Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saurin yin shiru to itama Kuluwar a kunyance take dan haka sai tayi saurin fadawa kichin tana sosa kai! Wasila abin dariya ya bata sai ta shiga girgiza kai tana fad'in ''Ni dariya ma take bani wallahi." Rashida tayi dariya kasa kasa tana kallon kicin din.

Wani tsalan kunu ta kawo musu cikin kwanon sha da kufuna guda uku sai 'kullin sikari akai....Uwani ta gaisheta tanayi mata sannu suma suka gaisheta Ita kuwa ta kasa tsayawa a gurin kunyar hada ido da rashida take......Tana shiga kicin Wasila ta saka fuskarta cikin hijab taci dariyarta ta koshi, kai mara gaskiya dai ko a ruwa gumi yake.

Fitowa tayi daga kicin din da katon farantin silba da narkeken d'umamen towo an yanyanka shi sai miya tsululu towon sai iyo yake cikin miyar....Ta kalli rashida tana fad'in 'kawata ga d'umame nan idan kunsha kunun sai kuci kwaji dad'in tafiya da karfinku." Rashida tace"Mungode Kuluwa." Da sauri ta bar gurin tana kwalawa yaranta kira wai suzo su dauki kununsu da duk ta zuba musu a kufuna 'kudaje sai bin bakin kufunan sukeyi.....aikuwa da d'ai- da d'ai yaran suka dinga shigowa suna daukar kufonan kunun suna sha ba tare da sun wanke bakinsu ba.

Kawu Madu ne ya shigo da sauri yana fad'in "Ina Wasila da Rashida." Sukace gamu Kawu Yace." To maza ku fito ga motar abokina ya kawo ice yanzu zai fita cikin gari sai yaje ku a tasha ku shiga mota." Suka mike da sauri Rashida ta shiga dakin domin dauko musu jakar kayansu, dama tasu daya ce ta uwani daya.

Uwani ta mike tana yakar zuciyarta hawaye ne yake so ya 'balle mata tana mayar dashi, suka je bakin kichin din da Kuluwa ke ciki tana zaune dirshan gabanta da karon bokintin da ta dama kunu tana katsewa gefanta kuma tukunyar miya ca bude ga ludayi a kasa....Uwani tace"Zasu tafi." Sai ta hau washe baki tana fadin"Bari na taso inyi rakiya ni kuwa me zan baku. 'Yayan nan."? Fitowa tay ta shiga dakinta da sauri ta dauko wata yar takarda fara ta mikawa rashida tana fad'in 'Kawata ga yariruka kwa sanya ku gaishe da kawunan naku." Rashida ta karba tana godiya tabi bayan Wasila da Uwani da suka riga sukayi gaba.





Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*59*
Tun a mota yake jin alamun zazzabi zazzabi a jikinsa yasan kuma ba komai ne ya jawo mishi faruwar hakan ba sai alhini da damuwar da yake ciki idanunsa sun kad'a sunyi jawur! jijiyar kanshi ma ta tashi, yanda le'bunanshi suke a bushe haka ma'kogwaron shi yake dan rabonshi da ruwa ko abinci tun jiya da daddare da yasha coffee kafin ya kwanta, sam ya ma manta da wani abinci saboda tsananin damuwar da yake ciki....Yana kallon khalifa na tu'ki yana kur'bar lemo amma shi sha'awa ma baya bashi bakinsa duk ya bushe yana jin wani irin abu ya tokare masa a ma'kogwaronsa.
Ganin tashin hankali murarar a tartare da abokin nasa yasa ya d'an kalleshi bayan yayi parking din motar cikin gidanshi, Yace."Kayi hakuri abinda zan iya cewa da kai kenan! ka cigaba da addua kawai kan Allah ya tsare maka cikinka da ita kanta yarinyar wannan damuwar duk ba ita mafita ba, tunda dai Allah ya raba ganawa sai ka bar mishi ikonshi, ni munyi magana da ita a jiya ta kuma shaida min cewar mutukar ta haihu to zata kawo ma'ka d'anka har inda kake." Saurin kallonsa yayi yace."Okey ashe da sa hannunka ta gudu kenan." ? Khalifa yay saurin girgiza kanshi yana fad'in" No ka fahimce ni mana! Jiya nake fad'a mata cewa dole sai na sanar maka da maganar cikin ta nuna bata so nace mata ai tilas ka sai ka sani shine tace ko anfad'a maka ko ba a fad'a maka ba in ta haihu zata kawo maka d'anka kaji dalilin da ya sanya nayi maka wannan maganar amma wai maganar da sanya hannuna a cikin guduwarsu bata taso ba."

