Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga garesa zama dashi ko rabuwa dashi "
Tsayawa tayi ta daidai natsuwarta tare da goge hawayenta sannan ta cigaba da tafiya a kan step ta hango aryan da areef suna rige rigen Isa gurin mommy gabad'aya suka fa?a kan cinyar mommy dake zaune saman doguwar kujera tana ware musu hannuwanta alamun su taho gareta Hajiya mommy ta dubi jikokinta cike da farincikin ganinsu cikin koshin lafiya, yayinda qaunarsu ke cigaba da ratsa kowani sashi na zuciyarta ,ta shafi kansu daya bayan daya tana yiwa Allah godiya daya azurta Aliyu da kisna da samun kyawawan ya'ya wanda take qauna fiyye da komai a duniya , mikewa tayi tare dasu suka isa dining table inda Samir da aunty zee ke zaune suna murmushin jin dadi ganin areef ya tashi lafiya babu wata matsala kisna ta karaso jikinta a matukar sanyaye ta durkusa har kasa tana gaishe da mommy "Ina kwana mommy .."? "Lafiya lau mamana kin tashi lafiya ya karfin jikin"?"Alhamdulillah naji sauki sosai ta sake fad'ad'a fuskarta da murmushi dan kwantar da hankalin mahaifiyarta , ta juya inda samir yake ta gaishe dashi da aunty zee.
aliyu ya sauko yana ciccin magani kamar wanda aka yiwa wani laifi ya gaishe da mommy cike da girmamawa ta amsa masa cikin sakin fuska ita dai tana son Aliyu arayuwarta a natse yaja kujera ya zauna kusa da Samir aunty zee ta kalleshi fuskata dauke da murmushi tace "Aliyu gadanga kusar yaki an tashi lafiya "? " Lafiya ya amsa mata a takaice yana danne danne a wayarsa ita kam kisna bata ce masa komai ba illa matsawa daga gefensa da tayi ta samu guri kusa da mahaifiyarta ta tsaya dan bazata iya da balainsa ba, shi kuwa Samir ko kallon inda yake bai yi ba hakan kuwa yayi mugun dagawa Aliyu hankali ya dan saci kallon inda yake yaga ya balain hade rai kuma hankalinsa baya kansa yana wani guri zuciyarsa yaji yana rawa zai iya daukar fushin kowa a duniya amman banda samir shi din ajin farko ne a zuciyarsa da rayuwarsa ."
Abinci sun kai kala uku dake kan dinning table din duk aunty zee ce ta dafa , kisna ta zubawa kowa har uban gayya , babu Wanda mommy bata bawa aryan da areef kadan kadan sun ci ba , suna ci suna hira duk sanda aryan yayi kokarin bawa mommy labarin abinda ya faru jiya sai kisna tayi saurin kai lomar abinci bakinsa "ya fa koshi amman naga sai tura masa abinci kike kamar jira aryan yake mommy tayi magana ya kwa'be fuska tare da bu?e baki yana nunawa mommy abinci "ka koshi kou .."?ya gyada mata kanshi mommy ta janyo tissue ta tara a daidai bakinsa "zubar a ciki karki sake bashi komai cikinsa ya koshi "okay mommy ta cigaba da tsakurar abinci, ta kai spoon bakinta kenan taji aryan ya soma magana granny "yesterday when you not a round areef was shocked and papa ....
"Shut up wa tambayeka mai shegen surutun tsiya tayi maganar tare da kai hannunta zata buge masa baki zaraf taji an rike tsintsiyar hannunta tunda taji saukar hannu tasan shine take qirjinta ya shiga dokawa dan bata san abinda hakan zai janyo ba tsoro da matsanancin firgici ne ya ziyarce gaba-daya ilahirin jikinta,ta d'ago kyawawan idanunta ta zuba masa tana kallonsa fuskarshi babu walwala gashi ya ha?e rai kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa a hankali tayi kasa da kanta dan bazata iya jura kallon kwayar idanunshi ba yayinda har lokacin yake rike da tsintsitar hannunta yana hukuntata da idanunshi gabad'aya ta rikice saboda idanunsa dake yawo ajikinta cikin ?asaitacciyar muryarsa yace "don't ever try kisna Karki kuskura hannunki ya ta?a lafiyar jikin d'ana karya ya fada da kike ?o?arin dukansa "? A natse ta d'ago idanunta suna kallon juna ido cikin ido zuciyarsu na bugawa da karfi hankalinta yayi bala'in tashi bata son mommy ta san wani abu ya faru gashi yana ?o?arin fallasa komai tasan yayi haka ne dan mommy tayi mata fa?a yaji dadi "kana nufin shocking ne ya kama areef ta yaya hakan ya kasance "? mommy tayi magana hankalinta a matukar tashi tare da kamo areef din tana duba jikinsa take jikin kisna ya fara rawa ", Allah ne ya kikaye da tun jiya areef ya mutu bisa sakaci irin nata yanzu kuma aryan yayi magana tana ?o?arin dukansa nan ya kwashe komai ya fada momy ya karasa maganar yana numfasawa .."
Samir yace "ki kwantar da hankalinki mommy babu abinda ya samesa tun jiya ya ga doctor ayi masa duk abinda ya dace yayi maganar yana zabgawa Aliyu harara karaf idanun mommy ya sauka akan Samir "dan me zaka hararesa dan yayi magana idan kaine hakan ta faru killa sai kayi abinda ya fi nashi nan mommy ta dingawa kisna fa?a ta inda take shiga bata nan take fita ba ,momy ta kai hannunta ?aya ta daura akan hannun areef tana shafa tsintsiyar hannunsa , cikin rawar murya kisna tace "am sorry mumy banza sake ba dan Allah ku bar maganar nan haka wallahi ina jin kamar na mutu ta karasa maganar hawaye na wanke mata fuska ta mike da sauri zata bar gurin Samir yayi saurin kamo hannunta cikin nashi "ina kuma zaki koma kiyi zamanki babu mai sake miki fada akan yaranki wasu hawaye masu zafi suka zubo mata bazan iya cigaba da zama a nan ba gara kawai na kama kaina nice fa na haifi areef ta yaya zan yi abinda zai cutar dashi ko mahaukaciyar kan bola ce ni bazan cutar da d'ana ba ... ..'
Nan kuma jikin mommy yayi sanyi tayi shiru tare da daura hannunta akan dinnig table tayi tagumi tana Kallonta ganin yadda take kuka tun daga kasan zuciyarta yasa momy tace "shikenan kiyi hakuri amman kinsan kiyi kuskure ko "?"Nasani kuma na bada hakuri me kuma zanyi masa saboda Allah idan dai ba kasheni zai yi ba .... aryan ya matso kusa da momy ya rike hannuta gam kamar zai yi kuka saboda ganin kisna na zubar da hawaye "Am sorry mommy bazan sake ba stop crying I don't want to see your tears mommy please Ki daina kuka kinji granny kice ta daina kuka "zaki sha ice cream zan sa papa ya kai mu Ki sha ice cream kinji".
"kinga aryan ma hakuri yake baki yaranki suna matukar sonki sosai kiyi hakuri saboda su duk rarrashin da Samir da aryan ke faman mata , ha?e rai tayi taki yin dariya "me kike son ayi miki ki huce autar momy dan gaskiya bazamu barki haka cikin fushi ba , idan kika ki hakura nasan yau bamu ba ganin farar momy an tabo mata auta gabad'aya suka sa dariya har momy banda Aliyu da yayi bala'in bata rai jin furucin wai ya'yanta suna sonta shi kuma fa ko oho kenan "?
Fuskarta shimfide da murmushin jin dadi tace "zaku kaini gurin shakatawa "dan wannan ai mai sauki ne saki ranki yau ba sai gobe ba za'a kai ki duk inda kike so , dariya tayi Jin tautaunawarsu yasa aliyu ya mike ya koma kan doguwar kujera ya kwanta kasancewar weekend ne babu inda zashi samir yace "ranka shi dade sarkin zuciya kaji abinda uwar gida take bu?ata ya kamata ayi mata abinda take so yau tunda weekend ne " yayi maganar yana ha?e rai ha?e da harararsa kamar yace baza shi ba saboda kisna ce ta bukaci fitar amman bazai iya ba saboda Samir zai iya yin komai ga kuma uwar gayya mommy dake gurin ya kasa fadar haka yace "babu matsala idan kun shirya ka min magana kisna ta kwashe kwanuka da suka ci abinci ta shiga Kitchen ta dawo ta gyara dinning table ta sake komawa dan wanke kwanuka .."
