Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sukayi sai yaji gabanshi ya fadi sai ya kira sunan Allah yake samu sassauci! Hannunshi ne ya subce ya danno ma'adanar hotunanshi kawai hotunan da sukayi ita dashi ranar da al'amarin zai faru, suka wanke masa fuska, ya dinga duban hotunan yana mamakinta, sam! babu wata alama data nuna masa a ranar da zai gane ta shirya plan! Aje wayar yay dan baya son ya cigaba da kallonta sakamakon wani irin abu da yaji yana taso masa a cikin zuciyarsa, girgiza kanshi kawai yake yi babu shakka yarinyar nan tayi mishi ba zata!


****
Bayan shigarta daki kuka taci ta 'koshi kana taje tayi alwala tai sallah ta fito palo nan ta tarar dasu Uwani zaune suna mai da magana ita da rashida zama tayi kan kujera kafin tace"Rashida bani abinci naci rabona da abinci tun jiya dana bar nan." Rashida ta mike da sauri ta nufu kicin....Ta kalli Uwani dake shan kunu! tace"Uwani ina Camas."? Tace"Tuntuni tayi tafiyarta bayan rashida ta gama zaginta." Tace"Wane irin zagi kuma? Ke rashida me Camas! tayi miki kike zaginta." Tafada tana kallon Rashidan

dake kokarin ajiye mata abinci a gabanta." Tace."anti Wasila bayan shigarki daki Camas! ta dinga zuga Uwani wai sai munyi karuwanci kamar yanda takeyi shine nace ta tashi ta fita amma ban zageta ba." Uwani tace"Ma'karyaciyar banza da wofi kika zageni ma ballanta Camas." Wasila ba tace komai ba dan ba taji haushin zagin da rashida tayi wa Camas din ba saboda itama ta tsani tayi mata maganar karuwanci wato saboda taga bata gurin shine take zuga Uwani tana kara hawa! aikuwa da yardar Allah ba za suyi karuwanci ba........Abincin take cuccusuwa tana ya mutsa fuska duk da abincin me kyau ne amma sam bata jin testing dinshi a bakinta abubuwan da suka dame suna da yawa....Rashida ta mika mata ruwa tasha kana tace"Ki bani wayarki in kira Camas muje atm zan ciro kudi kudin dana cire jiya na bar jakar cikin motarshi bani da ko kwabo yanzu sai dari takwas da sukayi min shaura."
Rashida tace "Aikuwa babu kudi a wayar." Tace dauko min jakata dana zo da ita a daki." Rashida taje ta dauko mata jakar ta bata dari biyu tace taje ta siyo kati." bakin titi.


****

"Wai shin kiran me kake min ne? da alama dai an samu harka dan idan naga irin wannan kiran naka har dadi nakeji wallahi." Khalifa ne ke wannan maganar lokacin da yake kokarin zama kusa dashi

Ya dan gyara zamanshi yana fad'in"Ba alkairi ne yasa na kira ka ba." Khalifa yayi saurin kallonshi fuskarsa ta rage walwalar da ya shigo da ita yace."Allah yasa dai lafiya." ? Ya mike tsaye ya nufi bakin window hannuwansa duka a bayanshi, Khalifa ya bishi da kallo yana nazarin palon baiji motsin mutum ba, jikinsa yayi sanyi a hankali ya mike ya iske inda yake tsaye ya dafa kafadarsa a hankali yace."Meke faruwa ne? ina matar gidan take."? Ya juyo da wata iriyar fuska mara dad'in kallo yace."Na saketa."!!! Kalmar ta dinga yiwa Khalifa amsa kuwwa! a kunnansa, ya bude bakinsa na sar'kewa yace."Ka saketa."!? Girgiza kanshi yay yana so ya tabbatar masa! Khalifa ya dinga binshi da kallon mamaki kafin yace"Me ya faru! me yasa ka saketa!? me yasa ka yanke irin wannan hukuncin mara dad'i! duk da Allah ne ya hallatashi amma ba abune mai dad'in ji da fad'e a baki ba wallahi bakaji yanda naji a jikina ba fad'ar wannan kalma da kayi."