Girgixa kanshi ya shiga yi yace."Ban san a ina zanga 'kawarta ba mybe a samu wani labari a gurinta." Khalifa yace."Eh to ai kuma inda za'a sameta ne aiki." Yace."Zan duba wayarta baza'a rasa numbar ta ba." Khalifa yace."Yawwa hakan yayi kyau Allah yasa a dace yanzu dai ka kwantar da hankalinka mu shiga ciki kaci abinci ka huta tukkuna insha Allahu komai zaizo da sauki."

Girgiza kai kawai yay yace."Khalifa hankalina ba zai ta'ba kwanciya ba sai naga yarinyar nan, na 'kwallafa raina kan cikin jikinta burina kawai in ganta kuma in tabbatar lafiyar abinda ke cikinta." Khalifa yace." Shine ai nace damuwa da tashin hankali bashi ne mafita ba addua itace mafita kawai ka kwntar da hankalinka ka cigaba da addua.''
Murmushi mai ciwo yay khalifa bai san yanda yake ji a zuciyarsa ba shiyasa yake cewa ya kwantar da hankalinsa a maganar kwanciyar hankali ta 'kare a gurinsa yanzu mutukar ba ganin yarinyar nan yayi ba. A
Tare suka fito daga motar tamkar wanda 'kwai ya fashe musu a ciki suka nufi cikin gidan. ga gajiya ga rashin samun nasara.


****
Dake akwai tafiyar 'kafa tsakanin bakin titi da cikin 'kauye yasa suka samu babur irin na (kafu-kafu) ya shiga dasu ciki har 'kofar gidan Mai allo aka ajesu, kana suka biyasu hakkinsu.....Suna kokarin shiga gidan ya fito da cazbaha a hannunshi, kawai sai yay tozali dasu. Ya bude baki yana kallonsu cike da mamaki.
Idanun Wasila ya kawo ruwa rau-rau! ranar naka sai naka! Wai itace tazo garin Garko da 'kafafunta! Hawaye suka zubo mata a kumatu, kai a 'kasa suka isa inda yake suka zube gwiwa bibbiyu suna kuka! Tausayinsu ya kamashi da sauri yace."Ku tashi mu shiga ciki.'' Jikinsu a sanyaye suka mi'ke rashida taja akwatin kayan nasu suka bi bayansa.

Kamar dai koda yaushe Bitan na zaune a tsakar gida tsaf da ita jikinta sai kyallin mai yake da alama bata jima da yin wanka ba tana sanye da wani leshi ruwan ganye(kore) irin nada ta d'aure kanta tamau! da dankwalin leshin, cinyar ta farantin shinkafa ne tana tsincewa sai kawai ta tsinkayi muryar mijin nata yayi sallama, Da sauri ta d'ago kanta tana kallon bakin 'kofa, Yanzu yanzu ya fita ko mantuwa yay abinda take ayyana cikin ranta, sai kuma taga su Wasila a bayanshi.

