Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Girgiza kanta ta shigayi tana mamakin halin dan adam ko a mafarki idan ance mata Camas za tayi mata haka ba zata yarda ba sai gashi babu shakka mutum abin tsoro ne.

Yace."Je ki kira Rashidan mu fara zaman karatun yanzu." A hankali ta sauka daga bed din ta fita daga dakin, Ya dauke idonsa bayan fitar ta yana girgiza kanshi, yana jin zai iya sadaukar da farin cikinsa da duk wani jin dadinsa mutukar yarinyar zata samu walwala da farin ciki.


Lokacin da ta shiga
dakin, Hajja na zaune kan dadduma da carbi a hannunta ita kuma rashida ta idar da sallah tana kwance kan daddumar bacci na kokarin dauketa.......Ta samu guri ta zauna a nutse suka gaisa da Hajja tana tambayarta jikinta, Tace jiki da sauki alhamdullihi." Rashida ta mike tana mutsika idanunta suka gaisa tace"Kizo zamuyi karatu." rashida ta mike tare da zura hijab dinta suka fita daga dakin, hajja kuwa ido tabisu dashi haka kawai take tausayawa yaran.


Palo suka taddashi zaune kan katuwar dadduma gabanshi da al'kur'anai da kuma sauran litattafan addini........Ya bawa ko wacce al'kur'ani guda d'aya ya umarce su bude 'kasa, zasu fara daga fatiha ne.
Ko wacce ta bude nata a nutse yayi bisimillah ya soma karatu cikin nutsuwa da 'kira'arshi mai kyau da dad'in saurare, nutsuwa sukayi sosai suna saurarashi, sai da ya maimaita musu fatiha da fala'ki da nasi sau uku sannan yace su karanta masa yaji." A tare sukayi bisimillah suka soma karatun cikin nutsuwa, ya dinga sauraransu har suka kammala, yaji dadi sosai yanda ya biya musu haka sukayi, yace su rufe alkur'ani suka, Ya dauki littafin ahlari yana dubawa, a nutse ya soma karanto musu yana musu bayani dalla dalla bayanin jinin haila da hukunce hukuncensa bayanin janaba itama da hukuncinta shuru sukayi suna sauraranshi, dan wani gurin idan ya fada kunya ce take rufesu sai suka lura shi bai damu ba karatunsa yake yana so su fahimci abunda yake so su fahinta, bayan sun kammala karatun sai ya sallami Rashida ya mai da hankalinshi kan Wasila tana zaune jikinta duk yayi sanyi bata ta'ba tsammanin yana da ilimi irin hakaba sai taji ya sake yi mata wani kwarjini a idonta, A nutse yace" Wasila meye banbanci a cikin wankan haila da janaba niyya iri d'aya ake ko kuma ta bambamta."?

Ta dan kalleshi a nutse tace"Akwai bambamci mana." Yace."Kiyi min bayani sosai." Tace"Niyyar wankan haila daban niyyar wankan janaba daban amma duk wankan iri d'aya ne." Yace."Meye janabar meye kuma haila."? d'an tura baki tayi tana mi'ke kafafunta ita tagaji da wannan tambayoyin yace."Idan baki min bayani ba zan dauka baki da ganewa da saurin fahimta."

Tace"Janaba itace "Kamar mutum yayi rayuwar aure da mijinshi to janaba ta hau kanshi sai yayi wanka wanda ya zama farillah kamar yanda annabi ya koya mana."

