Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai taja tsaki! ta fita daga shagon......Ba tayi shawara da Wasila ba kawai ta soma d'aga hannu tana tsaida motacin mutane........ Khalifa dake driving yay saurin kallonshi hankalinsa na kan jaridar dake hannunshi yana dubawa yace."Duba wacan yarinyar kamar Wasilan ka." Yay gaggawar hanya nan ya hango rashida na d'agawa motarsu hannu, ya mai da kanshi kasa ya cigaba da abinda yake! Sai da suka kusa isa gurun rashida khalifa ya gane ba ita bace amma kuma gaskiya suna kama sai dai ita wannan tafi wasila haske! A hankali ya tsaida motar dai-dai inda Rashida take tayi gaggawar zuwa gurin........."Khalifa ya sauke gilashin motar a hankali yana kallonta, rashida ta marairace fuska muryarta na rawa tace"Dan Allah Yayana ka taimaka mana ka rage mana hanya nida 'yar uwata wallahi tun daga d'orayi muka zo nan a 'kafa kudin motarmu ya 'kare." Tunda rashida ta soma magana yake jin wani iri, maganarta sak! data Wasila, ta gefan ido ya dan kalleta, sai gabanshi ya fad'i! wannan fuskar ai kamar ya santa yarinyar nan ce kanwar Wasila, shiru yay bai ce komai ba, shi kuwa khalifa da bai san abinda ke faruwa ba yaji tausayin rashida yace."Ina 'yar uwar taki." Rashida tayi saurin fad'in gata can tsallaken titi." Yace."Yi maza ki kirata." Cikin farin ciki rashida ta tafi, dake hankalinta na kan khalifa sam! ba tayiwa Ahamdu cikkaken kallo ba ballanta ta gane shi.

"Anti Wasila taso ga mota can zat

a daukemu Allah sarki wallahi me motar nada kirki." Wasila na daga inda take zaune ta dinga kallon had'addiyar motar tana mamaki! anya kuwa, wata zuciyar tace wasila idan baku shiga motar nan fa babu wanda zai taimakeku gwara ku shiga ko bakin asibiti ne sai ya saukeku in yaso sai ki siyar da zoben hannunki." Sai ta yarda da shawarar da zuciyarta ta bata, ta mike tana karkad'e jikinta suka nufi motar.

Khalifa tun kafin su karaso yake mamaki! Fuskar wasila ba bakuwa bace a gurinshi itace wallahi." Ya furta ba tare da ya sani ba, kalmar ta sanya shi dago kanshi yana kallon inda yake kallo, kawai sukayi ido hudu da ita, sai dai ita bata ganinshi shike ganinta kasancewar gilashin motar me duhu ne.

Yace."Mutukar zaka dauki yaran nan cikin motar ka ka saukeni dan Na rantse ba zan had'a nuffashina dana wannan yarinyar ba." Khalifa ya dinga kallonshi cikin tsananin mamaki! yace."Haba! taimako ne fa shin bakaji abinda 'yar uwarta ta fad'a ba, tun daga dorayi zuwa nan a 'kafa akwai wahala, kayi hakuri kawai a daukesu ai ba wani abun bane." Sai kawai ya hau kokarin bude mota zai fita.....Khalifa yace." A'a me yayi zafi! bari kawai na basu kudin abun hawa ba sai ka fita ba." Yace."Hakan shi yafi maka alkairi." Khalifa ya bude ma'adanar kudinshi dake cikin motar dubu ashirin ya 'kirga ya zuge gilashin motar, suka had'a ido da Wasila sai tay saurin matsawa baya gabanta na faduwa, dan ta hango gefan fuskar mutumin nata kanshi a kasa yana kallon jarida......Khalifa shima bai nuna ya ganeta ba, sai ya mikawa Rashida kudin yace."Kanwata 'karbi kudin nan ku hau abun hawa, kinji ko abokina nada uziri shiyasa amma da da kaina zan dauke ku na kaiku har gida." Hannu na rawa Rashida tasa ta kar'bi kudin tana godiya ta kalli Ahamdu tana fadin"Mungode sosai Allah ya saka da alkairi." A nutse ya dago kanshi yana kallonta, itama ta shiga shock ganin fuskarshi, Yace."Ki godewa Allah." Sai ya mai da kanshi 'kasa, Khalifa ya kunna motar yana fadin"A gai da gida ko." cikin nauyin baki tace"Mungode." ta bar jikin motar, sai da motar ta bar gurin sannan ta wuce cikin sanyin jiki ta nufi inda Wasila ke tsugune kusa da wata bishiyar darbejiya kanta na kasa gabanta sai faman faduwa yake tana fadin"Innalilihi wa'ina ilaihi raji'un a zuciyarta.




