Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba na tafi domin a ranar ana bikin wata friend dina ne." Yace."Masha Allah kema ai yana da kyau ki futar da miji kiyi aure Zeey kin kwana biyu fa."
Zeey tayi dariya me shashshe'ka tace"Yalla'bai kenan aini da aure sai dai inga anayi namiji daya nake so a duniya amma ya'ki aurana."
Yasan inda maganarta ta dosa sai ya nuna bai gane komai ba, Yace."Zeey meye abunki? kina da ilimi sosai kana kina da kyau dai-dai gwargwado me kuma ake nema."?
Murmushin takaici Zeey tayi tace"Duk da ina da abubuwan da ka

fad'a yanzu to shi banyi masa ba."
Dariya yasa yana d'an sosa gemunsa yace."Haba dai sai kace makaho ni da ba dan nayi aure ba da kawai na shigo anyi dani." Zeey tayi wata dariya me shashsheka tana sake ma'kale murya tace"Ashe kasan inda maganata ta dosa tunda naga ka d'auko hanya, Yallabai ko yau kazo ni a shirye nake dama ai Ubangiji cewa yay kuyi Hud'u mutukar zakuyi adalci." Ya bud'e bakinsa zaiyi magana yaga ta jefar da cokalin hannunta ta mi'ke rai a 'bace ta bar gurun......Ya bita da kallo har ta bude daki ta shiga ta bugo kofar da karfin gaske.....sai kawai ya girgiza kansa ya cigaba da hira da Zeey inda take ta tsara masa kalamai ita dole sai ta samu shiga a gurinsa........Yace."Ki bari zan duba maganarki a tsanake zan kira ki a waya." Cike da farin ciki da jin dadi Zeey tace"Shikkenan Yallabai ina sauraranka." Kashe wayar yay ya ajiye ta kusa dashi ya gyara zamansa sosai ya cigaba da cin abincinsa.


Koda ta shiga dakin kwanciya tayi kan bed taci kukanta ta koshi ta kuma dauki al'kawarin yi masa rashin mutunci tunda dai shi bai san hakkin d'an adam ba in bansa wulakanci da rashin mutunci ya rasa ma a inda zaiyi hira da budurwarsa sai gidanshi kuma a gabanta lallai zata nuna masa cewar ta san abinda takeyi duk da take jahila to tasan ciwon kanta.


Sai da ya kammala cin abincinsa a tsanake tukkuna ya bita dakin, lokaci har tayi wanka ta kwanta tana bawa baby zahra nono ta tashi daga bacci, yazo ya tsaya kansu yana kallonsu, ganin yanda tayi bala'in shan kunu ne ya sanya ya kasa cewa da ita komai sai kawai ya tsuguna ya mannawa 'yarshi sumba a saman goshinta ya mi'ke ya fita daga d'akin.


