karkashin pot-ortority ne a garin  benue, tana samu kudi sosai ,mahaifinta ya jima da rasuwa dan a lokacin yana nema shekara goma ,ba wani girma tayi ba amman a lokacin mahaifiyarta ta damu tayi aure  dan lokacin shekarunta bazasu fi 25  ba kullum sai mahaifiyarta tayi mata mitar ta fidda miji sai tace mata ita bata samu wanda take so ba ,a lokacin akwai wani dan kawar  momynta  dake maseefar sonta dan kusan gaban kowa yake nuna  yana sonta tun daga lokacin dataji yana sonta ta dauki tsanar duniya ta daura masa ga wasu bad habit d'insa data tsana shaye shaye ga bala'in son mata duk macen daya ganin sai ya kyasa  wata rana mahaifiyarta ta sameta akan   nanyak  domin son sanin  ko tana da ra'ayinsa  bata mata mutsu  ba ila kalma daya data fahimtar da mahaifiyarta  bata son nanyak ya nemi matarsa a gaba itama zata kawo nata miji kwatsam  ta ha?u da haroon
sanadiyyar saurayin   kawarta ,  kallo ?aya tayi masa taji ya shiga ranta har taji zata iya aurensa a lokacin da bai wuce shekara   30  a duniya ba, tashin farko ta  nuna masa  tana son shi kuma da aure sai dai  ya nuna  mata  shi bashi da ra'ayin yin soyayya ko  aure a halin da yake ciki
a lokaci  kawarta Elizabeth  tace " dicter Karki wahalar da kanki  wannan guy din  bashi da lokaci soyayya   bare  lokacin  wani aure , gashi  baya zama guri daya kamar mai aljanu haka  yake bashi nan gari  bashi wancan gari  gashi duk abinda kika tsana daga nanyak  yana aikatawa yana shan sigari kamar hauka  kuma yana mu'amula  da mata dabam dabam  nasan kyawunsa ne ya rud'eki  ko "? dicter  ta girgiza mata kai alamun ba haka bane  "ba kyawunsa bane ele  har ga Allah ina son shi kuma zan iya muslinta  saboda shi matukar zai aureni  halinsa  kuma zan sauya shi  "da  digiri dinki da kyawunki dicter  zaki tsaya  'batawa kanki lokaci akan wannan "?" jobles  ne fa bashi da aikin yi  sai zaman banza  da shaye shaye  "koma dai menene ele ina son shi  haka  kika sani ko ta dalilina  ya samu natsuwar zuciya  ya zauna  guri  daya har ma ya daina abinda yake  gyada kai kawai Elizabeth tayi tare yi mata   addu'ar  fatan samun nasara tunda taga ta zurma  .
a hankali  dicter  ta dinga shigewa  haroon   tana fahimtar  dashi yadda take jinsa a zuciyarta  dariya maganarta ta bashi  tare da mata  wani irin kallon kasan ido wanda ya zame masa jiki  dan ya sha jin ire iren wannan banzar kalmar daga bakin yammata dayawa wanda shi sam bai d'aukesu da wani tasiri ba, dan gani yake har lokacin ba'a haifi matar da zai aura ba,duk yawon garuruwan da yayi bai samu macen da tayi masa ba bama zai kirga mata nawa suke binsa da sunan soyayya  ko aure ba ,har tambayar kanshi yake yaushe ma zai samu wacce zata sace zuciyarsa kamar yadda yake sace zuciyar yammata  ? face to face ya fitowa  dicter  ya nuna mata bai sonta  .
taji zafin ciwon  furta mata haka a ranta  sai dai ta danne  taki hakura da shi ta cigaba da binsa dan su shaku  a hankali  har  shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu tana zuwa inda yake shima idan ya bushi iska yana kai mata ziyara  ganin yadda haroon  ke kawo mata  ziyara yasa mahaifiyarta  ta soma mata mitar  akan lallai tace wa mai zuwa gurinta   ya fito suyi aure, ta cewa mahaifiyata ta bata lokaci zata masa magana wanda ita tasan har ga Allah ko tayi masa maganar kamar  dagulawa  kanta lisafi    zatayi dan ba aurenta zai yi ba  tunda ya sha fa?a mata baya shaawar yin soyayya dan baya son ayi breaking heart d'insa ko aure zai yi sai dai yayi kawai ba dan yana son matar ba  ,ganin kyawunta da tarin ilimin bai dauke hankinsa ba yasa ta shiga   kashe masa kudi  kullum cikin siya masa kaya take  tace zata maida shi karatu saboda lura datayi yana da tsananin ilimi sai dai bashi da kwalin da zai samu nagartaccen aiki shirme ya dauki maganarta tare da sharewa , a tsarinsa wata biyar zai yi  a benue sai gashi ya kusan lasar shekara  ,
sosai suka shaku da juna a cikin irin shakuwar da sukayi ne dicter ta bashi labarinta  ta karashe da  tambayarsa nashi labarin da  garinsa ganin yadda ta ajiye batun soyayya gefe   take bashi kulawa da  kashe masa kudi  duk kayan data gani muddin zai yi masa kyau sai ta siya masa haka albashi ta idan ta amso shi take mikawa ,shi yasa ya sakankace  daita ya fada mata shi dan wani gari ne  da yadda ake zuwa garin ilo  ."
Haroon  bai iya neman kudi  ba amman ya iya kashewa dan  baya d'agawa kudi kafa duk yawansu   suna shigowa yana cinyesu kamar wani dan caca a haka dai shakuwarsu ta juye zuwa sha'awa agurin haroon dan   har  suna romancing sosai lokacin daya nemi ya kusanceta  bata hanashi kanta ba dan ganinta   kamar wata dama ce  ta samu  tunda dicter  ta d'an d'ana haroon   ta sake  rikicewa  akansa ta  makale  masa taji duk duniya babu abinda  ya isa ya   rabata dashi ....."
  Aiko shigar farko sai ciki bata fahimci ciki gareta ba haka suka cigaba da muamula har abin ya zame musu jiki kullum suka ha?u sai sun kusanci juna sai biyu sau uku   sai da tayi wata uku  dauke da cikinsa ta fahimta  cike da murna tazo masa da labarin ciki yayi mata wani banzar kallo  tare da cewa "a she wawiya ce ke ban sani ba"?" me zanyi da wani ciki yanzu da zaki wani kwaso

Please Login or Register in order to submit comment