*_Ba cinye wa bace ba kuma burgewa bace ki dinga cushe cushen maganin matsi a matantakarki, ruwan d'umi kawai ya isa ya sanya gabanki ya matse ko da kuwa kinyi haihuwa goma ne, yana da kyau idan kin haihu a gida kije asibiti domin a duba matantakar ki ko kin samu matsala a gyara miki in kika zauna a gida bakije asibiti ba, akwai matsala idan kin 'karu guri ya had'e a haka mijinki ya shiga yaji kwararo! shikkenan kuma matsala ta afku a tsakaninku🙋🏻‍♀️_*






Littafin na kudi ne......![13/08, 6:37 pm] +234 906 803 2427: 'Yr Bngr Sys
*53*
Malam mai allo na shirye shiryen tafiya tsangayarshi, su Ahamdu suka sauka a garin......Tanimu d'anshi na biyu shine ya shaida masa zuwan ba'kin, Ya fito cikin babbar riga da koren rawani a nannade a kanshi, ganin su Ahamdu tsaye jikin motarsu ya sanya ya washe bakinsa, ya shiga yi musu barka da zuwa yana fad'in"Gwara da Allah bai sa na fita ba, dama yanzu nake shirin fita gurin karatu da sai da muyi sa'bani sannuku da zuwa sannuku." Cikin gidan suka nufa akwai wani babban zaure a soro wanda yake saukar baki a ciki dama kullum sai Bitan ta shiga ta gyara ta kunna turaran wuta dan haka ma yanzu dakin sai kamshi yake yi, Ahmadu da khalifa suka zauna......Malam mai allo ya zauna kan buzunsa yana fad'in"Wallahi ko jiya sai da nayi zancen ku nake cewa Hajara da Bittan su shirya suje suga dakin yarinyar nan akwai kuma 'kwan zabi dana aje mata sunanan da yawa nace su tafi mata dashi ta soya tunda nasan in tazo nan garin tana yawon soyawa taci."

mirmushi kawai Ahamdu yay yana tausayawa mutumin bai ce komai ba ya shiga gaisheshi ya amsa cikin walwala da farin ciki kai kana ganinshi kasan yana cikin farin ciki....suka gaisa da khalifa cikin farin ciki da barkwanci kafin ya tashi da sauri yana fad'in"Bari nasa bitan ta kawo muku abinci da ruwa."

Yana fita dakin yay shiru Khalifa yayi gyaran murya yana kallonshi yace."Yanzu baka tausayawa wannan mutumin ba! ya kake tsammanin zaiji idan ka sanar dashi abinda ka aikata dan Allah ka janye kudirinka ka kudurta a ranka ka mayar da ita, kar ma ka fada masa komai kawai kace kazo gaisheshi ne."

Shiru kawai yay baice komai ba, a zahirin gaskiya mutumin ya bashi tausayi sosai yasan zai shiga tashin hankali mutukar yaji da abinda yake tafe dashi, ammafa duk da hakan baya tunanin yanje kudirinshi shi kanshi a yanzu ya rasa wace irin 'kiyayya yake wa yarinyar sam yanzu baya ma so a dangantashi da ita, dan haka gwara kawai ya sanar mishi da abinda ke faruwa hausawa nacewa ta inda aka hau tanan ake sauka.