Da 'kyar bacci ya dauketa saboda tsabar bakin ciki da takaici, ta tashi da safe cikin rashin walwala har Hajja ta shigo dakin suka gaisa ta shirya zahra har taso ta fahimci wani abu amma dai ba tace mata komai ba itama so take ta cika ar'bain ta tafi ai tayi abinda tayi, Hajja na fita da Zahra ita kuma ta shiga toilet domin yin nata wankan.
Kafin ta fara wankan sai da ta shiga cikin ruwan d'umi tayi minti goma sha biyar sannan ta fito tayi wankanta da sabulai masu kyau da kamshi ta fito daure da karamin towel iya cinyarta.........Ashe yana zaune a dakin ya shigo tana toliet sai ya zauna zaman jiran fitowarta.......Ganin ta a haka fatar jikinta na wani irin she'ki da sul'bi ga santala santalan cinyoyinta a waje dik sai ya rasa nutsuwarsa ya dinga binta da wani mayen kallo har ta wuceshi ta nufi mirror tana zum'buro bakinta tare da sauya salon tafiyarta.
Kasa daurewa yay ya mi'ke ya nufi inda take......Tana sane ta bude towel din wai zata sake d'aurawa aikuwa ya hangota ta madubi hankali a tashe yaje ya ri'ke towel din yana kokarin fuzgewa daga hannunta.
Ta dan tureshi kadan ta bar masa gurin......Matseta yay jikin wardorbe yana rarraba idanunsa a jikinta..........Ta dinga ture kirjinsa tana son yin kuka amma dai ta daure saboda bata so ya dinga raina mata hankali....."Wai dan Allah meye haka bafa girmanka bane hakan da kakeyi ka kyaleni ni nasa kayana, kuma gidan nan dole ne ma na barshi dan ba zan zauna a inda ba'a bukatar dangina ba.'' A kausashe take maganar tana tuttureshi daga jikinta
Muryarshi ba sosai take fita ba yace."Wace irin magana kikeyi ne waye baya kaunar dangin ki da har kike ikirarin barin gidan auranki."
Sai ta fashe da kuka tana wani irin bubbuga 'kafafunta ta tureshi da 'karfi tana haki ta matsa gefe tana kallonshi tace"Eh dama zaka fad'i haka mana yau kwanan Inna Hajara nawa da tafiya ka ta'ba tambayata dalilin tafiyar ta!? Sannan yau kwanana nawa da haihuwa me yasa baka ta'ba tunani koda sau d'aya ne kace bari ka tura d'aya daga cikin yaranka domin yaje ya dauko mahaifiyata kan tazo taga abinda na haifa, na sani dama tuntuni na san da cewar baka dauki Uwata a matsayin komai ba dan da ka dauketa da daraja to da duk inda take kaje ka gaisheta da kanka kuma ka shaida mata na haihu da abinda na haifa.....To nagaji ni ba shashasha bace nasan kuma inda ke min ciwo zanyi tafiyata in yaso sai ka auro wacce kake ganin Iyayenta sune dai-dai da kai da kimarka."
Tana gama maganarta ta bude wardorbe ta duba kayanta t

a dauki riga da sket na wani had'addan swiss less ta shirya jikinta duk yana tsaye kamar gunki yana kallonta da mamakin kalamanta, bude kofar dakin ce ta sanya shi dawowa hayyacinsa, yay gaggawar kallon bakin kofar sai ya hango ficewarta daga dakin tare da jan kofar da karfin gaske.







Littafin na kudi ne!
Idan kika futar min da book keda Allah! Idan kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*77*
Ya jima a tsaye a tsakiyar d'akin yana mamakin irin maganganun da yarinyar ta watsa masa, ransa yayi masifar 'baci sosai ashe raini har ya soma shiga tsakaninsu tunda har zata iya d'aga masa murya! gurin magana tana fad'a masa duk maganar da tazo bakinta tana d'aga masa harshe kamar zata zageshi Idan tana so ta nusar dashi abinda ke zuciyarta ai sai tayi masa bayani cikin fahimta ba da irin wannan sigar ba, dole ne ma ya dauki tsatstsauran mataki a kanta, idan dan wannan abun na jikinta take kokarin zaginsa to taje ta ri'ke kayanta zai nuna mata shi d'an halak ne.
Koda ya fito daga 'dakin bai kalli inda suke zaune ba ya wuce bedroom dinsa ransa duk a jagule.

Wasila kuwa jin zuciyarta take wasai tunda ta samu ta fad'i abinda ke cikin ranta shikkenan itama ta dauki al'kwarin akan ba zata sake zama ya dinga raina ta ba ballanta har ya dinga d'aga wayar 'yan matansa a gabanta sai ta nuna masa itama macace wacce tasan abinda takeyi.


A shirye ya fito da shirin fita, ya tsaya suna magana da Hajja, Hajja tace"Nima fa na kusa tafiya tunda dai Allah yasa ta haihu lafiya shikkenan zan koma gida." Yace."Kiyi hakuri kiyi zamanki tare damu." Tace"A'a dai gwara na kuma gidana bana dinga zama cikin yara ba." Yace."Hajja ai zaman naki cikin Yara gyara kike ba 'barna ba." Wasila da kanta yake sunkuye tayi saurin dago kanta tana kallonsa, sai taga kamar magana yake fad'a mata kan Inna Hajara oh! wannan mutum baya barin takwana! wato Yana nufin Inna Hajara itake aikata 'barna kenan......Mi'kewa tayi ta bar musu gurin ba tare da tayi kuskuran kallonshi ba, Hajja ce ta bita da kallo sosai ta fuskanci akwai matsala a tsakaninsu amma kuma ba za tayi masu magana ba sai ranar da zata tafi tukkuna idan kuma sun dai-daita kansu shikkenan.

