Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, key tasa zata tashi mota, kiranshi ya shigo tayi banza da wayar har ta katse....Ta tashi motar ta tanaji wayarta nata famar ringnig amma taki dauka, har sai da ya gaji ya hakura.

Yana zauna rike da waya ya rasa ya zaiyi amma yarinyar nan ta shammace shi gabakidaya ya d'o

ra buri da tunani a kanta yana tunanin koda sunanan garin da suke ya ji ya san mutukar sun shiga garin tunda ba'ki ne nemansu ba zaiyi wuya ba, bai hakura ba ya cigaba da kiran wayar yana ta adduar Allah yasa ta dauka kawai sai yaji ta kashe wayar ma gabad'aya, ya dinga bin wayar tashi da kallo tamkar wani zautacce.


****
Yau kwanansu hud'u a Garko hankalinsu ya kwanta sosai Wasila ta mirmure ta samu lafiya sai abun da ba'a rasa ba, kuma laulayin ya danyi sauki sai dai jefi jefi take amai shima da safe takeyi kafin ta karya......Bata aikin komai Bitan da Rashida suke aikin gidan kullum malam mai allo cikin siyo mata kayan gon yake irinsu d'ata da goba mangwaro da sauransu, sannan kullum sai tasha rubutu da tofi safe da dare, ita kanta yanzu ta soma samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya mussaman in ta juya gabas yamma kudu da arewa tana ganin 'yan uwanta da danginta na shige da fice a gidan.....Ita kanta Hajara kullum a tafe take idan bata zo yau ba to gobe zaka ganta tazo kuma bata zuwa gidan hannunta haka kawai sai ta tazo musu da tsarabar kayan kwadayi.................

Malam mai allo da kanshi ya shiga kasuwar garin ya siyo musu abubuwan bukata dai-dai karfinshi yanzu babu wani abun da zasu nema su rasa a gidan dai-dai silafas na yawo a tsakar gida mai allo ya siyo musu ko wanne da nashi.



******
'Bangaran Ahamdu kuwa jinya ya kwanta ta tsayin sati uku har sai da Hajjah tazo gidan tayi jinyarshi wanda sai a lokacin ma ita ta san abinda ke faruwa, aikuwa ta shiga yi mishi fada tamkar ta ari baki, taji ciwon abinda ya aikata shi ba yaro karami ba, an samu yayi auran kuma baije ko ina ba ya fara saki, ai mutane ma sai su daukeshi karamin mutum......Ahamdu baya so ya fada mata dalilin da ya sanya hakan ta faru kawai dai yace mata tsautsayi ne da kaddara, ita kuma tace lallai sai ya kaita gidansu yarinyar tayi bikonta, nan yake shaida mata shima yanzu halin da ake ciki bai san inda yarinyar take ba, Hajjah ta dinga mamaki Yace."Naje can garin nasu gurun waliyyinta shine ya tabbatar min da cewar bata gurinshi amma yafi tunanin tabi mahaifiyarta garinsu, to inda aka samu matsala shine shima bai san wane gari ne ba."Hajja dai ta dauki laifin kacokan ta dora a kanshi ta kuma ce idan haka zai dinga auran yaran mutane yana saki to babu ubanda zai bashi auran 'yarshi mutukar ba kwad'ayayyan abin duniya bane......Tace kuma lallai idan ya samu sauki ya dauketa ya kaita can gurin mai allon a bashi hakuri a bisa abinda akayi mishi, bai musa mata ya amince da maganarta saboda dama can baya tsallake umarinta


****
Bayan Sati biyar.......Cikin Wasila ya fito sosai dan har ya hud'a zani yayi kurcici dashi kamar an kifa 'kwarya yanzu yana matakin wata biyar da kwanaki, tayi kyau sosai ta murje ta daina laulayi yanzu komai tana ci ta zauna lafiya ta daina amai da sauransu, sai dai kuma yanda cikin ke mata motsi a cikinta ne yake damunta, ga wani uban cin abinci da takeyi mutakar tana jin yunwa idan bataci abinci ba sai jikinta yay ta kyarma shiyasa kullum bitan cikin d'orawa da saukewa takeyi bata bari abinci ya yanke mata, sabida Wasila ta zama rumbu.