Malam mai allo ya shiga dakin yana gyara babbar rigarshi, sai fara'a yake yace." Kamar na sani yau na tashi Tanimu da sassafe ya tatso nono ashe ina da baki kai masha Allah naji dadin zuwanku Ahamdu." Yafada yana gyara zamanshi kan buzunsa.....Bitan ce ta shigo hannunta rike da wata kwarya me zane zane da fefe a samanta da ludai guda biyu tana fadin"Sannunku da zuwa."Khalifa yay saurin kar'bar kwaryar furar yana amsawa, ta dan tsuguna gefe tana gyara lullu'binta suka fara gaisawa, Ahamdu duk nauyi da kunya ya isheshi ganin yanda mutanan ke rawar jiki a kansu, Bitan na kokarin fita Kawu Habibu da Haraja suka shigo suma suna cike da murna da farin ciki, Mai allo ne ta tura danshi, Tanimu yaje ya sanar musu da zuwan su.....Suka gaggaisa cikin mutunci da mutuntawa Ahamdu duk jikinsa yayi sanyi da karamancin mutanan, Mutanan nada kirki da mutunci da kara babu shakka da karamcinsu Wasila ta dauko to da taji dadi, wannan mugun halin mybe daga can dangin uwarta ta daukoshi, abinda yake ta fada kenan a zuciyarsa......Khalifa ne ya iya shan furar shi kam ko ludai daya bai sha ba, tun daga sannan mai allo yasha jinin jikinshi dan bai san Ahamdu da irin wannan fuskarba babu walwala babu sakewa tun dazu suke hira da khalifa yayi shiru abinshi sam ba'ayin doguwar magana dashi zaiyi shiru mai allo jikinsa yay sanyi sosai,
Gyaran murya yay ya mai da hankalinsa kan Ahamadu yace."Jikina na bani akwai babban al'amarin dake tafe daku dan hauwasa sukance labarin zuciya a tambayi fuska hakikanin gaskiya alhaji Ahamdu ba haka nasan fuskarka ba, a sanin da nayi maka kai mutum ne mai walwala da sakakkiyar fuska ina fatan ba wani laifin wannan yarinya tayi maka ba, dan dama kullum cikin addua nake ubangiji Allah ya zaunar da ita dakinta ya kareta daga rudin duniya dana mahaifiyarta."

Khalifa dai 'kas yay da kanshi kunyar had'a ido yake da mai allo din da kaninshi Habibu, dan yanzu da ya sani ma yake da bai rako ahamdun ba sam baya son abinda zai daga hankalin mutane......'Dan numfashi ya sauke a hankali kafin yay gyaran murya yace."To Alhamudullihi arrama! naji dadi da ka dan fuskanci wani abu daga kallon yanayi na, Da farko dai kaine ka bani auran wannan yarinyar ni kuma biya sadaki na kar'ba bisa amana, to wani babban dalili ya sanya na yanke hukunci a kanta wanda nasan ba zai maka dadi ba, kayi hakuri haka Allah ya kadarta bazan boye maka ba Allah ya gafarta malam naso na rike amanar da ka bani amma zuciyata ta'ki aminta, da hakan.......Wannan yarinya tayi min abun da ya sanya naji na tsaneta gabakidaya bani son ganinta cikin gidana, ba kuma na son cigaba da zama da ita a matsayin matata, dalili kenan da ya sanya ni na saketa saki day........Kafin ya 'karasa mai allo yayi saurin fadin kalmar "Innalilhi wa'ina ilaihi raji'un!!!! Ahamdu yayi kasa da kanshi, mai allo ya shiga goge zufa da babbar rigarshi gumi ne kawai yake karyo masa,

Kawu Habibu kuwa fad'i yake " Garin yaya haka ta faru!? me yarinyar nan tayi maka me zafi da har zaka saketa Alhaji Ahamdu kada kayi mana haka."

Shi dai shiru yayi kawai kanshi a kas......Mai allo yace."Alhaji Ahamdu ka sanar min abinda ke faruwa me wasila ta aikata maka ka saketa nasan dai tabbas ba zaka aikata wannan abu ba sai da kwakkwaran dalili ina so kar ka rufe min komai ka shaida min abinda ke faruwa.

