Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi tunfil-azal ba mutum ne me son ruwan sama ya dake shi ba......Ta jima tsaye a parlon tana kuka kafin ta lalla'ba ta shige nata bedroom ta hau cire kayan jikinta ta daura towel ta nufi bandakin, to kafin tayi wankan ma sai da taci kuka ta koshi kana ta fito kanta nayi mata wani irin bala'in ciwo mara misali, tana kuka taje ta kudundune jikinta da bargo, tana rufe idonta......Shigowarsa dakin ya sanya ta mike zaune da sauri tana matsawa lokon gado dan tana ganin kamar zai daketa ne ko yayi mata wata illar mugun tsoronsa takeji tunda ta lura idan ranshi ya 'baci bai iya hukunci ba.

Kayan sanyi ya sanya a jikinsa masu kauri kanshi sanye da hular sanyi ya rufe har kunnanshi mugun sanyi yake ji mai shiga jiki ga zazza'bi na damunshi haka kawai ta janyo masa lalura.

Kafin yace komai ta soma kuka tana d'ad'daga hannuwanta sama da fad'in"Don Allah kayi hakuri wallahi ni babu ruwana, dama shin......Kasa karasa maganar tayi ta hau inda inda tana rawar baki." Ya zuba mata idanunsa yana kallonta fuskarshi babu walwala ko ta kwabo, yace."Ki nitsu ki daina wannam firgice firgicen da kikeyi." Hannunta tasa ta rufe bakinta hawaye na ambaliya a fuskarta, ya zauna gefan gadon yana kallonta har sanda ta dan samu nutsuwa, Kawai taji sautin muryarshi yana fad'in"Me kuka shirya akaina ke da mutanan naki? Kuna so ku kasheni ko.'!? Tayi saurin kallonshi tana girgixa kanta......Yace."Hakane mana." " Wallahi ba haka bane." Yace."To naji, Ina zaki bi As kike gudu."? Sai hawaye ya soma shatata! yace."Ba kuka nace kiyi min ba." Tayi shiru tana kallonshi, yace."Kiyi min bayani dallah dallah kan a'lamarin.'' Tayi shiru tana me sunkuyar da kanta kasa! Tsawa ya buga mata yace."Zazzabi nakeji a jikina yi min bayani abinda nace ba kuka nace ki min ba." bakinta na rawa ta shiga wassafa masa yanda suka tsara ita da As da yanda in ta kufce daga hannunsa zasu gudu fataskum sannan kuma ta kaishi kotu shi da mai allo kana idan al'kali ya raba auransu ta dawo ta cigaba da harkokinta, Ya dinga kallonta yana girgiza kanshi, Mahaifiyarta bata da hankali ko d'an! abinda yake ayyanawa kenan cikin ranshi, to idan ba rashin hankali ba me zai sanya ki zauna kina tsarawa 'yarki shirme da abinda zai cuceta har ta dinga kokarin kashe mata aure, amma babu komai shi ya san abinda zaiyi musu.

"Na yarda babu abinda ke damunki sai jahilci da da'kikanci! Allah yayi miki suttura kina nema ki butulce masa, me nayi miki? me kuma me allo yayi miki da har kike nufin tozarta mu ki kaimu gaban al'kali! kan anyi miki alkairi ke zaki mayar da sharri! ko da yake tarbiyace baki samu ba tun farko ku kusa ko alama ni bana ganin laifin Kawunki saboda yayi iya bakin kokarinshi a kanku, k

eda 'yar uwarki da ita kanta 'Yar uwar taki! amma dake keda da maman taki duk taron mahaukatane kuna adawa dashi Okey ni Ahamdu mutukar na cika d'an halak! sai nayi muku abinda kuke bukata, kafin ki tozartani ni zan tozartaki! Ni Ahamdu ba'ayi min na bari! idan kinga na bar abu nine nayi niyyar bari, Yau zaki gane asalin waye ni."!!!!