Yace."Na gamsu da wasu bayanan naki sai dai kuma har yanzu baki fayyace min meye janaba ba da yanda zan fahimta kince rayuwar aure ni dake yanzu haka rayuwar aure mukeyi ina so ki fahintar dani shin rayuwar aure wace iri? Kamar zata fashe da kuka tace"Kamar yaya."? Yayi murmushi yana kallonta a nutse yace."Kamar yanda nayi miki bayani." shuru tayi mishi yace."Nasan rashida ta fiki gane karatu bari na kirata tayi miki bayani kuma mutukar tayi miki bayani abinda nake so ku fahimta sai nayi miki bulala! ita kuma nayi mata kyauta.'' mi'kewa yake kokarin yi ta rikeshi tana kuka "Ni wane bayani zanyi to bayan nayi maka bayanin abinda na fahinta! Ni kar ka kira rashida me ta sani a cikin abinda kake fad'a ai har gwara ni nafi ta fahinta." Ya koma ya zauna yana dariya, yace."Ai saboda nasan kin fita fahintar ne yasa na sallameta ke nace ki zauna kiyi min bayani, to gashi kin kasa min bayani gamshashshe wanda zai sa na gamsu."
Hawaye ta share tana zumbura baki, gashi ta rirrike masa riga kusan ma rabin jikinta duk yana jikinsa, Cikin kasalalliyar murya yace."Tashi muje ciki ni nayi miki bayanin yanda abin yake, in yaso bayan na gama sai ki fahimci yanda janaba take a kan mutum." Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya, ya dan janyeta daga jikinsa yana kokarin mikewa ta rikeshi! ita bata so ya kira Rashida ai abin kunya ne ma ya tambayi rashida yanda janaba take! Shima dama wasa yake yi......Yace." bakya jin kunyar wani ya fito ya ganki haka kina kuka kamar kankanuwar yarinya."? Tace"Dan Allah kada ka kira Rashida wallahi na fahimta." Yace."Nima da wasa nakeyi ai, ai nace muje d'aki na nuna miki ko." Sauka tayi daga jikinsa ta koma gefe guda tana ya mutsa fuska......Girgiza kanshi yay ya mi'ke a nutse yana fad'in "Kinbi kin nukurkusa min jikina yana tsami! kizo kiyi min tausa." Kallonshi tayi kawai ya wuce bedroom dinshi Yana shiga ya cire jallabiyar jikinshi ya kwanta bed yana rintse idanunshi, da so samu ne ya samu ko dan romantic ne ya samu yayi to amma sam baya son takurawa yarinyar zai dai cigaba da daurewa Allah yasa zai iya............Bacci me nauyi ya daukeshi ita kuma ta zauna a palon saboda tana jin tsoro ta shiga dakin yayi mata wani abun, Hajja da rashida suka fito daga dakin.........Dai-dai da lokacin da Rabe ke shirya musu daninng, Wasila na kallonsu suka nufi daninng din tayi zamanta a inda take har suka kammala suka isketa Hajja tace"Lafiya baki karya ba ko bakijin dadi ne."? Tace"Hajja kafin asubah naci abinci bana jin yunwa yanzu sai zuwa anjima nasan zan nemi abinci." Hajja tace" To shikkenan ki dai dunga ci kina koshi domin ki samu kuzari da kwarin jiki duk da nagani baki wasa da cin abinci." Rashida tace"Ai hajja wannan baby nasan kato ne anti wasila fa kullum cikin cin abinci take babu dare babu rana." Hajja tasa dariya tana fad'in "Ai lafiyace ta jawo haka ana so mai ciki ta dinga cin abinci sai kiga ta haifi yaro lafiyayye mai ban sha'awa." Wasila dai murmushi tayi kunyar hajja take, sai ma ta mike ta nufi daki tana murmushi ita kanta tasan dolene ta haifi katon d'a dan ganin irin abincin da take narka sai kace jaka.......Kusa dashi taje ta kwanta a hankali ta d'ora kanta kan kirjinsa tana lumshe idanunta, sai taji saukar hannunsa a bayanta, tayi yunkurin mikewa ya riketa sosai! idanunsa a rufe! sai tayi luf a jikinsa tana sauke numfashi, jin baiyi mata komai ba yasa ta saki jikinta sosai bacci ya dauketa a jikinshi.