Ba tare da ya cewa khalifa uffan ba ya wuce shi yaje ya nemi guri ya zauna! hade da rufe fuskarshi da tafukan hannayeshi! Khalifa ya zauna kusa dashi yana me dafa kafadarshi da fadin"Ka fad'a min abinda ke faruwa ni ka barni cikin duhu."! Ya jima hannunsa rufe a fuskarsa kafin ya cire ya tsirawa khalifa ido tiryan tiryan ya shiga fad'a mishi abubuwan da suka faru ya kunna mishi rocouding muryar Wasila da As da irin tsare tsaren da sukeyi a kanshi, ya kuma tabbatar mishi da cewar ajiya Allah ne ya tsareshi dan a yanda 'yan daban gidan gomnati suka zo mishi to babu shakka zasu iya kasheshi ko suyi masa rauni.'

Khalifa ya jima yana mamaki gami da jajanta al'amarin! hakika abinda wasila ta aikata babban abune wanda ya cancanta da ayi mata ko wane irin hukunci, to amma kuma baiji dadin hukuncin da ya yanke a kanta, da tayi shawara dashi da farko ba zai yarda ya saketa ba, zai fahintar dashi cewar sakin bashi ne sulotion, ya zauna da ita tinda yayi wa kawunta alkawari kuma yayi mata uziri! duba da cewar akwai kuruciya a tattare da ita in yaso yayi mata horon da za tagane abinda ta aikata babban abu ne, shawara ta karshe da zai bashi shine yayi aure yayi rayuwa da matarshi a cikin gidan tana kallo yasan dole za tayi hankali ta shiga taitayinta amma yaji zafin sakin da yay wa yarinyar mutune ya mai da ta karamar bazawara.

Ajiyar zuciya ya sauke yace."A gaskiya banji dadin wannan abu ni da kayi shawara dani ba zan bari ka saketa ba, amma yanzu tinda har haka ta kasance please ka dauki niyya ka kuma 'kudirta a ranka kan cewar ka mayar da ita ni da kaina zanje na dawo maka da ita, sai shawara ta biyu shine kayi gaggawar yin aure domun ta gane kuranta.

Ya kalleshi yana ya mutse fuskarsa yace."Kafi kowa sanin idan na bar abu na barshi har abadah! a yanzu idan da wacce na tsana a duniya to wannan yarinyar ce na natseta wallahi, bani kaunar ganinta, saboda haka maganar ma in da

wo da ita bata taso ba, aure kuma sai na huta zanyi."

Khalifa yace."Kar kayiwa mai allo haka Ahamdu! ka duba daraja da furfurar dattijon! ka duba amanar da ya baka! aure baifi sati hudu ba har anyi an gama! wannan wace irin rayuwa ce."! Kai ya shiga girgizawa yana wani irin mirmishi na takaici yace."Komai abinka ba zan dawo da yarinyar nan ba taje kawai! shi kuma mai allo da kaina zanje nai mishi bayanin komai." Khalifa ya dinga kallonshi yana girgiza kanshi tabbas yasan halin abokin nashi! da zuciya da kuma ramuwar gayya ba tun yau ba! Yasan bai da hakuri ko kad'an! mutukar kayi mishi abu bai rama ba to shine yaga dama.

***
Ta kira wayar Camas! ta kai sau ashirin bata dauka ba, sai abu ya shiga bata mamaki! taje wayar tayi tana fadin"Ko bata kusa da wayar ne bari anjima na sake kiranta......Ita kuwa Camas! a lokacin suna tare da As yana shaida mata abinda ya faru dashi itama tana shaida masa irin hukucin da Wasila ta yanke kan cewa ta bar harkar Siyasa kuma ta tabbatar masa da cewar Ahamdu ya saketa yanzu haka tana gidanta.
As yaji dad'in labarin Camas! sai dai kuma baiji dadin furucin da tayi ba na cewa ta bar harkar siyasa hakika ta zama wani jigo a tafiyar tasu, dole ya shirya yaje gidan domin ya rarrasheta ta dawo kawai su cigaba da fafatawa,

Camas! na fita daga gest house din As kira ya sake shigowa wayarta koda ta duba taga Numbar Rashida ce sai ta kashe tana jan tsaki tasan dai zancen gizo baya wuce na 'koki! Tana kokarin shiga motarta text ya shigo ta bude tana dubawa.