Tace"A'a malam su wa nake gani a bayanka yau.''? Yace."Gasunan nima fita ta na hango zuwan su Wasila ce da Rashida." Bitan! ta ri'ke ha'ba babu yabo babu fallasa a fuskarta tace"To masha Allah sannunku kuzo ku zauna ga gurin zama." Mai allo yace."Kuje ku zauna." Sukaje suka zauna kusa da ita sai sunkuyar da kai suke mussaman Wasila dama itace akuyarta tayi kuka a garin.....Mirya na rawa tace"Kawu ina wu

ni mun sameku lafiya." ? Yana daga tsaye yake amsawa yana nazarinsu....Rashida ma ta gaishi ya amsa, kana suka shiga gaishe da bitan itama ta amsa cikin kulawa kafin ta mike a nutse ta nufi kicin....Mai allo ya dinga kallonsu zuciyarsa na karyewa 'yayan Yahuxa tamkar 'yayan cikinsa suke, duk yanayin da ya gansu na dad'i ko na rashin d'ad'i dole ya shiga damuwa, kallon farko da yay musu ya fahimci akwai damuwa da firgici a tartare dasu mussaman Wasilan da tayi firgai firgai da ita kamar ma mara 'koshin lafiya. Bitan ta fito daga kicin hannunta rike da samira mai hannun roba, ta aje a gabansu ta koma kicin din da sauri ta fito hannunta rike da wani farin jug ta bude randa ta debo musu ruwa ta aje a gabansu ta zauna tana fad'in" Kuci abinci kunji ko ku daina kuka da damuwa rayuwar nan kowa hakuri yake da ita."

Malam yay gyara murya yana kallon matar tashi yace."Zan fita kamar yanda na niyyata idan Allah yasa na dawo sai na zauna dasu, Insha Allah." Bitan tace"To malam ubangiji Allah ya tsare a dawo lafiya." ya amsa yana kokarin fita, Wasila da Rashida har rige rige suke gurin yi masa adduar dawowa lafiya ya amsa musu a lokacin da yake kokarin fita daga gidan.

Bitan taga sun kasa cin abincin tace"Ku saki jikinku fa kuci abinci insha Allahu ba zaku samu wata matsala dani ba, ni dama tuntuni ina tausayawa rayuwarku mutukar kun gane gaskiya kuma kun gana mahimacin Kawunan ku a gurin ku , ai magana ta wuce suma kansu Kawunan naku hankalinsu a tashe yake, amma nasan yanzu hankalinsu zai kwanta tunda kun dawo garesu."

Sai suka sake jin kwarin gwiwa a tare dasu, Rashida ta bude samirar abincin dake gabansu, burabusko ne (biski) yayi shar shar dashi sai kamshin man'kuli zuryan yake, ga maggi star guda biyu a gefe da yaji....Wasila taji yawunta ya tsinke sosai taji sha'awar cin burabuskon ta mike a nutse ta wanko hannunta, ta dawo ta zauna Rashida ma mikewa tayi taje ta wanke hannunta sukayi bisimillah tare da fara cin abincin.

Bitan ta mike a nutse ta shiga kicin ta kunna wuta, Girgi zata dora musu na mussaman, sabida yaran sun bata tausayi sosai da sosai sam basuyi sa'ar uwa ba duk wata wahala da suka shiga mahaifiyarsu itace sila shiyasa kwata kwata basa shiri da ita sabida munanan haleyenta gashi tayi ta zagin mijinta a gabanta, duk abinda za tayi wa yaran za tayi musu ne saboda Allah da kuma maraicinsu, ba dan halin Uwarsu ba..
Tas suka cinye burabuskon basu rage komai ba, Wasila tafi rashida ci dan daga karshe ma rashidan cire hannunta tayi ta bar mata ta 'karasa cinye tayi gatsa tana hamdala hankalinta ya kwanta sosai da tsabtar Bitan shiyasa kome ta girka ta bata zata iya ci......Bitan ta fito daga kicin hannunta rike da wani ma dai-dai cin kwando dafaffan 'kwai ne a ciki da yawa ta aje a gabansu tace ku 'kara da wannan yanzu zansa yara sunyi min cefene na sake dafa muku abinci. "Wasila tayi murmushi tana fad'in " Bitan mungode Allah ya saka miki da alkairi." Murmushi kawai tayi ta koma kicin tana cigaba da aike aikenta.