Kowa ya watse parloun ya saura daga Aliyu sai Samir duk yadda Aliyu yayi kokarin son magana Samir yayi masa banza ya dauke masa wuta a karshe ma ya mike ya nufi kofar fita shima ya mike da sauri ya biyosa wata irin zufa na karyo masa a goshi tamkar wanda aka watsawa ruwan sanyi a daidai kofar shiga parlou'n Samir ya sha gabansa yana kallonsa yana furzar da iska ,a hankali ya kamo lip's dinsa na kasa yana cizawa yana cigaba da kallonsa ganin bashi da niyyar cewa wani abu Samir ya raba gefensa zai wuce ya sake taresa
"haba Samir mai yasa zaka min haka ? "Yanzu saboda kisna zaka juya min baya kenan kana jin zafin abinda nayi mata bayan kai sheida ne akan......"
Numfashi Samir ya sauke tare da katse masa hanzari ta hanyar cewa "Ba haka bane muradi wannan accedent din daya faru ba laifin kisna a ciki amman kaki ka daga mata kafa, karka manta hakan zai iya faruwa akanka akan kowa duk abinda zakawa kisna nawa ido ne amman akan wannan ko ba kisna kake aure ba zan ji babu dadi a raina , Aliyu ya kamo hannun Samir ya rike gam cikin nashi "to kayi hakuri kasan yadda zuciyata take idan raina ya ?aci am really sorry ka daina fushi dani zan iya jurar komai ban da fushinka rungumeshi Samir yayi ajikinsa yana sauke numfashi "kai ma kasan bazan iya dogon fushi da kai ba, jiya zuwa yau ne gobe da kaina zan nemeka suka sake juna suka karasa cikin parlou'n suna magana kasa kasa ."
A can sama kuwa , kisna da aunty zee sun kulle kansu a daki kisna na koro mata abinda ya faru d'azu "ina tsananin jin tsoron hukuncinsa , aunty zee ki taimakeni dan Allah ki tayani addu'a Allah ya bani ikon cin jarabawa , kiyi min nasiha  aunty zee ko zanji sanyi zuciyata na zafi kamar zata tarwatse  ta kamo hannunta  ta dauka daidai saitin zuciyarta  ,a matukar  fusace aunty zee tace mai yasa kisna bayan   kinsan  halin zuciyarsa  zai iya aikata komai  mai yasa  kika ce ya baki takardanki gaskiya baki kyauta min ba bana son kina yin haka mahakurci mawadaci fa ki daina biye masa dan shi abinda yake so kenan ya dagaki a gindin yaranki ya bawa wata"wallahi  don inji sanyi ne Kuma ai bazan sake ba "shikenan inshallahu Allah zai duba lamarin  "Ameeen  abinda nike so daga  gareki  kenan don Ina jinki aunty zee  a raina don Allah ki kwantar  mun da  hankili bani da natsuwa kawai dauriya nake ta karasa maganar hawaye na silalo mata "Kiyi mun nasiha irin Wanda Kika saba min Ki fada mun gaskiya komai  dacin ta a yanzu a shirye nake da amsar duk wata nasiharki ,
" Sannan Kiyi mun  addua
Wallahi nasan duniyan nan ba matabbata  bace don Allah ki gayamun  gaskiyan abunda ubangiji yace Koda Raina zai baci nafison ki gayamun  abunda zai sa in tsira duniya  da lahira Don Allah yar'uwata  karki barni a wannan lokacin Ina matukar  bukatan shawaran ki na gari Wanda zai anfane ni  plsssss "Kisna aunty zeey ta kirata a tsanake ta d'ago idanunta dake cike da ruwan hawaye ta zuba mata batare data amsa ba sai dai tattara hankalinta da natsuwarta gareta " Allah yace  idan  ya ?addara maka zaman  aure da mijinka ka rikeshi tsakani  da Allah kuma da zuciya kada ka cutar dashi kuma kada ka nufesa da mugun sharri ina miki nasiha kamar  yadda kika bukata ki zauna da  mijinki  tsakani da Allah Karki sake ganganci cewa ya sakeki 
Ki zauna dashi da zuciya domin shi kanshi furta sakin zunubi ne ki barshi shi yayita cewa zai sakeki  abinda kika sani duk matar da tace mijinta ya saketa Mala'iku rahma na tsine mata dan haka ina miki nasihan ki daina
" Insha Allah na Miki wannan alkawarin  na gode na gode yar'uwata " aunty zeey ta mike tsaye "ni zan wuce ki dan huta kafin lokacin fitarmu  yayi "anya zan iya fitar nan kuwa da ma barshi kawai ?
