Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ashe kafin mijin nata ya mutu sai da ya fada musu abubuwan da suka faru a baya....."To ai hakika dama dole ce a wuyansu take idan basuyi ba ai sai a kira ki da shegiya gwara ma ki daina wannan magana dan bayan ya bada tinkiya anyi miki rad'in suna babu abunda ya kuma tsinana miki." Rashida tace."Gaskiya dai ki daina ci masa mutunci." Uwani ta fashe da kuka tana fadin"Sai ki zageni Rashida ki fito fili kawai ki zageni yau naga matsayina a gurin ki shiyasa ni Wasila tafi min ke sau dubu duk abunda tasan za tayi ta faranta min rai shi takeyi duk abunda nace tayi tana yi min babu musu ke kuwa fa sai dai ta nemo kudi kina daga kwance kice, to duk rashin mutuncin da kikeyi min sai na fada mata." Tana gama maganarta ta shige daki tana matse hawaye.....Wayarta ta dauka da Wasilan ta siya mata ta hau kiranta....Lokacin suna tare da mai girma governor suna meeting Wasila taga kiran amma bata dauka ba sai bayan sun fito daga dakin meeting din ta kira ta....Uwani na daga wayar ta fashe da kuka "Wasila maza ki zo gida Rashida na nan tana min rashin mutunci duka na ne kawai ba tayi saboda zuwan Malam mai allo."

Rai a 'bace! ta kashe wayar ta nemi numbar Rashidar.....Rashida ta daga wayar tana zumbura baki "Wallahi Rashida ki shiga hankalin ki! dan Kutumar ubanki me malam mai allon ya tsinana miki da har kikewa mahaifiyarki rashin kunya har kin manta irin wahalar da tasha akanmu ashe dama kika bawa malam din yaci mata mutunci kamar yanda ya saba to wallahi sai ranki yayi mugun 'baci! kan hakan." ''Aunty Wasila ki saurara kiji abunda yake faruwa." Rashida ce ke ta magana amma taki sauraranta sai zaginta take cikin jin haushi ta kashe wayar....Wasila ta tsaya tana mamaki! lallai Rashida bata da mutunci ta gama wahala da ita amma ta kashe mata waya....Mahaifiyar tasu ta kira tace"Kinga Uwani na soma zargin yarinyar nan wallahi harda hadin bakinta gurin zuwan Mai allo gidanan dan haka hankalina ba zai kwanta ba komai dare zan shigo unguwar in daukeku ku zauna cikin shiri." Uwani tace"Nima dama shawarar dana yanke kenan dan tunda malam din yazo nasan sauran ma suna tafe haka kawai su rusa mana rayuwa waye zai koma kauye ya zauna? sai dai duk abunda zasuyi suyi." Duk dai magana ta kare ku zauna cikin shiri." Uwani tace "To shikkenan sai kinzo." kashe wayar tayi ta iske inda Camas take zaune tana kallonta.


