Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace."Nida nafi so yau yau yarinyar nan ta kasance a dakinta bana so mu shiga hurumin ubangiji ya kasance muna wasa da aure, tunda an daura auranan to ta tare a dakinta barin ta haka sasakai zai janyo matsala babba tunda dai ita bata san halin da ake ciki ba.'' Yace."Tabbas maganar haka take malam babu damuwa insha Allah yau zata tare a dakinta kamar yanda ka bukata din." Malam yace."To bari in baka sadakin a hannuka ka mika mata da kanka tunda dai mu ba ganinta Zamuyi ba." Yace."babu damuwa Malam." ya ciro dubu biyar din ya mika masa ya sanya hannu biyu ya kar'ba, kana ya shiga yi masa godiya sukayi sallama cikin mutunci da mutuntawa.....Har bakin mota suka rakosu sai da motarsu ta 'bacewa ganinsu sannan suka juya cike da farin ciki sun auran da Wasila saura Rashida zuciyarsu wasai mussaman malam mai allo yana fatan d'orewar zaman lafiya ga Ahamdu da Wasila.


Cikin mota tunani kawai yake yi kan al'amarin duk ya rasa wane matsayi zai aje wannan auran nashi zuciyarsa na kawo masa shawarwari iri iri tabbas ko A lahira wani nacin albarkacin wani babu shakka yarinyar taci albakarcin dattijo malam mai allo a gurinsa, da ya dauki mummunar aniya a kanta albarkacin mutumin ya rage kashi tamanin daga cikin abunda ya tanadar mata amma dai duk da haka zai ba zai kyaleta ba sai ta gane bata da wayo......Haka suka isa gida tunani duk ya addabe shi yanzu ya za'ayi ma ya tunkari inda yarinyar nan take dame zai fara ne." ? Khalifa yace."Naga ka shiga tunani da yawa ka bari muje gida mu dan huta tunani ya dawo tukkuna nasan abunda ke damunka a yanzu amma aka bi komai a hankali mai sauki ne." Ajiyar zuciya ya sauke ya dan gyara zamanshi ya sake mai da idonsa ya rufe ba tare da yace komai ba.


Cikin wata lafiyayyiyar lifaya ta fito Tana baza kamshi turarruka masu tsada da sanyin kamshi, Tayi ado da gold 'kirar dubai masu jajayen stones a jiki shi kanshi gyaran gashin da tayi wa kanta abun kallo ne tamkar wata balarabiya haka ta zama babu shakka kudi na iya canza mutum nan take Wasila ya zanzu dai da zata shiga cikin labarawan Itopia sai ta saje dasu saboda yanda fatarta ta goge ta 'kara fitar da kalarta chocolate color dama can haka kalar fatarta take Rashida ce fara itace ta d'ebo haske babansu Uwani kuwa ba za'a kirata fara ba kuma ba za'a kirata baka ba kusan kalar fatarsu daya da Wasilan amma dai yanzu ta Wasilar tafi kyau da gogewa, takalmi mai tsayi ta sanya kasancewar ba ta fiye tsayi sosai tana tsaka tsaki dai! Hannunta rike da pose da key na motar ta take takawa sannu a hankali.....Camas dake zaune na latsa waya ta kalleta "Wow! Kinga yanda kikayi kyau kawata, gaskiya lifayar nan ta miki kyau wallahi ke kin jima bakiyi kyau irin na yau ba tamkar wata amarya lalle ne kawai babu a hannunki da kafafunki.'' Murumsi tayi tace" Haka kawai yau nace bari nayi shigar bare bari ashe nayi kyau."? Camas! ta kwalawa Rashida kira ta fito daga kicin....Ganin Wasila ya sanya ta rude! "Aunty Wasila kece dan Allah nima ina son lifayar nan ki siyamin wallahi kinyi kyau! sai kallonta takeyi tana dariya Camas tace " Wai tambaya takeyi tayi kyau shine na kira ki ki fada mata." Rashida ta hau kod'ata "Wallahi aunty Wasila ko makaho ne yazo kusa dake ya tsaya sai ya kiyayi kansa babu wanda zaice kin hada jinsi da bahaushen mutum kamar wata balarabiya." Ganin yanda suke sambatu ya sanya ta dinga musu dariya...Uwani ma ta fito daga daki ta dinga nata shirma da zasu fita ta dinga yiwa 'yar tata kirari sai kace wata maro'kiya ita Wasila ma dariya suka bata tace"aikuwa dai tunda shigar lifaya nayi min kyau zan dawo yin irinta....