*****
Sun shirya tsaf tsaf! shida Hajja suka fito harbar gidan nashi, ya fito da wayarshi yana neman numbar Khalifa sai kiranshi ya shigo da sauri ya kara a kunnanshi Khalifa yace "Anya kuwa tafiyar nan dani za'ayi kuwa! Wallahi Hafsa ce ta tashi da zazzabi me zafi yanzu yanzu zan kaita a dubata muna zargin dai ko an samu 'karuwa ne."

Yace."Ayya! Allah ya sawa'ke! babu matsala bari mu tafi kawai insha Allahu zamu shigo nida Hajjah sai mu dubata." Khalifa yace."Okey babu damuwa A mika min gaisuwa gurin aramma." Yace."Zaiji insha Allahu." Yana kokarin kashe wayar ne Khalifa yace."Allah yasa idan kaje kawai ga mutuniyar taka tana cire kafa da kyar! dan cikin nan yanzu nasan yayi kwari." Ya d'anyi ya'ke wanda hausawa suke fad'in yafi kuka ciwo "Khalifa bana tunanin akwai cikin nan fa." Khalifa yace."Kar ka cire tsammani abokina." Yace."To Allah ya amshi adduarka." Khalifa yace."ameen ya rabbi sai kun dawo kenan."? Yace."Insha Allah." Kashe wayar yayi ya mayar aljihu kana ya nufi

parking spece lokacin Garba nata 'kokarin karkad'e mota Hajjah na gidan baya a zaune, kawai shima sai ya bude ya shiga ya zauna kusa da ita, Garba ya shiga ya zauna maxauninshi ya kunna motor a nutse suka fita daga gidan, Yayin da ma'aikatan shi ke faman yi mishi fatan alkairi da dawowa gida lafiya.




Littafin na kudine......!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biyaba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*'Yr Bngr Sys
*61*
'Katuwar tabarma ce shimfid'e a tsakar gidan, Wasila na kwance hannunta rike da mafici tana fifita zafi ake sosai a garin ga dukanin alamu ruwan sama na dab da sauka mai allo yana gefe kan buzunsa da wani ma dai-dai cin allo a hannunshi yana rubutu, Bitan da Rashida suna daga can gefe suna aikin gyara zabbi wanda malam ya sanya d'anshi Tanimu ya yanka su saboda Wasila wai ta dinga samun kuzari da karin jini da lafiya shiyasa ba'a daukar lokaci ake soya mata kaji da dafaffan kwai duk sanda ya fita kasuwar cikin gari kuwa sai ya siyo mata manya manya kifi masu kyau da kara lafiya.........Ya d'an kalleta tana kwance tana aikin fifita sai gumi take Yace."Da alama dai yau garin ruwa ne zai sauka shiyasa zafin ya tsananta da yawa." mikewa tayi zaune tana gyara daurin dankwalinta tace" Kawu malam Allah zafin nan duk ya gigitani na rasa yanda zanyi." Murmushi yay yace."Bake kad'ai ba wasila nima Allah Allah nake in gama miki rubutunan in fita insha iska a waje duba dai dik girman gidanan babu iska ga rana ta game ko'ina." Bitan dake sauraron hirar tasu tace"Ai idan kaga irin wannan ranar to tabbata ta ruwa ce dan haskenta yayi yawa, dubi gabas ka gani hadari ne sosai shiyasa nake sauri in gama ayyukana kafin ruwa ya sauka." Wasila tace"Allah gwara ayi ruwan ko a samu sassauci ni akwana ma anayi.'' Mai allo yasa dariya yana fad'in "Wato ke kanki kika sani ko? idan anyi an kwana ana ruwa 'yan kasuwa suce me? wani fa sai ya fita zai samo abinda zai kaiwa iyali." Tace"Allah Kawu malam zafin ne ya isa Allah na tuba." Bitan tace"Aike Wasila dole ne kiji zafi saboda lalurar dake jikinki dama haka masu ciki suke da jin zafi." Tace"Aikam dubi wuyana kuraje duk sun fito, ni ruwan sanyi ma nake so." Mai allo yace."Wannan ne kuma baki isa ba! za'ayi miki komai wanda kike so amma banda shan 'kankanra." Marairaicewa tayi tace"Kawu malam ba 'kankanra zansha ba ruwan sanyi fa nace don Allah a taimaka asiyo min." Shiru yay yana cigaba da rubutunsa, ta dinga magiya tana karyar da kai! Yace."Bari Tanimu ya shigo." Da sauri tace''Kawu ka bawa rashida kud'in ai tasan gurin." Yace."Bana son aiken rashida gurin nan akwai maza." Shiru tayi tana had'iyar miyau da kyar ma'kogwaronta duk ya bushe! Kallonta yay ta bashi tausayi kwata kwata yanzu baya so yaga abinda zai 'bata mata rai ko ya sata a damuwa, ya kalli Rashida dake wanke hannunta bayan sun gama aikin, yace."Zo kar'bi maza jeki bakin gada gurin masu siyar da ruwan sanyi ki siyo mata kar a bada mai 'kankara." Rashida tace "To ta karaso da sauri ta 'karbi kudin, hijab tasa ta kama hanya ta fita bayan ta dauki wani jug mai dan girma.