Yana fita Garba ya daukeshi a mota kafin ya ajeshi cikin ma'aikatarshi yake Umartarshi da cewar idan ya saukeshi ya nufi can garin su Uwani Patskum yaje ya sanar musu da cewar Wasilan ta haihu idan da me ra'ayi zuwa yaga abinda ta haifa sai ya dauko shi yazo dashi.....Hakan ce ta kasance Garba na saukeshi sai ya dauki hanya kamar yanda ya umarceshi.


Suna zaune a palo bayan azahar dan uku ma ta kusa Rashida ma ta dawo daga makaranta, kawai sai sukaji sallamarsu su Uwani da Kuluwa dasu Inna Tabawa........Rashida ta mi'ke a guje taje ta bude musu kofar falon suka shigo ciki....Wasila ta mi'ke tsaye fuskarta cike da! walwala da farin ciki mara misaltuwa, Tabawa Iya mai waina da Uwani suka nemi guri suka zazzauna a nutse ita kuwa Kuluwa sai kalle kalle take tana ya'ke dafaffun ha'koranta da kyar ta zauna kan kujerar tana wani irin abu irin na marasa gaskiya......Hajja ta dinga fadin "Sannuku da zuwa kai masha Allah sannuku Wallahi ko jiya sai da mukayi zancenku ashe kuna tafe." Inna Tabawa tace"Aikuwa dai munata sa rana sai yau Allah ya nufa yau din ma Ai maigidan nan ne ya tura a ka dauko mu.....Kuluwa tayi saurin kar'be maganar tace"Wallahi kuwa ai rashin kud'in mota duk shine yayi mana cikas da tuni munzo anyi hidimar suna damu ace yarinya ta haihu babu danginta ai da kunya gashi duk muna raye a duniyar."
Wasila taji kamar ta kwada mata mari jin abinda take fad'a shashashar mace kawai daga zuwanta har ta soma sakin layi....Ita kuwa Hajja murmushi tayi kawai ta mi'ke tana kallon Rashida tace"Kije ki kawo musu abinci tunda Rabe ya fita.'' Rashida ta mi'ke ta nufi kicin cike da takaicin Kuluwa da haukanta.

Kuluwa sai washe baki take tana kallon baby zahra dake hannunta tace"Yarinyar tubarakallah kyakykyawa gata da jikin girma kamar tayi wata uku kai masha Allah." Uwani ta kalleta tana dan jan tsaki cikin ranta, shiyasa fa taki amincewa da zuwansu tuntuni saboda hauka da rashin kamun kai irin na kuluwan

Inna Tabawa ta kar'bi yar tana sanya mata albarka kana ta mi'kawa 'Yar uwarta iya mai wani itama ta sanya mata albarka ta mi'kawa Uwani, kunya ta hana ta 'karbar yarinyar sai dai tace"Allah ya rayata tafarkin addinin musulunci." Ganin ta kasa kar'bar yarinyar yasa Kuluwa dashare baki tace"Uwani kunya ki keji ne ai dole jikar 'yar fari hahahahaha." ta karashe maganar tana dariya kamar sabuwa

r mahaukaciya sai wani mutsu mutsu takeyi......Uwani girgiza kanta tayi tayi mata banza ba tace mata komai ba haka su Inna Tabawa dama suma haushinta sukeji.........Koda Rashida ta jere musu abinci kan daining Kuluwa kasa zama tayi kan kujerar sai kauyanci takeyi duk ta hargitsa musu guri.....Wasila tace"Rashida ki kwashe abincin daga dainnig din ki shirya musu shi kan daddumar can ta gefe sai sunfi jin dadin hakan."
Da sauri Kuluwa tace"Aikam dan gaskiya zama kan wannan abun ba zaiyi dadin cin abinci ba gwara mutum ya zauna a 'kas yanda abincin zaifi tsirga masa.

