Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaune sosai yana ya mutsa fuskarsa, hakuri kawai yake yi amma wannan kwanciyar da tayi a jikinsa ta ya mutsa shi, sosai ya d'an saci kallonta sai yaga tana hamma! da alamun baccin bai isheta ba, sai kuma ya mutsa fuska takeyi cikinta ne ya soma 'kullewa yunwa na sasakarta dama 'ka'ida ne idan tayi bacci ko yayane ta farka sai taci abinci.......Jikinta ne ya soma rawa, ta dinga zare ido tana mutsu mutsu ta rasa ya za tayi a yaron dake cikinta yana mata wani irin motsi da zillo tare danno mararta kamar me shirin fitowa waje, cikin rawar murya tace"Rashida ina kayanmu suke."? Rashida tayi saurin juyawa tana kallonta ganin yanda idanunta suka kad'a ne ya sanya ta gane yunwa takeji da sauri tace" Suna bayan mota." Still murya na rawa tace"To sai kizo ki dauko min kin san dai cewa nayi ki rike min a hannunki saboda zan iya bukatarshi cikin ko wane irin yanayi me zai sanya kisa a cikin akwati.'' Rashida tace."Yi hakuri anti Wasila ai mun kusa sauka." Tsaki taja tana motsa bakinta.....Ya kalli Rashida cike da kulawa yace."Menene."? Tace." 'kwai dafaffe ne Bitan ta bata shine tace na ri'ke mata a hannu na ni kuma wallahi na manta nasa a cikin jakar kayanmu gatacan a bayan motar." Shiru yayi kawai ya juya bayanshi da kanshi ya kinkimo jakar kayan nasu ya d'ora saman cinyarshi ya zuge zif din jakar ya soma dubawa.....Nan ya d'auko daurin leda yaluwa da dafa

ffan 'kwai a ciki kusan guda ashirin, a jikinta ya d'ora ledar ya mai da zif din jakar ya zuge kana ya maida ita inda take ya gyara zamanshi yana kallonta a nutse yace."Gashinan karkiyi kuka gama naga shi kike shirin yi." Shiru tayi masa ta cigaba da kokarin kwance ledar.......Kar'ba yay ya kwance mata ya d'auko d'aya ya soma 'bare mata , ya mi'ka mata ta kar'ba da sauri gutsira biyu tayi masa ta cinye.....Tana kallon hannunshi dake kokarin 'bare mata wani, Haka dai yayi ta aikin 'bare mata kwai tana taunewa sai da taci guda tara sannan ta hakura ya mi'ka mata ragowar ruwan swan din da yasha d'azu ta 'karba tana sha tana lumshe idonta sai yanzu taji dama dama a jikinta.

Uwani na tsaka da shanya kan katanga taji tsayuwar mota, dake katangar bata da tsayi sosai ana hange na waje kafin ta ankara taga Rashida ta fito daga cikin motar Wasila ma ta fito da sauri ta ajiye rigar dake hannunta ta nufi cikin dakin da take kwana mayafi ta dauko tayi hanyar fita tana kokarin yafawa a jikinta, a soro sukayi kicibus da Rashida sai ta rungumeta tana fad'in "Rashida sai yau kuka tunani dani ko? ke da waye a cikin mota ina Wasila ya jikin nata."? Rashida ta dinga kallon mahaifiyarta ta ganinta gaje gaje yayi masifar daga mata hankali, Wasila ta shigo ta gansu sai itama ta shiga bin Uwanin da kallo jikinta sharkaf da ruwa......Gashi duk tayi wani wujuga wujuga da ita. Uwani ta rumgume Wasila tana hawaye tace" Yarinyar nan kullum dake nake kwana nake tashi a raina Alhamudullihi jiki yayi kyau masha Allahu ga cikin ki ya girma dama ai nasan mutukar kun koma gaban mai allo zai kula daku mutum ne shi mai tausayi kuma yana kaunarku." Wasila da Rashida suka shiga binta da kallo jin abinda take fad'a kan mai allo wai yau Uwani ce ke yabon mai allo lallai duniya.

