Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare sai ta saki fuskarta sosai tana dariya tace"Sannu da zuwa gwara da Allah bai sa ka bawa mijina wahala ba kazo dama bana so ya fita ya barni ni kaina a gida naji dadin zuwanka." Ya danji wani iri da jin maganar Hafsa!wato shine mara galihu kenan wanda bai da mata mai tattalin sa yana yawo da daddare babu me cewa dan me.''?

Kan kujera ya zauna yana jan kafafun Afnan dake kwance kan kujerar tana kokarin yin barci, jin muryarshi yasa ta bude idonta a hankali ta shige jikinshi tana fadin "Dadyna yaushe kazo ina Aunty Amaryata."? Rungume ta yay yana shafa kanta yace." Baby Afnan iya rigima baki bacci ba."? Kai ta daga mishi tana lumshe idonta....Hafsa tace"Yanzu nan ta gama rigima ai ta gaji ta kwanta tana son yin bacci 'kiriniya da fitina a gurin Afnan sai a hankali."

Dan hararata yay yace."Ke waye yasan abinda kikayi kina yarinya gwara nata me sauki ne." Hafsa tasa dariya tare da wucewa daining tana fad'in "Governor da Afnan kenan ai fada a shirya." Shima dariyar yake yana shafa kan Afanan din yana lallabata tayi bacci.

Khalifa ya zauna kusa dashi yana me cire halar kanshi da fad'in"Yau na sha zurga zurga Wallahi da tun safe ban zauna ba."

Yace."Shiyasa nayi ta tsammanin shigowarka naji shiru kasan dai maganar nan ba zata yiwu ta waya dole sai mun tattuna akai , Alhaji Danliti ya matsa min da kiran waya kan dole sai mun bashi rancen kudi har miliyan saba'in wai zai shigo da kaya, kudinshi sun yanke kasan sam bana son mu'amula dashi saboda bai da dad'in sha'ani."

Khalifa yace."Mu aje maganar Alhji 'Danliti a gefe guda ni muhimiyyar magana ce nake tafe da ita." Ahamdu ya kalleshi a nutse yace."To ina sauraranka."

Khalifa ya dan gyara zamanshi sosai ya mai da hankalin sa kan abokin nashi ya bude bakinsa a nutse yace."Shin kasan matarka da ka saki tana dauka da cikin ka har na tsayin watanni uku da sati biyu."

Yaji wani irin shocking a jikinshi ya zubawa khalifa yana kallonshi yana so yayi mishi 'karin bayani. Khalifa ya gyara fuskarsa sosai alamun maganar da zaiyi mai muhimanci ce Yace."Wasila na da ciki kamar yanda kaji na fada maka da farko, Dazu ina kan hanya ta ta zuwa gidanka Hafsa ta kira ni a waya kan cewa inyi gaggawar zuwa babban asibitin murtala dake cikin gari ga abinda ke faruwa, dalili kenan da ya sanya kaji ni shiru banzo ba............Khalifa ya shiga warware masa abunda ya faru da Wasilan da irin sirad'in da ta tsallake dashi kanshi cikin jikinta da yake cikin wasiwasi da 'kila wa 'kala ya kuma tabbatar masa da cewar mutukar ana so cikin ya inganta a kuma haifeshi cikin salama da nutsuwa da kwanciyar hankali tilas yarinyar ta samu kulawa mai kyau sannan ne za'a samu dukanin abinda ake so."