Cikin nutsuwa ya shiga warware musu irin badakalar dake faruwa ya kuma kunna musu muryar Wasila da As din a lokacin da suke kulle kullensu, ya kuma tabbatar musu da cewar dalilin kenan da ya sanya yaji zama da ita ya fice masa daga rai! bayan haka kuma koda ya zauna da ita to zuciyarsa za tayi tai masa wasiwasi a kanta ba zai iya yarda da ita ba........Mai allo yace."Banga laifinka ba Ahamdu banga laifinka. Hakika yarinyar nan ta cuci kanta ta cuci rayuwarta, tunda irin rayuwar data za'bawar kanta kenan to babu mu babu ita, duk wani hakki nasu munyi kokari mun saukeshi amma kullum cikin bin zugar shaidan takeyi da bib zugar mahaifiyarta, Wasila ta cuci kanta ta samu dama ta watsar babu komai Ahamdu mungode sosai da jajurcewa kuma naji dadi matuka da kazo kasanar dani abinda ke faruwa dan da baka sanar dani ba ba zan sani ba, kullum zan ta tunanin yarinyar na dakinta tunda dai ni nasan ba zasu zo inda muke ba, amma babu komai, zamu kyalesu mu zuba musu ido dan ba zamu inda suke ba, duk sanda duniya ta koya mata hankali na tabbata zasu zo su nemi inda muke." Muryarshi na rawa ya 'karashe maganar wanda har Ya dan bashi tausayi sai dai baice komai ba kuma ya gagara hada ido dashi ballanta khalifa da tunda aka fara maganar kanshi a kasa baice komai ba........A hankali ya dan gyara kadan ya zura hannu cikin aljihu kudi masu yawa ya ciro ya aje gaban mai allo din yace."Allah shi gafarta malam mu zamu wuce saduwar alkairi insha Allah zumuncinmu ba zai yanke ba ka kwantar da hankalin ka banyi haka da nufin in 'bata maka rai ba, nayi hakan ne dan ganin kamar shine maslaha." Mai allo ya mike yana gyara babbar rigarshi yace."Haba Alhaji ai wannan yarinya ba zata rabamu ba kuma ni ban 'kullace ka ba kasan shi aure da mutuwa rai garesu dik sanda kwanasu ya kare shikkenan Ubangiji Allah yasa haka shine alkairi amma ba zan gaji da fad'in cewar yarinyar ta cuci kanta ba."


Har bakin mota suka rako su, Kawu Habibu kuwa ai tsabar bacin rai ya hanashi magana sosai yake ganin hauka da wautar yarinyar ta auri babban mutum attajiri irin wannan ta cutar da kanta, shi kam ai da yana da 'ya mace da yay masa huce haushi da ita.......Suna tsaye a gurin har sai da motar ta 'bacewa ganinsu.

Suka juya suka koma cikin gidan jikinsu duk a sanyaye...........Khalifa na drving yana girgiza kanshi gaskiya da ya sani kawai yake gurin rako Ahamdu mutane masu mutunci da karamci kawai ya watsa musu ' kasa a ido! meye rayuwa! yarinyar nan tayi laifi ta gane kuranta tayi nadama ta bada hakuri me ya kamata ayi sai a yafe mata Allah ma hakuri yake da bayinshi, kwata kwata baya son wannan d'abi'a ta abokinshi, ri'ko da ramuwa ba d'abi'a ce me kyau ba, ko babu komai yarinyar nan taci darajar masu daraja irinsu mai allo amma ya watsa wa idonshi kasa ya kalli tsabar idonshi yake shaida masa ya sakeki 'Yarshi.