Cike da takaicinta tace"Dan Allah Kuluwa ki nutsu mana bafa a aljanna kike ba da kike ta wannan rawar jikin haba! ki daina haka dan Allah idan ba haka ba to ni kada ki sake zuwar min gida dan ba zaki zo ki bani kunya ba.'' Kuluwa ta hau ya'ke cike da kunya tace"Yi hakuri 'yar nan al'amarin ya rud'ar dani wallahi ban ta'ba shiga irin wannan daular ba sai yau gaskiya ke d'in 'yar baiwa ce Allah ya samu a danshin ku."
Tsaki kawai Wasila tayi ta bar gurin, Uwani tace"Kuluwa kafin muzo gidan nan fa sai da mukayi magana dake wai me yasa kike hakane kada da mai gidan nan ya shigo ki bamu kunya a gabansa."
Kuluwa tace"Kai jama'a wai ya kuke so nayi ne? to shikkenan bari nayi gum! da bakina na daina sanya albarka tunda dai itace bakwa so nasa." Rashida tace''Hakan shine yafi alkairi dake." Kuluwa taja bakinta tayi shuru sai dai muzurai kawai takeyi tana gyara zamanta, haka suka ci abinci mai cike da nama da lemuka masu sanyi

Bayan sun gama cin abincin Hajja ta fito daga daki tana kallon Wasila tace"Yana da kyau ki kira mai gidan a waya yazo su gaisa tunda naji kamar suna cewa yau zasu koma." Ai kafi ma Wasilan tace wani abu Kuluwa tace"A'a ba yau zamu koma ba sai mun kwana biyu tukkuna dan haka malam yace mu zauna mu yauta tukkuna." Hajja tace"A'a to masha Allah hakan ma yayi kyau ai babu damuwa." Ita kanta Hajja ta fahimci matar kamar bata da hankali.
Wasila jikinta yay sanyi ganin abin na Kuluwa naso ya wuce gona da iri babu shakka baza ta so zamansu a cikin gidan ba ba dan komai ba sai dan kada su zauna Kuluwa ta zubar musu da d'an sauran mutuncinsu da suke dashi a idon maigidan dama hakan ma ya aka kaya yana musu wani irin kallo to ballanta kuma yazo yaga irin haukan da Kuluwa takeyi ai raini ne zai sake shiga tsakaninsu......Ke'bewa sukayi da mahaifiyarta Tace"Uwani gaskiya gwara ku tafi ni bana so ku zauna a gidannan saboda waccan matar mara hankali kawai idan Kunyi sallah sai ku tafi."

Uwani tace"Rabu da shashasha, ai dama mu ba zama zamuyi ba sai kace wasu marasa hankali yau din nan zamu koma tunda Allah yasa mun ganki lafiya da yarinyarki ai anyi barka ita idan zata zauna sai ta nemi guri kwad'ayayyar banza kawai."
Wasila tace"Ai naga alama so takeyi ta zauna min a gida kuma baza ta zauna ba wallahi." Uwani tace"To yaushe ma ai 'kafarmu 'kafarta." Wasila ta shiga bata labarin irin zaman da sukeyi dashi da kuma dalilin da ya sanya Inna hajara barin gidan.
Uwani tace"To in banda abinshi shikkenan daga an haihu babu wani gyara sai a koma masa ai ba zakiyi daraja a idonsa ba kada ki yarda ya kusance ki sai kin gyara kanki sannan kin tabbatar wannan d'inkin da akayi miki yayi dai-dai sannan idan kin koma masa a haka yazo yaji wani sauyi ai wulakanci ne zai biyo baya."
Wasila tace"Nima abinda nake so ya fahinta kenan ya kasa fahinta." Uwani tace"Aikuwa ba zai ta'ba fahimta ba tunda idanunsa sun rufe kiyi kokari kawai ki san yanda zakiyi ki biya masa bukatarsa idan ta taso kuma kada ki dinga yi masa rashin kunya tunda kinga ba sa'anki bane ni da nake mahaifiyarki watakila ma ya girme ni." Hawaye ta share tace"Uwani nifa bana mishi rashin kunya sai jiya da yau da safe kuma duk shine ya jawo kin san dama can ni bana shiri da wanda ba zai ga darajar iyayena ba Uwani banta'ba jin kaunarki da tausayinki cikin raina ba sai da na haihu sannan na tabbatar da cewar Uwa uwace kuma dolene kayi kishinta koda mahaukaciya ce." Uwani tayi murmushi a hankali tace"Ai dama baka ta'bata sanin me duniya take ciki sai ka haihu tukkuna zakayi hankali Allah yay miki albarka, dake da d