Tana fita dalleliyar motarshi ta karyo kwana zata shigo cikin layin......Yara yaran dake wasa a bakin hanya suka watse suna ihu da bin motar da kallo, Rashida na tsaye a bakin kofar gidan motar tayi parking a wani fili dake gefen gidan.....Wucewa take kokarin yi yay gaggawar bud'e motar ya fito gabanshi na wani irin fad'uwa, babu abinda yake fad'i cikin zuciyarshi sai alhamdullihi."!!! Rashida tayi saurin dafe kirjinta tana kallonshi Sai kuma ta washe baki wanda kana ganinta kasan tana cikin farin ciki.......Garba ne ya bud'ewa Hajja mota ta fito tana mita da fad'in " Zaman mota ai sai ya saka ciwo tafiya ba tafiya ba 'kafafuna duk sunyi tsami.'' Hannunta ya d'an ri'ke kana ta gyara sa takalminta da lullubin mayafin ta da ya sauka kafadarta........Rashida ta karaso gurin cike da nauyi da jin kunya take musu barka da zuwa! Ya dinga amsawa da sakakkiyar fuska kamar bashi ba sai wani dariya yake yana godewa Allah lallai Khalifa Waliyi ne ashe dai da gaske a maganarshi , ya tabbata tunda yaga 'yar uwarta itama tana ciki........Ya kalleta a nutse yace."Ina fata mai allo na nan." Tace."Eh yana nan yau bai fita da wuri ba ya tsaya yiwa anti Wasila rubuta." Da jin maganarta sai yaji tamkar an tsiyaya mishi ruwan sanyi mai madara a ranshi yaji duk wani kunci da tashin hankalinsa ya kau! sai ya dinga zumud'in shiga gidan, yana fad'in "To kije ki shaida mishi cewar mune muke tafe." Da sauri Rashida ta nufi cikin gidan cikin murna da farin ciki sai kace wacce akace ga mahaifinta ya dawo duniya......... Lokacin da shiga gidan Wasila ta tashi hakanan Bitan ma tana kicin tana gyara tukunya, ta zube a gabanshi da walwala a fuskarta tace"Kawu ga Alhaji Ahamdu mijin anti Wasila nan shida mahaifiyarshi yace a sanar maka da zuwansu." Mai allo ya jinge allon dake hannunshi yana kallonta Yace."To Masha Allah sune suke tafe cikin wannan ranar? maza karkade tabarmar nan ki gyara musu guri bari na shigo dasu Allah yasa ma ban fita ba da munyi sa'bani." Rashida ta shiga karkad"e tabarma tana sake share gurin da marmatsar da abubuwan dake kan hanya.....Mai allo ya sanya takalmansa a nutse ya fita daga gidan.........Tana 'kokarin fitowa daga band'akin ne hancinta ya sha'ko mata masifaffen 'kamshin turaransa da ba zata ta'ba mancewa dashi ba......Gabanta ya yanke ya fad'i lokacin da ta tsinkayi muryarshi yana sallama a gidan ta kuma tsinkayi muryar mai allo yana fad'in "Sannunku da zuwa Alhaji sannu kun d'auko rana Hajiya sannu da hanya, ku shigo ciki......'Kyauran band'akin ta ri'ke gam! jikinta na kyarma! ta dinga fad'in innalilihi wa'ina ilaihi raji'un! me ya kawo shi? me yazo yayi mana? me yake nema kuma? babu wanda zai bata amsa, ta cigaba da rike kyaure tana rawar jiki tana kuma juyo muryoyinsu a lokacin da suke gaisawa da juna. Jikinta ta duba daga ita sai zanin atamfa dan da zafi ya isheta bayan fitar rashida ruwa ta cika a bokiti taje ta kwara a jikinta wai ko ta samu sassauci babu abinda ke jikinta sai zanin atamfar da dankwalinshi, kamar