Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a kirjinsa.
Jikinsa ne ya mace suka zube ita dashi kan bed din tayi kwance a saman kirjinsa tana masa dukan wasa sai kuka takeyi, rungumeta yay jikinsa na rawa ya shiga sumbatarta ta ko'ina...


****
Cikin ikon Allah Wasila ta shige cikin 'yan mata 'yan ajinsu Rashida ta saje dasu ba zaka ta'ba cewa matar aure ce ba, kuma babu abinda ya gagareta gurin karatun dan dama kafin zuwan ranar jarrabawar yana dan koya mata wasu abubuwan dake kuma tana da saurin fahinta babu wani abu da shige mata duhu ko ya daga mata hankali sukayi jarrabawar fita daga secondary skull cikin narasarori masu yawa.

*****
Ana ya gobe zasu tafi Garko Kawu Habibu ya kira wayar Amadu yake shaida masa halin da ake ciki, cewar malam mai allo zai daura aure ranar juma'a mai zuwa, kuma ba da kowa sai da mahaifiyar matarshi Uwani, Amadu yayi mamaki sosai da maganar Kawu Habibu daga karshe yayi addua gami da fatan alkairi ya kuma tabbatar wa da Kawu Habibun cewa insha Allahu suna tafe kafin zuwan ranar..........Kasa hakuri yay ya kirata a waya yace."Akwai albishir din da zan shigo miki dashi, amma meye tukwicina." Tana dariya tace"Ai kaima kasa ni." Yace."Nasan me? kawai ki fad'amin tukwicina." Tace."To zan barka kayi sau goma." Dariya ya 'kyal'kyale da ita yana sake rike wayar a hannunshi, yace."Kamar gaske ko?

yarinyar daka amfara zaki hau ihu kina cewa na daina ke zafi kikeji."
Ma'kale wayar tayi sosai ta wani lumshe ido tace"E mana ai kaine kakeyi da 'karfi shiyasa." Yace."To me yasa idan na bari ke kikeyi da 'karfin."? Kunya ce ta rufeta ta hau inda inda! Yace." Ai nagane wannan kukan da kikeyi na sharri ne dan dana bari ke kuma kikeyi da kanki kukan d'adi ne ko."?
Sai ta soma shagwaba da sangarta tana fad'in "Ya bari ita bata so." Yana daiya yace."Na bari shikkenn idan na dawo gida bazan fada miki albishir din ba sai nayi sau goma kamar yanda kika fada kin amince." ? "Umm."! tace" Tana lumshe idonta wannan 'yar wayar da suke tasa gabakid'aya hankalinta ya tashi sha'awa duk ta taso mata......







Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*'Yr Bngr Sys
*84*
Aikuwa da ya dawo gidan ta dameshi kan lallai sai ya fad'a mata albishir d'in shi kuwa yay ta ja mata rai, sai da suka gama komai na rayuwarsu sannan yake shaida mata abinda ke faruwa, farin ciki ya lulli'beta tamkar anyi mata albishir da gidan aljanna gaskiya taji dad'i sosai da wannan abu dama itama sam bata son zaman mahaifiyarta ta a haka tunda dai ba wuce auran tayi ba, koda Rashida ma taji labarin abinda ke faruwa tayi ta murna da farin ciki da 'kyar sukayi bacci a ranar saboda farin cikin da suke ciki.


Gari na waye wa ta tashi da walwala da farin ciki sai shiri takeyi shi kam yana kwance yana kallonta kwata kwata baya son tayi nesa dashi dan dai bashi da yanda zaiyi ne kawai, ya shirya cikin manya kaya kamar dai yanda ya saba, duk ranshi babu dadi kawai dai yana kokarin daurewa ne amma duk da haka sai da fahimta to itama nata bangaran tasan tilas tayi kewarsa amma haka zata hakura dan gaskiya tana so taje ta gaisa da iyayenta sosai.....Kafin su tafi sai da ya fara kaisu gidan Hajja suka gaisa sosai Hajja tayi mamakin girman baby zahra yarinyar tayi wayo sosai sai kace wata 'yar wata biyar.
Hajja ta ke'be da Wasila tace"Dama inata so inzo gidan naku Allah be nufa ba to tinda Allah ya kawoki sai ki tafi da ajiyar da nayi miki."
Wani garin magani ne a cikin wani madaidaicin bokiti tace"Kullum ki dinga sha da madara ko nono daga can sakwatto nasa aka hada miki, ita kuma wannan zuma ce kada kiyi wasa da ita kullum kina shan murfi biyu safe da dare, idan kikaji dad'insu nasan da kanki idan sun kare zaki bukaci ayi miki wani." Wasila ta sunkuyar da kanta kunyar Hajja takeji sosai godiya tayi mata cike da kunya tana kara jin kaunar matar a cikin ranta.