Hajara ce tayi sallama ta shigo gidan tare da d'an autanta Lamir yana biye a bayanta.......Tsayawa tayi bakin kofa tana kallonsu, Sunkuyar da kai sukayi kamar munafukai. Bitan ta fito daga kicin taganta tsaye a bakin kofa tace"Ki shigo mana ai ba abin mamaki bane addua bata fad'uwa 'kasa banza." Hajara tace"Ai dole nayi mamaki Bitan! Yaushe suka zo kuma."? Bitan tace"Ke dai shigo ki zauna." Hajara ta karasa kan tabarmar ta samu guri ta zauna idanunta a kansu Wasila ta dinga tunano rigimarsu da Hajaran tana shan duka a gurinta a duk lokacin da sukazo garin, dan kwata kwata basa shiri sunfi shiri da Rashida......Cikin jin nauyi suka gaisheta ta amsa tana fad'in "Kunga uwar bari kenan."!? Sukayi 'kus! kansu a 'kasa, Hajara zata fara sababi! Bitan ta dakatar da ita da fad'in " Haba Hajara wannan ba kana bane! Kullum fa addua kuke kan Allah ya karkato da hankalin yaran nan gareku Allah kuma ya amsa adduarku sannan kice wani abu, don Allah kar ki fad'i wata mummunar magana kan yaran nan ki kyalesu ma suji da abinda ya damesu.

Hajara ta fashe da kuka tana fad'in "Haba Bitan! al'amarin nan fa akwai dam

uwa da ba'cin rai wallahi yaran nan sun sanya mu a fargaba da tashin hankali mussaman waccan mai 'katon kan tana sunkuyar da kai munafuka kawai Ai dama nace duk sanda kika kwaso kafafunki kika zo sai na ci miki mutunc.......Bitan tace" Ashe bakiji maganata ba kenan haba hajara."? Hajara ta kwance bakin zaninta ta goge hawayen fuskarta tana fad'in "Allah ya ji'kan ka Yahuza." Ai sai Wasila da Rashida suka sa kuka! Suna bata hakuri! Takaicin duniya ya ishi bitan Hajara tazo ta dagula al'amari ta tayarwa da yara hankali sai koke koke sukeyi......To itama hajaran da taga sun ki su daina kukan sai ta shiga rarrashinmu itama ba yin kanta bane tunawa tayi da d'an uwanta....Rashida da Wasila suka dinga bata hakuri da fad'in "Insha Allahu baxa su sake guje musu ba tunda sun gane basu da kowa a duniya da wuce su......Hajara taji dad'in wannan magana tasu sai tace " Komai ya wuce insha Allahu.


Hajara bata koma gidanta ba har sai da malam mai allo ya dawo suka gana da juna sannan tayi musu sallama ta tafi gidanta da al'kwarin dawowa gobe idan Allah ya kaimu.

Bayan sallahr isha'i mai allo ya samu nutsuwa duk suna zaune a tsakar gida bayan sun gama cin abinci, mai allo ya gyara zamanshi kan buzunsa yana kallonsu a nutse yace."Naji da dadi kuma nayi farin ciki da har kuka gane mahimancinmu a gurinku, yanzu kun gane cewar baku da wani gata a duniya da wuce Allah da ma'aiki da kuma ni da 'yan uwana, Mahaifiyarku ta dauke ku ta kai ku can cikin danginta, sun nuna muku cewar su basu da ala'ka daku , kamar yanda kuka fad'a min cewar da kyar ma suka bari kukayi kwana a guda a gurinsu, ni a ganina ba suyi lefi ba kamar yanda kuke tunani sun nuna muku mahimcin danginku ne, me yasa basu kori ita mahaifiyar taku ba? saboda sun san tasu ce kuma bata da wani guri da za taje idan ba gurinsu ba, naji dadi da faruwar hakan, na kuma tabbatar da cewar hakan zai sake sanyawa ku shiga cikin hankalinku ku gane meye rayuwa, alhamdullhi, Allah ne abin godiya a garun mu baki d'aya." Shuru yayi yana sauke numfashi kafin ya cigaba da magana yana me kallon inda Wasila take zaune, Yace."Jiya mijinki yazo garinan cikin tsananin rud'ani da tashin hankali yana shaida min cewar wai kina dauke da cikinsa a jikinki shin hakane ko ba haka bane? tunda dai ni kafin wannan zuwan nashi wattani uku da suka wuce yazo har nan ya shaida min cewar ya sake ki saki d'aya wanda a lokacin mukayi ta tsammanin zuwanki baki zo ba sai yanzu.

