Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

godiya da addua muryarta sai rawa takeyi......Yace."Babu komai ai dangina nayiwa meye abin godiya." Tace"Eh duk da haka nagode." Yace."Idan sun dawo zamuje namu umarar." Tace"Tom shikkenan yanzu kuwa zanje na fadawa Kawu wannan albishir din." Murmushi yay yace."Sai Allah ya kaimu gobe ko."? Tace"Tom Allah ya kawo ku lafiya."
Kashe wayar yay yana murmushi, suka hada ido da Khalifa dake zaune ya zuba masa ido, hummm! Wai Amadu ne ke hirar soyayya wanda da idan ance zaiyi sai yace shi bashi da lokacin yin haka.
Murmushi yay yace."Dama kana nan a zaune."? Khalifa ya murmushin takaici yana jan 'karamin tsaki yace."Ai baza ka gane ina gurin ko bana gurin ba tunda idanunka sun rufe."
Ya dan shafa kanshi As'usel da murmushi a fuskarsa yace."Khalifa ina son yarinyar nan wallahi." Khalifa ya mike yana fad'in "Ai ba sai ka fada ba duk ga alamu nan sun nuna." Mikewa yay ya bashi hannu suka tafa suna dariya a tare suka fita daga palon.

Wasila ta sanar da Malam alherin da Amadu yay musu, malam ya shiga tsananin farin ciki mara misaltuwa ya aika aka kira masa Kawu Habibu shima ya dawo gida saboda daurin auran ya tarasu ya shaida musu abinda ke faruwa, Inna Hajara ta dinga rangwada 'buda a gidan tana fad'in "Haihuwa mai rana Yau ni Hajara nice zanje wannan guri sai ta fashe da kuka tana fyatar hanci tace" Allah ya ji'kanka dan uwana insha Allahu kana aljannar furdausi, Bitan tace ta dinga rarrashinta da ta daina kuka domin yin hakan zai sanya su Wasilan hankalinsu ya tashi, da kyar Inna Hajara tayi shiru ta kama Wasila ta rungume a jikinta tana mata addua gami da hud'uba kan zamantakewar aure.


****
Alhamdullhi an d'aura auran Uwani da malam a gidan Kawunta dake Tudun maliki, bayan daurin aurane sai suka kuma nufi can pataskum din domin gaisuwa sannan kuma da dauko amarya, malam sai washe baki yake yana baza babbar riga Shi kuwa Amadu kunya ce take kamashi wai daurin auran Uwar matarshi ake sai dai kawai ya girgiza kansa yana murmushi.


Uwani tayi ado dai-dai gwargwado kuruciyarta ta sake fitowa tamkar bata haifi Wasila ba wani cewa zaiyi yayarsu ce anyi mata kitso da jan lalle tana sanye da sabuwar atamfa 'yar ingila jama'a sun cika gidan Kawu Madu sai hidima ake Kuluwa sai washe baki takeyi tana karbar baki, Kuluwa yanzu ta dan rage kazanta dan Kawu Madu ya soma dawowa hayyacinsa asirin da tayi masa ya karye dan da ya farga da irin kazantar da takeyi yace."Wallahi ta kuka da

kanta idan ya tashi aure zai aure mace mai tsabta 'yar gayu tunda shi ba kazami bane."
Aikuwa Kuluwa ta tsorata sai ta dage da wanka da wani had'e da kitso akai akai kuma garin Allah yana wayewa zata sa brush ta wanke bakinta tun yana futar da jini har ya daina, amma duk da wannan abun da takeyi Kawu Madu bai saduda ba yana nan da bazawarsa 'yar 'kwalisa har sun tsayar da ranar daurin auransu, Kuluwan bata sani ba sai dai jama'a da yawa sun sani shuru kawai akayi mata ana jiran ranar da amarya zata zo aga me zai faru.


Amadu kasa shiga gidan yay sai ya zauna cikin motar.....Kunyar hada ido yake da mahaifiyar matar tashi, to itama Uwanin tunda taji jama'a nata surutu da amabatar sunan mijin 'yar tata sai ta kasa fitowa tsakar gida ta zauna cikin daki abinta
Kawu Madu da kansa ya fita har bakin motar da yake ciki suka gaisa cikin mutuncin da karamci sannan fa mutane suka farga dashi sai suka dinga zuwa daya bayan daya suna gaisawa, ganin hakan kamar bai dace ba yasa ya fito daga motar yana gaisawa da jama'a cikin sakin fuska da dattako.