Suna shiga motar kiran As ya shigo wayarta ta dauki wayar tana dan ya mutsa fuskarta.....A nutse tayi sallama da sauri ya amsa yana fad'in "Gani a bakin gate din gidanki ki fito kawai muje mu dawo dan ma dai nayi alkawari ne da sai nace mu bari sai gobe ma futa yanzu aka kirani a waya karfe goma dai-dai muna da metting da shugaban 'kasa kin san tun safe ya shigo gari yanzu haka suna tare da mai girma governor."

Tace."To mai zai hana mu bari sai gobe." Da sauri yace." Ai ni kuma ba zan fuskanci komai ba gurin metting din nan mutukar banyi tozali da kyakkyawar fuskar nan taki ba." Murmushi tayi ta kashe wayar ta kalli camas tace"Ga d'an anace nan ya iso kawai ina zama na wai na shirya muje shan iska komai abunsa dole ya hakura dani wallahi wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa

Camas tace"Tunda dai yaki hakura ba sai kiyi kwance kwance ki kwashi rabonki ba." Ke dai kawai fito muje dare nayi kudi kam ai kamar mahaukaci haka yake samun a account. " Camas taji inama itace dan a zahiri As yafi Alhaji Ma'aruf sakin hannu shiyasa taso ace As din ne ke mu'amula da ita tasan da tuni ta wuce gurin........Kamshi turaranta shine ya buwaye shi, yana draving yana kallonta idanunsa sun kada sunyi jawur babu shakka yau Wasila ta kaishi makura ga bukatuwa da ita yana ganin koda bai shiga wannan ramin ba a'kalla dai ta bashi dama ya d'an rage zafi a jikinta....Da kyar suka isa 'katon gurin hutawar wanda sai wanda ya amsa sunansa ke zuwa gurin......gurin tamkar rana ko ina haske tar tar jama'a nata shigowa da motacinsu da yawa daga ciki tare suke da mata wasu karuwansu wasu matayen su kowa harkar gabanshi yake.........As yayi kwance a gabanta yana lumshe mata shegun idanunsa da suke cike taf da sha'awarta duk sun kankace saboda jaraba, ganin yana matsowa jikinta ne yasa tayi saurin matsawa tana 'bata fuska.....Yace."Yana da kyau yau daya ki bani dama ko yaya ne na ra'bi jikinki babu shakka zuciyata na azabtuwa da so da kaunarki ki bari na rungume ki ko zanji dadi a jikina"

Ranta a bace ta kalleshi "Haba As wai yaushe ne zaka daina yi min irin wannan maganar? na sha fada maka ni ba 'yar iska bace amma ka kasa fahimta ko dan kana ganin Camas! kawata ce shine nima kake zargin halinmu daya da ita, Wallahi da zanyi karuwanci da tuni nayi amma ni ba layina bane kaje ka nemi karuwa ta debe maka kewa bani ba, idan kudin da kake turo min da wannan niyyar ne to dan Allah daga yau kar ka sake kuma tunda ka kasa daukata a matsayin abokiyarka to ka goge numbarta dake wayarka bana bukatar wata mu'amula ta sake shiga tsakanina da kai. Mikewa yayi zaune yana marairace fuska yana so ya kama hannayenta ta fuzge da karfi ta mike tsaye da sauri jikinta na rawa...Camas na can tare da wani alaji suna zance ta iskesu rai a 'bace tace" Ni zan wuce gida Kya biyo bayana." Mutumin yace."A bari nazo na kaiku mana." Ko sauraransa ba tayi ba tayi hanyar futa....Ita ko Camas! ganin alhajin nada kumbar susa a tare dashi sai tace"Rabu da ita Alhajina idan da wata bukata da kake nema a gurina yi min magana kawai kar kaji shakka." Ya shafa fuska yana lumshe mata ido yace."Muje mu kama daki zuwa gobe da safe sai na sallame ki." Ba tare da wata doguwar jayayya ba tabi bayanshi.