Gidan suka shiga gabad'ayansu, Wasila ta dinga bin gidan da kallo ko ina kaca kaca da kazanta iri iri ga wani wari na tashi da alama shaddar gidan ta cika tana bukatar agaji warin yayi yawa.....Ta dinga bin mahaifiyarta da wani irin kallo na tsantsar tausayi da jin kai. a hankali tace"Uwani wannan wane irin 'kuraje ne a jikinki? dubi yanda fatar jikinki ta kod'e kinyi wani iri duk kin rame."! 'Kwallah ta cika kwarmin idon Uwani tace"Ku mu shiga ciki babu komai." Bin bayanta sukayi suna mamaki tabbal akwai abunda ke faruwa da mahaifiyar tasu.........Kuluwa ta fito daga dakinta kirjinta daure da dadd'aud'an zani!!! kanta babu d'ankwali tamkar hammatar d'an iska yayi wani cibiri cibiri dashi dan saboda tsabar dauda gashin kan nata har ya soma d'aukewa da kanshi wani guri da a kwai wani gurin babu.....Ganinsu Wasila yasa tasha kunnu tana fad'in "Ku kuma yaushe kuka zo."? Wasila tayi saurin kauda kanta daga kallonta dan ji tayi tsigar jikinta na tashi kallon gashin kanta ya sanya mata tashin hankali amai na taso mata....Rashida tace" Yanzu muka zo Baba mun same ku lafiya."? Kuluwa tace "Lafiya lau ina fata dai yau zaku juya domin dai muma bamu da abinda zamu baku koda yake dai ga uwarku nan na neman kudi zata iya daukar dawainiyarku." Babu wanda yace mata ta tafasa ballanta ta sauke suka shige dakin ina Uwani ke zaune tana jiran shigowarsu......Nan suka tarar da ita a zaune a gefen wata guntuwar tabarma ta zabfa tagumi! Wasila ta dinga bin dakin da kallo daki sai kace zai rufta ya durkushe gashi babu labule babu ledar kasa sai wata guntuwar tabarma wacce take nuni da cewar nan ne makwancin mahaifitar tasu.....Kwallah ta zubo mata murya na rawa tace"Uwani wannan wace irin rayuwa kike ma'kaskanciya, wannan d'akin da kike ciki ya ru'be wallahi saura kad'an ya rufta bakya tsoro watarana ya rufta dake."

Uwani na hawaye tace"Ya zanyi Wasila! Ya zanyi? nice na cuci kaina na kuma cutar daku na tabbata da kina gidan Alhaji Ahmadu da duk wannan wahalar bamu shigeta ba, nasan da tuni munfi karfin gurin zama da ci da sha da suttura, na cuci kaina na cutar daku Ubangiji Allah ya yaye mana wannan masifa."!!! Ganin tana kuka sai suma suka fara kuka ta goge hawayenta tana fad'in "Idan dan kunga ina kuka kuma kukeyi to na daina yi sai kuyi shuru." Wasila ta goge fuskarta tana kallonta.....Uwani a nutse

ta soma basu labarin wahalar da takesha a gidan da yanda kullum take cin ruwa sai kace agwagwa.

Wasila tace"Ai dole sanyi ya kamaki Uwani wannan wace irin masifa ce ace kullum mutum na cikin ruwa dubi fatar jikinki ta kod'e ta bushe ga wasu kuraje marasa kyawun gani sun feso miki a jiki.

Uwani tace"Wai sunanan ina sha musu magani da ai sunfi haka yawa a jikina." Wasila ta shiga girgixa kanta tana tunanin yanda za tayi ta kubutar da mahaifiyarta daga wannan ukuba.

