Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuce shi ya tari gabanta.
Sai ta 'bata fuska tana kallonshi......Shima fuska a 'bace yace."Me yasa kika sauya halinki? wane dalili ne ya sanya duk sanda na shigo dakin nan kike 'bata rai idan na zauna kusa dake ki sanja guri idan na rike hannuki ki saka min kuka meke faruwa dakene."?

Murya a sanyaye tace"Babu komai." Ya had'e ranshi sosai yace."Bana son 'karya ki fad'a min dalilin da ya sanya kike gudana ko zugaki akeyi ne."? Tayi saurin kallonshi......Yace." 'Kwarai kuwa ai da ba haka kike ba cikin 'yan kwanakin nan kika sauya d'abi'u dole ne nayi zargin ko zugaki ake."

Sai ta tsargu! ta dinga kallonsa tana son tayi magana! Sam bata so ya zargi Innarta dan tana so ya cigaba da ganin mutuncinta kamar yanda yake gani ba zata so ya gane cewar Inna Hajara ce ke zugata ba........Tace"Ni babu wanda yake zugani kawai dai ina ganin kamar be dace ba ace muna had'uwa a d'aki ni da kai saboda banyi ar'bain ba."

Ya dinga kallonta yana mamakin maganarta akwai kuruciya da rashin wayo a tare da ita, wannan maganar da takeyi sam bata da tushe ballanta makama kuma ba tunaninta bane, yasan innarta ce ke zugata.

A d'an kausashe! yace." A cikin wane littafin addini ki kaji ance dan mace ta haihu shikkenan ita da mijinta sai ranar da tayi ar'bain? wannan magana da ki keyi irin ta jahilai ce ba'ace dan kin haihu shikkenn sai ki dinga gudun mijinki ba! Ni ba yaro bane na kuma gane abinda kike gudu shiyasa nace wannan abinda ki keyi ba tunaninki bane zugaki akeyi kuma duk me zugaki zata kaiki ta baro ne Ko yau idan nayi ra'ayi zan iya shigowa d'akin nan na kwana tare dake dama ba'ace lallai ki kwana da wata ba ni zan iya kula dake da yarinyata." Yanda yake maganar ne yasa ta gane ranshi a 'bace yake sosai to itama ranta ya 'baci sosai jin yana 'kokarin cin fuskar Innarta a gabanta zuwa yanzu ta gane ya gane cewar Inna hajara ce ke zugata.
Murya na rawa tace"Inna Hajara kake kira da jahila kada ka manta fa a matsayin uwa take a gurina tunda kanwar mahaifina ce." Idanunsa tsaye a kanta yace."Ni da bakina kinji na zageta ko na ambaci sunanta nace da ita jahila." ? sunkuyar da kanta tayi tana kokarin mayar da kwallar dake kokarin zubo mata Tace."Ai ka gane itace shiyasa kake kokarin fad'a mata ba'kar magana a gabana to meye laifinta ai gyara kayan ka baya hana sauke mu raba." Murmushin takaici ne a fuskarsa ya bud'e baki kenan zaiyi magana zuruf Inna Hajar

a ta turo 'kofar d'akin ta shigo kafad'arta sa'be da baby zahra tana fad'in ''Kina ina ne Wasila zo maza kar'beta ki bata nono kada ta fara wannan kukan nata." Duk suka juya suna kallonta tana tsaye a bakin 'kofar shigowa..........Jikinta ne kuma yayi sanyi ganinsu kamar suna cikin 'bacin rai dan ta lura da Wasilan ma kamar kuka take, sai tayi maza ta juya zata futa tana fad'in "A'a Alaji ashe baka fito ba." Yay saurin 'karasawa inda take yana fad'in "Yanzu zan fito Inna bani ita mu gaisa." Ya mi'ka hannunsa ya 'karbi yarinyarsa Inna ta bud'e 'kofar dakin ta fice da sauri duk kunya ta isheta.....Hannunsa ri'ke da babynsa suka 'karasa inda take tsaye tana shashshekar kuka







Littafin na kudi ne!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
07084653262
*BINTA UMAR ABBALE*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
[8/24, 9:55 AM] .: 'Yr Bngr Sys
*75*