Kuka take sosai tana fad'in"Don Allah dan annabi kayi hakuri wallahi kuskure nayi kuma bazan 'kara ba nayi nadama ni na hakura ma da komai zan zauna da kai nasan kai mai kaunata ne tunda har ka ceto ni lokacin dana fad'a ruwa nagane rayuwa ba'a bakin komai take ba."

Yace."Tubanki na banxa ne Siyasar banga da Jagaliya kike so kiyi to zan baki lasisi a hannunki." Yana gama maganarshi yasa kai ya fice daga dakin." Ta kwanta tare da takure jikinta tana ta kuka da makyayatar jiki.

A daran ya kira dr Nasir yazo ya danyi mishi treatment ya bashi maganguna dan zazzabi da mura mai karfi ce ta kamashi, abinci yaci yasha magani kana ya shige bedroom dinshi ya rufe yayi kwanciyarshi akwai bacci me nauyi ya daukeshi.

Yanda taga dare haka taga rana, lokaci zuwa lokaci gabanta na wata irin faduwa, idanununta sun kada sunyi jawur tsabar kuka da damuwa da kuma tsananin zazzabi da ciwon kan dake damunta...........Asubah nayi taje tayo alwala ta fito ta duba doguwar riga mai hula mai dan nauyi tasa a jikinta kana ta tayar da sallah......Kwanciya tayi kan dadduma tana lumshe ido bacci mai dad'i yana fuzgarta, ya turo kofar dakin ya shigo, a zabure! ta mi'ke zaune tana gyara zaman hijab dinta da ya karkace.......Yana sanye da jallabiya fara tas da ita har yanzu kanshi na sunkufe da hular sanyi har kunnanshi kafafunshi ma safuna ne farare ya iske inda take zaune kanta a kasa tana watsa da 'yan yatsunta! Hannunsa guda dake cikin aljuhunsa ya zaro ya fito da wata takarda fara a nannad'e ya mi'ka mata......Dake kanta a 'kas! yake bata ankara ba sai da yace."'Kar'ba." tayi saurin d'agowa tana kallon hannunshi, gabanta yayi wani irin bugu! Innallihi wa'ina ilahi raji'un! Sai le'bubanta suka soma rawa suna had'uwa!!! "M....me zan kar'ba." Tafada tana kallonsa da gwala gwala idanunta da suka gaji da kuka." Kai tsaye yace."Abinda kike bukata ne nayi miki."! Sai hawaye ya wanke mata fuska! ta sa hannunta dake karkarwa ta kar'bi takardar! Shi kuma ya kama hanya ya fice daga d'akin......Kasa bude takadar tayi ta ajiyeta a gabanta ta 'kura mata ido le'banta sai rawa yake had'e da jikinta cikin ranta take fad'in "Ubangiji Allah yasa mutumin nan ba sakina yayi ba a lokacin da nayi nadama nake sha'awar zama dashi." Ihu! ta kurma bayan ta warware takardar ta karanta abinda ke ciki.

_Ni Ahmadu Musa Na saki matata Wasila saki d'aya idan ta samu miji tayi aure_

A sukwane ta bud'e 'kofar dakin ta fice palor hannunta rike da takardar tana gurshen kuka ta nufi dakin shi, lokacin yana 'balle magani zai sha kawai ta afko dakin......Kafafunshi taje ta rirrike tana kuka da shashsheka! "Dan girman Allah kada kayi mun haka! Wallahi nayi nadama bazan sake ba, zan zauna da kai bisa amana, ka mai dani dakina kar muyi haka da kai."!!! Baice mata uffan ba ya afa maganin abakinshi ya kora da ruwa ya aje goran ruwan kan bedside kana ya kalleta duk tayi wujiga wujiga! har wata 'yar rama tayi tsakanin jiya da yau d'in ga kuma alamun tashin hankali da fargaba da nadama nan a tare da ita, Yace." Lokaci ya 'kure miki ai bakiji abinda nace bane ? Idan kin samu miji kiyi aure Ahmadu ya barki har abadah."! Sai ta sake shi tana masa wani irin kallo! kamar zauntacciya tace"Wallahi babu inda zanje ina cikin gidana ni bana son saki ai kaine ka kar'be min budurcina kuma sannan zaka mayar dani 'karamar bazawara da 'kananun shekaruna, ni babu inda xanje dan ni ba bazawara bace kuma ni bani da wani miji idan ba kai ba.........Yayi bala'in shan kunu yana sake tamke fuska yace."Tun wuri ki kwashe duk wani abu da kika san naki ne a gidanan ki fice min a gida minti talatin na baki wallahi idan ba haka zan sanya su Garba suyi miki rashin mutunci sai kin fita da kwayayyar fata kamar yanda 'kawarki ta fita dashi."
Bubbuga 'kafafunta ta shiga a 'kasan dakin ta