Uwani ta kalli Rashida tace"Wai waye ya kawo ku a mota ne."? Rashida tace"Alhaji Ahamadu ne mijin aunti Wasila." Da sauri ta kalli Wasilan tana neman karin bayani......Rashida itace ta shiga fada mata yanda al'amura suka faru.....Uwani ta dinga washe bakinta tana fad'in "Alhamdullhi Allah nagode maka daka amsa adduata kullum.burina mutumin nan ya dawo garemu naji dadin wannan zuwan naku kuma yau zanyi bacci harda munshari." Wasila tace"To sai ki sauya kaya kije soro ku gaisa dan da kunya a shigo dasu wannan 'kazamin gidan." Uwani ta mike da sauri ta bude jakar kayanta ta dauko atamfar data rage mata dan duk kayan da tazo dasu Kuluwa ta sace taje ta siyar, sai dai kawai in ta fita taga kayanta a jikin mutane idan ta tambayesu sai suce kuluwa ce ta siyar musu shaddar wasila ma data sace gidan ma gari ta kai suka siya.........Suna kokarin fita daga cikin gidan Kawu Madu ya shigo gidan yana washe bakinsa hannunsa rike da kud'i sabbin 'yan dubu dubu kar kar dasu......Kuluwa yake kwad'awa kira ta fito daga d'aki da saurin gaske dan har zaninta na 'kokarin fad'uwa ta rike da kyau! tana fad'in "Malam ya akayi ne." Yace."Ki fito kizo ki dangwali arziki ki barshi ashe yarinyar nan Wasila matar babban mutum ce, ikon Allah yafi gaban wasa! Kuluwa kinga uban kudin da mijinta ya bani yana waje shi da abokinsa sunzo cikin wata 'karuwar mota kamar jirgin sama."! A d'amauce! Kuluwa tayi hanyar waje tana tafiya kamar zata kifa 'kasa saboda sauri! Kwata kwata ta manta a halin da take ciki babu dankwali da riga daga ita sai daurin kirji.....






Littafin na kudi ne....!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah What'spp numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*64*
Da sauri Uwani ta tare bakin 'kofar fita tana kallon Kuluwan cikin mamaki tace"Haba Kuluwa dubi yanayin da kike ciki babu suttura a jikinki kanki babu dankwali sannan kuma kike 'kokarin fita haka gaban siriki karfa ki manta mutumin nan babban mutum ne kamar yanda Kawu ya fada miki idan kin fita haka ai kin zubar mana da kima da mutunci ." Kuluwa ta hau ya'ke tana washe baki tace"Wallahi duk na manta babu riga a jikina Uban kudin dana gani hannun Malam su suka gigitani amma bari inje in sanyo riga ku jirani dan Allah." Da sauri ta koma cikin gidan jikinta sai rawa yake.....Wasila da Rashida suka bita da kallon mamaki matar mayyar kudi ce duk ta fita daga hayyacinta.....Kawu Madu kuwa na tsaye sai dariya yake yana ta dangwalar miyau a hannunshi yana lissafa kudin hannunshi, kamar zautacce ya kalli Uwani yace."Uwani kudin nan dubu hamsin ne wallahi! kai masha Allahu gaskiya naji dad'in zuwan mutumin nan Uwani ashe haka Allah yayi wa 'yar arziki amma saboda baki da hankali kika kashe mata aure, saboda kina mata bakin ciki, waye ya fada miki yanxu ana wasa da auran irin wad'annan mutanan? ai duk abinda ya faru ya fad'a min yanzu kafin na shigo sai ku godewa Allah da Allah yasa ya mai da auran dan da bai mayar da auran ba to da kun cutar damu wallahi dan wannan arzikin sai da mugani a nesa amma yanzu ko banza nasan zamu dinga samun zakka a kai a kai! idan Allah ya nufa ma wataran sai da kawai naji ance na fito an biya min kujerar makkah." Kawu Ya 'kare maganar tashi yana dariya had'e da gyara babbar rigarshi yana sake gyara xaman kudinshi a aljihu........Kuluwa ta karaso cikin wata kod'ad'diyar atamfa da wani ya mushashshen mayafi da duk ya tattare saboda tsabar yaga jiya da yau wai nan sune karshen adakarta, sai wani washe baki take ta kalli Uwani tace"Ai haka yayi ko."? Uwani dai shiru tayi dan bata da abince wa sam ma bata so Kuluwa ta bisu gani take zata iya yin wani abun na rashin hankali ita kuma bata so yanzu mutuncinsu a zube a gurin Ahmadu......Kawu ne yay gaba suka biyo bayanshi

A babban soron gidan suka tsaya Kuluwa sai l'eken kofar gidan take dan Kawu cewa yayi su tsaya anan zai shigo dashi Kuluwa duk ta 'kago sai d'aga kai takeyi tana lekawa.....Wasila taji tamkar ta gaura mata mari shin wai ita wannan matar wace irin mata ce mara kintsi da kamun kai.? 'Kamshin turaranshi ne ya bakuncin hancinsu gabad'aya, Uwani ta gyarq lullubinta hade da sunkuyar da kanta 'kasa kunyar hada ido take dashi sosai, Ita kam kuluwa fad'i take "Sannunku da zuwa Alhaji sannuku." Ahmadu da Khalifa suka samu gefe suka tsuguna a nutse aka fara gaishe gaishe, Ahmadu ya kasa tantance mahaifiyar matar tashi duk da ya ta'ba ganinta sau d'aya amma dai baya tunanin Kuluwa itace saboda yanda ta za'ke da yawa sai banbad'anci takeyi tana musu hirarraki Mikewa sukayi a tare Khalifa ne ya fara yin gaba shi kuma ya tsaya yana gyara rigarshi, kuluwa ta tsura mishi ido Kudi ya fito dasu daure a kyaure ya mi'kawa Wasila dake gefanshi a hankali yace."Ki bawa Momy ko." 'Kin 'karba tayi Kuluwa tayi wuf ta kar'be kudin tana washe baki da fad'in "Ai kunya ba zata bari ta kar'ba Alhaji Mungode kwarai Allah ya tabbatar da alkairi ya baku xaman lafiya." Uwani da Wasila ba suji dadin Abinda Kuluwa take ba, sai basu da yanda za suyi da ita......... Kuluwa da Kawu har bakin mota suka rakosu suna musu godiya da fatan alkairi, jama'ar garin sun taru suna mamakin irin bakin da Kawu Madu yayi, sai bayan motarsu ta 'bace daga gurin ne Kawu ya shiga yi musu bayani cewar Ai sirikin sa ne mutumin dake auran 'yar gidan Uwani 'yar 'kanwarshi.....
Uwani cikin gidan ta koma ta shiga daki ta had'a tagumi hawaye takeyi sosai takejin kewayar 'yayan nata amma ko babu komai zamansu a gidan Ahmadun sai yafi mata kwanciyar hankali fiye da su zauna a wani guri itama ta yarda mutumin nason 'yarta dan da baya sonta da bazai mayar da ita ba duk da tarin laifin da tayi masa.

Bayan azuhur suka sauka gajiya gami da jiri da zaman mota suka taru sukayi mata yawa, dan da kyar ma ta iya fitowa daga motar kafafunta duk sun sage sunyi tsami! Tana dan ya mutse fuska t