_Assalamu alaikum barkan ku da safiya da fatan kun tashi lafiya ya gida ya yara? madallah Jiya na fita anguwa tun safe ban samu nayi typing ba sai bayan na fita ne na kawo muku uzirina afuwa👏🏻 da yawa daga cikin ku nasan zasu dauka wani abu daban to nasan wad'anda suka san wacece binta baza su dauki rashin yin typing dina da wata manufa ba, amana d'aya ce kamar yanda na d'auki alkawari kuma na karbi kudin ku #600 domin ku dinga samun update na 'yar banga sau biyu a rana, to ku sani a cikin ku akwai wad'anda nayi wa uziri suna da yawa, kuma a rayuwa dole sai kayiwa d'an uwanka uziri mutum ba kullum yake samun abinda yake so ba, tinda na fara typing na 'yar banga ban tsaya ba ko hutun sallah ban tafi ba kullum sau biyu nake har 'yan normal gruop suna surutun hakan, ban ta'ba tsallake kwana biyu banyi typing ba inayi iya bakin kokarina duk domin na sauke nauyin dake kaina, Ni ina kokarin rike amanarku amma kuma wasu daga cikinku suna cin amanata to wannan be dameni ba saboda nasan kansu sukewa, watarana zan tashi bani da chaji watarana zan tashi bani da lafiya ko yarona, kunga typing ba zai yiwu ba, dole sai da nutsuwa nasan dai wad'anda suka san wacece binta zasu bada shaida a kanta ban kar'bi kudinku dan nayi wasa da hankalinku ba duniya dole sai kayiwa dan uwanka uziri, saboda haka dik sanda aka ga banyi typing ba to a fara tambayar lafiya tukkuna kafin aji bayani na, ku kar'bi uzirina kamar yanda nake kar'bar uzirinku...................Assalamu alaikum🙋🏻‍♀️_



Yana isa inda take tsaye sai ya rike hannunta ya jata suka zauna kan gado, baby Zahra ya d'ora mata a cinyarta cikin murya mai taushi yace."Ki bata nono kinga tana kuka bana so naga momyna na zubar da hawaye."
Ma'kale kafad'a tayi tana goge fuskarta cikin shagwaba tace"Uhm!Uhum! wato momyka ko? to nima ai momyna ka 'batawa rai." Ya rike kafad'arta yana dan sansana wuyanta a hankali yace."Ayi min afuwa nima Inna Hajara mamana ce kuma kema ai kin san duk abinda na fad'a akanta hakane yanzu gashi data shigo kin tabbatar da maganata ko."? Shuru tayi masa kunyarsa takeji sosai.....Murmushi yay yana dan daga mata girarshi a hankali yace."Ai naga kin fara sallah saboda haka yau dakin nan zan kwana dan kwana biyun nan kokari da hakuri kawai nakeyi sha'awarki zata kasheni." Cikin wani irin voice ya'karashe maganar.
Kallonsa takeyi tana d'an zum'bura bakinta tace"Ni wallahi A'a so kake ka sake farke gurin bayan kasan sai da aka yanka ni." Ya wani marairaice fuskarsa yana mata shu'umin kallo yace."Ai naji Likitarki tace gurin ya had'e ranar da mukaje asibiti."
Hawaye ta share tana sake zu'baro baki gaba tace"Eh duk da ya had'e ai amma tace sai anyi wata uku sannan wani abu zai faru." Jikinta ya sake shigewa ya d'ora ha'barshi kan kafad'arta tare da zura hannunsa ya ri'ko kungunta ya rike sosai yace."Kina so na mutu kenan wata uku da kike magana tamkar shekara uku ce a gurina ai ni yau ma bazan iya hakura ba yanzu kafin na fita zanyi saboda nasan innarki zata hanani shigowa da daddare." Yana maganar yana cusa hannunsa cikin rigarta