Tunda Khalifa yake maganar yake jin wani iri a jikinshi, ya shiga lissafin watannin cikin dai dai lokacin auransu ne dan a hasashen sa ma yana zargin haduwarsu da yarinyar ta farko ta same shi...........Jikinsa ne yayi sanyi sosai kafatanin hankalinsa ya karkata kan ingantuwar d'anshi da samun xaman lafiyarsa a cikin uwarshi, gabanshi ya dinga faduwa yana addua da godewa Allah da bai sa cikin ya zube a kan hanya ba! Ji yay wani irin gumi na keto masa, Khalifa ya lura abokin nashi ya shiga rud'u da tashin hankali sai ya dafa kafad'arshi a nutse yace."Yanzu wace shawara ka yanke dangane da yarinyar dashi babyn dake cikin cikinta." ? Ya dan kalli Khalifa cikin yanayi na damuwa yace."Nama rasa me zanyi wallahi Khalifa nagode kwarai da gaske Allah ya bar abota da zumunci mai amfani yanzu idan da babu kai mybe da tuni na rasa gudan jinina, bana haufi kan cikin yarinyar nan nawa ne Khalifa nasan lokacin da nayi abina." Khalifa yace."Haba babu komai wallahi ni da kai yanzu 'yan uwane mun wuce a kira mu abokai duk abinda nayi maka kaina nayi wa, ina tambayar ka matakin da zaka dauka dangane da yarinyar da abinda ke cikinta babu shakka dukaninsu suna bukatar kulawa mai kyau.......Yace."Khalifa kasan dai halina idan nayi magana kan abu ko kuma na yanke hukunci kan abu bana ta'ba barin abu daga baya in waiwayeshi, amma tunda haka ta kasance Zan sakata gida in killace ta sannan in hada mata komai na jin dadin rayuwa ta zauna ta cigaba da kula min da yaro na har sanda Allah zai sa ta haife mun abuna.....Idan ta haihu in taga zata shayar dashi ok idan taga bata da ra'ayin hakan zan nemi mai raino insha Allah amma bana ji sanadiyar wannan yaro ko yarinya na cigaba da zaman aure da ita.

Khalifa bai so jin haka da gareshi ba amma bashi da magana dama kuma yayi al'kawari kancwa ya bar cewa dashi ya mai da yarinyar, yasan duk sanda ya gane mahimancin ta a gurinsa zai dawo yana neman shawararshi, Sai kawai yace."Shikkenan hakan yayi dan gaskiya na fahimci akwai matsatsi da rashin sukuni da rashin abinci mai kyau a tare da ita da Mahaifiyarta da yar uwarta ina ganin idan anyi hakan zasu samu sakewa sosai kai kuma zaka samu lada kuma dan Allah ko bayan ta haihu ka kar'bi d'anka ko 'yarka to ka bar musu gidan da komai na ciki su zauna sada'katuljariya zaka samu lada."

Yace."Khalifa a yanzu yarinyar nan zan iya yi mata komai albarkacin gudan jinana da take dauke dashi kasan ni idan nayi kyauta bana waiwaye saboda haka bayan gida ma ni mai iya mallaka musu wani abun ne kar ka damu da wannan." Khalifa ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Hafsa dake karasowa inda suke......Ta zauna kusa da mijinta a hankali kai da ka gani kasan itama tana cikin damuwa, Wai shin Shi governor wane irin mutum ne? ace ayi ta abu d'aya haba ai yaci ace ya hakura ya dawo da yarinyar nan, ta lura kamar ma ya fiso yayi ta zama a haka babu aure da shekarunsa da komai shiyasa mutane ke masa kallon mara lafiya da sauransu. Irin abinda take ta fad'a kenan cikin ranta........Ya d'an kalli agogon hannunshi shifa da ba dan dare yaja ba da ya dauki khalifa sunje ya gano yarinyar nan ba wai dan ita zaije ba a'a dan abinda ke cikinta cikin fargaba yake sosai yana ganin kafin gari ya wace cikin zai iya zubewa...... Babu zato khalifa yaji yace."Tashi muje nagano yarinyar nan."