a rike hannun Rashida tana kokarin zama gefan shuke shuke! Ya fito daga cikin motar hannunshi rike da babbar rigarshi, Garba ya kar'bi rigar da wayoyinshi, hankalinshi na kansu yaga tana matse fuska cike da kulawa yace."Lafiya menene."? Shiru tayi mishi." Ya kalli Rashida yace."Ku shiga ciki mana karki bari ta zauna anan." Rashida ta kama hannunta suka soma tafiya, 'kafarta ta dama ce ta ri'ke ta kasa takuwa, ta rintse idanunta tana salati, dama tun a cikin mota takejin yanda cikin ke tattare mata yana dunkule mata guri guda, kwallah ta cika mata ido bakinta na rawa tace"Rashida 'kafana d'aya ta ri'ke gefan marata ya daure." Rashida tace"Ki daure anti wasila zaman mota ne yaja mu shiga ciki ka zauna sai in matsa miki kafafun naki." Yana tsaye suna magana da Garba yaga sun tsaya sai ya sallami Garba ya nufi inda suke.......Rashida na ganinshi tace"Wai kafarta ciwo take." Yace"Subahanallahi! to me ya jawo hakan."? Rashida tace "Nima ban sani ba watakila kuma zaman mota ne." Ya kalli Wasilan yaga tana kuka tana kokarin zama kasan gurin......Yace."Kada ki zauna anan mana tashi mu shiga ciki ki samu kiyi wanka sai ki kwanta ki huta."
Shiru tayi ta'ki tanka masa bala'in haushinsa takeji a ganinta ba kowa ne ya jawo mata wannan masifar ciwo ciwon ba sai shi.....Ganin tana had'a zufa a gurin rana na dukanta yasa ya sunkuya ba tare da yayi shawara da ita ba ya dauketa cak daukar jira jirai yayi mata ya nufi cikin gidan da ita......Duk da halin da take ciki sai da taji wani iri kunyar ma'aikatan gidan duk ta rufe ta tasan dai dole idan wasu ba sugani ba wasu zasu gani Uwa uba ga 'Kanwarta Rashida, rufe idanunta kawai tayi ta 'boye fuskarta cikin 'kirjinshi.....Rashida tabi bayansu tana sinne kai fuskarta dauke da murmushi sosai mutumin yake burgeta saboda irin kulawar da yake bawa 'yar uwarta.

Hajja tace"Subahanallahi! me ya faru haka."? Yace"Zaman mota ya sanya kafafunta tsami ta kasa tafiya dasu." Hajja tace"Aifa dama zaman mota ma ga mai lafiya babu dadi ballanta ga mai ciki sannu Wasila ka shiga da ita ciki tayi wanka sai suci abinci su huta.'' Baice komai ba ya shige da ita bedroom dinshi, kai tsaye bad ya kwantar da ita ya nufi toliet.

Mikewa zaune tayi a hankali tana d'an mikar da kafafunta wacce tafi takura mata da ciwo ta dan tasa kad'an! ta rintse idonta tana kiran sunan Allah can taji zillo a cikinta ta bude idanunta da sauri tana sauke ajiyar zuciya, yanzu zai isheta da kusurkusur a ciki idan ba abinci taci ba babu zaman lafiya.....Fitowa yay daga toilet din yana tattare hannun rigar dake cikin shi tayi saurin dauke kanta ya 'karaso inda take ba tayi aune ba taji ya dauketa, da sauri ta kalleshi ya d'aga mata girarshi guda, dauke kanta tayi tana zumbura baki kamar zatayi kuka itafa wannan za'kewar da yake a kanta sam baya burgeta taga sai wani rawar jiki yake mata tasan dai ba komai ya sanya shi yake mata hakan ba sai dan tana dauke da cikinshi.....A hankali ya dure ta tsakiyar bandakin yana mata wani munafikin kallo ya dora hannunshi a wuyanta, tureshi tayi ta jingina da bango (garu) gabanta ne ya soma faduwa, Ya sake matsowa kusa da ita, sai kawai ta saka kuka tana ture kirjinshi, cikin taushin murya yace"Wanka zanyi miki ba wani abu ba, ke kuka baya miki wuya ko."? Cikin nauyin baki da yanayi na gajiya tace"To ka barni mana nayi da kaina da can kaine kake min?" Ya shiga kallonta yana girgiza kanshi, yace." Daga yau nake so duk wata d'awainiya taki ta dawo hannuna ni mutum ne mai tausayin masu lalura irin taki, insha Allah mutukar ina gida zan dinga dauke miki dukanin laluranki har Allah ya saukeki lafiya."
Shiru tayi tana kallonshi anya kuwa zata amince da wannan dad'in bakin nashi? itafa tafi tunanin saboda cikin sa da take dauke dashi ne yasa yake rawar jiki a kanta.......Saukar hannunsa taji a bayanta yana kokarin zuge zuf din rigarta, ta dinga tureshi tana hawaye hakan be dameshi ba sai da ya cire mata kayan jikinta tas, ya kurawa cikinta ido da yayi kurcici a mararta, wata kwallah ce ta ciko a idanunsa, ya tsuguna gwiwa bibbiyu 'kasan toilet din ya dinga sumbatar cikin yana shafashi da hannunshi, Wann