Littafin na kudi ne!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*67*
To haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya cikin kwanciyar hankali gami da samun nutsuwa, sosai Amadu ke kula da Wasila ita da abinda ke cikinta, sunje asibiti likita ya tabbatar mishi da lafiyarta data yaronshi, yanzu itama ta saki jikinta sosai dashi tana zama suyi hira sosai in yana gida kuwa ta dinga kwanciya kenan a jikinshi daga tace wannan sai tace wancan Hajja da Rashida suyi ta kallon drama dan wataran ma idan sukayi wani abun hajja barin gurin takeyi, Rashida ma tayi ta jin kunyarshi tana mamakin yanda yayarta ta samu sake a gurinshi take zuba sangarta gami da shagwaba iya yanda take so shi kuma yana biye mata.......Idan suka zo zaman karatu da asuba ma sai sun gama rungume rungumensu kafin Rashida ta fito, dan wani sa'in idan wasilan ta rikitashi baya iya yi musu karatu me tsayi zaije ya kwanta yace sa had'u da daddare, to ka yaje ya kwanta haka zata bishi ta nan'ika da jikinshi, dole sai ya marmatsata sannan hankalinsu ke kwanciya ita dashi, akwai ranar da yaso ya sadu da ita ta hanashi, gashi ya kai 'kolulowa gurin bukata idonsa jawur ya fita daga d'akin, tayi kwance a bed tana hawaye, ita tsoronta Allah tsoranta annabi kar garin jin dad'insu yaronsu ya samu matsala, shiyasa bata so yace dole sai yayi sex kawai dai su tsaya iya romantic din har Allah yasa ta haihu........Ranar fushi yayi da ita ya shirya yayi ficewarsa harkokinshi, sai bayan tara da rabi na dare ya shigo gidan lokacin ita da Rashida ne a palon zaune suna kallon wani india film Rashida tayi mishi barka da zuwa ya amsa cike da kulawa yana tambayarta hajja tace"Taje ta kwanta.....bedroom dinshi ya nufa, yana jiyo muryarta nayi mishi sannu da zuwa, ya'ki amsawa, ta mike a hankali dan cikin nata ya fito sosai yanzu zama take da 'kyar ta mike da kyar tunda yanzu cikin ya kai watanni bakwai, bayanshi tabi wanda tana murd'a kofar dakin taji a rufe, ta tabbata key ya sanya, jikinta a sanyaye ta dawo ta zauna kusa da 'yar uwarta idanunta na kawo ruwa, wannan alamun da ya nuna ya nuna mata fushi yake da ita.....Rashida tace"Anti Wasila akwai abinda ke faruwa tsakaninki da Mijinki dan naga alamu tun a gurin karatu." Tace"Wane alamu kika gani.'? Tace"Yanzu fa ya shigo Kinyi mishi sannu be amsa ba, anti Wasila Allah kina 'kure hakurin mutumin nan sai bashi wuya kike nasan laifin naki ne wallahi." Cike da mamaki take kallonta tace"Har kike rantsewa laifina ne."? Rashida tace"Eh mana ni dai tsayin wata biyu da nayi a gidan nan banga abinda mutumin nan yayi miki na 'bacin rai ba kullum.cikin kyautata miki yake yi yana rarrashinki da kula dake, kinga kuwa dole nace laifinki ne." Shiru tayi tana nazarin maganar 'yar uwartata, babu shakka tsayin wata biyu da sukayi a gidan idan tace ga laifinsa tayi masa sharri kullum cikin tattashinta yake watarana ma abinci shike bata a baki, ta haye jikinsa tayi ta nu'kur'kusa bai ta'ba gajiyawa ba, tabbas laifi daga gurinta yake,

Ta kalli rashida a nutse tace"Nasan dai ke me hankali ce rashida idan na fad'a miki dalilin da ya saka yake fushi dani zaki daina ganin laifina, a gabanki komai ya faru kuma a gabanki likita ta gindaya min sharad'ai, kinfi kowa sanin irin 'bakar wuyar da nasha kafin wannan cikin na jikina ya zauna, duk wani 'kokari inayi masa domin na biya mishi bukatarshi duk hakan bai isheshi ba dole sai ya kwanta dani ni kuma ina tsoron wani abun ya faru dani da yaron dana ke dauke dashi a mahaifata." Rashida tace"Lallai anti Wasila dama saboda wannan matsalar ne yasa kike ta bashi wahala, gaskiya kin zalince shi wallahi ai itama likitan ba tace kar ayi ba cewa tayi a dinga d'aga 'kafa, tun a lokacin da cikin yake 'karami take wannan maganar to yanzu kuma ya girma ni ina ganin babu abinda zai same ki da yaron dake cikin ki kawai dai dan kin kasa kwantar da hankalinki ne yasa kike ganin kamar wani abu zai faru dake."