na yayyaga takardar sakin tana kuka wiwi da majina da hawaye sun had'e a fuskarta tana fad'in"Ni ban saku ba, babu inda zanje wallahi ba zaka mayar dani bazawara ba." Sosai ya shiga mamakinta da maganar ta wai ba zai mayar da ita bazawara ba ashe tana kishin kanta haka? amma kuma take neman saki da kanta har da ikirarin shiga kuto gashi kuma an saketa anyi mata yanda take so tana nadama! Tabbas bakin al'kalami ya riga ya bushe yanda yayi rantsuwa a kan ya gama zama da ita har abada ya gama taje ta 'karata da ba'kin halinta.

Da ta dameshi da kuka ya mike a zafafe! yana zare mata ido! bata tsorata ba sai ma sake gyara zamanta da tayi a dakin tana takurewa, yaje ya hau janta domin ta fice masa daga dakin kukanta na damun 'kwalkwarshi! Nan fa d'aya! labule ta kama ta rik'e tsam! tana turjewa wai ba zata fita ba......Ya kwad'a mata lafiyayyan marin da yasa taga gilmawar taurari a idanunta! Shouting dinsa taji a kunnenta yana fad'in" Kin fi son muyi irin wannan rabuwar ko okey......Janta ya so mayi ta rike 'kafar gado tana kuka da fad'in "Nayi nadama ba zan sake ba ni babu inda zani nan ne gidan mijina."! Sosai ta rike kafar gadon ta'ki saki! Kawai ya tattaro ta gabadaya ya dauketa bai dire ta ko ina ba sai palo, yana kokarin juyawa ta rike masa kafafu! Yau yaga jaraba da naci da 'kulafuci!! Fuzge kafarshi yayi yana jan tsaki! ya koma dakinshi, Ranshi idan yayi dubu ya 'baci.....Ita kuwa bayan shigewar sa dakin kwanciya tayi kasan carpet tana wani irin kuka da kiran mutuwa tazo ta dauketa ta huta da wannan kad'arar data afka mata.