Hajja har mota ta rakosu tana fad'in "Su gaishe da mahaifiyar tasu insha Allah ranar daurin aure tare da ita za'azo."........Garba ne ke driving Rashida na kusa dashi da baby a hannunta....Ita dashi kuma suna bayan mota sai kalamai take mishi wai ya kwantar da hankalinsa insha Allahu sati guda kamar yau ce."
Ya kalleta sosai yace."Ni nace miki sati guda zakiyi."? Ta kalleshi tana marairace fuska a langwabe tace"Hakafa kace dani shekaran jiya."
Yace."Takura min kikayi shiyasa na fada miki haka, yau laraba ko."? Ta daga kanta tana kokarin mai da hawaye, yace."Zan iya daurewa kuyi kwana biyu shima dan dai babu yanda zanyi ne! Ranar juma'a idan na shigo daurin aure sai mu tafi."
Murya na rawa tace"To baza muje pataskum din ba." Yace."Wane pataskum kuma Itama Momyn ai nan za'a kawo ta sai ku had'u kawai ku gaisa."
Tace."Ai sai dare za'a kawota kuma lokacin nasan mun tafi." Yace."Ni zanyi magana da Malam d'in kancewa ana daura aure a tura mota a daukota ke Ni da kaina ma zan tura Garba ya daukota da sauran 'yan uwa sai ku gaisa da juna.'
Shuru tayi masa domun ta fahimci duk dubarar da zatayi masa ba zai amince ba.
Haka suka isa Garko kowa na jin damuwa cikin ranshi mussaman shi Uban gayyar da yake fargarbar dare yay yasan kuma shi da bacci sai dai yaga anayi.

Amadu kafin ya tafi babu inda bai je sun gaisa ba cikin dangin Wasila yau kowa yaga mijin da take aure suka zama abun kallo a garin ba'yan uwansu kadai ba harda jama'ar gari fitowa suke suna kallonsu mussaman da wani matashin saurayi dake shiga kano sarin kaya ya gane fuskarshi sosai ya dinga watsawa mutane ai shine *Amadu Musa Ba.Iya.ka d'an takarar governor Kano* Aikuwa Jama'ar garin Garko tamkar an musu albishiri da gidan aljanna! suka fito kwantsinsu da kwarkwartasu suna ihu da fad'in "Allah ya baka mulki jahar kano fari mai farar anyi maliya mai ruwan 'kare kukanka." Ganin yanda Jama'a suka nuna masa 'kauna sukayi dafifi a jikin motarsa ya sanya ya koma cikin motar tashi ya bude wata ma'ajiya da yake aje kudi ya daukosu dami guda, ya wakilta mutane biyar yace."kowa a bashi abinda ya samu." Aikwa Jama'a sukayi layi suna ihu da 'kara yi masa kirari.....Wannan damar da ya samu ce ya sanya ya Umarci Garba da yayi maza maza yaja motar su bar gurin dan idan ba haka ba jama'a baza su bari ya tafi ba.
Su Wasila na cikin gidan Malam mata dam'kam tamkar suyi mata sujjada ita abun ma mamaki yake bata sai wani bata girma ake kowa so yake yayi tozali da ita, wato tun mijin nata bai zama governor ba har sun soma kiranta da matar governor dariya kawai take musu itama ta fito da kudi daga jakarta ta shiga raba musu......Deluwa sarkin kanzagi tace"Hajiya Wasila ina fatan idan kun samu mulki a Hannuku baza ki manta da Kauyen Garko ba domin dai nan ne tushenki asalinki Karamar hukumar garko na bukatar hanyoyi masu kyau, na bukatar wuta da ruwa da kuma makarantu gami da asibitoci sannan muna bukatar tallafi domin mu inganta harkokin noma da sauransu."
Wasila dukanin abinda Deluwa ta fad'a sai da ta rubuta a wayarta tace"Insha Allahu duk su kwantar da hankalinsu idan mijinta ya samu mulki a hannunsu Wannan karamar hukuma zata zama city za'a gyara sosai yanda kowa zaiyi sha'awarta.


Sai bayan magariba suka samu sassaucin mutane a gidan, Bitan ta shigo dakin bayanta goye da zahra tace"Oh! ai shikkenan kuma gidan nan zai zama sansani na jama'a duba dai mutane sun kasa bari ki huta abincin ma sun hana kici cikin nutsuwa."
Wasila tayi dariya tace"Bitan ai haka siyasa take dama zakiga mutum kwata kwata baida nutsuwa daga zarar na bar garin inace shikkenan kuma." Bitan tace"Aikuwa dai kuna kokari wallahi ga baiwar Allah nan itama an shiga hakkinta." Tafada tana kokarin kwance zahra daga bayanta.
Tace"Ki bata nono tasha Rashida zata shigo muku da abinci."Yarinyar na ganin mamanta ta soma cilla kafafu tana b'angala dariya.
Bitan tace"Ji ja'aira wai ta san uwarta."
Wasila na dariya tace"Bitan wannan yarinyar wayo ne da ita ai."
Bitan tay dariya tana kokarin fita daga dakin tace"Ai yaran yanzu dama da wayonsu ake haifarsu.
Tana fita Inna Hajara ta shigo gidan tare da dan autanta da yake dauke da kwanukan abinci."
Bitan tace"Yanzu Hajara sai da kika yi girki bayan komarwar ki gida."
Hajara tace"Murhu biyu nayi shiyasa nayi sauri."
Bitan tace"A gaskiya dai mana." Kicin ta nufa ita kuma Inna Hajara ta shige masaukin su Wasila.
Wasila tace"Inna Hajara sannu bakya gajiya da zurga zurga koda yake babu nisa sosai ai.....Hajara ta zauna tana fad'in"Ke ni zurga zurgar da nakeyi kullum ai koda kudi aka hadaki ba zaki iya ba." Wasila tayi dariya tace"Ai kam wallahi bazan iya ba, tace"Inna hajara shine tun bayan tafiyarki baki sake zuwa ba ko."
Inna hajara tace"Ke rabani da zuwa wannan gidan da ba'a bukatata a ciki."
Wasila kamar tayi dariya sai dai ta daure tace"Haba Inna waye baya bukatarki." Tace"Rufe min baki kina so ki kare mijinki ko? bayan kin san shine ya koreni daga gidansa to me zai kaini ni ba kwad'ayayya bace."
Wasila tasa dariya tace"Haba Inna yaushe zai koreki a gidansa Wallahi bakiji yanda yaji rashin dadi ba da ya dawo yaga bakya nan yayi ta fada wai nice nayi miki laifi shiyasa kika tafi."
Tace"Oho! dai ni duk abinda nakeyi dominsa nakeyi da har zai dinga jin haushina dan nace ki gyara kanki ai shine zai mora shiyasa ai koda ki kayi ar'bain banyi gigin zuwa ba dan nasan dole zaki zo da kafafunki, in yaso sai nayi miki abinda nayi niyya ba don halinsa ba kome za'ayi ai shi za'ayi wa amma saboda tsabar rashin hakuri irin nasa yake ganin aibun mutune."
Wasila tace"Dan Allah Inna kiyi hakuri magana ta wuce Yace a baki hakuri." Ta'be baki tayi tace."Uhmm! ni dama ai ba bakuwar zafi bace, Wannan kwanon da kike gani roman 'yan shilla ne mai had'e da maganin gyaran matantaka da kuma ni'ima ki cinye tas ki shanye roman duk wani abu da kika rasa gurin haihuwa idan kinsha wannan roman zai maye gurbinsa.