Karfe shida sun iso gidan......Lokacin Rashida da Wasila sun saka turare mai kamshi a dakin mahaifiyar tasu wanda ya sha jere mai kyau kuma na zamani, katon gado ne da katifa mai kyau sai katuwar sif mai murfi shida akwatinanta akai sai mudubi da drowars guda biyu koran kafet ne malale a dakin labule koraye da net dinsu, dakin yayi kyau sosai.
Su Kuluwa da Ina Tabawa da Ita mai waina suka rako Uwani dakinta Bitan ta karbesu hannu bibbiyu aka gaisa cikin mutunci da mutuntawa............Wasila bata samu sun ke'be da mahaifiyarta ba ya dinga kiranta a waya ta fito su tafi saboda dare ya soma yi....Uwani tace"Ki shige ku tafi daga baya sai ki dawo ina laifi ma da ya barki kikayi kwanaki biyu, Babu yanda ta iya haka tasa yara suka dauki jakar kayanta Rashida kam fujirewa tayi wai tunda babu makaranta ba zata bisu ba sai jarrabawarsu ta fito, Uwani kam bata ce mata komai ba itama zata fiso ta zauna a gabanta.....Wasila ta fito tana sallama da jama'ar dake gidan duk zuciyarta babu dad'i Inna hajara tasa yara suka fitar mata da kayayyakinta wajan motar......Ita Kuluwa fad'i take "Kice ina gaisheshi." Wasila ko kallonta batayi ba ta fice daga gidan, sukayi karo da malam zai shigo sai ta zube a kas tana kuka, Yace."meyasa kike kuka Wasila. Tace"Wallahi Kawu bana so na tafiya yau." Yace."Kiyi hakuri kibi umarin mijinki Allah yay miki albarka." Ta amsa da amin tana mikewa, Yace."Ina Rashidar."? Tace"Wai anan zata zauna sai sanda jarrabawarmu ta fito." Malam yace."Zancan banza zancen hofi! jirani anan na fito da ita."Ya shiga gidan yana baza babbar rigarsa, Rashida na dakin Uwani malam ya shiga gidan yana fadin"Ina Rashida. tace."Gani Kawu." Yace."Maza ki fito ku tafi ni bana son shashanci." Tace."Kawu Uwani ce tace."Na zauna." Sai ya daga labulen dakin yana fad'in "Uwani anya hukuncin nan yayi dai-dai kuwa."?
Ta dago kai ta kalleshi tace" Malam ai ba cewa nayi ta zauna gabadaya ba idan jarrabawarsu ta fito zata tafi."
Yace."To! to ai babu komai Allah ya kaimu." Labulan dakin ya saki Ya nufi dakin Bitan! lokacin ita kuma tana kicin tana ta kokarin raba abinci dan su Kuluwa suna nan basu tafi ba sai gobe tukkuna.

Dama tuntuni Garba ya shigar mata da kayanta cikin motar daga ita sai baby zahra da jakarta ta nufi motar, wanda yana hangota ya bude motar yana kallonta har ta 'karaso ta shiga tana kumbura fuska, baice mata komai ba ya mayar da murfin motar ya rufe, Garba ya shiga da sauri yaja motar suka dauki hanya.
Baby zahra ya kar'ba daga hannunta yana mata wasa sai kyalkyala dariya takeyi,
Yace."Momyna nayi missing dinki da yawa amma na lura ke da momynki baku damu dani ba, kunyi ki'ba kunyi lafiya kwana biyu."
Kallonsa tayi tana dan sassauta murya tace"Allah Habibi ka yanke min jin dadina ina tare da 'yan uwana kawai sai kace lallai sai mun tafi."
Yace."Akwai wani jin dadi wanda ya wuce ace kina tare dani."?
Shuru tayi masa tana gyara fuskarta, Yace."Ina Rashida."? A hankali tace"Wai ba zata dawoba sai jarrabawa ta fito." Yace."To karatun isilamiyyarmu fa." Ajiyar zuciya ta sauke tace."Ni na ma

nta ma wallahi sabida bana cikin nutsuwa kuma dai Uwani ce tace dole sai ta zauna."
Yace."To tunda Momy ce ta yanke wannan hukuncin bani da magana amma dai naso ta dawo yanzu domin mu had'a izifi talatin d'inmu da ita."
Tace."Itace ta jawowa kanta, idan ta dawo na koya mata inda aka wuceta." Yace."To malama." Shuru motar tayi na minti biyar ya dan kalleta yana kashe ido yace."Wane tanadi kikayi min." ? A hankali yay maganar saboda Garba. Fari tayi da ido tace" Kabari muje zaka gani."
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana Allah Allah su sauka gida yayi masifar d'okanta da kasantuwa a tare da ita.

A daran ranar sunyi soyayya sosai wacce ta sanya su zubar da hawaye dukaninsu suka tabbatar wa da kansu cewar idan babu d'ayansu a cikin rayuwarsu to babu shakka rayuwarsu tana cikin kalubale mai girma.