"Kasan Allah wannan abu da ka aikata ina me tabbatar maka da cewar sai kazo kayi nadama a gaba! Allah da kanshi shine ya halatta saki ya kuma umarce mu muyi amma ka sani duk ranar da akayi shi sai al'arshi ya girgixa! Ubangiji baya son kalmar gashi dai shi ya hallice ta, kuma kasan dole akwai jarabta wanda ubangiji keyi wa ma'aurata da irin haka ta ritsa dasu, ita yarinyar tata me kyauce tunda dai ta baka hakuri, ta kuma nemi yafiyarka, ka daina ganin kamar kasha wallahi Allah sai ya jarrabeka da masifar kaunar yarinyar a kuma lokacin da tayi maka nisa."! Khalifa ya karashe maganarshi cikin bakin ciki da damuwar abinda abokin nasa yake yi.......Yace." Sai dai kai Allah ya jarrabeka amma bani ba ni babu wani nadama da zanyi dan na rabu da wannan yarinyar Allah da zuciya yake aiki ba da wani abu so ka daina wannan maganar kawai."

Khalifa bai sake cewa dashi komai ba kan maganar suka shiga wata hirar khalifa ya kudiri aniyar daga yau ya daina sanya bakinsa kan maganar tunda dai haka yake ganin shine dai-dai da rayuwarshi shikkenan


**********

Kwanaki hud'u da faruwar al'marin, Wasila nata ciwo a tsaitsaye amma bata bari Uwani ta fahimci komai saboda duk sanda amai zai taso mata a sace take zuwa toliet ta kalato shi wani ya fito wani yaki fitowa ita da kanta ta zargi ciki a tare da ita sai dai tana so ta saci jiki Rashida ta rakata suke asibiti domin a tabbatar mata......Watarana haka takw wuni ba taci abinci ba saboda yanxu ba komai ke mata dadi a baki ba, wani sa'in ma abu in ta kalla bai mata za tai ta kalato amai tana ya mutsa fuska, duk daran duniya kuwa da zazzabi take kwana, Rashida taso ta fuskanci wani abu to amma ganin kamar wasilan na nuna mata lafiyarta lau yasa ta yi shiru da bakinta.



****
Camas duniya sabuwa, ganin Wasila ta daina kiran wayarta ya sanya ta saki jikinta ta soma fito da kudi suka hada kai da wani babban dillali dake harkar filaye da gidaje cikin unguwani masu kyau da tsada, ya kaita wasu manya manyan filaye a unguwar rijiyar Zaki cikin masu kudi, ya nuna mata su, yace."Kinga idan kika siyi wannan filayen to ina me tabbatar miki da cewar shekara me zuwa kudinsu ya ninku kin mayar da kudinki kinci riba, mai kauri, yanzu idan kina bukatar siyan filayen zaki biya miliyan hudu duk biyun kowane guda daya miliyan biyu ne, kafin shekara guda nasan zaki siyar dasu gabadaya miliyan takwas kinga kin zama hajiya babbah." yana dariya yake maganar yana kuma kara tabbatar mata da maganarshi, jin uban kudin da zata ci riba akai yasa ko neman ragi bai ta ta amince tace"Suje ya dauko mata takardun filayen sai su wuce banki ta bashi kudin.....Jiki na rawa Usaini dillali yay gaba tabi bayansa



****
As dai sarkin kulafuci da binbini bai hakura ba kusan kullum sai yazo gidan Wasila yayi ta magiya ta fito idan ta ga dama ta fita watarana kuwa haka zai karaci zamansa a mota ya tafi.......Yanzu ya daina so yayi lalata da ita so kawai yake ta amince masa ya aureta sabida jahlici kuma yake neman aure ba tare da ya bari tayi iddah ba, As din da ita Wasilan dik basu san abunda suke ba gwarama Wasilan zamu iya cewa bata sani ba tunda ba ilimin addini tayi cikakke ba shi kuwa As ya sani yake takewa yake zuwa zance...........Da dai yaga ta'ki bashi had'in kai sai kawai yace."Ya basu notice na wata biyu duk wani abu da suka san nasu ne to su kwashe su bar gidan idan ba haka ba to zaiyi musu tozarci da wulakanci tunda dai basu gaji mutunci ba, Uwani ta dinga bashi hakuri tana kwantar da kai, shi kuma ya dinga fad'a mata ba'kaken maganganu a fakaice! takaici ya sanya Wasila barin gurin, ta rasa yaushe Uwani za tayi hankali ta daina zubda mutuncinta saboda taulaci, sai wani rarrashin As din take kamar za tayi masa sujjada.