_Camas! kina ina ne? inata kiran wayarki baki dauka ba dan Allah kizo gidana yanzu zamuje banki zan cire kudi yanzu ina jiranki_

Tsaki taja mai tsayi lokacin da tagama karanta text din ta bude mota ta shiga tana fad'in"Shashasha kawai ai kud'in nan sun shiga accont dina kenan! ke kin tsira da gida ni na tsira da kudi a tafiyar nan! babu abinda baki mallaka ba dan'kareran gida iyayen kudi gwala gwalai, ni kuwa fa in banda wannnan fankon motar babu abinda na tsira dashi, saboda haka na cinye kudi wallahi komai za'ayi sai dai ayi." Tuka motarta tayi ta bar gurin hankalinta a kwance.








Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*51*

Wasila tayi ta tsammanin amsar Camas! taji shiru har wajejen karfe goma na dare bata daina kiran Camas! a waya ba, gashi dai tana shiga amma kuma taki dauka......Uwani tace"Wai kiran me kike mata ne? ni nasan da wuya Camas! ta dawo gidanan dan baki ga irin zagin da rashida tayi mata ba." Tace."Uwani ba wannan matsalar bace, kin san na fad'a miki jiya Ahmdu yace zai min bincike cikin accont dina sai na yanke shawarar kwashe kudina dake ciki na mayar accont din camas! kudin suna da yawa fa kusan miliyan biyar ne zuwa shida, a jiya na ciro dubu hamsin to jakar tawa na motarshi, ban dauko ba, wannan dubu dayan ma da nayi kudin mota gurin zuwa nan na siyi kati Allah ne ya taimakeni na tsinta cikin jakar dana zo da ita, kinga yanzu duka sau dari biyar a hannuna gashi ina ta kiran Camas a waya taki dauka."

Uwani ta soma tunani cikin fargaba da faduwar gaba tace"Anya Camas! ba amanarki zata ci ba kuwa irin wannan kira da ake mata ai yaci ace ta dauki wayar idan ba da abinda ta shirya ba.

Rashida tace"Aikuwa wallahi ko tana yawo da ubanta sai ta fito da kudin nan tabd'ijam! miliyan shida za ta cinye lallai bata da hankali.

Wasila tace"Allah nima jikina ya soma sanyi da al'amarin anya kuwa! amma dai bari na sake kiranta mu gani." Nan ta shiga kiran wayar Camas! gashi dai tana shiga amma babu amsa! dukaninsu hankalinsu yay masifar tashi mussaman Wasila da tasan wannan kudin su kadai ne suka rage mata kuma sune zasu taimaka mata ta 'bangarori da dama tunda dai ta 'kudiri aniyar barin harkar jagaliya......Sai kusan karfe daya na dare sannan sukaje suka kwanta dukaninsu babu wanda yay baccin arziki sai juyi sukeyi mussaman wasila da abubuwa suka taru sukai mata yawa, kuka take sosai shashshekar kunanta yasa Uwani mikewa zaune tana kallonta, Tsakanin d'a da mahaifi sai Allah sai taji tausayin 'yar tata itama ta hau share hawaye tace"Wannan kukan bashi ne mafita ba a gurinki, wai shin meye abun damuwa da tashin hankali dan wannan mutumin ya sakeki ke ba abin alfahari bane a gurinki za kici karanki babu babbaka yanzu fa wata dama kika samu da zaki cigaba da neman kudinki gashi Allah ya sanya miki nasibi a cikin harkar kina nema ki 'barar da damarki, ni dai idan zakiji maganata shine gobe idan Allah ya kaimu ki shirya ki tafi gidan gomnati domin cigaba da gudanar da harkokin siyasarki."