Bayan dawowarta da kwana uku Hafsa ta haihu d'a namiji ta haifa A ranar data haihu sukaje ganin jinjiri Hafsa ta 'karewa Wasila tanadi sosai tace"Wallahi kinji kunya ace wai wannan zuwan da kikayi shine na farko gidana ai ina sane dake shiyasa nima bana zuwa inda kike koda yake laifin ba na kowa bane na governor ne gashinan ai yana jina.
Amadu da yaga Hafsa ta fusata tana sakin maganganu sai ya fara kokarin kare kanshi da cewar shifa ba laifinsa bane nata tunda yana cewa suzo sai tace tana da uziri.
Wasila ta dinga mamakinsa babba dashi da karya, Hafsa tace" Ai nasan kafad'a ne domun ka wanke kanka dama ina ciki da kai kaine ke hanata zuwa inda nake nagode.
Sai ya shiga bata hakuri Wasilan na tayashi da kyar Hafsa ta sako ta basu jaririn suka dauka......Afnan ta samu abokinyar wasa, baby zahra ta makale jikin Wasila wai lallai sai ta bita su dinga wasa da babynta.
Amadu yace."Kome zakiyu ba zamu tafi dake ba ki hanamu kwanciyar hankali....Khalifa na dariya yace"Afnan fa tayi wayo yanzu ta daina kuka.'' Yace."Kome zaka fada kan Afnan ba zan yarda ba ai ni yarinyar ta shani na warke...........Amadu da Khalifa suka fita sabida bakin dake zuwa, Cikinsu harda Zeey da sauran 'yan gidansu, Zeey tamkar ba gidan 'yar uwarta tazo ba ta kasa sakin jikinta duk dan ganin Wasila a gidan wani irin kunyar yarinyar takeji sosai sai yanzu ta gane cewar abinda tayi itama bata kyauta ba.

Ana ya gobe suna wata 'kawar Hafsa tazo musu da lafiyayyan garin magani mai suna 'kare kukanka maganin na wahalar samu itama yayarta ce take can Ghana acan suke hadashi, maganin na kyau sosai sai dai tsada amma amfani daya zakayi dashi ka gane amfaninsa a jikinka, Wasila bata ji nauyin kud'insa ba ta dauki roba biyu dubu dari uku kenan duk roba daya dubu dari da hamsin....Tace zata bawa Hafsa kudin insha Allah.
Ita yanzu mutukar magani ta tabbatar da kyansa da ingancinsa ko nawa ne zata iya sawa ta siya domin ta gyara kanta da mijinta.


Saboda yawan 'Korafin da Matan Kawunsa Almu keyi masa na rashin zuwan Wasila gidansu ya sanya ya dauketa ya kaita gidan ta wuni tare dasu, sosai Wasila ta yaba da mutuncinsu gami da karamcinsu sun karbeta hannu biyu sun dauki Zahra sun rike wannan ya dauka wannan ya ajiye kamar zasu cinyeta wannan kadai ya sanya taji tana masifar kaunar su, basu tafi ba har sai da Kawu Almun ya dawo daga kasuwa suka gaisa ya dinga sa musu albarka gami da adduar samun zuria mai albarka, a gurguje sukaje gidan Hajja itama suka gaisheta, sai bayan goma na dare sannan
suka koma gida.

********
*BAYAN SHEKARU HUDU*

Abubuwa da yawa sun faru a cikin wad'annan shekarun da suka gabata masu dadi da marasa dad'i to masu dad'in dai sunfi yawa Inda Wasila da Rashida suka sauke al'kur'ani mai girma da sauran litattafan addini kana kuma suka samu gurbin karatu a jami'ar bayaro university Wasila na karantar harkokin kasuwanci wato business administration ita kuma Rashida tana so ta zama malam asibiti ne Wasila mijinta ne ya za'ba mata abinda yake so sai tabi ra'ayinsa domin a zauna lafiya, cikin shekara biyu da ta gabanta *Amadu Musa* Ya kar'bi mulki jahar kano daga hannun Lawan Rabo ya cigaba da tafiyar da mulki kan tsari babu cuta babu cutarwa yanzu al'ummar jahar kano hankalinsu ya kwanta basu da da wata fargaba tunda komai na rayuwa yay sauki! !!!!