As yabi bayan Wasila yana nema neman duniya bai ganta ba guri ne babba ga jama'a na shiga suna fita ya fita bakin titi ya jima a tsaye yana waige waige bai ganta ba, haka ya koma ciki domin daukar motarshi anan kira ya shigo wayarshi kan lokaci ya kusa da zasu zauna metting dole ya nufi government house din ba dan ransa yaso ba yaso ko yaya ne ya rage zafi da Wasila amma ya dauki alkawarin komai tsantsaninta sai ya rusa shirinta.

Tana ganin futar motarsa ta fito daga inda ta 'buya babu shakka As so yake ya yaudareta ya rabata da budurcinta wanda da ta jima tana tattalinsa, tabbas zata janye jikinta dashi da lamuransa tunda ta lura shi baya abu dan Allah.

Koda ta fito titin tsif! babu abun hawa na haya dama kuma ba kasafai a dai-dai ta sahu ke shigowa gurin ba saboda babban titi ne na masu hannu da shuni yawanci motocin gida sunfi karakaina a kan titin.....Tsoro yasa ta kasa tsaida motar kowa sai ta kama hanya ta dingi tafiya ga cokalelen takalmi a kafafunta.


Tana daf da futa babban titi motar ta fito daga wani babban layi mai dauke da dogwayen gina gine, dole tasa ta ratse a gefe domin ta bawa mai motar hanya, haushi da takaici ya turnuke ta ganin yanda mai motar ke dallare mata fuska da hasken fitilar motar....Ta sanya hannunta ta kare fuskarta tana jan tsaki!!!

Ahamdu dake gaban motar gabanshi ya fad'i Allah yasa dai idonshi ba gizo yake masa ba, sai da suka zo daf da ita ya tabbatar da zarginsa Itace! ma'kale a jikin bango tana jira su wuce! sai ya shiga tambayar kansa, Yarinyar nan daga ina take a cikin wannan daran? shin ita da waye? kuma meye ya fito da ita daga gida. Bashi da me bashi amsa dole sai ita, da sauri ya sanya Garba ya tsayar da motar ya bude motar da zama ya fito ya iske inda take ma'kure!

*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_

*Free Pege19*
Saboda yanayin hasken gurun ya sanya tun kafin ya karaso kusa da ita ta ganeshi gabanta ne yayi wata mummanar faduwa da azama! tayi kokarin barin gurin.....Taku biyu yayi ya cafki hannunta guda.....Cak! taja ta tsaya tana mai da nuffashi domin ganinsa ya sanya jikinta kyarma wanda shi kanshi sai da yaji a jikinsa sakamakon rike hannunta da yayi, Sai da ta dan samu nutsuwa sannan ta juyo fuska a had'e! Suka hada ido dashi yana tsaye shima tashi fuskar babu alamun wasa....Kafin tace"Komai ya mangantu.....'Karfe goma sha biyu na dare kina waje a matsayinki na 'ya mace mai daraja kin watsar da wannan 'kimar da Allah ya baki kin mai da kanki tamkar tunkiya kiyi nan kiyi can cikin dare saboda rashin sannin ciwon kai kin mai da kanki tamkar namiji namijin ma irin wanda bai san darajar kanshi ba."
murmushi tayi mai ciwo tace."
Idan hakane kai ma
Ashe kana d'aya daga cikin jinsin irin mazan da ka fad'a yanzu, Kai ma me ya fito da kai da daddare idan ka yarda da kanka? kana kirana tinkiya kai kuma sai ka kira kanka da bunsur......! kamar ya sanan sunan da zata kirashi dashi yayi saurin kife ta da mari! jikinsa na kyarma! yace."Ahir!! d'inki ki kirani da wannan suna! na kira da tinkiya din domin sunan da ya dace a kira ki dashi kenan, dube ki don Allah wai ke kinyi kwalliya kina yawo sa'ko da loko kina rabawa jama'a jikinki a banza job wane wawa ya jaki ya jaki ki bishi saboda rashin martaba kai ya jama'a ba zasu kira ki da sunanan tinkinya ba."!?

Wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubo mata a kumatu idan ta fahimci maganarsa anan shima yanayi mata kallon karuwa kenan? wai shin mai yasa mutane basa yi mata adalci ne a duniya ta tsani a kira ta da wannan suna, sunan tinkiya na nufin mace mara hankali mara ilimi mara nutsuwa da kamun kai....Tunda suke karawa da guy din bai ta'ba 'kona mata rai irin yau! ba su kansu hawayen dake zuba a fuskarta ta bata san sanda suka zuba ba, da budurcinta da komai yake kiranta da tunkiya.....Hannunta da cikin nasa ta fuxge! ta bar gurin a gaggauce!!! bayanta yabi ya sake ruke hannunta ta sanya karfi ta tureshi kuka take hai'kan! tsabar kalmar daya kira ta da ita tayi mata ciwo tana ji ma tamkar ta hadiyi zuciya ta mutu.......Yayi saurin tatar gabanta rai a bace yace."Idan baki tsaya ba wallahi yanzu a gurin nan zan tu'be ki na kwashi rabona duk da hakan ba halayyata bace zanyi miki hakane dan in nunawa duniya halinki....Gwara kawai ki tsaya ki daina sauri."

Hawayen fuskarta ta goge tace"Kai baka isa ka tu'be ni ba wallahi sai dai na tu'beka! kuma sai nayi maka sintir! zaka san wanda ka mara." murmushi ya saki hakika dauriya da jarumatar yarinyar na burgeshi, yace."Idan kin isa ke mara kunya ce ki 'kara taku d'aya anan gurin wallahi sai na baki mamaki! sai na tu'beki! kuma na gudu da kayanki ki 'kara taku daya ki gani."

Wasila ta kalli fuskarsa taga babu alamun wasa a ciki sai gabanta ya fadi tabbas zai aikata abunda ya fada bari kawai ta lallabashi su rabu lafiya amma sai ra rama abunda yayi mata.

Tsayuwa ta gyara tace"Wai shin yanzu da ka tare min hanya me kake nufi dani.'" Yace."Abubuwan da nake nufi dake suna daya wa saboda haka shige muje ki shiga mota muje."

Ta kalleshi she'keke! tana gyada kai! "Ko da kudi ba zan shiga motarka ba nasan idan na futa babban titi ba zan rasa abun hawa ba kawai ka fada mun dalilin da ya sanya ka tsare min hanya."

"Kin san ke mai laifi ce a gurina ko? so bana son jayayya kiyi abunda nace dake idan ba hakaba zan kira Yarana a waya so zu su baki mamaki! duk yawansu sai sun kwanta dake sunyi miki fata fata!!!!!! Tsorata tayi dajin maganarsa mussaman da taga yayi kici kici da fuska yana kokarin dauko wayarsa,, sai ta sassauta murya a hankali tace" Dan Allah kar ka kira su muje motar nayi alkawarin kome kake so zanyi maka amma kar ka kira yaranka su wulakanta ni."