Tun lokacin da mai allo ya firta maganar mijinta yazo taji duk wani kuzari nata ya dauke yawun bakinta ya tsinke gabanta ya shiga fad'uwa da 'karfi da 'karfi sai kawai ta soma fad'in kalmar innalilihi cikin zuciyarta, muryar mai allo ce ta dawo da ita hayyacinta yace."Ke nake sauraro Wasila." Ta d'ago kanta idanunta cike da 'kwalla tace"Eh Kawu in da ciki." Yayi jim! kafin yace."To masha Allahu, yanzu akwai aure a tsakaninku kenan? ko ku kuma bayan rabuwarku dashi cikin ya bayyana kanshi."? Ta goge hawayen dake kuncinta tace"Bayan mun rabu cikin ya fito.'' Shiru yayi yana girgiza kanshi kafin yace."Gaskiya mana, yazo nan hankali a tashe a jiyan ni har na soma tunanin ko da akwai aure a tsakaninku ashe shi saboda cikinsa ya biyo bayanki, to babu lefi ai idan Allah yasa Habibu ya dawo daga tafiya, tunda shine yake da numbar wayarshi sai ya kirashi ya shaida masa abinda ke da akwai, amma maganar zai daukeki ya killace ki kiyi mishi rainon ciki duk bata taso ba, anan ma zaki raini ciki ki kuma haife lafiya ba tare da wata matsala ba insha Allahu, wannan dai hakkinsa ne dole a fad'a mishi halin da kike ciki duk saboda jininsa da kike dauke dashi a jikinki." Kuka tasa tana fad'in "Dan Allah Kawu kar a fad'a masa bana so kawai a bari idan na haihu sai a bashi d'anshi Ni bana so yazo inda nake." malam ya shiga kallonta yana mamakin gursheken kukan da take.







Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*60*
Mai allo ya dan gyara zamanshi yana kallonta a nutse yace."Kiyi shiru ki kwantar da hankalinki ki daina kuma kuka, sanar dashi ba yana nufin cewa zaki koma gidanshi bane, A'a za sanar mishi ne domin fita hakkinshi, ba wai dan muna neman wani abu a gurinshi ba, yana da kyau ya san cewar har yanzu kina nan dauke da cikin nashi, kuma ya samu nutsuwar zuciyarshi, ni ba zanyi miki dole ba kamar yanda nayi a farko, ba zance tilas ki koma domin ki cigaba da zama dashi ba, zaki zauna ki samu nutsuwar zuciyarki ki haihu lafiya kana ki za'bi namijin da yayi dai-dai da rayuwarki ki aura."
Bitan tace"Wannan magana da kayi itace mai kyau, saboda haka ki daina kuka kuma ki samu nutsuwa da kwanciyar hankali ko dan saboda cikin jikinki insha Allah babu wanda zai miki tilas kan ki koma zama gidan shi tunda bakyaso to Allah ya za'ba miki abinda yafi alkairi." Wasila ta shiga goge hawayenta tana sauke ajiyar zuciya, Bitan ta mike ta nufi wani daki minti biyu ta fito daga dakin hannunta rike da fitilar kwai ta gyara a nutse ta gyara fitilar ta kunna ta koma dakin.....Kimanin minti goma tayi a ciki ta fito tana fad'in "Na gyara muku shimfida sai ku kwanta ku huta mussaman ke Wasila naga alamun gajiya a tare dake kiyi bacci sosai sai ki samu sassauci da nutsuwar zuciya." Suka mike a nutse suka shiga dakin..........Bitan ta zauna kusa da mijinta suka cigaba da tattaunawa dangane da al'amarinsu Wasilan.