Zabura tayi baby zahra dake hannunta ta kusa fad'uwa yay saurin riketa yana dan kallonta yace.''Baki da hankali zaki yar min da momy ko."? Tana tureshi daga jikinta tace"To ka daina ta'bani ko kuma in maka ihu! Inna Hajara ta shigo taga abinda kake." Sai yasa dariya yana kallonta yace."Idan kin min ihu! Inna Hajara ta shigo taga abinda nake meye a ciki dama ni nafi so ta gani itace zataji kunya bani ba."
Shiru tayi masa tana kokarin fito da nono domin bawa baby dake dan kuka......Taimaka mata yayi suka fito da nonon a tare, gabakid'aya idanunsa suka rufe ganin lafiyayyan nonon nata ya cika sosai gashi a tsaye nipple din ya sake tsukewa saboda tsotso, ya sauke ajiyar zuciya me zafi a hankali ya dora hannunsa saman brest din yana shafawa tamkar wani maraya ya d'ora kanshi a kafadarta......Wasila abu biyu ne suka dameta Yanda yake shafa fatar saman brest dinta shine ya sanya ta shiga wani irin hali gashi baby zahra ta kama nipple din tana ta tsotsa, sai tsigar jikinta ta dinga tashi duk ta rasa yan

da zatayi sai mutsu-mutsu takeyi tana dan tureshi yana sake makaleta a jikinsa.....Kuka tasa masa tana fad'in "Dan Allah ka bari wallahi babu dad'i."
Ya bud'e jajayen idanunshi da suka 'kankance yana kallonta kwata kwata ji yay bakinsa yay nauyi ya kasa magana a take jikinsa ya shiga kyarma wani irin sanyi ya dinga ratsa shi.
Tunda taga ya shiga wannan yanayin sai gabanta ya tsananta fad'uwa domin tana gane duk sanda yake cikin tsananin sha'awa jikinsa rawa yake.
Baby Xahra ya kar'be daga hannunta ya ajiyeta gadonta dake gefe, tana kallonshi yana kokarin 'balle botiran rigarshi da links....Sai tayi yunkuri barin gurin yay gaggawar rike hannunta.
Bakinta sai rawa yake takasa magana....Murya a hard'e yace."Ki taimaka min na samu stysifiend ba dole sai na shiga wannan gurin ba tunda kince da matsala ke kin san irin dubarar da zakiyi min ko."? Yana wani lankwashe kansa yake maganar.
A tsorace take kallonsa bakinta na rawa tace"Fita fa zakayi ka shirya tsaf kuma sai kace wani abu ni dai dan Allah ka mayar da rigarka ka tafi inda zakaje."
'Dan 'bata rai yay yace."Wai meyasa ne duk sanda zance miki ga abinda nake so sai kinyi min gardama meye a ciki dan kinyi min dabaru na samu biyan bukata kin san bana neman mata ko? kuma ke kadai ce matata to ki sani wannan halin naki zai iya janyowa na sake aure dan ni mutum ne mai yawan bukata da kuma san soyayya da kulawa."
Jin maganar aure yasa ta soma kuka tana kallonshi tace"To ai inayi maka kokari duk sanda zaka zo da bukatarka ina kokarin ganin ka samu gamsuwa ko ranar da zan haihu ma hakane ya faru, yanzu kuma ai haihuwa nayi ba sai ka hakura nayi ar'bain ba." Kansa ya dafe cikin 'bacin rai yace."Ba zakiyi abinda na umarceki ba." Matsawa tayi gefe tana goge fuska...."Ni dai ka bari nayi ar'bain." ! Yaji kamar ya kwad'a mata mari! Yarinya mai shegen taurin kan tsiya wai meye manufar ar'bain d'in nan da malam bahaushe ya tsira! Tsaki! me kar'fi yaja ya mi'ke tsaye yana maida botiran rigarsa ya d'auki hularsa da gilashinsa da ya aje ya sanya, ya kama hanya ya fita daga dakin ba tare da ya kalli inda take tsaye ba.
Yana fita ta nemi gefan gado ta zauna tana kuka ita tsoro takeji kada Inna hajara ta fahimci wani abun na faruwa a tsakaninsu ta tafi kwata kwata bata so ta tafi shiyasa kuma tana jin tsoransa kada yazo ya danneta ya lalata mata d'inki duk da likitan tace gurin yayi normal amma ai baiyi wani 'kwarin kirki ba.