Yace."Wuce muje." Gaba tayi da cokalalen takalminta har tana gord'ewa sai waiwaye take ko zata samu mafakar da zata arce babu gida gaba babu gida a baya.....Da kanshi ya bude mata mota ta shiga ya zauna kusa da ita fukarsa babu wasa, gabanta sai masifar faduwa yake shikkenan yau ta fada komar Ahamdu sai Allah kuma tsinewa babu irin wacce ba tayi wa As ba shine silar fitowarta da wannan daran da bai fito ba da tuni ta gida tare da mahaifiyarta da 'yar uwarta.

'Kasa tayi da kanta hawaye na d'iga ta dinga sanya gefan lifayar tana gogewa sam! ba taso ya ga gazawarta a kansa amma inaa ta kasa tsayar da hawayen dake zubar mata mutukar ta tuna kalmar da ya kira ta da ita sai taji zuciyarta ta karye *Tinkiya* wannan kalma tayi masifar ragargaxa mata jikinta da duk wani kuzarinta da kwanjinta a kanshi....... Gani tayi mai gadi na bude tangameman gate din gidanshi, tayi saurin dagowa tana kallonshi taga yayi masifar 'bata fuska, yana magana da securities din dake bakin gate din....Tsumu! tayi hankalinta a tashe kar dai guy nan ya kawo ta gidanshi ne domin ya keta mata haddi innalilihi wa ina ilahi raji'un! yanzu meye mafita....
Taga ya bude mota ya fita sai tayi yunkurin fitowa itama, da sauri ya mayar da murfin motar ya rufe da karfi dan har yana had'awa da hannunta, cije baki tayi tana duba ya tsanta, tunaninta kaf yanzu ya ta'alla'ka ne akan yanda za'ayi ta ku'butar da kanta daga hannunsa.


Can ta hango sun nufi bakin gate tayi saurin mikewa kan site tana le'kansa taga yana magana da securities akwai ta zata sosai parking spece da kuma bakin gate din ba tajin abunda yake cewa amma yanda ta lura da fuskarsa babu wasa yana musu magana mai muhimanci.....Juyowa tayi ta fara kokarin bude motar gam! take da mukulli ko wane murfi a rufe.....Hawaye ya tsinke mata, Innalillhi wa'ina ilaihi raji'un! Sake mikewa tayi tana le'kensa, Can ta hangoshi ya durfafo inda take tayi saurin zaunawa! jikinta na kyarma, yana bud'e motar hankalinta a kai tayi wuf!! ta fito fit! har sai da ta tureshi yayi saurin tsayuwa cikin zafin nama ya cafki 'kugunta ya rike tam! ya had'e bayanta da 'kirjinsa! Jini hannunsa kan kirjinta ya sanya tayi masa wata wawar bangaza ta sanya tsinin takalminta ta daki gwiwarsa guda! yayi gaggawar juyo da ita mari ya kifa mata!!!!! ya rike fuskarta da hannuwansa suka tsirawa juna ido.....Numfashi take saukewa mai zafi !! tana hura hanci! ga idanunta yayi jawur! Tsananin tashin hankali da fargaba ya gani cikin 'kwayar idonta, Ya gyada kanshi cikin jajurcewa yace."Ki shiga taitayinki ki kuma nutsu wannan haukan da kikeyi babu inda zai kai ki a gurina muje ciki in fad'a miki wani abun al'ajabi."!!

"Ba zan shiga gidanka saboda ni ba 'yar iska bace ka daukoni ne dan ka biya bukatarka ni nafi karfin ka idan kuma ka tsananta to za'ayi mutuwar kasko dani da kai a gidanan, dan nayi rantsuwa da Allah babu wani d'an iska da ya isa ya rabani da budurcina akan hakan zan iya aikata komai."