Har kusan karfe goma da rabi na dare Garba na layin su Wasila cikin matasa yayi basaja so yake yaga ta inda Wasila zata 'bullo, shiru asalima tunda ya zauna ko kare bai gani ba a bakin kofar gidan nasu.....Yananan zaune mutane suka fara raguwa saboda dare kowa na tafiya gida shima sai ya yanke shawarar tafiya dama a Mashin yazo roba roba ya sanya mukuli zai kunna kenan ya hango tawowarsu Wasila jikinta sai walwali ya keyi kasancewar material din dake jikinta mai kyalline wani bala'in kamshin turare ya bakunci hancinsa lokacin data giftashi ta suka shige ita da Camas! wace ta nufi gidansu ita kuma ta hau buga kofar gidan......Matasan dake kusa dashi ne suka fara magana kasa kasa..."Shegiya karuwa kawai ina su Mado nanan da sunci ubanta ta gama guje gujen ta dawo karuwar banza da wofi! ai sai munci ubanta wallahi." Zaginta sukeyi suna kwashe mata albarka garba na jinsu bai ce komai ba yana nan zaune yaga sun fito ita da sauran mutanan gidan.....Gidan suka kulle suka wuce simi simi kamar munafuka...nan yaji matasan dake kusa dashi na fad'in"Ai babu matsiyaciyar uwa sama sa wannan matar duk itace ta sanya ta take wannan rashin mutuncin dazu fa wan mahaifinsu ne yazo suka rufe masa kofa ai wallahi mun kusa tashin su daga unguwar nan." "Kai kasan me zamuyi ma yanzu."? girgiza kai yayi yace." Kone gidan zamuyi dan uwarsu in sun dawo su kwana a waje." Kai wannan shawara tayi kyau abokina." Tafawa sukayi suka mike tare.....Garba ganin sun bar gurin sai shima ya hau mashin dinsa yabi bayan su Wasila can ya hangosu tsallaken titi inda tayi parking din motarta suka shiga a take ya bi bayansu amma yanda yake binsu a hankali ba zasu dauka su yake bi ba.

Dake unguwar masu hannu da shuni ce ko ina haske babu duhu da tarin kazanta daga can bakin titi Garba ya tsaya ya kafe mashin dinsa a hankali yabi bayan motar inda yaga ta nufi wani estete wanda manya manya mutane ke zaune a ciki Garba yayi mamaki sosai babu shakka yarinyar samu kudi ganin motar ta tsaya a bakin gate din wani tangamemen gida ginin zamani, yana kallo mai gadi ya bude gate din ta shigar da motar ciki, sai ya juya da sauri ganin sucurity na nufowa inda yake, da sauri ya tashi mashin dinsa ya bar gurin a guje......A daran ya shaidawa Ahamdu unguwar da Wasila take sam baiyi mamaki ba saboda yasan zasu iya yi mata abunda yafi haka, kudi ne gasu nan a banzace ayi abunda ya dace an'kiyi ana watsar dasu a banza a wofi jirgin sama ma zasu iya siya mata mutukar bukatarsu zata biya.

Uwani da Rashida suka gigice ganin ubangidan da Allah ya mallakawa Wasila suka dinga shige da fice a gidan suna ta'be ta'ben abubuwa Uwani dai kusan zautuwa tayi saboda ta masifar rudewar da tayi taga uwar daula da duniyar da 'yarta ta cikinta ta samu.....Wasila tace "Ko wanne ya dauki daki daya ya ishe shi bukatar rayuwarsa Uwani kinga Abunda Allah yayi mana ko? da kina cewa muje muyi karuwanci shine zamuyi kudi da gaggawa to wannan sana'a da nakeyi mutukar ta karbe ka nan take zakayi arziki yanzu ina da kudi cikin account dina da ban san a dadin su ba kullum 'yan fadar mai girma governor tura min kudi suke bamu da matsalar komai a halin yanzu Allah ya yaye mana kuncin talauci ba tare da mun aikata sa'bo ba.

Uwani tace" Sai yanzu kuma na gane abunda kike nufi Wasila wallahi ni a daukata yanzu babu abunda ke saurin kawo kudi da gaggawa kamar karuwanci ashe akwai sana'ar da tafi wannan to Allah nagode maka da bai sa kun dauki gurguwar shawarar da nake baku ba."