za tayi kuka yanzu ni ya zanyi na fito ga mutane gashi ba suttura a jikina? tunanin da take kenan ta juyo muryar Mai allo na fad'in " Rashida shiga ki kira 'yar uwarki mana ni kaina a 'kasa ina rubutu ban san sanda ta tashi daga gurin nan da tana kwance a gurin nan da kake zaune." Yafad'a yana nuna masa inda yake zaune, sai ya shiga bin gurin da kallo kamar zai ganta a gurin......Rashida ta duba dakin bata ciki, Bitan dake kokarin fitowa daga d'aki tace"Ai inajin tana band'aki wanka take kasan dama yini take watsa ruwa bata son zafi ai." Mai allo yace."To to koda naji." Ahmadu kuwa jin abinda Bitan tace sai kawai ya shiga rarraba idanunsa a cikin gidan yana laluben ta ina zata fito......Aikuwa sai yaji motsin 'kyaure a wani 'bangare da sauri ya mai da idanunshi gurin......Ta fito a hankali kamar wacce 'kwai ya fashewa a ciki take tafiya, zanin jikinta ya d'angale saboda daurin kirji da tayi sai tayi amfani da dankwalin gurin kare kirjinta da fuskarta.......Gogon ya wani susuce a gurin ya dinga kallonta tin daga kafafunta har zuwa kanta, jikinsa yay wani bala'in sanyi lokacin da ya hango tudun cikinsa dake jikinta, rintse idonsa yayi yana tasbihi ga Allah ya sauke wata gawurtacciyar ajiyar zuciya, Ya bud'e idanunsa da sauri a dai-dai lokacin da take 'kokarin shiga d'akinsu santsin takalmin dake kafarta ya kusa kayar da ita, tayi axamar rike kyauran d'akin tana salati zubewa tayi bakin kofar lokaci guda zanin jikinta ya kusa sa'bulewa dankwalin da ta rufe kanta da kirjinta tuni yayi nashi guri, wani irin 'kullewa marar tayi tana murd'a mata.........kawai ganinsa tayi tsaye a kanta ya wani gigice yana sa'be babbar riga dama manyan kaya ya saka tunda duk sanda zaije gurin mai allo baya zuwa da tazarce na shadda ko yadi riga da wando da malin malin yake sanya........Shine yay bake bake a gurin yana fad'in "Subahanallahi! Kafin ta juyo miryar Bitan na fad'in " Haba Wasila sai da fa na hanaki saka takalmin nan saboda santsin sa sau nawa yana kokarin kayar dake dan dai kawai Allah na kiyayewa ne, kinga ni dai yau ga abinda ya ja miki." Bitan ta 'karashe maganar tana kokarin mikar da ita! Rintse idonta tayi tana fad'in "Wayyo cikina mara ta ciwo Bitan Ya Allah."!!!! Da sauri yay nufi shiga dakin zufa na karyo mishi Hajjah ta dakatar dashi tana hararshi, ita ta shiga dakin suka kama Wasilan suka janye ta daga bakin kofa! Shi kuma ya cire hularshi yana fifita da ita! Wannan wane irin tsautsayi ne? daga zuwanshi yana murna Allah dai ka taimake ni."! Abinda yake fad'a kenan ya koma ya zauna yana cigaba da fifita da hularshi fargaba duk ta cika masa zuciya......Mai allo ya kalleshi cikin naxari sai kawai ya girgiza kanshi yana murmushi a cikin zuciyarshi ya cigaba da d'auraye rubutun dake jikin allon hannunshi, Yace." Tuntuni naji Bitan nayi mata magana kan ta daina saka takalmin nan saboda rashin ji ta'ki dainawa, gashi yana so ya cutar da ita, tunda abin ya kasance da haka da kaina zan dauke takalman na fita dashi.''