Ya jima yana kallonta kafin yace."Ke! kina nufin kina sa budurci a yanzu, da har kike wani tada jijiyar wuya! okey to kar ki damu ba wannan bane manufata a kanki kawai dai yanzu na baki umarni kan ki nutsu kana kuma muje ciki na sanar miki da abun al'ajabin da ya faru dake."

Taji wani irin shocking ya kama jikinta shin wai wannan wane irin abun al'ajabi yake so ya fad'a mata ne? Ji tayi wata jarumta tazo mata a take tace"Muje amma akwai sharad'i idan ka kusance ni sai nayi maka illah." Yace."Na yarda." Gaba tayi tana gurd'ewa ga lifayar tsabar wahala duk ta warware sai silmiyowa takeyi tana gyarawa gashin kanta duk ya baje a kafadarta ribbon din ya fad'i a bakin mota......Bayanta yake bi cikin nutsuwa yake 'kare mata kallo warwarewar lifayar ya sanya ya fahimci kayan dake jikinta t_shart ce mai karami hannu sai dogon wando na jins amma ya da'me ta d'am-d'am! ya fito mata da mazaunai tamkar suyi magana....Dauke kanshi kawai tayi yai saurin wuce ta yaje ya bud'e kofar palon....Yana tsaye ta 'karaso da hannu yayi mata alama ta shiga ta tsuguna tana kwance takalminta dake mai igiya ne... Nan ma kasa tsayuwa yayi saboda yanda ya hango brest dinta sun bullotso ta saman d'amammiyar rigar dake jikinta sai ya shige palon ya tsaya...Ta shiga ya mai da kofa ya rufe da key.

Had'uwar palon da 'kayatuwarsa sam! bashi ne a gabanta ba burinta kawai ya fad'a mata abun al'ajabin ko ya nuna mata ta zuba masa furgitattun idanunta

Cikin wani irin taku iske inda take tsaye ya zura hannunsa cikin aljihu dubu biyar d'in sadakinta ya zaro ya kama hannunta ya sanya mata kana ya kalleta ido da ido yace."Ri'ke sadakin auranki da kyau!! Yau! ni *Ahamdu Musa* na cika d'an halak na tashi daga sunan gwauro na 'yantu na cika cikakken namiji inda nayi tattaki 'kafa da 'kafa na iske har Garkin Gargo na d'aura aure da Wasilatu 'Yar gaske Kawunki Malam mai allo yace na baki sadakin ki a hannunki ki lissafa su dubu biyar ne."!

Yana gama maganarshi ya sakar mata hannunta kud'in suka watse a kasan palon.....Bai damu ba ya nufi bedroom dinshi hankalinsa kwance.......Da wani irin mamaki take kallonsa har ya bude dakinsa ya shiga tana kallonsa tana jinn sautin miryarsa na amsa kuwwa a kunnanta *"Wannan shine sadakin auraki Ni Ahamdu Musa nayi tattaki kafa da kafa na iske garin Garko na daura aure da Wasilatu 'yar gaske na tashi daga sunan gwauro na 'yantu Kawun ki Malam mai allo yace na baki sadakin ki da hannuna."* Wannan maganganun kawai takeji a cikin kunnanta kamar yanzu yake fada mata idanunta tsaye a kofar dakinshi.......Kimanin minti goma tana tsaye a gurin tana jajanta maganar gani take ma kamar mafarki take sai da ta kai idanunta kan kudin da suke watse kasan kafet, sannan gabanta ta sake faduwa ta tsuguna kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta dinga daukar kudin tana hadawa guri guda tsaf! ta lissafa su dubu biyar.......
*"Ni Wasilatu ni aka daurawa aure da sadaki dubu biyar sai kace bazawara!! Bazawarar ma mara gata da galihu tir'kashi!!!! A fusace! ta mike! ''Karye ne wallahi! Ni Wasilatu nafi karfin ayi min wannan wulakancin Ni za'a daurawa aure ban sani ba Wallahi wannan auran dashi da babu duk d'aya a gurina."!!! Sai ta nufi kofar dakin nasa gadan gadan!! hannunta rike da 'kudin sadakin auran na ta."*
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_