To a ranar dai da kyar su Uwani sukayi bacci dan Wasila dakinta ta shige tayi wanka tayi kwanciyarta bacci mai dadi ya dauketa........A furgice! ta bude idonta tana salati! ta sanya hannu ta kunna fitilar gefan dago tana bin dakin da kallo kamar me neman wani abu....Kafafunta ta zuro kasa suka sauka kan kafet, ta jima a haka kafin ta mike ta nufi toilet fitsari kawai tayi ta dawo ta kwanta ta rufe jikinta da bargo amma banda fuskarta ta kasa kashe fitilar dakin tayi domin gani take kamar zai iya mamayarta kamar yanda ya mamaye ta cikin mafarkinta na yanzu, Tun da take a duniya ba ta'ba ta'ba mafarki wani d'a namiji ba sai yau! shin wai wannan mafarkin me yake nufi ne? meye ala'karta da wannan guy? ita dai tasan ba'kar gaba ce tsakaninsu to mai zai sanya yazo mata a mafarki yana mata murmushi saboda kuma tsabar wuce gona da iri har ya rungumeta yana tatta'ba mata sassan jikinta....Tayi sauri ta sanya hannunta a ramin cibiyarta sai taji tamkar hannunsa ne a gurin a lokacin da yake shafa mata cikin mafarkinta, jin tsigar jikinta ns tashi ya sanya tayi gaggawar cire hannunta daga gurin.....Rufin dakin ta tsurawa ido, itafa wannan mafarkin ya bata tsoro har yanzu tana hango fuskarsa da tattausan murmushi, shin wai abunda tayi masa bai dame shi bane da har zai zo yana mata murmushi, ita ta dauka zasu kulla gaba ne ita dashi wacce tafi ta da tsanani!!!!!!! Juyawa tayi ta rungume pillow tana lumshe ido....."Subahanallahi." Hannunsa taji a jikinsa ta mike a zabure! tana dube dube a dakin........Yau satin ta daya a gidanan amma bata ta'ba shiga tsoro da farga ba irin na yau! mikewa tayi ta zura hijab! ta bude dakin ta futa....Dakin da su Uwani suke nan ta nufa, gani take kamar in ta zauna a dakin ita kadai mafarkinta zai iya tabbata.....Duk suna tare dake bed din babbane su Rashida da Uwani anji Ac sai bacci akeyi, ta samu ta ra'be gefensu ta kwanta had'e da takure jikinta guri guda.......Ta jima a haka kafin bacci ya dauketa.


***
Cikin Shiri ya fito daga bedroom dinshi, Garba da Hadi na zaune a katafaran palon nashi suna ganin fitowarshi suka mike a tare gaisuwa suka mika amsa yana mika musu hannu sukayi musabaha da juna Ahamadu bashi da girman kai da d'agawa........Yana mutumta dan adam!! Garba ya isa inda yake yana gyara masa babbar rigarshi da yake yau shigar manya kaya yayi dakarkiyar galila ce a jikinshi green color wuyan babbar rigar anyi masa aiki na manya mutune wanda mafi aka sari masu sarauta keyi, yana gyara links dinshi Garba ya miko mishi hula zanna bukar 'yar gasken ya d'ora saman kanshi a sai ya sake wankuwa da kyau gyaran fuskarshi yayi dai-dai da tsarin askin dake kanshi saisaye yake yi bai fiye tara suma ba amma baya kwal kwabo ana masa saidaye ne agyara masa fuskarsa dai-dai da zamani....Duk wanda ya kalleshi sai ya sake kallo babu wanda zaice ya kai matakin shekurun da yake kai a yanzu.....tare suka futa dasu Garba mutukar ba nisa zaiyi ba baya tafiya da securities su Garba kadai yake dauka su raka shi, Garba ya bude masa bayan mota ya shiga ya zauna Hadi ya zauna kusa dashi ya mayar da murfin motar ya rufe.....Da sauri Garba ya zauna maxaunin direba tun kafin su iso bakin gate din mai gadi ya bude gate din.....Securities din dake zaune a bakin gate suka dinga daga masa hannu da fadin "A sauka lafiya Allah ya tsare a dawo lafiya." Shima hannunsa ya daga musu yana amsawa da "ameen." Har suka futa daga gidan......Sai da suka hau kwalta tukkuna Garba ya tambayi inda suka nufa, ya shaida masa inda zai suje gidan Hajiya Babba dake Zooroad. Garba ya dauki hanya kamar yanda aka umarce shi.
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_