Wasila taja majina tana goge fuska tace"Nifa Uwani na fada miki bazan sake yin wannan harkar ba na fada miki ni yanzu babban damuwa ta shine idan Camas! ta salwantar min da kudina ya zanyi da rayuwata da wane kudi zan kama sana'a me zan juya ni ba zanyi karuwanci ba kuma ba zan koma wannan harkar ba."

Uwani tace"Idan ya kasance Camas! ta salwantar miki da kudi ba sai ki maka ta kotu ba, sannan kina maganar sana'a to tunda kince ba zaki koma harkar siyasa ba kuma kince ba zakiyi karuwanci ba to me zai hana ki shiga wasan hausa (film) nasan mutukar kin shiga wannan harkar zakiyi arziki na ban mamaki."

Wasila ta dinga kallon mahaifiyar tata cike da tsananin mamaki! wai me yasa uwani take hakane? kullum bata da buri illa taga ta dorasu turba mara kyau! idan akwai abinda ta tsana a duniya bai wuce wannan harkar ba film! duk lalacewa ta tattare a gurin koda kai mutumin kirki ne kana wannan harkar jama'a ba zasu kalleka da kima ba.

Ba ta sake cewa da ita koma ba ta koma ta kwanta tare da juya mata baya tana addua cikin ranta tana jinta tana sake kwarzanta mata nasarorin harkar film din da yanda 'yan mata ke samun mahaukatan kudi mutukar sun shiga harkar....Uffan bata sake ce mata har dai taji shiru hakan ya tabbatar mata da cewar bacci ya dauke ta, sai ta mike a hankali taje ta dauro alwala ta fito a nutse ta tada sallah nafila tayi raka'a biyu ta dade sujjada karshe tana kuka da addua da fadin"Allah ya kawo mata agaji ya yafe mata kusa kuranta na baya.....Addua ta shafa ta kwanta kan daddumar bacci me nauyi ya dauketa.



Asubah suka tashi sukayi sallah Uwani ta koma tayi kwanciyarta, Wasila da Rashida suka zauna suna shawarwarin ya za suyi, Tunda yanzu ma sun sake kiran Camas! din bata dauka ba, Rashida tace",Anti Wasila bari gari

yay haske sai muje gidansu shegiya macuciya dama ni tuntuni bana kaunar abotarku da ita na tsaneta wallahi." Hannunta rike da wayar tana ta trying tace"Rashida bamu da tabbacin samun Camas! a gidansu shin ko kin manta ne? ko lokacin da muke unguwar sai tafi sati biyu bata kwana a gidansu ba tana can yawon bin maza watarana ma gidanmu take zuwa ta kwanta." Rashida tace"Na tuna yanzu to ya za'ayi a same ta."? Shiru tayi tana nazari itafa ba tasan ya za'ayi a sami Camas! ba dan bata tantance in da take ba......Rashida tace",Anti Wasila ki shirya sai na raka ki government house din nasan za'a iya samunta a can." Girgixa kanta tay tace"Har abada na bar wannan gidan tunda banda ala'ka dashi a halin yanzu, kuma bai zama lallai a samu Camas! a can ba, ban'ki ma idan anje gest house din Alhaji Ma'aruf mybe a iya samunta a can."! Rashida tace"To ki shirya muje can d'in." Shiru tayi tana naxari kafin tace"Rashida ba zanje ba kawai kyaleta don Allah ni na hakura taje kanta tayi wa in ta min maganar kudin shikkenan idan batai min ba na barta da Allah." Rashida tace"Ni dai da zaki min kwatacen gest house din da naje naci ubanta wallahi sai ta baki kudinki." Girgiza kanta tayi tace"Rashida ba zakije wannan gurin ba kawai dai tinda nace na kyaleta da Allah shikkenan."