an k'wallar dai da yake ta 'boyewa sai da ta sauka, yay gaggawar gogewa, tana kallonshi taji ya dan bata tausayi, dan janye jikinta tayi ta matsa gefe tana zum'bura baki.....Ya sake binta yana rike hannunta duk jikinsa yayi sanyi wani irin masifaffan son yarinyar yaji yana bin dukanin ilahirin jikinsa......A hankali yaja hannunta suka isa inda kwamin wanka yake ya dauketa ya shiga da ita cikin ruwan da ya had'a, ido jawur yake kallonta yana jin wani masifaffan fleening na taso mishi, soso da sabulu ya dauka ya shiga cud'a mata jikinta yana sakin ajiyar zuciya, kamar kwai yake ta'bawa haka yake cud'ata sai da ya tabbatar ya wanke ta tas kana ya dauki towel mai kauri ya nad'eta a ciki......Daukar ta yayi ya fito da ita ya zaunar gefan gado.....Vasilin ya dauko ya nufi inda take zaune, warware towel din ya shiga yi ta rike towel din mirya na rawa tace"Ni ka bari shafa mai ai bai da wuya zan shafa da kaina." Girgiza kansa yay saboda idan yace zaiyi magana cikin halin da yake ciki zai iya tona asirin kanshi, ya kar'be towel din daga hannunta ya aje gefe guda, a hankali ya haye bed din ya raba 'kafafunshi ya sanyata a tsakiya ya shiga shafe mata jikinta da vasilin din, girman nonowanta da yanda suka sake kumburi da bun'kasa shine yake gigitashi yake d'imauta shi ya dinga kokarin daurewa duk dan kar ya nuna zulamarsa a fili al'amarin ya gagara bai san sanda ya jefar da vasilin din ba ya sanya hannuwanshi duka biyun kan nonowan ya shiga lailayasu yana jan nipples din tare da sauke masifaffiyar ajiyar zuciya...... Da sauri ta mi'ke zaune tana kuka tana kare jikinta da blanket ta dinga watsa masa harara tana share hawaye......Hannu ya d'aga mata yana so yayi magana sai kuma ya fasa, jiki a sanyaye ya sauka daga bed din ya bude wardorve ya dauko mata riga da zani na atamfa (vilsco) ya mika mata muryarshi a 'kasa yace."Kar'bi ki sanya." Hannunta na rawa ta kar'ba saboda bata so tayi musu yace zai 'kara kusantarta, yana mi'ka mata kayan ya kama hanya ya fice daga d'akin hankalinshi a masifar tashe.
Da 'kyar tasa kayan tayi kwance a bed tana siyayyar da hawaye sam bata jin zata iya sakewa dashi kamar da a yanzu babban burinta bai wuce ta rabu da cikin dake jikinta lafiya ba............Bacci ne ya fara fizgarta sam yanzu bacci bayayi mata wahala, mussaman yanzu da ta samu daki mai cike da 'kamshi da sanyin na'urar sanyaya guri, bacci mai nauyi ya dauketa.
Jin shuru bata fito ba ya sanya Hajja tace Rashida ta shiga dakin ta gani ko lafiya? Rashida na shiga ta tadda ta kwance a bed tana bacci, murmushi kawai tayi ta fito tace "Hajja bacci takeyi." Hajja tace tace"Koda naji ai shuru din tayi yawa, to ga abinci can ke sai ki zuba wanda zai miki kici idan ta tashi sai taci nata." Rashida tace"Nagode hajja." Daining din ta nufa domin cin abincin.