****
Yau satin ta biyar da fitowa daga gidan Ahamdu rayuwa tayi musu tsanani sosai dan tuntuni kayan abincinsu sun kare sai dai kullum rashida ta fita bakin titi tayi musu cefane, watarana ma basa karyawa da safe da rana suke cin abinci suci da dare........Wasila ta rame tayi uban haske sosai dan duk wanda ya kalleta yaga mace mai yaron ciki nonowanta sunyi girma ainun! hannayenta da kafafunta sun dashe goshinta kullum cikin zuba kyalli yake yi........Uwani tayi masifar tashin hankalinta ta dinga zazzaginta tana fad'in "Wato ni zaki munafurta ko? to tun kafin na haifeki na san meye duniya ni zakiyi wa duniyanci ko!? to wallahi ko 'kinki ko kinso sai an zubar da wannan cikin dan ba zaki haifeshi ba."

"Uwani nifa ba zan aikata sa'bo ba wannan cikin fa da ubanshi ba shege bane kawai ki kyaleni ki tayani addua Allah ya rabumu lafiya." Uwani tayi kwafa tace"Ashe dama kina sane kikayi cikin har zakice min babu abinda ya shiga tsakaninki da me cikin tom shikkenan gobe da wurwuri mu shirya dani daku muje can gidan wanda yayi miki cikin mu shaida masa abinda ke faruwa domin ba zamu bar garinan ba sai ya sani tunda kince baza a zubar ba to sai a sanar da me shi."
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Uwanin tana nazarin maganarta, tana ganin kamar shawarar Uwani abar dubawa ce, hakan nada kyau, gwara kafin su bar garin yasan da zaman cikinsa a jikinta...








Littafin na kudine.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[13/08, 6:37 pm] +234 906 803 2427: 'Yr Bngr Sys
*54*
Da tunanin maganar Uwani bacci ya d'auketa, aikuwa gari na waye wa Uwani ta azalzalesu kan suyi shirya da wuri suje gidan dan kar ya suje basu sameshi ba, jikinta a sanyaye tayi wanka ta shirya cikin daya daga cikin shaddodin da ya kawo mata lokacin tana gidanshi, vasilin akwai ta shafa a jikinta ta daura dankwalinta kana ta zura hijab ta fito palo, nan ta tarar dasu suna cin dumamen towon masara da rashida tayi musu jiya shine suka aje d'umame domin su karya dashi da safe Rashida tace "Anti Wasila gashi can na aje miki naki nasan ki da son dumame." Girgiza kanta tayi tace"Bana jin zan iya cin wani abu yanzu sai dai idan mun dawo." Uwani na sud'e yatsun hannunta tace"Wai meye tun jiya da nayi maganar zuwa gidanan mutumin nan kike wani salo salo ne? ko kina zargin xaice cikin ba nashi bane."?

Girgixa kanta tayi tace"Nifa Uwani gani nakeyi da mun hakura da zuwa wallahi bana son wulakanci gidan akwai tsaro sosai bai zama lallai ma mu samu ganinshi ba, maganar ciki kuma ni bana jin wani tsoro ko shakka ciki nashi ne tunda yafi kowa sanin yanda ya sameni."

Uwani tace"Ai yau komai tsaronsu sai sun bari mun shiga gidan ai dalili me 'karfi ne yake tafe damu." Rashida tace"Ai shine dan Allah anti Wasila ki kwantar da hankalinki."
Sai da suka fito
Babban titi a kasa kana suka suka samu a dai-dai ta sahu ta daukesu har zuwan Unguwar tudun yola.


