Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace" daddy Ina Essha? Daddy Ina ku kaita? Duk ya birkece yakasa natsuwa sai tambaya su Essha yake...

Mamaki yahana Tycoon amsawa shima maimatar suna yakeyi "Essha Kuma? Ya juya gasu Ammi yace" wacece Essha kuma?ai'na take ?

Ammi ta girgiza Kai tace" mufa bamusan wata Essha ba, kila dai su Hafiz za su santa"

Hafiz yadaga hannu Alama basusan da wata Essha ba..

Haydar yace" Ammi bamu taba ji yakira maisuna na Nan baa"

Tycoon ya kalli Aliyu da duk ya birkece suna Essha kawai yake furtawa , ya dafashi yace" Aliyu mune fa, ur family, here is ur mom's ur siblings, ur friends and ur granny no one is bearing essha here, first of all wacece Essha?

Aliyu ya tsume fuska ya tsay ya yana kallasu shiru ya rasa wani amsa zai basu, a ranshi yace" waton kenan daddyshi a daji na yabar mishi Essha, No she's hurt,dad u can do that....yayi yikuri zai sauka,da sauri fawaz ya rikeshi yace" buddy kayi hakuri kayi a hankali fa, u re sick"

Ya kalli fawaz dake magana ya Soma hawaye yace" Essha fa, badai aguri ku ka bar min ita ba,ya daka tsawa sanda daki ya amsa da amo muryashi yace" Ina Essha na ,she's hurt, tana bukatar taimokona "

Tycoon yace" calm down son, Essha Kuma? Ai'na take Wai gayamin?

Aliyu ya fara sambatu Yana nuna both side nashi yace" dad she was here with me, tana bukatar taimokona daddy, maiyasa baku daukotaba ? Daddy ni zanje ,I will go and bring her,she's my wife " ya Mike ya balle drip dake hannushi, carnular kadai yabari, jini sai rushing yake daga hannushi Yana diga a kasa, zai balle sauran carnular dake lilo a hannushi, tycoon da uncle bello suka rikeshi suka zaunar dashi ama tirjewa yakeyi Yana kokari mikewa, ga Kuma jini nata zuba a hannushi.. fawaz da sauri ya dauko plasta da cotton wool yarike hannu Aliyu dake zubar da jini ya dressing hannu.. ya kalleshi gaskiya ya tausaya mishi, dun tunda suke da Aliyu baitaba shiga ciki wanan haliba..aranshi yace" ayya ba wani Abu aka bashi yasha dagaske ba, har Yana Kira masu suna da Basu taba Koda mu'amalane da Mai iritaba..

Aliyu ya kalli fawaz da daddy shi duk yazama abun tausayi yace" please daddy ku sakeni na je na dauko matata, tana bukatar taimakon, Kar su cutar da ita please daddy ka taimakeni 😭..





Comment & share πŸ₯°πŸ˜πŸ™



πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
DOCTOR ESSHA
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

WRITING BY
J Hajara

🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoya ta.πŸ€™πŸ»
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_______________________


3️⃣1️⃣&3️⃣2️⃣

Kowa sai bin Aliyu suke da kallo mamaki, yadda yake Kira Essha na dai a matsayi matashi, Ammi abun ya fara Bata tsoro da mamaki" ayya Aliyu kwaya na da akace yasha bai taba minshi kwakwalwa ba ko, dun ta sa yarota, tun tasowarshi soyaya bai dameshi ba, balle wata mace daban da har ya damin kanshi haka"


Mami ta Mike ta shafa kanshi tace" boy Kaine kuwa, u r hurting yourself ka kasa natsuwa, da Kira wata daban da mu bamu Santanba... talk to me mana boy, boy Dina jarumi ne baya ragonta, Mai yasa ka....Bata karasaba ta fashe da kuka...