Wasila tace"To shikkenan Innata nagode sosai babu shakka duk wanda ya rasa iyaye a duniya dole yayi kuka." murya na rawa ta 'kare maganar.
Inna hajara tace"To meye abin kuka kuma mu dai kullum fatanmu ki zauna dakin mijinki lafiya kiyi masa biyyaya domin ki samu rabauta duniya da lahira, itama Rashida addua muke kan Allah ya kawo mata miji nagari kamar naki."
Wasila tace"Ameen Inna insha Allah Rashida zatayi aure komai nada lokaci dama.
Tace"Inna gaskiya bazan boye miki ba naji dadi sosai da faruwar wannan abu Kawuna Malam zai auri Uwani wallahi ji nake tamkar babu wanda ya kaini farin ciki da faruwar al'amarin.
Inna Hajara tace" Shi al'amarin Ubangiji dama haka yake ai Allah ya kaddara akwai aure tsakanin Mahaifiyarki da Malam babu abunda zamuce sai dai muyi fatan alkairi shi kuma Yahuzu Allah ya jikansa ya gafarta masa."
Tana goge hawaye ta karashe maganar, itama Wasila taji zuciyarta na kokarin karyewa tuno mahaifinta da tayi sai dai kawai ta daure ta cigaba da yi masa adduar samun rahamar Allah a cikin zuciyarta.
Inna Hajara bata bar gidan Malam ba sai da ta tabbatar da Wasila ta shanye roman 'yan shillan nan sannan tayiwa Bitan Sallama ta tafi gidanta.
Koda malam ma ya dawo suka ke'be suna sake gaisawa da tambayar bayan rabuwa Wasila tace"Malam ji nake kamar nafi kowa murna da farin cikin da kasantuwar wannan abu kai da Uwani Allah Ubangiji ya sanya alkairi a ciki."
Mai allo ya dinga amsa cike da walwala da farin ciki, Yace."Hakan shine suttura da kuma mutumcin mahaifiyar taku."


****

Sai bayan goma da rabi ya shiga gida a gajiye sosai dan bayan sun bar garin Garko can 'karamar hukumar *Gaya* suka Wuce shi da Khalifa da jama'arsu, sai yamma lis suka dawo saboda yasan masu gidan basa nan yasa ya yada zango guest house dinshi Khalifa ya zauna yana d'eba masa kewa Sai da Hafsa taga dare yayi mijinta bai dawo ba ta kirashi a waya, sannan ne suka rabu kowanne ya tafi gidanshi

Yana sane ya'ki kiranta a waya sabida yana so yaga shin zata manta dashi ko a'a bini bini zai duba wayarshi babu text dinta babu kiran wayarta gashi sha biyu na dare har ta wuce........Allah sarki Wasila tana can network ya sakata a gaba tun bayan tafiyar Inna Hajara take ta kiran numbarshi tana 'kin shiga ko kuma data fara ringing sai ta katse har kuka tayi saboda bakin ciki kowa na kwance a daki cikin dare ta fito tsakar gida wai ko dakin ne babu network nan ma tayi tayi kiran baya tafiya, sai ta koma daki ta kwanta lamo tamkar mara lafiya bini bini ta duba wayarta ko zataga test dinshi shuru duk ta rasa abinda ke mata dadi da kyar bacci ya dauketa.


To shima nashi 'bangaran hakane, da kyar bacci ya daukeshi wanda tun yana saka ran ganin test dinta ya cire ya rungume filo kamar wani maraya yana fizgo bacci da karfi, gabadaya gani yay dare yayi mishi tsayi, dan haka uku da rabi nayi ya tashi yaje ya dauro alwala ya hau dadduma yay nafila, kafin ta dauki cazbaha ya wuce masallaci.