Khalifa ya kalleshi cikin mamaki yace."Yanzu da daran nan dubi time fa sha d'aya shaura." Ya d'anja tsaki yana mutsika goshinsa yace."Gabad'aya hankalina ya kasa kwanciya Khalifa ina jin a jikina kafin safiya cikin nan na iya zubewa ko wani abu ya faru, nasan mutukar banje na ganota ba ba zan iya rintsawa ba." Khalifa ya dinga kallonshi yana jijjiga kai yace."Shin wai ita kake son gani ko kuma abinda take dauke dashi."? Da sauri yace."No ni abinda ke cikin cikinta nake son gani ba wai ita ba meye gamina da ita." Khalifa yayi wani murmushin takaici yace."To ina me tabbatar maka da cewar ko kaje yanzu wahalar banza xakayi dan nasan tayi bacci kuma ka'idar masu lalurar ciki ba'a tashinsu daga bacci, kuma kana maganar ba dan ita zakaje ba to shi cikin naka in kaje ganinsa zakayi ido da ido ko kuwa zaka ce ta d'aga maka riga ne ka gani."? Ya shiga kallon Khalifa yana me nazarin maganarshi, Ya akayi kwakwalwarshi ta toshe ne? shifa a tunaninsa idan yaje yace ta bud'e masa riga yaga d'anshi! sai kuma yanzu maganar Khalifa ta sanya ya hango kuskuransa, yanzu dai babu aure a tsakaninsa da yarinyar nan yasan ko yaje bashi da hurumin rike mata koda d'an tsaya ballanta yace ta bud'e masa riga yaga d'ansa

Gumi ya shiga karyo masa ya ciro hankici yana gogewa ranshi sai 'kuna yake yi yarinyar nan tayi bala'in cutarsa yasan kuma yanzu shi da kwanciyar hankali har sai yaga d'anshi a hannunshi tukkuna

Khalifa yace."Hakuri za kayi gobe idan Allah ya kaimu sai mu je da wuri ku gaisa kasan kuma ko kaje babu ruwanka da ita tunda ba muharramarka bace." Sai yaji kamar ya kwad'awa Khalifa mari da jin maganar da ya fad'a Yaja karamin tsaki yana me mikewa tsaye da fad'in "Allah ya kaimu goben zan shigo da wuri muje, kuma a goben nake son sauya musu gurin zama duk domin samun nutsuwa da kwanciyar hankalina inaji a jikina mahaifiyar yarinyar nan zata iya zubar min da ciki koda kuwa ita yarinyar bata so." Khalifa yace."Kai kake wannan hasashen amma a dazu munyi magana da mahaifitar yarinyar ta tabbatar min da cewar kwanaki sunzo har gida domin su shaida maka abinda ke faruwa basu sami ganinka ba kaga kuwa idan hakane to bata da hannu gurin zubewar cikin ka." Yayi shiru yana nazarin khalifan kafin ya kad'a kanshi yana fad'in"Koma dai menene ni bazan ta'ba aminta dasu ba tunda sun shani na warke Allah ya kaimu goben kawai." yana gama maganarshi ya nufi hanyar fita, Khalifan ya mike yabi bayanshi.....Hafsa kam dama tuntuni tayi shigewarta d'akin Governor bai ta'ba 'bata mata rai irin yau ba mutum sai kace fir'auna zuciya kullum babu kyau ace kayi ta ri'kon mutum a ranka.



Yanda yaga dare haka yaga rana ya kwana yana juye juye da zumud'in son gari ya waye duk domin zuwa ganin gudan jininshi dake kwance cikin mahaifar Wasila......Asubar fari ya mike ya shiga toilet wanka ya soma yi kana ya dauro alwala ya fito ya shirya tsaf ya nufi masjid, ya kasance mutum na farko bayan liman da ya fara isa masalacin, sai ya zauna cikin nutsuwa ya fara jan carbi kafin liman ya tada sallah.



Misalin 'karfe takwas sun shirya tsaf! sun fito da jakkunansu, da duk abinda suka san nasu ne a cikin gidan, suka fito tare Uwani da Rashida suke jan akwatinan kayansu yayin da Wasila ke bin bayansu cikin sanyin jikinta, wani irin yanayi mara dad'i takeji a cikin zuciyarta.....Bakin gate suka nufa, Wasila ta fito da keys din gidan ta mi'kawa d'aya daga cikin masu gadi tace"Idan As yazo su bashi. masu gadin gidan kamar zasuyi magana sai kuma sukaja bakinsu sukayi shiru suna kallonsu suka fice daga gidan da akwatinan kayansu.......A jigaje ta 'karisa bakin babban titi dan wannan tafiyar da sukayi ya sanya ta haki! dan har sai da suka samu guri suka zauna ta huta tukkuna kafin su cigaba da tafiya.......Babur din a dai-dai sahu suka samu ya daukeshi zuwa tashar kabuga.