Aliyu da sauri ya rugume ta shima haweye yakeyi yace" Mami no, please don't cry, sshs karkiyi kuka, Essha ta ba wata daban bane Zaki santa Mami, she's my preety, my destiny, my wife"

Yasaketa Yana ta musu describing yanayi Essha Yana sambatu , ya rike hannu tycoon " daddy let's go zo muje mu dauko ta, Kar wani abun ya samaita, kaji dad zo muje"

Duk suka tsaya suna kalloshi cike da mamaki don aik aika Aliyu yafara Basu tsoro, yi yake kamar ya zare, kowa da yanda yake aiyana abun a zuciya, su Suleiman sufi kowa mamaki" yau Aliyu ne ke sambatu akan mace, Wanda su Basu santaba..

Ummi tace" eya lamari yarona, ba accident yayi a hanya ya boye suka shafeshi bako, sai Kira suna da kwantace mace yakeyi, duk kwantace na fa Mai suffar aljanu ce, gashi har baya, fara da ita, idonta kaza Wana kaza, Kuma Yana kirata a matsayi matashi, eya ba aureshi tayi ba ta shanye manashi?!!

Duk suka Amince da maganar ummi.... Aliyu yasa ihu kamar ba shi ba yarike hannu Ammi yace" No*3 Essha na ba aljana bace, mutum ce, Ammi ki yardadani... Ya rike Idrees Yana girgiza shi yace" Bro kaima ka yarda kenan cewa Essha na aljanace, a'a ya kadan kai" Bro please Kar ka yarda da batu ummi please.... Idrees rasa baki magana yayi Yana binshi kawai da ido yaje...

Yaje gaban tycoon yace" Daddy zo na kaika ka ganta, kaji dad don't say no please ka biyoni, please dad my heart is burning, in bagantaba zuciya na tarwasewa zaiyi , please dad ka ceceni" ya kife Kai a kirji tycoon yana kuka Mai cike da kunci,

Tycoon yace" calm down nayarda zan bika kanuna mi ita, if dat is d solution"
Yadaga da sauri Yana murmushi yace" dagaske dad" Tycoon ya lumshe minshi idon sanan yace" amafa zaka Bari sai gobe, kaga yanzu baka da lafiya"

ya Bata fuska yace" no daddy dat place it's not safe, za ta cutu aguri, Kuma dad na warke muje kawai"

Ya jijiga Kai yace" son yanzu dare fa yasomayi"

Ya shagwabe fuska" daddy muje yanzu if not za'a cutar da ita"

" Toh Aliyu muje"

ya rugumeshi yace" nagode dad"

Tycoon yace" u r welcome boy, can do anything for you....

Ummi matsifa takeyi wai anki yarda da zanceta, gashi yanzu ya biye mishi har da wani zuwa a dubata tace" wlh Nima sai na binsu Naga wanan ya Mai suffar aljanar na inhar dagaske ke ne"

Tycoon yasa aka Kira doctor yamishi bayani komai, doctor yace" ba matsala sir sai ku dawo"

Duk family su yake za su bisu, fawaz, Hafiz haydar Allah Allah suke suga yariya da ta ruda musu da aboki haka.. ajere motoci kuda takwas, manya manya Jeep ne, Aliyu dakanshi yake driving ,ayi ayi driver ya yi driving yaki, yafadi suna anguwar yace" baisaniba"

Shidai kawai abinda yasani zai kaisu guri Essha, su hudu ne a ciki motar daya, tycoon, mami, Ammi da oga boss din dake driving, saura Kuma su fawaz, su ummi siyama da su Idrees sai guda biyu Kuma bodyguards ne ke biye dasu..

Aliyu sai sharara gudu kawai yake , Mami suyi shiru suna kallo iko Allah, har su fara fita gari, da'a Ammi ta tambeya shi" Aliyu ba'akai bane?

sai yace " mun kusa"

Su matukar tsorata dasu ka ga Aliyu yayi corner ta hanya daji, ama duk suka zuba mishi na mujuya ba Wanda ya' iya cemishi ko da ka'ala.. har sanda ya tsayar da motar a ciki tsakiyar daji, ya Parker ya fito yace" dad, Ammi Mami kifito nane , duk suka bude suka fito..