Ya aje hular dake hannunshi a gefe yana fuskantar mai allon sosai, Yace."Shine babban damuwar dama, akwai kuruciya da rashin sanin ciwon kai a tare da ita shiyasa take aikata komai yanzu daba dan Allah ya takaita ba da mummunar faduwa za tayi." Mai allo yace."Allah dai ya kikeye." Mikewa yay hannunshi rike da rubutun ya nufi dakin......Binsa yay da kallo yana ji kamar yabi bayanshi sai dai kallon da Hajjah tayi mishi a d'azu yake tunawa.

Mai allo ya tsaya bakin 'kofar dakin yana mikawa Bitan rubutun hannunshi da fad'in "Bata tasha kana kuma ki shafe mata jikinta dashi, za taji sassauci rashin jin magana ne irin na mutan yau, takalma zan daukesu yanzu in fita dasu idan ya kasance ta shiga bandakin babu takalmi sai ta shiga haka ai lalurace tunda shi takalmin na baraxana da lafiyarta" Hajjah babah tace"Kwarai kuwa malam ka kwashe takalman a fita dasu tunda suna neman cutar da ita kuma mutukar tana ganinsu to ba zata daina sakawa ba."

Mai allo ya sunkuya bakin kofar ya kwashe sabbin takalman 'yan madina ya samu leda ya zuba a ciki ya daure ya rataye jikin wata kusa dake bangon gidan yana fad'in "Anjima idan zan fita zan fita dasu in bawa yara sayi amfani dashi."

Yana zaune yana kallon mai allon duk ya rasa abinda ke damunshi hankalinshi na cikin dakin burinshi ya sake tozali da ita da cikin jikinta, jikinsa ne yay sanyi ganin babu wata sakewa irin tada a tare da mai allon yasan dai sun gaisa cikin girma da mutunci amma duk wannan rawar jikin da mai allon keyi masa ya daina magana ma ba sosai sukeyi ba......Hajjah babbah da Bitan suka fito daga dakin, Hajja na fad'in "Ciki fari dama ai kyaga wauta iri iri Allah dai ya rabasu lafiya.'' Duk suka amsa da " ameen." Har dashi gogan da yabi ya zubawa hajja ido yana so yayi magana sai dai yayi shiru ya sunkuyar da kanshi 'kasa, tunda khalifa baya gurin to yanzu hajja itace garkuwa a gurinshi amma shi kanshi yanzu ya gane ya tafka babban kuskure sosai mugun kunyar mai allon ne ma ya rufeshi yanzu da wane ido xai kalleshi yayi mishi bayani dangane da abinda yake tafe dashi.