Tunda suka doshi bakin gate din gabanta ke gaduwa! tafiya suke fakam fakam! dama tun a bakin babban titin mai babur din ya sauke su, ya juya , sai suka shiga layin gidan da kafafunsu.......Suna shiga Estete din Su hango Garba a bakin gate din gidan, Gabanta ne ya fad'i sosai sai ta soma kiran innalilihi wa'ina ilaihi rajiun....To shima Garba shigowarsu estete din ya dauki hankalinsa dan da yana niyyar komawa cikin gidan sai yaja ya tsaya yana jiran isowarsu.......Ganin Wasila ya sanya ya shiga mamaki sosai suka gaisa Uwani tace"Munzo gurin mai gidane muna tafe da muhimiyyar magana dan haka ayi mana iso zuwa gurinshi."

Garba yace."To babu laifi bai jima da shiga ciki ba ya dawo sallahar asubah bai kuma sanar damu zuwanku ba amma babu matsala bari na farar sanar dashi a waya tukkuna." Garba ya matsa gefe guda yana laluben numbar Ubangidan nashi.......Cikin sanyin jiki ta jingina jikinta jikin gate din gidan tana dan sauke numfashi gami da adduar Allah yasa idan ya fito ya gansu ya mutuntasu, a rayuwarta ta tsani wulakanci da tozarci!

Garba yay ta traying din numbar Ahamdun ana ce masa wayar a kashe take, sai ya karaso inda suke da wayar a hannunsa yace."Kunga wayar tashi a kashe take wallahi mybe bayan shigarshi ya kasheta dan wani sa'in idan zai kwanta baya barinta a kunne saboda baya son damu idan yana bacci idan ba sauri kuke ba zaki iya jira nan da awa biyu ko uku ya tashi, ko kuma kuje ku dawo." Uwani tace"A'a bari dai mu jira d'in." Yace."Shikkenan." Har ya shiga gidan sai kuma suka bashi tausayi yace."Ku shigo ciki ku xauna cikin wancan rumafar." Wasila tace"Babu damuwa kawai zamu tafi ba sai mun shigo ba." Uwani ta harareta tana fad'in "Kina da tabbacin dawowa gidan ki sameshi domin ki shida masa abinda kike dauke dashi da har zakice ga zance ga magana tunda dai muna da tabbacin yana gidan bacci yake ai sai mu jirashi ya tashi."

Ranta ne ya d'an baci! shin wai dole ne sai ya san tana da ciki ne, idan ta haihu ta kawo masa d'anshi ko 'yarshi kada ya kar'ba! Ina dalili kawai zasu zauna cikin maza sai kace wasu al'majirai! Tace"Tunda dai ku zaku zauna to ni zanyi gaba sai kun taho." Uwani tace"Ai sai kije me kunnan 'kashi wacce ba'a fada mata magana guda taji." Ba tace komai ba ta kad'a kanta ta wuce wani irin ba'kin ciki na sasakar zuciyarta, Allah yasa duk wannan abin da suke Garba baya gurin ya koma ciki amma ya bar musu karamar kofar a bude, sai suka shiga, can cikin rumfar suka nufa suka samu guri suka zauna zaman jiran fitowarshi........Wasila kam bakin titi ta nufa ta samu babur ya dauketa ya mai da ita gida, sam ba zataje ta zauna masa a gida ba ciki dai nashi ne komai za'ayi in ta haifu dole ya dauki abinshi.


Bacci yake yi mara d'ad! sai mutsu mustu yake yana rungume pillow ya juya can ya juya nan! ya takure jikinsa guri guda yana sake matse pillow da cije bakinshi, da alama mafarki yake yi mafarkin kuma mara dad'i ga yanayin yanda yake ta juye juye yana ya mutse shimfidar gadon...........Ya jima cikin wannan yanayin kafin naga ya bude idanunsa da sauri bakinshi na motsi da alama salati yake......Idanunshi na kalla nagansu tamkar garwashin wuta saboda ja! kuma sun dan risina........Ya mike a hankali tare da zuro kafafunshi kasan gadon yana me dafe kanshi da hannunsa guda, kimanin minti goma ya dauka kafin naga ya mike tsaye! yana layi da tangad'i! idanunsa ya sauka gaban rigarshi, wani abu ne a mi'ke tsaye carr! yana nema ya huda rigar ya fito! Toilet naga ya nufa cikin wata iriyar tafiya kamar wani

Please Login or Register in order to submit comment