"Wai wannan wane irin wulakanci ne ? na shigo gidanka tun safe ka shanya ni a palo sai kace yaronka ina ta fama zaman jiranka kai kana can kanayin abinda ya dameka, idan ba zaka fito ba zanyi tafiyata ba wai ban san gidan bane."!!! Ahamdu yake waya da khalifa lokacin da yake kai komo a tsakiyar palon nashi......Khalifa ya fito daga bedroom d'insu kunnanshi ma'kale da waya yayin da Hafsa ke biye da bayansa hannunta rike da turare da kuma hularshi tana gyarawa.

Ahamadu ya dinga watsa musu harara kamar idonsa zai fad'o 'kas! Yace." Ga d'an iska kun bari yana muku jiran gida kun shigo ciki wai me yasa bakwa gajiya da abu guda ne."!! A zafafe yake maganar......Hafaa ta gumtse dariya kanta a 'kas tana sanyawa mijin nata links din hannunshi tace"Allah ya huce zuciyar governor ba wai abinda kake tunani muke ba, lokacin da kazo gidan bamu dad'e da tashi ba shiyasa."

Ya maka mata harara yace."Ke kika san wannan ni a gurina karfe shida na safe ba safiya bace lokacin duk wani me himma yake tashi domin gudanar da harkokinsa na yau da gobe ke kuma a lokacin kike sake ma'kalewa wai ke gaki wacce ta iya soyayya."

Khalifa yace."Wai meye laifina nan ne? tayi fa 'kokari sosai kawai kazo mata gida da asuba kuma kace sai kaga yanda kake so ba zai yuwu ba lokacin da kazo ma ni ko tashi banyi ba wayarka ce ta tasheni." Yace." Dan Allah ni muje dubi time kun 'batawa mutane lokaci mtsss!. Duk suka bishi da kallo cikin mamaki masifa yake musu sai kace sune suka sashi ya aikata abinda ya aikata shine kuma zai zo ya d'aga musu hankali basuji ba basu gani ba...


A mota ma sai mita yakewa Khalifa, wanda tun baya ramawa har ya shiga ramawa ya dinga yi masa shagu'be duk domin ya fahimci cewar shifa d'an taimako dan haka ba zai zo ya dinga d'aga mishi hankali ba idan yana so ya cigaba da samun nutsuwa da kwanciyar hankali to yayi gaggawar dawo da iyalinshi gabansa, To
wannan magana da khalifa yayi itace ta kashe masa baki yayi shiru sai dai jefe jefi yakan ja tsaki ya duba agogon dake daure a hannunsa.


Dai-dai gate din gidan khalifa yay parking ya shiga horn da sauri daya da sauri mai gadi ya bude gate din dan duk sun dauka As ne sai bayan motar ta shiga cikin gidan ne suka gane cewar bashi bane..........Shine ya fara fitowa kafin Khalifan ya fito.......Dake masu gadin biyu ne daya sai ya tsaya bakin gate din daya kuma ya nufi in da suke....Gaishesu ya shiga yi yana so yayi magana amma be san me zaice ba yaso dai ya shaida fuskokinsu mussaman Khalifa da shine yayi zuwan karshe cikin gidan.......Shine ya fara yin gaba da nufin shiga cikin gidan sosai Kafin Khalifa yace."Ka d'an dakata na kira wayarsu naji ko." Dan tsayawa yayi yana ya mutsa fuska, Khalifa ya kira numbar wayar Rashida dan itace me waya kuma numbar ta ya kar'ba, Wayar na hannunta tayi saurin d'agawa tana kara wayar a kunnanta lokacin suna tsakiyar tasha suna ciku cikun hawa mota........Tayi ta fadin "hello " hello "hello network da hayaniya sun hanata jin muryar Khalifa inda shi kuma nashi 'bangaran yana jin muryar ta rad'au! sai dai dik inda take tana cikin hayaniyar jama'a da ababen hawa! Fad'i yake " Rashida kina jina? kina jina." Da karshe ma sai wayar ta tsinke yay gaggwar cirota daga kunnanshi yana dubawa.....Mai gadin dake tsaye yace."Yallabai mutanan gidan fa basa nan dan tun sassafe suka fita da akwatinan kayansu da alama sunyi balaguro ne."! Ya wani juyo a sukwane! yana kallon gate man d'in bakinsa na motsi......Mai gadin yace."Amma dai ina kyautata zaton yanzu basu isa tasha ba ko sun isa baici ace sun tashi ba tunda kasan dole kafin mota ta tashi sai tayi lodi sai dai kuma muma bamu san inda suka nufa ba."