Ahmadu kuwa kai tsaye ke'bantaccan gurin hutawarshi ya nufa dake bayan gidanshi, yayi kwance kan wani irin gado mai kamar lilo yana lilashi idanunshi a rufe abin duniya yayi mishi yawa, ada da bata kusa dashi yana daurewa amma kuma yau din nan da ya kusance ta yaji hankalinshi ya tashi sosai wanda har baya so ya sake shiga gidan ya ganta gudun aikata abinda baiyi niyya ba, ya kuma lura da yarinyar kamar tana tsoranshi yanda take zabura idan ya kusanci jikinta tilas dama hakan ta faru a tsakaninsu tunda rabuwa ce sukayi ita dashi mara dad'i! amma dai shi yanzu babu sauran wani 'kulli a cikin ranshi ya amince da tubanta kuma yana so suyi zama na kwarai zaman da kowane ma'aurata keyi, ammafa ya zauna yayi tunani da nazari hakan ba zata kasance ba har sai yayi kokarin dauke idonshi daga kanta, ba zai yuwu ba ace daga dawowarta ya fito da zulamarshi a fili dole ya dinga dauke kansa yana kuma nuna mata ba wannan ne ma'kusudin abinda ya sanya ya dawo da ita gidanshi ba, da wannan shawarar ya mike ya nufi cikin gidan dai-dai lokacin da ake kiran sallah la'asar.....Hajja da Rashida ne zaune a palon suna kallo suna hira ya shigo sannu yay musu ya nufi bedroom dinshi hajja tace"Yana da kyau idan ka shiga ka tasheta tayi sallah barcin yamma bashi da dadi ko kad'an Mafi akasarin masu ciki kuma sunfi s

on irinshi." Yace."Kwarai kuwa Hajja annabi ma ya hanemu da yin bacci tsakanin azuhur da la'asar bari na tasheta yanzu."
Yana shiga dakin ya tarar da ita ta tashi idanunta na kallon rufin dakin....Ya karaso kusa da ita cike da kulawa yace."Ki tashi kiyi sallah ina fatan 'kafar naki ya daina ciwo."? Daga masa kanta tayi yace."To alhmdullhi." Toilet ya nufa ta bishi da kallo tana ayyana abubuwa da yawa a kanshi ya fito daure da alwala ya fice daga dakin, a hankali ta sauko daga bed din ta nufi toliet din bakinta ta wanke sannan ta d'aura alwala ta fito, sallahr ma da kyar tayi saboda yana take jin wata shegiyar yunwa idanunta har rufewa sukeyi saboda rawar jiki wuyanta da hijab din da tayi sallah ta fito tana rarraba ido a palon......Hajja da Rashida na daki suna sallah sai shi kad'ai ne kan kujerar daining yana had'a abinci ya hangi fitowarta, had'a ido sukayi ta dauke kanta jikinta babu kwari ta nemi kujera ta zauna, ya gama had'a abincin cikin plate ya dauko a nutse ya kawo mata inda take, ba tayi musu ba ta 'karba ta dora saman cinyarta ta fara ci da bisimillah a bakinta ya kawo mata ruwa da lemo ya aje gabanta ya juya domin komawa daining din ta bishi da kallo tana mamakin yanda ya zama wani silent babban mutum mai kudi da shekaru gami da tarin ilimi na boka dana isilma shine ya mayar da kanshi bawa a gurinta, mamaki take sosai sai kuma wani sashen zuciyarta ke fad'a mata cewar "Duk wani abu da zai miki shi a yanzu yanayi miki shine saboda d'anshi ko 'yarshi da kike dauke dashi amma da babu cikinsa a tare dake kallo baki isheshi ba sai dai idan jarabarshi ce ta kawo shi. Girgixa kanta tayi kawai tana adduar Allah yasa ta sauka lafiya tagani zai cigaba da hidima da ita ko kuwa.





Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book na barki da Allah! Kema kika karanta baki biya ba na barki da Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*65*
Koda ya kammala cin abincinshi sai ya mike a nutse ya nufi bedroom dinshi yana tafiya tamkar wanda 'kwai ya fashewa a ciki, shi kad'ai yasan abinda ke damunshi, hakika dawowarta gidan nashi na barazana da lafiyarshi dan tun suna cikin mota yake ta fama da joystick dinshi yana hanata aikata abinda takeso dan duk abinda yake daurewa yake yi a yanzu dai idan ba samu yayi ya rage damuwa ba to tabbas dai ya san

Please Login or Register in order to submit comment