Sofia da rahma su tsorata daji yanda daji yake motsi, don ba alamu wani Dan Adam na rayuwa a ciki, Kara tsutsaye ne kawai da macizai da abubuwa da baza arasaba ke tashi, gashi yayi dulum dulum..

Ai da gudu suka rugume Ammi, su ka kakemeta..

Ummi da siyama sai Bari..

Ammi tace" Auzibillahi, Aliyu Ina ka kawo mu Kuma?

Tycoon sai bin daji yake da kallo, Yana mamaki yanda Aliyu yasan daji, don daji Mai hatsari ne ba kowa bane keshiga, sai ka shirya kanka...

Aliyu yayi murmushi" yace Ammi Essha na ana take, tana can a bukka kuzo muje"

Wa?!!! Hafiz da Isa har suna hada baki.. Hafiz yace" gaskiya badaniba" da gudu suka shiga motar suka rufe ..don daji ya matukar Basu tsoro..

Isa yace " gaskiya batun hajiya gaskiya ne da tace Yaya da aljana yayi gamo"

Suleiman don tu fitowar daga motar jikishi ke Bari saban tsorata yace" buddy kana nufi kenan ana ku ka hadu? Yayi tambaya har muryashi na rawa.. Aliyu ya gada Kai alama eh Yana murmushi...

Suleiman yace" lallai da sake, Kai badaniba" ya make a baya Aliyu yace" Buddy su San ka baza su cutar da mu ba"

Aliyu ya Bata fuska yace" Mai kake nufi??

Yace" su suke gani mu ba mu muke gani su ba, shiyasa na boye a baya ka Koda wani abun zai faru, kaga su Saba da Kai , Kuma na ga baka tsorata ba" ya Kara noke fuska a baya Aliyu..

Siyama tace" gaskiya shi ne Yaya, tsoro na keji da Allah kuzo mu bar na guri tunkafi dare yayi ko ummi?

" Eh mana, da Allah umaru kuzo mubar daji na tunda wuri, gashi ma ba ko haske... Mami kam kasa magana tayi..


Tycoon yace" ku natsu mana aduba, Bari a kunna haske". Ya umarci driver's da su Kuna fitilu motoci.. duka Jeep takwas a kunna fitilolusu, farare kal kal, ya haske guri gabadaya, ya kalli Aliyu da duk jikishi yagama sanyi yace" son Ina take?

"Daddy a can ne, zo mu karasa " ya furta murya a sanyaye... Ya jasu suka Kara sa dai dai spot din da abun ya faru, ama ba Alama wata bukka a guri, kamar ba abunda aka taba ginawa a gun..

Aliyu ya rikice ya daburce sai zangaya wuri yake Yana" wlh daddy ana ne, daddy bataa, su dauke ta, daddy ka taimakeni 😭 ummi Mami Ammi wlh ana Essha take, ana aka daura Mana aure, my heart is bleeding ya rike sai tin zuciya shi, ya saki ya da fe kansa da hannu bibibbiyu Yana gani komai da ke daji Yana juya Masa, numfashi sama sama ya ke fita, a hankali ganishi yayi rauni , idanuwansa suka rufe ruf ruf Nan ya sulale ya fadi kasa....

Da sauri wani guard ya sukeceshi , tycoon dakeciki tashi hankali da gani hali da Aliyu yake ciki murya na rawa yace" sanshi a motar Abuja zamu koma, da sauri suka tada motoci, Idrees ya zauna a mazauni driver Yana driving dinsu Ammi, hankali su duk a tashe yake, Airport suka wuce, ambulance aka kira da sauri akasa ma Aliyu abun numfashi akasan Masa don ceto rayuwarshi..........





Love ur comments guysπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°



Comment shareπŸ₯°πŸ˜ πŸ™



πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
DOCTOR ESSHA
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

WRITING BY
J Hajara

🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ


Kungiya d'aya tamkar da dubu.masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.πŸ€™πŸ»
https://www.facebook.com/107980080946102? referrer=whatsa
_______________________




3️⃣3️⃣&3️⃣4️⃣


Baya jirgi ya daga, suka sauka a Abuja, motar asibiti fawaz yakira suka duguma sai asibiti, family din tycoon suga tashi hankali dun Dakar aka ceton Rai Aliyu, kwana shi nagaba, a ICU ROOM aka ijeshi, bamai shiga sai dai su hangoshi ta window glass din kofar daki, duk ya rame a lokaci daya, yakara haske fayau sai hanci...

Fawaz ya fito Yana sharce gumi duk jikishi yayi sanyi yace" daddy kuje gida mu zamu kuladashi inshallah, kusamu ku huta kodan lafiya ka"

Idrees yadafashi yace" daddy you always encourage us da muriga juriya baikamata ace kanuna kasawaka ba, Yaya zai samu sauki inshallah,.kayi hakuri muje gida ka huta, kaga yadda Yan news suka taru a baki gate, nasan damuka zasuyi"

Tycoon ya gyada Kai Yana haweye yace" muje ku"

Mami tace zata kwana ita..

Siyama tace" haba Mami kiyi hakuri Yaya ba'abunda. Zai sameishi , gasu yaya haydar zasu kuladashi"

Mami Taki fiti fiti, Dakar siyama da Isa suka convienceing nata tabisu, su Rahman har su fara bacci.. suna kaiwa gida acikisu babu Wanda ya iya bacci, Tycoon kwana sallah yayi Yana roko ubangiji ya fitar da danshi daga ciki Wana hali, hk ma Ammi da Mami

*********************
Daddy karami karfe 6:00pm cib suka isa gari lafia duk da gudu da yaketa sharewa, tun a hanya hajiya ke tayi dashi ya tsaya a kaita wani asibiti ama yaki..

Suna isa direct DASH(Dalhatu specialist Hospital) babba asibiti gari , Yana karasawa ya Parker motar aciki haraba asibiti , ya daukota, hajiya ta fito tayi office din likita, Babba likita asibiti Dr. Abass ne mahaifi bestie (sumaiya) da gagawa yasa nurses suka fito da gado tura Mara aka kaita ciki ... Dr Abbas sai tambaya daddy karami yake maiyasa maita?

Daddy karami da sai sharce gumi yake ya girgiza Kai yace" likita ka ceto rayuwa ta da Allah, Kar wani abun yasameta, zanje na sanar ma iyeyeta da Allah likita"

Dr Abbas ya girgiza Kai ciki tausayi ya shige daki da aka kaita, tashi hankali sosai ya ziryace shi gani hali da take ciki, ya Raya aranshi Aya ba fyade aka mataba... Ya Kira nurses Nan suka dafa masa, suna kokari tsayar da jini dake fita ta kasanta" ya Allah!! Wani Rashi Imani ne haka? Ya fada ciki tsoro gani hali da yariya ta ke ciki...

Fitowa yayi baya suyi nasara tsayar da jini dake zuba a kasata, Allah yasa ma tana da isashe jini imbahakaba har Kari jini sai amata(Aliyu yayi babba aiki😁) su sa mata leda ruwa da allurori ya Kuma Basu umarni da suyi mata dinki a jikita...

A can gidasu Essha kuwa, family din su shiga tashi hankali, na Rashi zuwa su Essha, tayi, Dan tun two suke expecting dawuwarsu, ama gashi har magriba tayi Basu karasoba...

Daddy Essha sai ziriya yakeyi a ciki parlour rike da waya a hannushi, mummy ne gefeshi zaune kan dogo sofa din parlor ita da anty zainab , ta zuba tagumi ita Sam hankali ta bai kwanta ba tafi kowa daga hankali, su amir su na islamiya.

Daddy Yana ta trying duka lambobisu baya shiga, ya Kira Big mum can k.d ta shaida mishi cewa tun safe suka tashi, Killa hold up ne ya rikesu a hanya...