Rashida tace"shikkenan bari na hada mana abin kari." Wasila ta mike suka shiga kicin din tare, sto ta bude tana duba abinda yay musu saura na kayan abinci shinkafa ce gatanan duka bata kai rabin buhu ba sai kwalin indomee biyu da taliya da macaroni mansu ma ya kare da kayan maggi babu siga saura kwali daya gwangwanin madara da milo biyu ya rage, hankalinta yay masifar tashi tace"Rashida abinda yay saura kenan?" Rashida tace"Eh mana kinga ni dai.'' Frige ta bude wayam! babu komai a ciki sai robobin lemo da ruwa wanda suka sha suka mayar ciki......Tace"Innalili wa'ina ilaihi raj'iun." Fita tayi daga kicin din ta koma palo ta zauna, tana kuka yanzu idan kayan abincin nan ya kare ya za tayi.......Shikkenan zasu komai rayuwar kuncin da sukayi a baya, Sai hawaye ya shiga zubowa daga idanunta tana tausayawa rayuwar da zasuyi nan gaba.

Tananan zaune Rashida ta fito da fulas din shayi da wata karamar kula data zubo musu indomee a ciki ta aje taje ta dauko sauran kayan da zasuyi amfani dashi gurin cin abincin, ta hada musu suka fara karyawa Wasila dai cin indomee kawai take hankalinta duk baya jikinta tunaninta ya ta'allaka gurin yanda za tayi asirinsu ya rufu....Rashida tace"Anti wasila ina gold din da kika siya kwanaki ba sai ki siyar dashi ba nasan kudin zasu isa ki fara sana'a dasu." girgiza kanta tayi cikin tsananin damuwa da neman mafita tace"Rashida kin mata ranar da Ahamdu ya dauke ni da sunan matarshi, ranar nayi ado da da gold din har nasa lifaya keda Camas! kuka dinga kwarzanta kyawun da nayi gabakid'aya gold dina na gidan Ahmadu in banda wannan zoben dake hannuna." Rashida jikinta yayi sanyi sosai babu shakka suna cikin tsaka mai wuya dama abinda takeji kenan gashi kuma ya faru, tace"Shiyasa tuntuni nake hanaki wani abun saboda dama ni tuntuni na dawo daga rakiyar Uwani wallahi duk wata masifa da muke ciki itace ta jefamu kullum burinta muje mu samu kudi ita tana zaune a gida, Allah ya baki miji nagari me kudi babba mai hankali wanda zai rike ki da kyau ta zugaki kin kashe auranki, gashinan komai ya jagu'be! dama abinda nake ta tunani kenan." Ajiyar zuciya ta sauke tace"Rashida mu bar wannan maganar don Allah hausawa nacewa tun ranar gini tun ranar zane duk abinda kikaga ya samu bawa to da sanin Allah, ammafa wani abun mutum shike janyowa kanshi Ni da uwani mun so zuciyarmu kuma gashinan ta kaimu ta baro amma babu komai Allah yasa ya zama izina a garemu ni da ita, yanzu mu gama karyawa sai muje can d'orayin gidansu Camas ko Allah zai sa mu same ta."

Uwani nacan na bacci suka shaida mata inda suka nufa cikin bacci tace dasu Allah ya kiyaye suka kadai kansu suka fita daga gidan.


Asabe mahaifiyar Camas! na zaune a kujera 'yar tsuguno tana tsince shinkifa taji sallamarsu, ta amsa tana musu sannu da zuwa tabarma ta shimfida musu tana fad'in "Wasila yau kece a gidan

namu, Ina tace Hadiza zata rakani inga inda kuka koma Allah bai nufa ba sannunku da zuwa." Suka shiga gaisawa, Asabe na tambayarsu Uwani sukace tananan lafiya lou. Wasila tace"Camas! kuwa tanan."? Asabe tayi kasa da kanta ran nan a 'bace tace"Yaushe rabon hadiza da kwana a gida ai tafi wata uku sai dai takanzo duk bayan sati biyu to wannan karon ma kinga satin ta uku bata zo ba." Wasila tace"Ayya! mybe tananan tafe." Asabe tace"To Allah yasa." Shiru sukayi kafin su ta mike Asabe tace"Har zaku tafi bazaku tsaya kuci abinci ba." Wasila tace"A'a Asabe mungode." Har soro ta rakosu tana fadin su gaishe da Uwani da kyau kafin tazo.