"Gaskiya Rashida bana jin zan iya amincewa da bukatarshi dan ni 'kadai nasan irin 'bakar wuyar da nake ci babu ciki ma ballanta yanzu da wannan cikin ai nasan mutuwa zanyi kawai yayi hakuri Har Allah yasa na haihu.'' Rashida tace" Ni wallahi bana so naga kina 'bata masa rai duk sai

naji babu dadi dan Allah ki bashi hakuri anti."

"Ki kyaleshi zai huce da kanshi, ni ba zan iya wannan bita zaizai d'in ba, sai ma ya d'auka na damu dashi ne." Rashida ta 'bata rai! ta tsani halin taurin kai irin na 'yar uwarta wallahi, kawai dan taga yana sonta ne shiyasa take masa wulakanci ita sam ba taga aibu ba dan ta bashi hakkinsa rana daya yayi ai ba laifi bane.


Wanka tayi ta shirya cikin kayan bacci ta nemi gado ta kwanta tana jiran shigowarsa kamar yanda ya saba, ko mai dare idan ya dawo koda tayi bacci sai ya tashe ta akwai wani Ice cream da yake siyo mata mai dad'i sai tasha shi take samun nutsuwa, yau tana tunani ko ya siyo ko bai siyo mata ba, tana dai jiran shigowarshi d'akin.......daga zaman jira bacci ne ya d'auketa, ba ta tashi farkawa sai kusan d'aya da rabi! ta kwanta da tunanin Ice cream dan har mafarki tayi ta mi'ke zaune tana dube dube a d'akin wai ko ya shigo ya tarar tana bacci ya aje mata duk ta gama dube dubenta bata ga komai ba, ranta ya 'baci sosai ta riga ta kwallafa ranta dashi dan tayi masifar sabo da shan Ice cream din, bude kofa tayi ta nufi d'akin nashi, har yanzu kofar a rufe take......Yana 'kokarin mikewa daga kan dadduma yaji alamun ana ta'ba 'kofar dakin, a nutse ya karasa bakin kofar ya murza key din dake jiki kofar ta bud'e ita ya gani tsaye tana cikin rigar bacci iya gwiwa mai hannun shimi cikinta ya fito sosai dake rigar irin me kwanciya a jiki ce, kanta babu hula sai dai gashin kanta daure yake cikin katon ribbon, Ya d'an bita da kallo babu yabo babu fallasa yace."Menene."? Kamar zata fashe masa da kuka tace"Ina Ice cream din."? Yace."Ajiya kika bani da zaki tambaye ni Ice Cream yau ban shigo dashi ba." Tayi narai narai da ido tana shirin yin kuka, kofar dakin yake kokarin rufewa, tayi saurin shiga dakin tana kalle kalle......Ya nufi bed ba tare da yace mata komai ba ya zare jallabiyar jikinsa daga shi sai boxer ya haye bed dinshi yaja bargo ya rufe jikinsa.......Ta jima tsaye a dakin tana sha'kar bakin ciki kafin tace"Kaine fa kayi al'kawari kace kullum zaka dinga kawo min tunda babynka yana so da kasan ba zaka cika al'kawari ba da baka d'auka ba." Yanda ta fad'i maganar zaka gane a kufule take dama ance zuciyar me ciki a kusa take.....Yana jinta yayi mata shuru, yana lumshe idonsa, Girgiza kanta tayi da tayi niyar fita sai kuma ta fasa tinkis tinkis ta karasa bakin bed din ta tsaya babu zato yaji gunjin kuka a tsakiyar kanshi, kuka take sosai hawaye na zuba a fuskarta, ya mike zaune da sauri yana kallonta, hannunta ya rike ta fuzge tana cigaba da kukanta, ya 'mike da sauri ya lalubi jallabiyarshi da ya cire ya zura da sauri ya kama hanyar fita daga dakin, idan akwai abinda ya tsana a duniya to bai wuce kukanta ba, ya kan rasa tunaninshi gabadaya idan yaga tana kuka da damuwa, Ice cream dinta na mota, 'bacin ran da yake dauke dashi ne ya sanya bai shigo mata dashi ba, bayanshi tabi dai-dai lokacin da taga ya bude kofar palon ya fita, sai tayi tsaye a tsakiyar palon tana jiran dawowarshi