Da safe da kyar ta karya duk takaici ya isheta, ga mutane sai shigowa sukeyi wai sunzo gaisheta sai kawai ta koma daki ta kwanta tace da Rashida duk wanda yazo tace musu bacci takeyi.
Haka kuwa Rashida ta dinga sallamarsu, da cewar bacci take wasu masu naci zama sukeyi wai sai ta tashi sun gaisa da ita Wasu kuwa sai suce bari su tafi sa dawo da yamma.
Wasila na ciki tana ta famar kiran wayar tashi wannan karon tana shiga sai dai kuma bai daga ba, nan ma zuciyarta ta sake hasala ta goge hawaye tana mikewa zaune......Sake kiran wayar tayi a karo mara adadi dai-dai lokacin da ya fito daga toilet da alama wanka yay dan ga jikinsa nan duk ruwa, da sauri ya karasa inda wayar take ya dauka, ajiyar zuciya ya sauke ya zauna gefan bed kana ya daga wayar.
Kuka ta fashe dashi harda shashsheka, yaji duk jikinsa yay sanyi gabakidaya a rayuwarsa ya tsani yaji tana kuka....
A tausashe yace."Menene."? Tace"Me yasa ka ki daukar waya zuciyata kamar zata fashe."
Ya sauke ajiyar zuciya yana furzar da wani huci daga bakinsa, yace."Sai kuma kiyi kuka babu sallama da gaisuwa da tambayar yaya na kwana."?
Tace."Duk hankalina ne a tashe wallahi zuciyata sai sa'ke sa'ke take min."
Yace."Ina Mommyna." A hankali tace"Tana can gurin Bitan."
Yace."Kun tafi kun barni da damuwa ko."? Tace."Wallahi nima da kyar nayi bacci ban san haka nake sonka ba sai da na kasa samunka a waya ji nake kamar nayi tsuntsuwa nazo inda kake."
Yaji wani irin dadi na ziyartasa, yace."Nima haka naji na kuma gane kece mahad'in rayuwata." Dariya tayi tace"Nagode mijina, yanzu kayi break fast ko."
Yace."Nakasa komai tunda na tashi kinga ni da kyar ma nayi wanka." Tace."Wayyo babyna da ina nan Wallahi ni zanyi maka wanka in rungumeka in shafa maka mai in saka maka kaya."
Yayi wani killer smile kafin yace."Tunda ni baby ne idan kinyi min wanka kin shafa min mai kuma kin sa min kaya sai ki bani nono nasha ko."
Ta saki dariya da shashsheka tace"Allah da ina kusa zan baka kasha."
Yaji tsigar jikinsa ta tashi Yace."Mu bar wannan maganar kada kisa nazo inda kike yanzu."
Ta 'kyal'kyale masa da dariya tace"Ai dama kaina ka fara maganar." Yace."Tom na daina maganar." ya cigaba da cewa yau zan tafi katsina amma kuma komai dare zan dawo insha Allah." Tace"Wayyo Habibi Katsina me zakaje kayi."? Yace."Zanje Gurin abokina mana mutumin da yazo dubaki lokutan da baki da lafiya."
Jiki a sanyaye tace"To Allah ya tsare min kai ya dawo da kai lafiya." Ya amsa da "ameen." Yace."Kinga yanzu na dan samu sassauci zan iya cin abinci sabida kin bani kulawa duk da bakya gabana naji dadi sosai Allah yay miki albarka."
A nutse tace"Ameen." Bari na bari ka nutsu kayi break sai na sake kiranka ko."
Yace."Okey my Princess! Murmushi tayi ta kashe wayar tana fad'in "Nazama gimbiya kenan.....Cike da nishadi ta fito tsakar gidan gidan malam ta cigaba da hada hada da jama'a masu shigowa.


Gangami!! da turnu'kun!! haya'ki!!! nake hangowa kan titin zuwa gidan gomnati wato government house, mutane sunfi dari biyu sun kashe titi sai 'kone -'kone sukeyi suna tada 'kura gami da 'kona tayoyi suna watsa fetur suna 'kyasta ashana, sai ihu sukeyi suna buga ganguna, guri ya hargitse da hayaniya gami da haya'kin! wuta, dan wasu ma har sun soma galabaita duk da sune suka saka kansu abunda sukeyi din basu sare ba so sukeyi su shiga cikin government house din domin su cimma manufarsu kan mai girma governor Lawan Rabo, mafi akasarin jama'ar da suka tada wannan tarzomar iri-iren wad'anda aka rusawa gidaje ne da masana'antu gurun aikin titin jirgin 'kasa wanda ko rabin aikin ba'ayi ba an dakata gashi su kuma anyi musu al'kawari za'a biya su diya shuru kakeji malam yaci shirwa kullum 'karya daban ta gobe daban sam basa gajiya da shiga gidan redio suyi karya, sukuwa suka ga rainin hankalin yay yawa kawai suka yanke wannan hukuncin duk da sun san wannan abun da sukeyi din xai iya barazana ga rayuwar wasu daga cikin amma dai duk da haka sukaji suka gani domin suna so su kwaci hakkinsu da'aka danne musu,
Mai girma governor Lawan Rabo hankalinsa yay masifar tashi sosai ya lura Jama'ar Jahar kano suna so su ga karshen sa dan duk abinda ke faruwa a kan titin yana gani ta cikin CCTV Dan haka sai kawai ya umarci Securities kan suje suyi aman wuta da alburusai a gurun wanda kwanansa ya 'kare shi ya jawo kansa.
Ba tare da 'bata lokaci ba kuwa, Police din gidan gomnatin suka shiga motocinsu suka durfafi kan titin suna sakin harbi ko ta ina!







Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
*END🔚*

*ALHAMDULILLAHI*

*85*
Gurin ne ya sake hargitsewa da hayaniya dalilin zuwan Securities din, kafin kice kwabo jama'ar da sukayi dafifi a kan titin sun soma gudu saboda gabakidaya harbin bindigar da Police din keyi yayi masifar razanasu, sai kowa ya soma kokarin ceton ransa, amma dai duk da haka sai da harbin ya samu wasu daga cikinsu suna kwance a gurin suna ihu jini tamkar yay magana kan titin yayi kaca kaca sai hayaki ne yake tashi a gurin gashi gari ya soma duhu magariba ta gabato.....Governor na ganin abinda ke faruwa ya kira d'aya daga cikin mutanan da ya tura yace."Maza a kwashi wa'inda suka jikkata akai su asibiti, Allah sarki mutum kusan bakwai sun mutu 'yan uwansu sai kuka suke suna d'ora hannu aka hade da tsinewa Lawan Rabo albarka suna tur da wannan mulki nashi....Amadu na katsina tare da Abokinshi Alh Muktari labari ya samesu dan sai da suka ga abinda ke faruwa a labarai, hankali a tashe sukayi sallama da abokinshi ya dauko hanyar dawowa gida.....Koda ya iso bai nufi gida ba kai tsaye gidan redio na *Salama* ya umarci Garba ya saukeshi, abinda bai ta'ba faruwa ba kenan wai ya shiga gidan redio dan ya yad'a manufarshi,
Tashar redion Salama taji dad'i sosai da zuwanshi, kafin kice me sun fara sanarwa yanzu yanzu d'an takarar governor kano mai girma *Amadu Musa* zaiyi magana dangane da abubuwan dake faruwa a wannan jahar.
Jama'a duk suka maida hankalinsu gurin sauraran jawabinsa.....Ya fara da bisimillah had'e da addua kamar yanda annabi ya koya mana kana yace."
*Hak'ika banji dad'in wannan abunda ya faru ba a yau! hankalina ya tashi matuka! ganin yanda jama'a suka jikkata wasu har suka rasa ransu, Duk abinda wannan gomnati tayi muku bai kamata ku dauki irin wannan mataki ba, don yin hakan ba zai amfanar daku komai ba sai 'bacin rai gami da nadama da dana sani, na tabbata yau wasu daga cikinku suna nan cikin bakin ciki da damuwa rashin Iyaye da 'yan uwa mata na gida suna kuka saboda wannan tashin hankalin Wata mijinta ya mutu wata mijinta ya 'kone ko ya karya, duk saboda wannan hatsaniyar data afku, wannan abun da jama'ar wannan jaha sukayi bai dace ba shi wanda kukeyi dominsa din baza ku ganshi ba ballanta ku cimma burinku akansa, duk abinda hakuri bai baku ba rashin sa ba zai baku ba, kuyi hakuri ku barshi da Allah bisa ga zalintarku da yayi sannan kuma cigaba da yi mana addua kan Allah ya cika mana burinmu a cikin wannan tafiya, mutukar Ubangiji Allah ya dam'ka min mulki wannan jahar zan share muku hawaye zakuyi mamaki sannan dukanin wanda yay asarar gidanshi ko masana'antar sa wannan gomnatin insha Allahu Ni Amadu! na kar'bi wannan mulki nayi muku alkawarin biyanku hakkinku, wannan titin kuma da suka d'auko gadan! gadan! sunayi ni dama nasan ba iyawa zasuyi ba ku zuba musu ido, mu idan muzo namu salon daban yake da nasu, babu wani abu nasu da suka bari wanda zamu d'ora aikinmu akai komai sabo zamu 'kir'kira! babu algus babu almundahana a ciki, zamuyi mulki bisa amana da tsoron Allah Insha Allah! Daga karshe nake muku fatan alkairi al'ummar wannan jaha mai albarka ku cigaba da addua kan Allah ya kawo mana sauyi mafi alkairi sannan kuma na umarce ku da kada ku kara tada wata tarzoma, saboda yin hakan bashi ne mafita ba, mafita shine ku bamu had'in kai aranar za'be! kowa ya fito ya za'bi Jam'iyyar mu mai albarka tun daga sama har 'kasa, ku za'bi Jam'iyyar CPC Sa'a! Wasalamu alaikum."*