*NA SADAUKAR MUKU DA WANNAN PEGE 'DIN*

Rahima Aliyu
Hauwwa Saudia
H.Rabi 'kofar bai
Fatima Yakubu
Nafisat Ahamad
Zahra Kaduna
Fatima Binta
Jamila Abubukar
Mum Basma
Maimuna bichi
Ummu Yusif
Atou Tabalak
Anty Zeey Kazaure
Zainan Khabir Ishak
Jamila Yusha'u
JiddatulKhairi

_*Kuna da yawa sosai masoya wanda baiji sunanshi ba afuwa zamu hadu a gaba ina mutukar alfahari daku masoya Ubangiji Allah ya 'kara 'kauna ta gaskiya*_
~~~~~~~~~~~~~
*Free Pege20*
Lest Free Pege

A fusace! ta buga 'kofar d'akin ta shiga, yayi hanzarin juyowa jikinsa sanye da rigar wanka da alama yayi shiri tsaf wanka zai shiga dan yana daf da bakin toilet din....Idanunta a rufe ta durfafo inda yake tsaye yana kallonta ga mamakin sa sai yaga ta d'aga hannunta dake ri'ke da kud'in zata watsa masa yayi hanzarin ri'ke hannun! suka tsaya suna kallon junansu.....Sai yanzu ta lura da irin kayan dake jikinsa, rigar wanka ce mai bud'ad'addan gaba kuma bai daure ba ya sake ta faffad'an kirjinsa mai cike da yalwar gashi yana a bayyane kuma karamin wando ne a jikinsa wanda da ya d'ameshi.

da sauri ta sunkuyar da kanta 'kas! gabanta na masifar fad'uwa Ganin yanda wandon jikinsa ya masifar matse shi ba ta ta'ba ganin zahirin namiji ba sai yau! Har yanzu hannunsa na rike da nata wanda kudin ke ciki yana watsa mata wani irin kallo yace."Kar ki kuskura kiyi min watsi da kudi a d'aki idan kikayi sai ranki ya 'baci! hakkin ki ne kije dasu duk wanda ki kaga damar bawa ki bashi wannan bai dami kowa ba." Hannunta ya saki ya kama hanya zai shiga toilet d'in! aikuwa ta watsar da kud'in kasan dakin tana fadin "Wallahi wannnan auran dashi da babu duk daya suke a gurina ka kwashi kudin sadakin ka bana sonka bana ra'ayin auran mutum irinka da har zakaje har mahaifata kasa a dauro maka aure dani to yanzu ba gobe ba sai ka sake ni dan wannan budurcin nawa na mai rabo ne." Da jarumta take maganarta kuma tsakaninta da Allah take....Ya juyo cikin wani irin yanayi yana bin kudin da ta watsar a 'kas! wato dai sai da ta watsar masa da kudi a d'aki saboda taurin kai!! Nufar ta yayi cikin tsanani na 'bacin rai!!
Sosai ta tsorata! da ganin yanayinsa sai ta soma ja da baya yana sake tunkarar ta tana sake matsawa gabanta sai duka yake yana daka haka suka dinga yi har sai da suka dangane da jikin bango. (Garu) d'aga hannu yayi kamar zai mareta! sai tayi saurin kauda fuskarta ta sanya dukanin hannunwanta ta kare tana sakin 'karamin ihu!! Shiru taji ta bud'e idonta a hankali tana kallonshi ta kafar hannunta yana tsaye daf da ita ya dafa hannunsa guda a jikin bango ya tokare ta sannan faffadan kirjinsa dake bud'e yana gogar hannayenta, 'Das!d'as gabanta yake fad'uwa lokaci guda ta rasa miyau! a bakinta ya bushe kamas!!! Sai

Please Login or Register in order to submit comment