*Free Pege17*
Hajiya Babbah na xaune a palonta tare da wasu 'yan mata guda biyu Suhairat da Salimat 'Yayan mutun d'aya ne wato Hajiya Maryam wacce ta kasance 'kanwa ga Hajiya Babbah! kasancewar Allah bai bata haihuwa ba har mijinta ya rasu.mutane ke ta nani'ka mata 'yayansu mussaman 'yan uwanta waccan ta turo 'yarta gobe waccan ma ta turo 'yayanta jibi duk dan ganin daular dake tattare da gidan....Suhairat ce mai nacin zuwa gidan saboda kawai tayi katari da Ahamdu mutumin da ta kwallafa ranta a kanshi take masifar sonsa shi kuma bai san tana yi ba sai tayi zuwa goma gidan ba ganshi ba dan bai fiye zuwa da safe ko da yamma ba sai dare yake zuwa gaisheta, to yau dai sunji dadi jin Hajiya tace sunyiwa waya dashi yace zai shigo da wuri Suhairat ta sake gyara fuskarsa ta fesa turare ta 'kame! a kan mujera Salimat kuwa sai dariya takeyi mata tana fad'in"Allah yasa dai ya kyasa dan na lura kinyi masifar matowa a kan mutumin nan." Suhairat tace"Ke dai bari 'yar uwa ni wallahi da zai aureni da gudu zan yarda ina masifar sonsa komai nashi yana burgeni mutum kamili ga nutsuwa kamshin turaransa ma abin alfahari ne." Salimat ta dinga 'kyalkyala dariya tana tsokanar yar uwar tata......Cikin nutsuwa da kamala ya shigo palon bakinsa dauke da sallama. Dukaninsu suka mike tsaye suna masa barka da zuwa, kamshin turaransa ne ya cika musu hanci Suhairat sai murmushi takeyi tana gyara masa gurin zama....Ya zaune a nutse yana fadin" Suhairat kune yau gidan? ina Hajiyata." Wani fari tayi da ido tace"Wallahi kuwa Mune yau a gidan Hajiya na daki bari na kirata." Ta juya tana tafiya cikin wata iriyar siga.....Oho bai san tanayi ba dan idanunsa na kasan kafet, Tare suka fito da Hajiya babbah tana masa barka da zuwa ya amsa yana tambayar ta gida.....Suhairat ta dauko mishi lemo da ruwa ta tsiyaya masa ta mika mishi.....Ba tare da ya kar'ba yace."Bana jin zansha komai yanzu nagode Suhairat." Jiki a sanyaye ta ajiye cup din ta nemi guri ta zauna kusa da Hajiya......Yace."Ina ta son zuwa Allah bai nufa abubuwa sunyi yawa hajiya a gafarce ni." Tace."Ai babu komai Ahamdu dole ne ayi muku uziri saboda yanayin harkar taku ta jama'a bayan nan kuma nasan akwai hidimomi da yawa Allah dai ya taimaka." Ya amsa da "ameen." Palon yayi shiru Yana so yayi mata maganar dake tafe dashi amma zaman su Suhairat a gurin ya hanashi shi mutum ne mai sirri yafi son komai nashi a cikin tsari dan ya lura da yarinyar kanta rawa yake yasan dai zancen gizo baya wuce na koki ga yanayin yanda take masa kwarkwarsa za tace itama sonsa takeyi.

Gyaran mirya yayi a nutse yace."Hajiya muhimiyar magana ce take tafe dani dan daga nan ma idan na tashi can gidan Kawu Almu zan nufa." Hajiya Babba tace "To babu laifi Ahamadu Allah dai yasa maganar dake tafe da kai irin wacce take bakina ce da nayi mutukar jin dadi." Murmushi ya saki wanda yasa Suhairat shagala gurin kallonsa Yace."Yana da kyau yaran nan su dan bamu guri." Hajiya ta kalli su Suhairat da suka kasa kunne suna so suji maganar ko kunya babu tace."Suhairat ku shiga ciki mana." Simi simi suka mike sam basu so hakan ba mussaman Suhairat tafi so ya fadin maganar a gabanta da jikinta na bata wani abu.