Hajjah ta gyara zamanta a nutse tace"Malam gurinka nazo domin magana mai muhimanci nake tafe da ita.'' mai allo ya gyara zamanshi yana kallonta a nutse yace."Hajiya ina sauraranki." Hajja tace"Malam da farko dai ina me baka hakuri a bisa abinda ya faru, nasan dole rayukan ku su 'baci saboda duk mutumin da akece an saki d'anshi dole ne ranshi ya 'baci mussaman idan anyi bunkice an duba anga babu 'kwakkwaran dalilin da ya sanya aka aikata sakin kamar dai yanda al'amarin nan faru, yarinyar nan wasila an saketa ba tare da wani dalili me karfi ba, tabbas an shiga hakkinta mutuka!! kuma irin wannan sakin shine ubangji baya so.....To amma nasan dai kai mai ilimi ne kuma kasan kaddara dai- dai gwargwado kasan cewar duk abinda Allah ya kaddara sai ya faru a kan bawanshi to sai ya faru, saboda haka ina so dukaninmu mu dauki wannan abun a matsayin kaddara wacce ta riga fata......Kuma hakika naji dad'i sosai da ya kasance cewa sakin an aikata irin wanda musulunci yake so, akwai sauran dama a halin yanzu, dan haka muke ro'ko ayi hakuri yarinyar nan ta koma d'akinta."

Mai allo ya sauke ajiyar zuciya mai 'karfi! yana kallon matar.....Hakika matar nada mutunci da kima da kuma sanin ya kamata ko ga yanayin kalamanta, baya jin zai iya wani ja'inja kan maganarta mutukar shi Ahmadu da yarjewarsa take masa bikon matarshi, zai amince da maganarta, sam baya so a zo ayi abu irin na baya ma'ana a koma gidan jiya, Ahamdu ne me aure ba Hajjah ba kuma shi ake so ya furta da bakinshi kan cewar ni wane na janye sakin da nayi wa mata wance na mayar da ita dakinta yanzu tana matsayin matata kamar yanda addinin musulunci ya tanada, to mutukar yaji wad'annan kalmomi daga bakinshi, bashi da tace addini ya riga ya halasta masa matarshi tunda dama ba tayi iddah ba." Yace."To masha Allah Hajiya, ai dukanin abinda kikaga ya faru dama da sanin Allah duniya babu wanda ya isa ya tsarawa kanshi rayuwa face wacce Allah ya tsara masa, auran Ahamdu da Wasila ya 'kare a lokacin da Allah yake so, kuma a sanda yake so zai iya sanyawa su koma su cigaba da zama mutukar rabo bai 'kare a tsakaninsu ba, Ni bani da tacewa anan gurin hakanan itama yarinya bata da magana, tunda a yanzu addinin musulunci ya bashi dama a hannunshi, zai iya yankewa kanshi hukunci, ina nufin ya d'auki aniya a zuciyarshi kancewa ya mayar da matarshi ko kuma akasin hakan duk wannan damar yanzu a hannunsa take, Yanzu ni shi nake jira ya furta min da bakinshi cewar ya amince yarinyar nan ta cigaba da zama matarshi ko A'a."? Mai allo ya 'kare maganarshi hankalinshi a kwance.

Hajjah babba tace"Eh gaskiya ne malam maganar ka na kan hanya a yanxu magana na bakinsa dani da kai duka 'yan fatan alkairi ne domin dukaninmu ba zamu haramanta abinda ya halasta ba saboda haka magana yanzu tana gurunka kai muke sauraro." Hajja ta'kare maganarta tana me zuba masa idanunta.........A nutse ya d'ago kanshi zaiyi magana kenan, Ta fito daga dakinsu, sai duk suka zuba mata ido har ta tattako a hankali ta 'karaso inda suke zaune! gaban mai allo ta dur'kusa tana hawaye da rike masa hannuwa tace"Kawu kaine fa kace ba zaka sake takurani ba! Kawu ashe ka manta al'kawarin da kayi min ranar da muka zo garinan kace ba zaka sake yi min tilas ba, zaka barni da kaina na za'bi miji wanda yayi dai-dai da rayuwata na aura." Da sauri! ya d'ago kanshi yana kallonta jin abinda take fad'a! da cikinsa za take tunanin yin aure? Kafin ya gama tunani ya juyo muryarta na shashshe'ka tana fad'in "Kawu ni daina bana son na koma gidanshi, sabida ba zan iya rayuwar da nayi dashi a baya ba, Zargina yakeyi Kawu nasan kasan aure da zargi a musulunci ya haramta ni kawai a kyaleni na haifu lafiya sai a bashi d'anshi." Cikin kuka da yanayi na damuwa take maganar gashi ta ruk'e hannun Kawunta katamau!