a jahar duk wani al'kawari da Amadu ya dauka ya sauke musu tare da taimakon mataimakin shi Sunusi Alhasan *Khalifa* Su Wasila ana gidan gomnati ana cin duniya sosai tayi wani uban kyau! da k'iba da kwarjini ta zama babbar mace, shekarun Zahra biyar, Wasila ta soma sha'awar haihuwa sai dai ta riga ta sanya inplan duk saboda karatunta wanda takeyin basaja, gurin shiga makarantar duk da ko bata rufe fuskarta da niqab ba babu wanda zaice ita matar governor ne sai dai kawai idan an duba yanayin fatar jikinta da hutu da kuma irin manya manyan motocin da ake kawota makarantar dan wataran ma harda securities suke tafiya, idan taga jama'a naso su fahimci wani abun sai kawai ta hana securities din binsu, tasa Rashida tajasu a mota.
Senator Nura mai wakiltar kano ta tsakiya shine ya kwallafa ransa kan Rashida wanda tun tana janyewa har dai ta amince masa saboda ta lura da mutumin yana da kirki da mutunci kuma yana sonta tsakani da Allah, yanzu haka saura watanni Biyu daurin auransu.

*****

Camas! Kuka wiwi takeyi gami da nadamar abinda ta shuka yanzu neman Wasila take ruwa a jallo ta nemi yafiyarta bata san yanzu ganin Wasila ma wani gagarimin aikine babba, kusan kullum sai taje government house din securities suka koreta dan babu wanda yake mata kallon mai hankali tana yawo da yaggagun kaya shaye shayen da ta dinga yi ya mai da ita shudu shudu! Ga mahaifinta ya dade da rasuwa, sai mahaifiyarta suke zaune a gida duniya gabakid'aya ta juya mata baya duk wanda suka buga harkar siyasa sun watse As da su Alhaji Ma'aruf suma takansu suke dan Amadu ya kama governor Lawan Rabo ya gar'kame! suma sai da yasa hukumar Efcc ta tuhumesu, duk wani satar kudi da sukayi da kadarorin da suka siya sai da suka fadi inda suke Amadu duk ya kwace komai yace kudi na talakawa ne......Dukaninsu da gidan da suke ciki suka dogara shima kawai ya bar musu ne albarkacin aure da Haihuwa.

****

*BAYAN SHEKARU BIYU*

Wasila ta kammala karatunta cikin nasarori da samun cigaba, a rayuwa yanzu Wasila tana da ilimin da zata iya gogayya da duk wani jinsin mutum ba'kar fata ko farar fata, tana jin turanci sosai dan watarana ma idan ba tayi ra'ayin yin hausawa ba da turanci take magana, a cikin shekaru biyun da suka gabata, akayi bikin auran Rashida ta tare a gidanta, Uwani kuma ta haifi tagwaye duk maza tare da malam mai allo, hakanan Hafsa ma ta sake haihuwa inda ya kasance tazararsu da kishiyarta Aysha babu yawa, dan tun bayan samun gomnatinsu Khalifa ya kara aure yanzu haka Khalifa nada yara hud'u inda Amadu keda 'Daya........Ganin ana barinsa a baya sai ya tashi hankalinsa, yace."Tunda an gama karatun aje a cire inplan d'in.
To itama dama a dame take haihuwar take muradi, Rashida ce ta cire mata aikuwa aranar da aka cire yini tayi tana zubar da jini ga jikinta yay tayi mata ciwo, sai da ta kwanta jinyya na kwana biyu sannan ta dawo hayyancinta, Jini na daukewa Yallabai ya bud'e Wuta, kullum in bai fita ba yana aikin abu guda, Itama gwanar da yake kullum cikin gyara take bata damuwa, Cikin ikon Allah kuwa ciki ya bayyana a jikinta, sosai sukayi farin ciki ita dashi, ba tare da 'bata lokaci ba ya shirya musu tafiya zuwa 'kasa mai tsarki domin suje sununa farin cikinsu gurin Allah Subahanahu wata'alah!!!

*ALHAMDULILLAHI*


```Jama'a nan na kawo 'karshen wannan littafi mai suna 'YAR BANGAR SIYASA! Ina ro'kon Ubangiji Allah ya yafe min zunubai na, Abinda na rubuta dai-dai Ubangiji Allah ka bani lada, abinda na rubuta na rashin dai-dai Allah ka yafe min👏🏻 Ku d'auki abinda yake da amfani ku watsar da mara amfani Nagode Jama'ata Allah ya 'kara kauna❤️ Sai mun sake saduwa daku a cikin sabon littafina mai suna```
*A KWAI WATA A 'KASA!!*

```Wannan littafin ba zance komai a kansa ba saboda ni nasan komai🤭amma kai/ke duk ina bukatar kusan meke 'kunshe cikin littafin!
AKWAI WATA A 'KASA!!
Kada ku sake a baku labari! yana nan zai zo bada jimawa ba.```






GA MASU BUKATAR PAID BOOKS 'DINA TO SAI KU TUNTU'BENI TA WANNAN NUMBARS D'IN.
👇🏻

*08089965176*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*


LITTATAFAN MARUBUCIYAR:

*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BAL
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment