Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Basu mamaki karshe ma zubamishi Ido suke. Gani yanda suhaima ke juyashi son ranta.. yakeyi, dayake ba soyaya Allah bane har wani tsorata yakeji, suhaima duniya ta takeci da tsinke, ta taka duk Wanda taga dama, ba Mai tsawata mata, yau itane a Wana kasar gobe a wacan..

Suna nema shekara bakwai kenan da aure , suhaima ko Bata wata batayiba, haydar Idrees, Hafiz duk matasu su haihu, haydar na da biyu, Hafiz da Idrees na daya duka mata, fawaz da Suleiman su ma duk suyi aure da yayya..

Aliyu tun abun bai damusa, har ya Soma damushi na Rashi haihuwa, yanaso shima
Yaga kwaishi a duniya ,ga dukiya ya Tara ama ba yara daza su Sanya shi nishadin, fawaz yabashi shawara suje asibiti a dubasu, yazo yasami suhaima da zance, ta daburce da Bata taba tunani Rashi haihuwa zai dameshiba, nandana ta Amince tasa abunda ta taka...
Suhaima duk hospital da sukaje kafi suga Doctor sai ta zangaya ta bribing doctor na,dun yasa Aliyu ne da matsala, wani sirri suhaima da bakusaniba, lokaci da zata cire ciki na hudu maihafata ya lalalace aka cire ciki da mahaifar gabadaya, shiyasa batasan Aliyu yasani, har kasa waje suje don adubasu, dayake Yar duniyace tasan yadan zata shawo kan doctors su amince, waesu inbasu karbi kudi ba har Basu kanta tanayi don su yarda..

Aliyu gani duk inda sukaje abun daya yake nunanawa cewa he's infertile" ba zai haihu ba, yasa ya yarda yatara komai nashi yabar ma sarki Allah ...



Yau ma hajiya binta ne tazo har gida ta masu Ammi gori Rashi haihuwa da dansu baiyi , harda cewa ita tasan yarta ba juya bace, ita fa tanaso gani jikokita su San yanda zasuyi, sanda Tama su Ammi tas kafi tabar gida cike da matsifa har ta fita ba Wanda ya tanka mata..

Aliyu na gefe Ammi zaune, Ammi kam ta zuba uban tagumi , Aliyu nata aiki lalashi yace" Ammi kuyi hakuri Kar ku Bari abunda ta fada ya dameku, haka Allah ya tsara min, ga yayya kanena su isheni rayuwa"

A hankali Ammi ta Dora hannuta sama na Aliyu tare da tsareshi da Ido , gani yadda damuwa ta fito karara a fuskarshi , a fili ya sauke ajiya zuciya yakalli Mami Hadi da cewa " please Mami kuyi hakuri da halisu, Mami komai Mai wucewa ne"

Mami taja tsaki tace " tir da hali iri na waena mutani, ba uwa ba ba yarba, Sam Basu San kadaraba , badu Allah ya kadara aure ba, ai kafi karfi wanan mata taka, da Bata gaba Bata baya, mtchewew , Allah na na zai kawo maka sauki"


















😭😭😭😭😭😭😭😭
Anty Aisha Allah yajiqaki ya Kai rahma da haske kabariki πŸ™ Wanda suka rigamu gida gaskiya Allah yajiqasu ya Allah πŸ™πŸ˜­πŸ˜­


Manage please ba time yanzu πŸ™πŸ™πŸ’–β€οΈ


πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
DOCTOR ESSHA
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

WRITING BY
J Hajara



🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ

M.W.A


Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.πŸ€™πŸ»


Https://www.facebook.com/107980080946102? referrer=whatsa
_____________________________________



5️⃣4️⃣&5️⃣5️⃣



Aliyu ya durkusa da Kai yace" ki yi hakuri mami please"

Ciki tsawa tace" Dalla can rufe min baki, Sam bakason ji laifita , yariya ba tarbiya ko kadan.