uk zuriar da zaki samu." Wasila ta amsa da ameen tana goge hawaye ta mike a nutse ta shiga janyo manya manyan akwatinan dake gefe a jere
Manya manya atamfofi ta shiga fitowa dasu da mayafai masu kyau da tsada, ta zubesu gaban Uwani tace"Ki za'bi wad'anda sukayi miki sauran kuma sai ki bawa su Inna mai waina." Uwani ta shiga d'aga atamfofin tana dubawa tace"Masha Allahu mungode sosai Allah yayi miki albarka." ta amsa da ameen tana zuba mata kayan cikin sabuwar akwati.....Wani dan karamin akwati ta dauko ta bude kudi masu yawa ne a ciki ta tura gaban Uwanin tace"Ki d'ibi iya yanda kike so wannan kud'in da tarin atamfofin nan na samesu ne a haihuwar da nayi....Uwani ta tsorata da ganin Uban kudin dake cikin akwatin tace" Ki dai bani abinda kikayi niyya Wasila duk wannan kudin naki ne."? Girgiza kanta tayi tace"Uwani basu kadai bane ma kinga wad'annan takardun shaidar mallakar rumfuna ne cikin babbar kasuwar dake cikin gari (sabon gari) wanda maigidan ya mallaka min duk saboda ya sameni cikkakiyar budurwa yanzu haka ban san iya adadin kudin da ake samu ba cikin ko wace rana, yace dai zamuje a bude accont ya dinga sanya min kudin a ciki." Uwani ta fashe da kuka tana kallon 'yar tata tace"Nagode Allah da mazon Allah da Allah be sanya kun d'auki hud'ubata ba kun zubar da mutuncinku a titi nasan da mutumin nan be sameki cikkakiyar mace ba da ba zai miki wannan halaccin ba, kuma da tuni zamanku Baiyi nisa irin haka ba ('kalube gare ku 'yan mata kuyi tattalin budurcinku domun ku mi'ka shi ga wanda ya dace shine mijin auranku, koda namiji bai maka kyauta ba to abin alfahari ne ya sameki cikakkiyar mace)

Wasila tace" Kinga dama abinda nake ta so ki gane krnan nima nasan da bai sameni da budurci ba da tuni ya sakeni wallahi." Uwani ta goge hawaye tace"A koda yaushe ina alfahari dake Wasila kuma kullum cikin shi miki albarka nake shiyasa kike ta samun cigaba a rayuwarki, nasihata zuwa gareki shine kiyi wa mijinki biyayya ku zauna lafiya da juna kada naji kada kuma nagani yanzu wannan mutumin shine uwarki da ubanki kuma shine gatanki duk wani umarni da zai baki kibi mutukar bai sa'bawa addinin Allah ba." Wasila tace"Insha Allah Uwani zanyi kokari nagode....... Wasila ta irgi kudi kimanin dubu dari biyu ta zuba mata cikin akwatin tace "Uwani gashinan ki siyi waya kiyi sana'a da sauran ga numbar wayata zan rubuta miki idan kun koma gida sai ki kirani mu dunga gaisawa duk kuma abinda kike so ki siya kici abinda baki dashi kiyi min waya insha Allah zamu zo nida rashida bada jimawa ba." Uwani tace"Kudin da kika bani basuyi yawa ba kuwa kada na aje Kuluwa ta sace." Wasila tace"Kada ki aje akwatin a gidanta ki kai kayanki kidan Inna Tabawa." Uwani tace"Yawwa to hakan zanyi." Mi'kewa sukayi a tare suka fito palo, suka tarar da Rashida da Kuluwa sai musayar yawu sukeyi Hajja na musu dariya Kuluwa da dai taga kowa nayi mata kallon mahaukaciya sai ta shiga taitayinta ta kimtsa kanta sai dai har yanzu ba ta daina mamaki da al'ajabi ba.