Littafin na kudi ne....!
Kika fitar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
alliya:
'Yr Bngr Sys
*49*
Kofar dakin nashi ta tsirawa ido tana daga inda take kwance hawaye sai zurara yake daga idanunta, shikkenan ta cuci kanta! shikkenan ta tashi daga budurwa ta koma bazawara! abinda ke tayi mata yawo kenan a kwakwalwarta! Wani sashe na zuciyarta yake kara tunasar da ita abinda ta manta, itace fa take so a saketa kuma yanzu murna ya kamata tayi ba kuka ba, da ba tayi wannan tunanin ba sai yanzu? Hawaye ya sake kece mata, sam ba tayi wannan tunanin ba sai yanzu da Allah ya jarrabeta da son auran take tunanin zawarci! mikewa tayi xaune tana goge hawayen fuskarta palon take bi da kallo tana 'kissima abubuwa da yawa, Dole ne ta nemawa kanta mafita, dan daga yanzu ta daina daukar hud'ubar mahaifiyarta a ganinta duk itace ta ingizata fadawa wannan halin, zawarci da kuruciyarta, yanzu ta daina ganin laifin Rashida gashinan Allah ya nuna mata gaskiya tun kafin ayi nisa, Hotonshi dake manne a wata kusurwa ta dakin ta zubawa ido! hawaye masu zafi suka sake yanke mata, wani irin bala'in sonsa taji sabo na ratsa zuciyarta, ta mike ta isa inda hoton yake tana kallonsa, yana zaune kan wata had'addiyar kujera sanye da farar shadda! sai murmushi yake yi! tsayin ta ba zai kai inda hoton yake ba tana so ta dauko ta kasa, sai ta kura mishi ido tana fad'in "Tunda ka sakeni dole na tafi na bar maka gidanka! nayi nadamar abinda nayi maka! ba'a hada baki dani ba akan a cutar da kai kamar yanda kake zargina! kawai nima shaidan ne ya zugani amma yanzu nagane abunda kake so ka gane! zan tafi in bar maka gidan ka tunda ka saken.......! sai ta kasa karasawa ta zube a gurin tana dukan kujera hade da wani irin kuka mai cin rai!!! kimanin minti goma tana cikin wannan halin kafin ta mike zumbur! ta nufi dakinta, Wani tunani tayi a yanzu dai babu mai sasanta al'amarin nan sai mai allo shine zai shiga cikin maganar yasa Ahamadu ya mai da ita.
Ta dauki karamar jaka ta zuba kayanta, wayoyin da ya siya mata tun jiya ta mantasu a motarshi, hakan bai dame ta ba a yanzu, hijab din da take sallah ta zura ta fito tana goge hawaye, kofar dakin shi ta kalla har yanzu tananan a kulle, taji zuciyarta ta sake karyawa, tabbas ya nuna mata shi din dan halak ne! sam bata ta'ba tsammanin zai saketa kaitsaye ba sai gashi tun bata dangana shi da al'kali ba ya yanka mata ticket, ta bude kofar palon ta fita zuciyarta na tsananin harbawa, shikkenan duk wannan daula da jin dad'in sun zama labari Shikkenan duk uwar soyayyar da yake mata lokacin da suke marking love ta yanke, ta sanya hannu ta share hawaye tana tuno irin rayuwar jin dadin da suka dingayi yanda suke soyayya suna jiyar da kansu dadi! kuka tasa tana girgiza kanta haka nufi bakin gate ta kasa tsaida hawayen fuskarta yanzu idan Ahmdu bai mai da ita ba wace irin rayuwa za tayi........Dukaninsu sunyi mamakin ganinta da jakar kaya tana kuka, Garba ya hana abude mata kofa ta fita yace dole sai ya sanar da mai gida....Ta tsaya gefe tana goge fuska tana addua Allah yasa idan yazo ya tausaya mata yace ta koma gidan......Ya kirahi a waya lokacin baccinsa baiyi nisa ba sosai ya daga wayar Garba yay masa bayanin abinda ke faruwa. Kai tsaye yace."Ku bude mata kofa kuma kabi bayanta kaga ina ta nufa." Garba yace."Shikkenan yallabai." Kashe wayar yay yace su bude mata kofar, Jikinta a sanyaye taja jakarta ta fita daga gidan......Garba sai da ya dai-daici ta fita babban titi kana yabi bayanta, aikuwa yaga tana tare abin hawa! shima ya tare ya shiga yace da direban ya bi bayan babur din dake gabanshi duk inda yayi, haka kuwa akaiyi, Wasila ta sauka a bakin titi ta biya me babur kudinshi ta ganganra domun shiga Estete din da gidanta ke ciki, Garba na biye da bayanta bata sani ba. Sai bayan yaga shigarta gidan ne ya kira wayar Ahamdu ya sanar mishi da cewar ga inda taje Yace."shikkenan kyaleta kawai ka dawo gida." Garba ya mai da wayarshi aljihu ya bar bakin gate din.
[8/8, 12:03 PM] .: Uwani Camas! Rashida na zaune suna karyawa Wasila ta tura kofa ta shiga, dukaninsu suka maida hankalinsu kofar shigowa, kawai suka ga Wasila ta shigo fuskarta a jeme idanunta yayi wani irin ja! sun kara girma ga fuskarta ta nuna al

amun tashin hankali da nadama gami da dana sani! Da sauri Uwani ta mike tsaye tana fad'in" Yaya na ganki haka? Cikin damuwa yanzu dama muke maganarki ina cewa kiyi maza maza kizo mu taf.......Kafin ta 'karasa maganar dake bakinta taga Wasilan ta zube tsakiyar dakin tana kuka hade da dafe kanta tare da fad'in"Na shiga uku na lalace."!!! Uwani gabanta ya yanke ya fad'i sai ta dur'kushe gaban 'yar tata tana karkarwar jiki ta rirri'kota jikinta tana tambayar ta abinda ya faru!!! Wasila ta shiga tutture ta tana shashshekar kuka da fad'in "Kece kika jawo min wannan masifar duk wani wahala da zan shiga a rayuwa ta kece!!!!! Uwani taji wani gumi ya tsinke mata! Wai shine meke faruwa ne? Rashida da Camas! suka iso inda take durkushe tana kuka! Kawai sai ta kama Rashida ta rungume 'kam!'kam! tana wani irin kuka.! Rashida taji zuciyarta ta karye itama sai ta soma kuka tana tambayar ta abinda ya faru!! Cikin hard'addiyar magana tace"Rashida ya sakeni! Ahmadu ya sakeni!! ya sakeni Rashida na gane abinda kike ta so nagane yanzu Uwani ta cuceni na cuci kaina innalilihi wa'ina ilaihi raji'un"! Da jin wannan maganar dake fitowa daga bakin Wasila sai kawai Uwani taja tsaki tana fad'in" To sai me? dan ya sakeki? dama ai haka muke bukata bai wahalar da kanshi ba bai wahalar damu da sharia ba, dan haka sai muji dadin yin harkokinmu cikin kwanciyar hankali, ni wallahi na dauka ma ko wani abun yayi miki ko kuma zakice kina da ciki shiyasa ma hankalina ya tashi." Wasila ta d'ago kanta tana kallon Uwani sai ta hau girgiza kanta takaici da bakin ciki fal ranta, Wai Mahaifiyarta ce ke murna da mutuwar auranta dan dai bata san yanda takejin bakin ciki bane cikin zuciyarta......Bakinta na kyarma! tace"Uwani murna kikeyi da mutuwar aurana."? Uwani ta kalleta cike da mamaki tace"To ai abun murna ne abinda muke nema ne fa ya samu to meye zaki damu kanki.

Ta hadiye wani kutun bakin ciki da ya tokare mata a makoshi, tace"Nayi nadama nayi dana sani Yanzu nagane abinda 'Yar uwata keso na gane, dakin mijina shine suttura a gareni daku baki daya! Na gane duniya ba matabbata bace, a jiya dani daku da As mun nufi Ahmadu sharri sai Allah ya mayar dashi kanmu, idan da da 'karar kwana da sai da a tsinci gawata a wani gari ruwa ya tafi dani, nan ta shiga warware musu abinda ya faru da ita jiya da irin taimakon da Ahamdun yayi mata, Uwani taja tsaki da fadin"To sai me dan ya fito dake daga ruwa aiko bai fito dake ba, idan Allah yasa zaki rayu zaki rayu....Wasila nifa bana sonki da wannn mutumin tunda bai san mutuncina ba bai ganina da daraja da mutunci, Yafi daukar wancan munafikin mutumin da daraja, sabida haka na tsani tarayyarku ke dashi wannan sakin da yayi miki shine dai-dai ni a gurina Nasan ke ba karamar mace bace zaki samu wanda ya fishi ki aura."

Hawayen dake fuskarta tagoge tace"Uwani wai me yasa kike da ri'ko ne!? ki rabamu da dangin mahaifinmu saboda tsananin rikonki sannan kin sanyamu muyi musu rashin kunya kawai saboda ra'ayinki kin hanamu muje inda suke komai mai allo yayi mana mun yafe mishi kuma ni yanzu na daina ganin laifinsa a kanmu tunda muma ai bamu ganin kimarshi muna mishi fitsara da rashin kunya shiyasa ya kyalemu kuma sau nawa yana daukarmu kina zugamu mu gudo gida.....Ni yanzu shi kadai ne gatana shi zan nema domin ya sasanta ni da mijina domin hauwasa nacewa ta inda aka hau tanan ake sauka."

Uwani ta mike tsaye! ranta idan yayi dubu ya 'baci tace"Wasila idan kika saka kafa kikeje gurin wannan mutumin to wallahi ban yafe miki ba! mutukar nice na haifeki naci wahalarki kikaje gurin makiyina ban yafe ba, Saboda baki da hankali har zaki kirani mai riko meye banyi muku ba keda "yar uwarki shine har kike kokarin fifita Kawunki a kaina to na fada miki kikaje Garko gurin mai allo sai na tsine miki kin bi duniya." Wasila da Rashida suka fashe da kuka jin abinda Uwani ke fada, zagi ta uwa ta uba takeyi wa mai allo daga karshe ma fashewa tayi da kuka ta shige daki........Camas! dake tsaye ta kalli Wasila tace"Nifa wallahi banga abinda damuwa ba dan ya sake ki Haba kawata kamar ba kece wacce na sani ba shin wai me ma Ahmadu nan yake dashi ne

? Kawai ki watsar dashi ki cigaba da harkokin ai kamar yanda Uwani tafada wallahi sai kin samu wanda ya fishi kudi kyau mukami da sauran jin dadin duniya kefa matar manya ce."

Wasila ta shiga girguza kanta bakin cikin duniya ya taru yayi mata yawa! Wai jama'a me uwani take so da itane shikkenan tunda tace bata yafe ba idan taje gurin mai allo ta amince da hakan zata zauna a gida amma kuma sai ta nemi mai ciyar da ita, Bayan haka kuma tayi al'kawarin har abada ta bar harkar jagaliya zata zauna ta killace kanta a gida.....Tace"Camas! dole fa naji ciwo mutuwar aure babu dadi wallahi ban san ina son mutumin ba sai da haka ta kasance dani, kina maganar zan sake samun wanda ya fishi ni bana fata nafi so kawai na koma dakina." Camas! tace."Yanzu dai kina nufin kin bar Siyasa kenan."? Tace"Kwarai kuwa na bar wannan harkar abadah." Uwani tace"Baki isa ba wallahi! Waye zai dinga daukar dawainiyarmu." Wasila ta kalleta sosai tana nazarin maganarta, tace"Uwani kinga ni bana son ki d'aga min hankali tunda kin hanani zuwa gurin kawuna shikkenan maganar dawainiya kuwa kowa yayi dawainiya da kanshi, wannan gidan ma da muke ciki kada ki sanya ranki zaki dawwama a cikinsa, domin har yanzu governor bai bani takardar shi ba, da ko wane lokaci yana iya tashinmu mussaman idan yaji hukuncin dana yanke, saboda haka dake da Rashidan kowa ya nemi mafita, kada kuma kiyi la'akari da cewar ina da kudi a banki, kudina basu da wani yawa nima zan nemi wata sana ar ne."
Uwani tace"Ai ba lallai sai siyasa zakiyi ba akwai sana'oi da zaki ki samu kudin da zaki cigaba da daukar nauyinmu saboda haka kije kiyi shawara ni dai na fada miki ban amince ki koma gidan wannan mutumi ba kuma ban amince kije gurin wannan dattijon banzan ba." Tsabar bakin ciki da takaici bai bar Wasila tace komai ba idan ta fahimci maganar Uwani tana so ne ta turata d'aya sana'ar da tuntuni take so tayi ita kuma ta ta'kiyi (karuwanci) Mikewa kawai tayi ta shige daki ta barsu suna surutu Har dai Fada ya hard'e tsakanin Rashida da Camas! domin dai Camas! ita ke kara inginza Uwani tana sake baud'ewa! Yayin da Rashida ta fahimci haka sai ta hau cuccusawa Camas! ashar tana fad'in ta fice ta bar musu gida su dai Allah yasa sun gane gaskiya kuma karuwanci insha Allahu ba zasuyi ba, ita dai tunda ta dauki karuwanci sana'a to taje tayi! Camas! ta rataya jakarta ta fice daga gidan bayan sun gama zage zage da Rashida.