"baki da hankali dan Allah ki kwanta ki huta  kafin yamma tayi zan wuce dasu areef ma dan  karsu dameki ".
*****"
da yamma duk suka shirya kisna ma ta shirya cikin riga da siket wanda ya ?an kama jikinta ta d'aura abaya a saman kayan ta nad'e kanta da mayafin abayar ,tana tsaye gaban mirrow ya shigo d'akin  ya bude wardrobe dinsa kallo ?aya tayi masa ta ?auke kanta hankalinta ya rabu gida biyu wani naga mirrow wani na garesa ya dauki kayan da zai sauya ya rufe wordrobe ya shiga bathoroom ya sauya kaya ya fito ya tsaya a bayanta ta lumshe ido saboda saukar numfashinsa da taji a daidai saitin wuyanta ,ya dauki cumb ya hau gyara sumar kanshi bayan ya gama ya zuba mata ido ta cikin mirrow batare daya ce komai ba  jikinta ne ya bata ita yake kallo ta d'ago kanta a hankali idanunsu suka tsarke cikin juna sake matsota yayi sosai kamar zai hadeta da jikinsa take ta sadaukar da hakan ce zai faru sai dai abun mamaki taji yaja dogon tsaki ya zagayeta ya ajiye cumb din hannunsa  ya juya wani naunauyen ajiyar zuciya  ta sauke tana satar kallonsa tana  karasa shirinta har ya gama ya fita yana jan tsaki  , tana kokarin fitowa aunty zee ta shigo "wooooowwww gaskiya kinyi kyau sosai  "? Kyan banza tunda wanda akayi dominsa ma bai san ayi ba "karki damu ko bai furta ba yaji dadi bazai dai nuna miki bane kinga muje ke kadai ake jira ta riko hannuta suka fita .."
Kai tsaye *sharma sheik* suka nufa had'ad'd'en guri ne daya fi ko wani gurin shakatawa a kasar misra tsari da kyau ,guri ne wanda ko turawa idan sun kawo wa kasar ziyara nan suka fi hallarta saboda tsaruwansa ,duk wani abu na shakatawa akwai shi a gurin ,tunda suka shiga gurin aryan ya makale mata yayinda areef ke rungume a kafad'an Aliyu suka nufi wani bangare dabam dan shi babu inda bai sani ba aguri, yawon zuwan da yake ne ma suka ha?u da nawal .."
A hankali take rausaya wanda daman haka tafiyarta take aryan na rike da hannunta tana kallon yanayi gurin ,
mutane kala dabam dabam ne gurin kowa rayuwarsa yake babu ruwan wani dani har ta karaso inda aka kilance domin wasan yara ta shiga aryan na rike da hannuta gam yana ganin inda suka shigo murnarsa ta k'aru uwa uba hango lilo da yayi ,ya fixge hannunsa dake rike cikin nata ya kwasa aguje taku biyu tayi ta damko shi ta daga shi sama "zaka hau lilo ne babana "? Ya gyada mata kai alamun "eh .
"okay kabi a hankali zan kai ka da kaina kaji babana ya sake gyada mata kai sai dai jikinsa har rawa yake ya matsu basu karasa gurin lilon ba ,a natse ta karasa ta d'aurasa ya saki murmushin jin dadi wanda har fararen hakoransa da dumple dinsa suka bayyana, ya tafi suuuuuu ya sauka ya sake dawowa da gudu "mommy sake d'aurani " ta sake daukarsa ta d'aurashi tana sakar masa murmushi "mommy ina areef kije ki amso shi guri papa shi shima ya hau lilo "papa zai kawo shi karka damu yarona tana cikin magana ta jiyo kamshin turarensa ko bata d'ago kanta  ba tasan mammalakin kamshin dan haka taki d'agowa ta kamo hannu aryan tana jin sautin muryar areef yana kiran aryan amman taki tsayawa dan bata son tashin hankali tunda duk suka kasance sai yayi abinda ya bata mata rai  suka nufi wani guri ta tsaya hannunta daya  dafe da kafad'an aryan suna kallon larabawa ."