Anty zainab tace" Alhaji ka kwantar da hankali ka za su karaso, kila haka dine, kasa yanayi hanya"

Mummy ta yarfa hannu kamar Mai shiri kuka tace" haba mana, go slow tun safe ace har yanzu Kuma ana trying lambobisu baya shiga, Wana wani iri go slow tun safe haryanzu, Kai ni gaskiya hankali na bai kwanta ba"

Aina'u tace" mummy sha'ani network ne Kar ki daga hankali ki inshallah zasu karaso ciki koshi lafiya" Tana rufe baki suka ji horn din motar , an bude gate, da sauri suka fito har suna rige rige.. Daddy da ya rigesu fita yaga Ashe motar su amir ne sun dawo daga islamiya, suna fitowa daga motar, mufeedat ta nufi daddysu tace" daddy sis Essha ta dawo?

Ya girgiza Kai yace" autar mama don't worry kinji sis Essha suna zuwa " ya fada Yana shafa mata kai...

Amir yace" daddy datzu da muka fita break na Kira layi sis Essha Yana ringing Bata daukaba"

mummy ta zabura ta nufeshi tace" layi ya shiga? Kara trying amir". Ya fida waya daga ciki aljihu ya dialing number Yana ringing ama ba'adaukaba..

Tace" Kara trying na daddy karami ko na hajiya" duka layi in yakira Yana ringing ama ba'adauka..

Anty zainab tace" hmm Allah yasa dai lafiya suke... Bata Gama rufe baki ba sukaji horn din motar, atare duksukayi ajiya zuciya... Daddy yace" gasunna ma su karaso"

Gate man na bude gate, daddy karami ya shigo da motar ko Gama parking baiyiba ya sauko a firgice Yana haweye ya nufi Daddy.. suka binshi da kallo mamaki gabasu na faduwa...

Daddy yace" lafiya ya na gaka a haka Ina saurane? Jini Maine Kuma a jikika?

Daddy karami duk ya firgice sai sharce haweye yakeyi yace" Essha, Essha .... Mummy da Daddy dam sukaji gabasu ya fadi..

Daddy yace" Ina Essha din, maiye samaita? Accident kukayi komai ya jera mishi tamboyoyi a take har jikishi na rawa..

Daddy k. Yace" tana asibiti, ku zomuje, ku yafeni nakasa rike amana, kunyafe nakasa Kare Essha""

Mummy taji kanta na juyawa tace" Wai Mai kake nufi ne? Wani asibiti ? Maiyesameta? Ta fada Tana haweye...

Yace" ku zomuje ku zomuje" mummy ko hijab Bata dauka ba, dogo rigane a jikita sai mayafishi ciki tashi hankali suka dunguma sai asibiti... Hajiya suka samu a baki kofa ba'abunda takeyi sai kuka, har da shesheka da sauri mummy ta nufeta tana hawaye ta dafata murya na rawa tace" Essha na ta mutu ko? Hajiya ta girgiza Kai.. mummy tasa kuwa kamar ta zare tace" ki gayamin gaskiya Kar ki boyemin da Allah hajiya, ta mutu ko? Kamar zautaciya takeyi...

Daddy ya janyeta yace" ya'isa "

" No ka kalleni Ina Essha , Ina take?

Hajiya bataiya cewa komai ba tayi daki da aka kwantar da Essha da hanzari suka bi bayata, suna shiga suka tarda Essha kwance hannu da drip, da mugu sauri mummy ta karasa wajenta tana girgiza ta da dukkani karfita, ama Essha ko gezau, Kara tasaki Mai karfi Wanda amonsa yacika daki da suke.. "ESSHA" ta fada Tana Kara girgiza ta, ciki tashi hankali idon ta ya sauka aka kafata , taga layi jini nabin kafata, ta Kara kallo da kyau, na kafa damata har yasoma bushewa, tasa Kara a karo na biyu, ta Mike ta nufi saiti kafa ta daga dogo riga ta leka,Nan take ta runtse ido, kirjita ne ya shiga bugawa da Karfi gaske, saitin zuciyarta na fat-fat Kamar zata yi tsalle ta fito , ta Soma furta " inalilahi waina ilaihi raju'un, inalilahi waina ilaihi raju'un" a hankali ta sulale a wajen ta zauna ta rike kai.. tana kallo Essha tana hawaye...