Tayaya ma Allah zai Bari mu hada zuri'a da tababaru mutani na? Tir wlh..... Ta sausauta murya ta cigaba" Aliyu ka kwantar da hankali ka, Allah sai ya nunamusu ikonsa, tunda har gori suke ma. Yanzu Ina ita suhaima ?

Yace" tana gida Mami"

" Oho nasan yazun haka tana na tana shaidaci da ta saba ta Tara maza da mata ana ma shaidaici a gida. Wai Aliyu Mai ye ya Sha kan ka ne? Instead of ka gyarata Naga kamar ma tsorata ma kakeji"

Ta kalli Ammi tace" Ayya Ammi mutani ni na a haka suka bar Aliyu kuwa? Dun in zan iya tunawa tun Ranar biki na Essha ko wata ke da suna daya ke Kira kamar zai zauce akata , itama ya manta ta, ko a tambayeshi ma cewa yake bai Santa ba.

Ama ana yata damu da Essha Essha ana daura aureshi da suhaima mukaji shiru, something is fishy, Kai mutani na Basu da kamshi gaskiya"

Aliyu naji Mami ta Kira suna Essha yaji gabashi ya fadi, ya tsaya shiru deep down yanason tuna Mai suna, ama yakasa tunawa kawai ya basar da zance.

Ammi ta kadai Kai tace" ko ma Mai ye akwai Allah, mu da Allah muka dogara"

Aliyu ya Mike yace" zan wuce, zan bin na duba fawaz a hospital"

Mami ta amsa da toh boy sai anjima, ka ci abinci fa?

Ya amsa da inshallah mamina"

Ya fito duk jikishi a sanyaye, Yana isa gaba motoci bodyguards da sauri suka bude mishi kofa ya shiga suka bar gida sai hospital .
Suna isa aka bude mai ya fito, Kai tsaye office din fawaz ya wuce, , ya tardashi ya na hada files, yayi sallama,

fawaz ya amsa yace" a buddy Kai ne da Rana haka?

Aliyu bai amsaba ya Mika mishi suka yi musaba ya nemi guri ya zauna ya lumshe Ido, fawaz ya aje files din.

ya karasa gefeshi yace" yadai buddy? Badai haryanzu kasa magana aranka bane?kayi hakuri ka rugume kaddara, ni na zanbaka Dana na har abada, kullum suna ka yake Kira uncle Mai dimple, ya matukar sabawa da kai.

Buddy kowa na alfahari da Kai, yara da manya, a yau Dina zanfi kowa fariciki ace Kai ne ka raini dana. Please Buddy Kar kasa damuwa aranka"

Aliyu ya dago Yana murmushi yace" Thanks buddy, nagode da kulawarka, ni basan damuwa komai a Raina ba dun nasa haka tawa kadara yake, bara ga dan cikina ba kaga kuwa dole na rugumeshi da hannu bibibbiyu na Kara gode Mai da ya bari ni a haka"

Fawaz yace" hmmm, toh naji buddy, yanzu Mai ke damuka?Naga Yana yika ya canza ne"

Yace" hmmm fawaz kasa dai Kai kadai nake gayama sirri na, kasan kuwa bai wuce matsala na da suhaima ba" ya dafa Kai ya cike da takaici yacigaba " ni Sam suhaima Bata gamsar Dani, yaushe ma ta kullani , sai inhar ta ta bukatar ne ya taso, ni wlh am tired, ni Ina ni a jiki na ba haka abun yake ba, na suhaima ne dai......... .. da sauri fawaz ya sa hannu ya rufe Mai baki

yace" Buddy sirri kune fa ka da ita kayi hakuri, tayaya bara kaji daban baya ka taba Dana musu yariya mutani Essha"

Aliyu yasake ji gabashi ya fadi, ya Bata fuska yace" Wai ku Mai ke damukune? Ku bin ku dameni da zance wata Wai Essha , nace basantaba ku dai na hada ni da ita" ya Mike a fusace zai fita...

Fawaz yayi sauri ya rikoshi yasan buddy nashi da zafi Rai yace" Allah sarki, Koda jima ko ba Dade nasan gaskiya zatayi halinsa, mu dai mu yi iya kokari mu, mu nemanta bamungataba, mu bar ma Allah komai, Addu'a na a kullum shine duk wani mugu da ya asirce zuciya ka Allah ya tona asirisa, munsa komai bayanda mu ka' iya ne"

Aliyu yakara hada fuska yace" mallam dakata , Wai Mai kake nufi da kalama na naka ne? Kasani a duhu"


Fawaz yayi murmushi yace" nasa baza ka ganeba ai, Kar kada mu ace komai nisa jefa kasa zai dawo da Allah muka dogara ba da mutum ba"

Aliyu yakasa gane idan fawaz ya nufa da waena kalamai sai binshi yake da kallo tuhuma, zai magana fawaz ya dakatar dashi yace" Da Allah buddy karike sallah da adduoin, sune makamin mummuni ga duk wani azzalumi dake so cutar dashi"

Aliyu yayi ajiya zuciya yace" toh naji,zauna kasa yanda zakayi Dani, maguguna da nakesha na Mara basamin aiki ko kadan, ka rubuta min strong ones, Buddy nasha lime da Liptop har na gaji, yanzu haka jinake kamar marana zata fashe dauriya kawai nake"

Fawaz ya sauke ajiya zuciya cike da tausayawa yace" kayi hakuri, maganishi kenan ka Kara aure, zai fi maka sauki"

Aliyu yace" what! Aure! Ina bazan iya ba, bazaiyaba" Yana rufe baki idonshi ya sauka akan wani document yaga a rubuta Dr Aisha Ahmad, yaji gabashi ya fadi yace" Doctor Wana fa daga ina? Ya nuna document din dake kan table...

Fawaz yayi murmushi yace" document din Dr Aisha kenan data kware a ko wani fanni daya dagaci mata, har da iri matsaloli iri naka, India su riketa ta na musu aiki, muna bukatar irisu buddy sun dawo gida su yi aiki a gida, shiyasa muka dage aka subar mana ita Dakar dai suka sake mana ita, jibi ma zata dawo Nigeria zata fara aiki a national hospital, abun mamaki ma fa she's just 24, Buddy ya kamata kashirya kaje Kai da suhaima ta dubaku, Buddy Kar ka cire hope kaje gobe zaka fi samu ta hankali a kwance, har suhaima ma zata magace mata ehhhh kagane ai"

Aliyu yayi murmushi yace" Ni fa na cire hope, na bar ma Allah komai, ina ne ba jeba, ama duk results din dayane am infertile , no buddy bari kawai ni ba inda zan Kara zuwa"

Fawaz daji haka baiyi kasa a gwiwa ba yata bashi baki da Karfi gwiwa har Aliyu ya Amince zashi"

"Ama ka shaida wannane na karshe , daga Wana Bara na Kara zuwa wani asibiti ba"

Fawaz yayi Jim jikishi yayi sanyi yasan halishi Sarai da kafiya bayada yaiya yace" eh Buddy, ama da Allah Kar ka gayama suhaima zaka india, ka bari sai ka Gama shiri sai ka gayama ta itama ta shirya"

Ya kalli fawaz fuska tuhuma yace" maiyasa?

Fawaz yace" please kawai dai kayi yanda nace ,da Allah buddy?

Aliyu ya daga kafada yace" badamuwa naji zanyi yanda kace"

Fawaz yace" yawwa tom yanzu zakira asibiti na shirya muku appointment na gani ita doctor din, yanda muka shirya zan kiraka na sanar da Kai, da Allah buddy ka tafi da safe irisu 5 to 6 Dina"
.

Aliyu yayi murmushi ya rugumeshi yace" inshallah, thanks buddy "

" No Haba Dm yiwa kaine" fawaz ya fada Yana murmushi...

Yace" toh ni zantafi, ka gyada madam da boy Dina"

Fawaz yace" inshallah zasuji"

Suka fito fawaz ya rakashi har baki motar , ya shiga aka tada motoci, ciki motar yasa P.A nashi ya shirya mishi flight to India gobe da safe.. ya amsa da toh yallabai ba matsala, suna. isa gida ya tarda suhaima da kaweyenta maza da mata , kamar yanda Mami ta fada kuwa,rawa suke tirkawa kamar a club, sun cika gida da Kara, Aliyu na shiga kowa yakama kanshi, dun suna shakashi sosai, suhaima maganishi tazo ta rugumeshi, kamar soko ya saki mata murmushi tajashi suka haura sama.




New Delhi
*************************

Washe gari, gari na gama wayewa, sadik ne ya sauko daga kan gado baki shi dauke da addu'a bacci, tun baya ya idar da sallah asuba kenan ya kwanta sai yanzu ya farka.. mummy shi yagani tsaye a kanshi tana mishi murmushi, da Hindi yayi sauri yace " *Shubh prabhat* *mummy* "( Ina kwana mummy)

Essha Bata amsaba ta Bata fuska ta Kama kunnuwashi duka biyu har sanda yasa Kara, tace" sau nawa zan gayama kariga gaisuwa da hausa eye? Ina kwana zakace, Ina kwannnnnaaa " taja kwana.. ta turaci take Magana, dun sadik yafita ji Hindi sosai


Yarike kunne yace" *Maaf kijeyega mum* "(sorry mom)

Tace" ba hakuri zaka bani ba, yi gaisuwa Kuma da hausa" ta fada da turanci

Sadik yace" *Aap isse* *kaise bolenga mum* ?( How do you prounance that mum?)

Ta Kara ja kunne tace" wato inama fada yare Hindi na shine ka Kara fada ko? Toh fada Ina kwana zakace, oya fada"

Sadik yayi murmushi yace" En kwanaa mum" ya fadashi a Hindi tune..

Essha batayi niyya dariya ba, sanda ta dara , tana dariya tace" repeat what you just said?


Sadik ya zata yayi gwanita har da gyara murya yace" En Kwanaa mummy"

Essha ta sake fashewa da dariya ta zugureshi a Kai ..

Sadik Yana dariya shima ya Mike harda buga kirji yace" *Chit mat karo*, *main hausa padhunga* *mum*"(mum Kar kidamu zan koyi hausa)

Essha naji ya fadi haka tayi murmushi ta jawo shi gefeta ya zauna da turanci tace" Sadik kafi munkoma kaiya Koda gaisuwa ne Kar granny ka tama ka dariya, learn it fast" Bata gama rufe baki ba sai ga arudhati tashigo da gudu da karami gift box a hannu ta Yana kyalli taisa gaba Sadik taije akan ciyarshi.

Tana murmushi tace" *Janam diwas Mubarak Sadik*(Happy birthday sadik) ta fada Tana boye daya hannuta na hagu.

Essha ta dafa Kai Tace"dole inakoma gida nasha fada da Daddy, gabadaya yaro baiji yareshi ni dai na banu, shame on me nasan duk laifi nane"

Sadik bai amsa Taya murna da Arundh tamishi ba ya Mike yana leka hannuta data boye a baya yace" *woh Kai hai*? (Mai kike boyewa)

Arudh tayi murmushi tajashi gefe tasomishi magana kasa kasa a kunne da yare tace" Sadik yau Holi(Ranar biki kaloli) Kuma mummyka batason yi wasan Holi, shine nakawo colours, here are the colours" ta fitar da leda da ta boye , ta bude leda tacigaba" here are colours, Neela(blue), hara(green), Gulabi(pink) and laal(red) so Sadik let's surprise her with Holi colours "

Suka nufo Essha da hankalita na kan wayata, guri aiki ne aka kirata ta amsa kenan Bata gamaji abunda zasu fada ba taji anzuba mata gari colours a jiki, suka hada baki guri cewa" Happy Holi festival Dr. Essha " suna Gama fadi haka suka fice a guje..

Essha takaici duk yakamata ta Mike ta kalli kanta a mirror taga yanda jikita da fuskata ya baci da colours harda wayata , bama iya gane fuskata taja tsaki, a fusace ta bin bayasu, Tana fitar taji drums ne kawai ke tashi , duk abanta street da gari colours kowa sai bidiri akayi saboda murna Holi.

Ta Kara ja tsaki zata koma ciki kenan ta hango sadik can tsakiy titi, duk jikishi da Rabin fuskarshi yabatashi da colours ga Kuma motar na ta sharoro gudu zatayi kanshi da sauri Essha ta karasa ta jayeshi .

Dai dai lokaci da Aliyu dake cike motar ya zuge glass dayaga yaro da driver shi yakusa kadewa, isowarsu kenan sufito daga Airport, ba hanya a babba titituna duk yayi cikoso, shine suka biyo ta street dinsu Essha.

Aliyu yadaga Kai ya kalli sadik kenan sai ga Arundh tazo da guduta ta Kara watsa musu colours a fuskokisu har ba'iya gane kamanisu.. Aliyu sai binsu yake da kallo gabashi na faduwa yasa hannu zai bude motar, suhaima tayi sauri rike handle din ta tareshi cike da gadara tace" Haba darling ka cika tausayi da yawa, kaga fa yaro ba abunda yasameshi, wasanshi ma yakeyi.

Kuma kasan hali indiyawana Basu da yarda" ta Kara ja murfi motar ta rufe..

Driver yace" yallabai kayi hakuri, sha'ani hanyoyi kenan a Delhi na sai hakuri"

Suhaima taja tsaki tana tsuke fuskar don haushi tafiyar takeji , tafiyar yazomata a bazata bahakatasoba dun Bata shiryaba. ... Aliyu har suka bar layi bai bar kallo su Essha ba, yaso ace ya sauka kodan yagasu, baisan maiyasa ganisu yasashi ji faduwar gaba ba.

Bada jimawaba suka isa haraba asibiti , babba tarba aka musu zuwa office din babba Doctor, su samu tarba cike da girmamawa, Essha kadai ake jira , bakita su karaso, sukira layi kanta duka baya shiga, babba Doctor yaba su hakuri na Rashi zuwa Doctor da zuka zo wurinta, yace shi zai dubasu"
Aliyu ya amsa badamuwa " Babba doctor ya dubasu da kanshi, su Sha gwanje gwanje, suhaima hankalita duk a Tashe yake, tsora ya cika ranta fal, kamar zatayi kuka dun tasa asiri ta ya kusa tonuwa, tarasa sukuni kanta har wani zufa takeyi duk ssnyi Ac daya cika office din, baya likita yagama gwanje gwanje shi yace musu suyi hakuri su dawo gobe , dun karba results duk abunda yanuna zasuyi kokari sumusu aiki akai.

Suhaima taji haka taji wani sanyi aranta, ta shaida ma kanta cewa sai tayi abun da zai sa bara su dawo asibiti na ba gobe, dun dagani likita ya mata kwarjini bai da wasa gashi ya Soma tsufa , suka mike zasu fita kenan, Pooja tashigo rike da files a hannuta, tana gani Aliyu ta ware Ido mamaki da tsoro yasata zubar da files a kasa Hannu ta na Bari, dun mamaki ma kasam magana tayi.

Aliyu yatsaya Yana kallo ikon Allah yanda ta sare musu hanya ta Kuma kafeshi da Ido, baidamu ba don mata dayawa su Saba mishi haka, suhaima ta ja hannushi cike da kishi ta buge Pooja suka fice.