Jikinsa ya soma wani irin rawa! yana kyarma! kafafunsa suka shiga kyarma Cikin tsawa da d'aga mirya Yace ."Wane irin wawanta ne wannan!? Wane irin sakarci da hauka ne yasa zaku barsu su fita! meye amfaninku a gidan!? waye ya basu izinin fita da jakkunan kayansu!? ina kuma suka tafi? Ina zasuje! min da gudan jinana? sai muryarshi ta shiga rawa yana wa tsawa masu gadin mugun kallo babu marasa tunani da kwakwalwa kamarsu da har suka barsu suka fita daga gidan sun riga sun cutar dashi mutukar sukayi sanadiyar zubewar cikinsa dama tun jiya yake ji ajikinsa akwai abinda zai faru, Ya kalli khalifa yana tsuma!!! Yace." Ko ina suka nufa sai na lalubosu! dan basu isa su yanke min
wannan hukuncin ba, kawai ka shiga mota muje." Yana maganar ne a sanda yake nufar motar tasu cikin gaggawa da kuma saurin gaske ya bude motar ya shiga
khalifan dake tsaye cikin mamaki! ya rasa ma tunanin da zaiyi ashe wasila bata da hankali dama? tanajin abinda likita tace dangane da lafiyarta da babynta amma zata dauki jiki suyi tafiya mai nisa cikin mota mai kwajab kwagab! babu sakarkaru sai masu gadin gidan da suka barsu suka fita daga gidan........Da saurin gaske yabi bayan abokin nashi ya shiga motar da gaggawa ya mayar da murfin ya rufe Ahamdun yaja motar da karfin gaske, ya nufi kofar fita daga gidan cikin sauri wanda yake bakin gate din ya matsa gefe guda yana zazzare idonsa.





Littafin na kudi ne......!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap Numbar
*07084653262*[14/08, 12:04 pm] Farida Books: 'Yr Bngr Sys
*57*
Zaman motar ne ya isheta ta dinga ya mutse fuskarta tana dan tsartar da yawu ta tagar motar kanta ne ke sarawa tana jin wani irin amai na taso mata, hayaniya ta mutane duk ta cika mata kunne ga warin fetur da tsamin hammatar wata mata dake kusa da ita d'aga rigarta ta fito da nono ko kunya ba taji tana shayar da yaronta alhalin motar da akwai maza a cikinta, haushin matar ya sanya ta dinga dauke kanta tana jan tsaki wasu matan sam babu kintsi da kamun kai cikin motar haya mai dauke da mazan da ba muharraman ta ta fito da nono kowa nagani gashi da ta motsa warin hammatar ta zai buga......Mutum biyu kacal ake jira motar ta tashi Wasila duk ta kosa su tafi ko ta sha'ki iska mai dad'i bayan warin hammatar matar ma mazan dake ciki wasun sy wari sukeyi abinka da wanda rana ta daka....Uwani da rashida kam hira sukeyi suna cin awara da suka siya kafin su shiga motar...Kira ya shigo wayar rashida dake kan cinyarta. Da sauri ta kalli Wasila dake zura kanta tagar motar tana shakar iska tace"Anti Wasila kinga Khalifanan ya sake kira." Tace"Ki daga mana to." Rashida ta d'aga wayar tare da fad'in "Hello." Khalifa dake driving yay sauri mika mishi wayar ya kar'ba da sauri yana kokarin kara wayar a kunnensa ta fad'i 'kasan site sakamakon rawar da hannunsa yake yi....Kasancewar wayar ta bugu da karfi yasa ta mutu ya dauko da sauri ya kunna ta bude, ya lalubi numbar yana sake kira, A dai-dai lokacin ne kuma wasu matasa suka shigo motar direban motar ya Umarci rashida ta gyara sosai domin su samu gurin zama garin gyarawa wayar dake cinyarta ta fad'i kasan motar ba tare da ta sani ba....Aikuwa shi wanda zai zauna kusa da ita ya sanya hannunsa ya dafe ta, a take yay dubarar cire sim din lokacin da Rashidan ta juya suna magana da Wasila ya jefa wayar karkashin kayanshi, Rashida matsatsi da xafin mota ya sanya ta manta da wayarta burinta kawai su tashi saboda zafin ya isa.....Aikuwa sai da direba ya cika motarsa tsaf sannan ya shiga ya zauna maxauninsa ya tashi motar suka fita daga cikin tashar suka dauki hanya