A hankali wani mutumi  ya zo ya tsaya kusa da kafad'anta wanda sauran ka?an kafadunsu ya hadu da juna ta waigo a hankali suka hada ido ya kashe mata idonsa daya "sannu ko " yayi magana cikin harshen larabci  saboda siffarta  gabad'aya ta nuna masa balarabiya ce ,  cikin sanyayyiyar muryarta tace " ban fahimci abinda kace ba cikin harshen Ingilishi   tana matsawa daga kusa dashi , jin abinda tace  ya sake motsata sosai kamar zai rungumota  "Masha Allah a she yar kasar ku ce  "ko zan iya sanin sunan malamar tun da kika shigo gurin nan naji kin kwanta min a rai ko zaki iya bani dama na mallaki zuciyarki "?a matukar frigice ta waiga bayanta ganin Aliyu bai gurin ta sake maida idanunta kanshi tare da cewa "no.." sannan ta bar gurin da sauri tana tafiya tana waigen bayanta kawai ta ji   tayi karo da mutun  a matukar firgice ta furkanci mutumin da suka yi karo ba kowa bane illa Aliyu gabanta yayi wani mahaukacin bugu ganin har   wayar hannunsa  ta subuce kasa tayi saurin dukuwa shima ya duka tana daura hannunta akan wayar hannunsa na sauka akan nata a tare suka d'ago suna kallon juna , qirjinsu ne ya  buga  a tare kusan second goma suna kallon juna kafin daga baya yayi saurin mikewa kamar wanda yaga mugun abu ,"bashi wayarsa muje ki bani minti biyu kacal ma ya  isheni ,damuwata nasan inda kike a matukar tsorace ta mike tsaye jikinsa na rawa ta mikawa aliyu wayarsa batare data yiwa mutumin magana ba, sai dai yanayin bugawar zuciyarta sai ya baka tsoro saboda da karfi yake bugawa jikinta sai rawa yake , kasa amsar wayar yayi ya kamo gefen lip's dinsa ya ciza da karfi yana kallon zara zaran yatsun kafafunsa sai areef ne yasa hannu ya amsa wayar ,kana ya kai dayan hannunsa ya yaja kumatun aryan yana masa murmushi ."
Aryan ya sakar masa murnushin shima "na hau lilo kace pa........Tun bai kai ga karasa maganar ba ta soma tafiya dashi , mutumin ya kasa biyota saboda ganin  kamar Aliyu  muradi ne tsaye a gabansa dan wasan kwallon  daya fi so a rayuwarsa kuma wanda duniya take ji dashi  siyansa ma sai kasa ta   shirya yana ?o?arin masa magana Aliyu  ya bar gurin babu shiri ya biyo  kisna yana mata magana jikinta da zuciyarta dake rawa yasa ta kasa saidashi sannan ta kasa tsayawa bare ta sheida masa matsayinta , bata tsaya a ko'ina ba sai a haraban gurin inda ta hango aunty zee da ya Samir jingine ajikinsa mota suna shan ice cream ta karasa gurinsu da sauri tana sauke numfashi "ke lafiyarki"? Aunty ta fada tana dubanta ta janyo hannunta aunty zee suka koma gefe "Kalli bayana zaki ga wani mutumi sanye da kaya ash colour"
"Eh na ganshi lafiya me ye hadinki dashi "?"Bina yake  wai na bashi address din inda nake ko na bashi number wayata kuma wallahi ya Aliyu ya ganshi ni tsoro nake ji Kar ya nuna min halinsa da rashin mutuncinsa a cikin mutane aunty zee dan Allah muyi mu bar gurin nan tsoro nake ji   ."
aunty zee tayi dariya " ya Aliyu yayi masa magana ne daya ganku"?
"Bai ce mana komai ba hasalima bai nuna ya damu ba "sharesa kawai ki kwantar da hankalinki ki cigaba da lamuran gabanki kema ki nuna ko ajikinki shi dake aurenki ma bai damu ba saboda me ke zaki damu ?" Dan Allah aunty zee wallahi tsoro nake ji  "Common  saki jikinki   dan daga nan ma shopping zamu  ina bukatar ?ananan kaya "dawowa sukayi gurin Samir "gulmar me kuka je kuka yi dan bakwai rabowa da gulma "? "kai kuma baka rabo da saka wa mutane ido ba suka yi dariya banda kisna data rasa natsuwarta Aliyu bai karaso gurin ba sai bayan minti goma ya fito yana taku kamar baya son taka kasa ya shiga mota batare da yayi musu magana ba yayiwa motar key "kai kai malam meye haka tafiya zakayi ka bar mu anan ko me kake nufi "?