Uwani tace"To Hajja mun fito mu zamu tafi." Hajja tace"A'a ba zaku tsaya maigidan yazo ba ku gaisa." Uwani tace"Ai yamma tayi." Hajja tace"Kuma da naji Kuluwa tace kwana biyu zakuyi." Uwani tace"Haba Hajja kamar wasu marasa hankali ai tunda munga lafiyar yarinya da abinda ta haifa zaman me zamuyi." Kuluwa tayi saurin kallonta tana so tayi magana, Uwani tayi bala'in shan kunu babu fuska, Kuluwa ta sunkuyar da kanta 'kasa ranta duk a 'bace! lallai idan sun koma gida sai ta shukawa Uwani rashin mutunci tunda tana ba'kin cikin su zauna suyi kwana biyu su dandali arziki.
Hajja tace"To ke Wasila baki kira mijin naki a waya ba, ai be dace ba ace su zo baizo sun gaisa ba." Tace."Hajja kina ji fa Inna Tabawa tace shine ya tura aka d'aukosu ai yasan da zuwansu."

Hajja tace"Eh 'kwarai kam amma kika sani ko wani abune ya dauke masa hankali tunda kinga kwana biyun nan abubuwa da yawa suna dauke masa hankali, yana da kyau ki sanar masa da zuwan nasu watakila ko mantawa yayi." Tace"Shikkenan Hajja." Daki ta nufa domun kiran wayarshi kamar yanda Hajjan ta umarceta sam bata so suyi ta jayayya da matar.

Suna tare d

a khalifa yaga kiran wayarta sai ya aje wayar suka cigaba da abinda sukeyi shi da Khalifan wanda har ya shiga mamakin ganin bai daga wayar ba ya sanya yace."Da alama dai 'yan mata da zawaran dake damunka ne tunda naga baka dauki wayar ba.'' ba tare da ya bawa maganar mahimanci ba yace."Wasila ce." Khalifa ya kalleshi cike da mamaki yace."Lefi tayi kenan ake hukuntata ta wannan hanyar." Murmushin takaici yay mai tafe da bacin rai yace."Khalifa na ta'ba ganin wanda ya samu damar da wannan yarinyar ta samu a kaina kuwa."? Khalifa ya girgiza kansa yace."Gaskiya ban ta'ba gani ba nima kana sonta sosai dan duk wasu alamu sun nuna." Ya girgixa kanshi cikin takaici yace."Nima nasan da haka khalifa wannan damar data samu ce ta sanya take takani yanda ranta yake so yarinya 'kankanuwa ta dinga nuna ni da yatsa tana daga mun murya gurin magana tamkar zata zageni."
Khalifa yace."Subahanallahi! me ya janyo hakan." ?Tsaki yaja yace."Saboda kawai na nemi hakkina shikkenan cibi ya zama 'kari."
Khalifa yace."Ban gane ba."? A nutse ya kalleshi ya dan gyara zamansa ya soma warware masa abinda yake faruwa tsakaninsu."
Khalifa yace."Kai nifa shiyasa sam bana son wannan zaman jegon wallahi duk daga wannan zaman ake lalata maka mata , yanzu ita wannan matar abinda tayi shine dai-dai da girmanta da komai ta dinga d'ora yarinya kan turba mara kyau, idan bata sauke maka bukatarka ba gurin wa zakaje tunda kai ba manemin mata bane."
Ya sauke ajiyar zuciya ransa a 'bace yace."Allah Khalifa yarinyar nan tayi wasa sai na 'kara aure bana son hauka da da'ki'kanci wallahi kuma zata gane bata da wayo." Khalifa yace."A'a kayi hakuri dai ka cigaba da rarrashinta kasan yarinya ce."Tsaki yaja yace."Allah ya sawa'ke khalifa bazan kuma zuwa gunta sa wata bukata ba taje ra rike kayanta nima na rike nawa zan kuma fara neman aure."
Khalifa yace"Yanzu ka sauka daga kan ra'ayinka kenan."?
Yace."Duk wani abu da zanyi itace ta jawowa kanta ni babu ruwana." Khalifa yace."To Allah ya za'ba abinda yafi alkairi." Ya amsa sa ameen." Lokacin kiran ta ya sake shigowa wayar tashi yana ganin sunanta ya kashe wayar yana jan tsaki.