Inna Hajara ce kadai a palo ita hajja ta shiga daki domin daura alwalar sallahr walha to tana ganin wucewarsa ba tare da ya ko kalli inda take ba sai jikinta yay sanyi a hankali ta mike ta nufi dakin Wasilan.....Ta tarar da ita xaune tana kuka. Zama tayi kusa da ita a hankali tace"Goge hawayenki." Wasila ta goge hawayenta tana sunkuyar da kanta.....Inna Hajara tace"Ni banzo da niyyar na kashe miki aure ba Wasila, na lura mijinki bashi da hakuri ko kad'an, ni kuma ke nake tausayawa saboda irin wahalhalun da kika sha kafin ki haihu Uwa uba akazo aka yanka ki aka d'inke kamar 'kwarya, dole a sanya ido sosai a kanki domin ingantuwar lafiyarki! Bayan haka kuma dole ne kafin ki komawa miji sai an gyara miki jikinki domin haihuwar da kikayi duk wata ni'ima da kike dashi babu nida a tunanina ma ina so idan zan tafi gida muje tare dake can in gyaraki sosai da sosai to amma tunda naga take taken mijinki to zan tattara nawa nawa na tafi dama akan dole nake zaune a gidan, bana so yazo ya dinga jin haushina ko ya fahimci cewar nice nake hanaki biya masa bukata."

Tun kafin Inna hajara ta 'karasa maganarta ta rike hannuwanta tamau! tana kuka sha'be!sha'be! "Wallahi Inna ba zaki tafi ba sai nayi ar'bain sai kace wata mara gata da galihu! ai haihuwar fari nayi kuma koda zanyi haihuwa goma a gidanan kina da damar da zaki zo ki zauna tare dani tunda ina cikin gidan.....Inna nasan abinda nakeyi nima bazan yarda ya haike min ba kawai ya cuceni bayan ban gama dawowa dai-dai ba, na amince zan jure ko wane irin fushin da zai dauka dani nasan idan ya gaji zai daina.."
Inna hajara tace"A'a Wasila ni bazan so kullum ki dinga kwana da tsiniwar Allah da mala'ikunsa ba, kibi mijinki sau da '

kafa kiyi masa biyayya kan abinda yake so ni dai na fad'a miki yau yau zan tafi dan naga kamar haushina yake ji to zai dawo ya tarar na bar masa gidansa.
Wasila ta dinga kuka tana bata hakuri Inna Hajara ta rufe idonta ruf ta fita daga dakin domun zuwa ta had'a kayanta.......Hannunta na kyarma ta d'auki wayarta ta shiga kiransa.....Lokacin yana cikin company sa tare da ma'aikatansa yaga kiran wayar tata ya'ki dauka har yanzu haushinta yake ji
Ta kira ya kai sau biyar bai dauka ba sai kawai ta aje wayar ta fito palo tana goge fuskarta tasan haushinta yake ji shiyasa bai dauki wayarta ba, tana fitowa palo ta tarar Inna hajara da hajja suna fafatawa, Inna Hajara taurin kan tsiya ne da ita ta'ki sauraran hajja hannunta ri'ke da jakar kayanta ta kama hanya ta fita Wasila tabi bayanta har wajen harabar gidan......Garba ya iso gurin da sauri ya karbi jakar kayan hannunta shi baiyi tunanin wani abuba saboda ya dauka inna zata tafi gidane....Can parking ya nufa da jakar kayan ya fito da mota har inda suke tsaye Inna hajara ta bude ta shiga tana 'bata rai! Wasila kallonta kawai takeyi domin ita har ta gaji da magiya da bata hakuri, tana tsaye har garba yaja motar suka fita daga gidan, ta girgiza kanta ta juya domin komawa ciki tana kokarin mayar da hawayen dake so ya zubo mata.
Tana shiga ta tarar da Hajja a tsaye a tsakiyar palon itama tana cikin alhini na tafiyar Inna hajaran Tace"Wasila kodai wani abu akayiwa hajara ne irin wannan tafiya haka da gaggawa, kuma na lura kamar dai ranta a 'bace yake."!
Ta d'an d'auke hawaye a hankali tace"Haka kawai ta tubure wai gida zata tafi babu abinda akayi mata."
Hajja ta zauna kan kujera jikinta a sanyaye tace"To ai shikkenan Allah ya sauketa lafiya." Ta amsa da "ameen tana kokarin shiga d'aki.