"Hajiya na samu matar aure insha Allahu ranar juma'a ta jibi za'a daura aure." Maganar data fito daga bakinsa kenan.....Fuskarta da yalwataccan murmushi tace"Alhamdullihi Ahamdu baka ta'ba zuwa da labarin da yayi min dadi kamar wannan ba masha Allahu to amma kuma al'amarin baiyi sauri ba kuwa ko bazawara ce ne."? Ya girgiza kai "Budurwace Hajiya." Tace."To to masha Allah amma kuma abun yazo min bagatatan banyi shirin komai ba ko da yake dama haka aure yake dashi da mutuwa ba'a shirya musu in lokaci yayi sai anyi, shin yarinyar 'yar wace unguwa ce kuma." Yace." Yar wata karamar hukama ce a wannan jahar sunan garin nasu Garko amma anan tayi rayuwarta Unguwar dorayi daurin auran dai Can Garko zamuje ayi." Tace."To Ubangiji Allah yasa za'ayi damu ya tabbatar mana da alkairi." Ya amsa da "ameen Hajiyata, ni zan wuce can gidan Kawu Almu babu wani abu da kike bukata ko."? Tace." Alhamdullahi Ahamdu bana bukatar komai ka wadatani da duk abun bukata kafin wani ya kare kasa an kawo wani babu abunda zance sai da nace Allah ya saka maka da alkairi ya jikan iyayenka." Yace."ameen Hajiyata Ubangiji Allah ya barmin ke na dinga ganinki ina jin dadi." Tayi dariya da fadin"Wace ni Ahamdu ai mutuwa rigar kowa ce zan mutu kaima zaka mutu." Ya mike yana kallon a gogon dake daure a hannunsa yace."Duk da haka dai Hajjah ina fatan kiyi rayuwa mai tsayi a duniya tace."To Allah yasa Ahamdu Allah yayi maka albarka ya baka 'yaya masu albarka." ya amsa da ameen yana mata sallama har bakin kofa ta rakoshi tana sanya masa albarka


Suhairat dake la'be bakin kofa ta silale 'kasan daki ta fashe da kuka "Shikkenan na mutu ni suhairat shikkenan karyata ta kare zaiyi aure ina zaune duk na kori masu sona saboda dashi bai san inayi ba na shiga uku na lalace." Kuka take sosai Salimat na bata hakuri Hajjah ta shigo dakin.

Tace"Ke suhairat lafiya kike wannan kukan." Rungumeta tayi tana shashsheka take fada mata tsayin shekarun da tayi tana jiran Ahamdu amma yanzu yazo yace zai auri wata.

Hajjah tace"Inda Ahamdu zai aureki da tuni ya aure ki Suhairat ni da kaina nace ki hakura dashi ki zabi miji cikin manema auranki ki aura kikaji ni ba zanyi masa tilas ba, saboda yaron ya daukeni a matsayin uwa yana min biyayya komai nake so yanayi min ban haihu ba amma an haifar min addua ce tsakanina dashi ni dai shawarar da zan baki shine ki hakura dashi ki fito da miji cikin ma nema auranki ki aura magana ta wuce."

Suhairat ta mike daga jin hajjah tana kuka mayafinta ta figa ta dauki handbang dinta ta fice....Salimat ce kawai tayi wa Hajjah sallama tana bata hakuri kan abunda Suhairat din tayi mata.....Tana fitowa harabar gidan taga Suhairat ta figi mota a guje ta fice daga gidan....Girgiza kai kurrum tayi ta sanya direba ya dauketa domin kaita gida.....' Yan asalin unguwar galadanci ne.