Samir yayi magana tare da lekowa cikin motar "idan baku shigo ba zan wuce wallahi sanin halinsa yasa ya bu?e motar da sauri yana cewa" ku shigo muje wannan sarkin zuciyar ya hau sama ko wa ya kunnosa oho?.
jiki kisna a sanyaye ta shiga gidan baya idan aunty zee ke zaune hira Samir yake masa amman yayi masa banza aunty zeey tace "ranka shi dade dan allah ina son siyan wasu dogayen riguna .Aliyu bai ce mata komai ba sai gani tayi ya faka a bakin *kaafor mall* batare da yace uffan ba .
"muje kisna bani da abinda zan siya aunty " tayi magana muryarta can kasa "Ke dai muje ta bude bangaren da take ta fito suka shiga rike da hannun aryan ."
Samir yace Aliyu tun d'azu ina maka magana amman ka shareni me yasa kake takurawa rayuwarka ne kana son kisna me yasa bazaka manta komai kuyi rayuwarku ba tsaki yaja "dan Allah karka daga min hankali banason damuwa " malam ka bada kai bori ya hau kaima ka dinga shiga sawun ........
"Please Samir mai yasa har yanzu ka kasa fahimtata ne ?sanin kanka ne soyayya bata gabana ko nawal daka ga zan aura tausayi ne yasa zan aureta ba wai soyayya ba, idan kuma soyayyar zanyi kisna bata cikin jerin matan da zan iya so kayi hakuri idan maganata ta maka ciwo "
Tsaki Samir ya ja "dadina da kai wallahi taurin kai kamar mutanen farko yarinya tana sonka yanzu ka bata dama kaki " takaici ya rufewa Aliyu zuciya ya bude murfin kofa da karfi  ya fito a kufule tare da saba areef a kafad'ansa Samir ya biyo bayansa yana cewa "gaskiya lamarinka akwai gyara  ana gabas kana yamma  kana bukatar addu'a Allah zan fadawa momy ta mike tsaye a samu ka soma soyayya  "dan Allah ka rabani da batun soyayyar nan bani da lokacinta ...."
Cikin mall din suka shiga kai tsaye Aliyu yayi layin takalman yara suna tafiya suna hira da Samir har suka karaso kusa dasu aunty zee, muryarsa tasa ta jujowa idanunta ya sauka akan Samir "baby ta kira sunansa ya waigo da hannu tayi masa alamar yazo ya karaso ya tsaya a bayanta tare da daura kanshi a kafadanta "ta yani zabar kanana kaya kema kisna Ki zabi wanda kike so yayanki ya biya ,kananan kaya masu yawan gaske da dogayen riguna masu kyau ta dinga ?auka ,duk abinda ta gani indai ya burgeta sai ta ?auka ganin kisna ta ki ?aukar komai ,yasa ta dinga zabar mata bom short da riguna masu kyau wanda zasu dauki hankalin mijinta sannan suka kara gaba suka bar kisna dake tsaye rike da hannun aryan kamar ance ta juya bayanta idanunta ya sauka akan mutumin d'azu yana tsaye rungume da hannuwansa duka a qirji ,tsura masa ido tayi tana kallonsa mutun kamar aljani har zata bar gurin taga gara kawai ta tsaya ta fada masa gaskiyar ita din matar aure ce ya daina binta a hankali ya karaso ya tsaya a gabanta yana kare mata Kallon tsab irin typing din matar da yake so ce ya dade yana neman irinta bai samu ba sai yau sautin muryarsa taji ta doki kunneta "tunda nake arayuwata ban taba ganin halittar data ?auki hankali ba irinki dan Allah kibani dama na zamo abokin rayuwarki, farinciki da bakinciki ne suka hade mata a lokaci daya ,ga mijinta na tsananin nuna mata kiyayya ,ga wani na mata naci ta so shi wanda a yan sakonin da suka gabata ya daura idonsa akanta batare da yasan ko ita din wacece ba ."
Ta tsuke karamin bakinta gashi dai  magana take son yi  amman ta kasa sarrafa harshenta kawai ta juya zata wuce yayi saurin shan gabanta " ki tsaya ki fa?a min sunanki da address din inda kike kafin ki wuce dan bazan bari ki subuce min ba saboda  na dade ina nema irinki  ...."??
Mmn sudais
????????????
  CUTAR DA KAI
     ????????
????????????
Free page 13
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ?aya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...????
 

Please Login or Register in order to submit comment