Ya shigo hannunsa rike da ledar Ice cream din ya ganta tsaye a tsakiyar palon, kai tsaye inda take ya nufa ya mi'ka mata ledar Ice craem din babu kunya ta sanya hannu ta 'karba tana tura baki ta juya zata barshi a gurin, ya rike hannunta na dama, ta juyo tana kallonshi, Hausawa suka ce me nema baya fushi, dik yanda yaso daurewa kasawa yayi kawai sai ya tsinci kansa da rungumeta a jikinshi yana shafa gashin kanta, a hankali ya talfo fuskarta yana so ya hada bakinshi da nata, ta dan kautar da fuskarta, harshensa ya sauka kan ha'barta sai kawai ya shiga tsotsa ha'barta da kumatunta da le'bunanta, tsigar jikinta ta shiga mi'kewa, kafafunta ne suka shiga kyarma ta dan ture fuskarshi tana so ta bar gurin ya matseta sosai dan har sai da tayi 'yar 'kara, shaf ya manta da cikin jikinta saboda hankalinshi baya tare dashi, harshensa ya zura bakinta ya shiga tsotsa yana lumshe idanunsa, itama rintse idanunta tayi ledar hannunta na 'kokarin fad'uwa 'kasa! daurewa takeyi amma ta kasa kawai sai ta yar da ledar hannunta ta sarkafo wuyansa da hannuwanta tana wani irin rawar jiki ta shiga shan baki

nshi, tana lumshe idonta, tayi bala'in missing din bakinshi da yawunsa mai za'ki da gamsawara, sosai suke sucking din junansu, har dai suka gagara tsayuwa ya zauna kan kujera ya dorata a cinyarshi, suka cigaba da sucking din bakin junansu duk sun wani gigice sun ma'kal'kale junansu.





Littafin na kudi ne...!
Kika futa da book din nan keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*70*
'Dumin jikinta da kuma yanayin yanda take shafa jikinsa ya sanya jikinsa ya mutu bacci me dad'i ya daukeshi, a hankali ta d'ora hannunta kan nasa dake 'kasan mararata sai taji ya sake janyota jikinshi ya rike kugunta cikin jikinta yayi wani irin zillo lokaci guda mararta tayi mata wata irin dam'ka! rintse idonta tayi tana cize bakinta ta kasa motsawa kawai saboda bata so ya tashi a baccin da ya daukeshi......Ta jima tana jin ciwon mara kafin a hankali a hankali yayi sauki! sai da baccinsa yayi nisa sannan tayi dubara ta zare jikinta anashi ta gyara mishi bargon jikinsa kana ta fita daga d'akin

Palo ta tarar dasu Rashida suna hira ta dan zaune a hankali tace"Rashida had'o min tea ba zan iya zaman dainnig din nan ba." Rashida ta mike da sauri tana fad'in "To anti Wasila.'" Hajja ta kalleta cike da kulawa tace"Sannu kinji ko ai yanzu tilas kiyi ta jin sauyi iri iri a jikinki tunda ciki ya tsufa sai dai fatan rabuwa dashi lafiya."

Tace"Wallahi kam hajja ni kadai na san abinda ke damuna duk dare da kyar nake bacci ga ciwon kwankwaso." Hajja tace"Dama ai me ciki komai na jikinta ciwo yake ciwon kwankwaso kuma dole ne gabobinki ne suke budewa insha Allahu idan kika zo haihuwa ba zaki sha wuya ba." Tace"Allah yasa Hajja."
Rashida ta 'karaso hannunta rike da madaidaicin cup da tea a ciki sai plate wanda ta hado mata da soyayyan dankali da kwai. 'kasa ta sauka ta dan mike kafafunta ta soma kur'bar tea din tana had'awa da dankalin.