****
Wasila ta tashi da wata iriyar kasala da mutuwar jiki, dan ta jima ma a daki kafin ta fito cikin kayatacciyar kwalliya gold kamar yayi magana a jikinta har yatsun 'kafafunta gold ne tana sanye da legos less dan gasken tayi daurin ture kaga tsiya gashinta ta daure shi da katon ribbon ya kwanta a kafadarta idan ka kalleta sai ka dauka irin masu shegen karatun nan ce saboda yanda takeyin mu'amula cikin jan aji da isa......Uwani da Rashida sai girki suke su sauke su dora suci wannan su sha wannan duniya ta samu.

Tunda ta kunna wayarta sa'konni ke shigo mafi yawanci daga abokanan harkarta ne maza sunfi yawa babu wanda ta duba a cikin messages din wayar dai kawai take latsawa tana ya mutse fuska, ita kadai tasan me takeji a jikinta har yanzu gabanta bai daina faduwa ba mutukar zata tuna da mafarkinta na jiya.....Kiran As ne ya shigo wayar ta sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka suka gaisa yace anya zaki fito yau kuwa?
Ya mutsa fuska tayi tace"Yau dai zan huta a gida Gaskiya sai dai gobe." Yace."To babu laifi ko nazo na taya ki hira ne."? a ya tsine tace"Ina da abokanan hira ka huta kawai." Mara zuciya sai ya sake cewa "Okey anjima zan shigo zamuje musha iska." Tace."Ba damuwa sai ka shigo amma dai ka bari sai bayan sallahar isha'i." Yace."Haka za'ayi gimbiya." Hira suka dan ta'ba tayi masa sallama da fad'in zata kwanta bacci ba dan yaso ba ya hakura. Kashe wayar tayi tana tsaki....Camas! tayi sallama ta shigo palon....Taci uwar kwalliya da material mai uban tsada wani shegen dinki akayi mata mai fitar da tsaraici gashi bata sa mayafin kirki ba Camas an samu duniya har mota ce da ita sannan itama Alhaji Ma'aruf yayi mata alkawarin mallaka mata gida cikin gidajensa da yake ginawa.....Tace."Kawata ya yau dai duk na ganki babu kuzari ne na jima da zuwa government house ina jiran zuwanki sai yanzu As yace yau ba zaki fito ba sai gobe."

"Camas yau hutawa zanyi wallahi na gaji kullum kana cikin maza shegu suyi ta kare maka kallo wani ma yana sane zai zo ya gogi jikinka wai bai sani ba, na kusa daina wannan harkar tunda bukatata ta biya." Camas tace"Wallahi karki soma shin me na kasa yace ballanta ya bawa na sama me kika mallaka me kika ajiye a account dinki karfa ki manta yanzu lokacin da zaki sake zage damtse ki tatsi abunda kika tatsa wanda ko bayan mulki ya bar hannunsu kin samu kasonki me tsoka ai wallahi ni yanzu na fara har sai naga abunda ya turewa buzu nadi." Ajiyar zuciya ta saki a hankali tace" Duk da haka dai zan dinga daga kafa ba kullum zan dunga zuwa government house din ba, kina sane dai da kallon da jama'ar gari ke mana ko wasu fa karuwau suke daukarmu, na tsani ace min karuwa wallahi." Camas! tace" Sun dade basu kirani da karuwa ba abunda ya damesu ne idan kace zaka daka ta mutane sai su cuce ka.'' Shiru kawai tayi tana girgixa kai ta tsani a kirata da karuwa gwara Camas idan sun kirata da karuwa babu laifi tunda tana ta'bawa amma ita ba taji ba bata gani ba ana kiranta da kalmar da tafi tsana a rayuwarta.