Dukaninsu suka bita da kallo mussaman gogon da duk jikinsa yayi sanyi ya dinga kallonta yana hango tsabagen 'kiyaysrshi a cikin kwayar idanunta......Sai yaji wani irin ba'kin ciki da takaici ya turnu'keshi! wato har wani kuka take tana nadama da fad'in ba zata koma gidanshi ba, to me yake mata da za tace ba zata koma gidanshi ta cigaba da yin rayuwar da tayi a baya ba? shin tun da suke yaushe yayi zarginta? shine zai fad'awa kowa cewa ita d'in kamila ce kuma nitsatstsiya tunda ta kawo mishi burducinta! bai ta'ba zarginta ba sai sanda wannan al'amarin ya faru!!!! 'Kwafa yay cikin ranshi, ai magana a hannunshi take ba'a hannun wani ba, malam mai allo na shirin yayi magana, Ya rigashi da gyaran murya kafin yace."Ai maganar saki tuntuni na janyeta malam yarinyar yanzu haka a matsayin matata take, wannan dalilin ne ma ya sanya ni dauko Hajja domin tazo ta baka hakuri a bisa abinda ya faru tsautsayi ne da kaddara amma insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba." Mai allo ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace."To madallah Alhaji naji dad'in wannan kalmar taka kuma Wasila zata koma gidanka insha Allahu amma ina so in baka shawara ko kuma in tunasar dakai duk da cewar ka sani, Allah da kanshi ya hallata saki amma kuma baya so a akaita shi, kayi kuskure a lokacin daka yanke hukunci, bance yarinyar ba tayi maka laifi ba tabbas tayi laifi wanda ya dace ka dauki ko wane irin mataki a kanta, amma banda saki, ni a ganina ba tayi abinda za'a saketa ba, saboda ita mace komai girmanta da shekarunta abar tausayi ce ballanta yarinya 'karama irin wannan!? Ka saketa tana da ciki, abinda ba'aso sannan ta amshi laifinta ta nemi afuwarka ka koreta daga gidanka, bazan 'boye maka Alhaji yarinyar nan ta wuya da wannan cikin na jiki kafin su zo nan kenan, sai bayan zuwansu, dana tsananta gurin yi mata tofi da rubutu sannan ta samu lafiya har kazo ka ganta haka, ina fad'a maka da can kwanakin baya kazo da sai ka tausaya mata mutuka dan abincin kirki bata iyaci sai yame yame irin nasu, to Alhamdullhi yanzu lafiya ta samu tana iya cin komai ta zauna lafiya, saboda haka nake baka shawara da kuma tunasarwa kan cewar duk wani abu da matarka za tayi maka na kuskure to ka dinga sanya hankali da nutsuwa kafin ka yanke hukunci akai dan saurin saki bashi ne hukunci ba, wallahi Alhaji da kazo bayan yarinyar nan ta haihu to banga dalilin da zai sanya in tilas ta mata cewar sai ta cigaba da zama da kai ba, zan dai baka dama ka shiga cikin zawarawanta idan har kana da muradin hakan."
Ya dinga kallon mai allo cike da d'umbin mamaki! wato shine ma zaibi layin zawarawa sai kace wani shashasha! tsaki yaja cikin ranshi mai allo bai ta'ba 'bata masa rai ba irin yau! amma sai ya shanye ya dake! ya hakura tunda dai magana ta'kare ai shikkenan........A nutse yace."Arrama insha Allahu hakan ba zata sake faruwa dukanin abinda ka fad'a gaskiya ne tsautsayi da 'kaddara basa wuce kan kowa, saboda haka insha Allahu magana ta wuce a gurina zan rike yarinyar nan tsakani da Allah da manzonsa, Saboda haka yanzu sai su shirya kayansu ita da 'yar uwar tata mu tafi in yaso sai ta dinga d'an d'ebe mata kewa har Allah ya sauketa lafiya"...............Da jin

Please Login or Register in order to submit comment