****
"Haba Uwani wai dan Allah tun yaushe nake miki magiya kan ki kaimu muga d'akin yarinyar amma kin'ki kaimu kullum nayi miki magana sai kice zamuje to sai yaushe zamuje? kada fa ki manta da cewar kwanaki dani dake mukayi lissafin watannin cikin yarinyar har ki kecewa cikin ya isa haihuwa nace watakila ma ta haihu to kinga yana da kyau muje muga halin da ake ciki." Kuluwa ce zaune a gaban Uwani take wannan maganar cikin 'kas'kantar da kanta.......Uwani ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Kuluwan kamar ba itaba wai yau an wayi gari Kuluwa nayi mata magana cikin kalami mai dad'i lallai duniya kenan.

Tace"Kuluwa ba wai bana so muje bane gaskiya bana so muje gidanan kiyi wani abu da zai sanya kima da mutuncinmu ya zube mutumin nan ba karamin mutum bane kuma kinga mu sirikai ne dole mu kama girmanmu ke kuma kuluwa baki da girma sai na jiki idan kin amince cewar xaki kiyaye kuma zaki nutsu sosai to shikkenan sai mu shirya idan Allah ya kaimu dani dake da Kawu da kuma su Inna mai waina muje muga abinda yarinyar ta haifa."
Cikin kwantar da kai Kuluwa tace"Haba Uwani wallahi bazan aikata abin kunya ba zan kula sosai bazan baki kunya ba insha Allahu." Uwani tace"Shikkenan to yanzu zan tashi na shirya na nufi gidan Inna Tabawa domin na shaida mata halin da ake ciki." Kuluwa tace"To hakan yayi bari idan na sauke abinci sai na d'an d'umamaki ruwan wanka kafin ki tafi kiyi sai kinfi jin dad'i." Mikewa tayi ta nufi kicin........Uwani tabi ta da kallo cike da mamaki.





Littafin na kudi ne!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*76*
Koda Rashida ta dawo ta tarar Inna hajara ta tafi itama sai da taji rashin dad'i tayi ta tambayar Wasila dalili, kunya ta hanata fad'a mata kawai sai tace"Rashida kin san dai rigimar Inna hajara dama da kyar na samu ma ta zauna tayi wad'annan kwanakin amma babu wani abu da akayi mata wanda zai sanya ta tafiya kawai dai dama tayi ra'ayi ne." Rashida ta amince da maganar Wasila suka zauna suna jimamin tafiyar Innar tasu.

To can 'bangaran su mai girma governor Lawan Rabo sun tada aiki sosai shida mu'karrabansa duk dan ganin yanda al'ummar jahar suka tashi hankalinsu gurin ganin sun rusa tafiyarshi da kuma jam'iyyar da yake ciki gabakid'aya jamiyyar da yake ciki dashi kansa sun daina power gabakidaya jama'a nata komawa jam'iyyar *CPC* jam'iyyar su Amadu kenan duk ta doke sauran jam'iyyun da suke adawa da junansu......Hankali mai girma governor yayi masifar tashi, babu shakka idan ya tsaya kallon ruwa to kuwa kwad'o zaiyi masa 'kafa, tuni ya kira 'yan fadarshi irin su As da mataimakinsa suka zauna zaman meeting inda suka yanke shawarwarin da suke ganin zasu taimaka musu gurin campaig, governor ya fitar da miliyoyin kudi ya rabawa 'yan gwangila irinsu As yace aje ayi duk abinda ya kamata a cikin jahar domin a jawo hankalin jama'a jam'iyyarsu........As suka fara aiki gadan gadan inda suka fara rushe rushen gidajan jama'a da masana'antu wai zasuyi babban titin da jirgin 'kasa zai dinga wucewa, jama'a da yawa suka shiga halin damuwa an rushe musu muhalli ba'a basu diya ba masu sana'oi suma an rugaza musu guri ba'a biyasu ba, a mai dasu gida an tsuganar, takaici ya ishesu sai kawai suka soma shiga gidan redio suna zage zage da fad'in Allah sai ya saka musu wannan zalincin da ake musu.....Mai girma governor ya tafi katsina gurin abokinsa ya samu labarin abinda yake faruwa a jahar tashi, a take ya kira As yace ya shirya da kanshi ya shiga gidan redio yayi bayani wanda zai dauki hankalin jama'ar gari su amince da manufarsu.
As ya shiga gidan redio na salama ya dinga zabga 'karya da 'karairayi kan cewar mutukar jama'ar gari sun sake za'bar lawan rabo to babu shakka zasuji dad'i a wannan karon komai zaiyi sauki za'a samu sauyi na rayuwa sannan yace."Duk wanda aka rushe masa gida da gurin sana'arshi a gurin aikin titin da sukeyi to duk su kwantar da hankalinsu za'a biya su hakkinsu......Ashe jama'ar gari sunyi dafifi a wajen gidan redion koda su As suka fito dashi da 'yan rakiyarsa da 'kyar suka sha dan ma da akwai security a tare dasu amma dai dik da haka sai da sukayi raga raga da gilashin motocinsu suna tafad'in "bamayi! kano ta d'an musa ce."

Ranar Amadu da Khalifa sun sha dariya hankalinsu kuma ya kwanta sosai ganin suna samun nasara a cikin tafiyar tasu kullum 'kara samun masoya sukeyi ta ko wane fanni.


Tun ranar da Inna hajara ta bar gidan a tsakaninsu suka daina samun jituwa wanda gaisuwa ce kawai take had'asu daga haka shikkenan zai fice harkokinsa, kuma koda ya dawo gidan yaga bai ga Inna Hajara baice mata komai ba itama ba tace masa komai ba, dukaninsu sun shiga cikin damuwa mai tsanani babu kamar ya ita kullum sai tayi kuka, ita bata ga abin fushi da daukar gaba ba ta lura yana da hakuri sosai amma bai iya fushi ba dan haka sai ta yanke shawarar tunkararsa ta bashi hakuri idan ya hakura shikkenan idan bai hakura ba zata rabu dashi duk ranar da ya gaji ya sauko dan kanshi.............Yau da wuri ya shigo gidan dan goma ma ba tayi ba, sai da ta bari Hajja da Rashida sun bar palon tukkuna ta fito daga dakinta tayi kwalliya sosai sai 'kamshin turare take.
Murd'a kofar dakin tayi ta shiga da sallama a bakinta.....Babu kowa sai dai tana jin alamun motsi a toilet dinshi ta dan zauna gefan gadon tana bin dakin da kallo yaushe rabonta da shigowa tun ranar suna gashi yau kwananta talatin da bakwai da haihuwa saura kwana uku tayi ar'bain......Tana zaune tana sa'ke-sa'ke ya fito daga toilet d'in 'kungunsa daure da towel da karami a hannunsa.
Had'a ido sukayi tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na fad'uwa.....Kadaran kadahan ya kalleta ba tare da yace komai ba ya 'karasa bakin mirror ya dan tsaya yana sake

goge fuskarsa.....A sanyaye ta mi'ke ta isa inda yake tsaye ta 'karbi towel din hannunsa tana so ta goge masa jikinsa, sai kawai ya bar mata gurin, Ta bishi da kallon mamaki yaje ya nemi guri ya zauna gefan gado yana shafa vasillin a jikinsa, ba tayi zuciya ba ta isa inda yake a hankali ta sanya hannunta ta 'karbu vasilin d'in tana marairaicewa, Ya mi'ke kawai ya barta a gurin........Wardrobe ya nufa domin daukar jallabiyarsa, da gudu taje ta rungume faffad'an bayansa tana shashshekar kuka tace"Kayi hakuri kaji." Ajiyar zuciya ya sauke yana dan jin sassauci cikin zuciyarsa, shima dik abinda yake daurewa kawai yake yi yana dai so ya nuna mata kuranta ne, amma ba dan ya cuzguna mata ba, idan da ta kwantar da hankalinta shima ai yasan abinda yake yi ba zai ta'ba cutar da ita ba, amma ranar nan ya kwadaitu da ita mutu'ka ya kuma nemi ta a gaza masa ta'ki! dashi d'in manemin matane to babu shakka a ranar sai yaje ya biyawa kansa bukata amma haka ya hakura ya cireta daga cikin ranshi duk dan ya nuna mata kuskuranta

A nutse ya jiyo da ita suna fuskantar junansu, kasa hada ido tayi dashi ta sunkuyar da kanta 'kasa tana goge fuskarta, a hankali ya sanya hannunshi ya goge mata hawayen fuskarta ya tallafo fuskarta sosai cikin tafin hannuwansa ya kallonta.
Takasa d'aga kanta ta kalleshi saboda kunya da kuma tsabar kwarjin da Allah yayi masa.
Murya a kasa kasa yace."Me kikayi min kike bani hakuri."? Sai ta dago fuskarta tana kallonsa.

Ya sanya d'an yatsansa saman le'banta na 'kasa yana shafawa a hankali a hankali shi dai yana masifar son le'bunanta.

Kasa cewa tayi komai ta maida kanta 'kasa tasan yana sane yake tambayar ta yafi kowa sanin kan abinda yasa take bashi hakuri.
Murmushi yayi a hankali ya cika fuskarta ya juya ya dauko jallabiya cikin wardrobe yana fad'in "Ina momyna ko tayi bacci."? A hankali ta d'aga kanta tace" Yanzu nan na lalla'bata ta kwanta.....Hannunta ya ri'ke yace."Muje parlo yau ke zaki bani abinci a gajiye nake."

Taji dad'in yanda ya saki jikinsa sosai wannan ya sake tabbatar mata da cewar ya hakura da fushi da ita kuma ta lura dama kamar daurewa kawai yakeyi yana hakuri.

Ya zauna kan kujera yana dan dubawa babbar wayarshi yace."Ki had'o abincin ki kawo min nan zanci." Da sauri ta nufi daining din ta had'a mishi abincin komai da komai ta kawo gabanshi ta ajiye......'Kasa ya sauko hankalinsa na kan wayarshi yana dan juya abincin da cokali, sai ta kar'bi cokalin ta fara d'ebo abincin tana sa masa a bakinsa.......Kar'ba ya din gayi ba tare da ya kalleta ba hankalinsa gabakidaya yana kan wani text da Zeey tayi mishi.
Kafin ma ya gama karanta text din kiran wayarta ya shigo wayar tashi.
Dama tuntuni ya goge number ta cikin test dinta ma dan tasa sunanta ne ya ganeta.
Ganin numbarta tace ya sanya shi daga wayar a nutse yay sallama dake hands free ya bud'e Wasila najin muryar Zeey tana fada'in "Ranka ya dad'e barka da dare yau dai naci sa'a an d'auki wayata."
Gabanta ne ya shiga fad'uwa sai hannnta ya soma rawa tana kokarin sanya masa a bacin a baki cokalin ya su'buce daga hannunta abincin ya zube a jikinsa sa kasan gurin.
Dan dubanta yay yana dan gyarawa hankalinsa nakan maganar da zeey ke masa yace."Zainab ya kike ya gida ya kwana biyu."
Zeey tace"Alhamdullhi yallabai Wallahi kwanaki nayi ta kiran wayarka domin nayi maka Allah ya raya baka dauka ba nace to ko wani laifin nayi.'"?
Murmushi yay a hankali ya dan koma saman kujera yace." Ai ke bakya laifi Zainab mybe lokotan da kike kiran wayar ina da uziri ne shiyasa amma nagode kwarai kuma naji dadi da kulawarki."
Zeey tace"Ai har taron suna nazo sai dai ban dad'e

Please Login or Register in order to submit comment