Dakin na shimfide da lede sabuwa da lalubewa masu dan kauri sai katifa ma dai-dai ciya mai cin mutum biyu jakar kayanu ajiye a gefe, dakin dai ya ishesu su biyu ba tare da wani ya takurawa wani ba.....Wasila ta cire hijab din jikinta, ta janyo akwatin kayansu tana dubawa kaya mara sa nauyi zafi takeji idan da son samu ne ma ta watsa ruwa, saboda zafin da takeji, Da kyar ta samu wasu riga da wando irin marasa nauyi sosai ta saka a jikinta, ta nemi ta gyara tufkar gashinta, Rashida dake kokarin kwanciya kan katifar tace"Anti Wasila ni kuwa zan baki shawara.'' Ta kalleta tana fad'in "Wace irin shawara."? Rashida ta mi'ke zauna a hankali tace" Dan Allah ki koma gidan Ahamdu wallahi shine marufar asirinki yanzu idan kince wani auran zaki sakeyi to ai baki san wanda zaki aura ba, kin san yanzu auranan zamani nan sai a hankali, amma ni ba tun yau ba nake sha'awar auranki dashi wallahi, kuma idan kin duba kinyi tunani fa za kiga bashi da laifi dangane da abinda ya faru a tsakaninku, ke koma yana da laifi to naki laifin yafi nashi, saboda haka nake baki shawara kan dan Allah idan yazo da niyar mai dake gidanshi ki amince kawai ki koma zakiji dadi muma muji dadi."

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon 'yar uwar tata tace"Wato Rashida har yanzu kwadayi da hange ne cikin ranki ko? Rashida ta girgixa kanta alamun a'a.......Ta cigaba da cewa''Idan ba kwadayi ba me zai sanya kice min in koma gidanshi? Kince nafi shi laifi Eh na yarda na fishi laifi kuma na amsa laifina amma me yasa lokacin da nayi nadama na nemi afuwarshi bai yafe min ba? lokacin da nake kuka nake neman gafarar shi a lokacin ji nakeyi zan iya zama dashi cikin ko wane hali saboda yayi min hallaci ya kuma yi min abinda ba kowa ne zai iya ba, ni ba nufina a kasheshi ba ko a cutar dashi, amma na lura shi abinda yake zargi kenan......Kinga duk mutumin da yake zarginka hankalinsa ba zai ta'ba kwanciya dani ba, Ni nasan koda na koma gidanshi to koma mu 'kan'kare za'ayi sabida yana zargina, sannan kuma ni bana jurar wulakancin da raini sam mutumin nan baya ganin mahaifiyarmu da daraja da mutunci ban san dalili ba ko dan yana da kudi ne oho! , naji ciwo sosai ranar da kuka zauna a gidanshi keda Uwani ya wulakanta ku, yana da kudi yana ganin babu wanda ya isa! sannan kice na koma gidanshi, ai ko zan koma auranshi sai ya mutunta mahaifiyata, ballanta ma bana sanyawa zuciyata cewar watarana zan koma gidanshi in cigaba da zama a matsayin matarshi, kawai Allah ya hada kowa da dai dai shi."
Rashida tace"Wallahi ba Kwadayi bane ni kawai mutumin yake burgeni yana da kirki da tausayin talakawa kinsan dama ance dan adam tara yake bai cika goma ba, kuma ni a ganina ba wai baya ganin girman u

wani bane kawai dai kinsan wasu masu kudin kuma ranar da mukaje ai bai san cewar mune ba shiyasa, ni daina zan cigaba da tayaki addua kan Allah ya karkato da hankalinsa kanki gaki dauke da cikinsa ai dole ma nayi sha'awar ki koma hannunshi kuji dadin rainon danku." Tsaki taja tana fad'in "Ranki zai 'baci mutukar kika sake yi min wannan banzar maganar."! Rashida tayi shiru tana kallonta.....Mikewa tayi taje ta kwanta tare da rufe kafafunta, maganar rashida tasa duk wani bakin cikin dake damunta ya dawo sabo, dal! ta dinga jan tsaki tana juye juye, hawaye ta share tana sake tuno lokacin da take birgima da ihu a gidanshi tana rirrikeshi ya taimaketa ya hakura ya mai da ita yanayi mata wulakanci, ai wallahi ta bar auranshi mutukar ta cika ita d'in 'yar halak ce........Da kyar bacci ya dauketa mai cike da mafarkai marasa dad'i.