****
*RANAR JUMA'A*

Su shida ne kacal a cikin motar Ahamdu Kawu Almu da abokinshi sai Khalifa da mahaifinshi Alhaji Iliyasu sai Garba dake gaban mota yana draving, kasancewar shine yasan gidan ya sanya zai jagoronce su.....Ahamdu da Khalifa suna sanye da kaya iri daya farar shadda ce kal dinki babbae riga da yar ciki hula iri daya agogo iri takalamsu iri daya hattata da links dinsu iri daya ne sosai idan ba fada akayi ba ba zaka bambance waye angon ba a cikinsu.

Can bangaran su Malam mai allo kuwa sun shirya tsaf dan tuntuni malam ya shaidawa limamin dake sallahar juma'a a babban massalacin dake garin cewar bayan an idar da sallah akwai daurin auren da za'a gabatar.......To lokacin da suka sauka garin ana ta shirye shiryen tafiya massalaci dan haka a gurguje suka daura alwala suka bi ayarin mutane ya zuwa masjid d'in.

Bayan liman ya gabatar da hud'uba kamar yanda addini ya tanada sai aka tayar da sallah........An idar da Allah anyi addua kana kuma aka shiga daurin aure.............Ana shafa fatiha Garba da Khalifa suka soma rabon alawa da goro gami da dabino cikin bakar leda za'a bawa mutum goro da alawa daurin aure yayi albarka jama'a sai addua suke gami da fatan xaman lafiya ga amarya da ango.






_Muje Zuwa_
*BINTA UMAR ABBALE*
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_



*Free Pege18*
Su Kawu Almu suka rufawa Ahamdu baya zuwa gidan Malam mai allo dake cike taf da dangi, katuwar tabarmar dake shimfide a tsakar gidan suka zazzauna aka shiga gaishe gaishe 'yan uwa sai tambaya sukeyo waye angon ne tsakanin Ahamdu da Khalifa.....Ahmadu yayi kasa da kanshi a lokacin sai ya tsinci kanshi da jin kunya duk da a zuciyarsa auran yayi shine da wata siga ta daban amma sai yaji kunyar mutanan mussaman malam mai allo dake ta kai kawo yana hidima da mutane kana ganinshi kasan yana cike da farin ciki....Khalifa ne ya dinga nuna shi yana fad'in"Gashi nan wannan ne angon bani ba.'' Tsoffin ciki suka soma yi masa d'an biki suna tsokanarshi da fad'in ya tsinci dami akala tunda ya samu nasarar auran Wasila saboda haka ya riketa da kyau dan ba karamar mace bace." Shi dai jinsu kawai yake yi yanayin yanda suke mu'amular su ya bashi sha'awa mutuka kuma ya lura suna masifar son su Wasilar halinsu kawai suke gudu, magana cikin magana suke masa hannunka mai sanda kan yarinyar kan yayi hakuri da halinta da dai sauraransu, sai ya kara jin jikinsa yayi sanyi da al'amarin auran yanzu kuma ya soma da ya sani tunda shi har cikin zuciyarsa ba da manufa me kyau ya auri yarinyar ba amma kuma darajar iyayenta na nema ta sauya masa tunani.

Lafiyayyan towon shika da miyar taushe aka kawo musu miyar taji manshanu gefe guda kuma ga soyayyan naman zabi nan fal katuwar silba......Babu wanda yayi wasa a cikinsu duka suka zage suka ci abincin dan tsabarta da kayatuwarsa tamkar a restaurant babu wata alama da zai nuna abincin karkara ne kwanika sabbi aka zubo musu dalili kenan da ya sanya suka saki jiki suka ci suka koshi suka kora ruwa mai sanyi irin na randa.


Bayan sun kammala sai suka shirya tafiya gida,Malam mai allo ya ke'be da Ahamdu yana masa maganar kan ya za'ayi da tariyar Wasilar Yace." Ya bar komai a hannunshi.'' Malam mai allo

Please Login or Register in order to submit comment