Abin kamar al'mara kiran wayar yake ana ce masa a kashe take, ya kira ya kai sau ashirin maganar dai daya ce wayar a kashe take! Ya d'ago kanshi yana wata irin zufa bakinsa na rawa yace."Khalifa wai meke faruwa ne? Wayar nan fa ta'ki shiga kana ji da kunnanka a kashe take Why! Wad'annan yaran naso su sanya zuciyata ta buga!!!!!!! Khalifa tsorona Allah tsorona Annabi kar cikin nan ya zube, ko a samu wata matsalar nasa raina akanshi."Ya 'kareshe maganar cikin rauni da sarewa da al'amarin.

Sosai ya bawa Khalifa tausayi yace."Ni ina tunanin network ne matsalar Amma kar ka damu abokina insha Allah cikin nan ba zai samu matsala ba muje tashar kabuga insha Allah xamu samesu idan ma motarsu ta tashi ai mun san inda suka nufa kai tsaye sai mu wuce can garkon ni da kaina zanyi wa mai allo bayanin komai."

Hularshi ya cire ya ciro hankici ya goge fuskarshi da saman kanshi, Yana jin wata irin fargaba na kamashi yanzu da wane ido zai kalli mai allo to me ma zaice masa idan sunje? Yace"Khalifa bani da wani bayani da zan iya yiwa mutumin nan saboda ina jin kunya wallahi in ce masa saboda d'ana ko 'yata dake cin Wasilan zan dauketa kasan da akwai nauyi." Khalifa yace."Kar ka damu zanyi mishi bayani."
Ya shiga girgiza kanshi yana fad'in "Kamar nasan abinda zai faru shiyasa jiya nace maka muje inda suke da yanzu duk hakan bata faru." Khalifa yace."Ni nayi mamaki wallahi saboda jiya lafiyar Allah muka rabu dasu ko da wasa basu shaida min cewar zasu tafi wani gurin ba amma basu kyauta ba wallahi kuma Wasila tayi wautar gaske."

Girgixa kanshi kawai yake yana adduar Allah yasa su samesu a tasha don shi kam yana bala'in jin kunyar had'a ido da mai allo.