Washe gari da safe da rubutu ta fara karyawa malam mai allo ya fara rubuta mata a'lkur'ani ya Umarceta tayi bisimillah tasha kana ta shafe cikinta dashi, sai da ya tabbatar tayi yanda yace din sannan hankalinshi ya kwanta...........Bayan sun karya ne, sai sukayi wanka, rashida ta taya Bitan gyaran gidan ita kuwa Wasila dama tana yin wanka ta kwanta bacci mai nauyi ya dauketa.
****
Ya tashi cike da rashin walwala da rashin kuzari gabakid'aya duniya tayi mishi zafi ya rasa abinda zaiyi ya samu sassauci, da kyar ya samu ya kur'bi tea kofi daya, yayi kwance kan kuje daga shi sai singlet da wando iya gwiwa, wayarshi yake dubawa, ya bude ma'adanar hotonanshi, ya lalube pictures dinsu yana kallo, ji yayi hankalinsa ya tashi ya mike zaune yana rawar jiki, dan wayar har sai da ta kusa faduwa ya riketa da kyau, ya kurawa fuskar wayar......Da sauri ya mike ya nufi dakinshi, drowars ya shiga budewa nan naga ya fito da Pose dinta da sababbin wayoyin da ya siya mata, zama yayi gefan bed ya kunna wayar yana dubawa, numbobin mutum uku ya gani tashi data As sai kuma wacce yaga ansa Hdz Camas! da sauri ya dauki numbar awayarshi dan yana zargin itace numbar yarinyar da yake nema tayi mishi karin bayani......sai da ya kira sau uku kafin A daga wayar, Camas na kokarin shiga sabuwar motarta kira ya shigo wayarta koda ta duba taga sabuwar numbar bata damu ba saboda tasan tana hurd'a da mutane sosai Ta daga wayar da sallama a bakinta.

Ya amsa a nutse yana fad'in "Ina magana da Hadiza ko."? Tace " Eh ko kace Camas! dan haka jamaa ke kirana." Ajiyar zuciya ya sauke, wanda har sai da taji a kunnanta, ya mike ya kunnanshi makale da wayar ya fito palo ya zauna kan kujera a Yace " Nasan Zakiyi mamakin me magana dake, Ni ne Ahamdu Mijin kawarki Wasila."
Camas taji gabanta ya yanke ya fadi har sai da wayar ta kusa faduwa, baki na rawa tace"Yallabai ina wuni." ya amsa a nutse yace."Tambayarki zanyi.' Tace."Allah yasa na sani." jikinta duk yayi sanyi dan tayi tunanin ko zai tambayeta kan kud'adan wasila ne wanda ta riga tayi fata fata dasu mussaman da taji labarin sun bar gari gabad'aya sai ta sake sakin jikinta tana facakarta da kudi.

Yace."Ko kin san ina 'kawarki suka koma da zama."? Shiru tayi tana tunani, Yace."Ke nake sauraro." Tace"Yallabai ban sani ba wallahi dan nima sai labari naji a gari wai sunyi tafiya amma dai nafi tunanin ko can kyauyensu suka nufa Garko."

Yace."Basu nufi can ba domun kawun su ya tabbatar min da cewar basu je mishi ba ya dai ce yana tunanin sunbi mahaifiyarsu, shin ko kin san inane garin su mahaifiyar tasu." Tayi shiru tana tunani kafin tace"Wallahi na san sunan garin amma ya kwanta min bari yanzu in kira mahaifiyata a waya nasan ita bazata rasa sani ba, insha Allah zan kira ka sai na fada maka."

Yace."Okey to ina sauraranki."! Camas! ta kashe waya tana tunani cikin mota, shin me yasa guy nan yake son sanin inda Wasila take, ko dai zai mayar da ita ne a matsayin matarshi, tabdijam idan hakane kuwa wallahi ba zata fad'a mishi

Please Login or Register in order to submit comment