Daki yayi tsit bakiji komai sai sautin kuka mummy da hajiya.. Daddy yagamy rudewa yakasan fahimtar komai dake faruwa,.

Ya kalli daddy karami bakishi na rawa yace" Wai mai ke faruwa ne? Ku gayamin ku barni a duhu. Maiyesameta?

Mummy Dakar ta ' iya bude baki tace" Abba Essha, Essha was raped, fyade aka mata " ta sake fashewa da kuka...

Daddy kansa ya dafa, ji yake kamar zai balle daga madaukarsa, bugun zuciyarsa ya tsanata wajan bugawa.. ya nufi hajiya da kanta na kasa sai shesheka takeyi yace" hajiya ki gayamin zance na Dana keji karya ne, ki gayamin gaskiya "

Hajiya na kuka ta kwashe duk abunda ya faru tundaga farko haduwarsu da kungiya har zuwa su asibiti ...
Daddy da mummy su matukar firgita daji wanan labari ... Haweye ke sauka a idon daddy kamar an balle famfo yace" inalilahi waina ilaihi raju'un Allahum arjini fi musibati*2....

Tunda hajiya ke bada labari anty zainab ke haweye take haweye, Bata taba jin labari iri haka Mai firgirtawa da abun al'ajabi ya taba faruwa ba ko da a film ne ko littafi ....

Daddy ya rike saitin zuciyarshi Yana girgiza Kai yace " Essha Dina ne aka aurar da ita, ga yaro da ba'asanshiba , ba'asan asalinsa ba, Allah Mai iko ya share haweye " alhamdullila tun da har aka daura aure, ba fasikaci suka aikata ba, haka ma yazo da sauki, aure alkhari ne, toh maiyasa kuka bar shi a can baku daukoshi ba?

Daddy karami yace" mun rikece ne da gani hali da Essha take ciki, shiyasa na Manta da batun yaro" dai dai lokaci Doctor Abbas ya shigo daki ya tardasu fuskokisu cike yake da haweye...ya Mika ma daddy Essha hannu sukayi musabaha..

Doctor Abbas yace" kuyi hakuri zata farka, firgice da tsoro ne ya hadasa mata Suma,ya kalli daddy" inason gani ka a office na..

Daddy yakasa magana ya bin baya Doctor Abbas zuwa office nashi , baya su zauna .. Dr .Abbas ya kalli daddy ynda ya shiga damuwa, ya kadan kai" Yaya ku ka Bari haka ya faru da ita? Dr. Abbas ya Mike a fusace yanuna daddy da yatsa yace" ga abunda na ke fadama kenan akullum inmu hadu, kadaina sake ma yaraka da yawa, kullum Kai burika ka, ka farata musu ne baka tsawata musu ba, baya kuma kasa hali yaran zamani na, Wana ya'isa ya zama ishara a gareka, yawa bama yaraka freedom shi ya janyo aka ma Essha fyade . A matsayi na na makwabcika nake gayama gaskiya " Daddy ya bude baki sheke Yana kallosa har yagama magana , mamaki zance sa ya hanashi bashi amsa.. bai San asali magana shine har ya ke hukuci yake Daura minshi laifi.. toh Wai ma shin maiye aibu wanan duk ka sake ma yaraka, wanan ai sunnah ne na Ma'aiki (S.A.W.) ka riga farata ma iyalaka, ka Dora musu da tarbiya nagari, takura, matsi ko iyaye suriga hade ma yarasu gira shine zai sa yaro ya natsu no yawaici ma shine ke cefa yara ciki wani hali( kaluballe agaremu iyaye).

Daddy aranshi yace" wani amsa yaka mata ya ba bawa Allah na? Kai na ma fasa gayamishi abunda yafaru" baice uffan ba ya Mike yabar office din fuska cike da damuwa..
Yana fita Dr Abbas ya tabe baki yace" tundama iriku bakusan gaskiya, kullum Kuna tsakiyar yaraku Kuna washe musu hakora Wai shi so😲, Kaya sai Wanda suka sa, Tayays bara'aji sha'awa yi musu fyade ba, toh kawace da yanta ma na kusan rabasu very soon "ya kada hannu..