Littafin na kudi ne......!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*alliya:
'Yr Bngr Sys
*50*

As ne zaune a tsakanin 'yan sanda sai zare ido yakeyi rigar jikinsa duk tayi jirwaye fuskarsa duk tayi burd'in burd'in da cizon saura idanunsa sunyi jawur! fuskarsa ta kara baki sai maikon yake yi tamkar wanda rana ta daka!......."Yanzu Yallabai tinda kace baka son kowa yaji maganar nan daga mu sai kai sai kuma Ahmadu to mun amince zamu rufa maka asiri amma tare da alkawarin muma zaka yi mana ihisani baka so sunanka ya 'baci a gari mutane suyi maka kallon kwarto manemin matan mutane to zamu lullube sirrinka baza mu watsa a media ba muna so muji nawa zaka biyamu." As yace."Ku fadi ko nawa ne wallahi zan baku bana so Ahamadu yazo gurin nan ya sameni saboda nasan karon mu dashi ba zaiyi kyau ba, kuma ni ku daina zargin na nemi matarshi harkar siyasarmu ce ta hadamu da ita ba wani abun ba." dan sandan yace."Ka daina maganar Ahmadu domin tuntuni mun kirashi a waya ya tabbatar mana da cewar mu sake ka saboda bashi da lokacin ka, yanzu tsakaninmu da kai ne." As ya sauke ajiyar zuciya yana jin sanyi cikin ranshi yaji dadi sosai da Ahmadu bai tona asirin abinda ke faruwa ba.....As yace."Nace ku fadi ko nawa kuke bukata zan baku." Babban cikinsu yace "Za bamu miliyan hamsin." As ya zare ido yana kallonshi. Ba zaku samu miliyan hamsin ba yanzu." Dan sandan yace."Ashe kuwa kana so muyi maka tonan silili." As yace."Bana so kuyi min tonan silili wallahi zan duba nagani amma dai yanzu zan fara sa muku miliyan talatin daga baya sai na cika muku sauran." Sukace Su basu yarda ba As ya shiga tunanin ina zai samu kudi cash a hannunshi duk kudinshi yana siyan filaye ne da gidaje da gonaki! yanzu duka kudin accont dinshi basu fi miliyan saba'in ba dama yana sanya rai kan governor zai bashi wata kwangila to anan yake so yayi cuwa-cuwar shi, wata shawara ce ta fad'o masa yace."kuyi hakuri ku kar'bi! Miliyan talatin nayi muku al'kawari nan da sati biyu zan baku ashirin din." Sukayi a rubuce ta da sharadin idan bai cika musu ba sun shirya tsaf zasu tozarta shi.
Ya mike yana karkade rigarshi ya dauki hularsa yasa kana daya daga cikin 'yan sandan ya daukeshi a mota ya kaishi gidanshi, dake Tarauni.


Bacci yayi mara dad'i mai cike da mafarkai marasa dadi, sai wajejen azuhur ya tashi yay wanka ya fito damuwa fal cikin ranshi, bayan yay sallah ya dauki waya ya kira Khalifa tare da shaida masa cewar yazo gidanshi yana son zasuyi magana! Hausawa sukace abokin kuka shi ake fadawa mutuwa.....Baici wani abincin kirki ba, ya kwanta a kan kujera yana duba wayarshi, nan yay ta ganin numbers din mutane da rocuding din Wasila da As duk wani magana da Wasila keyi da As da Camas sai da ya gani dake wayarshi tana adana mishi abubuwa koda kuwa ya goge su, Al'amarin yayi ta bashi mamaki! ashe haka yarinyar nan tayi nisa, dama duk sanda ta dauki wayarshi abinda takeyi kenan! sosai ya dinga mamakin hatsabibancin ta, yana ganin rabuwa da ita shine yafi al'kairi a rayuwarshi.....Amma kuma har yanzu yana jin wani irin tsunkuli da zuciyarsa takeyi masa mussaman idan ya tuna da abubuwan da suka faru a tsakaninsa da ita a cikin zamantakewar

Please Login or Register in order to submit comment