Suna fitowa Wasila tace na fad'a miki dama kinga munyi asarar kudin motarmu ko? gashi bamu dana komawa gida tsakanin dorayi da tishima akwai nisa sosai dan da kyar ma aka kawo su a dari biyar kona pure watar basu dashi.....Rashida tace"Mu shiga gidanmu wanda muka bawa malam 'Dayyabu nasan idan yananan zai bamu kudin mota da zamu koma gida." Wasila taji dadin maganar Rashida sai suka nufi layinsu na da, suna shiga layin suka hango, gidansu ya koma katin sai da kayan provision! tsayawa sukayi suna mamaki! wani yaro da yazo wucewa ya shiga kallonsu yaso ya ganesu Wasila tace"Kai waye cikin provision din can." Yaron yace."Jazuli ne na gidanmu malam d'ayyabu ne ya siyar masa da gidan shi kuma ya ruge yayi kanti." Wasila da rashida suka shiga mamaki! ashe malam dayyabu haka yake sun bashi gida domun ya zauna ya siyar ya kar'be kudin ya gwammace yayi ta yawon haya da yara da mata, cikin unguwar dama su Wasila da gidan malam dayyabu sune talakawa, gwara su wasila ma gidan kansu ne shi kuwa malam dayyabu gidan haya ne duk lokacin karbar kudi sai anyi rigima dashi masu unguwa sun taru a kanshi sannan zai bada kudin, shinda wasila ta tausaya masa suka bar mishi suna ganin tunda sun samu wani me zasuyi dashi ashe bayan tashin su da sati biyu malam dayyabu ya siyar da gidan ya kama haya ragowar kudin yasa a aljihu yana cin karansa babu babbaka dasu.......Ajiyar zuciya suka sauke a tare suka kama hanya suka bar gurin zuciyarsu cike da wasi wasin yanda zasuyi.


Sosai suka dingi tafiya kan titi wanda tun suna magana suka daina tafiya kawai sukeyi suna yanke yanken hanya har Allah yasa suka fito titin gadon 'kaya! Rashida ta sharce gumin dake goshinta tana haki! tace"anti wasila zama zanyi na huta na gaji wallahi." Wasila tace"Mu samu guri mu zauna nima nagaji." Suka sami guri dai-dai Gate din shiga Management suka zauna suna hutawa, sunanan zaune daliban dake makaranta suka soma fitowa 'yan mata maza zawara da matan aure wasu na fitowa da motocin su wasu wasu kuma na tare abin hawa! Wasila ta dinga kallonsu suna bata sha'awa suna da gata suna da galihu sunyi dacen iyaye sun tsaya musu kan ilimi su kuwa fa! sune nan sune can! Sai taji zuciyarta ta karye hawaye ya tsinke mata! tayi gaggawar sunkuyar da kanta kasa tana sharewa bata so Rashida ta gani sannan kuma jama'ar dake gurun suma bata so su gani, tana dago kanta suka had'a ido da Suhairat ita da kawayenta bakin wata mota! Zasu shiga macace take driving din, da sauri ta kauda kanta gabanta na faduwa tace"Rashida tashi mu tafi." Rashida tace"Anti wasila dan bari mu sake hutawa wallahi gurin akwai iska." Tace."Rashida hutun jaki da kaya kikeyi kawai ki tashi mu tafi mu samu mu fita babban titi na sabon titi." Rashida ta mike tana yafa mayafinta sukayi gaba.......Motarsu Suhairat ce taci burki a gabansu, da sauri suka matsa baya Suhairat ce ta bude motar ta fito sauran suna ciki suna hangensu