****
*Camas! tare da Usaini dillali*

Malam Usaini dillali yayi nasarar damfarar Camas kudin manya manyan filaye guda uku kud'in sun kai kimanin miliyan shida da rabi dan bayan kudin Wasila har da nata tasa a ciki kusam miliyan biyu usaini yayi mata roman baka inda yake cewa kafin shekara kudin filayen zasu kai miliyan goma ko fiye da haka, duk ya bata dakardun gaibu ya gudu ya bar gari dama ba'asan daga inda yazo ba..........Camas ta zama tamkar mahaukaciya lokacin da taje taga filayenta wani attajiri yana aikin gina gidan gona dashi, ihu! ta dinga kurmawa tana zagin masu aikin gurun wai filayenta ne waye ya basu damar ta'ba mata.....Tana wani irin huci! ta d'auko musu takardun filayen tana nuna musu, duk suka kar'ba suna dubawa, sai suka kwashe da dariya sunayi mata kallon mahaukaciya, babban cikinsu yace."Amma ke jahila ce wallahi wane shegen ne ya fada miki wannan takardar fili ce? hahaha! takardun wuta da ruwa ne saboda dakikiya ce ke baki fahimci abinda aka rubuta a jiki ba." suka dinga dariya suna kallonta........Wayarta ta dauko a fusace! take neman numbar husaini sai dai kiran duniya sai ace mata layin ma baya aiki kwata kwata, ta sharce gumin dake goshinta ta kallesu daya bayan daya tace''Idan kun san wata baku san wata ba, 'yan sanda zan kira muku sune zasu rabani daku shegu tsinannu barayi." Daya daga cikinsu yace."Zaki ci ubanki yanzu." Waya ya ciro ya kira mutumin da ya sanyasu aikin......Minti goma sai gashi cikin wata arniyar mota, ya karaso gurin yana me neman karin bayani, kawai tsaurin ido na Camas! sai ta hau kund'uma masa ashar har tana 'kiransa 'barawo mutumin ranshi ya baci da sauri ya kira *Anti daba* yace suje da ita su tuhumeta a inda yay sata idan ta'ki fada musu su ragargajeta! Tun a gurin suka dinga kwada mata mari suna haurinta da kafafunsu, sosai ta tsorata ta dinga kuka tana bawa mutumin hakuri yace."Ai sai kin fada musu inda naje nayi sata." Camas hankalinta yay masifar tashi ta dinga kuka tana data sani, haka dai *Anti Daba* suka tasa kyeyarta har ofis dinsu.


****

Cikin kaya marasa nauyi ya fito palo yay bacci har ya gaji, baccin da ya jima bai yi irinshi ba.......Kai tsaye daining ya nufa dan da wata irin yunwa ya tashi daurewa yayi yayi wanka gami da sallah sannan ya fito palon , hankalinta a kanshi lokacin da ya fito palon sai ta fara yunkurin mikewa Rashida tace"Anti Wasila ki koma ki zauna ki fada min abinda kike so sai nayi miki." Girgiza kanta tayi tace"Aikin lada zanyi Rashida." Hajja da rashidan suka bita da kallo lokacin da ta nufi inda yake wanda su sai lokacin ma suka san ya fito palon
Har ta'karaso inda yake idanunsa na ka

nta, ya dan sassauta fuskarsa yana yi mata wani irin kallo wanda kana ganinsa kasan na tausayi ne.
A hankali tace"Ya jikin."? Sai ya tafi tunani shaf ya manta plan dinshi, da sauri ya dan ya mutsa fuska yace."Yanzu kam alhmadullhi." tace"Ka jima kana bacci dan har nayi tunanin tashinka kaci abinci kasha magani gashi lokacin shan maganin ya 'kure biyar ta kusa."

Ya aje cokalin hannunshi yana kallonta a nutse yace."Gwara ma da baki tasheni ba dan da kin tasheni mybe ki 'kara min wani ciwon ne tunda kin san bana so a tasheni ina bacci.'
Tace."Eh nima tunanin da nayi kenan."
Ya cigaba da kokarin zuba abincin, cikin nutsuwa ta kar'bi plate din tana kokarin zuba mishi ta hada masa komai ta tura gabanshi.

Yace."Allah yay miki albarka." Cikin zucci ta amsa, tana goge hannunta da tissue yace."Sai ki 'karasa ladanki ko." Ta kalleshi tana son karin bayani.

Girarsa ya daga mata fuskarsa da murmushi me kayatarwa, tayi kasa da kanta tana dan murmushi ta gane abinda yake nufi sai kawai tayi niyyar barin gurin, yace."Idan baki bani da hannuki ba to ba zanci ba."

Ta juyo tana kallonshi cikin shagwaba tace"Bafa mu kadai bane a palon." Yace."Eh nasani tunda kina jin kunya dauko abincin muje daki.'" Makale kafada tayi tace"ka bari idan anjima sai na baka yanzu dai kaci wannnan da kanka."

Ya wani lumshe idonsa yana mata shu'umin kallo yace."Idan anjima ba abinci nake so ki bani a baki ba, wani abu nakeso ki bani." Tace"Koma meye nayi alkawari kai dai kaci kasa magani." Yace."Kince Kinyi alkawari ko."? Daga kanta tayi alamun E yace."To zo ki zauna gabana naci abincin ina kallon fuskarki.'' Dariya tasa tana kallonshi, tace"Idan na zauna kusa da kai ba zakaci abinci sosai ba idan ka gama ci na dawo.'' Da murmushi a fuskarsa yace."A ganinki idan kina kusa dani zan kasa cin abinci ko? baki sani ba xaman ki a kusa dani shine zai sanya na cinye abincin ba tare da nasani ba." Kujerar daning din ta gyara ta zauna tayi tagumi tare da tsira masa ido tace"Shikkenan gani na zauna amma minti biyar na baka ka cinye abincin gabanka." Yanda ta fad'i maganar ya bashi dariya yace."ki dai 'kara minti biyar su zama goma abincin fa nada yawa." Murmushi tayi tace"Tom na kara minti uku." Yace." Okey." Agogon hannunshi ya d'an duba biyar da minti da minti biyu......Sai yay bisimillah ya fara cin abincin da sauri da sauri yana had'awa da lemo Dariya take kunshewa ganin yanda yake cin abincin hannu baka hannu kwarya wai baya so lokacin ya cika bai cinye abincin ba...........Ya d'ago kanshi suka had'a ido lokacin ya cika bakinshi da abinci me cike da ganyayyaki ga nama dariya take tana nuna bakinsa da hannunta 'kasan ha'barshi kan gemunsa duk miya! ta dinga kyalkyala dariya tana kallonshi......'Bata fuska yay da sauri ya kalli agogon hannunsa yaga biyar da kwata....Kallonta yay da sauri! itama tayi saurin kallon agogon hannunta, biyar da minti goma sha shida, Still dai da mirmushi a fuskarta ta d'aga masa hannunta mai daure da agogo tana nuna masa lokaci,
'Bata rai yay yace."Agogonki na latti." tace."Agogona dai-dai yake tafiya kai ka 'kara minti hud'u kan mintinan dana baka dan haka al'kawarinmu ya rushe. Murmushi yay wanda ya tsaya iya la'bbanshi ya mika hannunsa yana kokarin daukar tissue tayi saurin cirowa tana goge mishi bakinshi dai-dai inda ya 'bata a gurin cin abincin.....Kunyace ta rufe ta ganin yana mata wani irin kallo ta juya zata bar gurin......Hannunta ya rike yana me narkar da kwayoyin idanunsa cikin nata.

Taji wani irin yanayi a jikinta, a duk sanda zai mata irin wannan

Please Login or Register in order to submit comment