Khalifa ne kawai ya iya fitowa daga motar bayan shigarsu tashar ya kutsa cikin mutane direbobin motoci yana dube duben motocin mutane, ko kusa ko alama bai hango koda kyallin mayafin wata daga cikinsu ba, haka ya gaji ya nufi inda motar su ke fake.....Shi kuwa uban gayyar tamkar wani zautacce ko kuma mara kunne yana ri'ke da waya a hannunshi sai kiran numbar Rashida yake tamkar mai kunnan 'kashi ko kuma kurma yana jin abinda matar nan ke fad'a masa cewar wayar a kashe take amma ya kasa daina kiran wayar.......Ganin Khalifa ya doso motar tasu cikin sanyi jiki ya sanya shi rarraba ido yana jiran karasowarsa...
Khalifa yace."Babu fa alamun yaran nan cikin tashar nan kawai shiga mota muje." Jiki a mace ya bud'e mota ya shiga duk yayi wani laushi kamar mara lafiya....Khalifa yaja motar suka fita daga tashar duk rayukansu babu dad'i.......Sai da suka hau kwalta sosai kana ya sauke numfashi yana huci! yace."Khalifa Allah banta'ba ganin sukuwar uwa irin uwar wad'annan yaran ba, ni yanzu ma ita nake jin haushi wallahi." Khalifa yace."Gaskiya tayi wauta itama data d'auki yarinyar nan da wannan lalurar suka dauki hanya bayan sai da na fad'a mata dokar da likita ta kafa kan 'yar tata shiyasa wallahi mace komai shekarunta watarana ta tafka maka wani abun haushin sai kaji kamar ka d'ora hannunka akanka.

Yace."Nifa babu ruwana Allah cikina ya samu wata matsala sai na dauki mataki kanta da ita da uwar tata." Khalifa yace."Ai kaji irinta wai kai me yasa kake hakane? Matar nan fa ta tabbatar min da cewar sunzo har gidanka da maganar cikin basu samu damar ganinka ba suka hakura suka koma kan me yasa za kaga laifinta anan bayan tayi kokarin ganin an fita hakkina."
Tsaki! yay yaja bakinsa yayi shiru yana muzurai! da ya tuno wani abu sai gabanshi ya fad'i! gaskiya yana bala'in son cikin nan nashi a yanzu ji yake zai iya hakura da komai na rayuwa mutukar cikinsa zai tsira.




Tafiya suke mota na gwajab gwajab yayinda ciwon ciki da mara ya tsananta a gareta ta! ta dinga sunkuyar da kanta tana zufa da kiran sunan Allah gumi ko ta ina d'iga yake a jikinta, tsabar yanda take jin jiki sunan Allah kawai take kira tana jin wani irin imani na ziryartar ta anya kuwa wannan cikin bashi ne ajalinta ba? abinda take fad'a kenan cikin zuciyarta.


Sun isa garin Garko Lafiya sai da kuma lokacin mai allo ya jima da fita tsangaya, Tanimu ne yay musu jagora har makarantar tashi.....Mai allo na tsakiyar al'majiransa ya hango zuwansu sai ya mike a nutse yana fara'a yana musu barka da zuwa......Cikin wata rumfar kwano da babu kowa a jiki suka nufa. Ma allo da kanshi ya karkade musu tabarma suka zauna sai aka shiga gaishe gaishe, Ahamdu sai sunkuyar da kanshi yake duk kunya ta dabaibayeshi sai yanzu yake jin kunyar dattajon yaga shi kuwa sai fara'a yake yana tambayarsa gida da harkokin yau da kullum. Khalifa yace."Alhamudllhi malam komai na tafiya yanda akeso sai da aita tayamu da addua." Mai allo yace."Addua munanan munayi har sai da numfashin mu ya dauke."

Khalifa ya ja gwaron numfashi kafin ya gyara zamanshi a nutse yace."Allah shi gafarta malam dama mun biyo sahun yaran nan ne wato ina nufin Wasila da 'kanwarta da kuma mahaifiyarsu, domin muji shin sun iso lafiya! sannan kuma muna da tabbacin cewa nan suka nufo dalili basu da wani gurin in ba nan d'in ba, Allah shi gafarta malam babu maganar rufe rufe cikin maganar nan Yarinyar nan Wasila na dauke da ciki har na tsayin watanni uku da satika kuma akwai matsala mai girma tattare da ita da d'an dake jikinta wannan shine babban dalilin ma da ya sanya shi Abokin nawa yace."Lallai ilallah sai munzo domin mu tabbar da zuwan nasu cikin 'koshin lafiya."

Mai allo ya dinga kallon Khalifa cikin mamaki da kad'uwa ya d'an gyara zamanshi kafin yace."To Idan na fahimci inda maganarka ta dosa anan

Please Login or Register in order to submit comment