Gabansu ta tsaya tana watsawa Wasila kallon banza tace"Ke matar babban mutum ina zuwa haka? ya naga kina yawo a kasa ko satar hanya kikayi kika fito yawon tazubar d'in da kika saba."!? Wasila tayi shiru tana kallonta Rashida tace"Haba Suhairat wace irin magana ce wannan? kin manta anyi muku tsakani da anti wasila meye ruwanki da ita yanzu." ? Suhairat tayi dariya tana gyara zaman glass din dake idanunta tace"Rashida daga tambaya sai cibi ya zama 'kari! ai gani nayi bai dace ace kamar wasila matar *Ahamadu Musa* na yawo 'kasa ba, ai kamata yay mu ganta cikin katuwar mota

wacce ta amsa sunanta, ko da yake dai ina jin satar hanya tayi ta fito, Okey karfa ku damu da maganata, ba wani abun nake nufi ba, saboda haka na barku lafiya." Wasila da Rashida suka bita da kallo har ta shige motar tasu suna kallonta tana she'ka dariya tare da tafawa da 'kawayenta tana nuna wasila da hannunta su kuma sai dariya sukeyi, kafin wacce take driving din ta figi motar a guje suka bar gurin.

Wasila ji tayi gwiwowinta sunyi bala'in sanyi ta inda har ta kasa motsa kafafunta da niyar tafiya sai kawai ta nemi gefan titi ta zauna rana na kwallare mata fuska zufa! ta shiga ketowa daga jikinta

Rashida itama ta zauna kusa da ita tana fad'in"Amma wallahi suhairat din nan bata da mutunci shegiya guzumar banza wacce ta rasa mashinshine anti wasila ki kyaleta don Allah mybe suna da labarin Ahamdu ya sake ki shiyasa suke murna da dariya amma babu komai ai duk abinda mutum yayi kanshi.

Ba tace komai ba tana dai sauraran Rashidan da duk rarrashin da take mata ita kuma sai nanata kalmar innalilihi wa'inna ilaihi raji'un takeyi a zuciyarta, ji tayi komai na rayuwa yayi mata zafi ta dinga nadamar kuskuran da tayi a baya, kanta ne ma ya soma yi mata ciwo, rana ce ko damuwa ce ko kuma rashin bacci ne? babu wanda ya sani sai Allah.

Kusan mintina ashirin suka dauka a zaune a gurin masu babur din a dai-dai ta sahu sai tayi suke musu wai ko zasu shiga kowa na ganin lamun ba shiga zasuyi ba sai ya buga babur dinshi yayi gaba!..................


Cikin 'kwalleliyar ranar dake kan ganiyar ta, suka fita, titin sabon titin gidan 'kankanra lokacin sunyi masifar galabaita mutuka gashi ko na pure watar babu Wasila taja hannun Rashida suka fake wata inuwa still dai a bakin titin suke zaune suna mai da numfashi suna kallon ababen hawan dake shige da fice a gurun......."Wasila anti Wasila yunwa nakeji da shiru kinji ma'kogwarona kuwa kai anya ba zamu nemi taimako ba kuwa."?

Wasila tace"Nima nagaji Rashida taimako a ina zamu nema."? Anti wasila mu nemi left gurin masu motar gida sai sunfi sauki akan masu a dai-dai ta sahu tunda su kinga sana'a suka fito." Wasila tace"anya kuwa Rashida."

"Allah anti wasila ba zamu iya kai kanmu gida ba akwai fa nisa gashi ko rabi ba muyi ba." Wasila tace"Akan muyi left din nan ai gwara mu tambayi wannan me shagon na tsalleke watakila ya taimaka mana." Rashida tace"Bari naje ki zauna dan na lura kamar jiri ke d'ibanki." Tace"Wallahi jiri nake rashida yi sauri kije Allah yasa ko dari biyu ya bamu." Rashida ta tsallaka titi domin zuwa gurin me shago........Mai shago najin bukatar Rashida yace "Duba daya ma zan baki amma shigo ciki na aunaki." Rashida ta gane abinda yake nufi duba da irin yanayi kallon da yake mata na iskanci! sai

Please Login or Register in order to submit comment