Cike da takaici da mugun ba'kin ciki ta fito daga d'akin murya na rawa Tace"Hajja bai dauki wayar ba watakila ko baya kusa da wayar ne." Hajja tace"E to hakan na iya kasancewa." Mikewa tayi ta shiga daki tana fad'in "Ku dan jirani na fito."
Uwani dasu Inna Tabawa suka mike Wasila ta jagorace su suka fita Ita Kuluwa zama tayi har sai da Hajja ta fito daga daki ta mi'ka mata karuwar ledar dake hannunta tace"Gashinan turaman atamfofine da mayafai da sabulai sai ku kasafta a tsakaninku." Kuluwa ta kar'be da sauri jikinta na kyarma sai washe bakinta take tana ta zabga godiya, Hajja tace."Babu komai Kuluwa ku gaida gida mungode."

Suna can parking spece Kuluwa takaraso hammatar ta ma'kale da ledar kayan da Hajja ta basu sai murna takeyi tace"To Wasila da Rashida mu mun tafi sai mun sake zuwa ke Wasila idan maigadan nawa ya dawo to ki mi'ka gaisuwata gurinsa tunda dai rowarsa kike mana." Wasila tana daure fuska tace"Zai ji ku gaida gida ku gaishe da Kawu Madu." Suka dinga amsawa da "ameen." Duk suka shiga cikin motar Garba yaja suka fita daga cikin gidan......Wasila da Rashida suka juya jikinsu a sanyaye suka koma ciki To itama Uwanin dai daurewa kawai takeyi amma zuciyarta babu dad'i sam! tana bala'in 'kaunar 'yayanta kamar yanda suke 'kaunarta.





Littafin na kudi ne......!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*78*



_*Sa'ko na mussaman zuwa gareka Amadu 'kawayen Wasila irin su Mumy Farhan, Bomis Zainab kankara Mrs Aliyu Nafisa Buhari Hauwa Chindo, Sakina Ummee da dai sauransu, sunce kayi hakuri dan Allah karkayiwa Wasila kishiya kayi mata uziri saboda yarinya ce, idan kuma ka kuskura ka 'kara aure to zaka gane baka da wayo dan duk wacce zaka aura ba zata kama 'kafar Wasila ba, zaka dawo inda kake salati kana kiran sunan Allah😅🤭 babu ruwana Sistar Sakina ce tafad'a🕺🕺 sannan Sistar Jamila tace duk wacce zaka aura sunanta salamatu salam dan ba zata iya da jarabarka ba🕺 babu ruwana! Jamila da Ummee ne suka fad'a ni dai 'yar aike ce......Momyna tace kayi auranka dan ba Wasila ce kadai mace ba, takwara Fatima Yakubu ma haka tafad'a Sai sistar Hadiza Shall itama haka tace ka more rayuwarka, Shafa'a S Yari da Bilba sunce kayi aure ka more rayuwarka💃🏼🔥 ni dai na isar da sa'kona Amadu sai ka yanke shawarar da zata fishe ka, nima nace ba Wasila ce kad'ai autar mat.......🙊😌*_



Cikin sanyin jiki suka koma cikin gidan Hajja ta gansu duk babu kuzari a tare dasu tace"Ai kam ni kaina naso su zauna su danyi kwana biyu ku samu sakewa da mahaifiyarku amma ace daga zuwa sai su tafi wallahi banji dadin hakan ba sai kace wad'anda ake kora."
Rashida ta goge hawaye tace"Nima naso su zauna wallahi yanzu anti Wasila yaushe zamuje to." Wasila ta kalleta ranta duk babu dad'i tace."Sai an d'an kwana biyu baby tayi 'kwari zamuje insha Allahu." Hajja tace"Kwarai kuwa hakan yana da kyau, Allah ya kaimu ya bamu lafiya mai amfani." Duk suka amsa da "ameen."

To har dai kusan goma da wajan rabi bai shigo gidan ba Hajja na kokarin shiga daki ta kwanta ya shigo da sallama a bakinsa......Dukaninsu suka amsa suna masa sannu da zuwa.
Ya kalli Hajja

Please Login or Register in order to submit comment