Pooja kuwa kamar ankafata kasan motsi tayi tana kallosu suka fice, suna fita da daddewa ta dawo hayacita tabin bayasu da sauri, Kash Bata ci musu ba, koina ta duba na asibiti Basu , ta tsaya shiru ta kasa gasgata abunda tagani, Mai Kama da Sadik sak, bambaci kawai daya ne shi Wana Babba ne, sadik Kuma yaro ne, ai da sauri ta juya ta koma office din babba Doctor da ya dubasu ta Tara shima bashi har ya fice, ta bugi table, ta kalli gefe daya tana tunani" Aya Wana danagani ba maihafi sadik bane, Kai ima ba papishi bane su hada dangi, Kai let me call doctor" ta ciro waya a pocket din labcoat ta , ta dialing number Essha Yana ta ringing ba'a dauka ba tace" oops na tuna yau birthday din sadik" ta fice da sauri har Tana tuntube ta isa guri motar tajashi zuwa gida, kafi taisa go slow ya tare, kamar ace ta daga Kai ta hango Aliyu ciki motar, Pooja ba hali taje gurisu, dun har suyi u_turn zuwa daya titi, Saba rudewa ta fitar da Kai Tana ta kwala mishi da Suna Sadik , sai binta ake da kallo, Aliyu kam ko harka gabashi yakeyi baimasan tana yi ba saboda akwai da tazara a tsakani su.

Tana kallo motarsu Aliyu ya tashi za subar wuri, da sauri ta bude murfi motar zata fito, watar motar ta Kara Parker a gefeta, ba hali fitar tana kallo motarsu Aliyu ya wuce..Pooja kamar tayi kuka tsabar takaici , hanya su na budewa da sauri tayi u_turn tabi baya su, haryanzu ba sa'a dun Bata cimasuba, jiki a sanyaye taja motar ta zuwa gida...........








❀️Love you guys ❀️


More comment more typing β€οΈβ€οΈπŸ™πŸ™


πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
DOCTOR ESSHA
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

WRITING BY
J Hajara


🌍 *MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ

*M.W.A*

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta. πŸ€™πŸ»
https://www.facebook.com/107980080946102? referrer=whatsa
___________________________


5️⃣6️⃣&5️⃣7️⃣



Pooja na parking ta fito, ta shiga ciki jiki a sanyaye, ciki gida ta tarar da yara da manya. a decorating gida da ballons gabadaya, ta nufi parlor, takara gani wani decorations da ya rudata
Ya yi kyau batasan sanda ta furta wow ba, gaskiya decoration din birthday din ya mata kyau, har wani babba balloon aka sa a sama tsakiyar parlor, Center kuwa table da ke dauke da babba cake na favorite cartoon show na Sadik wato PJ Masks, wow cake din PJ masks ya hadu, Ash color ne jiki cake din, left side din kuwa owlette ne, middle Kuma cat boy , right Kuma gekko,( Don't mind me oooπŸ˜† duka sunayana actors din PJ masks ne, Kar kurikece😁).

Tsakiyar cake din kuwa 7 ne Mai dauke da candle a ciki( Kai gaskiya Mai cake din ta kware) .
Pooja ta share hawaye tana ta shafa cake din a hankali tace" Sadik mummyka na matukar sonka, tana tsoro abunda zai rabaku ne kawai, but very soon nasa komai zai zo mata da sauki" ta Kara bin parlor da kallo decoration din ya gama haduwa, harda number ballon Mai dauke da seven da aka kafashi a tsakiyar aluminum balloons dake gefe parlor, gefe guda Kuma Happy Birthday Sadik akasa da flowers na zangaye da rubutu, ga white bulbs da akasa a gida gabadaya sai ya bada wani yanayi Mai annashiwa, Kai guri birthday yagama haduwa, Pooja ta nemi guri ta zauna tana bin yara da ke ta wasa su da kallo, can Arundh ta shigo da guduta ta Sha wanka tayi kyau gashi kana yasha gyara, Pooja ta kirata tana tambayarta Ina su sadik? Ta Bata amsa da cewa taje Airport dauka brother nata"

Da Hindi tace" mummy surprise birthday ne fa aka hada ma sadik, mummy guri ya mi kyau"

Pooja tayi murmushi tace" nasani saura kifada Mai da baki ki na surutu na"

Arudh ta rufe baki tana dariya...



πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

Essha ne ke tuki a hankali harta iso Airports din, tana fitowa sai waige waige take tana neman Amir, can ta hangoshi zaune ya makala earpience a kunne, sai danne waya yake hankalishi a kwance, Batama ganeshi ba, sanda ta Kara murza Ido da kyau, Amir yazama wani handsome guy, da sauri ta karasa wajashi ta bashi bugu Wasa a kafada tana murmushi. Amir naji a tabashi ya Mike a zabure, Yana ganita yafara zuba murmushi cike da tsokana yace" kaga manya ba, Doctor Essha, sis kiga yanda kikara kyau, wow sis bamaraki da indiyawa ma"

Taja mishi kunne tana murmushi tace" haryanzu baka canza bako, tsokanar na"

Yayi murmushi yace"sis Ina fa zan canza, gaskiya sis we really miss you, daddy yace nafada Miki gobe, gobe na ba sai jibi ba, ki koma gida, kiga zamu koma tare kenan"

Essha daji haka jikita yayi sanyi, ba haka tasoba, ama dole tabin umarni Daddy, tafison ako yaushe ta riga farata mishi..

Amir ya katse mata zance zuci ta da " where is my son? Yau ne birthday shi ko?

Tayi murmushi ta kada Kai ..

Yace" toh Ina yake?

" Kai amir sauri Mai kake, yana gida nannyshi tana shiryashi,muje na daukoshi "

Yayi murmushi yace" to muje sis ko Doctor zance"

Bata bashi amsa ba tayi gaba da jakashi Yana biye da'ita , suna isa baki motar ta kunna motar ta bude ta bude ma Amir ya shiga , itama ta shiga, suna Bari Airports sai gida ummulkulsum nanny sadik, suna zuwa suka tarar sai fitina yake mata, yayi kyau jiki shi sanye da black jeans trouser da jeans jacket itama baki, gashi kana yasha gyara, he looks cute. Yasa nannyshi a gaba Wai sai ta hada mishi Khirr( sweet ne da indiyawa ke hadishi da shinkafa da sugar) ya damaita lallai shi Khirr yakeson ci.

Tace" toh Sadik bara na hada ma"

Basu ma lura da shigowar su Essha ba, sanda takara doka wani sallama , nanny tayi sauri amsawa tana murmushi ta musu barka da zuwa tayi hanya kitchen.
Sadik na daga Kai yaga Uncle Amir tsaye Yana mishi murmushi da gudu yaje ya rugumeshi, Amir ya tsaya yana kalloshi girma yaro yabashi mamaki, Essha gani kallo da amir yake ma Sadik ne yasa ta zargu duk ta rikece a tunanita, yagane wani Abu ne , da sauri ta yi gyara murya kamar Mara gaskiya da turanci Tace

" Sadik yau ga uncle Amir"

Sadik ya Mike daga jiki uncle shi yakali fuskar shi ya na Mai murmushi yace" Namaste uncle"

Amir bai amsaba sai bin sadik yake da kallo, yaro ya burgeshi, Kuma yashiga ranshi sosai. Sadik gani bai amsaba bane sai yasa hannu ya waving a fuskar Amir.


Amir ya dagoshi Yana murmushi yace" my boy yakake?

Sadik bin baki Amir uncle nashi kawai yake da kallo yanda yaga ya furta yakake , shi dai yaji my boy ama yakake dine bai ganeba..


Amir ya Bata fuskar ya kalli Essha yace" badai haryanzu Sadik baiji hausa ba?

Ta gyada mishi Kai.

Yace" lallai sis ke da daddy ne, gobe akwai drama, sis ki duba fa , ko yakake din ma baisani ba, wlh muna da ja aiki.

Shifa fa yaro fa, da yare da yatashi dashi nefa yake rikewa har girma, yanzu inmukoma Nigeria, misali ya shiga mix din yara da basaji turanci balle asa wani yare Hindi, kiga Sam basai ji dadi har ya sakeba, gobe Allah

Please Login or Register in order to submit comment