Daddy na fita magaganu Dr Abbas ne ke masa yawo akai, sai tambayar kansa yake" ayya Dr Abbas ne kuwa amintace makwabcishi, shine yake gayaminshi haka, bai tayashi jaje ba, bai Kuma San kan magana ba shine ya yake hukuci, hmmm yayi ajiya zuciya, Yana gode ma Allah a yanda kaddara nashi yariya yanzo a haka , da aure akanta komai ya faru.. yama kanshi alkawari baya family shi bawanda zai gayama ko da kuwa abokaina shi ne, dun yasa tabas bawanda zai yarda da zanceshi, ya bar ma Allah komai, ya share haweye Mai dumi da suka zubo mishi......





Ur comment is my strength 😎πŸ₯°






Comment &shareπŸ₯°πŸ˜πŸ˜˜πŸ™


πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
DOCTOR ESSHA
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ

WRITING BY
J Hajara

🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION πŸ“š πŸ–ŠοΈ

Kungiya d'aya tamkar da dubu. masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.πŸ€™πŸ»
https://www.facebook.com/107980946102? referrer=whatsa
____________________



3️⃣5️⃣&3️⃣6️⃣

Ya share haweye Mai dumi da suka zubo mishi, ya nufi daki da aka kwantar da Essha,Yana kaiwa baki kofar suka ci karo da daddy karami da haryanzu kuka yake, daddy ya kalleshi duk ya hargizai yajashi gefe suka zauna a kujeru da aka jera agefe dakuna. Baya su zauna. Daddy ya kalleshi yayi ajiya zuciya yace" yakamata ka daina kuka na haka duk abunda yasamu bawa mukadarine daga Allah, yanzu kawai munjira farkawata"

"Yaya kunya hada Id......

Daddy ya daga mishi hannu yace" ya'isa haka, Kar ka Manta fa duk abunda yasamu bawa haka Allah ya rubuta mishi, ni musulmi ne kaima haka, Kuma duk muyi Imani da kaddara, Ina Kara godema Allah ba keta mata haddi sukayi ba, aure suka hada rokona ana shine Allah yasa ya zamto alkhari, idan da rabo za su hadu tom, dun ace matar mutum kabarisa, fatana Allah yaba Essha lafiya da juriya"

Daddy k ya amsa da ameen yaji dadi kalamai daddy, sukara kwantar mishi da hankali, suna zaune suyi jungum sanda aka Kira sallah magarib suka Mike zuwa masalaci dake ciki asibiti.

Har akayi isha'i, Essha Bata farka ba, mummy na makale a gefeta , wata likita daban tazo takara dubata ta tabatar musu cewa suyi na bada jimawa ba zata farka.Dare ya tsala dukasu ba bu Wanda ya runtsa mummy da Daddy, hajiya da daddy k tun baya isha'i, Bala driver ya wuce dasu gida dun su huta.. Essha kuwa can tsarka dare ta farka batama gane kosu wa ye akanta sai kuka take tana fisge fisge tana magaganu" hajiya kuce mishi ya sakeni wlh basan aure, na tsaneshi, mugu ne, hajiya ki taimakeni"

Daddy da gudu yaje yakira likita dake da duty a daren yana zuwa ya mata allura bacci, mummy kam tayi kuka da Bata tabayishiba..

Washe gari sai misali 1:30pm na Rana Essha ta farka." Alhamdullila ta farka" maganar nurse din data zo dubanta ta ratsa dodo kunnuwansu haka yasasu juyowa a hautsune Dan gani zahiri abun da kunnuwasu suka jiye musu" Tabbas ta farka" mummy ta fada lokaci da idanuwansu suka hade waje daya, da sauri ta karasa wajenta tana " Essha daddy" ta fada Tana kokari ruko hannu ta, Essha ta Mike da ga kwance da sauri ta rugume mummy ta, ta fashe da wani kuka Mai kashe jiki Mai sauraro, mummy ma haweye takeyi tana shafa kwantace gashi

Please Login or Register in order to submit comment