Amadu na gama Jawabinsa gari ya dauka anata hayaniya kowa na fadar albarkacin bakinsa, haka can ma gidan gomnatin Governor Lawan Rabo da mataimakinsa da kuma mabiya bayansu hankalinsu yay bala'in tashi, governor Lawan Rabo ya dinga da ya sanin hukuncin da ya yanke na tura securities da yayi suka dinga harbi, yasan har duniya ta nad'e jama'a ba zasu ta'ba mantawa da zamaninsa, ba, aikuwa yana jikin wannan jimamin kiran mai girma shugaban 'kasa ya sameshi, lallai yau yake so ya nufi Abuja domin yana so ya zauna dashi.
Lawan Rabo ya shiga rudani mutuka yayin da mataimakinsa yayi nasa guri dama shi d'an ba ruwa na ne tunda duk shawarar da zai bashi baya dauka yanzu data kwa'be masa sai y

aje yaji da matsalarsa.
As da sauran jama'arsa ne suka rakashi can fadar shugaban 'kasar.


Duk da suna cikin karkara sai da labari ya samesu, dan Wasila har jawabin mijinta sai data saurara, hankalinta a tashe ta dinga kiran wayarshi domin taji lafiyarsa, wayar bata shiga da alama dai gidan Malam bai da network me kyau.


Sai misalin goma shaura na dare ya shiga gidanshi, yay wanka ya fito palo wanda yay dai-dai da shigowar Khalifa suka zauna suna sake tattauna maganar.........A dai-dai lokacin ta sake gwada kiransa a waya a kaci sa'a wayar ta shiga, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke tace"Habibi sannu da hanya ina fatan ka dawo lafiya."
Yace."Na dawo lafiya lou har yanzu ban samu sukunin kiran wayarki ba."
Tace."Nima tun dazu nake ta neman wayarka network yana hanawa, na saurari Jawabinka dazu kano babu lafiya ashe." Yace."Eh gashinan jama'a nata fama wai sai sun halaka governorn ku Lawan Rabo."
Tace"Dan Allah daina cewa governor mu wallahi na tsaneshi mugu ne." Yace."A haba dai yanzu kin fita daga jam'iyyarsu kenan."? Kamar zatayi kuka tace"Ka bari bana so dan Allah."
Ya dan shafa saisayayyar sumarshi yace."To na bari ina Mommyna." Tace"Tana goye a bayan Bitan." Yace."Wai ita wannan Bitan din bata gajiya da hidima ne."?
Murmushi tayi tace."Mutuniyar kirki kenan." Yace."Ina kaunar matar sosai saboda tana kaunarki gashi yanzu tana gwadawa kan Mommyna." Mirmushi kawai tayi, yace."Kin san wani abu."? Girgiza kanta tayi tana lumshe ido yace."Gabad'ayansu Malam Kawu Habibu Inna Hajara Momynmu da ita Bitan! Dukaninsu zasuje Umara insha Allah sati biyu masu yawa." Wani irin farin ciki ne ya lullubeta kamar tayi masa ihu a wayar sai dai ta daure ta dinga zabga masa

Please Login or Register in order to submit comment